ABOKAI KALA HUDU NE

Hakika kowanne mutum da Allah ya bama daukaka ko daraja awani fanni na rayuwa, dole zai samu masoya kala-kala. Kamar yadda kuma zai iya samun Makiya da Mahassada nau'i daban daban.


1. Akwai wanda yake da'awar cewa shi Masoyinka ne. Amma ba zai tashi matsowa jikinka ko kuma nuna maka soyayya ba, sai lokacin da yaga wata nasara ta samu gareka. Amma idan kishiyar nasara (wato Asara) ta samu, ba zaka ganshi ba. Dama ni'imar ce ta kawoshi.

- Wannan ba abokin kirki bane, ba masoyin gaske bane. Kayi hankali dashi.

2. Akwai wanda yana nan tare dakai ko yaushe, amma duk abinda kasa agaba sai ya tayaka kuyi. Ba ya yi maka musu, ko gyara acikin lamarinka koda ya ganka akan kuskure haka zai tayaka kuyi.

- Wannan masoyi ne amma yana da rauni acikin soyayyarsa. Kayi hankali dashi.

3. Akwai wanda yana tare dakai ko yaushe amma idan yaga abin alkhairi tare dakai sai ya binne labarin. Idan kuma yaga mummunan abu tare dakai sai ya watsa ma duniya. Ta wajensa ake samun Miyagun labarai game dakai.

- Wannan Makiri ne, Mahassadi ne. Ka nisanceshi tun kafin yayi maka illa. Idan kuma ba zai yiwu ka nisanceshi ba, to lallai ne ka rika boye masa sirrinka.

4. Akwai masoyin da ko yaushe yana tare dakai azuciyarsa ko kuma afili. (Koda ba ya yi maka zakin kalamai).

Duk lokacin da ya ganka akan alkhairi sai ya taimakeka kuyi. Idan kuma ya ganka akan kuskure sai ya gyara maka koda ranka ba yaso.

- Wannan shine masoyi na gaskiya. Ka rikeshi da kyau domin irinsa suna da wahalar samu.

Hakika Allah yana cewa:

"MASOYA AWANNAN RANAR (WATO ALKIYAMAH) SASHENSU ABOKAN GABA NE GA SASHE. SAI DAI MASU TSORON ALLAH".

Wato aranar Alqiyamah abokai zasu zamanto masu Qin gamuwa da abokansu, saboda tsoron ko zasuyi jayayya dasu agaban Allah.

Amma wadanda suka gina abotarsu bisa gaskiya da rikon amanar juna da tsoron Allah, sune zasu rabauta.

Zasu zama sanadiyyar samun rahama ga junansu (Kamar yadda hadisai da dama suka tabbatar).

Ya Allah ka hadamu da mutanen kirki masu Qaunarka, kuma wadanda Soyayyarmu dasu zata amfanemu awajenka.

Ka rabamu da miyagun abokai na fili da boye. Ka kiyayemu daga sharrinsu da makircinsu. Ameeen.

Wannan sadaukarwa ce ga dukkan abokai da Masoya.

Comments