Jin Dadin Aure
Babban abin da mai son jin dadin aure ya kamata ya lura da shi shi ne:
Mace ta gari, ita za ta iya zama masa zinariya, duk lokacin da ta yi datti in aka wanke sai qyalqyalinta ya fito sarari.
Amma aure don kyau (wanda shi muke yi yanzu) kamar baqin qarfe ne da aka shafa masa kumfar zinare, yana daukan ido da ban sha'awa, da zarar ka yi amfani da shi Daya, Biyu qyalqyalin zai fita munin kuma ya bayyana, daganan ba sauran sha'awa kuma, galibi qyalqyal-banza din nan su maza suka fi so.
Shi ya sa mai haja yake tallata musu don samun kasuwa, maganar gaskiya duk wani dan kasuwa riba yake nema.
Mace ta gari za a same ta da:
1) KAMEWA: Daga duk wani abu da zai sosa wa maigidan ta rai, a kanta ne ko gidansa ko abincinsa da sauransu.
2) GASKIYA: In za ta yi magana ba ta qarya, domin samun riqe gidan gaba daya.
3) ZA'BIN MIJINTA A KANTA: Tana buqatar abu amma in baya so za ta barshi, ko ta yi don shi yana so koda kuwa ba ta so.
4) AMINCEWA: Duk abin da yake so ta yi ta amince, don yarda da cewa ba zai halakar da ita ba, tana qaunarsa.
5) TAWALU'U: Ta qanqar da kai gare shi koda kuwa tana da ilimi, arziqi da shekaru sama da shi, kamar dai Khadeejah RA da Annabi (S.A.W)
6) NATSUWA: Kar ta riqa tuno abubuwan da suka gabata, kuma ta dena tsoron masu zuwa.
7) KUNYA: Ta riqa jin kunya, wannan ado ne gare ta, masamman in tana tare da mijinta a cikin jama'a, wannan zai qara masa qaunarta.
8) KWANCIYAR HANKALI: Mantawa da matsalolin rayuwa da qoqarin tura farin ciki ga mai gida koda suna cikin matsala.
9) GODIYA: Duk abin da ya zo da shi a nuna masa jin dadin zuwa da shi komai girmansa komai qanqantarsa.
10) HAQURI: A kan duk abin da zai bayyana daga miji (wannan ne kawai muka dauka alhali suna da yawa)
11) TSAYUWA QYAM: A wajen bauta da qarfafa mijin da 'yan su
12) AMANA: Ta zama mai amana, kar ta yarda maigidan ta ya ga ha'incinta koda kuwa sau Daya ne, ta riqa gaya masa abin da za ta yi domin maganin shedan.
13) CIKA ALQAWARI: Yana Daya daga adon mace da namiji.
14) TSORON ALLAH: A duk abin da za ta yi.
15) DANNE ZUCIYA: Yayin da aka baqanta mata rai.
Wadannan abubuwa guda 15 su suke nuna mace ko miji nagari, kada ka riqa binciken qyalqyal banza, ke ma ki dai na kallon kudi ki duba rayuwarki idan kin shiga gidansa, komai kudinsa in ba kwanciyar hankali ba za ki ji dadinsu ba.
Na yi wani nazari sai na gano iyayenmu na baya sun fi mu sanin aure da matsayinsa, wannan ya sa in za a yi wa namiji aure murna da farin ciki yake dabaibaye shi, har ana buga misali cewa:
"Wace fara'a kake yi haka kamar wanda ya yi amarya?"
Ita kuwa amaryar kuka take yi tun da 'yan kwanaki kafin ranar auren, sabo da zullumin irin rabuwa da iyaye da kuma tarin aikace-aikacen da za su hau kanta.
Yau sai muka sami kanmu angon zullumin sha'anin gida duk sai ya dabaibaye shi har ka ji ana buga misali:
"Tunanin me kake yi haka kamar wani mai mata?"
Ita kuwa murna ta cika ta har ji take kamar ta kai kanta, duk wani party za ka ganta cikin fara'a, ita da kanta take raba katin gayyata.
Gaskiya akwai buqatar gyara, mace ta gari aikinta Daya ne ga mijinta mai rassa da yawa, wato shigar da farin ciki a zuciyarsa ta duk hanyoyin da suka halasta,
Don haka bai yiwuwa a sami mace ta qwarai sai wace ta hada kyau na 6oye da na sarari, ta ba da rayuwarta ga Allah sannan hidimar mijinta, ita ba mijin take fara kallo ba, a'a, wanda ya saka ta ta bi shi wato Allah (SWT).
Babban abin da ke jawo qauna kyawun 6oye da na sarari.
Kyawun 6oye shi ne:
Tsoron Allah, girmama iyayen miji da daukansu a matsayin mijin, son 'yan uwansa, kunya, ibada da rashin rowa ga 'yan uwan miji.
Kyawun sarari kuwa:
Iya kwalliya, sa tozali, abin hannu, zobe da sutura mai kyau, lalle da turare kuwa suna da sirrorinsa na shigar da qauna da daga sha'awar miji da janyo hankalinsa da qarfi da matso da shi kusa.
Wannan ya sa muslunci nan take ya bayyana rufe qafa a sarari a maimakon fuskar da ake tsammanin ita ke fitar da kyawun mace, ya hana mace saka turare ta fita, har Annabi ya sifanta mai fesa turare ta fita da MAZINACIYA!
Abin da zai ba ka mamaki, ba macen da ta yi aure ba ta tsallake matakin budurci ba, da wani abu ta riqa jan hankalin samari?
Matanmu yau (wasu) sun dauki aure a matsayin qaddara kawai, su yi aikin gida, su haifi 'ya'ya, su yi raino, wannan ya sa ba sa kwalliya sai dare, ko in za su fita, hatta yaransu qanana marasa hankali sun san kwalliyar fita waje, wata macen ma bata san qanshin turaren mata ba bare ta gaya maka.
lalle kuwa kadan ne daga cikin mata suka san matsayin sa, in ka ga sun yi to, akwai wani sha'ani, babbar sallah ko qarama, mauludi ko sauran bukukuwa, wadan da ba ruwan su da lallen mace, lalle don sha'awa ake yin sa, kenan mutum Daya kacal ake masa, shin kina yi masa ko sai akwai sha'ani a gidanku?
Mace Allah ya riga ya yi ta kyakkyawa, sai in ba ta iya gyara kanta ba,duk lokacin da wani ya ga muninta ya rabu da ita, wani zai ga kyawunta ya dauka, Allah (S.W.T) ya riga ya qawata son mata a zuciyar maza.
Ko mijinki yana yaba adonki ko baya yi, ki tabbata yana jin dadin kallonki, ke ado ce, tauraruwa, farin wata sha kallo, ki ji tsoron Allah ki saka wannan baiwar da Allah ya yi miki ga mijinki don farin cikinsa da kwanciyar hankalinki.
Biyayya ga miji ba mai iya wa sai mace ta tagari, da yawa mata suna so a ce su ne wadan da Annabi (S.A.W) ya sifanta dinnan da (Nagari) sai dai biyayyar ce ta yi qaranci, ko za a yi sai dai a gabansa in ya matsa an watsar kenan, wallahi na taso na taras da iyayenmu mata magabata suna kwatantawa.
Furaat Bn Sa'ib yake cewa Umar bn Abdil'Azeez ya ce: wa matar sa lokacin da
ya ganta da wani jauhari da ubanta ya ba ta "Ki za6i Daya cikin Biyu, ko dai ki mayar da shi baitul mali ko kuwa ki ba ni damar rabuwa da ke!"
Ta ce "A kan me ne? Na fi sonka sama da ninkokinsa"
sai ya sa aka mayar,yayin da ya rasu dan uwanta Yazeed ya hau karaga sai yace in tana so zai dawo mata da shi, ta ce: "Wallahi sam! Ya hana ni amfani da shi yana da rai sai bayan ya rasu zan dawo da shi?"
To mace kenan ta gari a gidan miji na gari.
Asma'u Bnt Kharijatul Furaziy take cewa 'yarta ranar buden kanta "Yanzu fa kin fita daga sheqar da aka qyanqyashe ki zuwa shimfidar da ba ki san ta ba, da abokin rayuwar da ba ki san sa ba, ki zamar masa qasa sai ya zamar miki sama, ki zamar masa shimfidadda zai zamar miki turaku, ki zamar masa baiwa, zai zamar miki bawa, kar ki nace wajen neman abubuwa don kar ya guje ki, kar ki yi nisa da shi don kar ya manta da ke, idan ya matso, ki kusance shi, in ya ja jiki, ke ma ki dan ja da baya, amma ki kiyaye hancinsa da kunninsa da idonsa, kar ya shinshini komai a wurinki sai qamshi, kar ya ji komai sai kyakkyawan abu, kar ya ga komai sai wanda zai burge shi.
Mace ta gari takan yi qoqarin ta zama wa mijinta aljannarsa ce, ba ta son ta ga gazawarta a idanunsa, don haka takan yi farin ciki in taga murmushinsa, takan damu matuqa in ta ga fushinsa ko da ba da ita yake ba,ba ta jinkiri a wajen abinci, kuma ta iya dafawa ba tare da almubazzaranci ba, ita ce amin taccen abokin shawararsa, mai iya riqe masa sirri, ba ta yarda wani ya sani ko waye kuwa, sannan ga taimako.
Allah sarki! Na ga wani maqwabcinmu ya tashi tafiya haji yana tunanin abin da zai bar wa iyalinsa, sai matar ta ce kar ya damu ga masara can a gidan wane buhu 12 ta saya, sai ya yi mamakin in da ta samo kudin, ta ce masa, wanda yake badawa ne, in aka yi aikin gida kudin ya ragu sai ta 6oye sabo da tunanin gaba, yau kusan shekara 7 ko fiye, da faruwar haka, in ka sami mace irin wannan wace iriyar godiya za ka yi wa Allah?

3448
ReplyDelete3448
Delete