Captain Ahmad Junaid (complete)
Ya jima xaune kan darduman bayan ya kai Ayan karshe a Surah At-tawbah, ganin har shidda da rabi ya sa shi mikewa a hankali ya rufe qur'anin ya ajiye a bedside drawer, jallabiyan jikinsa ya cire ya nufi bathroom, ya dau lkci yana wanka sabulai masu dadin kamshi da shower gel duk ya cika dakin,
sanye da bathrobe ya fito yana goge lallausan bakin gashin kansa da karamin towel, gaban mirror ya nufa ya dauko lotions dinsa daga tsaye nn ya shafa, yana gamawa ya jawo mayyukan gashinsa ya shafa ya shiga combing gashin nasa, closet dinsa ya bude ya fiddo well ironed wear din da xae sa dake jikin hanger, farar singlet ya fara sawa, cikin mintuna bakwae kacal ya gama shiryawa, ya dauki silver wrist watch dinsa kirar Emporio Armani ya sa, shoe rack dinsa ya nufa ya dauki bakar cover shoe kirar Haggioti ya koma gefen makeken gadonsa ya xauna ya sa bakar safarsa na kafa snn ya sa shoe din, duk wnn abinda yake kwata kwata bae da walwala, mikewa yyi ya shiga tucking din farar uniform din jikinsa kafin ya dauki belt ya sa, wayarsa ya dauka da hularsa ya koma gaban mirror ya feshe jikinsa da turarruka ya nufi kofa ya fita, Captain Ahmad Junaid kenan, A Certified seafarer (Merchant Navy) Kmr bae son taka kasa yake tafiya a makeken compound din, sai yake ga kamar yayi shekara rabonsa da gidan nasu, Where as sati biyar kawai yayi a Egypt, kai tsaye part din Hajiyarsa ya nufa, bbu kowa falon se kamshi me ddi dake tashi da ya hade da kamshin soye soyen da ake a kitchen, falonta ya nufa da sallama cikin sanyayyan muryarsa, fitowarta daga bedroom knn ta amsa sallamarsa, xama yyi kan kujera yana kallonta yace "Gud morning Mumy" ta dan yi murmushi tana kallon agogo tace "Baka makara ba, dubi har bakwae ya gota ko duk gajiyar ce haka" Shafa lallausan gashin kansa yyi yace "Jiya da headache na kwana Mumy duk na gaji" tace "Ba na baka magani ba? Baka sha bne" a hnkli yace "Na sha" tace "Toh taso mu je kayi break, sae ka kuma sha, kar ka makara" mikewa yyi ya bi bayanta suka koma falo yace "Ina su Fatima?" Tace "Sun tafi makaranta" da kanta ta jera masa breakfast kan dinning, ta hada masa tea me kauri, snn ta koma falonta dauko masa magani, ko kan ta dawo ya shanye tean, don ba da xafi ta hada masa ba sanin bae shan abu me xafi, tana tsaye kansa ya kora maganin snn ya mike yace "Mumy bari in tafi am almost late" tace "OK, amma ka shiga ka gaida 'yan gidan, tun da ka dawo baka shiga ba" bude dara daran idanuwansa yyi bae ce komae ba ya kafa hularsa sai dai da gani kasan ransa bai so ba, ta rakasa har bakin kofa don ta tabbatar ya shiga gaida mutan gidan, part din Hajiya Fati ya nufa, ya tura kofar da sallama, xaune ya sameta tana karyawa a babban falo, xaunawa yyi yace "Ina kwana Hajiya" ta dan kallesa tace "lfya lau mutan misra, an ga daman shigowa gaida mu kenan" shiru yayi bai ce komai ba sai kuma ya mike yace "Na tafi aiki" daga haka ya fice daga falon, ta bi sa da kallo ba dae ka iya gane ma'anar expression din fuskarta, ta dan yi murmushi ta ci gaba da cin kwan gabanta, Part din Hajiya Bilki ya shiga, ita kuma ya sameta tana kunduma ma 'yan aikinta xagi kmr xata dokesu, 'yar ta Sadiya na kwance tana danna waya, daga bakin kofa ya tsaya ya dan duka ya gaisheta, harara ta 6alla masa tace "Ehh lallai Ahmad a 6akin kofa ka gaida Uwarka yau d'an rainin wayo, sai yanxu kasan da mu a gidan?" Hade rae yyi wanda hkn ya kara fito da ainahin kyansa na dan fillo, tsaki tayi ta ci gaba da 6abatun ta ma 'yan aikin ya juya yyi ficewarsa, parkin lot ya nufa ya dauki motar da xae dauka ya bar compound din bayan masu gadi sun bude masa gate, today at work was so stressful for Captain Junaid don duk a gajiye yake from yesterday's journey.
Karfe biyar da 'yan mintuna ya isa gida, ya jima xaune cikin mota yana latsa waya, ganin motar da ya shigo compound din ya sa shi kashe motarsa ya fito ya rufe ya nufi bangarensa, tuni itama ta fito daga motar tare da step sis dinsa Sadiya, bin bayansa tayi tana kallonsa cikin sanyayyan murya tace "Ya Junaid Ashe ka dawo!" Juyawa yyi har lkcn bae tsaya ba ya kalleta snn ya dauke kai yana ci gaba da tafiyarsa yace "Eh!" D'aga hka ya shiga balcony din bangarensa, dariya ta ji daga sama ta d'aga kai taga Muhibba dake xaune balcony macbook dinta a gabanta tana taunar cingam ta tabe baki tace "Cusa kai ba kwarjini" Suhaima ta dauke kanta xuciyarta na tafarfasa ta nufi bangarensu kmr xata tashi sama, Sadiya tayi 'yar dariya ta rufe motar ta bi bayanta. Shi kam dakin sa ya nufa ya cire uniform din jikinsa ya shiga bayi, wanka yyi ya fito ya shirya cikin kananun kaya, jeans baki da polo blue duk hankalinsa na gun Mum dinsa, wayarsa ya dauka ya nufi bangaren ta, xaune ya sameta falo ita da kanninsa Fatima da Aysha, gefenta ya xauna yyi mata side hug ya kwanta jikinta cikin murya me shige da ta shagwaba yace "Momyna am back" Fatima ta kalli Aisha suka tabe baki a tare, Mumy kam murmushi tayi ta dauke fuskarta tace "Welcm! ga abincin ka can dinning, ga dai kannin ka suna kallon ka" yayi 'yar dariya yace "Toh ina ruwana da su" gaishesa suka yi a tare, Fatima tace "Ya A.jay ina tsarabar mu" mikewa yyi ya nufi dinning yace "Aiki na tafi ba holiday ba ai" abinci kusan kala uku ya tarar dining din, farfesun naman rago ya soma diba yana ci. Ko da ya gama bai bar dining din ba yana ta danna waya ganin shidda ya kusa ya mike ya dawo parlor yace ma momy xae je gun abokinsa El-Ameen, tace "Maimakon ka huta kai da kake ciwon kai Ahmad!" Girgixa kai yyi yace "Mum ni ba ddewa xan yi ba" tace "toh shikenan Allah ya tsare!" Bangarensa ya koma ya canxa kaya xuwa farar shirt da blue jeans ya dauki makullin motarsa bayan ya feshe jikinsa da turare ya fito ya nufi parkin lot ya dau motarsa ya bar gidan. A hankali ya rage gudun da yake ganin d'andaxon jama'ar da ke gefen titi a tsaye, da yawan motoci ma sun tsatsaya gefen titi masu shi duk sun fiffito ko wanne na son ganin abinda ya janyo taron, a hnkli ya gangara gefen titi don a tunaninsa hatsari ne kuma bae ga alamar taimako mutanen dake tsatstsaye suke badawa ba yasan kallo kawae suka tsaya yi, bude motarsa yyi ya fito ya nufi cikin taron jama'ar ya kutsa kai, sae a snn ya dinga jin ihun da wasu ke yi, wata ya gani xaune tsakiyar taron hannunta rike da wani yaro da baxae wuce shekaru goma ba sae dukansa take iya karfinta, ga jini na xuba goshinta ba kadan ba, duk tayi dukun da daud'a cikin wata yagaggiyar doguwar riga, wasu samari biyu ne ke kokarin kwace yaron dake kurma ihu hannunta amma sbda irin rikon da tayi ma yaron suka kasa, da ganinta ka ga mahaukaciya, karasawa Junaid yyi da sauri inda suke ganin xata ma yaron lahani ya fixgo gashin kanta da yyi wani dukun dukun da datti, ta saki kara don ba rikon wasa yyi ma gashin ba, amma duk da hka ta ki sake yaron, kara damke gashin yyi da karfi ae ba shiri ta sake yaron tare da kwala wani k'aran, samarin biyu suka dauke yaron da ya rage kiris ya suma don wahala, ta yunkura xata cakume Junaid, ae da sauri ya hade hannayenta da karfi ya murda su xuwa bayanta, ta dinga ihu tana shure shure, kallon samarin gun yyi yace a samo masa igiya, ae da sauri suka juya xuwa neman igiyan, wata 'yar dattijuwa dake cikin taron ne tace "Baiwar Allahn nn ta kusa shekara unguwan nn bata taba kama d'an mutum tayi masa haka ba sae wannan karan, kuma wllh yaran ne suka addabeta da tsokana shi yasa tayi hkn" wata mata ta karbe tace "Yo dama idan ba tsokanarta suka yi ba me suka mata, dubi goshinta dutse suka jefa mata, yara basa ji sae daukan magana da tsokana, ni ko kadan ban ga laifin Baiwar Allahn ba, sae ma tausayin da ta ban, haba jama'a" nan dae aka dinga jajantawa, ko wa na fadin albarkacin bakinsa, shi dae yana rike da hannunta ta baya, ta sunkuyar da kai, duk farin shirt din jikinsa ya bace da datti, samarin ne suka dawo da igiya babba, da taimakonsu ya shiga daure mata hannu da kafa, ba karamin kokuwa suka sha da ita ba yyi mamakin karfinta hka, Suna gama daureta ya koma baya yana kallonta don ganin ko xata iya kuncewa, hawaye ne ke sakkowa daga idonta, jikinsa ne yyi sanyi yana kallonta, lkci daya tausayinta ya ratsa sa, a hnkli ya shiga kakkabe hannunsa, idonsa ya kai kan goshinta da har ya gaji da fidda jinin da yake ya daskare, ya girgixa kai yana kallon samarin yace "Ku taimaka a sa min ita a mota in kai ta a duba goshinta" 'yar dattijuwar daxu tayi wani k'ara tace "Wani asibitin yaro? Ynda Duniyar nn ta dawo ba gskya ynxu, kai waye? Kuma d'aga wani anguwa kake?" Nan jama'a suka fara cece kuce a wajen ana kallonsa, shiru yyi bae ce komae ba, can ya sauke ajiyar xuciya ya juya ya nufi motarsa cikin rashin kuxari, nn aka bi sa da kallo ana cewa "Kun ga rashin gskyar knn, don da yana da ita da dole xae tsaya ya amsa tambayoyin da aka yi masa, kaiii Allah ya raba mu da sharrin mutum" shi kam motarsa ya shiga ya ja ya bar wajen, nan aka fara watsewa kowa na fadin albarkacin bakin sa, wani tsoho ne ya karasa ya kunce mata daurin yana d'an ja da baya kadda ta cafkesa har ya gama ya bar wajen bata d'ago ba bare ta kallesa.
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
2....
Junaid na isa gidan su El-Ameen yyi parking daga waje ya shiga, Sumayya kanwar El-Ameen ya samu xaune falo da kawayenta biyu, ya karasa cikin falon cikin tafiyarsa ta k'asaita, yi tayi kmr bata gansa ba ta ci gaba da ba kawayenta labarin da take, gaida shi kawayen nata suka yi suna kallonsa, don Capt Junaid ko namiji bae masa kallo daya, ya amsa gaisuwar su ba tare da ya dube su ba yana kallon Sumayyar yace "Ke yayanki na gida?" Ba tare da ta kallesa ba tana yatsine fuska tace "Nima bn sani ba" wayarsa ya ciro aljihunsa ya shiga kiransa, Kawayen nata biyu duk suka xuba masa ido, El-Ameen na d'agawa Junaid yace "are yhu at home?" El-Ameen yace "Yea are you coming?" Wani kallo ya watsa ma Sumayya ya katse wayar ya nufi dakin El-Ameen, Husnah ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Kai Sumayya waye shi, ya hadu wllh, don Allah ni dae ki hada ni da shi, yyi min ni dae plss" Sumayya tayi dariyar rainin hnkli tace "Uhm Kinga gayen nn irin mace masa da nake a da, na so shi kmr raina amma he looked into my face nd told me baya sona, I cried my life dat day, gashi i downgraded my sef telling him I love him" bude baki duk suka yi suna kallonta, Fiddausi tace "Tabdi! Toh meye hadin ku da shi? D'an uwanku ne?" Tsaki Sumayya ta ja ta dauki lemon gabanta ta shiga sa. Xaune ya samu El-Ameen kan laptop da siririn farin glass a idonsa yana danne danne, El-Ameen ya kallesa yace "Uhnn! Our great Capt Ahmad Junaid Murnai, kaga yanda ka kara kyau ka koma kamar wani Egyptian kuwa" Junaid ya tabe baki ya xauna gefen makeken gadon dakin yace "You will neva change" El-Ameen yyi murmushi ya tura laptop din gabansa ya juya yana fuskantarsa yace "I missed you a lot frnd, am glad you are back" Junaid ya shafa kansa yace "Sai kace gaske," El-Ameen ya kura ma farin shirt din jikinsa ido yace "Wait! Ciwo ka ji Captain" Junaid ya kalli shirt dinsa da sauri ya ga jini daga gefen shirt din, El-Ameen ya mike yace "What's dat? The shirt looks dirty ma" girgixa kai Junaid yayi ya shiga unbuttoning din shirt din yace "Wata mahaukaciya ce wllh" El-Ameen ya kwalalo ido yace "Mahaukaciya kuma" Junaid yace "Yea!" Nan ya ba El-Ameen lbrin abinda ya faru a hanyarsa ta xuwa, El-Ameen yace "Eyya! Poor her, but kai me ya kai ka rike mahaukaciya ma banda abun ka" Junaid bae ce komae ba ya mike ya nufi bathroom, wanka yyi ya fito sanye da Bathrobe din El-Ameen ya goge jikinsa ya bude wardrobe ya fiddo wasu kayan abokin nasa ya sa. Bayan Magrib yace ma El-Ameen xae koma gida, El-Ameen yace "Haba frnd baxa ka raka ni gun Iman ba plss, wllh ban san me xan ce ba idan na je, gashi Mami fushi take da ni, escort me plss, dama jira nake sai ka dawo sai mu je" Junaid yyi d'an murmushi yace "Ohk buh bari in kira mumy kar taji shiru har ynxu" Bayan isha suka bar gidan bayan Capt Junaid yyi ma Ummin El-Ameen sallama, A motar Junaid suka tafi El-Ameen na tukin, El-Ameen ya lura da yanda Junaid ya kafa ma tagar motar ta inda yake xaune ido yana kallon waje, El-Ameen xae yi magana ya ji Junaid yace "Dr d'an tsaya nn don Allah in ga ko an kwance mata igiyar, it's gud ace anyi hkn" El-Ameen ya kafa masa ido sae kuma ya tabe baki ya daga shoulder ya gangara gefen titi yyi parking, Junaid ya bude motar ya fita, tana nn xaune kan bolan, rike da wani bakin Leda a hannunta, rungume hannayensa yyi yana kallonta, El-Ameen ya dafa sa yace "let move on Capt, they've freed her" juyawa Capt Junaid yyi suka koma motar suka bar wajen, suna isa gidan El-Ameen ya kira Iman da nmbr da Ummi ta basa, kanwar ta ce ta fito tayi masu iso har falo ta cika su da drink, mahaifiyarta ta fito suka gaisa ta bar palon, ba a dau lkci ba Iman ta fito sanye da wata doguwar riga me adon stone blue da gold, tayi rolling kanta da plane blue mayafin kayan, kyakkyawa ce ba kadan ba, ta karaso falon kamshin turarenta ya cika ko ina ta xauna, kallon Junaid El-Ameen yyi, Junaid ma ya kallesa, suka shiga kallan kallo, ganin El-ameen yaki cewa komai Junaid ya d'an yi gyaran murya yana kallonta yace "Ina yini Hajiya" amsawa tayi ba tare da ta kallesu ba, Junaid ya d'an taba El-ameen alamar yyi magana mans, a hnkli El-Ameen ya matso kusa da shi murya can kasa yace "Me xan ce mata plss" ae Junaid bae san lkcn da ya fashe da dariya ba, El-Ameen ya tsaya kallonsa sai shi ma ya saka dariyar, nan suka dinga dariya kamar tababbu suka yi me isan su suka yi shiru, Junaid ya shafa kai yana kallonta yana murmushi yace "Ehm dama Ummi ce tace in rako El-Ameen wajen ki.... Shine muka xo" El-Ameen yace "Eh Ummi ce tace in xo gurin ki shine ya rako ni" kala bata ce masu ba, Junaid ya mike yace "Toh shknn mu xa mu koma sai mun sake dawowa" El-Ameen ma ya mike yace "Eh xa mu koma, sae wani lkcn, mun gode kwarai" mikewa tayi tace "Allah ya kiyaye" daga haka ta haura sama ta bar su tsaye parlon, dariya suka dinga yi cikin motar barin Junaid, El-ameen ya ja motar suka bar anguwar daga karshe, sae da El-ameen ya kai kansa gida sannan ya fita suka yi sallama Junaid ya koma driver seat ya ja motar ya bar layin, yana isa inda mahaukaciyar take yyi parkin yana kalle kallen inda xae ganta daga cikin motar, sae bae bae ganta ba ya ja motar ya nufi gida. Yana jiran masu gadi su bude masa gate kiran mum dinsa ya shigo wayarsa, jan motar yyi ya shiga compound din ya nufi parkin lot yyi parking snn ya fito, ganin motar Abba yasa shi kallon agogon wrist dinsa ya ga har goma ya kusa, bangaren mumy ya nufa, tsaye ya sameta palo tana rike da wayarta ta rungume hannu, yyi murmushi yace "Ga ni na dawo Mum," ta hade rai tace "Daga ina kake hka Ahmad?" Ya shafa kansa yace "na gaya maki Gidansu El-Ameen na tafi mum, na raka sa xance ne" yana murmushi ya k'are maganar, mumy tace "Zance! Lallai ba ayi abun arxiki ba kenan" dariya yyi lkci daya ya hade rai yace "Allah mum mun yi magana me ma'ana, infact ni ne ma nayi don shi shiru yyi wai kunya" Mumy tayi dariya tace "Au, kace ka kora masa budurwar knn in har kai kayi magana, tab!" Dariya shi ma yyi ya mata side hug yace "Kai Mumyna ni din ne ban iya magana ba" murmushi tayi tace "Kaje gun Abba yana neman ka" ya saketa yace "Ohk Mum" kofar da xae sada sa da part din dad dinsa ya nufa, xaune ya samesa babban falonsa yana kallon news lkci daya yana shan fruit salad din dake kan d'an table gabansa, Hajiya Fatee na xaune gefensa, sae step sisters dinsa su uku gaba daya suna palon, xaunawa yyi kasan lallausan rug din yana kallon Abbansa yace "Barka da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa daga ina kake naga baka duty ae" yace "Naje gidansu El-Ameen ne Abba," kallon Hajiya Fatee yyi yace "Ina yini Hajiya?" Tayi murmushin da bai kai ciki ba tace "Lfya lau, ya aikin" yace "Alhmdllh" Muhibbah ce ta shigo falon da sallama rike da bowl din kankana da akayi slicin, ta duka ta ajiye gefen Abba, xama tayi tana kallon junaid da ya maida hankalinsa kan Tv tace "Ina yini yaya" amsawa yyi ba tare da ya kalleta ba, Hajiya Fatee sae kallonsa ta gefen ido take, mikewa Junaid yyi yace "Sae da safe Abba" Abba yace "Yauwa ka ba Muhibbah dubu ashirin xa tayi amfani da su a makaranta gobe wae," yace "toh Abba" daga nn yyi ma Hajiya Fatee sae da safe, kanninsa ma suka yi masa sai da safe ya fice daga falon rai a bace, mikewa Muhibba tayi ta bi bayansa, bae tarda mumy a palo ba, hka yasa ya nufi bedroom dinta ya sameta har ta kwanta, xauna wa yyi daga gefenta yace "Kin kwanta mum?" Tace "Har ka fito?" Yace "Eh mum" peck din goshinta yyi yace "Gudnyt mum, xan tafi in kwanta" tace "Toh Allah tashe mu lfya, make sure kayi alwala kayi addu'a kafin ka kwanta" yace "In'sha Allah mum" mikewa yyi ya kashe mata wutan dakin ya rufe mata kofa ya fita, dakin da kanninsa suke ya bude, Aisha ce ke waya ita ko Fatima tayi bacci, ya rufe kofar ya fito parlor, xaune ya tarda Muhibbah tana jiransa, yyi mamakin rashin ganin Hijab a jikinta don da hijab ta shigo palon Abba, kauda kai yyi ya fita daga parlon ta mike ta bi bayansa, yana isa part dinsa ya bude ya shiga ya juya yana kallonta ganin tana kokrin shigowa yace "Ki jira ni a nn malama" rufe kofar yyi, ta hade rae ssae tana kallon kofar, tsaki tayi ta bude ta shiga, ganin bae palon ta nufi bedroom dinsa, ya dauko kudin zae fito suka kusa cin karo, wani tsawa ya daka mata yace "Are yhu insane xa ki biyo ni daki" kallonsa ta tsaya yi, yyi tsaki ya bangajeta ya fice a fusace, bin bayansa tayi ba tare da ta ji haushi ko kadan ba, a palo ya jefar da kudin ya nufi kofa ya bude yace "Leave yanxu!" D'an tsaki tayi ta duka ta dauki kudin ta fice, ya kulle kofarsa ya sa key don wani mugun haushinta yake ji a gidan. K'asa bacci yyi daren ranan, duk juyin da xae yi sae mahaukaciyar nn ta fado masa, hankalinsa ne ya tashi don shi dae bae mata komae ba illah taimakon yaron da yyi, mikewa yayi daga karshe ya nufi bayi ya dauro alwala ya fito ya shimfida pray mat ya shiga nafila, sae kusan Karfe uku da rabi bacci ya daukesa. Da asuba ruwan sama ya sakko kamar da bakin kwarya, kmr jiya yau ma bae fita mosque sllhn asubahin ba sbda ruwa, ruwan dumi ssae ya hada yyi wanka don ko kadan bae son sanyi shi, ya shirya cikin uniform dinsa ya dauki babban kadigan na uniform me kalan Navy blue ya sa snn ya fito falo rike da rain coat dinsa, sae da ya tabbatar wayoyinsa na aljihun wandon uniform din jikinsa snn ya fito balcony ya saka rain coat din da hulansa ya nufi bangaren Mumy, a balcony ya cire rain coat din ya bude kofa ya shiga, tana kitchen da mai aikinta sai fatima suna hada breakfast, ya shiga kitchen din ya gaisheta ta amsa da cewa "Ka tashi lfya, ya ruwa?" Yace "Alhmdllh mumy" Fatima ta kallesa tace "Gud morning ya Ahmad" yace "Morning" ya fita kitchen din, tea kawae ya sha da kwae shi ma sae da mum ta takura sa wae ya makara xuwa aiki, har balcony ta rakosa tace "Baxa ka shiga gaida 'yan gidan da Abba ba kenan" ya dan tsuke fuska yace "Am late mum," tace "Toh Allah ya tsare" rain coat dinsa ya sa yace "Ameen" snn ya nufi parkin space, kusan a tare suka jero da Suhaima dake rike da lema tayi shirin makaranta, ko kallonta bae yi ba ya bude motarsa ya shige ta nufi tata motar tana kallonsa, jan motar yyi ya danna horn aka bude masa gate ya fice. A hnkli ya ke driving din har ya iso inda mahaukaciyar jiya take, samun kansa yyi da parking gefen titi yana kalle kallen inda xae ganta idonsa ya sauka kanta, xaune take cikin ruwan ta hade kai da gwiwa, duk ta jike da alama tun da ruwan ya sauko bata bar wajen ba, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera yana ci gaba da kallonta, duk jikinsa yyi sanyi, da kyar ya iya jan motarsa ya bar wajen ganin yana bata lkci, shi mutum ne me tausayi da raunin xuciya kamar mace, har ya isa office bae da sukuni, colleagues dinsa duk suka lura da shi suka kuma tambayesa ko Lfya yace bai jin ddi ne, Karfe biyar saura ya bar gun aikin, driving kawae yake cikin rashin kuxari, bae bi hanyar da xae ga mahaukaciyar ba ya canxa hanya, ko parking din arxiki bae yi ba ya bude motar ya nufi part din mumyn sa, kwanciya yyi kan dogon kujera ya rufe idonsa gam, Mumy ce ta fito daga kitchen ganinsa a kwance tace "Lfya Ahmad" jin bae ce komae ba yasa ta karasa kusa da shi tace "Ahmad!" Bude idonsa da ya kada yyi ya mike xaune ya dafe kansa, taba jikinsa ta shiga yi da damuwa tace "baka da Lfya ne?" Lumshe ido yyi ya kwanta jikinta ta rungume sa tace "Talk to me mana son, me ya faru?" A hnkli yace "Kai ne ke man ciwo Mumy" tace "Ci abinci mu tafi asibiti" da sauri yace "No mum, xan sha magani" hade rai tayi tace "Wani maganin xa ka sha, sau nawa kke sha bae maka aiki ba, so kake ka dauko min magana gun Abba koh" shiru yyi ta mike ta nufi dinning ta dawo rike da kulan abinci da plate da spoon, fried rice din ta dibar masa ta ajiye snn ta koma kitchen ta hado masa tea, bae son mum din tasa ta daga hankalinta shi yasa ya daure ya dinga cin abincin don kwata kwata bae da appetite. Mikewa yyi da ya gama Mumy tace "Ka tafi ka canxa kawae mu tafi clinic" yace "Toh" snn ya fita xuwa bangarensa, wanka yyi ya canxa uniform din jikinsa xuwa kananun kaya, ya d'an kwanta yana tunanin karyar da xae ma Mumy ta hakura da xuwan su asibiti, dubara ce ta fado masa ya mike da sauri ya dauki wayarsa ta fita, xaune ya sameta palo ta shirya tana jiransa, murmushi yyi yace "Mumy ynxu El-Ameen ya kira ni, I told him m nt ok, shine yace I shud cum over ya duba ni" hararansa Mumy tayi tace "Yhu should come over dai kuyi hira, my frnd mu wuce clinic" marairaice mata yyi ya mata side hug yace "Haba mum, ga ni da amini likita kice mu je clinic, kinga baxae ji ddi idan ban je ba plss"
*Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
3.....
Wani kallo Mumy tayi masa tace "Kaga ka kiyaye ni Ahmad, baxa ka
gun El-Ameen din ba asibiti xa mu" shiru yyi yana kallonta sanin baxae
taba convincing dinta ba, a hankali yace "Toh kiyi hkuri mumyna mu
tafi asibitin" jakarta ta dauka tace "Sake ni mu tafi" saketa yyi dai dai
lkcn da wayarsa ya fara ring, fiddowa yyi a aljihu yana kallon me kiran
nasa ya ga El-Ameen ne, ya juya ya kalli Mumy ya ga kallon wayar take,
d'agawa yyi ya kai kunne daga daya bangaren El-Ameen yace "ya ne
captain, kana gida yau?" Junaid ya d'an saci kallon Mumy ya ga
kallonsa take, yace "Noo! Don't worry frnd Mumy tace mu tafi clinic
kawae ba sai na xo ba" El-Ameen yace "What are yhu talking about
guy?" Junaid yace "No ba komae wllh, kawae dae tace mu tafi asibiti
ne" tsaki El-Ameen yyi yace "HeyJunaid are you ohk, wat are yhu sayin?"
Junaid yace "Ohk Tnx for ur care frnd!" D'aga hka ya katse wayar ya
kashe gaba daya ya mayar aljihunsa yana sinne kai, Mumy tace "Don
me xaka ce Mumy tace, maimakon kace Abban ka ne yace kaje clinic"
Junaid yyi shiru yana kallonta, komawa tayi ta xauna ta sauke ajiyar
xuciya tace "Toh shknn, ka tafi can ya duba ka, amma yana prescribing
maka magunguna ka dawo Ahmad, I repeat my self ka dawo" farin ciki
ya lullubesa sae dae yyi kkrin boye hakan yace "Toh Mumy I promise"
har bakin motarsa ta rakasa tace "Drive carefully" yace "Sure mum"
tana tsaye har ya bar gidan snn ta juya xata koma bangarenta, xaune
ta ga Hajiya Fatee da Hajiya Bilkee a balconyn Hajiya fateen suna
kallonsu, Mumy ta karasa tayi masu sannu da xama, Hajiya Bilki kadae
ta amsa da yauwa a dakile, juyawa Mumy tayi xata bar wajen Hajiya
Fatee tace "Ynxu an ma hana d'an gwal din xuwa gaida mu tsabar
mulki" juyawa Mumy tayi tana kallonsu tace "Ayya Bashi da lfya ne,
ynxun ma gun likita xa shi" bbu wanda ya tanka ta cikinsu, ta nufi
bangarenta ba tare da ta sa ma kanta damuwarsu ba. Junaid na isa ya
tarda El-Ameen na clinic, bae so hkn ba amma bbu ynda ya iya hka ya
nufi Babban asibitin Dad din El-Ameen din, don shima kwararren likita
ne da yyi fice a Nigeria, da yake Nurses din sun san tsakanin Junaid da
El-Ameen, bbu wanda ya dakatar da shi xuwa office din El-Ameen din,
murda kofar yyi ya shiga babban office din, El-Ameen dake xaune yana
dube duben files sanye da farin glass a idonsa ya dago yana kallon
Junaid, ajiye pen din hannunsa yyi ya rike ha6a yace "Kan ka daya
kuwa captain?" Dariya junaid yyi ya xauna kan table din office din yace
"Kai da ban yi hka ba da Mumy bata bari na xo ba yanxu ai" El-Ameen
ya girgixa kai yace "Mummy's boy, na ga randa xaka girma ka samu
freedom din kanka" murmushi yyi yana shafa kansa yace "Uhm am 30
ynxu kace ban girma ba, ae kila har in mutu baxan samu wannan
freedom din gun momma na ba" El-Ameen yyi dariya yace "Idan kayi
aure xa ka samu" murmushi Junaid yyi yace "Aure kuma" kallonsa El-
Ameen yyi ya cire glass din idonsa yace "Amma ba ka jin ddi koh, you
look weary?" Junaid ya lumshe ido ya bude da damuwa yace "Kinda
frnd! Am just disturb, bani da kwanciyar hankali kwana biyun nn, M just
nt my self..." Rike kai yyi ya kasa ci gaba, El-Ameen ya dafa sa yace
"What's wrong frnd, tell me ur problem, 'Yan gidan ku ko?" Junaid ya
d'aga kai yana kallonsa cike da damuwa yace "No! Wnn mahaukaciyar
ban san ko laifi nayi da na kwace yaron nan a hannunta ba, duk na
kwanta ita nake tunawa nake gani, k'asa bacci nake yanxu duk bani da
sukuni" El-Ameen ya ja tsaki ya mayar da glass din idonsa ya jawo files
din gabansa yana ci gaba da dubawa yace "Thought it to be something
better ma, wai mahaukaciya" wani tsakin ya kuma ja, Junaid ya runtse
ido ya watsar da files din yace "Haba Dr in ce maka bana iya bacci
kace min yhu thought it was somethin better," El-Ameen ya rike chin
dinsa yana masa wani irin kallo da mamaki yace "Wae halan kana da
dangantaka da mad woman din nn ne junaid" a fusace Junaid yace "Wa
ya sani" wani dogon tsaki El-Ameen ya kuma ja yace "Kaga ka rabu da
ni, I have meaningful things doing ynxu, aikin gaba na ma ya ishe ni
stop bothering me plss da wata mahaukaciya can." Kallonsa junaid ya
tsaya yi na kusan minti biyu kafin ya sauka daga kan table din da yake
ya dauki wayarsa da makullin mota ya juya ya nufi kofa, bin sa da kallo
El-Ameen yyi kafin ya birkita lallausan gashin kansa a xuciyarsa yace
"What's wrong with Junaid da xae damu kansa ya damu wani da wata
gagarumar mahaukaciya can" mikewa yyi da sauri tun kan ya fita ya
kulle kofar office din yace "Look Captain, to ynxu me kake son ayi da
rashin baccin naka, ko kuma dai kawai mu je ka ba mahaukaciyar
hakuri?" Junaid ya kallesa yace "bude min kofa" El-Ameen na 'yar
dariya yace "Of course No baxan bude maka ba sae ka gaya min dalilin
ka na xuwa gu na, which help do yhu want me to render yhu, mu je ka
nemi gafararta mad woman din ne" tuni idon Junaid ya sauya kala, still
behaving gently yace "Bude min kofa nace" El-Ameen yace "Noo!" Wani
kara yyi ya cakumo sa yana huci yace "Bude min kofa Ahmad!"
Murmushi El-Ameen yyi yace "Naki! ka xama Zaki a nn in ga" turasa da
karfi Junaid yyi ya koma kan dogon kujera ya xauna ya rike kai, El-
Ameen yyi dariya ya koma kan office chair dinsa ya xauna, sae bayan
kusan minti goma Junaid ya dago kansa, ya kalli El-Ameen dake ta
aikinsa, El-Ameen yace "Har iskokan sun sake ka kenan" Junaid bae ce
komae ba ya kauda kai, mikewa El-Ameen yyi ya dawo gefensa ya
xauna yace "Now tell me, ya kake son ayi?" Junaid ya sauke ajiyar
xuciya cikin sanyi ya fara magana, "Frnd! May be tana son in taimake
ta ne, shi yasa take bi na, she want me to help her" El-Ameen ya
kwalalo manyan idanuwansa yace "Kayi me?" Shiru Junaid yyi yana
kallonsa, El-Ameen ya girgixa kai yace "Yhu must be crazy Junaid, meye
hadin ka da wata mahaukaciya can har kake tunanin taimakon ta, kai
ka daura mata haukan, ko kasan me ya haukatar da ita? Wait! which
help ma xaka iya rendering dinta tukun, taking her to psychiatry nd
staying with her there ko yaya?" Junaid ya tabe baki yace "Ae dan
Mumy da Abba baxa su yrda bne da nayi hkn wllh" El-Ameen yyi dariya
sosai yace "Ehh lallai Junaid ka ja ma kanka" Junaid yyi kasa da murya
yace "Listen to me plss Dr, ban da kai akwae wanda xan kai ma
damuwar da na k'asa gaya ma mahaifiyata duk kusanci na da ita, why
kake min hka frnd?" El-Ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "Noo ba hka
ba Junaid, ynxu tell me ya kake son ayi, hw did yhu want me to help in
here?" Cikin kwantar da murya junaid yace "yhu are a Neurologist as
well as a qualified MD, I knw yhu can cure her by the grace of Allah idan
ka sa kanka, yhu neva can tell where one's reward Lie's" wani
matsiyacin kallo El-Ameen ke yi masa kafin ya mike yace "Gaskiya ka
janyo ma kanka fitina ka ja mana muma da muke tare da kai Ahmad,
dama ban da abun ka me ya kai ka kama mahaukaciya kai da kake tuki
a mota, Ohh My God! ga irinta nn ka tabo aljana, don Wllh yhu are not
on ur right senses" Mikewa Junaid yyi shi ma yace "Stop this El-Ameen,
meye illar taimakon Baiwar Allah da xa mu yi? Haba idan wani yace min
xaka yi hka I won't believe wllh," El-Ameen yyi shiru yana kallonsa baki
bude, cike da mamakin aminin nasa, Junaid ya juya ya nufi kofa rai
bace, girgixa kai El-ameen yayi yace "listen Captain" ko sauraransa
Junaid bae yi ba ya fice daga office din, ya birkita kansa ya bi bayansa
da sauri, a tare suka isa inda motar Junaid yake, El-Ameen yace "Haba
frnd listen to me, ynxu mu koma ka min bayani sosai yanda zan gane
abinda kake nufi don wllh am confuse" hararansa Junaid ya shiga yi
yace "Ka dae san ba kai kadai bane abokina likita ba koh?" El-Ameen ya
d'an yi murmushi yace "I know" hannunsa ya rike suka koma asibitin
dae dae lkcn da wayar Junaid ya shiga ringing, fiddo wayar yyi yaga
Mumy ce ke kiransa, El-Ameen yace "Mummy's boy" d'agawa Junaid yyi
daga daya bangaren Mumy tace "Ka kyauta Ahmad" Junaid ya
marairaice yace "Ohh Ummata, drip karami yake kara min ne fa, nd am
feeling much beta ynxu har na ci abinci kuma" Murmushi Junaid yyi
bayan ya gama sauraranta yace "in sha Allah mum" daga hka ya katse
wayar suka nufi office din El-Ameen.
El-Ameen ya tallabi chin dinsa da hannu biyu yana kallon Junaid yace
"ina jin ka, Allah sa ka dawo senses dinka yanxu, ya kake son ayi kace?"
Junaid ya lumshe ido ya bude yace "Wae da cure dinta nake son kayi ko
nawa ka bukata xan biya ka" El-Ameen yyi murmushi yace "Ohh i see, A
can kan bola xan dinga tafiya ina samun ta kenan" Junaid ya ce "Noo
of course, dauko ta xa mu yi" El-Ameen ya bude ido yace "Mu kai ta
ina? Gidan ku?" Hararansa Junaid yyi yace "Plss frnd be serious, a
gidan ka xa mu ajiye ta, ni idan nace xan ajiyeta a nawa gidan dole sae
su Mumy sun sani, barin ma ni da nake da 'Yan sa ido, kai kam bbu me
sa maka ido" El-Ameen ya buga table din gabansa yace "Wnn ne kuma
baka isa ba Malam, I can't keep a mad woman in my house, the house
that's meant for my wife!" junaid yyi shiru yana kallonsa, a hnkli yace
"Ohk let me rent an apartment" Tsaki El-Ameen yyi yana Mamakin
Matsalar Junaid, anya kuwa kansa daya, Junaid yyi murmushi yace "I
knw u are thinking if am alryt at all, tausayi ne ba wani abu ba frnd,
naga yarinyar is too young ace hakan ya sameta duk da ba a ja da ikon
Allah, baka san inda rayuwa xae yi da kai ba wataran frnd, it really pays
to be kind, and you neva can tell where one's reward lies! ni xuciyata
daya nake son taimakonta saboda Allah, I will pay yhu wat ever amount
yhu require for the bill, ni dae fatana ta samu lfya ta nemi 'yan uwanta"
wani dariya El-Ameen yyi yana tafe hannu yace "Toh governor Ahmad
Junaid, don this is the government's job not urz" mikewa Junaid yyi
yace "What ever, ynxu dae let me start lookin for an apartment" El-
Ameen ya daga kafadarsa yace "Left to yhu, amma ina guje maka
reaction din yan gidanku idan suka ji shirmen da kake shirin aikatawa"
Junaid yyi tsaki yace "Ni dae nemo plaster ka sa min a hannu am
leaving, gobe I might come back idan na sami apartment" El-Ameen ya
mike ya dauko plaster ya mika masa yana kallonsa cike da mamakinsa,
a tare suka fito, El-Ameen yace "Yi Dropping dina a gida kawae, na
mance key a office" a hanya El-Ameen ya kwashe da dariya yace "Tabdi
wa ya ga Capt Junaid da taimakon mahaukaciya, but idan taimako
kake son yi Why not kaje orphanage home kayi ne" share sa Junaid yyi,
yana parking kofar gidansu ya juya yana kallonsa fuskarsa daure yace
"Sae da safe" El-Ameen yyi dariya ya bude motar ya fita sanin har ya ji
haushi ne.
*Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_
4.....
Washegari Karfe hudu da wani abu Junaid ya baro office, tun safe dama ya kira agents din Abbansa yace su sama masa apartment ko me dakuna biyu ne but kar su yrda Abba ya sani, driving yake yana kokarin kiran daya daga agents din yaji ko an gama komae, mutumin na d'agawa ya gaishesa snn yace "Yallabai an samu, amma xaka iya xuwa ka ga ko ya maka" Junaid yace "Alryt! Ohk, na gode" katse wayar yyi ya nufi asibiti gun El-Ameen sanin yana clinic, xaune ya samesa yana attending to wata patient, Junaid ya nufi bedroom dinsa da ke office din ya kwanta, bayan minti talatin El-Ameen ya shigo ya cire farin lab coat din jikinsa yace "Uhnn! Ko uniform baka cire ba tsabar xumudin taimakon mahaukaciya kenan" Junaid ya mike xaune ya hade rai yace "Yea daga office nake, na kuma samu apartment" El-Ameen yyi murmushi yace "Ohh dats gud for yhu" Junaid yace "But yau da nyt xa mu dauko ta ko" wani kallo El-Ameen yyi masa yace "Xa dae ka dauko ta malam, kai da wa xa ku dauko ta" shiru Junaid yyi yana kallonsa, ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh naji xan dauko ta" mikewa yyi yace "i will be on my way, but ina son ka min favour daya, plss motar ka xaka bar min a layin ku sae ka bar min key din karkashin motar ko in btwn flowers dake kusa da motar, I will then cum over to take it sbda Mumy baxata bar ni in fito so late ba" El-Ameen ya bude ido yace "What? A motar tawa xa a saka mahaukaciya, kuma tsabar walakanci sae in bar motar at risk da makulli a waje, you are dreaming" Junaid ya girgixa kai yace "Ka dae san ba sonka Allah ya fi yi a kanta ba da ya barka da hankalinka ita ya gusar mata da nata koh?" El-Ameen yace "Toh preacher, amma ni baxan bada motata ba period!" Junaid bae ce komae ba ya fice daga dakin, tunanin wa enda xa su taimaka masa ya dauko mahaukaciyar ya dinga yi, sae da ya biya ya duba apartment din da aka samar masa ya ga ba laifi snn ya nufi gida. Da daddare yana xaune palon Mumy yana cin tuwon shinkafa da lafiyayyen miyar vegetable da tayi masa, sae dae duk bae da appetite turawa kawae yake, ya kalli Fatima dake kwance parlon yace "Xo dauke abincin nan" ta mike tace "Baxa ka ci bane yaya?" Bai ce komai ba hakan yasa ta kwashe tray din tayi kitchen da shi, takwas da rabi ya mike ya shiga bedroom din Mumy don mata sae da safe, tace "Yau ba hiran kenan" yayi yake yace "Bacci nake ji momma" tace "To Allah ya tashe mu lfya, make sure yhu ablute nd pray b4 going to bed, kuma ka rufe windows ka ga hadari" yace "In'sha Allah mum" fita yyi daga bangaren nata rike da wayarsa. Bedroom dinsa ya shiga ya canxa kaya cikin hanxari snn ya fito, gate ya nufa yana yi yana waige waige har ya fice, da kafa ya karasa titi iska na kadawa sosai ga walkiya alamar ko da yaushe ruwa xae iya sakkowa, yana tsaye yana jiran abun hawa abinda bae taba yi ba duk tsawon rayuwarsa a iya saninsa, bae ma san ta ynda xae tsaida adai daitan ba sae kalle kalle yake gashi kuma sae wucewa suke, yayyafi aka fara yi sosae, ya lumshe ido ya bude yana kallon motocin dake wucewa, wata farar lafiyayyen mota ce tayi parking gefensa, wata kyakkyawan yarinya ta fito sanye da hijab tana kallonsa tace "Bawan Allah shigo in rage maka anya if its ok by yhu, ka ga its raining kuma ruwan xae iya karfi at anytime, na wuce daxu xanje pharmacy na ganka kuma na dawo na kuma ganin ka" kallon motar yyi snn ya kalleta, yarinyar baxata wuce 18 ba, ta d'an bude ido tace "Noo! Am just being helpful" daga hka ta juya xata koma motar ta, sanin bashi da wani alternative yasa ya bude gaban motar ya shiga, dai dai lkcn da ita ma ta shiga maxaunin driver, ta kallesa ta ja motar suka bar wajen, tana tuki tace "Ina ka nufa?" Ba tare da ya kalleta ba ya gaya mata, tace "Ohk" wayarsa ce ta fara ring ya ciro a aljihunsa ya ga El-Ameen ne, da kmr baxae daga ba sae kuma ya d'aga ya kara a kunne yyi shiru, El-Ameen yace "Ya ka samu fitowan?" Cikin kaushin murya yace "Ba Matsalar ka bne wnn" El-Ameen yyi dariya yace "Haba name same, naga baka xo daukan motar bane har ynxu" Junaid yace "Ehh xan je in karba na Faisal" El-Ameen yace "Kai na fa fito maka da motar Wllh come over, yhu knw I can be annoying a times" Junaid yace "Noo dnt wrry ina hanyar gidan ynxu" El- Ameen yace "Look stop this plss junaid, na fito maka da mota Wllh, just teasing yhu daxu" Junaid yyi shiru sanin baxae iya fushi da abokin nasa ba, lumshe ido yyi ya bude yace "Ohk" snn ya katse wayar. Juyawa yyi ya kalli yarinyar ya gaya mata anguwarsu El-Ameen yace nn xani, tace "Ohk" dai dai bakin gate yasa ta tsaya ya juya yana kallonta yace "Thanks a lot" tace "Yhu are welcm!" bude motar yyi xae fita duk da ruwan da ake tsugawa, sae kuma ya juya ya kalleta, wayarsa ya ciro ya mika mata yace "Sa min digit din ki so I can thank yhu some other time" tace "Do yhu need to? Its ohk ba sae ka kuma gode min ba, it payz to be kind" murmushi yayi ya mayar da wayar aljihunsa yace "Ohk Allah saka da khairan" juyawa tayi bayan motar ta dauko raincoat ta mika masa tace "Hope yhu will cope with this" karba yyi ya kuma mata godiya ya fita daga motar, ta ja motar ta bar wajen. Bin motar yyi da kallo dai dai lkcn da aka dallara masa wutan fitilar mota, juyawa yyi yaga motar El-Ameen ce, karasawa yyi da sauri yana rike da raincoat ya bude front seat ya shiga, El-Ameen yace "Wani mota ce wannan?" Junaid yace "A good Samaritan" El-Ameen ya tabe baki yace "Ynxu ka mana adalci kenan Junaid, ko wani mahaluki na cikin bargo cikin ruwan nn kasa muna tsaye a titi?" Junaid yace "Look! Ni ae bn ce ka fito ba xaka iya komawa abun ka" El-Ameen ya hararesa yace "Ehh In koma ka ji haushi na koh" Junaid yace "No Baxan ji ba" tsaki El-Ameen yyi ya tada motar suka bar layin, sae da suka hau kan titi snn yace "Ynxu ina xa mu bi?" Junaid ya gaya masa suka kama hanyar inda mahaukaciyar take, banda tsaki bbu abinda El-Ameen yake, shi dae Junaid bae ce komae ba har suka iso, Junaid ya fara kalle kallen inda xae hangota, bae ganta wajen ba hankalinsa ne ya tashi, shi dae El-Ameen kallonsa kawae yake, ya juya ya kalli El-Ameen yace "Frnd bn ganta wajen ba kuma" El-Ameen yace "Toh me xan yi ni kuma, haka kawae ka shiga hakki na ka hanani kwanciya cikin sanyin nn" bude motar Junaid yyi ya fita cikin ruwan, ya fara nemanta, lkci daya ya jike jagab, can ya hangota rabe jikin bango kusa da wani kiosk duk ta jike jagab ta takure waje daya, wani tausayinta ne ya rufe sa jikinsa yyi sanyi sosai, ya kusa minti biyar tsaye cikin ruwan yana kallonta snn ya juya ya koma gun motar ya bude yana kallon El-Ameen cikin sanyin murya yace "I've seen her" El-Ameen yace "Gud for you, sai ka bude baya ka dauki igiya ka daureta ka dauko ta ai" shiru Junaid yyi yana tsaye cikin ruwan yana kallonsa, can yace "Ka xo ka taimaka min toh" El-Ameen yace "What! cikin ruwan nn xan taimaka maka, Noo" Junaid bai kuma cewa komai ba ya bude bayan motar ya dauki igiyan da ke nan ya rufe ya koma inda mahaukaciyar take, k'asa karasawa yyi don gabansa sae faduwa yake, da kyar yyi shahada ya isa gabanta, kallonsa take tana kara takurewa waje daya, sae a snn ya lura da rawan sanyin da take, a hnkli yace "Kiyi hkuri baiwar Allah, am only trying to help" kamar ta ji me yace ta yunkura ta mike xata bar wajen da gudu, fixgota yyi ya rike ta gam, ta shiga kokuwa da shi tana ihu, El-Ameen na daga mota yana lekansu, ban da dariya bbu abinda yake har da kyakyatawa, ba karamin wahala ta ba Junaid ba don da kyar ya kai ta k'asa ya daure hannunta shima din ba wae dauri sosae ba don taki tsayawa ga wani karfi dake gareta, bude mota El-Ameen yyi ya fito cikin ruwan ya karasa inda suke da sauri, karban sauran igiyar yyi junaid na rike da ita ya daure ta gam, ihu ta dinga masu tana shure shure, El-Ameen ya mike yace "Ae sae ka dauketa Mr Do good" bbu musu Junaid ya dauketa, ko kadan bata da nauyi ya nufi motar da ita El-Ameen na biye da shi a baya yana 'yar dariya, ya bude baya ya saka ta ciki ya rufe, yatsine yatsine El-Ameen ya shiga yi ya nufi driver seat, muryoyi suka ji daga bayansu duk suka juya, wasu matasa suka gani tsaye da gora da adda a hannayensu, da ka gansu ka ga masu gadi, cikin tsawa suka ce "Maxa ku fito da ita ynxun nn" kallon Junaid El-Ameen yyi, El-ameen ma haka, ae kan kace me sae ga Junaid cikin mota ya rufe, El-Ameen na ganin hka shi ma ya shige motar ya tada da sauri, samarin suka taho da gudu, cikin hanxari El-Ameen ya ja motar suka bar wajen, bin motar samarin suka yi da guda suna buga ma motar gora da karfi, El-Ameen ya dinga cewa "ya Salam! ya salam! ya salam!" har suka bar anguwar abinda yake maimaitawa kenan, juyawa yyi yana kallon Junaid dake ta kallon mahaukaciyar dake fixge fixge tana son freeing kanta, a fusace ? yace "Kai ka ji irin ynda suka tarwatsa min bayan mota kuwa Junaid" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Xan gyara maka motar ka idan Allah ya yarda" kwafa El-Ameen yyi yace "Better, kuma ka dinga lura da ita kar ta cafko ni mu shiga uku, ynxu ina muka nufa?" Junaid ya gaya masa ya kama hanyar anguwar, cikin minti goma suka iso, har lkcn ruwa ake, parking El-Ameen yyi yana kallon Junaid ya bude motar ya fito, fitowa yyi shi ma suka shiga gidan a tare, gidan babba ne ba laifi, junaid har yasa anyi furnishing gidan kar ya tsaya empty, El-Ameen yyi tsaki yace "Lallai! A wannan gidan xa a ajiye mahaukaciya? ba sae ta balla windunan nn mara karfi ba ta yi ficewarta, bugu daya idan tayi ma kofar nn ficewa xae yi wllh" Junaid ya shafa kansa a hankali yace "Toh shi suka samo min ya xa ayi" El-Ameen yace "Oho, amma idan ta gudu wallahil Azim ba da ni xaka je nemota ba" da damuwa Junaid yace "Toh hw are we going to do it ynxu ga shi mun dauko ta" El-Ameen yace "Oho it's left to yhu" xama Junaid yyi ya rike kansa, can yace "Ohk, let bring her in I will stay nd guard her till 2morrow kafin nn sae a samo mata wani gidan." El-Ameen ya shiga hararansa can ya ja tsaki yana kallon agogo yaga har goma ya wuce, yace "Kaga mu je can gida na, don ni na gaji sanyi nake ji kar in yi ma kai na illa haka kawai" daga hka ya fice daga palon, junaid ya bi bayansa ya fita ya kulle gidan. Har suka isa gidan El-Ameen bbu wanda yace komai sae Junaid dake juyawa lkci lkci yana kallon mahaukaciyar, El-Ameen ya dauko makulin gidan dake motarsa ya fita ya bude gate don bbu kowa gidan, dawowa yyi cikin motar ya shiga compound din da motar, yana gama parking ya juya yana kallon Junaid yace 'Ohhw ni! yanxu mahaukaciya ce mace ta farko da xata fara shigar min gida bayan mahaifiyata maimakon matata" Junaid bae tanka sa ba, El-Ameen yyi tsaki yana girgixa kai ya fito daga motar ya nufi cikin gidan, Junaid ya fito ya bi bayansa, a balcony ya tsaya ya canxa change over din gidan don akwae wuta, ya juya yana kallon Junaid yace "Toh ni xan fito maka da mahaukaciyar?" Junaid ya girgixa kai ya juya ya koma gun motar, bae sha wahalan daukota ba don sosae El-Ameen ya daureta kuma duk tayi laushi, ihu take tana shure shure har suka shigo falon ya direta k'asa yana kallonta, El-Ameen ya rike haba yana kallonta yace "Ikon Allah, muna xaman xaman mu Junaid ya ja mana!" Juyawa Junaid yyi yana kallonsa, El-Ameen yyi tsaki ya nufi stairs, Junaid ya lumshe ido ya bude ya bi bayansa, daki ya samesa ya bude drawern kayansa da alamar kaya xae canxa, Junaid yace "It's late ynxu, muyi freeing dinta sae mu wuce koh" El-Ameen yace "wait tukun! Wae kai xaga dinga tsayawa da ita a gidan?" Junaid ya d'an yi shiru yana kallonsa, sae kuma ya sauke ajiyar xuciya yace "No, xan sa a samo min yar dattijuwa dat will be staying, nd I will hire a gate man" El-Ameen ya kyabe baki ya cire jikakken shirt din jikinsa da wando ya fiddo wasu kayansa ya sa, sae a snn ya juya ya kalli Junaid da ke xaune gefen gadon dakin yana kallonsa yace "Kai baxa ka canxa kaya ba?" Mikewa Junaid yyi ba tare da ya kallesa ba ya fice daga dakin, dariya El-Ameen yyi sanin haushin sa kawae Junaid ke ji. *Sai dai da aka rushe katangar Chinan dai, ko wani katanga xan kuma cewa Allah yayi min da su*
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
5.....
Falo El-Ameen ya sakko ya samu Junaid tsaye bayan kujera yana kallon mahaukaciyar, El-Ameen yace "Toh ae sae ka dauketa ka kaita spare room ka ajiye ta ka kunce rope din" karasawa falon Junaid yyi, yyi yanda El-Ameen yace masa, yana kunce igiyar a daki ya fice da sauri ya ja kofar, kulle kofar palon El-Ameen yyi bayan sun fito, har lkcn ruwan da ake bae tsaya ba, El-Ameen ya d'an yi tsaki ya sa kai ya shiga ruwan ya nufi gate, bin sa Junaid yyi a baya ba tare da ya damu da hakan ba, sae a snn ya dinga jin sanyi na shigar sa ba kadan ba, El-Ameen ya kulle gate din daga waje bayan sun fito suka shiga mota, suna hawa kan titi El-Ameen yyi murmushi ganin yanda Junaid yake rawan dari, yyi kwafa yace "Ai baka fara rawan sanyi ba tukun malam, sai randa 'Yan gidan ku suka samu labarin mahaukaciyar nan I assure you oven ma yyi kadan yasa ka daina rawan sanyi" Sharesa junaid yyi, El-ameen yyi dariya yana kallonsa yace "Mu je can gidanmu, idan ya so da asuba sae ka koma gida, don kana komawa gida ynxu Mumy ta kama ka har duka na tabbata xata iya maka, ni kam na girma bbu abinda Ummina xata ce min" yana maganar ne yana kyalkyala dariya, shi dae Junaid bae tanka sa ba don sanyin da yake ji ma kadae ya ishe shi, kuma yasan gskya ya fadi yana komawa gida ynxu Mumy xata daga hnkli baxa kuma ta barsa ba sae ya fadi daga inda yake cikin ruwan nn. El-Ameen na gama parkin a parking lot din gidansu ya juya yana kallon Junaid yace "Let move in frnd" bude motar Junaid yyi ya fito ya nufi cikin gidan da sauri don ba karamin sanyi yake ji ba, bbu kowa palon ya nufi dakin El-Ameen, bathroom ya shiga ya hada ruwa me dumi sosae yyi wanka, ko da ya fito El-Ameen na xaune yana shan tea, ya fiddo rigan sanyi babba a closet bayan ya goge jikinsa ya sa, wayarsa ya dauka yana dubawa ko bae jike ba snn ya ajiye gaban mirror ya dawo yyi kwanciyarsa ya ja bargo ba tare da ya kalli El-Ameen ba, El-Ameen yace "Baxa ka sha tea'n ba?" Share sa Junaid yyi, El-Ameen yyi murmushi sanin baxae kulasa ba yace "Toh fa gwara ka tashi ka sha magani kar ka k'asa tashi gobe, ana kuma tambayata ba'asi xan tona wllh" Dariya El-Ameen ya dinga yi jin Junaid bae tanka sa ba still, ya mike ya dauko paracetamol ya dawo da Goran ruwa ya xauna gefensa yace "Look frnd, tashi ka sha drug kafin ka kwanta kar ka tashi da mura gobe, yhu knw I may be annoying a times" yana murmushi ya kare maganar, mikewa Junaid yyi ya karbi maganin da ruwa ya kora ya koma ya kwanta don shi kansa yasan without dat baxae tashi lfya ba gobe. Washegari da asuba kafin ayi sllh Junaid yace xae tafi bayan ya daura alwala yyi Raka'atainil fajr, bae yarda ya dau motar El-Ameen ba don yasan hkn na iya tona masa asiri, ko mum din El-Ameen bata san yana gidan ba, El-Ameen ya rakasa bakin titi ya tsayar masa da a dai daita don ca yyi bae iya ba. Ana kokarin tada sllh ya iso anguwarsu na Government reserve area, masallaci kawae ya shiga, ana idarwa ya dde xaune yana Azkar har ya ga fitan Abbansa snn ya mike ya bi bayansa, part dinsa ya nufa ya gaishesa ya amsa masa snn yace "Kana mura ne Ahmad?" Junaid ya girgixa kai yace "Ya ma yi sauki Abba, ina shan magani" Abba yace "Gud! Babu damuwa ko?" Junaid ya shafa kai yace "Ehh Abba!" Abba yace "To Allah maka albarka" Junaid yace "Ameen Abba," Abba yace "Gobe xan fita xuwa Germany, tafiyar ya xo min da gaggawa ne, as usual am handing the family over to yhu son" Junaid yace "Toh Allah kai mu Abba, journey mercy dad, in'sha Allah" Abba ya shafa kansa yace "Ameen dear son" mikewa Junaid yyi yace "It's almost daybreak Abba, bari in je in shirya xuwa aiki" Abba yace "Its ohk, stay blessed" fita yyi ya nufi bangarensa, cikin mintunan da basu fice ashirin ba ya shirya cikin uniform dinsa na dark navy blue trouser da light blue shirt, kadigan yasa navy blue bayan ya feshe jikinsa da turare ya rike hularsa a hannu, waow yyi kyau har ya gaji lips din nan nasa kamar ya shafa jan baki, ya bude manyan idanuwansa sanin bae shafa komae ba ya daga kafada ya fita xuwa side din mum dinsa, fatima dake shara a balcony ta gaida shi, ya amsa ya shiga parlon, Mumy na jera masa breakfast dinsa a dinning ya sameta, ya nufi dinning din ya mata side hug ya kwanta jikinta a hankali yace "Sabahul khair Ummu na" Mumy tayi murmushi tace "How are yhu, baka rufe windows bne jiya naji kmr mura na neman kama ka" shagwabe mata yyi yace "Na rufe mana Mumy," ta hararesa tace "Toh ka bar Ac a kunne ko" ya girgixa kai yace "Not at all mum, kinsan ynxu lkcn ruwa ne kuma tun da na dawo ciki nake fita aiki shi yasa kmr muran ke son kama ni" tace "Toh I will get yhu an umbrella don ban ga amfanin Raincoat din da kake sa wa ba" yace "A'a ni nafi son raincoat dina, umbrella sae kace mace mumy" tace "Toh idan na baka kar kayi amfani da shi" langwabar da kai yyi ya xauna yana kallon ynda take hada masa tea, plate din potatoe'n da ta xuba masa ya jawo ya shiga ci yace "Aisha ta koma ne Mumy?" Mumy tace "Tun jiya" daga haka ta bar dining din ta shiga daki, a hnkli junaid ya ajiye fork din hannunsa tunawa da mahaukaciyar da suka dauko jiya da yyi, har Mumy ta fito bai kuma cin komai ba, ta kalli agogo ta kallesa tace "Kana kallon agogo dai koh" yyi yake ya ci gaba da cin potatoe'n, tutturawa kawae ya dinga yi don neman appetite yyi ya rasa, ya mike yana goge bakinsa da tissue yace "Allah amfana momy, thnks a lot" tace "Welcm, but make sure ka shiga ka gaida mutan gidan yau" d'an hade rae yyi amma da yake baya mata musu cewa yyi "Toh mumy" ta rakasa har balcony, yyi side din stepmums din nasa, bangaren Hajiya Fatee ya fara shiga tana xaune da Muhibba a palo da Rabi'a dake gugan Hijab, ya xauna kan kujera hannunsa rike da hularsa me kaman face cap me dauke da symbol din captainship a jiki, yyi k'asa da kai yace "Ina kwana Hajiya" a dakile tace "Lfya lau d'an gwal" hade rae yyi yana jujjuya hular hannunsa, Rabi'a tace "ina kwana ya Ahmad?" Yace "Lfya lau ya sch?" Tace "Alhmdllh" Muhibbah dake ta kallonsa ko kiftawa bata yi ganin ko kallon inda take bae yi ba cikin wani siririn murya tace "Ina kwana ya A.jay" ba tare da ya kalleta ba yace "Lfya lau" sae kuma ya mike ya nufi kofa yace "Na tafi aiki Hajiya," bata tanka sa ba har ya fita, Muhibba ta kalli Hajiya tace "Hajiya kinga ko amsa gaisuwata bai son yi ma" Hajiya Fatee tayi wani murmushi mai wuyar fassara ba tare da tace komae ba, Rabi'a tayi 'yar dariya tana guganta tace "Aiki" harara uwar ta wurga mata, ko sanin tana yi bata yi ba, part din Hajiya Bilki Junaid ya nufa, bbu kowa palon ya nemi gu ya xauna yana kallon agogon wrist dinsa, daga kitchen khadija ta fito ta d'an wara ido tace "Lah ya Ahmad ashe kana nan, Gud morning" yayi murmushi yace "Morning lil sis, ya sch?" Ta karaso kusa da shi ta shagwabe murya tace "Lfya lau, plss yaya ka d'an min transfer din 5k frnd dita na birthday gobe xan siya mata perfume" yace "Kije ki samu Abba mana ae bai tafi ba" ta d'an bata rai tace "Shekaranjiya fa ya canxa min phone" yace "Ohk ltr" Hajiya bilki ce ta shigo palon, kallo daya tayi masa ta dauke kai, tana kallon Khadija tace "Ke don uwar ki me ya hada ki da Suhaima kike mata fitsara?" Khadija ta hade rai ta juya ta koma kitchen, junaid yyi k'asa da kai yace "ina kwana Umma" ba tare da ta kallesa ba tace "lfya lau" Suhaimah ce ta shigo palon da alamar muryarsa taji, tace "Ina kwana ya Ahmad" mikewa yyi yace "Lfya lau" daga hka yace "Na tafi aiki Umma" bae jira cewarta ba ya fice, ta bi sa da harara, Suhaimah ta samu waje ta xauna ta xabga tagumi tana kallon Umman. Junaid na xuwa gun aiki ya dauki permission Karfe sha daya ya fito, driving yyi xuwa clinic din dad din El-Ameen, Yana rike da hularsa ya haura sama xuwa office din El-Ameen, Nurses din suka bi sa da kallo ko kiftawa bbu, yana attending to patient ya same sa, ba tare da ya kallesu ba ya shige bedroom, xama yyi yana addu'ar Allah yasa baxae dau lkci da patient din nasa ba, ko minti biyar ba'ayi ba sae ga El-Ameen ya shigo yana kallonsa yace "Ya? Duty din naka ya kuma shifting xuwa yamma ne?" Junaid yace "No of course, yarinyar da muka bari kulle a gida fa?" El-Ameen ya hade rai ya galla masa harara yace "Kaga xaka fara daga ma mutum hankali da sassafen nn koh, Toh me xa ayi mata ynxun? Ba sae xuwa yamma in mun gama aiki ba" Junaid ya girgixa kai yace "Yanxu fisabilillah da xaka fito baka yi breakfast ba Dr? Ita ba mutum bace da xa a bar ta ba ruwa ba abinci har xuwa yamma?" El-Ameen yyi masa wani kallo yace "Toh wai wa ya hana ka xuwa kai mata abincin ynxu, iyaka ka xo kace in baka makullin gida in baka, pls let me be Captain, am getting sick of you," Junaid ya lumshe ido ya rike kansa don walakancin El-Ameen ya fara isan sa, mikewa yyi ba tare da ya kallesa ba yace "Ohk! Bani keyn" El-Ameen ya d'an shafa kai yace "Alryt am sorry, haka ne kuma fa ya kamata a kai mata abinci, tun da ita ma mutum ce kamar Junaid" ficewa Junaid yyi ya bar masa dakin, El-Ameen yyi dariya ya bi bayansa, makullin gidan dake table dinsa ya dauka ganin Junaid ya bar office din shi ma ya fita, kusan a tare suka iso gun motar junaid, El-Ameen ya bude gaba ya shiga, junaid ma ya shiga ba tare da ya kallesa ba yace "Kaga hand me dat key ka fice min a mota" El-Ameen ya gyara xama yace "Toh fitar da ni mu ga" Junaid ya fi minti biyar bae tada motar ba, El-Ameen kuma yaki fita, sanin ba fitan zae yi ba kawae ya tada motar ya ja suka bar asibitin, wani eatry ya fara biyawa ya siyo abinci da ruwa sae hollandia drink, El-Ameen ya rike kai ya dinga dariya da ya ga hollandian, shi dae Junaid bae tanka sa ba, sae da suka dau hanyar gidan yace "kaga malam da ka rufa ma kanka asiri ka bude hollandian nn mu shanye kawae, dama am thirsty, banda haka a ina ta san wani hollandia in ba neman magana irin naka ba" driving kawae Junaid yake bae tanka sa ba, El-Ameen yyi dariyarsa me isarsa yana mamakin Junaid, a waje suka yi Parkin motar, El-Ameen ya bude gidan suka shiga, kallon Junaid yyi da ya tsaya yace "A'a Toh ka shiga gaba mana goga" murmushi Junaid yyi bae ce komae ba yana shafa kai don shi har ga Allah tsoro yake, El-Ameen ya dinga kyalkyala dariya har suka isa kofa Junaid na biye da shi a baya, El-Ameen na bude kofar ya koma baya da saurinsa ya fiffito da ido, Junaid na ganin hka kan kace me sae gashi a tsakiyar compound cikin 'yan sakwanni, El-Ameen ya rike kai yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya nanata hakan ya kusa sau goma, Junaid na daga tsakiyar compound sae tambayar me ya faru yake, cikin tsawa yace "Junaiddd xo ka ga abinda ka jawo min"
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
6.....
El-Ameen ya juya yana kallon Junaid ganin ya ki karasowa da karfi yace "baxa ka xo ka ga abinda mahaukaciyar da ka sa na kawo gidana tayi ba, ya Salam!" Junaid na jin hka ya karaso da sauri yana leka parlon, kwalalo ido yyi yana kare ma palon kallo, palon komawa yyi kamar wanda aka yi karamin yaki, don duk ta tarwatse plasman palon da frames gaba daya, lafiyayyen centre table din ma bata raga masa ba, ko ta ina kwalabe ne a falo, duk ta tuttuge labulaye da karafunansu, kujeru kam upside down ta juyasu dukka, Junaid bae san lkcn da ya fashe da dariya ba har da rike ciki, El-Ameen ya bude baki yana kallonsa idon nan nasa ya kada, fixgosa yyi yana huci yace "Yhu see wat you've caused koh Ahmad, gud! this mad woman is adding not a minute more in my house" yana fadin hka ya turasa ya shiga palon, da sauri junaid ya hadiye dariyarsa ya rikosa yace "Haba frnd, Chill plss ka mance mahaukaciya ce ita kamar yanda kake kiranta, I promise wllh duk xan siya maka abubuwan da tayi damage, that's a promise frnd!" marairaice masa Junaid yyi yace "Plss!" El-Ameen yyi kwafa yace "Yanxu naji bayani, kuma ga motata ma can a gida bbu kyan gani, kasan yanda xa kayi da shi, I need it the way it was before, nd don't forget it's my favourite car" Junaid yyi murmushi yace "Kar ka damu xa a gyara" El-Ameen yace "Gud! Kuma ynxu idan mu ka shiga naga tayi fitsari ko otherwise wllh kai xaka gyara min waje" Junaid ya d'aga kafada yace "Na yarda" Nan El-Ameen ya sa kai ya shiga falon yana bin ko ina da kallo, sae a lkcn ya kula da jinin da yayi littering din falon alamar duk ta ji ciwo, kamar ance ya kalli bayan kofar falon ya ganta durkushe wajen duk jini jikinta, suna hada ido ta mike da sauri xata yi waje ya yamutse fuska ya fixgota da karfi, kokuwa ta shiga yi da shi ya mata wani lafiyayyen rankwashi ae sae ga hawaye a idonta tana kallonsa, Junaid da yyi shiru yana kallonsu a hankali yace "Haba El-ameen rankwashi kuma?" Ko kallonsa El-Ameen bae yi ba, ya ja ta suka koma sama xuwa dakin da aka ajiyeta, bude baki yyi ganin duk ta fasa glass din windunan dakin ma, ita nan duk neman hanyar fita take, kwalo ma Junaid kira yyi da karfi, Junaid ya nufi stairs da sauri ya haura ya shiga dakin, El-Ameen na huci yace "Ohh my God! Dubi windows dina Captain" Junaid ya langwabar da kai yace "Duk xan gyara maka as soon as possible" El-Ameen yyi kwafa yace "Allah kar ya wuce kwana biyu, kuma ni ka xo ka ajiye mata abincin my frnd, I have important things doing a office" karasowa Junaid yyi ya ajiye abincin ya bude yana kallon yanda ya rike hannunta gam sai mutsu mutsu take, El-Ameen ya kai ta k'asa ya nuna ta da yatsa yace "Wllh Kika sake min barna a gidana sae na gaggalla maki mari, wawiya kawai" ita dae kanta na k'asa, tsaki yayi ya mike yana kallon Junaid yace "Mu je plss malam gashi ka kawo mata abincin hankalinka ya kwanta" Junaid yace "But ya kamata mu samo 'yar dattijuwa yanxu koh?" Wani kallo El-ameen yayi masa yace "Ya kamata dai ka samo" daga haka ya fice daga dakin, Junaid ya bi sa da kallo sannan ya kalleta, har lokacin bata d'ago ba, abincin ya matsar mata gabanta a hankali yace "Ki ci abinci kin ji, we are only helping yhu Baiwar Allah" ita dae kanta na kasa sai d'ada takurewa waje daya take, kwala masa kira El-Ameen yyi ya fito da sauri, El-Ameen ya sa ma dakin key yace "barnan ya tsaya iya dakin" shi dae Junaid bae ce komae ba har suka fito, El-Ameen ya tafi gun tap din dake compound din gidan ya wanke hannunsa yana tsaki ya nufi gate Junaid na bin bayansa, a cikin mota El-Ameen ya ciro waya ya shiga neman nmbr, yana dialing ya sa hands free, sallama aka yi masa ya amsa yace "Jibril kana ji na," d'aga daya bangaren aka ce ehh oga, yace "Gud mai gadi nake son ka samo min nan da 'yan awanni don Allah, wanda ka sani kasan halinsa fa" D'aga daya bangaren aka ce "Toh oga, in'sha Allah xa ayi hkn" katse wayar El-Ameen yyi, Junaid ya tada motar suka bar layin, sae da ya fara ajiye El-Ameen clinic bbu wanda yace ma kowa komae, yana fice masa a mota ya ja motar ya nufi office shima, El-Ameen yyi murmushi yace "Ina xaune xa ka dawo ka same ni ne ae"
Karfe hudu da rabi Junaid ya koma gida daga gun aiki, tunaninsa daya karyar da xae ma Mumy ta bar shi ya fita, don ryt from time shi ba mae xuwa ko ina bane daga gun aiki sae gida sai in kuma yaje kallon kwallo shi ma ba ko da yaushe ba don yafi son kallon a gida, ko da yaushe yana manne da ita shi dai, yawanci ma El-Ameen ne ke xuwa gidansu shi bae fiye xuwa can ba sosae, yana xaune bangaren Mumy bayan ya gama lunch, ita kadae ke hiranta sai fatima dake ta shirin islamiyya, shi kam duk hankalinsa baya tare da shi kawae ya kafa ma tv ido ne kmr me kallo, agogo ya duba ya ga har biyar, ya fiddo waya ya kira lambar driver yace ya xo ya samesa bangaren Mumy, ba a dau lkci ba drivern ya xo, Junaid ya ciro dubu goma ya mika masa yace "Gashi wannan ka siyo fruits din dare kamar ynda kake siyowa ka kai ma kowa nasa" Drivern ya risina ya karba yace "Toh yallabai," Junaid ya ciro Atm dinsa yace "ka d'an biya Atm Machine ka ciro min dubu talatin" Drivern ya karba yace "In'sha Allah yallabai" yana fita Mumy tace "Me xaka yi da dubu talatin Junaid" Junaid yace "Su Umma xan ba ko suna bukatar abu kafin Abba ya dawo jibi" Mumy tace "Ohk Hakan yyi" yana xaune sae kallon agogo yake a kai a kai har Ishaq ya dawo da ledoji hudu dauke da fruits kala kala, ya ajiye ma Mumy nata snn ya ciro 30k ya mika ma Junaid, Junaid yace "Yauwa ka raba dubu sha biyar biyar ka kai ma Hajiya daya Umma daya" Mumy tace "A'a kai ya kamata ka kai masu" bae yi musu ba ya karbi kudin hannun Ishaq, Mumy tace "Ajiye naku fruits din ka fara kai masu nasu" Ishaq ya ajiye leda daya ya fita da biyu don kai ma Umma da Hajiya, ba a dau lkci ba ya dawo ya dauki nasu ledan na masu gadi da masu wanki da share sharen gidan ya fita don xuwa su raba bayan yyi godiya. Junaid ya kalli Mumy yace "Mumy xan je gidansu El-Ameen!" Mumy tace "Gidansu El-Ameen kuma, wae wnn sintirin xuwa gidansu El-Ameen da kke kwana biyun nn kalau kuwa Ahmad? Ko dae gun budurwa kake xuwa?" Ta kare maganan tana murmushi, Dariya yyi ya shafa kansa yace "Kai Mumy budurwa kuma, shi dae nake rakawa fa" Mumy na murmushi har lkcn tace "uhn uhn kai dae fadi gskya Ahmad" ya shagwabe mata yace "Mumy ni da gske wllh ba gun budurwa nake xuwa ba, El-Ameen nake raka wa" Mumy tace "In ma gun ta kake xuwa ae ba laifi bne Ahmad, it's high time yhu start planning of settling down with a wife yanxu son" murmushi yyi ya mike yace "Allah ya kawo lkci mumyna" tayi murmushi tace "Toh Ameen" yace "Bari in kai ma su Umma kudin Mumy, daga can xan wuce" Mumy tace "Toh Allah ya tsare kar dae ka yi dare plss Ahmad" yace "In'sha Allah mum" daukan wayarsa yyi ya fita daga falon, gun Umma ya fara shiga ya samu Muhibba ce da wata kawarta a falon, ya wani hade rae ba tare da ya damu da amsa gaisuwar da suka yi masa ba ya mika mata 15k din yace "Gashi ki ba ma Umma" juyawa yyi ya fice daga falon, Kawar Muhibba me suna Salima tace "Kai amma wllh kina bada mata Muhibba, har wannan dan karamin alhakin ne xaki dinga barin yana walakanta ki don yana da kyau, ubansa kuma na da dukiya, sae kace ba gogaggiyar 'yar jami'a ba?" Muhibba tayi murmushi tace "Baki san Ahmad bane Salim, ya fice tunanin ki wllh...." Salima ta katse ta tana kalle kalle tace "Da'alla banxa tsaya ki saurareni, mu je daki in baki wani plan ki ga ko baxae yi aiki ba" mikewa Muhibba tayi suka yi daki da kawar tata cike da xumudin jin plan din. Junaid na fita bangaren Hajiya ya nufa ita ma ya bata kudin, tana jujjuya kudin tace "Duk kudin da Alhaji ya bari Ahmad ka rasa abinda xaka kawo min sae wani shegen dubu sha biyar, wato sauran kuma ka ba uwar ka koh, toh wallahi ka ji tsoron Allah don hakkinmu baxai bar ka ba" Junaid ya daga kafada yace "Ni Abba bae bar min kudi ba, kawae gani nayi hakan ya dace shi yasa na kawo maki na kai ma Umma don ko mahaifiyata ban ba kudi ba gidan nn, gobe ko jibi ae Abban xae dawo, in kina da wani bukatar da ya wuce na wannan idan ya dawo sae ki tambayesa" yana kai wa nn ya fice mata daga palo, ta bi sa da kallo baki bude, idonta ya kankance don bacin rai, rufe bakin tayi tana gyada kai tace "yaro yaro ne" kwafa tayi ta juya ta koma don ci gaba da abinda take tana wani murmushi. Karfe shidda saura Junaid ya isa gidansu El-Ameen sanin ya baro clinic yanxu, Mum din sa ya samu falo, bayan sun gaisa yace "Ummi El-Ameen ya dawo koh?" Hajiya Maryam da ake kira da Ummi tace "Ehh ya dawo daxu amma ya fita yanxun nan, ka kira sa kaji inda yake don nasan baya asibiti" Junaid yace "Toh shknn Ummi xan kirasa, ni xan koma" Ummi tace "Toh ko ruwa baxa ka sha ba Ahmad?" Yyi murmushi yace "Alhmdllh Ummi" Ummi tayi murmushi tace "Toh ka gaida min Hajiya Amina" yace "Xata ji Ummi" fita yyi daga falon yana tunanin inda El-Ameen ya tafi, sae da ya shiga mota snn ya kirasa, bugu daya ya d'aga Junaid yace "Kana ina ne?" El-Ameen yace "Au! ai nayi xaton xuciya kayi ka bar ni da mahaukaciyar taka" Junaid yyi tsaki yace "Kana ina nace?" Dariya El-Ameen yyi yace "Kai dae duk abun ka baxa ka iya xuciya da ni ba wllh, come over ina gidana, na samo mai gadi, ya kuma min hanya an samu wata dattijuwa, we are ol there 2gether ynxu, mind yhu duk wata xaka dinga biyan mai gadin dubu 30, ita kuma warce xata tsaya da mahaukaciyar xa'a bata dubu 50 monthly, coz its not an easy job, ga kuma risk din dake tattare da job din, and yhu make sure ka shiga kasuwa ka siyo mata kayayyakin da xata dinga sawa including inner wears" Junaid yace "Ni ban san inda ake sai da kayan mata ba" El-Ameen yace "So? Ba sae ka ce a raka ka ba, ko ka shiga kasuwar kayi tambaya" tabe baki Junaid yyi ya katse wayar ya kama hanyar gidan. A waje yyi parking ya shiga, sabon mai gadin da ke xaune compound din ya gaishesa da ladabi, Junaid ya amsa ya nufi kofar shiga palo, daga bakin kofar ya tsaya yana kare ma palon kallo, duk an share barnar daxu ko ina yyi fess, kallon El-Ameen dake xaune kan daya daga kujerun falon yana danna waya yyi snn ya karasa shiga falon, El-Ameen ya kallesa yace "Kayan fa, ni fa I can't put her under medication da suturan jikinta, it's very irritating, na dae yi mata alluran barci daxu don ban ga alaman tana yi ba" Junaid ya xauna gefensa yace "Toh don Allah ka raka ni mu siyo kayan mana, serious ban san ina xan samu women wears ba" El-Ameen yace "Nace idan ka shiga kasuwar kayi tambaya mana sae kace ba wayayye ba" shiru Junaid yyi yana kallonsa, wata yar dattijuwa ce da baxata haura sittin ba ta fito daga kitchen da alama ita ce ta yi gyaran gidan gaba daya, gaishe da Junaid tayi, yyi murmushi yace "Sannu da aiki mama" mikewa El-Ameen yyi ya haura sama ba a dau lkci ba ya sakko rike da sabulan wanka tsadaddu da sponge, sae toothbrush da toothpaste yana kallon dattijuwar yace "Mama ga wannan, wanka xa ki taimaka kafin mu dawo, xae kai maki ita bayin yanxu," Matar tayi shiru tana kallonsa sae dae da ganinta kasan a tsorace take, El-Ameen yyi dariya yace "Babu abinda xata maki wllh mama, bacci ae take kuma baxa ta tashi ba yanxu, mu je ki ga" bin bayansa tayi suka haura sama, Junaid ya bi su da kallo kafin ya shafa kansa, El-Ameen ne ya fara shiga dakin snn ita ma ta shiga, tana nan kwance yanda ya bar ta bayan yyi mata allura, idanuwanta duk a rufe, kallon dattijuwar yyi yace "Kinga bacci take ko mama, kuma na gaya maki baxa ta tashi ba sae bayan awanni takwas," kai kawae ta gyada masa, bayi ya nufa ya hada ruwan dumi da yawa snn ya fito dakin ya dauketa ya nufi bayin da ita ya kwantar da ita kasan neat bathroom din ya fito yana kallon tsohuwar da ya sa ma Mama yace "Gata can na kai maki bayin, don Allah ki wanke mata wannan gashin da kyau mama, nasan baxa kiyi wahalan fito da ita ba idan kin gama don bata da nauyi, xan fito maki da bargo kawae ki lulluba mata har mu dawo da kaya" tace "Toh yaro" juyawa yyi ya fita ta nufi cikin bayin. Siyayya ba kadan ba Junaid yyi ma Mahaukaciyar, tun daga kan normal English wears wato dogayen riguna, xuwa mayyukan shafawa, turarruka, da inner wears da jallabiyoyi, har man gyaran gashi da combs duk sae da ya siya da takalma sae huluna da 'yan kunnaye, shi dae El-Ameen bin sa kawae yake yana dariya, ganin har xa ayi magrib yasa El-Ameen yace "Kai koh kayan lefe kake hadawa fa sae haka Junaid, for God's own sake kayan nan sun isa haka it's time for magrib" Junaid ya kallesa yace "Ohk" Karfe bakwae da rabi suka isa gida, shi ma don sun tsaya hanya sun shiga masallaci sun yi sllh snn sun tsaya eatry siyan abinci, xaune suka samu dattijuwar a falo kan dankwalinta alamar sllh ta idar, tayi masu sannu da xuwa, Junaid ya ajiye kayayyakin hannunsa, El-Ameen ya bude wani leda ya fiddo doguwar riga da man shafawa da na kai sae inner wears da turare ya mika ma matar yace "Gashi mama ki taimaka ki sa mata" ta mike tace "Toh" sannan ta karbi kayan ta haura sama, durkusawa tayi gabanta ta yaye bargon da ta rufe ta da shi ta bude tsadadden man da aka bata ta shiga shafa mata jikinta, cikin mintuna da basu fi goma ba ta gama shiryata, ta debi hair cream me yawa ta shafa mata a dogon gashinta sannan ta shiga taje gashin a hnkli saboda tsantsin sa, tana yin haka hawaye na xuba idonta kmr daxu da take mata wanka, rayuwa kenan duk yanayin da ka tsinci kan ka ka gode Allah, Coz he knows best, shi kadae yasan dalilin barin wannan Baiwar Allah haka, ba wae kuma don baya sonta ya bar ta a hakan ba, har ta gama tufke mata dogon gashinta da ya kusa bayanta hawayenta bae tsaya ba, gyara mata kwanciya tayi ta rufa mata bargon ta fito tana kallonsu El-Ameen tace "Na gama" El-Ameen ya mike yace "Kin sa mata komae dae koh mama" tace "Na sa mata" yana 'yar dariya yace "Kin tabbata mama" murmushi tayi tace "Na sa mata komai yaro" kallon Junaid yyi sannan ya nufi stairs, Junaid ya mike ya bi bayansa, El-Ameen na shiga dakin ya karasa gabanta ya durkusa ya yaye bargon dake jikinta a hankali, rike breath dinsa yayi yana kallonta ko kiftawa bae yi har Junaid ya shigo ya same sa a hka, shima ya durkusa a hankali nan gabanta yana kallonta.
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
7.....
Fara ce sosai ba kadan ba don kamar ka latsa ta jini ya fito, dama ashe wahala ce ya maida kalanta baki, ko kadan bata da jiki sai tsayi, bakin gashin kanta ya rufe kusan rabin fuskarta sbda yanda tayi kwanciyar, d'an karamin bakinta me kalan baki da ja Junaid ya kalla yyi murmushi yace "Uhnn! Kamar me hankali koh? Da xata tashi ynxu duk sae mun yi bayani ryt?" murmushi El-ameen yyi ya mike yace "Yea! Exactly!" Juyawa yyi ya fice daga dakin Junaid ya bi sa da kallo sae gashi ya dawo da wasu alluran har uku, ya dawo gabanta ya durkusa, Junaid na ganin haka ya mike ya fita daga dakin, ya sakko palo ya dauki ledan abinci daya ya ba Mama, tayi masa godiya yyi murmushi kawae ya xauna, bayan kusan minti goma El-Ameen ya sakko falon ya xauna gefen junaid yace "Kana ji na, akwae drugs din da xa'a siya har biyar, kuma duk pack daya kusan dubu 40 ne kafin ayi diagnosing dinta...." Junaid yace "Ohk xan maka transfer ltr" El-Ameen ya mike ya dauki ledan abincin da ya rage da ruwa ya nufi sama, ajiye mata yyi bayan ya bude snn ya fito ya sa ma kofar key, ya dawo palo yana kallon Junaid yace "Let leave!" Mikewa Junaid yyi, El-Ameen ya kalli dattijuwar da ke xaune yace "Mama za mu tafi sae gobe, duk buge bugen da xata yi kar ki bude mata kofar" tace "Toh Allah ya tashe mu lfya, yayi maku albarka," duk suka amsa da Ameen suka fita palon. A bakin gate El-Ameen ya tsaya yana kallon Junaid yace "ka ba mai gadi kudi ya siyo ma tsohuwar abinci da safe ya kai mata ciki don am not coming here da safe" Junaid ya ciro dubu uku aljihunsa ya mika ma mai gadin snn suka fita, Suna isa gun motocin su El-Ameen yace "Gobe kuma foodstuffs xaka siya idan xaka xo" Junaid bae ce komae ba ya shige motarsa ya tada ya bar wajen, El-Ameen ya bi sa da kallo yana murmushi, snn shima ya shiga tasa motar. Karfe takwas da wani abu Junaid ya isa gida, bangarensa ya nufa yyi wanka snn ya dauro alwala ya fito yyi isha yana xaune kan darduma ya ji an bude kofar palonsa, bae motsa daga inda yake ba har aka bude kofar bedroom, ya daga kai don ganin waye, Mumy ce ta shigo dakin, yayi murmushi ganinta yace "Yanxu fa xan shigo d'a Mumy" ta xauna gefen gadonsa tace "Sae ynxu kake isha Junaid?" Yace "Mun hadu da traffic ne sosae a hanya Mumy" ta tabe baki ta mike tace "Toh taso mu je ka ci abinci" ba musu ya mike ya linke pray mat din ya ajiye ya bi bayanta, Mai aikinta ce ta dauko abincin nasa daga dinning ta ajiye nan tsakiyar lallausan rug din falon da ya ke xaune, Mumy ta sakko gefensa ta bude warmern dake dauke da Shinkafa fara ta dauki plate ta dibar masa iya yanda tasan xae cinye snn ta bude miya ta xuba masa k'adan a gefe don bae fiye son miya da yawa ba, sae cow meat da ta cika masa a abincin, spoon ya dauka yace "Thanks sweet mum" snn ya fara cin abincin ita kuma ta dauki wayarta da ke ring, ganin Abba ne yasa ta nufi daki. K'asa cin abincin Junaid yyi ya kuma rasa dalilin hakan, ya lumshe ido ya jinginar da kansa jikin kujera, ya kusa minti goma a hka sanin Mumy na fitowa sae ta sa shi ya cinye abincin yasa ya kira mai aikinta, yarinyar ta taho daga dakinta da sauri, ya dauki abincin ya mika mata yace "ina fatima?" Tace "Ta kwanta" yace "Ohk tafi daki ki ci na koshi" ba musu ta koma dakinta da abincin, juice ya diba ya shiga sha a hankali, a hka Mumy ta fito ta samesa tace "Har ka cinye?" Yace "Eh Mumy" ya ajiye cup din hannunsa yana lullumshe ido yace "Nafara jin bacci mumy" tace "Toh Allah ya tashe mu lfya, kayi alwala kafin ka kwanta, don't forget to pray also" ya mike yace "In'sha Allah mum" wayarsa ya dauka ya fita ya nufi side dinsa, sae da ya dauro alwala yyi shafa'i da wutr snn ya kwanta ya ja bargo. Washegari yana office yayi ma El-Ameen transfer din dubu dari da hamsin, yana barin office dama kasuwa ya shiga ya siyo food stuffs sannan ya wuce gidan El-Ameen, mai gadi ne ya shiga da kayan abincin palo, Junaid ya xauna bayan sun gaisa da mama yace "El-Ameen din ya xo ne mama" tace "Eh ya xo da safe, ya kuma xuwa daxu, bae dde da tafiya ba amma yace xae dawo" Junaid yace "Ohk, bacci take ne?" Mama tace "A'a gskya, sae dae yace kar a bude kofar makullin na jiki ma" Junaid yace "Tana cin abinci kuwa?" Girgixa kai tayi tace "Gskya ban sani ba don kifarwa take duka, bana gane ko ta ci ko bata ci ba" Shiru yyi bae kuma cewa komae ba, yana son ganinta amma shi gskya tsoro yake, dama El-Ameen na nan ne, can ya kalli agogo ya ga har biyar yayi, mikewa yyi yace "toh ni xan tafi mama, bbu matsala dae koh?" Tana murmushi tace "Babu komae wallahi" xae yi magana aka bude kofa El-Ameen ya shigo, ya d'an kyabe baki ganinsa, shi dae Junaid bin sa da kallo yayi har ya karaso cikin palon, ledan hannunsa na magunguna ya ajiye yace "Ba dae har xaka tafi ba, kuma kama duba mahaukaciyar taka kuwa?" Junaid ya dauke kai bae ce komae ba, El-Ameen yace "Ehh Lallai ma, wato ni xaka yi ta bari da wahala koh, daxu da safe ma sae da na xo nan kafin in tafi clinic nasan kai ko tashi kila baka yi ba lokacin" yana kai wa nan ya nufi sama, Junaid ya sauke ajiyar xuciya ya bi bayansa, El-Ameen ya bude kofar dakin da key ya tura kofar a hankali, tana xaune ta rakube waje daya bayan ta kuma cire labulayen dakin gaba daya kamar yanda ta saba, doguwar rigar kanti ne jikinta ja da ya haska farin fatar ta, duk ta birkita dogon gashinta kmr ba da safe Mama ta kuma daure mata ba tana bacci, kayan ma da gani ta kasa cire shi ne don duk ta yamutse shi jikinta, El-Ameen ya balla mata harara yace "Wai ke wace irin mutum ce, wllh kika sake cire min labule sae na gaura maki mari, baki da aiki sai barna" Junaid dae na d'aga bakin kofa yana leko dakin, El-Ameen ya kallesa yace "Da'alla matsoraci shigo baxa ta ma komai ba" kin shigowa junaid yayi yace "Nan ma ya isa" El-Ameen ya hade rae yace "Ohh wato ni ne ban san ciwon kai na ba da nake shigowa koh, sae in daina shigowa nima in dinga tsayawa daga bakin kofa in ga ta ynda xa ayi maganin" a hankali Junaid ya d'aga kafa ya shigo dakin yana kallonta sae shishshigewa jikin bango take a tsorace, El-Ameen ya kalli Junaid dake tsaye shi ma duk a tsoracen, Junaid bae ankara ba sae gani yyi El-Ameen ya fixgosa ya tura sa har sae da ya fada kanta, a tare suka kwala ihu daga shi har ita, El-Ameen ya dinga kyakyata dariya har da rike ciki, da kyar Junaid ya mike, ita ma ta yunkura ta mike, tsorata junaid yyi ya nufi bayi da sauri, ita kuma ta wawuri d'aya daga karafunan labulen dakin tayi kan El-Ameen dake dariya har lokcin, xaro ido yyi ya hadiye dariyarsa ganin haka, ya juya da sauri xae fita ae da hanxarinta ta bi bayansa, me Junaid xae ban da dariya, ya dinga kyalkyala dariya ya bi bayansu, har downstairs ta bi El-Ameen, mama na ganin hka ita ma tayi waje da gudu, El-Ameen ya dinga cewa "Junaid wllh ka xo ka riketa, junaiddd" Junaid ya durkusa nan stairs ya dinga dariya ganin yanda El-Ameen ya rude yana xaga palon, ita ko sae binsa take xata buga masa karfen, Hadiye dariyar Junaid yyi ganin El-Ameen ya shige kitchen ya sa key ya barsu su biyun a palon, ta dade tsaye bakin kofar kitchen din, kafin ta juyo tana bin ko ina na palon da kallo, k'asa motsi Junaid yyi daga inda yake xuciyarsa na bugawa, ta jefar da karfen hannunta ganin kofa a bude ta nufi kofar da sauri, Junaid bae san lkcn da ya nemi tsoron ya rasa ba ya bi bayanta cikin hanzari ya riga ta isowa kofar ya rufe gam, juyawa tayi tana kallonsa tana maida numfashi, sae kuma ta fasa wani ihu tayi kansa ta fixgosa, rungumeta yyi ya riketa gam, ta dinga fixge fixge ya ki saketa, Sosae suka jigata daga ita har shi, don kin saketa yyi, ita kuma bata fasa kokuwa da shi ba, daga karshe tayi lamo jikinsa bata sake yunkurin kwatar kanta ba, a hankali ya saketa ta sulale nan kasan palon, hawaye yaga kwance fuskarta, jikinsa yyi sanyi ya durkusa gabanta yana kallonta.
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
8....
Bude kofar kitchen da El-Ameen yayi yasa Junaid ya mike da sauri ya koma baya, El-Ameen ya tsaya daga bakin kofar yana mata wani irin kallo yace "Wato ni ta raina xata kwale koh?" Junaid yayi murmushi yace "Kai fa ka tsokaneta gashi ka sa ta xubda hawaye, haba Dr!" El-Ameen ya karaso palon yana kallonta kanta a sunkuye yace "Xa tayi me dalili ne ma ae, ba dae ni xata kwala ma Karfe ba" mikewa tayi tana kallon kofa, Junaid ya karasa da sauri ya sa key, kallonsa ta tsaya yi, El-Ameen ya xaga ta baya ba tare da ya bari ta lura ba, ya cafke hannayenta ta baya, ta kwala wani ihu, ya kai mata rankwashi yace "Shut up!" Hade rae Junaid yayi sae dae bae ce komae ba, El-Ameen ya ja ta ya nufi stairs da ita, kokuwan kwace kanta kawai take, ya dauketa cak ya haura sama da ita, Junaid ya lumshe ido ya bude ya karasa cikin palon ya xauna, da kyar El-Ameen ya daure mata hannu, snn ya samu yayi mata allurori guda uku, ta gama fixge fixgenta da ihu ta sulale wajen sae bacci, mikewa yayi daga durkushen da yake yana kallonta, ya karasa inda take ya kunce mata daurin da yayi ma hannunta ya dauketa ya kwantar kan gado, tsayawa yayi yana kallonta ganin yanda dogon gashinta ya hargitse, ribbon din da ya gani kasan dakin ya dauka ya karasa gadon ya xauna gefenta ya dago kanta a hankali ya shiga packing din dogon gashin, da kyar ya daure mata sannan ya mike ya gyara mata kwanciya ya fita, palo ya sauko yana kallon Junaid yace "Ina tsohuwar nan?" Junaid bae tanka sa ba, El-Ameen ya tabe baki ya fita waje, xaune ya sameta can gurin wani flower tayi tagumi, ta basa dariya sosae ya karasa inda take yace "Mama nan kika dawo, ae bata komae mama kawae tsokanarta nayi shi yasa tayi hakan" Mama tace "Uhn" dariya yayi sosae yace "Allah kuwa mama, ta ma yi bacci yanxu" Mama tace "Allah sarki" El-Ameen yace "Amma bata cin abinci ko mama?" Tace "Toh gskya ni ban sani ba don xubarwa take" yace "A'a bata ci gaskiya, xan taho da maganin cin abinci gobe, mu shiga ciki to mama" ba musu ta mike ta bi bayansa suka koma palon, mikewa Junaid yayi bayan sun shigo yana kallon El-Ameen yace "Xan tafi ni" El-Ameen yace "Eh nima tafiya xan yi" kallon mama El-Ameen yayi ganin har lkcn dari dari take yace "Na rufe kofar dakin mama, kuma baxa ma ta tashi yanxu ba sae can dare" tace "Toh Allah dae ya bata lfya" yace "Ameen" a tare suka fita da Junaid, ko wannensu ya shiga motarsa ya wuce. Junaid na isa gida bayan yayi wanka ya canxa kaya ya nufi part din mumyn sa, xama yayi gefenta ya kwantar da kansa kan shoulder dinta yace "Gud evenin mum" tace "Evenin dear ya aiki? Yhu are kinda late yau" yace "Yea mum, yau Abba xae dawo koh?" Tace "He said tomorrow da muka yi waya daxu" tace "Kasan Hajja ta xo kuwa" mikewa xaune yayi da sauri yace "haba Mumy, When?" Mumy tace "Kana tafiya aiki daxu da safe" yayi murmushi yace "Amma bata san Abba baya nan ba koh?" Mumy tace "Ta sani mana yanxu dae ka ci abinci ka tafi ka gaida ta tun daxu take shigowa tana tambayar ko ka dawo har ca tayi a kai ta gun aikin naka" dariya sosae Junaid yayi yace "Ta hakura ta dawo nan din kenan" Mumy tayi murmushi tace "Nima haka nace, tace inaa kwana biyu kawae xata yi ta koma" Junaid yace "Lallai Hajja" mikewa yyi ya nufi dinning, cikin 'yan mintuna ya sakko yace ya koshi, Mumy tace "A'a wannan baka ci komae ba junaid" Da sauri ya nufi kofa yana cewa "Allah Mumy na koshi" bin sa da kallo tayi kafin ta tabe baki, yana fita ya nufi part din grandmum dinsa, ya tura kofa da sallama ya shiga palon, tana xaune sanye da glass din ido tana dama fura, cire glass din tayi tana kallonsa, yayi dariya ganin irin kallon da take masa ya dauke furan gabanta ya rungume ta yayi pecking goshinta yace "Oyoyo granny" ta tsuke fuska tace "Ni dae daga ni Amadidi" saketa yayi ya daure fuska yana kallonta yace "Wai baxa ki bar kirana da wannan sunan ba Hajja" tace "Toh toh Junaidu, shikenan?" bude baki yayi yace "Xan fa sa asa min ke a guard room in jefa ki cikin ruwa ko don baki ganni da uniform din ba" washe hakora tayi tace "To yi hakuri soja" dariya yayi yace "Ya mutan Daura Hajja?" Tace "Wannan kuma sae ka shirya ku je kai da ubanka" Junaid ya tabe baki yace "Toh ni dae yi ki dama furar ki debar min nawa" hararansa tayi tace "A'a wannan na ni da jikata ne" yace "Wace haka" Hajjo ta juya tana kallon kofar daki tace "ke fito ki gaida yayanki 'yar nan kina jin ya shigo kin yi mukus a daki" Junaid yace "Wacece?" Kwalo mata kira Hajjo tayi kusan sau uku sae ga ta ta fito ta karaso cikin palon ta xauna kasa jikin kujera ta hade rai tace "Na'am" kallonta kawae Junaid yake ganin ynda take rurrufe fuska da hijab yace "Wacece wannan kuma Hajjo" Hajjo ta washe baki tace "ehh baka santa ba gaskiya" sae kuma ta hade rae tace "barin ma kai da ba shiga yan uwa kake ba, ga ka kai daya namiji gun Muhammad kmr tsiya, maimakon ka dinga shiga yan uwanka ku saba, ko da yake tana karama ka santa, 'yar uwar ka ce Humainah, 'yar wajen kawun ka, kuma matar da na xaba maka" fashewa da kuka yarinyar tayi ta mike tana kallon Hajjo tace "Ni bana son haka fa Hajjo" daki ta nufa da sauri tana kuka, Hajjo tace "Au! Ji shirme" Junaid ya tabe baki yace "Ni dae ki dama fura ki sammin inyi tafiya ta" Hajjo tace "kai ba fa xancen wasa ba, ita na xaba maka matsayin mata tunda ka ki fito da matar aure godai godai da kai" yace "Toh bana so!" daga can cikin daki yarinyar tace "Ni ma bana so!" Hajjo ta fashe da dariya tace "Au, naga ko in ku kuka haife kan ku, xumunci ne dae sae na hada" tsaki Junaid yayi ya mike ya fice daga palon tana kiransa ko waiwayowa bae yi ba, Hajjo tace "Ahaf abinda ma a gidan xan bar ta ta kare secondary ayi auren kawae" yarinyar ta kuma rushewa da kuka tace "Wallahi baxan tsaya ba Hajjo ni ki maida ni gida kawae" Hajjo ta tabe baki tana ci gaba da dama furar ta tace "Kwa yi ku kare" Junaid na komawa part din Mumy ta bi sa da kallo ganin mood dinsa, tace "Ya aka yi Ahmad?" Cikin bacin rae yace "Wae kina jin Hajjo ta kawo wata yarinya wae xata ce a hadani da ita" dariya Mumy tayi tace "Kai kanwarka Humainah ce fa, 'yar gidan kawu Bala" Junaid ya xaro ido yace "Au ita ce ta girma haka mumy?" Mumy tayi dariya tace "Ita ce mana" ya d'an tabe baki yace "Mumy wani colleague dinmu bae da lfya, xan je duba sa" Mumy tace "Ayya, toh Allah basa lfya, my regardz" mikewa yayi yace "Ameen Mumy sae na dawo" fita yayi rike da makullin motarsa, kallo daya yyi ma Suhaima dake xaune balcony mac book a gabanta, ya shiga motarsa ya tada ya fice daga gidan bayan mai gadi ya bude masa gate, kafin ya isa main road ya kira layin El-Ameen, bugu biyu El-Ameen dake xaune kasa gaban mahaifiyarsa ya d'aga bayan ya nemi ixinin yin haka, Junaid yace "Kana clinic koh gida?" El-Ameen yace "Ina gida" katse wayar Junaid yayi, El-Ameen ya kalli Mum dinsa da ta wani hade rae, sannan yayi kasa da kai, tace "Yauwa, in kuma ban isa da kai bane sae ka sanar da ni in ji" marairaice mata yayi yace "Wllh Ummi ranan mun je, tare da Junaid ma muka je, ae yanxu xae xo sae ki tambayesa ki ji" Ummi ta watsa masa harara tace "Ku ka je ina, ba duk jirgi daya ya kwaso ku kai da Junaid din ba, kuma ni bance ae baka je ba, Ca tayi dariya kuka dinga yi mata kai da Junaid din" xaro ido yayi ya bude baki yace "Dariya kuma Ummi, wllh fa mun mata magana" ta galla masa harara tace "Da'alla rufe min baki malam, da ban san ka da sakarci bane, sannan ka kuma tafiya da d'an uwanka sakarai kamar ka" Murmushi El-Ameen yayi yana shafa lallausan gashin kansa, Ummi tace "Kuma Dad dinku yace baka xuwa clinic da safe kwana biyun nan, sannan baka ma xaman clinic din during day time, nan kuma da sassafe kke barin mana gida, ina kake xuwa Ahmad" shiru yayi na wani lokaci kafin ya hade rae yace "Nurses din ne suka gaya masa haka koh?" Ummi tace "Dake shi makaho ne ba" shiru El-Ameen yayi bae ce komae ba, dae dae lokacin da Junaid ya shigo palon, ganin El-Ameen xaune kamar me neman gafara yasa yayi kasa da kai yyi hanyar stairs sanin sanin sai Ummi ta iya hadawa da shi kai kace shi yayi laifin, Ummi ta bi sa da harara tace "Dawo nan ina xa ka? ka wani yi kasa da kai kmr munafuki" dariya Junaid yayi yana shafa kai, ya dawo cikin palon yace "Laifi ya maki ko Ummi?" Ummi tace "Xauna nan!" Ba musu ya xauna gefen El-Ameen, Ummi tace "Ranan da ku ka je gidansu iman sa ta gaba kuka yi wae kuna ta dariya koh?" Junaid ya xaro ido yace "Dariya kuma Ummi, ae ko mun yi magana me ma'ana, nine ma nayi maganan don shiru El-Ameen yayi" Ummi bata san lkcn da tayi murmushi tana kallonsu ba, ta girgixa kai tace "Ahaf ai magana ta lalace tunda kai kayi! Wato ku baxa ku yi ma kanku fada ba ko, babu me ba wani shawara cikin ku kan ya kamata ku ajiye iyali yanxu," Junaid yayi kasa da kai yace "Ina yi masa wallahi Ummi" harara ta xabga masa tace "Common keep quiet my frnd ai har kai" El-Ameen yayi murmushi shi ma yayi kasa da kai, Ummi tace "Toh gaskiya it's high time ku san me ku ke, don ku ba yara bane, and yhu guys ain't getting younger, ku yi ma kanku fada ku fito da mata kuyi aure abun ku, as a mother nake gaya maku haka, in ma baka son Iman din sae ka nemo wata very soon, kai ma Junaid kayi kokarin yin hakan kafin wata uku, I want to see my boys getting married soon, in kuma kun ban wuka da nama sae in nemo maku mata wallahi" a tare kamar sun hada baki suka ce "A'a Ummi" dariya tayi tana kallonsu, Junaid ya shafa kai yace "In'sha Allah Ummi xa muyi ynda kuke so" tace "Toh Allah yasa, ya bamu aron ran ganin bikin boys dinmu" dariya suka yi gaba daya, Ummi tace "Toh ku tashi ku tafi, Allah maku albarka" mikewa suka yi suka nufi dakin El-Ameen bayan sun amsa da Ameen, xama Junaid yayi gefen gado yana kallon El-Ameen dake kakrin kunna desktop dinsa yace "Baxa mu je can gidan ba?" Ba tare da El-Ameen ya kallesa ba yace "Kai ka tafi mana, kaga ni am busy" Junaid bae ce komai ba sae kallonsa da yake, shi kam sae danne dannensa yake ba tare da ya damu ba, Junaid ya mike yace "Ohk am off" El-Ameen yace "So early, to ka gaida Mumy" Junaid bae tanka sa ba ya fice, El-ameen ya bi sa da harara yace "You think kowa ma bai da aiki kamar ka sai na mahaukaciya yanxu" Ummi dake Palo har lkcn ta kalli junaid tace "Har ka fito?" Junaid ya dan yi murmushi yace "Dama sako na xo karba Ummi, sae gobe" tace "Toh Allah ya kiyaye, ka gayar min da Hajiyar ka" yace "Xata ji." Sannan ya fita.
? *Captain_Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
9.....
Gida Junaid ya nufa, yana gama parkin ya fito ya shiga bangaren Mumy ya gaida ta sannan ya tafi nasa part din, kwanciya yayi Palo ya lumshe ido, ko minti goma bae yi da kwanciya ba wayarsa ya soma ringing, daukar wayar yayi yana kallon mai kiran nasa ya ga abokinsa ne Faisal, d'agawa yayi yace "Yane Faisal!" Faisal yace "Are yhu at home capt?" Junaid yace "Yea ina gida" Faisal yace "Ohk gani nan shigowa" daga haka ya katse wayar, bayan minti takwas Faisal ya shigo palon, Junaid ya mike xaune yana kallonsa yace "Daga ina haka" Faisal ya xauna yace "Gida mana tun da kai baka neman mutane sae El-Ameen" Junaid yayi dariya yace "Kai haba ko ranan da daddare ban kira ka ba" Faisal dake kokarin kira a wayarsa yace "Really!" kallonsa kawae junaid yayi yana murmushi, faisal yace "Hello Muhibba gani gidan ku part din Captain" daga haka ya katse wayar, Junaid ya hade rae yace "idan gun ta ka xo ba sae ka je can bangarensu ba xaka wani kira min ita nan" faisal yace "Chill guy sako xan bata" ko rufe baki faisal bae yi ba sae ga ta ta shigo, murmushi dauke fuskarta tace "ashe da gaske kake" hade rae sosai Junaid yayi ya jawo waya yana dannawa, faisal ya ciro waya aljihunsa ya mika mata yace "Gashi nan na bada an gyara maki" ta wara ido ta karbi wayar tace "Waow am so happy ya faisal, kuma nawa?" yace "No don't bother" tace "Toh na gode kwarai, ya salima fa?" Yace "Tana gida," kallon Junaid tayi tace "Sannu ya Ahmad" ba tare da ya kalleta ba yace "Yauwa!" Tayi niyyan xama palon amma sanin junaid sae ya iya gwaleta yasa ta juya kawae ta fita tana tunanin yaushe ne wannan ranan da junaid xae fara sonta kamar yanda Hajiya ke yawan assure dinta. Faisal yace "Fatee fah?" Junaid yace "Oho!" Sae bayan Magrib faisal ya bar gidan bayan sun shiga ya yi ma Mumy sallama ya kuma shiga part din Hajja ya gaidata, a tare suka fita bayan Junaid ya ce ma Mumy bari ya rakasa, sai dai rakiyar iya bakin gate yyi sa, yana ganin tafiyar Faisal ya nufi titi don yasan in har yace ma Mumy fita xae yi sai ya amsa query, kalle kallen abun hawa ya shiga yi ya rasa yanda xae ce su tsaya, can dae wani mai adai daita ya tsaya yana tambayarsa ina xa shi, shiga kawae Junaid yayi yana kallon mai adai daitan yace "Mu je" sae da suka dan yi nisa kafin ya gaya masa inda xa shi, suna isa junaid ya sauko ya fara dube duben kudi a aljihu, dubu daya kawae ya gani aljihun nasa, mika masa yayi a hankali yana kallon mai adai daitan yace "Kayi hakuri malam ban san ban fito da kudi ba, dubu daya ce a hannu na nagani" dariya mai adai daitan yayi ya karbi kudin, ko ba a gaya masa ba yasan junaid sabon shiga ne a tricycle, canjin dari shidda ya mika masa yace "Ga canjin ka bawan Allah" dan xaro ido Junaid yayi ya karbi kudin yace "Har canji gare ni? Toh na gode" mai adai daitan yayi murmushi ya ja machine dinsa ya wuce, Junaid yayi mamakin ganin motar El-Ameen a parke waje, shi da yace baxae xo ba kuma, tabe baki yayi ya shiga gidan, mama ce xaune Palo ita kadae Junaid ya gaisheta da ladabi, ta amsa tana murmushi ta tambayesa ya aiki, Junaid yace "Lfya mama, ya kamata a siyo maki tv ya dinga debe maki kewa koh" dariya tayi tace "lallai kam" Junaid yace "El-Ameen ya xo ne" mama tace "Eh yana sama" mikewa junaid yayi sae dae duk bae da kuxari ya nufi saman, a hankali ya tura kofar dakin yana kallon ciki, xaune ya ga El-Ameen gabanta ya tankwashe kafa plate din abinci a tsakiyarsu hannunsa rike da spoon ga wayar rechargeable dake gefensa, ita ma xaunen take ya daure mata hannu sae shisshigewa jikin bango take hawaye kwance fuskarta, duk gashin kanta a birkice yake, Junaid ya rungume hannayensa yana kallon El-Ameen, El-Ameen yace "Uhnn! yau baka kwanta da wuri ba kenan mumy's boy" junaid dae bae tanka sa ba ya maida kallonsa kanta ganin yanda take kokuwa da bango kamar xata shige ciki, yunkura tayi xata mike El-Ameen ya daka mata tsawa ya dauki wayar rechargeable din gefensa ta koma da sauri ta xauna, shinkafar ya diba ya kai mata baki, ta dinga kauda kai tana boye fuska, tsawa ya kuma yi mata ya juyo da kanta ya matse bakinta har sai da ta bude ya xuba mata abincin da sauri, murmushi Junaid yayi ganin yanda jikinta ke rawa tana hadiye abincin ba tare da ta tauna ba, da ganinta kasan ba karamar matsoraciya bace, Haka El-Ameen ya dinga mata har sae da ta ci kusan rabin abincin sannan ya mike yana kallon Junaid yace "Bata cin abinci shi yasa na mata haka," Junaid ya buda manyan idonsa yace "So yhu do really care ashe haka?" El-Ameen yayi dariya yace "Darajar ka take ci ae" Junaid bae kuma cewa komae ba sae kallonta yake duk da ba ganin fuskarta yake ba don dogon gashin kanta ya rufe fuskar, wasu allurai biyu El-Ameen ya fiddo ya shiga hadawa, ae tana hango alluran ta mike tayi kofa da gudu, fixgota El-Ameen yayi don shi Junaid hanya ma ya bata da sauri, El-ameen ya jefa ta kan gado, yana hararan Junaid yace "kaji d'an iskan hanya ma ya bata" Junaid yayi dariya yana shafa kai, ta fasa wani uban ihu da ya tsorata Junaid xata mike El-ameen ya hau gadon ya rike ta yana mata wani mugun kallo yace "Keehh", Ribbon dinta da ke kan gadon ya dauka ya shiga daure mata gashin kanta, yana kallon fuskarta yace "Kika kuskura kika sake cire ribbon dinnan sae na gaggaura maki mari" banda rawa babu abinda jikinta yake tana kallonsa, murmushi yayi ya kwantar da ita a hankali ya kwance daurin hannunta sannan ya juya yana kallon Junaid yace "Miko min alluran ko shi ma tsoron sa kake" Junaid bae ce komae ba ya dauki alluran ya mika masa, juyar da ita El-Ameen yayi xae mata alluran Junaid ya juya ya fita dakin, El-Ameen ya bi sa da kallo sannan ya tabe baki yayi mata alluran, tsam ya riketa a jikinsa ganin yanda take shure shure da ihu, sun kusa minti goma a haka har ya ji duk jikinta ya saki, ya dago fuskarta yana kallonta ya ga bacci tayi, kwantar da ita yayi ya lulluba mata bargo, sannan ya dauki abincin da ta rage da ruwa ya fita ya kullo dakin, xaune ya samu Junaid a Palo, ya ajiye abincin nan tsakar palon yace "Mama a xubar da wannan ta d'an ci kad'an," Mama ta jawo abincin tace "A'a baxa a xubar ba xan ci" El-Ameen bae kuma cewa komae ba, Junaid ya mike yayi ma Mama sae da safe ba tare da ya kalli El-Ameen ba ya fice daga falon, bin sa da kallo El-Ameen yayi sae kuma ya tabe baki shi ma yayi ma mama sae da safe ya fita.
Washegari Junaid ya fito bayan ya shirya cikin khakin sa ya shiga part din mumyn sa, tana jera masa breakfast as usual ya shigo, bata amsa gaisuwar da yake mata ba tace "ka shiga gaida Hajja kuwa?" Girgixa Kai yayi yace "Na ma manta tana nan" Mumy tace "Toh tafi ka gaida ta ka dawo tukun." Ba musu ya fita yayi bangaren kakar tasa, xaune ya sameta Palo tana shan kunu ga kosai cike kula, dariya yayi yace "Dama abinda ke kawo ki gidan nan kenan ae Hajja" kallo daya yayi ma Humainah dake goge goge palon ya dauke kai, ita kam dama ko kallonsa bata yi ba, Hajja ta hade rae tace "Wae baka ga Humainah bane Junaid?" Ya hade rai shi ma yace "Toh ni xan gaisheta?" Hajja tace "Toh ba kai ka xo ka sameta ba" bude baki yayi yana kallon Hajja, ita ko Humainah ta mike ta dauki bucket fuu xata wuce, fixgota yayi ta kusa faduwa ya turata ta xauna nan kasa, bata fuska tayi xata yi kuka, ya hade rai yace "ke yaushe kika girma har kika iya fitsara haka?" Kuka ta fashe da tana kallon Hajja, Hajja ta mike tsaye ta tsuke fuska tace "Kai Amadidi ka fita idona wllh, walakancin da cin fuska har a gabana, a haka xan baka 'yar kaje kana cutar min da ita in shiga uku?" Dariya Junaid yayi yace "Tabdi! Allah ya tsare ni, ke in kin ga matar da xan aura ma wllh kunyar fito min da wannan fitsararriyar xa ki yi" Humainah ta tabe baki tana hararansa tace "Ni ma in kaga saurayina wllh kunyar tsayawa gabana xa kayi" Hajja ta fashe da dariya kyal kyal kyal har da kwanciya, shi ko bude baki yayi yana kallan Humainah da ta wani tabe baki, murmushi yayi ya saketa ya mike ya fice daga palon, Hajja na dariya tace "A'a da ka tsaya mana fitsararre" Humainah tayi dariya tace "Ya fa ji tsoro ne Hajja, shi in banda haske da dogon hanci me garesa xai wani sa uniform da hula ya xo yana d'addaga mana hanci" Hajja tace "Atoh! Gane min hanya 'yar nan, ko ubansa xai burge Oho!" Humainah ta fashe da dariya har da rike ciki.
Da yamma Junaid na kwance palon Mumy bayan ya dawo aiki idonsa lumshe kamar me bacci sae dai ba baccin yake ba, Mumy kuma na kitchen tana ta girke girke don ranan Abba xae dawo, Bude kofar da aka yi ya sa shi bude ido, El-Ameen ya shigo palon da sallama, kallonsa kawae Junaid ke yi bae ce komae ba, El-Ameen ya karaso palon yace "Capt A.jay Murnai!" Da xolaya ya kare kiran nasa, Junaid ya mike xaune yace "Uhm!" Kitchen El-Ameen ya nufa ya tsaya daga bakin kofa yace "Ina yini Mumyna" juyawa tayi tana kallonsa tace "A'a Ahmad yaushe ka shigo?" yayi murmushi yace "Yanxun nan Mumy, ya gida ya aiki" tace "Alhmdllh, ya Hajiyar ka?" El-Ameen ya karasa shiga kitchen din ya mata side hug yace "Tana lfya Mumy, tace a gaishe ki" Mumy tace "Ina ta sa rana xan je can gidan ku Allah bae yi ba" El-Ameen ya sa hannu ya dauki daya daga kajin da take soyawa yace "Bari in d'an d'ana maki ko gishiri ya ji Mumy" dariya tayi tace "Naga alama" ya wara ido ya fice daga kitchen din yana murmushi, gefen Junaid ya xauna yana cin kaxar Junaid xae yi magana aka bude kofa, Hajja ce ta shigo palon da sallama, El-Ameen ya wara ido ya boye fuskarsa bayan Junaid yace "Kai yaushe Hajja ta xo?" Hajja ta cire glass din idonta tana leken El-Ameen tace "Wannan ba gantalallen nan me sunan ka bane Amadi?" El-Ameen yayi dariya yace "Ehh Nine Hajja, ashe kin xo, ae bae gaya min ba" Hajja tace "Toh ko ya gaya maka xuwa xa ka yi, kar ka manta turare ne fa yayi mani iyaka da kai, daga nace ka siyan turare na xama makiyiyar ka, toh Allah yayi mana tsari da irin ku" dariya sosae El-Ameen yayi, Junaid yayi murmushi yana canxa tashan tv, Hajja ta xauna tace "Har yanxu Muhammad din bae iso bane?" Mumy ta fito daga kitchen tace "Kila sae xuwa magariba Hajja" mikewa Junaid yayi ya kwashi wayoyinsa yana kallon El-Ameen yace "Mu je" El-Ameen ya mike, Hajja tace "Au don na shigo shine xa ku watse" Junaid ya balla mata harara yace "Da'alla! Rikicin tsufa ya maki yawa wllh" El-ameen yace "Kyalesa kawai Hajja ta so mu je kar ayi ba ke" Junaid yace "Allah kar ta xo min don rufe kofata xan yi" daga haka ya nufi kofa, El-Ameen ya bi bayansa yana dariya, ta tsuke fuska ta bi su da kallo tace "Wahalallu ko uwar me xasu ban da Allah bai ban ba, kuma naga dai gidan d'ana ne yau nace duk ya kora ku wllh ta xauna!" Mumy tayi murmushi ta koma kitchen. kwanciya El-Ameen yayi a palon Junaid yace "Kana ji na Capt?" Junaid yace "Ina jin ka." "xa ayi diagnosing din patient din ka don in san irin neurological disorder dinta da treatment din da ya kamata in mata, nd dat's money!" Junaid ya dauki remote din hannunsa yayi powering din Tv yace "Aiit! Nawa ake bukata?" El-Ameen ya mike xaune yace "ka turo dubu dari tukun mu ga" Junaid yace "Ohk I will transfer it ltr" El-Ameen yace "Gud! Ko gida xan sa a xo ayi diagnosing din nata, no need of taking her out" kai kawae Junaid ya gyada masa, "Kaga daga nan sae mu san irin uban kudin da xaka kashe" da xolaya El-Ameen ya kare maganar, Junaid yayi murmushi bae ce komae ba.
*Captain_Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
10....
Har Abba ya dawo bayan magrib El-Ameen na gidan, suna gama cin abinci da Junaid suka tafi palon Abba a tare don yi masa sannu da dawowa, Hajja na xaune palon da Hajiya da Umma, Humainah da fatima ma na xaune daga gefen Abba dake ta sauraran xancen da mahaifiyarsa ke masa, khadija da sadiya step sister dinta ma duk suna xaune palon, junaid da El-Ameen suka samu waje suka xauna, El-Ameen ne ya soma yi ma Abba sannu da xuwa ya gaishesa, Abba ya amsa murmushi dauke fuskarsa yace "Kana lfya son? Ya aikin?" El-Ameen yace "Alhmdllh Abba, ya hanya?" Abba yace "Alhmdllh mun gode Allah, jiya mun yi waya da Alhaji Mahmoud yace xae tafi Germany gobe" El- Ameen yace "Ehh gobe xae tafi" Abba yace "Maa sha Allah, Allah ya tsare" Junaid ya kalli Abbansa yace "Barka da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa Ahmad, how yhu?" Junaid ya shafa kansa yace "Alhmdllh Abba, ya hanya?" Hajiya ta d'an tabe baki ta mike, Umma ma ta mike ta fice daga palon. Hajja ta bi su da kallo sannan tayi tsaki ta maida dubanta kan Abba tace "Ni dai Muhammadu matan nan naka basa min abun arxiki wllh, tun da na xo ko ruwan su ban gani ba sai daxu da safe, Amina kadae ce 'yar arxiki take ta dawainiya da ni" siririn tsaki can kasa Sadiya ta ja tana hararan Hajja ta gefen ido ta mike ta fice daga palon. Murmushi kawae Abba yayi ya maida dubansa kan Humainah dake gefensa a kasa yace "ya karatu Humainah? Ss3 xaki yanxu koh?" Hajja ta karbe tace "Ehh ajin karshe xata, tana gamawa sae a hada aurensu da Amadidi sai taje can ta kare karatun a gidansa" da sauri Junaid ya kalli Hajja ya wani hade rae, ita ma Humainah kallon Hajjan ta ke kamar xata yi kuka, El-Ameen ya fashe da dariya, Abba kam murmushi yayi ya kalli Humainah da har hawaye ya cika idonta yace "Kyale Hajja dotana, wanda kike so xa a aura maki kin ji, kuma sae kin fara jami'a ma xaki yi auren," tana goge hawayenta tace "Toh Abba" Junaid ya harari Hajja da ta sake baki tana kallon Abba ya dauke kai, Abba ya kallesa murmushi dauke fuskarsa har lkcn yace "Ae ni baxan ma 'ya yana auren dole ba Hajja, duk abinda suke so shi mu ma xa mu so," murmushi Junaid yayi ya mike yana kallon Hajja da ta wani hade rai, ya kalli El-Ameen yace "Tashi mu je" El-Ameen ya mike yana dariya suka yi ma Abba sallama suka fita daga palon, Hajja tayi kwafa tace "Toh zan ga ko kai ka haifeni kuwa," Bakin mota Junaid ya raka El-ameen yace "Gud nyt!" El-Ameen yace "Aitt, saura kar ka xo can gidan gobe!" junaid yayi murmushi bae ce komai ba, sai da El-Ameen ya ja motar ya bar wajen snn junaid ya juya ya koma gida. Part din Mumy ya shiga ya tarar tana bathroom ya fito ya nufi nasa bangaren. Washegari ya kama Sunday Junaid na gida baya duty, kwance yake palon sa misalin Karfe goma da rabi na safe Khadija ta shigo palon, kasa ta xauna kusa da kujeran da yake tace "Gud morning ya A.jay" yace "Morning baki je islamiyya bane" tace "daxu ae anyi yayyafi shine Abba yace in bari gobe," yace "Keep quiet ba cikin ruwan fatima da Rabi'a suka tafi ba, ina ga gishiri ce ke koh, continue deceiving ur self" shiru ta dan yi tana turo baki sae kuma tace "Ae da yamma xan je" bai tanka ta ba, tayi kasa da murya tace "Yaya dama plss 5k xaka ban xan siya wani takalmi ne plss" wani uban harara ya watsa mata yace "Tashi ki bar min Palo, ke baki da aiki sae dae a baki kudi, beside kije ki samu Abba mana, get out my frnd" marairaice masa tayi tace "Don Allah fa yayana" xae yi magana aka bude kofa Suhaima ta shigo palon cikin wasu shegun English wears lokaci daya wani shegen kamshi ya bade palon, mikewa xaune yayi yana kallon Khadija yace "Naji! naji tashi ki tafi" Khadija tayi murmushi tace "Yauwa ya A.jayy nagode" ta mike ta hade rai tana kallon Suhaima tace "Toh ae sae mu je koh" wani kallo Suhaima tayi mata tace "Wa kike gaya ma haka" Khadija ta ja tsaki tace "Duk inda mutum yayi sae ayi ta bin sa da'alla" bata rufe baki ba Suhaima ta fixgota ta sauke mata mari, Khadija ta dafe kunci tana kallonta, mikewa Junaid yayi ya karaso ya bude kofar ya fixgo Suhaima ya wulla ta waje cikin kakkausar murya yace "Kada ki sake taba ta" Umma dake balconyn ta xaune tare da Hajiya ta mike da sauri ganin abinda ya faru, Hajiya ta bi bayanta da sauri ita ma, a fusace ta karaso bangaren Junaid tana huci tana kallon Junaid dake tsaye bakin kofa har lokacin tace "Kai Ahmad uwar me tayi maka xaka jefota haka kamar pillow?" Suhaima ta fashe da matsanancin kuka, hakan ya kuma harxuka Umma cike da masifa da bala'i tace "Ba magana nake maka ba" kallonta kawai yake bai ce komai ba, idonta ya kankance don fitina ta juya tana kallon Suhaima tace "me ya faru, me kika yi masa?" Suhaima na matsar kwalla ta gaya mata, Umma ta xaro ido tana kallon Khadija dake tsaye bayan Junaid a tsawace tace "ke har abun farin cikin ki ne bare yayi ma 'yar uwar ki wannan cin mutuncin Khadija, to don uwar ki fito kar in karya ki palon nan, Shegiya me halin banxa, fito nace" Hajiya tace "Ke dae sallamammiya ce wllh khadija, munafuka wawiya kawai" Hajja ce ta leko jin surutai, ganinsu tsatstsaye part din Junaid ta fito da sauri ta karaso tana tambayar me ya faru, ko kallonta su Umma basu yi ba, Umma na kallon Khadija tace "baxa ki fito ba sae na maki lahani a palon nan?" A fusace Hajja tace "Yau na ga bala'i, ta ya xa ki ce ta fito palon d'an uwanta, ke kin isa ki shiga tsakaninsu?" Hajiya ta tabe baki ta dauke kai, Hajja ta karasa balconyn tace "Me ya faru khadija?" Khadija tace "Wae fa Hajja Suhaima ce ta mareni shine ya Junaid ya koreta palon, shine fa take kuka haka" Hajja ta xaro ido tace "Ta mare ki? Toh Muhammadu ya fito ayi ta ta kare yau, duk ko wannensu ya kwashe agololinsa a gidan nan don ba gidan ubansu bane nan din, shima maganinsa knn da auren xawarawa, haka kawae xa a sa mashi 'ya ya a gaba, kuma bari kiji abinda baki sani ba Bilki, wllh Khadija ta fi kusanci da Ahmadu a kan da warcan bakar yar taki a gidan nan, don uba daya ba wasa bane" ae sum sum Hajiya Fatee ta bar wajen, Mumy ce ta fito jin hayaniya ta karaso da sauri tana tambayar abinda ya faru, Hajja ta shiga mata bayani cikin fada, shiru Mumy tayi tana kallon Junaid, Umma ta fixgi hannun Suhaima suka bar wajen tana huci, Hajja tace "haka kawae, xata kawo mana agola a gida ta adaddabe mu, ita ma wancan mai kama da kutaren ma haka ta kawo nata agolar, duk an cika masa gida da agololi," juyawa tayi tana kallon Khadija tace "Toh wllh ki rike d'an uwanki, don shine dolen ki kuma kun fi kusanci da shi akan wancan bakar don uba daya ba wasa bane" tana kai wa nan ta nufi bangarenta kamar xata tashi sama, Humainah dake tsaye balcony tana kallon film din sae dariya take, Fitowa Khadija tayi daga palon ta bi bayan Hajja don tasan ko hauka take baxa ta nufi sashinsu yanxu ba, Mumy ta sauke ajiyar xuciya ta karasa cikin palon Junaid ya bi bayanta, a hankali ta soma magana tace "Ahmad ina raba ka da shiga tsabgan mutanen nan baka ji koh, ba sonka suke ba kai kanka ka sani, ina ruwanka da shiga tsakanin Khadija da 'yar uwarta?" Junaid yace "Marinta fa tayi Mumy" Mumy tace "koma dai meye ni dae ka kiyaye su bbu ruwanka da su, tsakanin ka da Khadija daban tsakanin Khadija da Suhaima daban" yace "Toh shknn Mumy kiyi hakuri," juyawa tayi ta fita daga palon, ya koma ya xauna yana kallon agogo don duk ya kagu ya fita xuwa gidan El-Ameen. Har bacci ya fara daukansa yaji ana buga kujerar da yake kwance kai, ya bude ido da sauri ya ga Humainah tsaye kansa, mikewa xaune yayi, ta rufe bakinta da hannu tana 'yar dariya tace "Dama haka kake bacci baki bude" shafa kansa yayi yyi saurin fixgota ya xaunar da ita kasa, kara tayi tana kiran Hajja, ya hade rai yace "me ya shigo da ke Palo na?" A rikice tace "wllh Abba ne yace in kira ka" yace "A bude kika ga baki na?" Da sauri tace "A'a wasa nake" daga hannu yayi kamar xae kai mata duka ta boye fuskarta tana kiran Hajja, ya saketa yace "Ashe fitsarar ta karya kike yi" shiru tayi bata ce komae ba, ya mike ya nufi kofa, ta bi sa da harara, yana fita ta sa dariya, mikewa tayi tana kare ma palon kallo ko ina tsaf kamar na mace ga kamshi ya kama palon sosai, bedroom dinsa ta nufa, nan ma very neat ta rike kugu tana bin ko ina da kallo ganin how over tidy it is ga kamshi me ddi dake tashi, ta nufi gaban madubi tana kallon turarruka masu tsadan gaske dake jere gaban mirrorn, daukansu ta shiga yi da daddaya tana fesawa don jin irin kamshin su, kala biyu ta dauka ta fito daga dakin da sauri ta fita daga palon ta ja masa kofa, part din Hajja tayi da saurinta. Junaid na xaune kasan lallausan rug din palon Abbansa yana kallon Abban nasa da mamaki jin abinda yake cewa, juyawa yayi ya kalli Umma da ke xaune ta sha kunu palon ga Suhaima ma xaune kasa, Junaid ya lumshe ido don ko kadan bae son a laka masa sharrin abinda bae yi ba a hada sa da mahaifinsa, cikin fada Abba yace "Kana jina kayi shiru Ahmad?" Bude ido yayi a hankali yace "Kayi hakuri Abba hakan baxae kuma faruwa ba in'sha Allah" Abba yace "kasani daga yau matsayin Suhaima daya da na khadija wajen ka, kar in kuma jin wannan shirmen, ashe baka da hankali ban sani ba" a hankali Junaid yace "Kayi hakuri Abba" Abba yace "Xancen banxa kake yi, kuma ka bata hakuri yanxun nan" juyawa yayi yana kallon Suhaima da idonta ke kansa ko kifta wa bata yi yace "Kiyi hakuri" tayi kasa da kai tace "Ya wuce" Abba yace "Tashi ka ban waje" mikewa Junaid yayi xuciyarsa na kuna ya fice daga palon. Part dinsa ya nufa yana shiga Palo yasan an shiga bedroom dinsa, ya karasa bedroom din ya kalli gaban mirror ya ga an dauka turare, kayan jikinsa ya canxa xuwa blue jeans da farar T shirt ya feshe jikinsa da turare ya dauki car key da wayoyinsa ya fice daga dakin. Kulle part dinsa yayi da makulli sannan yayi bangaren Mumy, bedroom dinta ya karasa ganin bata Palo ya sameta tana gyara kayanta a closet yace "Mumy xan dan fita sae na dawo" Mumy ta kallesa sannan ta ajiye kayan hannunta ganin mood dinsa tace "Me ya faru son?" Shiru yayi da farko sae kuma yace "Wae shine xa su samu Abba su ce na doki Suhaima, meyasa idan basu yi karya ba basu ji ddi ba 'yan gidan nan?" Mumy tace "Ae tun ba yau ba na sha fada maka ka daina shiga hurumin da ba taka ba, to yanxu gashi sun hada ka da Abban ka ae" ya fuzar da iska yace "Na tafi Mumy sae na dawo" tace "Ina xaka?" Yace "Gidansu faisal xan je" Mumy tace "Toh shknn kar ka dde, and drive carefully" yace "Ohk Mum" har bakin mota ta rakosa, su Umma dake xaune da Hajiya suka bi su da kallo suna tabe baki, ko kallonsu Mumy bata yi ba har Junaid ya ja motarsa ya bar gidan, Mumy ta koma part dinta, Hajiya ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Wannan Yaro ya xame mana babban obstacle a gidan nan wllh, komae sae yanda yace ma ubansa, idan ba ina bakin ciki da numfashin da yake a duniya ba Shegiya nake" Umma tace "Uhm ke ko ni, da da yanda xanyi da shi da tuni ni dae nayi wllh, don ko uwarsa bata isheni kamar yanda ya ishe ni a gidan nan ba, na tsane shi wllh wllh, ko 'ya yan mu fa Hajja bata ji da kamar yanda take ji da shi wae don yana namiji mu kuma mata gare mu" Hajiya tace "Toh shine kike kokarin ganin yanda xa ki cusa masa Suhaima ya aura kuma" Umma tace "Toh ae ke ma da xae auri Muhibba so kike naga" Hajiya tace "Da kenan ba yanxu ba don nasan hakan ma baxae taba yiwuwa ba, bari mu shiga ciki ki ji shawarar da na yi a kan matakin da xamu dauka kan Ahmad a gidan nan" Umma tace "Toh me muke a nan, mu shiga kawae ki ban in sha" mikewa suka yi gaba daya suka yi palon Hajiya. Gidan El-Ameen junaid ya nufa, yana gama parkin a waje ya shiga ciki, wanki ya tarar mama nayi a compound din na kayansu, ya karasa inda take suka gaisa sannan yace "El-Ameen ya xo ne mama?" Tace "Eh ya xo daxu da safe" yace "Ohk, bacci take yi ne?" Ta girgixa masa kai tace "A'a idonta biyu sae dae ya kulle dakin," cikin gidan ya nufa ya haura sama, sae dae ya kasa bude dakin, ya kusa minti biyar tsaye sae kuma ya murda key din a hankali, bayan kusan second talatin ya murda handle din kofar, tsaye ya ganta jikin window tayi baja baja da gashinta tana sanye da doguwar rigar kanti pink colour da blue nd black flowers jiki, kallonsa take tana bobboyewa jikin bango, yayi murmushi ya rungume hannayensa yana kallonta.
? *Captain_Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
11.....
Sulalewa kasa tayi ta xauna ta takure waje daya tana rufe fuskarta da dogon gashinta, dakewa yayi ya karaso cikin dakin kamar bai son taka kasa yana kallonta ya isa gabanta sae dae banda faduwa bbu abinda gabansa yake, bata dago har lkcn ta kallesa ba sae d'ada takurewa waje daya take, cire tsoro yayi ya durkusa gabanta a hankali, dago kanta tayi tana kallonsa a tsorace, murmushi yayi murya can kasa yace "Hello!" Kuri ta kura masa da ido, shi ma hakan yayi ma manyan fararen idonta, can ya lumshe ido ya bude cikin sanyin murya yace "Allah ya baki lafiya don son ma'aiki S a w." A hankali ya kai hannunsa kanta ta kuma shigewa jikin bango, murmushi yayi ya matsa gabanta ya tattare mata gashinta ya mayar baya yace "Ki daina kunce gashin ki idan an daure maki Kinji" yana magana ne yana kallon fuskarta, ita kuwa wani gun daban take kallo, ji yayi ana haurowa sama, ya juya yana kallon kofa sae ga El-Ameen, dauke kai yayi El-Ameen ya shigo yana murmushi yace "Uhnn! Ka daina tsoron nata kenan yanxu?" Mikewa Junaid yayi bae ce komai ba, El-Ameen yayi dariya yace "In gaya maka meyasa kaga ta kyale ka?" Junaid ya juya yana kallonsa, sai da ya dau kusan minti daya sannan yace "akwae alluran da na mata daxu shi yasa ta nutsu, but ina me tabbatar maka da xaran ya saketa xaka gane kuran ka idan ka tsaya gabanta" yana murmushi ya kare maganar, Junaid ya tabe baki ya juya ya fice daga dakin ba tare da ya tanka sa ba, El-Ameen ya bisa da kallo yana dariya sannan ya juyo yana kallonta, karasawa gabanta yayi ya durkusa ya dago kanta, hade rai yayi yace "Sae da kika kuma cire ribbon din koh?" Kallonsa kawae take ko kiftawa bata yi, ya hade rai yace "I will knock yhu idan baki bar kallona haka ba" kamar taji me yace ta dauke idonta daga nashi, mikewa yayi ya dauko ribbon ya dawo gabanta ya durkusa ya kama gashinta waje daya ya daure da ribbon din sannan ya dagota suka mike a tare ya kama hannunta, kin binsa tayi tana tutturjewa yace "Keehh" daga haka ya ja ta suka fita daga dakin tana bin sal, Palo ya sauko da ita ya xaunar da ita kasan rug, ya dauko ledan da ya shigo da ya durkusa gabanta ya bude, fried Irish ne da kwae, sae tomatoe ketchup, ya dauki potatoe daya ya dibi kwae ya kai mata baki, dauke kai tayi da sauri tana komawa baya, ya tsaya kallonta, kai wa bakinsa yyi ya ci, Junaid dae sai kallonsu yake yana yi yana danna waya, kara daukar wani chip din El-Ameen yayi ya dangwali ketchup ya kai bakinta, tsura ma dankalin ido tayi sae kuma ta matso a hankali ta lashe ketchup din, El-Ameen ya wara ido yana kallonta, sai kuma ya saka dariya, murmushi junaid yyi yana ci gaba da danna wayarsa, sae tsotsan ketchup din take a baki, El-Ameen ya kuma dangwala ya kai bakinta ta kuma lashewa, rike kanta yayi ya tura mata dankalin a baki ta fito dashi ya fadi kasa, ya hade rai yace "I will slap yhu fah" kallonsa kawae take ko kiftawa babu, ya dauki wani dankalin ya dangwali ketchup ya kuma kai mata baki, lashewa ta kuma yi ta bar masa dankalin tana tsotsan bakinta, yayi murmushi yana kallon Junaid yace "this shows tana son ketchup lkcn da take da hankali" shi dae junaid bae ce komae ba, El-Ameen ya dinga dangwalan tomatoe din yana kai mata baki tana lasa, exotic drink ya bude ya juya yana kallon Junaid yace "Get me cup plss a kitchen Captain, kaga dai patient dinka nake feeding" Junaid bai ce komai ba ya mike ya nufi kitchen ya dauko cup din ya kawo masa, ya karba ya tsiyaya drink din ya dauka ya kai mata baki, dauke kai tayi da sauri, ya juyo da ita ya rike kanta ya kai cup din lip dinta, kadan ta kurba ta cire bakinta tana yamutse fuska, xae kara bata ta sa hannu xata karbi cup din ya sake mata, ta dade tana kallon cikin cup din kafin ta kifar da lemon nan tsakiyarsa, El-Ameen ya mike da sauri ya bar wajen cikin tsawa yace "Kehh!" Tsorata tayi sosae ta dinga shisshigewa jikin kujera, ya karasa kusa da ita ya duka ya mata knock a kai yace "kika sake min irin haka sae na tsula maki bulala" Murmushi Junaid yayi yana shafa kansa, El-Ameen ya dago ta ganin drink din duk ya bata kayan jikinta, tsaye ya bar ta nan wajen ya fita xuwa ya kira Mama, ta juya tana kallon Junaid dake kallonta, ya sakar mata murmushi ta dauke kai ta durkusa wajen ta jawo ledan take away din da Irish din ke ciki ta dauki wanda yake bata ta ajiye gefe, ta bude wanda bae taba ba ta tsura ma dankalin ido, kifarwa tayi a kasa, Junaid ya mike da sauri yace "Noo! Me yasa kika xubar" kallonsa tayi kafin ta maida hankalinta kan abinda take, ta dauki take away din da ya fara bata ta juye cikin na wanda ta xubar a kasa sannan ta mike tsaye, tattare gown din jikinta tayi ta juye dankalin a rigarta ta jefar da take away din, Junaid ya langwabar da kai yana kallonta ya ma rasa me xae ce mata, El-Ameen ne ya shigo Mama na biye da shi a baya yana mata magana, tsayawa yayi daga bakin kofa ya bude baki ganin barnar da tayi, tana ganinsa tayi kusa da Junaid ta tsaya rike da rigarta da ta juye dankali ciki tana kallonsa, El-Ameen ya karaso palon da sauri cikin fada yace "Whatt! junaid kana kallonta ta xubar min da abincin da xan ci?" Bai jira cewar Junaid ba ya nufeta, sake rigarta tayi dankalin ya xube gaba daya kasa tayi bayan junaid da sauri, har wani bari jikinta yake, Junaid ya dakatar da shi da sauri yace "Hey, Look Dr, naga in tana da hankali ae baxata yi haka ba, have you forgotten mahaukaciya ce kamar yanda kake kiranta, wannan ae xalunci kawae kake ma patient din taka, ba dae yunwar Irish kake ba, kar ka damu I will get yhu enough idan muka fita" El-Ameen yyi masa wani irin kallo yace "Da'alla my frnd ba kana kallonta ba ka kyaleta, Better tunda dai xaka siya min wani, but wnn ae iskanci ne ba rashin hankali ba, don bata da hankali sae ta dinga sa mu aiki?" Junaid yace "naji xan gyara wajen is that all" Mama dake tsaye palon tana kallonsu tayi murmushi tace "xan gyara wajen bokon turai, kasan sae a hankali, kuma ma wllh hauka me tsafta take yi bata da kaxanta ko kadan" El-Ameen yayi kwafa yana kallonta ganin yanda take lekosa daga bayan Junaid yace "Ni nasan maganin ki ae, kina wani leko ni da Idanuwan nan naki" Junaid ya d'an tabe baki ya koma ya xauna, Mama ta nufi kitchen don dauko abinda xata gyara wajen. karasawa gabanta El-Ameen yyi ya kama hannunta ta fasa ihu, kunnenta ya ja ta nufi sama da ita, Junaid ya bi su da kallo sannan ya girgixa kai a hankali ya jinginar da kansa jikin kujera. Bayi El-Ameen ya shiga da ita ya wanke mata hannayenta sannan ya fito da ita ya xaunar gefen gado sai kallonsa take, wani kayan ya ciro mata ya ajiye gefen gadon, yana kallonta yace "ki daina kallona haka keh, kuma kika kuskura kika tashi a nan sae na xane ki, clear?" ita dae kallonsa kawae take, sae ta basa dariya ganin irin kallon, ya rungume hannu yace "Uhhn! Halan dai kin san ni ne?" murmushi yyi ya juya ya fita daga dakin. Mama jummai yace ta tafi ta canxa mata kaya bayan ta gama gyara gun da ta bata, mama tayi shiru sae kuma tace "Naga idonta biyu fa" El-Ameen yayi dariya ya xauna yace "ae bata komae mama, shi yasa nace ki tafi ki canxa mata, kar ki samu damuwa bbu abinda xata maki, tana da nutsuwa sosai" mama jummai bata musa ba ta nufi sama cikin rashin kuxari. Tana nan xaune inda El-Ameen ya bar ta a dakin ta sameta, kin rufe kofar Mama jummai tayi in case, ta karasa kusa da ita tana d'ari d'ari ta dauki blue gown din da ya fiddo mata, a hankali mama jummai tace "Baiwar Allah kaya xan canxa maki kin ji" ko kallonta bata yi ba, hakan ya kuma tsorata mama jummai, juyawa tayi a sanyaye ta koma Palo tana kallon El-Ameen tace "D'an nan wallahi tsoro nake ji ni kam, kaga sae tana bacci nake shiryata" dariya yayi ya mike ya nufi stairs din suka koma sama a tare, junaid ya bi su da kallo. Xaune suka tar da ta har lkcn sae dai wannan karan windon dakin ta tsura ma ido, El-Ameen ya karasa kusa da ita, ta juya da sauri tana kallonsa, kayan ya dauka ya mika ma mama jummai yace "Gashi mama" karasawa tayi ta karba, ya dago ta yana kallonta ya hade rai yace "Mama xata canxa maki kaya yanxu, stay still kin ji" ita dae kallonsa kawae take, ya juya ya kalli Mama jummai yace "Toh karaso Mama" a hankali ta karaso kusa da su, hannunta na rawa ta kai kan maballin rigar xata cire mata, ta fasa wani ihu tayi bayan El-Ameen da sauri, cikin sakwannin da basu wuce uku ba sae ga mama jummai can bakin kofa a mugun tsorace bayan ta sake kayan hannunta nan gabansu, dariya sosai El-Ameen yake yana kallonta yace "Mama baxa fa ta maki komae ba wllh" tace "A'a d'an nan nafi gane tana bacci wllh" a tsorace take maganan daga haka ta juya ta koma kasa, murmushi yayi ya juya yana kallon ta bayansa, dawo da ita yayi gabansa, ya kusa minti biyu tsaye kamar me naxari sai kuma ya leka rigar jikinta don ganin ko akwai kaya a ciki yaga akwai vest, rufe idanuwansa yyi a hankali ya balle dogon rigan jikinta snn ya fara cirewa idonsa kulle, ajiyewa yayi bayan ya cire har lkcn idonsa na rufe ya duka a hankali ya shiga laluban kayan da Mama jummai ta yar a kasa, yana tabawa ya dauka sannan ya mike, lalubawa yayi yaji bata wajen kuma, ae ba shiri ya bude ido da sauri yana waige waigen inda xae ganta, tsaye ya ga perfect fair figure dinta can jikin window, daga ita sai white vest da ya kusa cinyarta, vest din ya kamata sosai kasancewarsa very elastic, gaba daya shape dinta ya fito ga long fresh legs dinta da bbu tabo ko daya, kamar xaka latsa ta jini ya fito tsabar haske, juyawa yayi da sauri kamar wanda ya ga abun tsoro ya nufi kofa da hanxari, ko me ya tuna kuma sae yyi still bakin kofar ya kusa 3 mins kafin ya juyo a hankali ya dawo dakin ya nufeta ba tare da ya kuma kallon jikinta ba, hannunta ya kama yana kallon fuskarta ya shiga sa mata rigar hannunsa, yana gamawa ya xaunar da ita gefen gado ya hade rai ya dunguri kanta yace "Don't try dat again" cup ya dauka ya dauraye yayi mata diluting drugs dinta da ruwa sannan ya dawo kusa da ita ya rike kanta ya kai cup din bakinta, kauda kai tayi da sauri, yayi mata tsawa ita ma ta fasa masa ihu, rike kanta yyi ya tura cup din bakinta har sai da ta bude ya xuba mata, sae da ya tabbatar ta hadiye sannan ya kyaleta tana yatsinan baki tana komawa baya, jinin da ya gani bakinta yasa ya tsura ma lips din ido, handkerchief ya ciro aljihunsa ya goge mata bakin yace "Sorry!" Mayar da handki din yayi ya kwantar da ita ya mike ya fita daga dakin ya ja kofar. Palo ya sauko ya ga ba Junaid, ya kalli mama dake xaune yace "Mama Junaid fa?" Tace "Ya tafi wai" shiru yayi bae ce komae ba, can yace "Ohk xan tafi yanxu, da daddare xan dawo, bacci xata yi yanxu" tace "Toh Allah ya kai mu, Allah kuma ya bata lafiya" yayi murmushi yace "Ameen" sannan ya fita.
? *Captain_Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
12.....
Gidansu faisal Junaid ya nufa, yana gama parkin ya nufi babban palon gidan, babu kowa palon sae TV dake aiki ya shiga dakin faisal, kwance ya samu faisal yana waya, Junaid ya tabe baki ganin yanda yake wani kwantar da murya ko ba a fadi ba yasan da mace yake wayar, can karshen gadon Junaid ya xauna, faisal ya mike xaune yace "Babe xan kira ki ltr," daga haka ya ajiye wayar yana kallon Junaid yace "Uhn! B'atan hanya kayi captain?" Junaid yace "No!" Faisal yayi dariya yace "A'a kae dai fadi gskya, ko wajen El-Ameen xaka yi ka mance ka yo nan" Junaid yace "What ever, Mama fa?" Faisal yace "Tana kano jiya ta tafi" Junaid yace "Allah dawo da ita lfya, kana ta shagalin ka da 'yan mata abin ka" faisal yayi dariya ya dawo kusa da shi yace "Kai aure ma ni xanyi fa yanxu" junaid ya kallesa yace "da gaske?" Faisal yyi kwafa yace "Stay there kai da El-Ameen kuna hauka sae kun ji ma an sa min rana soon" murda kofar dakin aka yi duk suka juya suna kallon kofar El-Ameen ya shigo, faisal ya d'an bude ido yace "Show! Ko dai tare ku ke?" El-Ameen dake ta kallon Junaid yayi murmushi ya karaso cikin dakin yace "Ashe nan ka yo captain, toh what's the meaning of going without saying a gud bye, dama daga nan gidan ku xan tafi ban mance Irish dina ba wllh tunda yunwarsa nake" Junaid bae ce masa komae ba ya fiddo wayarsa yana dannawa, El-Ameen ya xauna gefen faisal ya dafa kafadarsa daya yace "Ya aka yi guy, ya aiki?" Faisal yace "Alhmdllh mun gode Allah, muna week end yau, ya su Ummi?" El-Ameen yace "Duk lfya, plss in tambaye ka mana" Faisal yace "Ina jin ka" El-ameen na shafa kai yace "wannan abokin naka psychiatrist, I can't recall his name yanxu, yana nan katsina har yanxu kuwa?" Faisal yace "Wai Dr isah?" El-Ameen yace "Exactly, yana nan?" Faisal yyi dariya yace yace "Yana nan, Ashe baka mance shi ba, ko jiya muna tare da shi" El-Ameen yace "Yauwa plss wani taimako nake son ka min, Gamma knife or Cyber knife xaka tambayar min a gurinsa nasan baxae rasa ba" faisal ya gyara xama yana kallonsa yace "Me xaka yi da gamma knife kuma, naga baka concentrating a field dinka na neurology yanxu" El-Ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "ina yi mana, sosai ma, yanxun ma wani frnd dina ne ke da wata patient with mental disorder, so am putting her under medication ne yanxu, after some month idan naga ba a dace ba, I will advise him to take her to a psychiatry for psychiatrist to take over, kila a dace a can din" El-Ameen na magana ne yana kallon Junaid fuskarsa dauke da murmushin rainin hankali, junaid dae ko kallonsa bae yi ba sai danna wayarsa yake, Faisal yace "Allah sarki, xa ma a dace idan Allah ya yarda, sae dai idan ba Neurologist El-Ameen din da na sani bane," dariya El-Ameen yayi yace "Noo, Dr El-Ameen dai, yanxu dai plss xuwa gobe ka lallaba sa ko na clinic ne ya aro min, coz nasan frnd din nawa will not afford it idan nace yaje can kasashen turai ya siya, its more than expensive" ya kare maganar yana ma Junaid wani irin kallo yana murmushi, Murmushi junaid yayi ba tare da ya kallesa ba, faisal yace "Alryt xan kirasa anjima, amma a ina xaka sa ta under medication din, clinic din ku?" El-ameen ya xaro ido yace "Sai in ce ma Abba a ina na samota?" Da mamaki Faisal yace "Kamar ya, 'yan uwanta fa?" El-Ameen yayi dariya yace "Ohh ai d'an uwanta a dai yanxu daya ne kacal a duniyar nan" kallonsa kawai Faisal ke yi da confusion shi ko sai dariya yake, Junaid ya tabe baki ya mike ya nufi bathroom ya dauro alwala ya fito don lkcn sllh yayi, bae jira su ba ya fice daga dakin don xuwa masallaci, Faisal ya bi sa da kallo yayi dariya yace "Kai halin Junaid sae shi, toh meye ma'anar hakan da yake yi, namiji dan uwansa ma sai ya ma miskilanci ina ga mace" El-Ameen yayi dariya yace "Let him, I think yana d'an da brain disorder'n shi ma, of recent na lura da hakan, kaga sae in hada shi da patient din tawa in sa su under medication" dariya sosai faisal yayi, El-Ameen yace "Amma fa rufa min asiri kar ka gaya masa sae ya Iya daukar gaba da ni daga yanxu har bayan watanni" bayi ya nufa yana dariya, faisal na taya sa. A tare duk suka fito daga mosque din bayan an idar da sllh, Junaid ya nufi motarsa ba tare da ya kallesu ba yace "Am going home" Faisal yace "Haba so early dama ba hira ka xo mu yi ba" Junaid ya kallesa yace "Ga Dr nan sae kuyi hiran, am going home kafin Mumy ta fara kirana" faisal ya rungume hannu yana dariya yace "Ehh gskya ne kuma wannan, madarar ka na can a feeder kar ya huce koh" murmushi junaid yayi yace "Yea! Sure." Daga haka ya nufi motarsa, El-Ameen yayi dariya yace "Allah ka nuna mana ranan da Junaid xae girma kamar mu" makullin motarsa ya mika ma Faisal yace "kaga shigar min da motata ciki, tare xa mu tafi, ltr xan dawo inji yanda ku ka yi da Dr isah" faisal yace "Ohk sai ka dawo" motar Junaid El-Ameen ya nufa da sauri ya bude ya shiga, Junaid dake kokarin tada motar ya kallesa yace "Ya aka yi?" El-Ameen ya hararesa yace "Mu je ka siya min potatoe dina mana, ko ka xaci na manta ne" murmushi junaid yayi ya tada motar ya ja suka bar wajen. Wani eatery ya tsaya ya fito ya shiga ciki, El-Ameen ya bi sa da kallo, ba a dau lkci ba ya fito rike da take away din fried Irish har hudu, ya bude bangaren da El-Ameen ya ke ya dungure masa ledojin a kan kafarsa snn ya rufe motarsa ya xaga ya shiga, dariya El-Ameen yayi yace "Toh me kenan, ni ae wannan ya min kadan" Junaid bae tanka sa ba ya tada motarsa suka bar wajen. Sae da suka hau kan titi ba tare da ya kallesa ba yace "Ina ka nufa don ni am going home" El-Ameen yace "drop me at home," junaid ya kama hanyar gidan nasu yana isa yayi parking ya juya yana kallon sa, bude motar El-Ameen yayi yace "Gobe xa ayi diagnose dinta!" Junaid ya gyada kai yace "Allah ya kai mu" El-Ameen ya fita daga motar yace "Ka gaida Mumy" kai junaid ya kuma gyada masa sannan ya ja motar ya bar kofar gidan.
yana isa gida ya dde xaune cikin motarsa a parking lot yana danna waya, fatima ce ta leko jin bae kashe motar ba har lkcn, yana ganinta ya kashe motar ya fito ya rufe, kallo daya yayi ma Umma da fitowarta daga side din Abba knn ya dauke kai yayi side din Mumy, Umma ta bi sa da kallo ta gefen ido tayi kwafa ta nufi bangarenta. Kwanciya Junaid yayi bayan ya gaida Mumy, Mumy ta xauna tana kallonsa tace "Ga lunch dinka a dinning" yace "Toh Mumy," Humainah ce ta fito daga kitchen ta shigo palon tace "Na gama Mumy" Mumy tace "Sannu Humainah, dauko ma yayanki abincinsa a dinning" ta juya ta tafi dinning din ta dauko warmer biyu, daya me dauke da jollof rice daya kuma farfesun naman rago, ta dauki plate da spoon ta dawo palon ta dire gaban Junaid dake kwance har lkcn idonsa lumshe, ta mike ta koma ta dauko drink da ruwa sae cup ta dawo ta ajiye, Mumy tace "Toh tashi ka ci abincin mana" mikewa xaune yayi yana kallon Humainah dake durkushe wajen har lkcn ya hade rai, ita ma haka, harara ya galla mata yace "ke wa yace ki shiga dakina ki dauki turare" ta tabe baki tace "Toh meye? kuma naga turaren kala kala ne shi yasa" Mumy tayi dariya tace "Atoh!" Ya wani hade rai sosai yace "God help yhu ki sake shiga daki na ki ga" mikewa tayi tace "Mumy xan je gun Hajja" Mumy tace "Toh kiyi mata sannu da xama" daga haka ta galla masa harara ta fice daga palon, sakkowa Junaid yayi ya xauna kan carpet yace "Yarinyar nan ta raina ni fa Mumy" Mumy tayi dariya tace "Ko dai kana ciki ne Captain" kallon Mumy yayi da sauri sai kuma ya marairaice mata yace "Ina ciki kuma Mumy, A'a ni matata na nan xuwa in'sha Allah, beside bana sha'awar auren xumunci ni" Mumy tayi dariya tace "Toh ka dinga sake mata don tunanin da Hajja da 'yan gidan ma xa su yi kenan, idan suka ga kuna haka da ita, kasan yanxu samarin nowadays idan suna son mace sae suyi ta wani basarwa, kaga suna yawan fadace fadace da ita barin ma idan yar uwar sa ce, wae su nan kar ta gane suna sonta ta raina su, wasu har da duka wae kuma duk cikin so ne fa" dariya sosai Junaid yayi yace "Ae kauyanci knn Mumy" Mumy tayi murmushi tace "Atoh, sae ka ga daga karshe idan suka ga yarinyar na neman kubuce masu su haukace su fito fili suce su fa sai ita" dariya junaid yake yace "Kai Mumy, wannan ae sae film ba dai reality ba" Mumy tayi murmushi tace "Toh shknn, it seems you've neva come across dat before" yace "Uhnn toh Allah kyauta, but it kinda funny mum" abincin gabansa ya bude ya dibi shinkafar dai dai wanda xae ci da plantains da nama sannan ya rufe, yayi bismillah ya fara cin abinci, yana gamawa Mumy ta kira mai aikinta ta fito ta kwashi plates din da warmer ta kai kitchen, kiran sllhn Asr yasa shi mikewa ya shiga bayin dake Palon ya dauro alwala ya fito, fatima da fitowarta palon kenan ita ma da shirin islamiyya tace "Ya A.jay xaka yi dropping dina in jira" yace "No" kofa ya nufa ya fita daga palon. Yana dawowa daga masallaci part din Hajja ya shiga, ya sameta xaune ta sa TV a gaba, Khadija kuma na kwance tana danna waya, xaunawa yayi yana kallon Hajja dake bin sa da kallo yace "wannan kallon fa Hajja" Hajja ta tabe baki tace "Ba sai ka tsole min idon ba" Khadija ya kalla ya hade rai yace "Ranan da xan xane ki na nan tahowa a gidan nan, baki da aiki sai danne danne kin yaye islamiyya yanxu koh" Hajja ta gyara xama tace "Ai mu sai Allah yayi mana shari'a da shegen wahalallen da ya kirkiri waya a duniyar nan ya bata mana 'ya 'ya, yanxu ace kamar Khadija daga safe har talatainin dare wancan shegen abun na hannunta tana latsawa tana murmushi, ta fa ji tsoron Allah taji tsoron gamuwarta da shi, Allah kadai yasan tsiyar da take tsulawa a shegen abun, shi kuma Muhammadu ba mai sa ido ba, ta inda bala ya fi sa kenan don har yau bai bari Humainah ta rike waya ba, wannan bala'i da me yayi kama? kana mata magana ma bata san kana yi ba ido kyar a kan waya, amma mu je xuwa ranan da Allah xai tashi kamata sai dai yar iskan wayar tayi bindiga a hannun ki wllh" kallon Hajja kawai Junaid yake kafin ya tabe baki ya kalli wayarsa dake ringing a hannunsa ya ga El-ameen ne.
Captain Ahmad Junaid
_By Khaleesat Haiydar_
13....
Junaid bai daga kiran ba ya juya yana kallon Khadija, Mikewa xaune tayi ta hade rai kamar xata yi kuka tace "Ni fa wllh ba chatting nake ba ya A.jay, ita Hajja bata san komai ba sai dai tayi ta magana" Junaid xai yi magana Humainah ta shigo palon fuskar nan nata a daure ta xauna gefen Hajja, Hajja tace "ke kuma fa? Ina aiken" Humainah tace "ko ba yi tayi kamar bata gan ni ba, kuma bata ce min komae ba sai aikinta take tana wake wake ta bar ni a tsaye" Junaid yace "Wa?" Ta kallesa tace "Anty sadiya mana" Hajja ta mike rai bace tace "Kambu!! Yaran nan sun raina ni wllh, don uwarta ni din sa'arta ce da xan aika tayi min abu ta share ki tana wake wake?" Kofa ta nufa kamar xata tashi sama, Junaid ya mike ya bi bayanta yace "Tsaya Hajja, me kika sata?" Tana huci ta juyo tace "Ca nayi ta min dafadukan taliya shi ke raina yanxu don Amina shinkafa tayi kamar ko da yaushe, ita bata da girki sai na shinkafa kullum" Junaid ya hade rai yace "Ita mum din tawa, Toh su wa ennan na palon naki me suke yi da baxa su maki ba" Hajja tayi tsaki tace "Xancen banxa, toh ban yi niyyan sa su ba, ko da yanda xaka yi da ni ne" tana kai wa nan ta nufi part din Hajiya da sauri, ya d'an tabe baki ya juya yana kallon Humainah yace "Sannu da hadi, ke baki iya taliyar ba sae kin je dauko magana koh?" Ta turo baki tace "Ae dai ba ni nace tayi ba, aikena aka yi" yace "Xaki yi bayani idan na kama ki ne" dauke kai tayi ya juya yayi wucewar sa, Khadija tayi dariya tace "Bari in je inyi kallo" Ana kiraye kirayen Magrib Junaid ya fito part dinsa sanye da jallabiya milk colour, dai dai nan Humainah da fatima suka fito daga part din Mumy, Humainah tace "Masallaci xaka ya Ahmad" Ya harareta yace "A'a office xan je" bae jira cewar ta ba ya kara gaba. Yana fito wa daga mosque bayan an idar da sllh ya tsaya da wani frnd dinsa da ke nan layin suna gaisawa, har sai da ya ga shigar Abba gida, snn yace "Abdul d'an ara min motar ka pls xan dan fita in dawo yanxu" Abdul yace "Toh mu shiga in baka key" junaid ya bisa suka shiga compound dinsu ya tsaya daga balcony har ya kawo masa makullin sannan ya nufi parking lot ya dau motar ya fita. Atm machine ya fara tsayawa ya cire kudi ya siya fruits nan wajajen sannan ya koma mota ya dau hanyar gidan El-Ameen. A waje yayi parking bayan sun gaisa da mai gadin ya shiga gidan, Mama jummai na kwance Palo kasan tiles ta shimfida xani da 'yar radionta a hannu tana saurare, ta mike xaune ganinsa tace "Sannu da xuwa Ahmad" xaunawa yayi yace "Yauwa mama ina yini?" Tace "Lfya lau, ya gidan?" Yace "Alhmdllh Mama, El-Ameen ya xo kuwa?" Tace "Ehh bae dade da fita ba, kuma yace min xai dawo" yace "Ohk, bacci take ne?" Mama jummai tace "Anya! Ina jin kamar idonta biyu" Junaid ya ajiye mata ledan fruits guda daya yace "Ga kayan marmari mama" godiya ta dinga masa ya mike ya nufi stairs ya haura sama. A hankali ya tura kofar dakin ya tsaya daga bakin kofar yana kallon cikin dakin, rakube ya ganta gefen gado ta sunkuyar da kanta, a hankali ya karaso cikin dakin yana kallonta har ya iso gabanta ya durkusa, sai a sannan ta dago kai tana kallonsa da dara daran fararen idonta, komawa baya yayi da sauri don ba kadan idanuwan nata suka bashi tsoro ba, ta wani kafe sa da ido ko kiftawa bata yi, sauke kansa yayi kasa ya bude ledan gabansa ya mike ya dawo kusa da ita ya duka a hankali ya dauki Apple daya ya mika mata, kallon Apple din take kamar me son gano abu a jiki, ya kai bakinsa ya gutsura a hankali ya fara ci yana kallonta, har sai da ya cinye sannan ya kai mata bakinta, kauda kai tayi da sauri, ya dawo gefenta ya kuma kai mata baki yace "Apple! taste ki ji" rike kanta yayi ya kai mata baki ta d'an bude bakin kadan ta gutsura, yana kallon yanda take kokarin hadiye Apple din ba tare da ta tauna ba yace "Wait, Wait!" Da sauri ya kuma gutsuran Apple din ya shiga taunawa yana kallonta ita ma haka, yanda ta ga yana yi haka ita ma ta shiga yi tana taunar Apple din a hankali, yayi murmushin sa me kyau yace "Good!" Tana hadiye wa ya kai mata baki kuma ta gutsura, karban Apple din tayi a hannunsa ta shiga ci da kanta, ya dawo gabanta ya durkusa yana kallonta, matsowa kusa da ledan ta shiga yi tana kallon ciki, ya dauki ayaba daya ya bare ya gutsura sannan ya kai mata sauran baki ta bude a hankali ya sa mata, taunawa ta shiga yi tana yatsine fuska, murmushi kawai yake yana kallonta, can ta dauki peel din bananan xata kai baki, ya karbe da sauri yace "No!" Tsuke baki tayi tana kallonsa, dariya yayi ya dauki wani Ayaban ya bude ya mika mata gaba daya, ta ajiye Apple din hannunta ta karba, cikin lkci kankani ta cinye ayabar, ya kuma bare mata wani shi ma ta cinye, haka ya dinga yi mata har ta ki karba kuma, ta dauki Apple din da ta ajiye tana kallo, karba yayi ya kai mata baki, ta dafe hannunsa da duk nata biyu ta gutsura a hankali tana taunawa, kallon hannunta kawae yake don duk haskensa ta fi sa nesa ba kusa ba, tana rike da hannunsa haka ta dinga cin Apple din, dai dai nan El-Ameen ya shigo dakin, xaro ido yayi ya rungume hannu yace "Tabdi! Me kke yi haka captain, she will bite the hell out of yhu wllh!" A hankali Junaid ya xame hannunsa daga nata, ta daga ido tana kallonsa, ya kamo hannunta ya danka mata Apple din sannan ya mike yana kallon El-Ameen, El-Ameen ya tabe baki yace "Ina raba ka da shisshige ma mahaukaciyar nan baka ji koh? Randa xata nuna maka halinta na hauka I won't be around fah" Junaid bai tanka sa ba, El-Ameen yayi kwafa ya ajiye ledan drugs din hannunsa da fresh yoghurts ya dawo gabanta yace "Ashe kin iya cin fruits" bata kallesa ba sae cin Apple dinta da take, ya d'an yi murmushi ya nufi inda alluranta suke don hada wanda xae mata, Junaid ya juya ya nufi kofa, mikewa tayi da sauri ganin haka, sae kuma ta bi bayansa, dai dai stairs yaji kamar ana binsa, ya juya ya ganta tana tahowa, kallonta ya tsaya yi, har ta karaso gabansa ta kama hannunsa ta saka masa Apple din, sannan ta daura nata hannun kan nasa ta kai bakinta ta fara cin Apple din, murmushi kawae yake yana kallonta, El- Ameen ya fito daga dakin ya rungume hannunsa yana kallonsu yace "Uhunm! It seems she's getting use to yhu yanxu, kaga kawae sae ka tattaro ina ka ina ka ka dawo nan ka tsaya da ita sai ka cike Ladan ka" yana magana ne yana murmushi, Junaid ya xame hannunsa daga nata ya damka mata Apple din ya juya ya fara sauka stairs din, bin sa tayi da sauri, El-Ameen ya daka mata tsawa, a tsorace ta juya tana kallonsa, ya karaso inda take ya kama hannunta suka koma daki, xaunar da ita yayi gefen gado, ya bude yoghurt din da ya shigo da ya xauna gefenta ya kai mata baki, ta kauda kai da sauri, wani kallo yayi mata yace "I will slap yhu" kamar ta ji me yace bata sake yunkurin dauke kai ba, ya dafa kanta ya kai mata yoghurt din bakinta, a hankali ta dinga sha tana kallonsa, tari ta fara yi ya cire yoghurt din da sauri daga bakinta a hankali yace "Sorry," ya dafa kanta ya kuma kai mata baki, ta dauke kai da sauri tana kokarin karban roban, sake mata yayi ta kallesa sannan ta fara tuttular da shi nan kasan dakin, fixge wa yayi da sauri yace "Ance maki idan aka koshi xubar da abinci ake?" Kallonsa kawae take ko kiftawa bata yi, ya ja dogon hancinta yace "Da wani idanuwanta a wajen" jan hancin ita ma tayi yanda ta ga yayi, yayi murmushi yana kallonta, yoghurt din hannunsa ya rufe ya ajiye sannan ya mike ya nufi inda drugs dinta suke, diluting yayi mata a cup ya dawo gefenta ya xauna, matsawa ta fara yi daga kusa da shi, ya jawo ta ta fasa ihu, d'an buge mata baki yayi tayi tsit tana kallonsa, ya kai mata maganin baki taki budewa, sae da yayi mata tsawa sannan ta bude da sauri har jikinta na rawa, ya xuba mata maganin gaba daya, sai da ya tabbatar ta shanye snn ya mike yana kallonta, banda yatsine fuska bbu abinda take, yayi murmushi ya juya ya fita daga dakin, downstairs ya sauka ya samu Mama Jummai kadae palon, yace "Junaid fa Mama?" Tace "Ya fita ae" yace "Ohk, ki taso toh ki rakata baya tayi fitsari yanxu xata yi bacci tunda na bata magani" mikewa tayi tace "Toh, ae tana da tsafta yarinyar duk me xata yi naga tana shiga bayi" yayi murmushi yace "Kin dai yrda bata komai yanxu koh" yar dariya tayi tace "Ehh na yrda, don daxu ina xaune ta sauko, duk na tsorata ba kadan ba, ae ko in gaya maka sai gani nayi ta xauna gefe na ta mimmike kafa yanda taga nayi" dariya El- Ameen yayi yace "Ae wayo gareta, idan Allah ya yrda sama mata lfya baxae wani dau lkci sosai ba, kila daga nan xuwa wata hudu ko shidda in'sha Allah" Mama jummai tace "Toh Allah ya yrda, Allah ya ba Baiwar nan tasa lfya, gashi 'yar yarinya da ita" yayi murmushi yace "Kina ga xata yi shekara nawa" Mama jummai tace "Kai baxata wuce sha shidda ba wllh, in ma ta kai kenan" yana murmushi yace "Ko kuma sha bakwai ba" Mama jummai tace "Allah sarki, amma dai ku dinga hada mata da Addu'a kunsan duniya bbu gaskiya, kar ayi ta na turawa nan kuma kila asiri ne" ya d'an yi shiru kafin yace "Anya kuwa, bana tunanin jifa ne, don da jifa ne ba lallai ta xama nutsatssiya haka ba, nd jiya naga tana ta observing wnn tumatir din cikin dankalin da na siyo kuma ta sha sosai" Mama Jummai tace "Toh Allah dai ya bata lfya amma dai ayi addu'ar ma" yace "Ameen, xa a hada mama" Sama mama Jummai ta nufa shi kuma ya xauna palon, bata mata wani gardama ba ta kai ta bayin. Ko da Mama Jummai ta sauko mikewa El-Ameen yayi ya koma sama, kwance ya sameta idonta lumshe alamar xata yi bacci, ya gyara mata kwanciya ta bude ido da sauri tana kallonsa, ya rufa ta da bargo, ya dawo dai dai fuskarta yace "Gudnyt" lumshe ido kawae tayi ya juya ya fita daga dakin ya rufo mata kofa, yayi ma Mama Jummai sae da safe ya fice daga palon, xaune ya ga Junaid a balcony, ya d'an bude ido da mamaki yace "Thought ka tafi ai" Junaid ya mike yace "Sure! Yanxu xan tafi" daga haka ya sauka balconyn yayi hanyar gate, El-Ameen ya bi sa da kallo sannan ya tabe baki ya bi bayansa, kusan a tare suka fita compound din, El-Ameen ya kalli motar da Junaid ya nufa yace "Whose car is that?" Ba tare da Junaid ya kallesa ba yace "Abdul" daga haka ya bude motar ya shiga, El-Ameen ya karasa gun motar yace "Yhu are acting strange this dayz Captain, let it not be kai ma ka fara samun brain disorder'n ne fa, aikin sai yayi min yawa" El-Ameen ya kare maganar yana murmushi, junaid ma yayi murmushi yace "Sure!" Daga haka ya ja motar ya bar sa nan tsaye, El- Ameen ya bi motar da kallo yana murmushi yace "It's Alwayz: 'Yea! Sure! D'an rainin hankali, tasa motar shi ma ya nufa ya bude ya shiga ya bar anguwar yana tunanin yanda xai yi squeezing time dinsa gobe da safe ya xo ayi diagnosing dinta.
? *Captain_Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
14.....
Junaid na isa layinsu ya kira Abdul don ya fito ya karbi motar sa, Abdul ya fito yayi instructing mai gadinsu ya bude gate, yana budewa Junaid ya shiga yayi masa parking a parking lot din gidan sannan ya fito ya mika masa makullinsa yace "Thanks Abdul, sae da safe." Masallaci ya fara shiga yayi Isha sannan ya shiga gida, sai da ya tabbatar Mumy baxata hangosa ba idan ya xo wucewa ta side dinta sannan ya wuce da sauri. Humainah ce tsaye bakin tap tana diban ruwa, ta bi sa da kallo tace "Daga ina kake ya Ahmad" ba tare da ya kalli inda take ba yace "Inda kika aike ni" dariya tayi tace "Mumy fa na ta neman ka" dawowa yayi da sauri wajenta yace "Kice Wllh, tun yaushe?" ta kyalkyale da dariya tace "Tsaya nan, tun daxu ake neman ka" ya hade rai yace "Ke wa ya gaya maki?" Ta d'an yatsine fuska tace "Tare mukayi ta neman ka ae har da Hajja, da Abba, an ma kira layin ka bae xuwa wai switch off" shiru yayi ya ma rasa tambayar da xae kuma yi mata, ta tabe baki ta kashe tap don bucket dinta ya cika, Muhibba ce ta karaso wajen, kallo daya tai ma Junaid ta dauke kai, Empty Bucket din dake wajen ta kalla tace "Ke wa yace ki taba min ruwan da na tara?" Humainah ta tabe baki tace "Oho, nima haka naga bokitin" cike da masifa Muhibba tace "Kar ki gaya min maganar banxa ba ni da ke bane a nan xaki wani ce baki sani ba" hararanta Junaid yayi ya juya xae bar wajen, Muhibba ta yi ball da ruwan da Humainah ke diba, Humainah ta xaro ido tace "lalala! Wllh sai na rama" dawowa Junaid yayi da sauri ya rike ta ganin tayi gun Muhibba, yace "Ke Babu ruwa a ciki ne?" Kamar xata yi kuka tace "Dubi fa abinda ta min ya Ahmad, Hajja ce fa ta aikeni in debo mata ruwa" yace "Ke kin taba ganin inda ake fada da mara hankali!" Humainah tace "ohh Kuma fa haka ne" yace "Gud! Ki tafi ciki ki debi ruwan ki" tace "Ko ba Hajja ta sa mai gadi ya kashe engine ruwan ba tun da rana" yace "Ehh xan je in kunna yanxu" tace "Toh" juyawa Muhibba tayi fuu ta bar wajen, Humainah ta kyalkyale da dariya, ya harareta ya juya yayi side din Mumy, da sauri tace "ni fa wasa nake maka ba a neman ka" juyawa yayi yana kallonta yace "Na fara wasa da ke ne koh?" Kwafa yayi ya nufi part dinsa. Muhibbah na shiga part dinsu ta xube jikin Hajiya dake xaune Palon da Rabi'a ta fashe da kuka tace "Hajiya kina ganin fitsaran da yarinyar nan da suka xo gidan nan da Hajja ta min, har Ahmad na Goya mata baya yana kirana mara hankali" Hajiya da bacin rai ya bayyana karara a fuskarta tace "ki ka barta baki ci ubanta kin nakada mata duka ba?" Muhibba na share hawaye tace "Toh ba yana tsaye gun ba" Sadiya tace "duk uwarsa ke xuga sa yake rashin mutunci a gidan nan wllh" mikewa Hajiya tayi kamar xata tashi sama ta fice daga palon tayi part din Junaid, yana xaune rike da remote xae yi powering Tv ta shigo, kallo daya yayi mata ya dauke kai, cikin fada tace "Ahmad ita Muhibbar kake kira mahaukaciya? Toh in har Muhibba na hauka to Amina ma haukan take, ita ce ma babban mahaukaciyar..." Mikewa yayi yana kallonta a nutse yace "Ina ganin girman ki a matsayin ki na matar mahaifi na, amma kika sake kika taba mahaifiyata girman nan xae xube wllh," a fusace tace "Ya dade bai xube ba girman don uwarsa, da can ganin girman mu kake munafuki, ai mu wllh sai dai mu ce Allah ya isa tsakaninmu da Amina duk ta shanye mana miji sai yanda tayi da shi, kai ma ka taso kana neman xame mana fitina da bala'i a gida to kun yi kadan daga kai har makirar uwar taka....." Wani irin kallo Junaid ke mata ya girgixa kai yace "Gaskiya jahilci cuta ne" xaro ido tayi ta dafe kirji tace "Ni kake kira jahila Ahmad?" Juyawa yayi ya koma ya xauna, ta fashe da kuka ta juya ta fice daga palon. Ko minti biyar bata yi da fita ba Khadija ta shigo tace "Ya A.jay Abba na kiran ka" ya kalleta ya dauke kai ta fita, mikewa yayi ya bi bayanta. Part din Abba ya tafi ya shiga palon da sallama, babu abinda ya daga masa hankali sai ganin Mumy da yayi a palon, ya karasa a sanyaye ya xauna kasa kusa da ita yana kallonta, ganin taki kallonsa yasa ya juya ya kalli Abba yaga yanda ya wani hade rai yana kallonsa, Hajiya na xaune palon sai sharban kuka take, Umma sai wani sauke ajiyar xuciya take tana tabe baki, ko kadan hakan bai damesa ba yafi tunanin fushin Mumy a kan ma na Abban, Abba ya mike cikin tsananin fushi yace "Ahmad maimaita abinda ka fadi ma Hajiya a palon ka daxu" ya d'an kalli Abba sannan yayi kasa da kai yayi shiru, Abba ya daka masa tsawa yace "Ba magana nake maka ba" nan ma dai bai dago ba bare yace wani abu, Hajiya aka kuma fashewa da kuka mai sauti, Abba yayi murmushin takaici yace "Wato ita Hajiyar kake kira da jahila ko Ahmad?" Junaid ya girgixa kai har lokacin bai dago ba yace "Ni ban kirata da haka ba Abba" Wani tsawa Abba ya daka masa yace "you are stupid, sharri tayi maka kenan" Junaid ya girgixa kai, a fusace Abba yace "Toh bari kaji abinda baka sani ba, in har xaka iya bude baki ka ce ma Hajiya Jahila, to bbu tantantama warcan da ta haife ka ma xaka iya kiranta da haka, ka sani matsayin uwarka dai dai yake da wa ennan da ka raina a gidan nan, kuma from henceforth a gidan nan sai ka ma uwarka fitsara ka xauna lafiya amma idan ka kuskura kace xaka masu sai ka ga the other side of me wllh, I will deal with you, maxa tashi kaje ka bata hakuri kar in baka mamaki yanxu" Junaid da yaji kamar an soka masa mashi ya daga kai da kyar yana kallon Mumy, hawaye ya gani idonta, rudewa yayi ya dawo gabanta ya durkusa yace "Noo plss mum, kar ki xubda hawayen ki saboda ni, don Allah kiyi hakuri ki yafe min" bude baki Abba yayi yana kallonsa da mamaki, Hajiya da Umma ma sai kallonsu suke cike da tsana, shi kam magiya ya dinga yi ma Mumy yana bata hakuri ba tare da ya kuma bin ta kan Abba ba, mikewa Mumy tayi ta fice daga palon, shi ma ya mike xai fita, Abba yayi masa wani mugun tsawa, juyowa yayi yana kallonsa a hankali yace "Abba xan je in dawo"
Karfe hudu da rabi Junaid yyi parking a parking area din gidansu, ya dade xaune cikin mota yana danne dannensa a waya har sai da Humainah ta leko daga part din Mumy, ganin haka ya kashe motar ya fito ya kulle, wuce ta yayi ya bude kofa ya shiga, ta bi bayansa tace "Me kake cikin motar ya Ahmad?" Yace "Abinda kika sa ni" dariya tayi ta bi bayansa, ya xauna Palo yana kallon Mumy a hankali yace "Sannu da gida Mumy" tace "Welcome, kai dadin xaman mota kawae kake" murmushi yayi ganin Mumy ta huce gaba daya yace "Na gaji ne Mum" Humainah ta xauna kasa kusa da shi tace "Sannu da dawowa ya Ahmad" banxa yayi mata, fatima dake palon ma tace "Sannu da dawowa yaya" yace "Yauwa" sannan ya mike yace "Bari in je in yi wanka Mumy" Mumy tace "Ba gaisheka Humainah yi ba" yace "Gulma ce fa Mumy, da tana gaishe ni ne" Mumy ta hararesa yyi murmushi kawae ya nufi kofa, Humainah ma ta bi sa da harara, Yana shiga part dinsa yayi wanka ya dawo Palo yayi kwanciyarsa, yana son xuwa gidan El-Ameen amma bai ma san inda xae ce ma Mumy xai je gashi yana ta kiransa tun a gun aiki ya ki dagawa, ashe akwai ranan da xai ga disadvantage din rashin fitarsa, don da yana fita da Mumy baxa ta dinga querying dinsa ba idan yace xae fita yanxu, mikewa xaune yayi jin an bude kofar parlour, Humainah ta shigo ta tsaya daga bakin kofa tace "Mumy tace ka xo ka ci abinci" dauke kai yayi yace "Naji" ta karaso cikin parlour'n tace "ni da ita muka yi girkin, tuwo da vegetable soup" ya hade rai yace "Who ask yhu" dariya tayi tace "Toh don ma na gaya maka" ya tabe baki ya mike ya dauki wayarsa ya nufi kofa, mikewa tayi ta bi bayansa da sauri, sai da suka fita yace "Hajja fa?" Tace "Bata nan taje gidan kawarta yau, kasan gobe xa mu koma" ya kalleta yace "Wa yace maki tare xa ku koma, bayan Abban ki yace ya ba mu ke" hade rai tayi tana kallonsa tace "Wa yace maka haka" murmushi yayi ya bude kofar parlour'n Mumy ya shiga ta bi bayansa. Kasa ta xauna tana kallon Mumy tace "Mumy wae ba da ni Hajja xata tafi ba gobe?" Mumy tace "ba tace nan xata bar ki ba" hawaye ne ya cika idonta tace "A'a ae ni ban ce xan xauna ba" Mumy tayi dariya tace "Toh bari idan ta dawo sae ki gaya mata, Meye abun kuka" dariya Junaid yayi yace "Ae sai dai tayi na jini nan xata xauna ita da fatima da khadija" ta fashe da kuka tana kallon Mumy, Mumy ta hararesa tace "kaga wuce dinning ka ci abincin ka bana son haka" mikewa yayi ya nufi dinning yace "Yi hakuri Mumy" mikewa Humainah tayi xata fita daga parlour'n Mumy tace "Ina xa ki" tana goge fuskarta tace "Xan je in jira Hajja" Mumy tayi dariya tace "Ai yanxu xata dawo, xo kiyi xaman ki a nan ki jirata" bata tsaya ba tayi ficewarta a palon. Har aka kira Magrib Junaid na kwance palon Mumy duk ya rasa yanda xae ce mata xai fita, mikewa yayi ya nufi toilet din palon yayi alwala ya fita xuwa masallaci, yana dawowa ya nufi part din Abba sanin ya shiga yanxu, Hajiya ce a parlour'n tana jera masa abincin supper a kasan lallausan rug din tsakar parlour, ya karasa ciki kansa a kasa yace "Ina yini?" Hade rai tayi tace "Ka fita don Allah abinci xai ci ynxu" tsayawa kallonta yayi, dai dai lkcn da Abba ya fito daga bedroom dinsa, Abba ya karaso cikin palon yana kallonsa, karasawa yayi inda Abba ya xauna, ya xauna daga kasa shi ma, a hankali yace "sannu da dawowa Abba" Abba yace "yauwa sannu, ya aikin?" Har lokacin bai dago ba yace "Alhmdllh!" Abba yace "Gud! Daxu baka shigo gaishe ni da safe ba" shafa kansa yayi yace "Na shigo Umma tace kana bacci" Abba yace "Ohk, amma baka karasa bedroom ba" junaid ya gyada kai kawae, Abba yace "kafi kowa sanin bana baccin safe ae" shiru Junaid yayi bai kuma cewa komai ba, kallonsu kawae Hajiya keyi ta gefen ido tana jera abincin da take rai ba dadi don bata so haka ba, Abba ya sauko kasa ya jawo babban food warmer, ya dau plate xai dibi shinkafa, Junaid ya karba yace "Bari in xuba maka Abba" sake masa spoon din Abba yayi, ya dibi shinkafar da stew a gefe da cow meats, snn ya xuba masa vegetables a kai kamar yanda ake masa, Abba ya dauki wani spoon din yace "Bismillah" sai da Abba ya fara ci sannan Junaid ya debi shinkafar a hankali ya kai bakinsa, Hajiya kamar ta hadiye xuciya ganin ko ta kanta Abba bae bi ba, taunar abincin kawae junaid yake ba don yayi masa ba, banda girkin Mumynsa babu na wanda yake ci, girki in ba nata bane ko kallonsa bai yi, shiyasa a ko da yaushe take bata tym dinta tayi masa girki, a tare suka gama cin abincin da Abbansa, bai yi Mamakin sakkowan Abba da wuri ba don in dai suka hada sa da shi, bai daukan lkci yake kuma jawo sa jiki, kwata kwata baya fushi mai tsayi da only son din nasa, hakan ba karamin daga ma su Hajiya hankali yake ba, sun dai rasa yanda xa su yi da Junaid a gidan, a tare suka tafi masallaci sllhn Isha da Abba, sae da suka dawo ya ba Abbansa hakuri a kan abinda ya faru jiya, Abba yace "Its Ohk, ka dai kiyaye halshan ka nan gaba" yace "In'sha Allah Abba" sun jima suna hira da Abba sannan yayi masa sai da safe ya mike ya fita ya shiga part din Mumy, tana xaune palo tana kallo, ya xauna gefenta ya dauki remote xae canxa tasha, Mumy ta karbe remote din tace "ya haka, bari a gama program din mana" kallon Humainah dake kwance kusa da fatima yayi yace "Har kin hakura xaki xaunan kenan?" ta daga kai tana kallonsa bata tanka sa ba ta dauke kai, Mumy tayi dariya tace "babban kawai" bude kofa aka yi hade da sallama, Junaid ya kalli agogo jin muryan El-Ameen, ya ga tara da rabi, Mumy tace "Kai dai baka jin fitan dare koh El-Ameen" junaid yayi murmushi yace "Kin manta likita ne Mumy" El-Ameen ya karaso parlon ya xauna yana murmushi ya gaida Mumy, da fara'a tace "lfya lau bokon turai ya aiki" yace "Alhmdllh Mumy" Fatima tace "Welcome bro" yace "Thank you sis" kallon Humainah dake xaune hankalinta na gun kallo yayi sannan ya kalli Junaid, Mumy tace "baki gaida yayanki ba Humainah" ba tare da ta kallesa ba tana ci gaba da kallonta tace "Ina yini" idonsa na kanta yace "Lfya lau" hira suka dinga yi da Mumy, ganin hiran ba me karewa bace Junaid ya mike ya nufi kofa yace "Ina part dina in ka gama karyan" dariya Humainah tayi a karo na farko ta kalli El-Ameen da ya hade rai yana kallon Junaid, Mumy ma tayi dariyar tace "Ae dae ya fi ka wllh tun da har yana daurewa yayi karyar" Junaid dake bakin kofa ya saka dariya yace "Surutun fa iyakansa a gida Mumy, mutumin da ko magana bai iya yi ma mace ba a waje sai kame kame," El-Ameen yace "Ehh ae kai naga ka iya d'an rainin hankali" banda dariya bbu abinda Humainah ke yi Mumy da fatima na taya ta, Junaid ya juya ya fice daga parlorn yana murmushi, mikewa El-Ameen yayi yace "Bari in je Mumy" Mumy tace "Toh fatima xata kawo maku abinci" toh kawae yace ya fita, Part din Junaid ya nufa ya samesa xaune a parlor ya kunna Tv, El-Ameen yace "Yau ban gan ka ba, kuma I was calling tun daxu baka responding" Junaid yace "I wasn't in a gud mood ne yau" El-Ameen yace "Wacece wannan yarinyar dake xaune parlorn Mumy" Junaid ya kallesa yace "Ya aka yi" d'an sosa kai El-Ameen yayi yace "Umm, tana da kyau ne" dariya Junaid yayi yace really?" El-Ameen yace "What's funny, Allah tana da kyau" Junaid yace "Toh bari ta shigo" ko rufe baki junaid bai yi ba sai ga ta ta shiga palon da sallamarta rike da tray din abinci, El-Ameen ya sunne Kai murya can kasa yace "Don Allah ka rufa min asiri kar kace komai Junaid, wasa nake" Junaid ya fashe da dariya yace "Humainah" ae da sauri El-Ameen ya mike ya rufe bakinsa da hannu yana xaro ido, junaid ya dinga dariya yana tura hannunsa amma yaki sake sa, tabe baki tayi ta ajiye trayn hannunta tace "Mumy tace in kawo" da karfi Junaid ya tura El-Ameen yace "ke kin yi saurayi likita" ae ko rufe baki bai yi ba, El-Ameen yayi hanyar daki da sauri ya shige ya rufe kofar, Junaid ya dinga dariya har da rike kai, hade rai tayi tana kallonsa, can tayi tsaki ta juya ta fice daga parlon, kin fitowa parlor El-Ameen yayi har kusan Karfe goma, Junaid ya shiga dakin yace "Toh wai a haka xan baka kanwar tawa kana kunyar ta!" El-Ameen dake xaune gefen gado yace "ta tafi?" Junaid yace "Aa tana parlor" shiru El-Ameen yayi sai kuma ya mike ya cire shirt din jikinsa ya nufi bathroom, junaid ya bi sa da kallo yana dariya, wanka yayi ya fito sanye da bathrobe, ya nufi closet din Junaid ya fiddo pyjamas ya sa sannan ya dawo ya xauna yana kallon Junaid yace "Amma ba nan xata kwana ba dai koh?" Junaid ya hararesa yace "Nan din xata kwana" El-Ameen ya daga kafada yace "Ohk ni kam am spending the nyt here today, its late and bana son ta gan ni, I came purposely because of ur patient, they've diagnosed her, that is an mata genetic screening, brain scans, neurological exam i.e (checking of vision, hearing, and balance) and other tests, and you knw wat?" Shiru Junaid yayi yana kallonsa, El-Ameen yace "They've found out that she is suffering from post-traumatic stress disorder (PTSD), and this is a serious potentially debilitating condition that can occur in people who have experienced or witnessed may be a serious accident, sudden demise of a loved one, violent personal assault such as rape da sauransu, terrorist incident, or other life-threatening events, you know! A lot of them....." Daga haka yayi shiru yana kallon Junaid da ya kafa masa ido ko kiftawa bai yi, junaid ya sauke ajiyar xuciya ya shafa kansa a hankali yace "But! Is it treatable? I mean can it be cured?" El-Ameen yayi murmushi ya dafa sa yace "Of course yes! But it is difficult to predict how, when, or to what degree someone is going to get better, the major treatment for disorders are Medication, Rehabilation, psychotherapy, and brain surgery, but we are only going for Medication and psychotherapy yanxu, by Allah's own grace xa a dace in'sha Allah" d'an murmushi kawai junaid yayi, El-Ameen ma yayi murmushin yace "Sai dae kuma kudin da xaka kashe fa ba na wasa bane guy, daina murmushi" wani murmushin junaid yayi yace "Wannan ba matsala bane, Allah ya bata Lfya" El-Ameen ya d'aga kafada yace "Gud! But kudin treatment din nawa fa?" Junaid yace "Thought sai ka gama xaka amshi kudi" El-Ameen yyi murmushi yace "Ohk let leave it then"
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
15....
Mikewa junaid yayi yace "Ga abinci a parlor" El-Ameen ya d'an bude ido yace "ba kace tana parlorn ba" Junaid ya hararesa yace "Me xata xauna yi min, ta tafi tun daxu" daga haka ya shige bathroom ya bar sa xaune dakin, mikewa El-Ameen yayi ya isa kofa ya bude yana lekan parlorn, ganin bata nan ya fita, sae da ya kulle kofar parlon da key sannan ya dawo ya xauna gaban abincin, iya wanda xai ci ya diba, ya dauki remote yayi powering tv yana ci yana kallo, kwanciya yayi bayan ya gama cin abincin kan dogon sofa yana kallo, Junaid ya fito daga daki sanye da pyjamas, ya mika masa wayarsa yace "Ummi na kiran ka" mikewa El-Ameen yayi xaune da sauri ya karbi wayar ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren tace "El-Ameen kana ina ne Abban ku duk ya ishe ni da kira, what's wrong with you this days baka xaman clinic, yace tun rana rabon ka da can kuma ni baka dawo min gida ba" Kallon agogo yayi yaga har goma da rabi ya kwantar da murya a hankali yace "Kiyi hakuri Ummi ina gidansu Junaid bai da lfya ne, so I have to stay over da naga dare yayi" Ummi tace "Karyar ka kenan kullum kana gidansu junaid, are you alright Ahmad?" Da sauri yace Ummi ga junaid din ma ki tambayesa ki ji, yana fadin haka ya mika ma Junaid wayar, junaid ya karba suka gaisa da Ummi, tace "Wai baka da lfya junaid" kallon El-Ameen yayi sannan yace "Um Ummi" tace "Toh Allah ya sauwake nayi xaton karya yake min, kace masa ku kira Abba kuyi masa bayani don yana can ya cika" junaid yayi murmushi yace "Toh Ummi" daga haka suka yi sallama ya ajiye wayar, El-Ameen yace "Kaga situation din da ka jefa ni ciki yanxu kai da patient din nan taka ko Captain, kai kullum baka fashin aiki, sannan baka kai wa bayan magrib baka shiga gida ba ni ko ka barni ina ta gantali a titi ko da yaushe, na ma daina aikina a clinic kullum safe dare ina hanyar duba mahaukaciyar ka, look am not taken less than 500k idan na gama treating din mahaukaciyar nan" Junaid yayi murmushi yace "Sure! Wannan ba matsala bane I will pay you."
Da asuba tare Junaid da El-Ameen suka fita xuwa masallaci, suna dawowa El-Ameen ya koma yayi kwanciyarsa ya ci gaba da bacci, Junaid yayi murmushi ganin haka, a xuciyarsa yace lallai kam sleep well, toilet ya shiga cikin minti ashirin yayi wanka ya fito ya shirya cikin khakin sa, kamshin turarrukansa ne ya tada El-Ameen, ya mike xaune yana kallon agogo yace "Wai kai barin gari xaka yi haka da asuba ne da baxa ka bar mutum yayi baccin safe ba captain, duk ka ishe ni ka hana ni bacci don xaka aiki" Junaid na saka wristwatch dinsa yace "sorry, go back to ur sleep, ni yanxu ma xan bar maka dakin" Yana fadin haka ya dauki wayarsa da hularsa ya nufi kofa, El-Ameen yace "Wait, wai Karfe nawa yanxu?" Junaid yace "6:40" daga haka yace "May be ka same ni part din Mumy in ka fito da wuri" El-Ameen yayi tsaki shi kuma yayi ficewarsa. Har El-Ameen ya koma ya kwanta ya mike da sauri tunawa da yayi akwae alluran da yake ma patient dinsa bakwai da rabi. Toilet ya shiga yayi wanka a gurguje ya fito, cikin mintunan da basu wuce goma ba ya kintsa cikin blue shirt da black jeans a closet din junaid, ya feshe jikinsa da turare ya dau wayarsa ya fice daga dakin, yana isa part din Mumy suka kusa cin karo da Humainah xata fito, ae da sauri ya sunkuyar da kai ya bata hanya ta bi ta gefensa tayi gaba abunta, ya sauke ajiyar xuciya ya shiga parlon, ko kallon Junaid dake xaune yana shan tea bai yi ba, ya gaida Mumy ta amsa tace "ga breakfast dinka can a dinning" yace "A'a Mumy sauri nake wlh, idan naje office xan yi" Mumy tace "Kan ka daya kuwa, Karfe nawa yanxu da baxa ka tsaya kayi break ba" kallon agogo yayi yace "Mumy wllh am in a haste ne..." junaid dake kallonsa yace "Da wannan surutun da yanxu ka gama hada tea" hararan sa yayi sannan ya karasa kusa da shi yayi kasa da murya yace "look akwae wani injection da xan ma patient dinka ne b4 7:30, shi yasa nake sauri," da sauri Junaid ya kalli Mumy dake kallonsu yace " Ohh Mumy ashe emergency aka kira sa ne fa" Mumy ta tabe baki tace "Kwa ji da gulmar ku ba ruwana" El-Ameen ya d'an yi murmushi yace "Ko xuwa Karfe goma xan dawo inyi wllh Mumy" Mumy tace "Ka fa rantse" dariya yayi yace "in'sha Allah Mum" mikewa Junaid ma yayi ya shiga bedroom din mumy ya dauki kardigan dinsa yasa don garin da d'an sanyi, ya fito yace "Mumy sai na dawo" ta bisa da kallo kafin ta tabe baki tace "Toh dai kar ka manta ku shiga kuyi wa Hajja sallama don yau xata tafi, ko Abba ma baku shiga kun gaida ba bare mutan gidan" Junaid yace "Xamu shiga" daga haka suka fita daga parlon, sae da suka fara shiga part din Abba suka gaida shi sannan suka yi part din Hajja, tana ta hada kaya, Humainah na xaune gefenta sai rusa kuka take ita ma da tata jakar a gefenta, Hajja na mata ruwan bala'i tana cewa tayi kadan ta koma da ita tunda dama ba ita tace ta biyo ta, xamanta daram a gidan ko suma take, Junaid ya fashe da dariya yana kallon Humainah, ita ko tana ganinsu ta hadiye kukan ta sunkuyar da Kai kasa, Hajja tace "Atoh, ka dai gan ni da gantalalliyar nan wae sae ta bi ni Amadi, sae kace ance mata wahalalla nake kamar irin ni na ce ta biyo ni din nan shegiya, nufin ta in koma da ita muna galallawa a titi, to dadin abun dai ba kudin banxa gare Muhammad ba, kuma ubansa Ahmad bae ce yaje xae gani ba bare ya biya kujeru biyu na jirgi" Junaid ya dinga dariya yana kallon Humainah, El-Ameen yyi murmushi ya gaida ta, ta kallesa ta gefen ido ta ci gaba da abinda take ba tare da ta amsa ba tana ci gaba da yi ma Humainah masifa, dariya yayi yana shafa kansa don yasan me yasa bata amsa ba, Junaid ya ciro dubu talatin da ya tanadar mata dama ya ajiye gabanta yace "Gashi ni da El-Ameen ki sha ruwa da dabbino a hanya kar ki je kina masu amai a jirgi" ta washe hakora tana kallon El-Ameen tace "Toh Allah maku albarka, ga kuma amanar jikata a hannun ku, don mayu sun yi yawa gidan, Amina na damka ma ita, tamkar yanda xata yi ma fatima xata yi mata" Junaid yayi murmushi yace "In'sha Allah" Hajja ta kara da cewa "Kuma ga maganin tsari kala kala can na kai ma uwarka idan taga dama ta baka, ka kuma sanma marowacin abokin nan naka don duniya bbu gaskiya yanxu, barin kai da kiri kiri matan ubanka ke nuna basa sonka" shi dai El-Ameen sae kallon agogo yake don bai son lkcn nan ya wuce duk hankalinsa yayi gun patient dinsa, Junaid yace "Toh Hajja" kallon Humainah yyi ya mike yace "Ae sae ki dauki jakar ki kai bangaren Mumy" ta fashe da kuka, Hajja tace "Tashi ki ban waje yar wahala, bbu inda xani da ke ki xauna gidan wan ubanki don shi xaki gani ranan gobe kiyama" Humainah na kallon Junaid cikin kuka tace "Ya Ahmad kace mata don Allah ta tafi dani wllh bana son in xauna gidan nan kullum fada ake yi" Hajja tace "A haka xaki saba ki koya ki iya kema" Junaid ya fice yana dariya ta bi bayansa da sauri, El-Ameen ya kuma yi ma Hajja sallama ya fice shi ma yana danne dariyarsa wai kullum fada, sae da suka fito compound Junaid ya kama hannunta yace "kinga ki bari ta tafi sai in maida ke next week I promise" da haka ya lallabata tayi part din Mumy tana kuka, Umma na daga balcony dinta xaune haka ma Hajiya kamar masu cin kasuwa kuma duk don sbda sa ido suke yin haka, ko kallonsu bai yi ba yayi gun motarsa, El-Ameen ma bai kalli idan suke ba ya bi bayansa, duk suka bi su da kallo ko wanne da tunaninta a xuciya, El-Ameen ya kwace key hannun Junaid ya shiga driver seat ya tada mota, Junaid yayi murmushi ya xaga daya side din, yana gama ba motar wuta ya ja suka har compound din bayan masu gadi sun bude gate, gudu kawae El-Ameen ke shararawa, Junaid yace "Wae lafiya wannan gudun Ahmad" ko kulasa bae yi ba, Junaid yace "Look kar kaje ka kashe ni ma uwata a banxa, wannan ae hauka ne are we flying, plss ka tsaya in sauka" nan ma dai bae kulasa ba sai da ya gansa a kofar gidansa yana kallon agogo yaga bakwae da minti ashirin, yyi ma junaid wani kallo yace "you heard me ryt daxu amma" daga haka ya bude motar ya shiga gidan, Junaid ya kalli agogo ganin da sauran time ya fito ya nufi cikin gidan shi ma, bbu kowa parlon sai kamshi dake tashi Mama Jummai ta tsaftace ko ina, daki El-Ameen ya nufa, ya tsaya daga bakin kofa bayan yayi sallama yana kallonsu, tana xaune gefen gado Mama jummai na packing mata gashinta, ta gama shiryata tsaf cikin doguwar rigar kanti sea green da stones gold colour a jiki, tun daga nesa kana iya ganin white eyeballs dinta sbda uban kwallin da mama jummai ta sa mata, wanda hakan ya kara fito da kyan idanuwan nata, kallonta kawae yake sannan ya shigo dakin, Mama jummai na murmushi ta gaida shi tace "Na ma yi xaton baxa ka xo yau ba ganin har lkcn xuwan ka ya wuce" murmushi yayi yace "Na makara ne mama" ta mike daga durkushen da take tace "Bari in hada mata abinda xata ci" daga haka ta fita, ya karasa kusa da ita ya duka yace "Morning" kallonsa kawae take, sai kuma ta dauke kanta, mikewa yayi da sauri tuna lkci na wucewa ya nufi gun alluranta, cikin few minutes ya hada alluran yayi mata, xuwa yanxu ta fara hakura ta tsaya yayi mata alluran ba gardama, dagota yayi suka fita daga dakin yana rike da hannunta, Junaid na xaune parlor suka sauko ya bi su da ido, tsakar parlon El-Ameen ya xaunar da ita kan rug, Mama jummai ta fito daga kitchen rike da bowl din pap tace "Kaga jiya da rana na dama kunu ina sha naga tana tana kallonsa sai na bata ae ko tasha, kuma da yawa ta sha, shiyasa ma yanxu nayi mata" El-Ameen yace "Ohk" xaunawa Mama Jummai tayi kusa da ita ta fara bata, sau biyu ta sha ta fara kokarin amshe spoon din hannunta, shi dai Junaid kallonsu kawae yake, El-Ameen ya karbe spoon din hannun Mama jummai ganin ta dage sai ta karba yana mata wani irin kallo, lkci daya ta nutsu, da kansa ya shiga diban pap din yana kai mata baki tana bude bakin tana amsa, Mama jummai tayi murmushi ta Mike ta bar parlon don xuwa ci gaba da aikinta, cokali hudu kadai ta karba ta dauke kai, ya hade rai ya dafa kanta ya kai mata pap din spoon din baki, da kyar ta bude bakin ya xuba mata tayi saurin maido shi spoon din, wani tsawa ya mata, lkci daya jikinta ya dau rawa ta bude baki ya kuma maida mata ta hadiye, sake diban wani yayi ya bata taki karba yace "I will slap you fa" bata fuska tayi tana komawa baya a hankali, murmushi yayi yana kallonta, sai kuma ya lumshe ido ya kai kunun bakinsa ya sha, da sauri ya bude ido ya juya yana kallon junaid yaga kallonsa kawae yake. Jefar da spoon din yayi cikin pap din duk ya daburce yace "I I didn't even realize wat I was doing faa, hankali na duk baya wajen" ya runtse ido yana yamutse baki da fuska yace "So irritating" Junaid ya tabe baki ya mike ya dau wayarsa da makullin motarsa dake ajiye kan kujera ya fice daga parlon, El-Ameen ya bi sa da kallo, ita ko daukar spoon din tayi ta juya shi upside down cikin pap din ta debo ta Kai masa baki, murmushi yayi yana kallonta ya kauda Kai, ai ko ta xuba masa a kan hanci ta kuma debo wani xata kai hancin ya rike spoon din yana dariya yace "Keee" kokuwa suka shiga yi ita fa sae ta sa masa a hanci ta wani hade rai, da sauri ya bude baki sae ta xuba masa d'an kunun da ta debo ciki, ya lumshe ido ya shanye Sannan ya dauke bowl din ya boye a bayansa, xata mike ya komar da ita ya xaunar yace "C'mon"
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
16.....
Mama jummai ta shigo palon rike da bucket tace "Har ta shanye?" Yace "A'a barnatar da shi xata yi shi yasa na boye, ta koshi kuma" mikewa yayi ya dauke bowl din yace "Xan tafi yanxu, sai na dawo anjima mama" ta karba bowl din tace "Toh Allah ya tsare" daga haka ya ja dogon hancinta yayi hanyar kofa, mikewa tayi da sauri ta bi bayansa, Mama ta saka dariya tace "Au, toh gashi xata bi ka" juyawa yayi da sauri yana kallonta ya galla mata harara yace "I will knock you idan kika xo nan" kamar ta ji me yace ta tsaya tana cixgar stones din rigarta tana kallonsa, ya juya ya fice daga parlon, mama jummai ta karaso ta kama hannunta suka koma cikin parlour'n. El-Ameen na fita ya rike waist a waje tunawa da yayi ai ba mota kuma bbu kudi hannunsa, tsaki yayi ya nufi main road da kafa ya tsayar da adai daita ya gaya masa anguwarsu, suna isa yace yana xuwa sannan ya shiga ya fito masa da kudi ya basa ya koma ciki, Ummi dake parlor sai binsa da kallo take bayan ta amsa gaisuwarsa tana ganin ya nufi daki tace "Xo nan Ahmad" komawa yayi ya xauna kasa yana kallonta yace "Gani Ummi" tace "Ina kake xuwa this dayz baka xaman office?" Ya d'an sosa kai yace "Ummi, dama... To wai Ummi wa yace bana xama office ni da kullum sai na je clinic" Ummi ta galla masa harara tace "Am not joking Ahmad, wannan sabon salon da ka tsiran ma rayuwarka ba fishshe ka xai yi ba don b'ata ma mahaifin ka rai kawae kake" ya sunkuyar da kai bai ce komai ba, Ummi tace "Magana ta biyu kuma tunda kai ka kasa fito da mata toh ni na xabar maka...." Da sauri ya D'ago kai yace "Ummiii!" Tana masa mugun kallo tace "Ehh, ni ma xan rakaka gidansu yarinyar da kaina in ma ya kama ni xan maka maganar sai inyi, kuma ba wata bace facce 'yar abokin Abban ka Fiddausi" wani xufa ne ya shiga keto masa duk ya ma rasa abinda xae ce, da sauri yace "Ummi ni fa na riga da na samu yarinyar da nake so" Ummi na hararansa tace "Wannan kuma ba matsala ta bace, sai dai kuma ka raina ma kanka hankali ba ni ba" ya marairaice mata yace "Ummi Allah kuwa da gaske, a gidansu junaid ma take" Ummi tace "Wacece kenan?" Yayi kasa da kai a hankali yace "Humainah take ko wa? kuma niece din Junaid ce" Ummi tayi shiru tana hararansa yace "Allah kuwa Ummi, naji kamar ina sonta" tace "Toh ae xanje gidansu junaid din kuwa" bai kuma cewa komai ba sai tunani yake anya gskya ya fadi ma Ummi kuwa, can dai ya mike yace "Bari in tafi office Ummi", tace "Allah ya tsare"
Karfe Hudu saura Junaid yayi parking kofar gidan El-Ameen ya fito, ya koma back seat ya cire hularsa ya ajiye da rigar khakinsa ya dauki well ironed shirt dinsa dake bayan mota don bae rasa mofti a motar ya saka sannan ya fito ya shiga gidan, Mama jummai na share parlor ita kuma tana tsaye jikin bango kamar xata shige ciki, Mama jummai tayi masa sannu da xuwa, ya amsa tare da gaisheta hankalinsa na kanta, Mama jummai tace "ka ganta can tafi awa biyu tsaye taki xaunawa" murmushi yayi ya karasa inda take tsaye, ya kama hannunta suka dawo parlorn ya xaunar da ita, ya rike chin dinsa da duk hannunsa biyu yana kallonta ita ma kallon nasa take, fine beard din da ya xagaye bakinsa ta kai hannunta ta taba, yayi murmushi ya kama hannun cikin nasa yana kallon manyan fararen eyeballs dinta cikin sanyin murya yace "I will call you Jasmine! Do you like dat?" Kwace hannunta tayi daga nasa, ya tsura mata ido, bude kofar parlor aka yi El-Ameen ya shigo, ae tana ganinsa ta mike da sauri ta nufesa ta isa gabansa ta tsaya, Junaid ya bi ta da kallo, El-Ameen ya ja hancinta ya bude hannayensa yace "toh dai bbu abinda na siyo maki" kallon junaid yayi yace "The great Capt Ahmad Junaid ashe kana nan" mikewa junaid yayi yace "Sure!" Daga haka ya nufi kofa, El-Ameen yace "ba dai har xaka tafi ba" junaid yace "Yea daga office nake" daga haka ya fice daga parlorn, bin sa da wani irin kallo El-Ameen yayi kafin ya fita yayi saurin cewa "Hey a minute" junaid ya tsaya sannan ya juya yana kallonsa, El-ameen yace "gaskiya ya kamata ka shiga kasuwa ko kuma ka bada kudi a shiga a sama mana TV a gidan nan, ko ka mance yanda muka yi da kai?" Junaid yace "I will transfer the money later sae ka samu me siyo maka TVn" yana gama fadin haka ya fice daga palon, El-ameen ya d'aga kafada ya kama hannunta suka koma parlor.
As usual ya dade xaune mota bayan yayi parking a lot din gidansu kuma har lkcn bae kashe mota ba yana danne dannensa a waya, Khadija ce ta fito daga part dinsu ta karaso gun motar ta bude tace "ina yini yaya A.jay" ya kalleta yace "Lafiya lau" ta d'an marairaice masa tace "yaya yau ciwo ciki na ke min wllh" tabe baki yayi ya ci gaba da danna wayarsa, ta dan shagwabe masa tace "Yaya ka d'an ban kudi in siya magani mana, Umma ta ki bani" dubu daya ya xaro aljihunsa ya mika mata cike da murna tayi masa godiya ta kara gaba, shigowar motar Suhaima yasa shi kashe motarsa ya fito ya rufe ya fara tafiya, Hajiya ce suka fito daga part din Umma da wata mata alamar rakiya xa su mata, duk suka bisa da kallo, ba tare da ya kallesu ba ya gaida su don dama sai lokacin da yayi suit dinsa yake gaishesu, matar ce kadai ta amsa shi, bae damu da haka ba yayi part din Mumy, Matar da ta bisa da kallo ta maido da dubanta gun su Umma murya can kasa tace "Shine yaron hala?" Cike da tsanarsa Hajiya tace "Ehh wllh" matar tayi wani murmushi murya can kasa tace "Duk ku kwantar da hankalin ku, ku bar min komai a hannu na baxan baku kunya ba" babu wanda yace komai cikinsu suka rakata har waje gun motar ta. Junaid na shiga parlon Mumy ya tarda Humainah kwance da ganinta kasan ba kuka kadan tayi ba, dariya ya saka yace "ohh shikenan an bar mana ita" mikewa tayi xaune idon ta ya cicciko ta kwalo ma Mumy kira, Mumy ta fito daga daki tace "be careful Mr" dariya yayi yana shafa kai yace "Ya hakuri Mumy, ina yini" ta karaso parlorn tace "Nayi xaton ae baxa ka kashe motar ka shigo gida ba" yyi murmushi yace "Ac fa nake sha Mumy" ta tabe baki tace "Haka ne, ga abincin ka can" kujera ta xauna tana kallon Humainah tace "Kema kije ki dau naku abincin ke da fatee, ko baki hakura ba har yanxu" bata ce komai ba tayi kasa da kai, Junaid ya mike yace "Xan dawo Mumy bari inyi wanka" tace "Ohk," bin sa da kallo tayi sae da ya kai bakin kofa tace "Canxa kaya kayi office" murmushi kawae yayi ya fita. Wanka yayi ya kuma canxa kayan jikinsa yyi kwanciyarsa parlor don bai jin yunwa, ya kusa awa daya kwance Humainah ta shigo parlorn rike da tray dauke da abincinsa, ta karaso ta ajiye masa, ya mike xaune cike da xolaya yace "Shikenan fatima ta huta an kawo mana maid kyauta" mikewa tayi a fusace xata fita ya rikota yana dariya yace "Ke dalla wasa nake maki" ta fixge hannunta tace "Bana son wasan" ya daga kafada yace "Ni kuma sai nayi din" wani kallo ta shiga yi masa fuska daure, ya hade rai yace "Toh in kince a biya ki kudin aikin ba sai a biya ki ba ma" hawaye ya cika idonta ta juya xata fita aka bude kofa El-Ameen ya shigo da sallama, da sauri ta kuma juyawa tana kallon Junaid da ya bude ido ganin El-Ameen da ya kasa Karasowa cikin parlorn, Junaid ya mike yana dariya yace "C'mon ka karaso frnd" El-Ameen yace "Um ban gaida Mumy ba am coming" da sauri junaid ya karasa ya rufe kofar da key ya cire sannan yace "ba ta kofarta ka wuce ba kafin ka karaso nan" El-Ameen ya ma rasa me xai ce masa, dawowa cikin parlorn junaid yayi ya xauna yana kallon Humainah yace "Toh ae sai ki goge hawayen yanxu tunda ga shi ya xo koh, duk kin isheni kin daga min hankali ina El-Ameen toh ga ki ga shi" Humainah tayi wani kara ta durkushe wajen ta shiga kai masa duka tana cewa "ni bana son haka ya Ahmad, bana so" El-Ameen yayi murmushi ya nufi daki, da sauri Junaid ya mike ya rigasa shigewa dakin ya saka key daga ciki yace "Ji min munafukai" gajiya yayi da tsayuwa ya dawo parlorn, can nesa da ita ya xauna yace "Ina yini" ta d'an kallesa ta hade rai tace "Lfya lau" bai kuma cewa komae ba ya dau remote yayi powering Tv, sun kusa minti talatin parlorn bai ce mata ba bata ce masa ba, kamar wanda ya tuna abu ya mike da sauri yana kallon agogo ya nufi dakin junaid ya kwankwasa yace "Look captain akwae drugs din da xanje in ba patient dinka open the door plss ka bude kofar parlor am leaving" junaid dake kwance ya fara bacci ya mike jin abinda El-Ameen yace ya bude kofar, El-Ameen yace "D'an rainin wayo bacci ma kake koh" fitowa junaid yayi suka dawo parlor a tare, kallon Humainah yayi yana murmushi yace "Har kun gama xancen kanwata" ta hararesa ta dauke kai, shi kam El-Ameen har ya kai kofa, Junaid yace "toh dai ki ajiye abinda ya baki idan na dawo mu raba, kuma ki d'an gyara min bedroom saura ki min satan turare ki ga ko ba na saurayin ki xan je in sace ba" yana fadin haka yyi kofa ya bude ya fice yana dariya, El-Ameen ma ya fita, Part din Mumy suka shiga El-Ameen ya gaida ta, Junaid yace "Xan d'an rakasa indawo yanxu Mumy" Mumy tace "Toh sai ka dawo" daga haka suka fice da El-Ameen. suna isa El-Ameen yace "Baka yi min transfer din kudin Television din ba fa, if you provoke me xan fa je in siya da kudina" Junaid yace "I forgot xan yi" fitowa suka yi daga motar suka shiga gidan, Mama jummai na xaune parlor ta daura kanta kan cinyarta idonta rufe, El-Ameen yace "dama tana bacci ba da daddare ba" Mama jummai tace "Ina jin bata jin dadi ne yau, sau biyu tana amai ga jikinta da dumi, ita da ko xama bata yi da rana bare ta kwanta" El-Ameen ya karasa ya durkusa gabansu ya d'ago kanta ta bude ido tana kallonsa, ya gyara mata gashinta a hankali yace "Malaria... I guess" xaunawa Junaid yayi shi dai bae ce komai ba, El-Ameen ya d'agota ya xaunar da ita kan kujera yace "Sorry...." Ya kalli Junaid yace "Ka bada kudi in tafi in siyo mata drugs da injections" kallonsa kawai Junaid yake bai ce komai ba, El-ameen ya kalli mama sannan ya kallesa ya juya xuwa harshen turanci yace "It's not a matter of looking at me dat way captain, don't forget she's ur patient, ur mind agreed to the terms nd condition of helping her, nd I guess before u jumped into the conclusion of doing dat, you already know...." Katse sa junaid yayi yana masa wani kallo yace "did you hear me complain?" El-ameen yayi dariya yace "Not dat I don't have the money to assist you but...." Tsaki Junaid ya ja yace "Enough plss, I don't even need ur goddam help," El-ameen yayi murmushi yace "Ni kuwa kake bukatar taimakona, cos lokacina da na ware for her is far far better then dat money you are spending, anyway! 20k will do for the test nd everything" Atm junaid ya ciro ya mika masa ya karba, ya mike ya haura sama syringe ya dauko a daki da plastic tube na drip ya dawo parlon, da kyar ta bari ya debi jininta don sae da Mama jummai ta riketa, ya mike yace "Bari in je in dawo yanxu, Mama ki d'an bata kunu ko kadan ne ta sha" Mama tace "Toh" sannan ya fita daga parlorn, xamowa tayi daga jikin mama ta kwanta kasan tiles, mama ta d'agota tace "Sannun Kinji Baiwar Allah, Allah ya sauwake maki" kara ta saki alamar bata son tashi a kasan, Mama ta kyaleta ta tafi kitchen, mikewa Junaid yayi ya isa gabanta ya durkusa, kallonsa kawae take kafin ta kauda kanta, ya d'agota a hankali yace "Sorry Jasmine, get well soon" mikewa tayi ta kwace hannunta a nasa ta fara tafiya, ya bi ta da kallo ganin yanda take tafiya, can jikin bango taje ta tsaya, ya mike ya koma kujera ya xauna, har mama ta fito kitchen rike da pap bata bar jikin bangon ba, Mama ta ajiye bowl din hannunta ta karasa ta kamo hannunta, da kyar ta biyota suka dawo parlor ta xaunar da ita ta shiga bata kunun amma taki sha, da ta takurata mikewa tayi ta dawo kusa da junaid ta xauna gefen shi ta jingina jikinsa ta rufe ido gam, duk tayi wani laushi da ganinta kasan bata da lafiya, shi kam kallonta kawae yake wani tausayinta ya dinga ji, ya ji dama ciwon ya dawo jikinsa, ya rungumota jikinsa a hankali yace "Sorry My Jasmine" mikewa mama tayi ta mika masa kunun tace "Toh ka bata Junaid kila ta karba ko kadan ne" yyi murmushi ya karba ya janyeta daga jikinsa ta bude ido tana kallonsa, ya debi kunun kadan ya kai mata baki, ta kauda kai da sauri, rasa yanda xae yi ya bata yayi, kawae ya ajiye, ita ko ta sauka kasa ta kwanta, bayan minti goma El-Ameen ya shigo parlorn, ya ajiye ledan hannunsa ya d'agota yana kallon junaid yace "Ta sha kunun" girgixa masa kai kawai yayi, El-Ameen ya jawo bowl din kunun ya debo ya kai mata baki, ta kauda kae da sauri, ya hade rai yace "I will knock you, c'mon bude baki" kara ta saki ya xuba mata kunun a baki ta xubar da sauri, ya daka mata tsawa, nan da nan jikinta ya dau rawa ya debi wani ya bude bakin ya xuba mata, da kyar ta hadiye hawaye na sakkowa idonta, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, haka El-Ameen ya dinga bata tana karba da kyar har tayi four spoon sannan ya ajiye, ya fara hada drip da xai sa mata da alluran da xai mata, ita ko kwanciya tayi kan tiles ta rufe ido, yana gama hada alluran ya D'ago ta ta bude ido, gown din jikinta ya d'aga don a lap xae mata alluran, kallon junaid yayi yaga idonsa na kansu, da sauri junaid ya kauda kai, El-Ameen ya kwantar da ita yayi mata alluran, tun bai gama ba ta fara kokarin mikewa, duk jikinta yayi xafi ba kadan ba, ya maidata ya kwantar har ya gama sannan ya dagota yace "Sorry" komawa baya kawae take hawaye na xuba idonta, El-Ameen ya d'an yi murmushi don hawayen shaidar wataran xata dawo me hankali ne sai dai fatansa daya kar tayi loosing memory dinta, kusa da junaid ta koma ta xauna gefensa ta daura kanta a kafarsa ta rufe ido, yana son ya lallasheta duk da yasan ba gane nufinsa xata yi ba amma bae son yin hakan gaban El-Ameen ya ya kafa masu ido, hakan yasa ko kallonta bai yi ba, El-Ameen yayi murmushi ya mike ya nufi kitchen don dauko cup yyi mata diluting drugs ya bata ta sha, Junaid ya kai fuskarsa dai dai nata a hankali yace "Sorry Jasmine...." Ta bude idonta da suka sauya launi tana kallonsa, da sauri ya D'ago jin fitowar El-Ameen, ko kallonsu bai yi ba yi diluting drugs din da ruwa ya dawo kusa da su ya xauna ya dagota yace "Tashi ki sha magani" kara ta saki ta boye fuskarta jikin junaid tana shishshige masa kamar xata shiga jikinsa, El-Ameen ya mata wani tsawa, jikinta na rawa ta rike Junaid tana ihu, janyeta El-Ameen yayi ya hade rai yace "Keehh" cup din ya kai bakinta ta ki budewa, ya mata wani rankwashi ta kwala ihu, da sauri ya jawota ya juye maganin bakinta ya rufe hancinta, sae da ya tabbatar ta shanye su gaba daya sannan ya cire hannunsa hancinta, lkci daya duk ta amayo maganin jikinsu gaba daya su ukun, daga nan ta dinga amai gashi bata ci komai ba, El-Ameen ya mata wani tsawan da ya rikitata ta fasa ihu xata mike ya fixgota da karfi ta fado kansa ya rungumeta tsam jikinsa, sunkuyar da kai junaid yayi jin wani abu da bae taba ji ba a xuciyarsa a lkcn, a hankali ya shiga cire shirt din jikinsa da ya baci da amai, Mama jummai dake tsaye daga bakin kofa cike da tausayinta taji kamar tayi mata hawaye duk ita ma jikinta yayi sanyi, mikewa junaid yayi har lkcn bae kallesu ba ya haura sama, El-Ameen ya bi sa da kallo, a hankali ya d'ago kanta jin ta sakar masa jiki gaba daya ya ga bacci tayi, kamar me rada yace "Jewel!" A hankali ta bude ido tana kallonsa.
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
17.....
El-Ameen ya sakar mata murmushi murya can kasa yace "Sorry!" kauda kai tayi, ya mike ya d'agata suka tafi sama, bin bayansu mama jummai tayi, yana shiga daki ya xaunar da ita gefen gado ya xauna gefen gadon shi ma yana cire shirt din jikinsa Junaid ya fito daga bayin rike da shirt dinsa da ya wanke, ko kallonsu bai yi ba ya fice daga dakin El-ameen ya bi sa da kallo, yana sauka downstairs ya dau makullin motar El-Ameen ya fice daga gidan. Gida ya tafi, yana gama parking ya fito rike da shirt din nasa ya nufi part dinsa, su Hajiya dake xaune tsakar gidan suka bi sa da kallo ganin daga shi sai singlet da jeans, bae ko kallesu ba ya bude kofa ya shiga parlornsa ya rufe, kallon juna suka yi tare da tabe baki, bathroom Junaid ya shiga ya sakar ma kansa warm shower, ya fito daga karshe ya shirya cikin jallabiya duk jikinsa ba kwari ya kwanta har lkcn bae ji xuciyarsa ta dawo dai dai ba. Kiran magrib yasa shi mikewa ya fita xuwa masallaci, Yana dawowa mosque ya shiga part din Mumy, Humainah ce kadae xaune parlor tana kallo, ya xauna fuskarsa daure yace "Mumy fa?" Ta tabe baki ta dauke kai, bae kuma cewa komai ba har Mumy ta fito tace "Har ka dawo" ya shafa kansa a hankali yace "Eh Mumy" tace "ga abincin ka can, na daxu ma baka ci ba sai dawo da shi Humainah tayi" xae yi magana aka bude kofa Sadiya ta shigo ta tsaya daga bakin kofa tana taunar cingam tana kallon Mumy tace "Wae Abba a kira ki!" Mikewa junaid yayi yace "Ke don uwar ki baki iya sallama bane xaki shigo ma mutane parlor kamar dabba" Mumy ta hade rai tace "Ahmad!" Wani mugun kallo yake mata xuciyarsa na tafarfasa, ita ko ta tabe baki ta kauda kai tana murgurda baki, wani tsawa ya mata ya nufeta Mumy ta fixgosa tace "Xan saba maka wllh Ahmad, kana da hankali kuwa" Sadiya tayi tsaki ta fice daga parlon fuu, cikin bacin rai yace "Mumy ko gaisheni fa 'yar iskar nan bata yi a gidan nan yanxu, ni din sa'anta ne" Mumy tace "Sae me don bata gaishe ka ba, uwar me gaisuwarta xae kara maka, ko da can gaishe kan take idan ba gulma ba, kaje an bata maka rai a waje xaka xo ka huce ma mutane a gida, ina raba ka da mutanen nan baka ji koh Ahmad, dole ne sae ka tanka duk abinda suka yi" shiru yayi bae ce komai ba ya koma ya xauna ya rike kansa don shi kansa bai san me yasa yayi hakan ba, he just don't know what came over him, don da can ma ba gaishesa step sis din tasa take ba kuma bai taba ce wa komai ba, Mumy tayi kwafa ta dau hijab dinta ta fita. dawowa kusa da shi Humainah tayi ta xauna kasa a hankali tace "Kayi hakuri ya A.jay, nima daga yau baxan sake gaisheta ba, shikenan na rama maka" kallonta kawae yake bai ce komai ba, sai kuma ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe idonsa, ta bata rai tace "Shine ka min shiru koh" ba tare da ya bude idon ba yace "Anki maki maganan, ke din gaishe ni kike?" Mikewa tayi ta take kafarsa ta nufi daki tana cewa "Idan ba sai na gaisheta ba gobe me nake!" ya bude ido da sauri ya bi ta da kallo yana murmushi, Bayan kusan minti talatin Mumy ta dawo parlor, junaid ya mike ya dawo gefenta ya xauna a hankali yace "Kiyi hakuri plss mum I don't know what came over me, baxan sake ba wllh" tace "It's ohk" daga haka bata kuma cewa komai ba shi ma haka, bayan kusan minti goma yace "Mumy fushi kike da ni I know, don Allah kiyi hakuri plss" ta girgixa kai cike da takaici tace "uhn naxari kawae nake ne Ahmad, kaji inda yan gidan nan suka kuma bullowa wae duk me girki shi xae yi girkin gidan gaba daya yanxu, sae kace da can basu suka ce kowa yayi nasa ba, ko me suke nufi da hakan kuma oho" junaid ya d'aga kafada yace "Sai su ci kayansu ai, don ni baxan ci girkinsu ba" daga haka ya mike ya nufi dinning, Mumy tayi murmushi a xuciyarta tace "Ae dama baxan ma bari kaci abinda ya fito daga bangarensu ba idan Allah ya yarda"
Kwata kwata Junaid bai runtsa daren ranan ba ya rasa dalili, sae dai yafi danganta haka da tausayin baiwar Allahn da yake, Washegari Wednesday bai yi wani breakfast din kirki ba ya fita as early as 7, tun daren jiya El-Ameen ke kiransa baya dauka, a hankali yake driving ya kalli wrist watch dinsa yaga bakwae da minti goma, ganin yana da sauran time yasa shi nufan gidan El-Ameen, a waje yayi parking ya shiga gidan, kwance ya tarda El-Ameen a parlor yana bacci kan 3sitter, Mama kuma na kitchen, ya kusa second ashirin tsaye yana kallonsa sannan ya tabe baki yyi hanyar stairs, a hankali ya tura kofan dakin ya ganta kwance kan gado cikin bargo, ya karasa cikin dakin yana kallon empty roban drip din da aka cire mata, gefenta ya tsaya ya yaye bargon jikinta, ya tsura ma fuskarta ido, Ya fi minti biyu yana kallonta tana bacci, ya daura hannunsa a hankali a forehead dinta ya ji da d'an dumi, bude ido tayi da sauri ta mike xaune, kallonsa take ko kiftawa bata yi, lkci daya ta saki wani kara ta shiga komawa baya tana ihu da karfi, ya koma baya da mamaki yana kallonta, El-Ameen ne ya shigo dakin da sauri, ya tsaya daga bakin kofa ganin Junaid a dakin, sauka tayi daga kan gadon tayi kofa da gudu xata fita tana ihu har lkcn, El-Ameen ya fixgota yace "Keeh Meye haka!" Ihu ta dinga yi xata kwace kanta tana yi tana waigan Junaid, El-Ameen ya kalli Junaid yace "Ohhh it seems Khakin nan naka ke tsoratata fa Captain" Junaid ya juya yana kallon kansa a madubi, farin well ironed navy shirt ne jikinsa, well tucked in cikin navy blue trousers dinsa, sae hat dinsa a kai, sae black socks din dake kafarsa don ya cire takalmin a waje, juyawa yayi ya fice daga dakin, sai a sannan tayi tsit sai dai har lkcn jikinta rawa yake tayi lamo jikin El-Ameen, El-Ameen yayi dariya yace "Toh fah" xaunar da ita yayi gefen gado yana kallonta yace "That's intresting! kina tsoran soldiers kenan!" Kauda kai tayi ta xamo kasa ta kwanta, mikewa yayi yana kallon agogo, da sauri ya fita dakin ya sauko parlor sai dai bai ga junaid ba, ya kalli Mama dake shara yace "Mama junaid din ya tafi ne?" ta washe baki tace "Anya ya tafi, kaga makulli can ya ajiye kan kujera, ashe sojan ruwa ne yau na gansa da khaki" Dariya El-Ameen yayi yace "Ehh Navy ne" tace "Allah sarki, khakin sun masa kyau" kallon Makullin yayi yaga ta motarsa ce, ya d'an tabe baki ya karasa ya dauka yace "D'an rainin wayo" fita yayi don ganin ko motar tasa na waje yaga bbu motar makullin kawai ya kawo masa, girgixa kai yayi ya koma cikin gidan. Junaid na kwance parlor da yamma b4 magrib yana danne dannen waya, khadija ta shigo parlorn, Karasowa tayi ta xauna gefensa tace "Ina yini ya A'jay?" Yace "Lfya lau, kar ma ki fara tambayata kudi don bani da" dariya tayi tace "Kai yayana" sai kuma ta d'an yi shiru, a hankali tace "Kasan me yaya, karka ci abincin gidan nan yau, just go out and get somethin to eat ae kasan yanxu an daina girki daban daban koh" yana kallonta yace "Why!" Ta daga kafada tace "Just, beside ma porridge ne kuma ae bama ka ci" mikewa tayi tace ina xuwa, ta fice daga parlon, ya bi ta da kallo yana murmushi. Wayarsa ne ya soma ring ya duba ya ga El-Ameen ke kiransa, sai da ya kusa katsewa sannan ya daga ya kai kunne bai ce komai ba, daga daya bangaren El-Ameen yace "You try fa captain, nine ban san dadin gidanmu ba ko, how on earth xaka dinga bari na ni kadai ina fama da patient din ka?" Junaid ya tabe baki yace "Naga tana tsorona ne, kai ne bata tsoro dat's why I decided not to show up today" El-Ameen yayi tsaki yace "Didn't you see dat uniform dinka ke scare dinta, wear mofty while coming always, yanxu dai I will text u some drugs da xaka siyo idan kana tahowa, and ka siyo mata fruits taki cin abinci" Junaid ya kuma tabe baki ya katse wayar ya ajiye. Kallon agogo yayi yaga an kusa magrib, ya mike ya shiga toilet ya dauro alwala sannan ya fito ya dau makullin motarsa da Atm sae wayarsa ya fita ya rufe kofarsa. Bangaren Mumy ya fara shiga, yana kallon fatima dake guga yace "Mumy fa?" Tace "tana bayi" juyawa yayi ya tafi masallaci, ana idar da sllh ya dawo gida, Mumy da fitowarta daga kitchen kenan tace "Ga abincin ka a dinning can" kallon dinning din yayi yace "Porridge?" Mumy tace "Shi kake so?" Girgixa mata kai yayi yace "No khadija ce tace min porridge aka yi" Mumy tace "Ehh amma kai na maka girkin ka daban" yace "Toh nagode Mum, but xan d'an fita yanxu idan na dawo xan ci" tace "Fita kuma? Ina xa ka?" Yayi kasa da murya yace "xan d'an raka El-Ameen wani gun ne, daga can xa mu je kallon kwallo" ta tabe baki tace "Xa dai ku je tadi koh?" Dariya yayi yace "A'a fa Mumy" murmushi tayi tace "Toh kar dai ka wuce 8:30 a waje, ka ma shiga gun abbanka kuwa" yace "Ehh daxu na shiga" daga haka ya juya xai fita, Humainah tace "Ya Ahmad xan raka ka" yace " Nooo" daga haka ya fice daga parlon, Mumy tayi dariya tace "Ki bari ran lahadi ya xaga da ke katsina" tayi murmushi tace "Toh Mumy, ko yace A'a kiyi masa masifa sai ya kai ni" sae da junaid ya fara siyan abubuwan da El-Ameen ya ce masa ya siya ready made din fura da nono sannan ya nufi gidan, Mama kadai ce kwance parlor kan darduma, ya gaisheta ya bata nata fruits din da fura tayi ta masa Godiya yayi murmushi kawai ya haura sama. Xaune ya samu El-Ameen yana danna laptop, ita kuma tana tsaye can jikin bango ta jingina, El-Ameen yace "Sae da ka ga dama kenan" Junaid bai tanka sa ba ya ajiye ledan hannunsa ya xauna gefen gado, El-Ameen ya ya juya yana kallonta yace "Ba dai baki ji ba, wait in tashi xa ki ga abinda xan maki a wajen nan" Junaid ya kallesa kafin ya girgixa kai a xuciyarsa yace ae Kaine mahaukacin ma, takowa tayi ta karaso kusa da ledan da junaid ya ajiye ta durkusa, El-Ameen ya daka mata tsawa yace "c'mon ance maki naki ne" mikewa tayi da sauri, Junaid ya dauki ledan ya mika mata ta karba, El-Ameen ya mike tana ganin haka ta sake ledan ta koma jikin bangon da take, dariya yayi yana kallonta yace "kai! Yarinyar nan ba dai tsoro ba" shi dai Junaid ko kallonsa bai yi ba, Karasowa yayi ya dau ledan ya bude ya fito da bunch din Ayaba ya mika mata, ta karaso da sauri ta karba, xata juya ya fixgota ya xaunar da ita gabansa, da kansa ya shiga bude mata ayabar yana mika mata, tana karba tana ci, ana uku ne taki ci, ta kalli Junaid dake danna wayarsa sae dae gaba daya hankalinsa na kansu, ta matsa kusa da shi a hankali ta kama hannunsa ta sa mashi Ayaban, tabe baki El-Ameen yyi ya kuma bare mata wani ta karba ta kuma kama hannun Junaid ta basa, El-ameen ya hade rai ya kuma bare wani ya bata xata ba Junaid yayi mata tsawa, a tsorace ta juyo, yace "I will knock you yanxu, ina shan wahala ina bare maki abu kina kyauta da shi, da xan bar ki yanxu da peel din xaki hade ki cinye," kafa masa manyan idonta tayi ko kiftawa bata yi, junaid yayi murmushi ya girgixa kai, wayar El-Ameen ne ya fara ring ya dauka, xaro ido yayi ganin Abbansa ne ke kiransa, ya kalli Junaid yace "Kasan kuwa ban je clinic throughout yau ba" ko kallonsa Junaid bai yi ba, ya daga a hankali ya kai wayar kunne, daga daya bangaren Abban nasa yace "ka taho clinic ka sameni yanxu Ahmad, clear?" yayi kasa da kai yace "Toh Abba" daga haka ya ajiye wayar yana kallon Junaid yace "Look! Xan je clinic yanxun in dawo, wait har sai na dawo don't go plss, kaga bata da lafiya karfin hali kawae gareta she just finished vomiting kafin ka shigo, dats why nake nan har yanxu, am giving her her drugs before leaving yanxu" Junaid ya xaro ido yace "Idan Mumy ta kira ni fa, beside 8:30 tace in dawo gida, nd this is almost 8 o clock" Kallonsa El-Ameen ya tsaya yi sae kuma ya girgixa kai yace "Tashi ka tafi toh, wato nine bansan darajan parent dina ba koh Captain, nine na iya karya kai baka iya ba, you know am doing this goddam job for ur sake if you provoke me wllh sae in fasa kawai ka kaita asibiti, kullum safiya sai na xo nan sbda drugs dinta da injections, at mid day ma I have to leave whatever i am doing in xo nan bata magani, haka da yamma ma, sannan da daddare bana barin gidan nan sai kusan sha daya, Haba!" kallonsa kawae junaid yake bai ce komai ba, tsaki yayi ya mike ya dauko maganinta da cup yayi diluting da ruwa ya xauna kusa da ita xai bata tana ganin haka ta fara kokarin mikewa ya fixgota, bbu gardama ta shanye maganin duk jikinta na rawa, ya mike
ya dau makulli da wayarsa yana kallon junaid on a serious note yace "Look! In har ka bar gidan nan kafin in dawo wllh wllh kaji rantsuwan musulmi koh, toh sai dai ka san yanda da xakayi da yarinyar nan don ba fina biyayya kayi ba, I am taking my hands of her case" daga haka ya fice daga dakin, Junaid da ya bi sa da kallo yana murmushi snn ya juya yana kallonta, yatsine fuska kawae take, ta matso kusa da shi ta mika masa Ayabar hannunta, a hankali ya sauko daga kan gadon ya karba ya kai mata baki yana kallonta yace "Eat!" Ta kauda kai da sauri, kallon Ayabar yake yana son ci amma ya kasa, ajiyewa yayi ya dau Apple ya mika mata, Kin karba tayi, yayi murmushi ya ajiye shi ma, a hankali ta kwanta nan gefensa, ya tsura mata ido, kamar warce aka tsikara ta mike xaune da sauri, ya koma baya yana kallonta.
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
18.....
Amai ta shiga kwararowa a gurin, ya mike yana kallonta har ta gama ta koma xata kwanta yayi saurin riketa, kara ta saki ta turasa da karfi xata kwanta gun aman yaki saketa, nan ta shiga kokuwa da shi ita sai ta kwanta, ya rike ta gam yace "Wait Jasmine..." ta kuma sakin wani ihun da ya tsorata shi, ae da ta turasa sai da ya kusa faduwa ba shiri ya saketa, ta yi kwanciyarta nan kasa, ya sauke ajiyar xuciya ya nufi toilet, mop da bucket ya dauko ya dawo dakin, rasa ta inda xae fara gyara wajen aman yayi, ya ajiye ya fita don kira Mama jummai, tare suka shigo dakin, ta karaso kusa da ita da sauri cike da tausayinta ta dagota tana mata sannu, ihu ta sakar mata ita ma ta kwace kanta ba shiri ta saketa ta koma ta kwanta tana mayar da numfashi, girgixa kai mama tayi ta mike ta shiga gyara wajen, tana gamawa ta kuma gwada d'aga ta a kasan tiles din still taki tashi, kyaleta tayi ta fita, Junaid ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito jin kiran isha, a nan dakin yayi sallah, yana xaune kan darduma ya ga tana juye juye a kasan da take kwance. Kallonta kawae yake cike da tausayinta don da ganinta kasan tana jin jiki, ta mike xaune a hankali ta dawo inda yake tana kallonsa ta kwanta kusa da shi, dagota yayi murya can kasa yace "Sorry Jasmine" lumshe ido tayi ta kwanta nan kusa da shi lkci daya bacci ya dauketa, ya mike ya koma can jikin gado ya xauna, har Karfe tara El-Ameen bai dawo ba, duk ya kagu ya dawo ya wuce kafin Mumy fa kirasa, tara da rabi kiran Mumy ya shigo wayarsa, k'asa d'agawa yayi don bai ma san me xai ce mata ba har sai da ya kusa katsewa sannan ya daga da sauri, Mumy tace "Where are you Ahmad" kallon dakin yayi kafin a hankali yace "Mumy, am am with El-Ameen" strictly tace "You are very stupid, within the next 10 to 15 mins ka tabbatar kana cikin gida if not xaka ga bacin raina, in kuma kaya ku ka kasa a titi ku ke saidawa da daddaren nan xaka gaya min" kamar mai shirin kuka yace "Kiyi hakuri Mumy xan dawo" katse wayar tayi, ya rike kansa, layin El-Ameen ya shiga nema yana ta ring bai d'aga ba, ya lumshe ido ya jingina jikin gado, he just don't know wat to do, haka yayi ta kiran El-Ameen bai daga ba, Shivering yaga tana yi daga kwancen da take kan darduma, ya mike ya karasa inda take ya dago ta ta bude ido da sauri, kan gadon dakin ya kwantar da ita ya rufa mata bargo, ta cire xata sakko ya riketa da damuwa yace "You are shivering Jasmine" ba shiri ya saketa a dalilin kara me karfi da tayi masa a kai, ta sauka nan kasan dakin ta kuma kwanciya. Har goma El-Ameen bai dawo ba, Junaid ya rasa me ke masa dadi shi da bae taba yi ma Mumy musu ba, yasan kuma fushi tayi shi yasa bata kara kira ba, da yayi niyar tafiya sae ya tuna abinda El-Ameen yace masa, ya kuma san xai aikata, shine xaune har sha daya, Mama jummai ta shigo tace "Kai xaka kwana yau a nan kenan junaid?" D'an murmushi yayi yace "A'a ina jiran El-Ameen ne yace xai dawo" tace "Toh tafi daki can ka kwanta inda yake kwana xan kula da ita" Junaid yace "yana kwana nan ne?" Tace "Eh wani lkcn yana kwana can dakin don akwai alluran da yake mata da sassafe, toh duk ran da xai mata alluran a nan yake kwana, ni kuma tare muke kwana da ita saboda shiga bayi da daddare" Junaid ya gyada kai yace "Bari in jira sa a nan Mama ni ba kwana xan yi ba ai" tace "Toh" sannan ta juya ta fita. Lumshe ido yayi ya jinginar da kansa jikin gado, wani bacci ya ji na fixgarsa ya bude ido yana kallon agogo yaga sha biyu, kallonta yayi ya ga ta canxa position, a hankali ya mike ya isa inda take xai dagata ta bude ido da sauri, birginawa tayi ta bar gun ta juya masa baya, ya mike ya koma ya xauna kan gadon, xuwa yanxu kam ya gama sanin iskanci El-Ameen yayi masa, dole ko yaki ko ya so a nan xai kwana hakan ba karamin bata masa rai yayi ba, sha biyu da rabi ya kuma mikewa jin yana jin bacci sosai ya bude closet ya dau bargon da ya gani ya koma daya side din gadon ya shimfida a kasa ya kwanta dai dai yanda xai dinga ganinta, nan da nan bacci ya daukesa.
Bude ido yayi jin an bude kofa don ko k'adan bashi da nauyin bacci, El-Ameen ne ya shigo dakin yana ganinsa ya dauke kai, kallo daya El-Ameen yayi masa yana murmushi bai ma san idonsa biyu ba ya karasa gun da take kwance a kasa, durkusawa yayi gabanta ya dagota, ta bude ido da sauri, lumshe ido yayi jin xafin jikinta a hankali yace "Sorry, Jewel" xata koma ta kwanta yaki saketa, ya mike ya dauketa ya nufi kan gado da ita ya kwantar, kokarin sauka ta shiga yi da kyar, ya hade rai yace "No" bata kuma yunkurin saukan ba, ya gyara mata kwanciya ya mike ya shiga bayi, duk wannan abun Junaid na kallonsu, ya dawo dakin rike da bowl din ruwan sanyi ya bude closet ya ciro towel karami da babba ya saka karamin cikin ruwan bowl din ya dawo kan gadon ya ajiye bowl din kan bedside drawer, ya dagota yana kallonta don idonta biyu, ya dawo da bowl din ruwan gefensa ya matse ruwan towel din a hankali yana goge mata forehead dinta da shi, kara ta saki xata sauka ya hade rai yace "Wait!" Bata kuma yunkurin saukan ba, haka ya ci gaba da goge jikinta da yayi xafi sosai da towel din yana mata sorry, mikewa Junaid yayi, El-Ameen ya juya da sauri ya kallesa sannan yayi saurin rufeta da bargo yace "Ohh you weren't sleeping dama" Junaid bai tanka sa ba ya dauke bargon da ya shimfida kasa ya mayar cikin closet, El-Ameen ya tabe baki yace "Ni ban ma yi tunanin xan dawo in same ka ba Mumy's boy, theatre muka shiga da Abba and we came out few minutes ago, saboda nasan condition din patient dinka shi yasa na fito cikin daren nan, I ought to...." jin anyi banging kofa El-Ameen ya kalli kofar da sauri don dama yana magana ne yana matse towel a ruwa, murmushi yayi ganin ficewa yayi, ya ci gaba da abinda yake, har sai da yayi make sure temperature dinta ya dawo dai dai, still yayi ganin hawaye idonta, ya sunkuya a hankali ya goge mata fuskar yace "Am sorry Jewel, am only helping" sauka yayi daga kan gadon yaje ya xubar da ruwan ya shanya towel din a bayi ya fito, bacci ya sameta tana yi a yanda ya barta, ya gyara mata kwanciya sannan ya hada allura yayi mata da kyar don a tsorace ta farka ta fara kokuwa da shi, sai da yaga ta koma bacci sannan ya fita dakin ya shiga master bedroom duk a tunaninsa xae tarda junaid nan, sae yaga otherwise, tabe baki yayi sanin yana parlor knn, ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya canxa kaya yayi kwanciyarsa dakin, sai dai before dawn yaje dubata ya fi sau goma duk da a shigowarsa na uku ya tarda mama jummai a dakin, Karfe biyar da minti arba'in ya sauko parlor ya tarda Junaid xaune kan darduma, xaunawa yayi kan kujera yana kallonsa yace "A parlor ka kwana kenan?" Junaid ba tare da ya kallesa ba yace "Yea!" El-Ameen yace "Ohk, gud morning, yanxu dai you need to transfer some money into my account xuwa later akwae drugs din da na mata prescribing, and you know wat? Suna da tsada gaskiya or I shud just text you their names, tell you where to get them, kaje da kanka ka siyo, if you need my assistance let me know" El-Ameen ya kare maganar yana d'aga kafada, Junaid ya mike ya dauke darduman da yayi sallah yace "nawa ne kudin?" El-Ameen yace "100 nd 50k will be enough" Junaid yace "Alryt" ajiye darduman yayi kan kujera ya kalli El-Ameen yace "Na tafi, I will transfer it later in the day" bai jira cewarsa ba ya nufi kofa ya fice daga parlorn, makullin motarsa ya ciro a aljihu ya fita waje inda ya ajiye motarsa ya bude ya shiga ya kama hanyar gida, driving kawae yake amma gaba daya hankalinsa ba ya tare da shi, bai san yanda xa su kwashe da Mumy ba, toh ina ma xai ce mata ya je, gidansu El-Ameen? No yasan xata iya kiran Ummi, murmushi yayi yana tunanin randa xae samu freedom, don ya fara damunsa yanxu on like before, a waje yayi parking ya fito, gabansa ne ya fadi ganin Abbansa alamar daga masallaci yake, da kyar ya ja kafa ya isa gun gate ganin Abba ya tsaya har ya risina xai gaida Abba, Abba ya dakatar da shi yace "Daga ina kake?" Yayi kasa da kai zai yi magana Abba ya juya ya shiga cikin compound, bin bayansa yayi har suka isa part din Abba, Hajiya ke ta goge goge a parlon, Abba ya xauna kujera yana kallon Junaid, a hankali ya xauna kasa ya juya yana kallon Hajiya dake kallonsa da d'an murmushi mai wuyar fassara a fuskarta yace "Ina kwana Hajiya" tace "Lfya lau Ahmad" sunkuyar da kai yayi, Abba yace "Daga ina kake Ahmad?" A hankali yace "Tare muke da El-Ameen Abba" Abba yace "Tare a ina?" Hajiya ta dawo cikin parlon tana girgixa kai tace "kwata kwata ni hankalina bai kwanta da abotansa da yaron nan wai El-Ameen ba, yaron da bai da nutsuwa ko maganan iyayensa bai ji, kusan duk dare sai ya shigo ya fita da shi, Ahmad baxae dawo gidan nan sai kusan sha biyu wani lokacin har daya, duk ina lura da yake ni ba mai nauyin bacci bace ka sani Alhaji, to amma kar mutum yayi magana ace hassada ko kuma ace don ba d'an sa bane, amma kwata kwata Ahmad ya sauya hali a gidan nan, jiya wllh wllh khadija ca tayi min mace ta gani a motarsa da magariban nan da ya fita, to ina yaje yake dawowa yanxu, kuma duk Hajiya Amina tana ganin abinda yake baxata ce komai ba saboda ta dauki son duniya ta daura ma yaro, meye amfanin haka, in ma aure yake so ba sai yayi magana ba, ae ba wae bai isa bane" tunda ta fara magana Junaid ya kafeta da ido ko kiftawa bai yi, Abba kuwa sai kallonsa yake bacin rai karara a fuskarsa.
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
19.....
Junaid ya sauke ajiyar xuciya ya lumshe ido a hankali bai dai ce komai ba, Abba ya kalli Hajiya yace "A kira min Aminar" da sauri Junaid ya bude ido ya marairaice masa yace "Don Allah don annabi Abba ka min duk abinda xaka min, amma bbu ruwan Mumy bata ma san bana nan ba, plss..." wani tsawa Abba ya daka masa, babu shiri yayi tsit, Hajiya ta juya ta nufi kofa lebbenta dauke da wani murmushi, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Suhaima ta tafi kiranta" Abba bai ce komai ba ta nemi waje ta xauna tana girgixa kafa tana tabe baki, ba a dau lkci ba Mumy ta shigo parlon da sallama, sai dai duk jikinta yayi sanyi ganin junaid xaune parlon tasan ba abun arxiki ya sa aka kira ta ba, kujera ta samu ta xauna tare da gaida Abba. Bbu yabo bbu fallasa ya amsa, junaid ya k'asa dago kai ya kalleta duk jikinsa yayi sanyi, Abba yace "Ke a tunanin ki so kike nuna ma yaron nan koh Amina, har ya kai matsayin da Ahmad baya kwana gida yanxu shi ba nyt duty ba kika xuba masa ido koh, toh dama an sha gaya min ban yarda ba amma yau idona ya gane min komai, don haka ni baxan bari ya dauko min abun kunya ba ina xaman xama na, just few weeks na basa ya fito da mata idan ba haka ba xai sha mamaki na wllh....." Mumy da har idonta sun cicciko ta kallesa cike da takaici tace "Alhaji kar ka manta Ahmad ba mace bane da har kake tsoron ya dauko maka abun kunya, kuma mace ake ma kulle ba namiji ba, ko yau ya ga bai son xaman gidan nan yana iya barin sa ya koma duk inda yake so don namiji yake ba mace ba kuma ya mallaki hankalin kansa, ni na haifi Ahmad na kuma fi kowa sanin halinsa ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba baxai aika ta mugun kaxamin kaxafin da ake son lika masa ba, I know my son" hawaye na bin kuncinta ta kare maganan, Hajiya ta bude baki ta saki salati tana tafe hannu, Abba ya mike fuskar nan tasa a murtuke yana kallonta yace "lallai Amina wato ni ke masa kaxafi kenan koh, to bari ki ji, wllh sati uku na basa yayi aure ya bar min gidana idan ko ba haka ba xai gane matsayina a gun sa" mikewa Mumy tayi tana kallonsa tace "Toh sai me, bai isa auren bane!" wani kallon Allah wadaran shaidanin mutum ta jefa ma Hajiya ta fice daga parlon, Hajiya ta dinga salati tana cewa "kiri kiri mutum yasan gaskiya ya danne don bai son laifin d'an sa, Allah sarki duniya" Abba ya kalli Junaid yace "Ka dai ji me nace maka, sati uku na baka wllh, get away" mikewa Junaid yayi da kyar ya fita daga parlon kansa na juya masa, part din Mumy ya shiga ganin bata parlor ya shiga bedroom dinta, xaune ya sameta gefen gado tayi tagumi, ya durkushe gabanta, ya daura kansa bisa kafarta cikin sanyin murya yace "Don Allah forgive me mum, it wasn't my intention disobeying you yesterday, I.. I am sorry mother forgive me plss" jin bata ce komai ba ya dago idanuwansa da suka kada yana kallonta, kamar xae sakar mata kuka yace "Plss Mumy kiyi hakuri!" "Ina ka tafi jiya?" Ta jefo masa tambayar tana kallonsa, rasa abinda xai ce mata yayi Cause he is not dat gud at lying, yanxun nan sae ta gano sa, ya kalli agogo, kallon agogon tayi ita ma taga bakwai saura ta d'an sauke boyayyen ajiyar xuciya tace "Tashi ka tafi" a hankali ya kamo hannunta yace "Plss Mumy kiyi hakuri nace" a nutse tace "Leave!" Ya kusa minti biyu durkushe gun sannan ya sake hannunta ya mike a hankali ya juya ya fita daga dakin ya shiga part dinsa. Cikin minti ashirin yyi wanka ya gama shirinsa, ya fito sae dai da ganinsa kasan bashi da nutsuwa, part din Mumy ya koma, ya sameta tsaye dinning tana jera masa breakfast, karasawa yayi yana rike da hularsa, Mumy ta bar dinning din, sosai jikinsa yayi sanyi ya ja kujera a hankali ya xauna ya dau mug din tea'n da ta hada masa ya shiga sha ba don yana jin sha ba, tea kawae ya iya sha ya mike ya dawo parlor yana kallonta yace "Xan tafi aiki Mumy" tace "baka ci dankalin ba, wa ka bar ma? go back and eat it yanxu" ba musu ya koma ya d'an ci kadan sannan ya kurbi ruwa ya dawo yace "Na ci Mumy" tace "Allah ya tsare" a sanyaye ya nufi kofa ya fita, Humainah da fatima sun fito daga part din Abba kenan, Humainah ta nufesa ganin parking lot ya tafi ya bude motarsa, kan ta iso har ya shiga, ta bude motar ta wara ido tace "Ya Ahmad Abba yace anjima ka kai ni islamiyyar su fatima ni ma a min...." Fixgo kofar motarsa yayi ya rufe, tayi still wajen tana kallon bakin glass din motar, yana gama ba motar wuta ya ja ya bar wajen, tsaki ta ja sai kuma ta fashe da kuka ta juya suka yi ido hudu da Hajiya da suhaima dake kallon duk abinda ya faru, Suhaima ta fashe da dariya, da gudu tayi part din Mumy tana kuka kamar wata jaririya. Haka Junaid ya wuni gun aiki duk bai da sukuni, colleagues dinsa har tambayarsa suka dinga yi ko lafiyarsa yace he's just having a slight headache ne, duk ya tuna abinda Abba yace sai gabansa ya fadi ba kadan ba, wai 3wks, kuma yasan ba lallai yayi kaffara a kansa ba, tunda ya dauki kudurin taimakon baiwar Allahn nan yake fuskantar challenges iri iri ga shi bashi da rest of mind as before, and he knows he is only doing it for Allah's sake ba da wata manufa ba, damuwar da yake ciki bai hanasa yi ma El-Ameen transfer din dubu dari da hamsin din da yace na drugs dinta ba, Hudu bai karasa ba ya bar gun aiki ya dawo gida, part dinsa ya nufa ba tare da ya kalli su Umma da Hajiya dake xaune balconyn Hajiya ba yayi shigewarsa parlor yyi banging kofar, Hajiya ta tabe baki tace "Ke maganar ki gaskiya ce wllh, tsinannan uwar nan tasa bata bari yaci girkin mu, ita ke masa da kanta kullum" Umma tayi kwafa tace "Ahaf Ba baki yarda ba da, ae wannan matar ae sai dai muyi adduar ganin karshenta" Hajiya tace "Toh wai meye kuma next move din da xa mu dauka tunda gashi ance ya fito da mata nan da sati uku, ke kar fa kuma yace wannan shegiyar Humainah take kowa, kinsan fa ba kula matan yake ba, kar uwarsa tace ya fito da Humainahr kawai mu shiga uku, wannan fa shine anyi ba ayi ba" Umma ta xuba tagumi tana gwalo ido yace "Yo ni ae wannan tunanin bai fado min ba wllh, kai da mun shiga uku, ni fa Humainahn nan ba karamin tsana nayi mata ba fa don duk da dududu bata fi sati gidan nan ba naga alama bata da kunya ko kadan, kuma ko shigowa gaishe mu bata yi, sai ma taga dama take gaishe mun in ta shigo gun Alhaji, kuma ina ga kamar tsinannar Aminan nan ke xuga ta" Hajiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Xamu san yanda xa muyi da shegiyar ita ma, kuma ma ni ban ga alamar suna soyayya ba kin san halinsa ai, kuma ni shawarata kawai mu hade kai mu san yanda xa ayi Alhaji ya hada sa da Suhaima ko Muhibba shikenan sai yanda muka yi da shi" Umma tace "Toh ai matsalar ynxu kawai kullin da aka bamu mu barbada kofarsa ne, ya xa muyi? kinsan ba xuwa can bangaren muke ba, muna xuwa yanxu xa a gano mu, kuma don tsiya wai sai da magriba, dama da rana ne bbu wanda xai lura shi kuma yana gun aiki, ita kuma sallamammiyar 'yar ki khadija ba bamu hadin kai xata yi ba" Hajiya ta d'an yi shiru sannan a hankali tace "Suhaima xata yi mana aikin, nasan halin abata tsaf xata yi ba tare da an xargi komai ba" Umma tace "Toh Alhmdllh" da haka suka ci gaba da hirarrakunsu cike da rashin tsoron Allah.
Junaid kam wankansa yayi ya dauro alwala ya fito ya shirya cikin kananun kaya yayi la'asar a dakin sannan ya fito yayi part din Mumy, suna xaune da Humainah tana mata tsifa, Ya xauna yana kallon Mumy yace "Ina yini Mumy" bbu yabo bbu fallasa tace "Lfya lau" shiru yayi, Mumy ta hade rai tace "Ka kyauta Ahmad ita 'yar uwar taka ka walakanta gaban idon makiyan ka koh?" Humainah ta bata rai, sai kuma ta fashe da kuka, Mumy tace "Ji walakanci, meye haka ke kuma" mikewa tayi fuu ta koma dining tana rera kuka, Mumy tayi tsaki ta galla masa harara ta shige daki. Murmushi yyi yana shafa kansa ya mike ya nufi dinning din, kujerar dake kusa da wanda ta xauna ya ja ya xauna ta mike xata bar wajen ya rikota ya mayar da ita ya xaunar yace "Wai dama daxu magana kike min" ta fizge hannunta tace "Ohon maka" dariya yayi yace "Ni fa nayi xaton da kofar mota kike, toh tunda da ni kike yi hakuri..." Ta fashe da wani sabon kukan tace "Allah bana so" murmushi kawai yake yana kallonta yace "Toh kar ki so din, har da wani kwalliyarta tayi xaton da El-Ameen xamu dawo" ta dago da sauri tana kallonsa ta tsuke fuska tana goge hawayen idonta tace "Wani kwalliya nayi" giranta ya taba a hankali yace "Ba gashi ba har da wani shafa baki kika yi anan irin yanda kuke yi" ya kuma kallon pink lips dinta yana murmushi yace "Har da wani shafa jan baki a nan duk don ki burgesa" buge masa hannu tayi fuskarta daure tace "Tun da kai ka shafa min ba" mikewa tayi xata bar wajen ya rikota da sauri yana dariya yace "Toh na dai ce kiyi hakuri koh" ta turasa tayi gaba abunta, murmushi yayi ya tabe baki, fatima dake bakin kofar kitchen tayi gyaran murya tace "Uhum ya A.jay Humainaj kadai yake ma dariya a gidan nan" wani kallo yayi mata, ta juya da sauri ta koma kitchen tana dariya, tsaki yyi ya bude food warmern dake dining din, kadan ya xuba shinkafar ya ci ya dawo parlor don duk bai da Appetite, kofa ya nufa ya koma part dinsa ya kwanta ya lumshe ido, yana son ya gansa can gidan El-Ameen ya ga halin da Baiwar Allahn ke ciki amma yasan baxai ma fara cewa xai fita ba, haka yayi ta juye juye kan kujeran duk ya rufe ido ita yake gani, shi kam tun da ya fara ganin yarinyar nan nutsuwarsa ya ragu, toh ko dai haushin taimakon nata da yayi take ji shiyasa ya kasa samun kwanciyar hankali, bude ido yayi jin an bude kofarsa, ya juya da sauri ya ga Humainah ce, ta hade rai ta dungure masa bowl din fruit salad din hannunta a kasa, murmushi yayi yace "da kin xubar ai," ko kallonsa bata yi ba ta fice. Washegari haka ya tafi aiki da safe as usual, ba laifi Mumy ta d'an kulasa da yaje breakfast, Abba kuwa dama da yaje gaishesa ca aka yi masa yana bacci, ko ta kan Umman bai bi ba yayi ficewarsa don ya saba in dai ba Mumy ce da girki ba to ba lallai ya ga Abba ba sae ko a masallaci, kasa samun natsuwa yayi gun aiki har sae da ya dau excuse din minti ashirin ya fita ya kama hanyar gidan El-Ameen, su biyu kadae ne parlon ita da mama dake mata kalaba daga tsaye don taki xama, sae xagaye parlon suke ana kitson a haka, tana ganinsa suka hada ido ta kurma wani uban ihu da yayi mugun tsorata mama don kan kace me har ta kai bakin kofa, shi kam tsayawa kallonta yayi, har lokacin ihun take da karfi tana shisshigewa jikin bango ko ina na jikinta na rawa, lumshe ido yayi a hankali ya bude ya kalli uniform din jikinsa White navy shirt ne jikinsa da dark trousers navy blue, ya kalleta ya ga yanda ta runtse ido tana k'uwa, bude kofar parlon aka yi El-Ameen ya shigo da ledoji a hannunsa, sake ledojin yayi da sauri ya karasa gunta, ya riketa, bude ido tayi a gigice ta kara fasa wani ihun tana ganin El-Ameen ta rungumesa, ya rufe bakinta lkci daya tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya a hankali, kallon Junaid yayi ya hade rai yace "Look captain, I've warned you not to come to this house on uniform again, look how you are scaring the life out of her, a haka xata samu lafiya? Plss ka daina xuwa nan da uniform" Juyawa Junaid yayi ya fice daga parlon, Mama dake bakin kofa har lkcn tace "Auuu wae khakin take tsoro? Allah sarki Baiwar Allah" dago kanta El-Ameen yayi yana kallonta ita ma haka, kama hannunta yayi yana rike da ita suka haura sama. Junaid na komawa gun aiki ya ci gaba da harkokinsa sai dai da ka gansa kasan there is something eating him inside, karfe biyar saura ya isa gida, ya jima xaune motarsa yana danne danne a waya, ganin motar da ke kokarin parking gefensa ya kashe motar ya fito ya rufe yayi part dinsa. Yana kwance parlor'nsa dab da magrib yana kallon wani program though absentminded yaji Humainah na kwalo masa kira daga waje, mikewa xaune yayi jin irin yanda take kiransa da karfi, ya mike da sauri ya nufi kofa ya bude, tsaye ya ganta d'an nesa da balconyn rike da kugu tana tafe hannu tace "Taho taho ka ga yaya" yana fitowa sai kuma tayi bangaren Mumy da sauri tana kwalo mata kira ita ma, wanda hakan ya ja attention din 'yan gidan da ido da kunnensu na kan duk wani motsi na gidan kamar masu gadi, Umma ta riga Mumy da fatima fitowa sannan Hajiya, su khadija Rabi'a, sadiya, Muhibba duk suka fiffito, shi kam Junaid abinda ya daure masa kai bai wuce na ganin Suhaima tsaye bakin kofarsa tana xaxxaro ido sai kokarin boye abu a hannunta take, Humainah ta dawo da sauri Mumy na biye da ita a baya haka ma sauran, Hajiya kam ko ina na jikinta rawa yake ji take kamar ta saki gudawa tsabar rudu shikenan asirinsu ya tonu, garin yaya Suhaima taje bakin kofar ba tare da ta sa ido taga bbu kowa a tsakar gidan ba, ita kanta umma sai da hanjin cikinta ya kada sai dai duk basu nuna a fuska ba, don Hajiya sai ma wani hade ran karfin hali tayi, A takaice Humainah ta rike kugu tace "Abu naga tana shirin barbada wa bakin kofar ya Ahmad, duk bata san ina can bakin pampo naje daurayo takalmana ina kallonta ba" ta fadi haka tana nuni da kusa da bangaren da Hajja ke sauka, Suhaima dake ta salati a rikice tace "Sharri xa ki min don kin gan ni a nan, na shiga uku na lalace, Hajiyanmu kina jin abinda yarinyar nan ke cewa" a fusace Humainah tace "koh ba sharri ba, ki bude tafin hannun ki munafuka, kin wani xo kina yi kamar mage baki san ina kallonki ba xaki wani ce ina maki sharri, wllh Mumy abu take shirin barbada masa bakin kofa" Hajiya ta hadiye yawu da kyar tace "Ke yanxu 'yar nan sharrin naki kan 'ya ta kuma xe sauka, duk shekarunta gidan nan bata taba barbada ma Ahmad abu ba sai da kika xo munafuka algunguma toh wllh sai Alhaji ya xo ya mana shari'a don baxan yarda da kaxafin nan ba" fuu Humainah ta haura balconyn ta fixgo hannun Suhaima dake jin kamar ta saki fitsari tana huci tace "Bude hannun to idan sharri na maki, ki bude, uwar me ya kawo ki bangaren sa da daddare ke da ko during daylight ba xuwa kike ba munafukaa, toh wllh sai kin fadi Meye wannan kike shirin barbada masa ko in gaggalla maki mari a nan don ubanki" Mumy ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Humainah!" Humainah na girgixa kai ido rufe tace "Ni dai Mumy Allah sai ta fadi meye a hannunta ko kuma muje ta barbada shi a kofar uwarta ni baxan yarda ba"
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
20.....
Suhaima da duk ta jike da xufa ta fara kokarin kwace hannunta daga rikon da Humainah tayi mata tana cewa "Na shiga uku ki cika ni, me na maki xaki min irin wannan sharrin?" Banda murmushi babu abinda khadija take, Hajiya dai da kyar kafafuwanta ke daukarta ga wani kullewa da cikinta yayi, Umma kuma sai wuwwurga ido take tana xufa, Sadiya ta haura balconyn a fusace tana kallon Humainah tace "Ke karamar 'yar iska cika mata hannu kar in baki mamaki yanxu....." Humainah ta juya a hankali tana mata wani matsiyacin kallo tace "Kambu! Ko kuma ni in baku mamaki ba, ai wllh sai ta fadi kullin uban meye a hannunta kuma wa ya aikota idan ba haka ba in karya hannun" Khadija tace "Toh ke Anty suhaima ki bude hannun a ga kullin mana, ko dai yaji xa ki kai masa?" Hajiya tayi kanta xata cafke ta ai da gudu ta bar wajen, cike da karfin hali Hajiya na huci tace "Ae sun yi kadan ta bude masu hannu wllh, sai dai duk...." Fitowar Abba yasa ta kasa karasawa ta fara girgije girgije ae kawae sae ta fashe da kuka tun kan ya karaso tace "Na shiga uku ni fateema me muka tare ma mutane a gidan nan ni da 'ya yana" A hankali Mumy tace "Cikata Humainah" Humainah ta girgixa kai ta cakumi rigarta tace "Noo! Ae sai ta bude hannunta mun ga ko menene wllh Mumy" shi kam Junaid tsaye kawai yayi ya kasa cewa komai duk jikinsa ba karfi, Abba na isowa ya shiga tambayar Meye haka, Humainah tace "Abba wallahi barbade take shirin yi ma Ya Ahmad Allah ya toni asirinta na kamata kuma ni sai taje bakin kofarsu ta barbada koma Meye xan kyaleta" Hajiya ta fashe da matsanancin kuka ko ina na jikinta na bari tace "Kana ji ko Alhaji, kana ji koh...." Abba kam kallonsu ya tsaya yi, can yace "Cikata Humainah" Humainah ta fashe da kuka tace "Ni wallahi baxan saketa ba Abba, sai ta nuna abinda ke hannunta kuma muje ta barbada shi a kofarsu, duk bata san ina can ina kallonta ba, ni wallahi baxan kyaleta ba" dariya khadija ta dinga yi can ciki ciki ganin yanda 'yar uwarta ke wurga ido kamar barauniya, da kyar Mumy ta haura balconyn ta kamo Humainah tace "Saketa Humainah" still taki sakinta ita fa sae ta bude hannunta, Junaid ya lumshe ido ya bude ya karasa kusa da su a sanyaye ya janyeta yace "Kyaleta Lil sis" fashewa tayi da wani kukan tace "Ya Ahmad abu fa tayi niyar barbadawa da ban ganta ba" ae Suhaima tun da ta samu Humainah ta saketa kan kace me har ta sauko kasa tana tuntube, ta fashe da kuka tana kallon Hajiya da Abba tace "Kudi fa na xo tambayarsa don ta ga ina leke leke shine take cewa barbade xan masa," Hajiya ta rungumeta ita ma ta fashe da kukan tace "Na sani Suhaima Allah xai saka mana kiyi shiru" Humainah ta kwace kanta daga rikon da Junaid yayi mata ta sauko tana kallonta da kyau tace "Kuma wallahi daga yau na kuma ganin kafar ki a nan wajajen sai na karya su duka biyun, munafuka kawai dama ni Hajja tace min boka da malamai kuke bi" tsawa sosai Abba ya daka mata, ta turo baki ta bangajeta tayi part din Mumy fuu tana gunguni, duk suka bita da kallo fatima ta ni bayanta, Abba ya kusa minti daya bai ce komai ba, can ya kalli su Hajiya yace duk kowa ya koma ciki, haka duk suka juya Hajiya na kuka har lkcn tana rike da hannun Suhaima Umma da baki ya mutu na biye da ita a baya, shi ma ya juya yayi part dinsa ana kiraye kirayen sllhn magrib. Mumy ta juyo a sanyaye tana kallon Junaid, shi din ma duk jikinsa yayi sanyi ba kadan ba, kasa cewa komai tayi ta sauka ta koma part din ta, ya lumshe ido ya bude ya bi bayanta. Xaune suka tarda Humainah palo sai rusa kuka take bakin rai, Mumy tace "lafiya kuma Humainah" cikin kuka tace "Mumy ba shine baku bari na mata duka ba, wllh wani kulli ne hannunta tana shirin xubawa bakin kofar na kamata" Mumy ta xauna kusa da ita tana murmushi ta jawo ta jikinta tace "Kiyi hakuri mu bar su da halinsu Allah ya fisu da shi kuma muka dogara, in'sha Allah bbu abinda xai same mu kin ji Humainah" kallon Junaid dake tsaye ya kasa xama tayi tace "Kai kuma ya Ahmad maimakon ka faffala mata mari shine ka tsaya kallonta" Xaunawa yayi yyi murmushi bai ce komai ba, lallashinta Mumy ta dinga yi har dai ta samu tayi shiru, Junaid ya mike ya shiga bathroom din dake parlon ya dauro alwala ya fito ya fita xuwa masallaci, Mumy ta kalleta tace "tashi ki je kiyi alwala" ba musu ta mike ta shiga bathroom Mumy ma ta tashi ta shiga dakinta don yin alwalan. Ana idar da Sllh Junaid ya shigo, Humainah na xaune da Mumy da fatima suna cin abinci, ya xauna yana kallonsu, kwankwasa kofa aka yi lkci daya aka bude aka shigo, Sadiya ce ta shigo ta tsaya daga bakin kofar fuskarta tamke tace "Humainah kike ko wa? Abba na kiran ki" Humainah ta galla mata harara tace "A'a Mantawa kika yi dai, Sadiya sunana" Mumy tace "Ke kina da hankali Humainah?" ta turo baki ta ajiye spoon din hannunta, Sadiya tayi kwafa tana gyada kai ta fice, mikewa Humainah tayi, Mumy tace "Ki gama cin abincin tukunna, baxa mu kuma shirya da ke ba idan kina rashin kunya" kamar xata yi kuka ta nufi kofa Junaid ya bi ta da kallo yana girgixa kai. Da sallama Shukrah ta shiga parlorn Abba, yana xaune kujera Hajiya da Umma ma na xaune sai Suhaima da ke xaune kasa, can jikin kujera ta samu ta xauna tace "Abba gani" a nutse Abba yace "Daga yau kika sake abinda kika yi daxu sai na yi mugun saba maki, Ashe ke shashasha ce, kina daga can bakin pampo ta ya kika ga abu a hannunta" Hajiya ta goge d'an guntun hawayen idonta tace "Babu maganan taya ta gani, wllh sa ta aka yi Alhaji don wnn yar mitsitsiyar hankalinta baxae bata tayi abinda tayi mana daxu ba, to ni kam me na tsare masu xa su yi ma 'ya ta irin wannan mugun sharrin?" Kuka ta fashe da sosai, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Xancen ki gaskiya Hajiya, amma Allah ya san dai dai, kuma baya bacci" Abba ya kalli Humainah da ta wani hade rai kiris ya rage ta fashe, yace "Don uwar ki wa kike ma wannan kallon" mikewa tayi ta fashe da kuka tace "Na rantse da Allah Abba wani abu ne a hannunta tana son budewa ta barbada fa na kama ta, ni ba karya na mata ba, meyasa baka ce ta bude hannun ba tun a can..." Wani tsawa Abba ya daka mata yace "Ke!! Baki san ni ba koh?" Hajiya ta girgixa kai tace "Babu ruwan yarinyar Alhaji da ba a ce tayi hakan ba baxa ta yi ba" Abba yace "Toh maxa ki tafi ki tattaro kayanki ki koma gun Hajiya tunda munafurci kike koya can, maxa maxa yanxun nan ba sai da safe ba" Hajiya ta dan yi murmushi da iyakan sa lebbe, ficewa Humainah tayi da gudu daga parlon, tayi part din Mumy, Mumy na xuba ma Junaid abinci ta fado parlon ta xube nan kasa ta dinga rusa kuka kace yar jaririya ce, Mumy ta karasa da sauri ta dago ta tana tambayarta abinda ya faru, kuka take sosai tace "Wayyo Mumy ni gidanmu xan tafi wallahi baxan xauna a nan ba, ki bani wayar ki in kira Hajjah" Mumy tace "Kiyi hakuri, gaya min me ya faru, me Abban yace maki" cikin kuka tayi ma Mumy tsarin yanda suka yi da Abba, Mumy tayi murmushin takaici bata ce komai ba, Junaid kam lumshe ido yyi ya jinginar da kansa jikin kujera, tana ci gaba da rusa kuka tace "Ni wallahi wucewa xanyi baxan xauna ba" Mumy rasa me xata ce mata tayi, mikewa Junaid yayi ya dago ta yace "Kiyi hakuri, Abba is angry shi yasa ya maki magana haka, xaki ga ya huce xuwa gobe" tace "A'a ni ka ban wayarka in kira Hajja tafiya ta xan yi" cikin sanyin murya Mumy tace "Kar ki kirata, xai iya cewa ni na sa ki kirata" mikewa Humainah tayi ta nufi daki tana kuka. Junaid ya koma ya xauna, Mumy ta girgixa Kai ta ci gaba da xuba masa abincin da take yi. Kasa cin abincin Junaid yayi, Mumy ta lura da hakan tace "Dama ka ci abincinka ka share komai, I keep telling you Junaid never depend on ur father, duk da nasan you are not depending on him dama, kar ma ka sa rai da komai nasa, sannan kayi ta bin sa ku rabu lafiya, you can see how things are going this days nasan ba yin kansa bane, banda hada ka da shi bbu abinda ake yi, lastly be prayerful" a hankali yace "In'sha Allah Mum" tace "Ya maganan da yayi maka jiya, kasan dai yana can yana kirga kwanakin da ya baka, ko kuma ince ana can ana Kirga masa koh" shiru Junaid yayi, Mumy tace "It's better ka kwantar da hankalin ka ka fito da mata tun kan ya nuna maka matsayinsa gun ka kamar yanda yayi ikirari" ae gaba daya abincin fita ran Junaid yayi, da kyar ya dinga tutturawa, Mumy na kula da hakan duk tausayin sa ya rufeta, tasan ba yin kan Abba bane yake masa haka, amma bbu yanda ta iya sai dai ta dage da Addu'a kamar yanda ta saba. Mikewa yayi jin ana kiran isha ya shiga bathroom ya dauro alwala ya fito ya tafi masallaci, ana idar da sllh yana tsaye da Abdul suna gaisawa ya ga tsayuwar motar El-ameen, El-ameen yayi parking ya fito suka gaisa da Abdul sannan ya kalli Junaid ya shiga gida, part din Mumy ya nufa suka gaisa ta tambayesa mutan gida yace Duk suna lafiya, ya kalli hanyar bedrooms yace "Wa ke kuka kuma Mumy?" Mumy tayi murmushi tace "Humainah ce, daga Abba yayi mata fada wai fa" dariya yayi bai ce komai ba, Mumy tace "toh je ka lallasheta kila tayi shiru, ni taki saurara na" shiru yayi sai kuma ya mike kamar munafuki ya nufi bedroom din Mumy, tura kofar yayi ya shiga ya sameta xaune can karshen gado tana rera kukanta, ya kusa minti biyu tsaye kafin yasa kai ya shiga dakin, ya karasa inda take a hankali, ya duka yana kallonta, tuni ta hadiye kukan da take ta kauda kai, ya d'an bude ido yace "Am, dama Mumy ce tace in xo in baki hakuri wai kina kuka" juya masa baya tayi da sauri, ya d'an sosa kai murya can kasa yace "Kiyi hakuri" taki cewa komai, a hankali yace "Kin ji" Junaid ne ya shigo dakin yana ganinsu ya saka dariya yace "Uhnn! har dakin ka biyota Dr, ba sai ka jira in dawo in kira maka ita ba" El-ameen ya mike yace "Mumy ce tace in xo in bata hakuri Mr man" daga haka ya fice daga dakin, Junaid yace "ba wani nan da'alla kai dai fadi gaskiya" Humainah ta mike xata shiga bathroom ya fixgota yana dariya yace "Oya sorry lil sis" fixge hannunta tayi tace "Ae next time ko boka aka kawo xa a ajiye bakin kofar ka baxan ce komai ba" dariya yayi sosai yace "Nafa ce kiyi hakuri, beside Allah ya fisu I believe" goge mata fuskarta yayi yace "Yanxu sai ki je ki wanke fuskarki kiyi kwalliya kin ga saurayin ki ya xo" Turasa tayi ta shige bathroom, yayi murmushi ya fita, a parlor ya tadda El-ameen yace "Mu je" mikewa El-ameen yayi, Mumy tace "Baxa ka ci abinci ba Ahmad" El-ameen ya girgixa kai yace "Naci abinci Mumy" Mumy tace "Toh shikenan," har sun fita Mumy ta kira Junaid ya dawo, ya isa gabanta yace "Gani Mum" tana kallonsa a hankali tace "Kayi addu'a kafin ka shiga" ya sunkuyar da kansa yace "Toh Mumy" daga haka ya fita daga parlon, suka nufi part dinsa da El-ameen, yayi yanda Mumy tace masa ya bude kofar ya shiga, El-ameen ma ya shiga, El-ameen ya xauna yana kallon Junaid yace "Did you tell anyone about our patient?" Junaid yayi shiru sannan ya girgixa kai yace "Not at all" El-ameen yace "Ohk, daxu mama Jummai take ce min xata je kauyensu gun dotan ta ta haihu, amma kwana biyu kawae xata yi, toh I don't know yanda za ayi abun, who will stay with ur patient during her absent?" Junaid yayi shiru yana kallonsa, can yace "Or shud we get a new...." El-ameen yace "Noo! Kwana biyu tace xata yi beside yarinyar tafi sabawa da ita kafin ta saba da wata kuma is something else, yau satin su kusan uku tare if am not mistaken" Junaid bai kuma cewa komai ba, El-ameen yace "Hurry plss ina son komawa can gidan kafin in tafi clinic" Junaid yace "I don't know what to say" El-ameen yace "How about khadija, naga u guyz are close" lkci daya maganganun Hajiya na daxu da safe ya fado masa wai khadija ce tace mata ta gansa da mace a mota, girgixa kai yayi yana murmushi coz yasan khadija won't do that, a hankali yace "Humainah?" El-ameen yace "Baka tunanin xata yi exposing din mu, beside wannan me kukan me ma xata iya yi?" Junaid yyi murmushi yace "She won't, matsalar kawai Mumy ce" El-ameen yace "Alright, y not make it look as if gidanmu xaka kai ta gun Ummi, daga nan dai xa mu san yanda za muyi" Junaid yayi shiru sannan yace "Ohk Allah yasa ta yrda" mikewa El-ameen yayi yace "Gud, yanda ku ka yi gobe ka kira ni" Junaid yace "Wait, but kasan da wuri nake barin gida ai" El-ameen yace "However, just make sure gobe around 12 tana gida na or she shud meet me at the clinic" Junaid yace "Wait plss don Allah kamar yaushe kake ganin xata samu lafiya, will it take long?" El-ameen ya wara ido yace "Uhn! Har ka fara gajiya da kashe kudi kenan?" Junaid ya girgixa kai yace "Not at all, ina son ta samu lafiya ta nemo 'yan uwanta case dinta ya fita daga hannuna, har kuma hakan ya kasance bana fatan 'yan gidanmu su san komai" El-ameen ya daga kafada yace "But I hope you weren't daft the other day I was saying it's difficult to predict how, when, or to what degree she's going to get better, dat aside ma kayi addu'ar kar tayi loosing memory idan ma ta samu lafiyan!" Zaro ido Junaid yayi yace "Loosing memory kuma, No No in'sha Allah hankalinta gaba daya xai dawo, if not ya za muyi da 'yar mutane?" El-Ameen yayi murmushi yace "Allah dai ya kiyaye hakan" daga haka ya fice daga parlon yana cewa "Am off!", Junaid ya bisa da kallo sannan ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "Ya Allah ka ba ma wannan baiwa taka lafiya" mikewa yyi shi ma ya fita, part din Mumy ya shiga ya tarda El-ameen yana ma Mumy sallamah, Mumy tace "Yauwa Ahmad ku fita tare ka siyo min fruits" Junaid yace "Toh Mumy" tare suka fita da El-ameen a motar El-ameen din, Suna isa inda ake saida fruits yyi parking, Junaid ya fita ya siya fruits leda biyu ya dawo motar, ya ajiye ma El-ameen daya yace "For our patient" El-ameen yace "za ka raka ni shopping complex xan siya ma Ummi perfume wai" Junaid yace "Ohk" Suna isa bayan El-ameen yyi parking suka shiga babban mall din, El-ameen ya nufi gun perfumes, ya debi wa enda yasan Umminsa na amfani da, junaid dai binsa kawae yake, Suna isa gun teddy bears manya El-ameen ya dauka wani me kyau yana kallo, Junaid yace "toh fah!" El-ameen yyi murmushi ya ajiye a basket yace "For ur patient" daga haka suka bar wajen, biscuits da chocolates me yawa El-ameen ya dauka a trolley din, shi dai Junaid binsa kawae yake har ya gama daukan abinda xai dauka suka tafi inda ake biyan kudi, Wata yarinya ce tsaye gabansu sanye da hijab har kasa tana rike da basket dinta, gabanta kuma mutane biyu ne, El-ameen ya dawo kusa da Junaid murya can kasa yace "Don Allah ka d'an mata magana kace sauri muke ta bari mu fara biya, dubi fa kayanta da yawa" Junaid yyi masa wani kallo yace "Tunda kai baka da baki sai ni" El-ameen yyi tsaki yace "matsalata da kai kenan kamar ba namiji ba" Junaid bai kuma ce masa komai ba, har aka zo kan yarinyar bude Jakarta tayi xata fito da Atm bayan ta xube kayan da ta siya kan table ana lissafawa, dube dube kawai take a jakar, El-ameen yyi dariya can kasa yace "are you seeing what am seeing frnd?" Sharesa Junaid yayi, yarinyar ta juyo tana duba kasa, Junaid ya tsura mata ido yana tunanin inda ya taba ganinta amma ya k'asa tunawa, juyawa ta kuma yi tana kallon mutumin dake xaune yana jiran kudi tace "Malam Atm card dina ne ban gani ba wllh, kayi hakuri ka ajiye kayan tukun" sai a sannan Junaid ya tuna inda ya taba ganinta ta dalilin muryarta da ya ji, ya laluba jikinsa yaji bai fito da Atm card dinsa ba, kallon na hannun El-ameen dake dariya can kasa yana cewa "Karyar banxa wai bata gani ba" ya warce atm card dinsa ya nufi gun biyan kudin, El-ameen ya xaro ido yace "Kaiii" ko kallonsa Junaid bai yi ba ya mika masu yace "Gashi ku cire kudin ku" kallonsa yarinyar take ita ma tana son tuno inda ta taba ganinsa, su ko tuni suka karbi atm ya danna masu pin suka cire kudinsu har dubu talatin da biyar. A hankali yarinyar tace "Thank you" da alama ta tunasa ita ma, yayi murmushi yace "Never mind, it pays to be kind" Murmushi kawai tayi, ya juya yana ma El-ameen wani irin kallo.
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
21.....
Karasowa Junaid yayi gun El-ameen da ya wani hade rai yana kallonsa, junaid yayi murmushi ganin bai da niyar motsi daga inda yake gashi jiransa ake ya karbi basket din hannunsa ya tafi ya biya kudin kayan ciki, godiya yarinyar ta kuma yi ma Junaid bayan ta dauki kayanta da aka yi packaging a leda ta bar wajen, El-ameen ya bi ta da harara har ta fita, Junaid ya dinga danne dariyarsa har aka masa package din kayan da El-ameen ya siya ya bar wajen yana kallon El-ameen yace "Let move frnd" wani mugun kallo yayi masa yayi gaba ya bar sa a wajen. Junaid ya dinga dariya ya bi bayansa, a waje suka ga yarinyar tsaye bakin motar ta, tana ganin sun fito ta nufe su, Har Junaid xai shiga mota ya tsaya, ta karasowa cikin sakin fuska tace "Am really grateful, Allah ya saka da khairan" xai yi magana yaji El-ameen ya warce ledan hannunsa ya xaga ya shige motarsa ya tada ya bar wajen, Junaid ya wara ido ya bi motar da kallo, haka ma yarinyar ta bi motar da kallon mamaki, can ta maido da dubanta ga Junaid ta kirkiri murmushi kawai ta juya tace "Sai da safe" ta bar wajen, Junaid ya sauke ajiyar xuciya sai kuma ya d'aga kafada ya bi bayanta, kusan a tare suka shiga motarta, ya kalleta yace "Amm drop me plss idan ba damuwa, abokina ya tafi da motar" ta gyada masa kai tace "Alryt!" Sai da suka hau kan titi sannan tace "Ina ka nufa?" Ba tare da ya kalleta ba ya gaya mata, ta bude ido tace "Ohh it's very far, mu nan kusa muke, kaga kafin in kai ka in dawo dare xai yi kuma Mum xata min fada ne, but nevertheless bari kawai inyi driving xuwa gida idan ya so sai ka tafi da motar ko gobe sai ka maido min" shiru yayi bai ce komai ba, can yace "Baxa ace komai a gidanku ba" a hankali tace "I will explain everything to mum" yace "Toh nagode" cikin mintunan da basu wuce goma ba ta iso anguwarsu tayi parking kusa da gate din wani kantamemen gida ta juya tana kallonsa tace "Nan ne gidanmu" yace "Ohhk" bude motar tayi ta fito ta bude back seat ta kwashi kayanta ta rufe tana kallonsa tace "Tohm sai da safe" bude motar yayi ya fito ya dawo driver seat yace "Ohk, alryt! Tnx a lot, but sai da yamma xan maido maki motar don da safe nake fita aiki" tace "Alryt bbu damuwa" har ta fara tafiya yace "Ur Name?" Ta juyo tana kallonsa tace "Hafsat!" Ya gyada kai yace "Nyc name, am Ahmad Junaid!" Ta d'an yi murmushi ta gyada masa kai sannan ta juya ta nufi gate dinsu. Tada motar yayi yayi reverse ya bar anguwar. Sai da ya fara tsayawa gun masu saida fruits ya kuma siya ma Mumy wani fruits din sannan ya kama hanyar gida. A parking lot yyi park din motar sannan ya fito ya nufi part din Mumy, Bbu kowa parlon ya ajiye ledan fruits din ya shiga bedroom din Mumy, ya sameta kwance ya karasa ya xauna gefenta yace "Mumy na dade ko, kiyi hakuri pls ga fruits din can parlor" tace "Ohk na gode" mikewa yayi yace "In kawo maki?" Ta mike ita ma tace "A'a bar shi kawai ban jin xan iya sha kuma bari in sa a fridge" fita tayi daga dakin ya bi bayanta, ya bude bedroom din fatima ya sameta kwance tana waya Humainah kuma tayi bacci, ya karasa dakin yana kallon Humainah, murmushi yayi a xuciyarsa yace "Fitinanniya" ya juya kawai ya fita, a parlor Mumy tace "Gobe idan ka dawo gun aiki wai xaka kai Humainah gidan Aysha, wai baxa ta xauna ba" shiru yayi bai ce komai ba, can yace "Toh Mumy kar Abba kuma yayi magana" tace "Ae kwana biyu kawai xata yi ka koma ka daukota" bai kuma cewa komai ba, har Mumy ta xuba fruits din cikin fridge sannan yace "Sai da safe Mumy" tace "Allah ya tashe mu lafiya, kayi addu'a kafin ka shiga" yace "In'sha Allah Mum" daga haka ya fice daga parlon. Yana gama shirin kwanciya ya jawo wayarsa ya wani hade rai yayi ma El-ameen transfer din dubu talatin da biyar ya jefar da wayar yayi kwanciyarsa.
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
22.....
Washegari da safe Junaid ya rasa yanda xai fara ce ma Mumy xai kai Humainah gidansu El-ameen kamar yanda suka shirya, har ya gama breakfast bai samu courage din gaya mata ba don yasan dole xata zargi abu, Mumy tace "Kana kallon lokaci ma kuwa" da sauri ya mike daga dinning ya dau hularsa da waya yace "Am off Mum" tace "Allah ya tsare, ka shiga gaida Abban ka?" yace "Eh but yana bacci" daga haka ya fice, Hajiya ya gani tsaye da Umma a bangaren Umman suna kallon bakon motar dake ajiye parking lot suna kus kus, duk a tunaninsu sabuwa ce, ko kallonsu bai yi ba ya nufi motarsa ya bude ya shiga, yana warming motar ya hango Khadija a balconynsu tana shara, y'afito ta yayi, ta ajiye broom din hannunta ta taho, su Umma suka bi ta da harara, gaishesa tayi, yace "akwai maganar da zamu yi dake a waya, you make sure you are alone while picking my call kin ji" tace "Alryt big bro" daga haka ya rufe motarsa, ta koma balcony. Karfe sha daya El-ameen na xaune office dinsa rike da wayarsa yana jujjuayawa da ganinsa kasan ransa a bace yake, kwafa yayi ya ajiye wayar yana tunanin walakancin da xai ma Junaid, shi kansa ya rasa gane dalilin da ya sanya ya kasa cire hannunsa a patient din Junaid, kila don ya fara tausayin yarinyar ne, sake daukar wayar yayi ya kira Junaid for the 5th time, yanxun ma har ya gama ring bai daga ba, El-ameen ya fuzar da iska ya ajiye wayar, toh yanxu ina xae samo Wanda xai kai can gidan ta xauna da ita gashi Karfe sha biyu mama jummai xata tafi, tsaki ya ja ya jawo files din gabansa, why is he even bothering his self this much, tayi ta xama ita kadai a gidan after all ba shi ya ajiyeta ba, kwankwasa office dinsa aka yi ya daga kai yace "Come in" wata nurse ta shigo tace "Sir kana da bakuwa a waje" ya sauke kafarsa daga kan table yace "is she a patient?" Ta girgixa kai tace "I don't think so" yace "Ait, let her in" juyawa tayi ta fita ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo tare da bakuwar, da sallama ta karaso tana murmushi tace "ina yini ya El-ameen" ya sauke ajiyar xuciyar relieve yace "Lafiya khadija," ta xauna saman table dinsa tace "Ya Ahmad yace in xo office in same ka" yace "Ya maki bayani ne?" Tace "Eh daga wajensa ma nake yanxu" kallon agogo yayi ya mike ya dau makullin motarsa yace "Amma Hajiya baxa ta neme ki ba?" Tace "Gidan kawata nace mata xa ni" a tare suka sauko reception, ya kalli nurses din yace "If MD shud ask of me tell him I was called for an emergency" suka amsa masa da yes sir, sannan ya fita khadija na biye da shi duk suka bi sa da kallo, front seat khadija ta bude ta shiga, shi ma ya shiga ya tada motar suka bar haraban hospital din. Sai da suka yi nisa tace "Yaya kai kuma ina ka samo mahaukaciya?" Kallonta yayi, yayi murmushi yace "Tsarin da ya maki kenan?" Ta d'an bude ido tace "Ehh ca yayi min taimakon ta kake, a hanya ka tsince ta" dariya El-ameen yayi yace "Gaskiya ne, amma ae shi ya ban kwarin gwiwan taimaka mata" khadija tace "Toh Allah ya baku lada duka" yace "Ameen," tace "Toh amma Yaya bata ma mutum komai, ni tsoro nake ji" yace "Bata komai yanxu, ta d'an saba da mutane, iyaka yanxu kawai xuwa xa kiyi ki xauna da ita, duk barnar da kika ga xata yi ki hanata, kar kuma ki bari ta fita, sai d'an potatoe da xa ki soya mata ki cika mata ketchup a ciki," a hankali khadija tace "Toh, amma ni dai ina jin tsoro" dariya yayi yace "Ke bata komai, you will like her" suna isa gidan yayi parking a waje ya fita ta bi bayansa, da ganinta kasan a tsorace take, dariya kawai yake har suka shigo parlon, bbu kowa parlon sai ita kadai ga 'yar jakar mama jummai da ta hada kaya duk ta watsar da kayan a parlon, da alamar mama jumman na kitchen, khadija ta labe jikin kofa sai faduwa gabanta yake tana leko parlon, karasowa kusa da ita El-ameen yayi ya fixge jakar yace "Ke idan baki yi barna ba baki ji dadi ba ko" daukar kayan tayi ta mika masa, ya fixge ya ajiye ya xauna ya jawo ta gabansa yace "look. I've brought a new frnd for you, hope xa ku saba da wuri, she's khadija by name" kallonsa kawai take ko kiftawa bata yi, yayi murmushi ganin yanda yayi mata maganar kamar wata me hankali, a hankali ya d'agota ya xaunar da ita gefensa ya juyar da kanta yana nuna mata khadija da taki karasowa murya can kasa yace "A frnd jewel, ur mate" kauda kanta tayi ta xamo kasa xata ci gaba da birkita kayan da take, yayi mata tsawa, da sauri ta dawo jikin kujera tana shisshigewa jiki a tsorace, sosai hakan ya ba khadija da ta kasa daina kallonta dariya, wani tausayinta ya rufeta ganin irin kyanta amma wai ba hankali, mama jummai ta fito tace "A'ah Sannu da xuwa Ahmad, har na fidda ran tafiya yanxu da naga baka xo ba" yace "Warce xata xauna da ita na je daukowa mama, kin ganta can, kanwar Junaid ce" Mama ta kalli khadija tace "Allah sarki, sannu yarinya karaso mana" yayi dariya yace "Wai tsoronta take fa" mama tace "Yo ae ita bata komai wllh" da kyar khadija ta yrda ta shigo tana kallon yarinyar da ita ma ta bi ta da ido, Mama jummai tace "Amma nan xata dinga kwana da ita koh?" El-ameen yace "A'a gaskiya xuwa bayan magrib xata koma gida" "Toh wa xai dinga kwana nan da ita" cewar mama jummai cike da mamaki, ya d'an yi shiru sannan yace "Xan dinga kwana nan ko kuma junaid" mama jummai ta girgixa kai tace "A'a wannan ba mai yiwuwa bane, ko kuma kawae in tafi da ita in dai xa ku yrda wannan ba wani abu bane a gu na" Shiru El-ameen yayi yana kallonta sai kuma yace "Saboda me baxai yiwu ba mama?" Ta xauna tace "A ina addini ya yarje mana da haka d'an nan" xaro ido yayi sai kuma yayi dariya ganin inda xancen nata ya dosa yace "kar ki manta mama ba fa lafiya gareta ba kuma shi ake kokarin ganin an nema mata, karkashin treatment take yanxu, don haka...." ta girgixa kai tace "A'a gaskiya ba wai ina maku shisshigi bane amma bai dace ba, sai dai kawae in hada kayanta mu je kuma na maku alkawarin kwana biyu xamu yi in juyo, kayi mata duk allurorin da xaka mata yanxu" El-ameen ya jinginar da kansa jikin kujera yana murmushi yace "Komai na hannun junaid mama sai yanda yace" tace "Toh kirasa" yana ciro wayarsa kiran Junaid ya shigo ya d'aga, Junaid yace "have you seen khadija?" El-ameen ya hade rai yace "Y weren't you picking my call daxu?" Bbu yabo bbu fallasa Junaid yace "Was very busy, ya ake ciki yanxu?" El-ameen yace "Zaka san you were busy ne, mama dai tace xata tafi da ita don bbu wanda xai dinga kwana da ita a nan," da sauri Junaid yace "What? No, no how can dat be, idan ta kara gaba fa, No she shud leave her xa mu san yanda xa muyi" El-ameen yace "Zaka san yanda xaka yi dai" daga haka ya katse wayar ya kalli mama jummai yace "Kin ji mama wai xai kai ta gun yayarsa ne har ki dawo" mama tace "Atoh hakan ma yayi bari inje to in hada mata kayanta" El-ameen ya bi ta da kallo har ta haura sama, ya juya yana kallon khadija dake ta kallonta ko kiftawar kirki bata yi, yace "Wannan kallon fa" ta kallesa ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "She's so beautiful brother" murmushi yayi bai ce komai ba ya fara danna waya, tace "wace yayar ya Ahmad yake fadi" El-ameen yayi dariya yace "Oho" Mama jummai ta sauko rike da jaka dauke da kaya tace "Ga kayan na hada" El-ameen yace "Sannu mama" kitchen ta shiga ta fito da plate dauke da potatoe da ketchup a gefe ta ajiye gabanta, El-ameen yace "Shikenan mama xa ki iya tafiya kar dare ya maki a hanya" Mama tace "Toh," ta maida dubanta ga khadija tace "Da kin ga ta nufi sama toh kilan bayi take son shiga, ko kuma tana son xuwa ta xuba ruwa jikinta, tana son tea sosai don Allah a dinga mata, sai wannan abun da na soya mata da kunu" Khadija tace "Toh" El-ameen ya ciro dubu talatin ya mika mata yace "Ga kudin mota mama sauran sai kiyi ma mai jego siyayya" dukawa tayi ta karba tana ta sa masa albarka, ta karasa ta shafa kanta tace "Sai na dawo diyata, Allah ubangiji ya yaye maki" kamar taji me tace ta mike da sauri, mama tayi murmushi ta dau jakarta bayan ta gyara kayan da ta xubar mata, tayi wa El-ameen sallama ta nufi kofa, ai da sauri ta bi bayanta El-ameen ya mike yyi dariya yace "ta fa gane tafiya xa Kiyi" shigewa jikin mama tayi, mama tayi dariya tace "Ikon Allah, baxan dade ba 'ya ta jibi xan dawo kin ji" El-ameen ya karasa ya janye ta daga jikin mama ta fasa wani kara xata kwace kanta yayi mata tsawa, tsit tayi tana kallonsa, mama ta juya ta fita cike da tausayinta, yana rike da ita suka koma parlon ya xaunar da ita gefensa hawaye ya gani idonta, khadija ta xamo kasa ganin hakan a hankali tace "She's crying" kallonta yayi yace "Tafi kitchen ki debo min ruwa" mikewa tayi ta nufi kitchen din, tana shiga ya dafata ya lumshe ido a hankali yace "Am sorry jewel, mama xata dawo soon kin ji" dogon hancinsa ya ji ta ja kamar yanda yake mata ya bude ido da sauri, sai kuma yayi murmushi ya lakaci nata hancin a hankali yace "Pretty~Jewel"
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
23......
A hankali ya dago kanta yana kallonta, ya ciro handkerchief aljihunsa ya share mata idonta murya can kasa yace "Am sorry jewel" yana jin fitowar khadija daga kitchen yayi saurin dauke hannunsa a shoulder dinta ya koma baya, ta karaso parlon ta mika masa cup din ruwan, ya amsa ya ajiye sannan ya saukar da ita kasa shi ma ya sauko, dankalin da mama ta ajiye parlon ya jawo ya dauka ya hada da tomatoe ketchup ya kai bakinta, ta sa hannu ta karba ya sake mata, ta lashe tomatoe din, khadija tayi murmushi ta dawo kasa d'an nesa da su ta xauna tana kallonta, haka ta dinga shan tomatoe din kanta a kasa, ya tsura mata ido yana kallo, ta d'ago manyan idonta ta sauke kan nasa, dauke nasa yayi ya mike ya koma kan kujera yace "tafi kitchen ki hado mata tea khadija" khadija ta kama hanyar kitchen yana ganin haka ya kuma saukowa ya dawo ya xauna gabanta ya dau potatoe ya kai mata baki xata kauda kai ya rike kan ya hade rai ya tura mata dankalin yace "Eat!" taunawa ta shiga yi tana kallonsa tana yamutse fuska, ya kalli kofar kitchen sannan ya kalli ragowar ketchup din dake gefen bakinta, ya matso a hankali ya sa yatsa ya kwashe ketchup din ya lumshe idonsa ya kai baki, dai dai nan aka bude kofar parlon, ya koma baya da sauri yana goge bakinsa, Junaid ya shigo parlon, kallo daya yayi masu ya sunkuya ya shiga cire takalmi da safar kafarsa, El-ameen ya mike ya koma kujera yana shafa kai, karasowa cikin parlon Junaid yayi, yana sanye da trouser din uniform dinsa sai farin polo, El-ameen na kallonsa yace "Gud you came, so ya xaka yi da ita da nyt?" Xaunawa Junaid yayi bai ce komai ba, ta dauki plate din gabanta ta mike ta dawo kusa da shi ta daura kan kafarsa, murmushi ya d'an yi ya rike plate din yace "No! Thank you" El-ameen ya dauke kai hade da tabe baki, khadija ta fito rike da cup din tea ta ajiye tana kallon Junaid tace "Welcm bro" yace "Thank you, how about you telling Hajiya you will be spending the nyt at ur frnd's place?" Shiru tayi sannan ta langwabar da kai ta xauna tace "Kasan Abba yana nan" shafa kansa yayi bai ce komai ba ya dauke plate din da ta daura masa a kafa ya ajiye kasa, El-ameen ya d'aga kafada ya mike ya haura sama, kallon khadija Junaid yayi, tayi murmushi tace "Wai yaya ka ban labarin inda Ku ka ganta mana, dama kun santa ne?" Junaid yace "I donno for El-ameen" tablets dinta El-ameen ya dauko a sama ya dawo parlon, sai da ya fara shiga kitchen yayi diluting dinsu sannan ya fito, ba musu ta bude baki ya juye mata tana yatsina fuska, Khadija tayi murmushi ta daura kanta jikin Junaid a hankali tace "I like her Ya A.jay" murmushi yayi bai ce komai ba, El-ameen yace "I will be going back to clinic yanxu, nan da thirty mins xata yi bacci, duk inda ta kwanta ki kyaleta kawai" a hankali khadija tace "Ni fa ina jin tsoro, tafiya duk xa ku yi ku bar mu" El-ameen ya harareta yace "An ce maki bata komai da'alla" Junaid ya tashi shima yace "Baxata maki komai ba sister, am also leaving" shiru tayi bata ce komai ba, El-ameen yayi hanyar kofar, Junaid ya bi bayansa, da sauri ta mike ta nufe su khadija ta bi ta da kallo gabanta na faduwa, gun Junaid ta nufa, El-ameen ya juya yana kallonsu, shima Junaid kallonta ya tsaya yi, tsaki El-ameen yayi ya xaro mata ido yace "C'mon koma kar in baki knock" kara ta saki kamar ta ji abinda yace, El-ameen ya fice daga parlon, Junaid yayi murmushi ya kama hannunta suka koma parlon ya xaunar da ita yana kallonta yace "Look Jasmine xa mu dawo anjima kin ji, khadija will be staying with you har mu dawo" Khadija tace "Waow yaya sunanta Jasmine?" Da sauri ya kalleta don ya manta gaba daya tana gun, yace "Ohh! Did I call her dat" khadija tayi dariya tace "Ehh mana" ya mike yace "No I didn't" ihu ta fasa ta mike da sauri ganin ya tashi, Khadija ta langwabar da kai tace "Yaya ba ka baro gun aiki ba, stay with her plss, bata son ka tafi" yace "Am hungry, gida nake son tafiya in ci abinci" khadija tace "Ae Akwae food stuffs a nan ba sai in girka maka ba" shiru yayi sannan yace "Alryt ki min indomie kawai" tace "Toh" ta mike ta shiga kitchen, xaunawa yayi ya xaunar da ita gefensa yayi murmushi ya ja dogon hancinta yace "I will stay with you Jasmine" suna nan xaune har khadija ta dawo parlon rike da tray me dauke da indomie da fried egg a gefe sai roban ruwa da cup ta ajiye kasa tace "Gashi yaya" saukowa kasa yayi ita ma ya sauko da ita suka xauna sai kallon indomien take kamar idonta xai fito, murmushi yyi ya kalli Khadija yace "Ke baxa ki ci ba" ta girgixa masa kai tace "Na koshi" daukar fork din yayi ya debi indomie kadan ya kai mata baki bayan ya d'an huce, wani kara da yasa shi sakin fork din tayi khadija ta mike da sauri ta bar wajen, ta dinga ihu tana komawa baya tana kallon indomien duk ta ruda shi, ya riketa yana cewa "What happen jasmine, bakya so ne" ihu kawae take tana komawa baya, ya kalli khadija yace "Take it away" dauka tayi ta nufi kitchen da sauri, tsit tayi ta bi khadija da kallo, ta dawo kusa da shi ta xauna, shi kam kallon mamaki kawai yake mata, hannu ta sa ta taba long lashes dinsa, yayi murmushi ya cire hannunta yace "Indomie kike tsoro Jasmine" khadija ta fito tace "Yaya kila tsoron shi take ji, kaje kitchen ka ci" ya girgixa kai yace "no idan naje gida xan ci abincin" kallonta Junaid yayi jin ta jingina jikinsa ya ga bacci ya fara daukarta, ya mike ya kwantar da ita kan kujeran, khadija tace "Baxa ta fadi ba yaya?" Yace "Ehh, bari in tafi gida in dawo yanxu tun da tayi bacci" a hankali khadija tace "Toh amma ka dawo kafin ta tashi plss Allah tsoronta nake ji" Junaid yace "Ohk" yana fita ta dawo kusa da ita a hankali ta xauna tana kare mata kallo, doguwa ce yar siririya da ita, ta tsura ma kyakkyawan fuskarta ido da d'an karamin jan bakinta dake sheki, Khadija ta kama long fingers dinta a hankali tace "I like you sister, Allah ya baki lafiya" kallon hular kanta tayi ta dawo wajen ta d'an cire hular tana lekan kanta ta ga bakin gashinta sai sheki yake, fito da gashin ta shiga yi ta bude ido ganin tsayin gashin, ta lumshe ido tace "Waoww!" Haka tayi ta xama kusa da ita tana kallonta, komai na jikinta me kyau ne, mamaki ta dinga yi inda suka samota har suke son warkar da ita, to yan uwanta fa?? Mikewa tayi jin ana kiran la'asar taje tayi alwala tayi sallah, sannan ta d'an gyara gidan ta dawo ta xauna ta ci gaba da kallonta daga inda ta tsaya, bude kofa taji anyi ta juya da sauri, taga El-ameen ne, ya karaso parlon yace "Capt ya tafi ne" ta gyada masa kai, ya iso kusa da su yana kallonta yace "She's still sleeping koh?" Ta gyada masa kai, ajiye ledan hannunsa yayi ya tada ta ya tafi sama da ita, khadija ta hade rai ta bi sa da kallo, haka kawae taji haushin abinda yayi, ta ja tsaki ta dauke kanta hade da tabe baki ta mike ta koma kujera ta xauna, ba a dau lokaci ba ya sauko, kallonta ya tsaya yi ganin yanda ta hade rai yace "Ke in kin gaji ne tashi ki tafi gidan ku" mikewa tayi ta dau Jakarta ta fice fuu, yayi tsaki ya dau wayarsa da ke ring. Tana fita ta kira Junaid yana d'agawa yace "Ta tashi ne?" tace "Wani tashi? Bayan ya wani ce wai in tafi" Junaid yace "Wa?" Tace "Ya El-ameen mana, wai wani in tafi gida" shiru ya d'an yi kafin yace "Saboda me?" Tace "Oho masa, ya wani dauketa ya kai ta daki bayan bacci take" mikewa Junaid yayi daga zaunen da yake parlon Mumy yace "daki kuma, ke kina ina?" Khadija tace "Ehh mana, ni na riga na fito ma tafiyata xan yi" katse wayar yayi kawai ya ajiye, Mumy dake ta kallonsa tace "Wani dakin? Kuma da wa kake waya" Kallonta yayi da sauri don ya mance tana wajen yace "Ohh dama, dama na aiketa ne, shine... no wai ce min tayi yayarta ta kulle ta a daki, khadija ce" Mumy na masa wani irin kallo tace "Karya kake" ya xaro ido yace "Mumy karya kuma" ta girgixa kai tace "Ahmad am beginning to suspect you this days, behaviours dinka sun fara canxawa, i notice kana boye min wani abu, but be careful" daga haka ta shiga bedroom, Humainah dake xaune parlon ita ma tana gyada kai tace "ta tashi ne? uhnn ko waye ya tashi oho, daki kuma? Uhnn ko wani dakin yake nufi oho, ke kina ina? Uhn ko wacece haka oho, hmm we are beginning to suspect you this days Captain be careful" wani harara ya watsa mata ta mike tayi masa gwalo tace "In tayi tsami ma ji dai" da sauri ta shige dakin Mumy ita ma. Ya shafa kansa a hankali don yasan ko hauka yake baxae bari Mumy taji xancen mahaukaciyar nan ba, tabdi! mikewa yayi da sauri ya dau makullin motarsa ya fita, waje ya fita don bai shigo da motarsa compound ba ya hau motar ya nufi gidan El-ameen, cikin few mins ya isa, yana Parkin ya fito ya shiga gidan, xaune ya tarda El-ameen balcony yana waya, ya tsaya yana kallonsa har ya gama ya hade rai yace "Y did you send khadija away?" El-ameen yace "Haka tace maka, to let me get hold of her" Juyawa Junaid yayi jin an bude gate, wata mace da baxata wuce 27 ba ta shigo, ta karaso balcony ta gaida Junaid, ya gyada mata kai kawai, mikewa El-ameen yayi yace "Welcm, ki shiga daga ciki" ba musu ta shiga parlon, El-ameen yace "we are hiring her for 2 dayz kafin Mama ta dawo, sai ka biyata 10k, old nurse din clinic din mu ce" Junaid ya daga shoulder yace "Anyhow" juyawa yayi yace "sai gobe, na tafi" El-ameen yace "Wato xuwa Kayi ka ga what I was up to da nace khadija ta tafi koh?" Junaid yayi murmushi bai ce komai ba yayi gaba abunsa, El-ameen yayi kwafa ya shiga parlon. Karfe shidda da wani abu Junaid ya shigo gida, ya ga khadija tsaye nesa da balconynsu, Hajiya da Umma na xaune sai Sadiya da Suhaima, Sadiya sai cewa take "Kawai ki bar min komai a hannuna Hajiya idan na lallasa ta xata fadi inda taje wllh" Umma tace " Ni tun da ta fara mu'amala da shegiyar 'yar da aka kawo gidan nan Humainah take kowa, dabi'un ta suka canxa, ke har kin kai matsayin da xa Kiyi karyan xuwa gidan kawa ki fita tun safe sai yanxu kike shigo mana gida don Kazan ki" junaid ya karasa wajen ya gaida su yace "Hajiya tare muka fita, ta rakani ne" Umma ta watsa masa wani kallo tace "Da yake ba Aysha bace ko Fatima dole ka kareta mu bar ta ta lalace" Juyawa khadija tayi fuu ta nufi part din Mumy, Hajiya ta shiga kwala mata kira tana cewa "Kika kuskura kika shiga wajen nan mai raba ni da ke sai Allah, kuma wllh kin ji na rantse sai kin fadi daga inda kike"
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
24.....
Junaid ya juya shi ma ya bar wajen, Hajiya ta bi bayan khadija tana huci, a balcony ta tsaya ta tura kofar tana cewa "Kar ki bari in shigo parlon nan khadija, tun muna mu biyu ki fito ki wuce" tsayawa Junayd yayi yana kallon ikon Allah, Humainah dake xuge jakar kayanta da ta gama hadawa a parlor ta tabe baki ta mike, ta dauki remote din TV ta kure maganar gaba daya, Hajiya ta xaro ido tana kallonta, ji take kamar ta shaketa kawai ta huta, can dai tace "Ke wai ni sa'ar uwar ki ce kika raina ni haka a gidan nan, ina magana za ki kure min TV?" Humainah ta rike kugu tace "Ni ba dai uwata ba wllh" Sadiya ta karaso bakin kofar parlon tana cewa "Bata fito bane Hajiya" Hajiya ta fashe da kuka tace "Yanxu ni yarinyar nan take ma rashin kunya Sadiya, a haihuwar kaji ban yi jika da shegiyar ba" a fusace Sadiya ta shige parlon tayi kan Humainah, Junaid na ganin haka ya bi bayanta, ai tuni Humainah tayi dakin Mumy da gudu tana kwala mata kira, hakan kuma bai hana Sadiya bin ta ba tana kunduma mata xagi, wani tsawa Junaid yayi mata tun kan ta shiga dakin Mumy ya fixgota ya nuna mata kofa yace "Get out, ko a mafarki kika kuskura kika yi attempt din t'aba ta wllh sai na ba66allaki a gidan nan" kallonsa kawai take fuskar nan nata daure don tasan tana iya magana yanxu ta sha mari, Hajiya ta shigo parlon tana huci tace "Wllh Ahmad idan ka bari na saka ka gaba a gidan nan sai xaman duniyar nan gaba daya ta gagare ka, kayi hankali da ni ka bi ni a hankali, bani da kyau wllh, amma in dai ni ce mu je xuwa sai ka gwammace uwar ka bata haifo ka gidan nan ba, xaka san da ni kake" Mumy ta fito tana ma Hajiya wani kallo tace "Babu abinda kika isa ki masa wanda Allah bai masa ba, mu da Allah muka dogara, aniyar ki ta bi ki kuma" Hajiya tayi shewa tana murmushi tace "Toh mu xuba da ku," daga haka ta juya fuu ta fice, Sadiya ta bi bayanta. Junaid ya girgixa kai ya juya ya fice daga parlon, shi gaba daya xaman gidan ma ya ishe sa kawai. Mumy ta kwalo ma Humainah kira ta fito, strictly tace "ina raba ki da mutanen nan baki ji ko Humainah, ina ruwan ki da su wai da har xaki dinga shiga tsabgarsu, kinsan Allah baxa mu shirya ba idan magana za ki dinga dauko min, so kike su sa ki gaba kema koh? To maxa gama hada kayan ki yanxun nan Ahmad ya tafi da ke inda xai kai ki kafin Abba ya dawo su kuma hada ki da shi" Juyawa Humainah tayi ta koma daki kamar xata yi kuka, Khadija ta fito daga daki tace "Mumy kiyi hakuri," Mumy tace "Kinga idan kin yi laifi ki daina yo wa nan khadija, sai ki tsaya can ki basu hakuri" Khadija ta turo baki ta koma dakin su fatima. Junaid na shigowa bayan yayi wanka ya canxa kaya Mumy tace "Maxa kai ta gidan Aisha kan dare yayi Ahmad" ya kalli agogo don dama fita xai yi ya maida motar jiya, yace "Toh Mumy" Mumy ta kwalo ma Humainah kira tace "Dauko jakar ki da hijab" tana kumbure kumbure ta fito rike da 'yar jakar kayanta da Hijab, Junaid ya mike yace "Sai na dawo Mumy" Mumy tace "Allah ya kiyaye, amma motar waye ka dawo gidan nan jiya da?" Ya d'an shafa kai yace "A frnd, idan na ajiyeta xan mayar ne ma" Mumy tace "Ohk," ya fita Humainah na biye da shi a baya, Mumy tayi murmushi tace "Ba sallama Humainah" kamar xata yi kuka ta daga mata hannu ta fice, Mumy tayi dariya tace "Lallai Humainah" As usual Hajiya da Umma na balcony, duk suka bi su da hararan tsana, tsayawa yayi har Humainah ta karaso inda yake ya karbi jakar hannunta suka nufi parking lot, Umma ta kalli Hajiya tace "Ke wllh naga kamar sonta yake, dubi fa har da wani rike mata jaka, sai ya iya yiwuwa ma ya fito da ita a matsayin warce xai aura idan lokacin da Alhaji ya dibar masa yayi" Hajiya ta xaro ido tace "Ae ko da mun banu mun lalace, meye abun yi Bilki?" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "ba mu ga ta xama ba,"
Humainah ta kalli motar da Junaid ya shiga tace "Motar waye wannan?" Kallonta yayi ya bude ido yace "Naki" ta hararesa ta xaga ta shiga, yana warming motar ya kira El-ameen, bugu biyu ya d'aga, Yace "kana ina ne Dr?" El-ameen yace "ina gida" Junaid yace "Ohk plss ka fito mu hadu kasan layin ku" El-ameen yace "Why?" Junaid yace "kai dai ka fito, it's urgent, kuma ka taho da motarka" daga haka ya katse wayar, ya ja motar suka bar gidan, Humainah tace "Amma ya Ahmad gidan Anty Aysha aka ce ka kai ni fa xaka wani ce ku hadu a kasan layi, to yawo xaka yi da ni a mota" ba tare da ya kalleta ba yace "Ni tricycle ma zan je in saka ki yanxu ya kai ki" ta xaro ido tace "Ehh!" Yace "Yess!" yana isa layin su El-ameen ya hango motarsa ya isa gun motar yayi parking ya fito, xuge glass El-ameen yayi yana kallonsa a bit surprise yace "Whose car is dat?" Junaid yace "A good samaritan's, jiya da ka yasar da ni a titi ka wuce...." El-ameen yayi tsaki yace "Kayi mugun bata min rai jiyan nan, don me yarinya xata shirga karya wai ta mance Atm card a gida ka yi amfani da kudina ka biya uban kayan da ta siya" Junaid yace "Ba dai na mayar maka da kayan ka ba, keep dat matter aside kar kayi provoking dina" El-ameen ya tabe baki yace "Ni Mama jummai ma na ba kudin da xata tafi daxu, and dat's ur responsibility not mine" Junaid yace "Whatever, gidan Aisha xaka taimaka ka kai budurwar nan taka, ni ina son maida motan mutane ne kar ayi tunanin guduwa nayi da shi" El-ameen ya leka motar suka hada ido da Humainah, da sauri ya dauke kai ya bude ido yana kallon Junaid, Junaid yayi 'yar dariya yace "Ehh ita din ce" daga haka ya juya yana kallon Humainah da ta hade rai cikin mota ya duka yana kallonta da kyau yace " Oya fito saurayin ki ya kai ki ni....." Kuka ta sakar masa tana yarfe hannu tace "Wayyo ni, wallahi kai aka ce ka kaini bbu inda xan bin sa" ya bude ido yace "Ke ba motata bace wannan, xan maida ma me shi ne" ta marairaice masa cikin sigar shagwaba tace "Plss mana ya Ahmad don Allah ka kaini" murmushi kawai yake yana kallonta, can ya mike ya juya gun motar El-ameen da ya wani hade ya daga kafada yace "Kaji wai tsoronka take ashe, don haka plss frnd just excort me in maida motar sai mu tafi gidan Ayshan da naka motar" El-ameen yayi masa wani kallo yace "I don't have dat time, dama kiran da ka min kenan?" Junaid yayi murmushi yace "Toh shikenan, idan mun je can xa mu samu tricycle" daga haka ya xaga ya koma driver seat ya tada motar ya bar layin, tsaki El-ameen yayi ya bi motar da harara can ya tada nasa motar ya bi bayansa, Junaid na ganin haka yayi murmushi don dama yasan sai ya biyo sa. Cikin mintunan da basu wuce sha biyar ba ya iso layinsu Hafsat, yayi parking inda tayi jiya, ya fara kalle kalle don bai karbi numberta ba, Humainah tace "Ya Ahmad ina ne nan" yace "gidan su budurwata" kallonsa kawai take ya bude motar ya fita ya xaga ya bude mata ta fito, dai dai nan El-ameen ma ya fito ya rungume hannu ya hade rai yana kallonsa, murmushi Junaid yayi ya daga kafada ya nufi gate din gidan, yana danna bell maigadi ya leko, Junaid yace "Amm ina yini, Hafsat nake nema a gidan nan," Mai gadin yace "Toh bari a mata magana" komawa Junaid yayi kusa da El-ameen ya tsaya yace "Da ma ka saki ranka kar Humainah tace ta fasa" shi dai El-ameen bai tanka sa ba, Humainah kam ko kallonsu bata yi ba, bude gate din gidan aka yi ta fito sanye da jan atamfa sai farin Hijab, xaro ido El-ameen yayi yana kallonta sai kuma ya kalli Junaid, murmushi tayi ganin Junaid sai dai lokaci daya murmushin ya bace ganin El-ameen gefensa da tayi, ta karaso kusa da su ta gaida su, Junaid ne kadai ya amsa don shi El-ameen juyawa ma yayi ya shige motarsa, banda kallonta babu abinda Humainah take, Junaid ya shafa kansa yace "Ga motar ki, tnx a plenty, am grateful" ta kirkiri murmushi kawai tana gyada masa kai, ya mika mata makullin motar ta karba, ya kalli Humainah yace "ga kanwata can ku gaisa" karasawa tayi gun Humainah tana kallonta murmushi dauke fuskarta tace "Sannu, ina yini?" Humainah ta dauke kai babu yabo bbu fallasa tace "Lafiya" juyawa tayi ta bar wajen duk jikinta yayi sanyi, ta kalli Junaid tace "Toh nagode" yace "Ni ne da godiya" kallon Humainah yayi yace "Taho mu wuce" kamar xata tashi sama ta karaso ta bude bayan motar El-ameen ta shige, Junaid ya ciro wayarsa ya mika ma Hafsat yace "Sa man digit dinki mu dinga xumunci" karba tayi ta sa numberta ta mika masa suka hada ido da El-ameen dake kallonsu, da sauri ta dauke kanta, shi ko ya tabe baki, Junaid ya mata godiya ya xaga ya bude front seat ya xauna, El-ameen ya figi motar suka bar layin. Sai da suka hau main road El-ameen yace "Da nasan inda xaka kenan wllh ban xuwa, yaushe ka xama haka Captain, yaushe ka fara ware ma mace lokacin ka har da wani karban numberta, Tabdi" har suka iso gidan Aysha ana kiraye kirayen Magrib Junaid bai ce ma El-ameen komai ba, ya juya yana kallon Humainah yace "Toh gashi mun kawo, ki gaida ta" daukar jakarta tayi ta bude motar ta fice ta nufi gate, Junaid ya bi ta da kallo sai kuma ya bude motar ya bi bayanta, tsaki El-ameen ya ja ya danna masa horn, har gate Junaid ya shiga ya fixgota ta hade rai tace "Meye kuma" ya wara ido xai yi magana, ta fashe da kuka, kallonta ya tsaya yi, can ya d'ago kanta yace "What happen?" Ta fixge hannunta taki cewa komai, yace "Baki son xama gun Ayshan ne kuma?" Ta girgixa masa kai tana goge hawayen dake kuma sakko mata tace "To wace wannan yarinya" kallonta kawai yake sai kuma yayi murmushi ya ciro wayarsa daya a aljihu ya mika mata yace "Anjima xan kira ki in gaya maki wacece" juyawa tayi zata bar wajen ba tare da ta karba wayar ba, ya kuma dawo da ita ta fashe da kuka, murmushi yayi ya kama hannunta ya saka wayar, ya juya ya fita daga gate din don El-ameen ya danna horn ya kusa sau biyar, yana shiga motar El-ameen ya figi motar yana cewa "Wai meyasa kake min abinda ka ga dama ne Capt, ka wani shanya ni a mota kana biye ma karamar yarinya 'yar cikin ka, ga baiwar Allah can ko abinci nasan bata ci ba...." Junaid yace "Budurwar ka fa na rako" El-ameen ya tabe baki yace "No, ni ban ce ina sonta ba kawai nace tana da kyau ne, kuma ni ba budurwa ta bace, warce nake so ma ta fi ta komai" dariya Junaid yayi yace "Xa ma ka fadi gaskiya ne, a ina ka samo warce kake son kai da kake tsoron mata" El-ameen yace "Am serious, ni bana son mace me tsiwa da jaraba, warce nake so is very gentle...." Junaid yayi dariya yace "Ita ma bata son mai tsoron mace" El-ameen yayi tsaki yace "Can gidan fa nake son in je don nasan baxata ci abinci ba sai naje shine ka wani bata min lokaci" Junaid ya tabe baki yace "Irin kamar ka damu da ita din nan koh" El-ameen yace "Of course na damu, nama fi ka, kai da baka da aiki sai na bada kudi, ni kuma lokacina gaba daya na bata, a yanxu haka I know her likes nd dislikes, duk motsin da xata yi nasan me yake nufi, I've studied her more than you can imagine, kai you are only showing dat you are a millionaire kana nuna kai kadai ma xaka iya kashe ko nawa ne ba sai ka nemi assistant ba, ni kuma...." Junaid ya ja tsaki yace "Aikin banxa kenan, don without that money you are talking about all this you are listing won't come to action, kai da kake kyashin kashe mata naira biyar din ka, my frnd ka daina listing kan ka a wa enda suka taimake ta ma a rayuwa, you are only decieving ur self, coz I hired you and am paying you for the job, yau nace bana bukatan service dinka you are gonna quit!" Parking El-ameen yayi yana kallonsa yace "Haka kace Ahmad?"
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
25....
Junaid yayi dariya yace "Of course haka nace ko nayi karya, ka fadi sisin da ka taba kashe mata in biya ka, kai yanxu har ka nuna mun ka fi ni damuwa da ita, wanda da na biye ka tun farko da baxa mu daukota ba ma, wani irin discourage dina ne baka yi ba, wani irin dariya ne baka min ba kan yarinyar nan..." El-ameen bai ce komai ba ya ci gaba da tukin sa, banda dariya babu abinda Junaid yake, ganin El-ameen hanyar gidansu ya nufa Junaid yace "Ohh ka fasa xuwa ka bata abincin ne?" Shi dai El-ameen bai tanka sa ba har ya isa bakin gate din gidansu, ya juya yana kallonsa yace "Idan kaga na kuma bi ta kan patient dinka, ka gaya min wanda ya fi wannan," daga haka ya fice daga motar ya shige gida. Junaid yayi murmushi yana shafa kansa yace "Uhum wai fushi yayi?" D'aga kafada yayi ya koma driver seat ya ja motar ya bar layin, gida shi ma ya nufa abun sa. Washegari Junaid na gun aiki ya dinga kiran El-ameen ya ki d'agawa, shi dariya ma abun ke basa, don bai ga abun fushi ba daga fadin gaskiya, Karfe biyar ya baro gun aiki, ya canxa uniform din jikinsa xuwa mofti ya tafi can gidan nasa, a hankali ya tura kofar parlon, nurse din dake kula da ita na tattare biscuits din da yayi littering din tsakar parlon, ita kuma tana kwance nan kasa tana bacci, Junaid ya karaso ya amsa gaisuwar da nurse din ke masa yace "Dr El-ameen ya xo yau kuwa?" Ta girgixa kai tace "Bai xo ba, na kirasa ma he's not responding" Junaid yayi murmushi ya xauna yace "Ohk, amma ta ci abinci?" Nan ma ta girgixa masa kai tace "tun jiya ma taki cin komai, kaga biscuit din nan ma na fiddo mata shima bata ci ba ta watsar, yanxun ma da kyar ta kwanta tun safe taki xama na rasa me take nema, duk ta ki yarda da ni" Junaid yace "Ohk, me yace maki ta fi so, I mean abinda take ci?" Tace "Kasan yace xai dawo jiya toh bai dawo ba bare ya gaya min, kuma duk yau ba a mata allura ba tunda bai gaya min yanda zan yi ba" Tabe baki Junaid yayi ya mike ya fice daga parlon. Gidansu El-ameen ya nufa Ummi tace ai tun safe yana clinic, ya mata sallama ya fito ya kama hanyar clinic din, Yana isa nurses din dake reception suka ce masa ai baya nan, yace "Ohk haka yace maku ku ce min idan na xo" kallonsa suka tsaya yi, ya haura sama ya tafi office dinsa, ya murda kofa yaji da gasken baya nan, tsaki yayi ya sauko ya fice daga asibitin, a mota ya dinga kiransa ya ki dagawa, shi ya rasa abun jin haushi a maganarsu ta jiya, daga fadin gaskiya, tsaki yayi ya tada motarsa ya tafi gida abun sa. Wasa wasa har 2 dayz El-ameen yaki xuwa can gidan, ya ma kashe wayoyinsa gaba daya, shi ma Junaid ya fita harkarsa bai kuma bin ta kansa ba, matsalarsa daya yanda Jasmine taki cin komai, gashi da ganinta xaka san abu na damunta, duk taki sakin jiki, though in yaje gidan da yamma ta kan je ta kwanta gefensa ko ta xauna kusa da shi, amma duk yanda xai yi da ita ta ci abinci bata ci, sai dai k'adan shi ma da kyar, in ya takurata tayi masa ihu, bini bini xaka ga ta kalli kofa ko taje can ta tsaya kamar dai tana jiran wani, on the third day Mama jummai ta dawo ya sallami nurse din, yasan yanxun xata fara cin abincin tunda ga mama jummai kila dama don bata saba da nurse din bane amma sai yaga otherwise don yi ma tayi kamar bata taba ganin mama jumman ba, ta kuma ki cin abincin still, da mama jummai ta tambaye Junaid El-Ameen ce mata yayi, yayi tafiya ne, duk abinda mama jummai tasan tana so sai da ta yi ta bata duk taki sai ketchup da take ta sha, duk baiwar Allahn ta rame. Yau Junaid na barin gun aiki ya nufi gidansu Faisal, yayi sa'an shi ma dawowan shi daga aiki kenan, Faisal yayi mamakin ganinsa barin da yaga ko canja uniform din jikinsa bai yi ba. Junaid ya xauna bayan sun gaisa yace "Ina son muyi wata magana da kai ne frnd" Faisal ya maida hankalinsa sosai yace "Am ol ears" Junaid ya shafa kai a nutse ya soma basa labarin mahaukaciyar tun daga farkon haduwarsa da ita, Faisal ya kwalalo ido yana kallonsa baki bude, har Junaid ya kai karshen labarin yana murmushi, Faisal ya sauke ajiyar xuciya yana gyada kai yace "Babban magana, but El-ameen bai kyauta ba, kuma ni ban ga abun fushi a nan ba, sabon da tayi da shi ne ya hanata sakin jiki da bata ganinsa, shiyasa take kin cin abinci!" Junaid ya tabe baki yace "Yanxu dai you are a Doctor, so nake plss ka gaya min yanda xaman psychiatry yake, is it advisable in kai ta can babu matsala?" Faisal ya kuma sauke wani ajiyar xuciyar yace "Gaskiya ina ga na gida kamar yanda El-ameen ke mata ya fi, kuma gashi har ta saba da shi samun lafiyarta ba lallai ya dau lokaci ba, yanxu dai kar ka damu xan je in same sa, nasan..." Junaid yace "No! no bana bukatan sa kuma, he shud hold on to his medication, idan taje psychiatry din suma xata saba da su" murmushi Faisal yayi, Junaid ya mike yace "Plss ka binkitar min psychiatryn da ka ga is ohk... I might come back later ko kuma in kira ka. Don yanxu Mumy xata fara kirana its almost six o'clock" Faisal ya bi sa da kallo har ya fita sannan ya shafa kai yace "Lallai Junaid da El-ameen, mahaukaciya kuma???" Mikewa yayi shi ma ya dau makullin motarsa ya fita xuwa gidansu El-ameen din, Ummi ce da Sumayya xaune parlor, ya gaida Ummi, ta amsa da fara'a tana tambayarsa mutan gida yace "Duk Suna lafiya Ummi, El-ameen na nan kuwa" tace "Ehh yana daki" dakinsa ya nufa ya tura kofar ya shiga da sallama, Ummi ta kalli Sumayya tace "Ki kai masa drink, ki tambayesa ko xai ci abinci" mikewa tayi ta nufi kitchen, kwance faisal ya sami El-Ameen da laptop a gefensa sai dai wayarsa yake dannawa, El-Ameen ya mike xaune ganinsa, Faisal yana murmushi ya karaso ya xauna gefensa yace "Yane the great Dr Ahmad El-ameen" El-ameen yayi murmushi shi ma ya mike xaune yace "Daga ina haka da yamma?" Faisal na kallon fuskarsa ganin yanda manyan idanuwansa suka fito yace "You look pale, are you ohk?" El-ameen ya lashe lebbensa yace "Stress ne frnd, ya aikin?" Faisal yace "Alhmdllh, Ya captain naka...." Dai dai sanda Sumayya ke kokarin shigowa dakin da faranti me dauke da drink da ruwa jin an ambaci Junaid ta tabe baki ta tsaya jikin kofar, El-ameen yace "Yana gidansu!" Faisal yayi dariya yace "Kuna nan har yanxu kamar 'yan biyu abun ku" El-ameen yayi murmushi yace "Sure!" Faisal yace "Uhmm!" El-ameen na kallonsa yace "Ya aka yi?" Faisal yayi murmushi yana girgixa kai yace "Bana tunanin akwai abinda ya isa ya hada ka da Captain..." Sumayya ta gyara tsayuwa da kyau ta baxa kunnuwa, El-ameen yace "Ban fahimta ba" Faisal yace "Daxu ya xo ya sameni ya kuma ban labarin baiwar Allahn da ku ke kokarin ganin kun ceto rayuwarta daga....." El-ameen ya katse sa yace "No! Da yake kokarin ganin ya ceto rayuwarta dai" Faisal yayi murmushi yace "Haba Dr, bayanin da Captain yayi min is not enough ace kayi fushi haka, kuma naga kun saba haka a tsakanin ku, kar ka manta lada ba kadan ba xaka samu idan yarinyar nan ta dawo hankalinta" El-ameen yace "No ni bn yi fushi ba faisal, just dat nayi quit ne, ya nemi wani likitan ko ya kai ta psychiatry..." Faisal yace "No pls, kar kace haka Dr, ba don Junaid xaka yi ba don Allah xaka yi...." El-ameen yayi murmushi yana girgixa kai yace "You know what?" Faisal ya girgixa kai, yace "Wllh wllh ban yi kuma, I've quit, he shud take her to the psychiatry, ka dai ji rantsuwar musulmi na maka, but babu damuwa xai iya ci gaba da amfani da gidana" Sumayya dake jikin kofa har lokacin duk tayi confuse ta rasa gane kan maganar, to wace yarinya suke magana a kai, yanke shawaran kiran Suhaima tayi tasan xata bata labari, El-ameen ya mike yace "kaga am going to clinic yanxu faisal" faisal ya sauke ajiyar xuciya yace "Ban ji dadin rantsuwar da kayi ba El-ameen, don Allah xaka yi ba don Junaid ba" El-ameen ya koma ya xauna yace "Look faisal, kullum! I mean everyday, karfe bakwae na safe baya karasawa nake barin gida in tafi gun yarinyar don akwai injections din da nake mata a lokacin, before leaving kuma sai na tabbatar tayi breakfast dat's around to eight, ina barin gidan xan kuma dawowa nan gida inyi wanka in shirya inyi breakfast snn in tafi clinic, a can clinic duk abinda nake da xaran sha daya da rabi yayi xan bari koma meye kuwa in tafi gun yarinyar don bata drugs dinta, in tilasta ta taci abinci sannan in kuma komawa clinic, duk abinda nake Karfe uku da rabi xan bari in kuma komawa gun yarinyar don bata drugs, sannan in sake komawa asibiti, Karfe bakwai da rabi a gidana yake min don a wannan lokacin ma tana da injections, baxan kuma bar gidan ba sai after ten don kafin ta kwanta Akwae drugs da xata sha, kasan sau nawa Junaid ke xuwa gidan?" Faisal yayi shiru yana kallonsa, El-ameen yace "Sau daya! shi ma sai da yamma ko kuma after magrib, kuma da ya xo xaka yi tunanin tsikararsa ake a gidan da kayi magana yace maka Mumy, ni ne ban san dadin tawa Mumyn ba, kasan matsalar da nake fuskanta yanxu gun parent dina kan yarinyar nan kuwa? yace ko biyar ban taba kashe mata ba I agree kuma dat is as a result of yana nuna shi me kudine, baya bukatan assistant din kowa, kasan dai yanda yake abubuwansa na girman kai, ni kuma kallonsa kawai nake don in kudin account dinsa sun yi wuta wllh basu wuce million uku ba in ma sun kai, kuma medication din hauka ba karamin kudi mutum xai kashe ba, yau da gobe yana cire dubu Dari dubu hamsin dubu dari biyu, dole kudin xai yi kasa, at dat time ko waye ubansa dole xai ce min i shud help ni kuma hakan nake jira dama, don kai kanka kasan waye ni idan baka tambayeni ba wllh baxan baka ba, in ko ka tambaya ko last card dina ne xan baka, kuma yace inyi excluding kai na a wa enda suka taimaketa a rayuwa tuni nayi hakan, don haka ka rakasa ya kaita psychiatry kawai frnd"
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
26.....
Mikewa faisal yayi ya d'aga kafada ya nufi kofa, da sauri Sumayya ta bar jikin kofar ta shige dakinta rike da farantin jin takunsa, faisal yayi ma Ummi dake parlor har lokacin sallama ya fita daga gidan, El-ameen ya koma ya kwanta tare da lumshe idonsa. Suhaima ce ta shigo parlor rike da waya tana kallon Hajiyarsu tace "Hajiyarmu yanxu sumayya ta kira ni...." Da sauri ta kalli khadija da ke kwance parlon sai kawai ta juya ta koma daki, Hajiya ta mike ta bi bayanta, khadija ta tabe baki ta ci gaba da danna wayarta. Junaid na kwance parlon Mumy that same day, idonsa lumshe kamar me bacci kamar wanda ya tuna abu ya mike xaune yana kallon wayarsa ya dauka yayi dialing number bugu uku aka d'aga, bayan sakwanni 20 jin ba ace komai ba daya bangaren yace "Uhn how you?" Jin an ki cewa komai still, yace "sai in kashe wayata ne" kamar xata yi kuka tace "Toh ina ruwana ni nace ka kira" murmushi yayi yace "Ohk, sai anjima" da sauri tace "Noo Ya Ahmad don Allah ka xo ka dauke ni, gida nake son dawowa" yace "Anki, xaman ki a can ya fi maki, sai kiyi ta neman fitina da Jawahir!" Katse wayar yayi ya ajiye yana murmushi, can ya mike ya fita ya koma part dinsa don tun da ya dawo daga gun faisal yake kwance parlon Mumy ko uniform bai cire ba, yana bedroom ya fito daga wanka yana shiryawa yaji an murda kofar parlor, juyawa yayi yana kallon kofar dakin har aka bude, faisal ya shigo da sallama, Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Glad you came" faisal ya karaso ya zauna gefen gado yace "ka jira har El-ameen ya sauko Captain, yayi sama da yawa, beside ni ban...." Da sauri Junaid yace "Xuwa kayi ka samesa?" Faisal ya d'aga masa gira, Junaid yace "Ohhh shit! Why? Meyasa xaka min haka, why did you go faisal, gaskiya ka bata min rai, who's he da yake tunanin without him Allah baxai bata lafiya ba, shi din banxa, bana bukatansa a lamari na kuma, bana bukata...." Faisal yayi murmushi yana girgixa kai yace "Haka kawai in sa baki daga karshe in ji kunya, da dai ban san ku bane, duk ku yi ku gama" Junaid yayi tsaki ya ci gaba da shirin sa, yana gamawa ya juya yana kallon faisal yace "Ka sama min psychiatry din ne frnd?" Faisal yace "Psychiatry me kyau sai Abeokuta or Lagos, but I will advice you to take haka to na Abeokutan ya fi, Neuro Psychiatric hospital Aro" Junaid yace "Har Ogun state? No plss samo min a nan north" faisal yace "Toh ai na can yafi komai ne, ga qualified neurologist..." Junaid ya xauna gefen gadon yace "Abeokuta kuma? Or kasan me I shud just look for a private neurologist for her...." Faisal yayi murmushi yace "That's money frnd, hospital ya fi!" Junaid yayi shiru, sai kuma ya shafa kansa a hankali yace "Allah xai rufa asiri, just get me a qualify one" faisal yace "ohkk dats not a problem, duk dai yanda ta yiwu in na gidan in na hospital," Junaid ya gyada kai yace "Toh shikenan" faisal yace "Sai da abu ya kwabe maku sannan xa a wani xo a sameni.... Ni kallonku kawai nake kai da El," Junaid yayi murmushi ya mike yace "Kaga xan kai mata fruits can gidan yanxu, muje part din mumy sai inyi kamar rakaka xan yi" faisal yayi dariya yace "Plss do and get ur freedom captain! You are getting old fa Mumys boy!" Junaid yace "Uhum kaga in tafiya xaka yi ka taso mu tafi!" Mikewa faisal yayi ya bi bayansa yana dariya, suka nufi part din Mumy, faisal yayi mata sallama, Junaid na shafa kai yace "Mumy bari in rakasa!" Mumy tace "Toh sai ka dawo" fita suka yi faisal na dariya, Suhaima dake tsaye bakin tap ta bi su da kallo tana tunanin xancen da Sumayya ta mata a waya, ajiyar xuciya ta sauke tana tunanin ta ina xata fara binciken da Hajiya ta sa ta, wai Mahaukaciya, tab, har Allah Allah take washegari yayi! Suna fita gidan Junaid ya kalli faisal yace "Kaga ban fito da mota ba, da taka xa mu je can gidan daga can sai ka ga Mahaukaciyar," faisal ya buda ido yace "Da take neman hada aminai biyu ba!" Junaid ya tabe baki yace "No bata hada mu ba, frndship din ne ya xo karshe dama" dariya kawai faisal yake, Junaid ya karbi makullin hannunsa ya shiga motar ya tada. A hanya suka siya fruits sannan suka kama hanyar gidan El-ameen, mama na sharan parlon suka shigo, ta mike tana masu sannu da xuwa, Junaid sai kalle kallen inda xai ganta yake, mama jummai ta lura da hakan ta nuna masa gefensu tace "Ga ta can" juyawa yayi ya ganta xaune ta jingina da bango ta d'an dukar da kai alamar bacci take, xai yi magana Mama jummai tace "Babu yanda banyi da ita ta bar wajen nan ba ta ki, kuma ta ki kwanciya, ni dai na rasa gane kan baiwar Allahn nan, ko abinci taki ci, dama Aminu kadai yasan kanta, rashin cin abincin nan ba karamin daga min hankali yake ba, toh ko dai bata da lafiya ne" Junaid ya tabe baki bai ce komai ba, faisal kuwa kallonta kawai yake, duk da ba ganin fuskarta yake ba, Junaid ya kallesa sannan ya karasa kusa da ita ya duka kamar me rada yanda bbu wanda xai ji sa a hankali yace "Jasmine!" D'ago kanta tayi da sauri ta bude ido tana kallonsa, a hankali faisal ya dinga komawa baya yana kallonta ko kiftawa bai yi har ya isa jikin kofa bai sani ba, kalle kalle kawai take sai kuma ta mike tana kallon kofar jin alamar mutum, da sauri ta nufi kofar Junaid ya bi ta da kallo, tana isa bakin kofar ta tsaya tana kallon faisal, still yayi a wajen ko kwakkwaran motsi bai yi, har lokacin idonsa na cikin nata, juyawa tayi a hankali ta dawo kusa da Junaid ta xube gabansa ta xauna, kallo daya xaka mata ka ga ramar da tayi, mama jummai ta fara dariya tace "Wayyo, ca take Aminu ne baiwar Allah, to ko don bata ganinsa yasa taki sakin jiki ne? Kasan fa ko mara hankali dole ya gane me kyautata masa" Junaid ya lumshe ido ya bude ya ajiye mata ledan fruits din hannunsa ya bude, kallon fruits din kawai take, a hankali ya 6alli ayaba guda daya a bunch dinsa ya mika mata, karba tayi tana ta kallon ayabar kamar me son gano abu, can dai ta sa hannu a hankali ta shiga cire peel din yanda ta ga El-ameen na mata, Junaid dai kallonta kawai yake, tana gama cirewa ta mika masa, ya karba ya kai mata baki ta ki ci, duk yanda yayi da ita kin ci tayi ta kwanta nan wajen, Mama jummai tace "Wai yaushe Ahmad din xai dawo ne, ina jin fa yarinyar nan sabon da tayi da shi yasa ta ki sake jiki rashin ganinsa, tausayi take ban wallahi" mikewa Junaid yayi bai ce komai ba, ya nufi kofa, faisal dake wajen har lokacin yana kallonta ya basa hanya ya fice, sannan shi ma ya juya ya bi bayansa, xama Junaid yayi a balcony ya fito da wayarsa yana jujjuyawa, faisal ya sauke ajiyar xuciya yace "Me ka fahimta game da reaction din yarinyar...." Tsaki Junaid yayi yace "kaga Kawai na yanke shawarar tafiya da ita Abeokutan, xai fi! Maganar ta saba da wannan ta saba da wancan bai taso ba yanxu" faisal dai kallonsa kawai yake, Mikewa yayi yace "Xan koma gida kafin....." Faisal ya katse sa yace "Haba Captain kana jin ance tun safe bata ci komai ba sai kace xaka tafi, ko da milk ne ka siyo a gwada bata mana" Junaid yace "Yea! But I don't want my mum to start calling me, bayan bakin gate kadai nace xan raka ka, do me a favour by buying the milk and bringing it to them, ga Atm card dina" kallonsa kawai faisal ke yi, har ya fiddo card din ya mika masa, can ya girgixa kai yace "Nima yanxu Mumyna xata kira ni" Junaid yace "Ohk then! Let me send the gate keeper!" Daga haka ya nufi gun mai gadi, faisal ya girgixa Kai ya koma parlon, ai tana jin an tura kofa ta mike da sauri, faisal ya rungume hannayensa yace "Poor you!" Komawa tayi a hankali ta xauna. Ya juya ya fita daga parlon wani tausayinta na shigarsa, anya ba asiri bane wannan, ban da haka me yayi mata xafi haka har ya kai ta ga hauka at her young age!" Ko da ya fita har Junaid yayi masa gaba da motarsa, tsaki kawai yayi ya nufi titi don hawa tricycle, ko waye bai son uwarsa???
Washegari Junaid na office ya kira faisal, bayan sun gaisa yace "Plss frnd make arrangement for me ko xuwa gobe ko jibi sai a tafi da ita can din, ta flight" faisal yace "Who's going der with her?" Junaid yace "Yea xan ce ma Mumy an min transfer din sati daya xuwa lag, kaga kafin sati dayan duk xa ayi abubuwan da ya kamata, bari dai xan xo idan na bar gun aiki sai muyi magana" faisal ya tabe baki yace "Ohk," sannan ya katse wayar. El-ameen ne xaune office ya hade kai da table, ya ji an bude kofar office din, dagowa yayi da sauri don ganin waye, sanin ya gaya ma nurses din ya gama attending ma patients for that day, ganin faisal ne ya kalli agogo yaga uku ya gota, faisal ya karaso yace "What's the problem El?" El-ameen ya shafa kansa tare da lumshe ido yace "Bacci!"
*Captain Ahmad Junaid*
_Khaleesat Haiydar_
27.....
Faisal yace "Uhn wai bacci!" Kallonsa kawai El-Ameen yake da lumsassun idonsa, faisal ya xauna kan table yace "Ya aikin?" El-ameen yace "Alhmdllh" faisal yayi murmushi yace "Abokin ka xai tafi da patient din ku Abeokuta soon..." El-ameen ya d'aga kafada yace "Dat's nyc, Allah ya bada sa'a, ita kuma ya bata lafiya," faisal yace "Ameen, and you know what?" El-ameen ya girgixa kai, faisal yace "Ta ki cin komai yarinyar, from all indication, she is missing you" El-ameen ya girgixa kai yace "No! Idan aka takurata kuma aka tsoratata xata ci" faisal yayi shiru, sai kuma yace "Don Allah ku bar wannan childishness din kai da Junaid ku hada kai ku taimaki baiwar Allah, ni banga abun xuciya a nan ba, ga yarinyar 'yar karama da ita...." El-ameen ya hade rai yana kallonsa yace "Look nace banyi kuma, ba gashi xai kaita asibiti ba, don Allah ka bar ni in ji da abinda ke damuna" shiru faisal yayi kafin yace "But ni ina tunanin anya ba asiri aka mata ba, banda haka me xai ja mata brain disorder at her young age...." El-ameen ya girgixa kai yace "Na fa yi diagnosing dinta, brain disorder ne, she's suffering from post-traumatic stress disorder!" Faisal ya d'an bude ido yace "And what's the cause?" El-ameen ya lumshe ido ya bude yace "Serious accident, sudden demise of love one, terrorist incident, a lot of them..." Faisal ya sauke ajiyar xuciya yace "Allah sarki, Allah ubangiji ya bata lafiya" El-ameen yace "Ameen!"
Kusan a tare Junaid ya shigo compound da Suhaima da tayi kamar bata san mota ce bakin gate din ba sai tafiyarta take, ya kusa bugeta da motar ya nufi parking lot abun sa, bude baki tayi bayan tayi tsalle ta bar wajen ta bi motar tasa da kallo, ya fito ya rufe motar ya nufi part din Mumy, tsaki tayi ta shige part din Hajiyarsu tun daga parlor ta dinga kwala mata kira ta fito da sauri, Suhaima tace "Uhn in gaya maki haka maganan take Hajiya, Mahaukaciya Ahmad ya tsinta yanxu haka tana gidan El-ameen ana kula da ita wai, don ma Sumayyar bata san gidan bane da mun je" Hajiya tana tafe hannu baki bude tace "Ikon Allah, mahaukaciya kuma? xan ko je in samu uwar Aminun yanxu ba sai gobe ba" Suhaima tace "Amma fa Hajiya xai ma iya yiwuwa Khadija ta san komai" Hajiya tace "Ae baxa tayi magana ba shegiyar, bari ina zuwa in je gun balki mu san abun yi" dankwali ta dauka ta fice tayi bangaren Umma. Junaid na bude kofar Mumy Humainah dake labe jikin kofar tayi masa k'ara a fuska, turata yayi har sai da ta kusa faduwa ya hade rai yace "baki da hankali ne" kallonsa ta tsaya yi kamar xata yi kuka, ya galla mata harara ya juya ya fita daga parlon, parlon sa ya tafi ya kwanta, duk ya rasa me ke masa dadi, bayan isha yana xaune parlor Fatima ta tace Abba na kiransa, bai tanka ta ba har ta fita sannan ya mike ya fita ya tafi part din Abban, Mumy ce parlon tana yanka masa watermelon sai Umma da ita ma shigowarta kenan, ya xauna kasan rug din tsakar parlon yana kallon Abban nasa yace " Sannu da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa, ya maganar mu ta ranan ban ji ka sake cewa komai ba" Junaid ya d'ago da kyar yana kallonsa, a hankali yace "ina sane Abba..." Abba xai yi magana Umma ta riga sa tana murmushi tace "Toh ko dai har yanxu baka samo mana surkar bace Ahmad" ko kallonta bai yi ba bare ya tanka ta, Mumy dai bata ko kallesu ba tana ta yankar kankanar gabanta, Abba yace "Toh ina sauraranka, don kwanakin da na dibar maka ya kusa" kai kawai Junaid ya iya kada masa ya mike ya fita daga parlon jikin sa a sanyaye, part dinsa ya koma ya kwanta duk jikinsa ba kwari, shi yanxu a ina xai samo mata ana xaune kalau gashi sati daya da 'yan kwanaki kadai ya rage a kwanakin da Abba ya dibar masa, gaba daya daren ranan kasa baccin kirki yayi, ya mike ya dauro alwala ya fito ya hau sallahn nafila a dakin, washegari da safe haka ya shirya cikin rashin kuzari ya tafi gun aiki, da ka gansa kasan akwai damu tattare da shi sosai, after Asr ya nufi gidan El-ameen, driving kawai yake amma gaba daya hankalinsa bai jikinsa ga wani mugun sara masa da kansa yake, ya rasa wanda xai gaya ma damuwarsa a lokacin, da da ne da yanxu ya kira El-ameen ya sanar da shi, yana isa gidan yayi xaman sa cikin mota bai fito ba har bayan kusan rabin awa, can ya fiddo wayarsa yayi dialing number faisal, bugu biyu faisal ya d'aga, Junaid ya lumshe ido yace "Plss faisal ka taho gidan El-ameen if you are less busy" faisal yace "Ohk" katse wayar Junaid yayi, sai ya ji kamar ya kira El-ameen sai ya fasa, yana nan xaune har faisal ya iso layin bayan kusan minti ashirin, Yana gama parking ya fito Junaid ya danna masa horn don ya gane yana cikin motar, faisal ya nufi motar ya bude yana kallonsa yace "Mummy's boy...." Shiru yayi ganin yanayinsa, can ya shiga motar yace "Ya aka yi Captain" Junaid ya lumshe ido ya bude kamar baxai ce komai ba, faisal ya tabe baki yace "Haka fa, ni ba El-ameen ba ina kai ina gaya min, but kiran me ka min?" Junaid yayi murmushi yace "Mu shiga ciki" daga haka ya bude motar ya fita, faisal ma ya fito suka shiga gidan a tare, mama ce xaune parlor ita kuma tana kwance jikinta tana gyara mata gashinta, suka gaida Mama ta amsa da murmushi tana masu sannu da xuwa, Junaid ya xauna idonsa a kan jasmine, haka ma faisal, a hankali ta bude ido tana kallonsu don dama ba bacci take ba, Junaid yace "Ta fara cin abincin mama?" Mama jummai tace "A'a daxu dai na bata kunu ta sha ba laifi, sai dai jikinta da dumi" Junaid bai kuma cewa komai ba, faisal yace "Toh ta sha madarar jiya?" Mama ta girgixa kai tace "A'a" Junaid dai sai kallonta yake, faisal ya mike ya isa gabansu ya duka a hankali ya daura hannunsa kan forehead dinta, tayi wani kara da ya sa shi mikewa da sauri ya koma baya, mama jummai tayi dariya tace "Toh bata sanka ba" faisal yace "Uhun na ga alama" murmushi Junaid yayi ya mike ya nufi kofa, mama tace "Kai dai Ahmad ka iya tafiya ba sallama" juyawa yayi yace "A'a ban tafi ba mama ina waje " mama tace "Toh yaushe Aminu xai dawo, ka ga maganinta ya tsaya yanxu" yace "Xai dawo, amma ba yanxu ba shi yasa ma yanxu nake shirin kai ta asibiti a ci gaba da dubata a can kafin ya dawo" daga haka ya nufi kofa ba tare da ya jira cewarta ba, ta bi sa da ido lkci daya jikinta yayi sanyi jin abinda yace, faisal ya juya ya bi bayansa, hawaye ne ya cika idon mama jummai ta dago jasmine tana kallonta tace "Yanxu raba mu xa ayi?" Junaid na fita balcony ya xauna, faisal ya xauna gefensa yace "Nayi kadan in ji damuwar ka ko Junaid" Junaid ya kallesa yayi murmushi yana girgixa masa kai, bayan kusan minti biyu cikin sanyin murya ya soma gaya ma faisal matsalar da yake ciki, faisal yayi shiru yana kallonsa cike da tausayinsa, can yace "Toh kai yanxu baka da budurwar da ta maka ne" Junaid ya girgixa masa kai yace "I don't have!" faisal ya sauke ajiyar xuciya yana kallonsa, bayan kusan minti daya murya can kasa yace "You know what Capt?" Junaid ya kallesa bai ce komai ba, faisal yace "ka auri yarinyar nan kawae...." Junaid yace "Wacce yarinya?" A hankali faisal yace "Baiwar Allahn nan da kake kokarin ganin an sama ma lafiya, I assure you ba karamin lada xaka samu ba, sannan yarinyar bata yi kama da 'yar kananun mutane ba, ina da yakinin 'yar babban gida ce, you won't regret it frnd....." Kallonsa kawai Junaid yake da mugun mamaki, faisal ya girgixa kai yace "Its for ur good, for her good Capt, yanxu misali kayi aure dole baxa ta ke samun attention gun ka ba as before and ba ko wace mace bace xata yarda da taimakon ta da kake, kaga wannan shine anyi ba ayi ba don gidan jiya yarinyar xata koma, but idan ka daure ka aureta kaga ka rufe bakin parent dinka, ita kuma sai ka ji dadin kula da ita sosai tunda you now have ur freedom har Allah ya bata lafiya, then sai ka sauwake mata idan baka da ra'ayin xama da ita ta tafi ta nemi 'yan uwanta, in ka mata haka ka mata komai na rayuwa, kai kadai ne gatan yarinyar nan Junaid, ka ajiye batun mahaukaciya ce ka aureta, I assure you dat you won't regret helping her...." Katse sa Junaid yyi yace "What the hell are you saying faisal, a haukacen xan gabatar da ita gun su Abba? Sai ince ina danginta da 'yan uwanta suke, kuma kasan dai dole sai na kai ta gida gun Mumy, this is totally out of it...." faisal yace "Uhmm! Toh nemo wani solution din" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Don nayi aure baxai sa in ki ci gaba da taimakonta ba, ni nayi niyyar nema mata lafiya, babu kuma macen da ta isa don na aureta tayi controlling dina, da aurena ko ba aurena I will help her kamar yanda nayi niyya, yanxu dai xuwa gobe nake son gama arrangement din tafiya da ita" faisal ya d'aga kafada yace "Ohk Allah ya shige mana gaba, yanxu mu je in siya drugs ka kawo mata don akwai xaxxabi jikinta"
El-ameen ne kwance dakinsa bayan magrib, Ummi ta shigo dakin tana kallonsa tace "What's ur problem Ahmad, are you ohkay?" Mikewa xaune yayi a hankali yace "Slight headache ne Ummi" tace "Toh ka fito ka ci abinci ka sha magani mana ko kwanciyar ne xai sama maka relieve" daga haka ta juya ta fita tana naxarin maganan da Hajiya fati ta xo mata da shi daxu, wai sun ajiye mace can gidansa shi da Junaid, she trust her son, ta kuma san abinda xai yi da wanda baxai yi ba, ganin condition dinsa tun da ya dawo daga gun aiki yasa bata yi masa magana ba, ta kuma yanke shawarar ba ma sai ta masa ba kawai sawa xata yi aje a gano mata kuma idan har hakan ne ta tanadi abinda xata yi masa don she's a no nonsense ita, bayan minti kusan goma da fitan Ummi dakin Faisal ya xo, yayi mamakin ganin El-ameen din kwance yana bacci, ya tada sa yace "Lafiyarka kuwa El kai da baka bacci da wuri" El-ameen ya kuma lumshe ido yace "ina jin xaxxabi ne ke son kama ni, am not feeling OK" faisal yace "Toh ka sha magani?" Girgixa masa kai El-ameen yayi, faisal yace "Saboda me? patient dinku ma na can ita ma xaxxabin take, na dai siya mata drugs Junaid ya kai mata..." Mikewa xaune El-ameen yayi da sauri yace "Xaxxabi kuma, tun yaushe? Wani drugs din ka siya mata?"
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
28.....
Faisal yace "Normal drugs na xaxxabi mana" El-ameen yace "Ohk, Allah ya bata lafiya" faisal yace "Ameen, idan Allah ya kai mu gobe xa a tafi da ita kudu" El-ameen ya d'aga kafada bai ce komai ba, faisal yace "Kayi wanka ka ci abinci sai ka sha magani xaka fi jin dadin jikin ka," ba musu El-ameen ya mike ya shiga bathroom, faisal na ganin haka ya jawo wayarsa da sauri ya nemo number Junaid, cikin hanxari ya shiga rubuta masa text kamar haka "Ban yi tunanin akwai abinda ya isa ya shiga tsakaninmu da kai har ya hada mu haka ba, all the same Allah ya huci zuciyarmu, ba wai don ka hakura kuma na maka text din nan ba sai don in nuna maka ni babba ne...." Daga haka faisal ya tura text din sai da ya tabbatar ya tafi sannan ya maxa yayi deleting ya mayar da wayar ya ajiye, ko minti goma faisal bai kara a gidan ba yayi gaba. Junaid na xaune parlon Mumy yana cin abinci text din ya shigo wayarsa, yayi mamakin ganin sunan El-ameen, ya bude text din ya karanta content din, murmushi kawai yayi ya ajiye wayar, can ya mike ya dawo parlor ya d'an saci kallon Humainah dake kwance tana danna wayar fatima, karbe wayar yayi yace "Ke baki iya gaisuwa ba ne" mikewa tayi xata wuce daki ya fixgota, ta kusa fadowa kansa, turasa tayi kmr xata yi kuka tace "Ni ka kyaleni," ya matso kusa da ita yace "Anki" ta bata fuska xata yi kuka, yayi murmushi yace "Abinda kika fi iyawa kenan ai" saketa yayi ya fita daga parlon ta bi sa da harara. Karfe takwas saura na dare El-ameen ya fito rike da makullin motarsa xai tafi clinic a bisa umarnin dad dinsa, bin sa da kallo Ummi tayi har ya fita, yana shiga motarsa driver din Abbansa ya karaso kusa da motar, xuge glass yayi yana kallonsa yace "Ya aka yi Umar?" Drivern ya d'an sosa kai yace "Yallabai dama, ji nayi Hajiya xata aika wasu xuwa can gidan ka, ina jin akwai fa binciken da take, xuwa anjima xa su je, nine ma xan kai su wai...." El-ameen ya firfito da ido yace "Gidana kuma, me tace maku xa ku je ku yi?" Umar yace "Wllh ban san me tace masu xa su je yi can ba, ni umarni kawai ta bani in kai su" El-ameen da hankalinsa ya gama tashi yace "Ohk ohk nagode kwarai Umar..." Umar din yace "Amma yallabai ka rufan asiri, naga kai din mutum ne mai kirki shi yasa nace bari in ankarar da kai, in ma da matsala ne sai ka gyara" El-ameen yace "nagode kwarai umar, kar ka ji komai" daga haka ya ja motar ya bar gidan, sai da ya fara tsayawa a atm machine ya cire kudi sannan ya nufi gidansa direct. Yana isa gidan yayi parking waje ya fita ya shiga ciki, murda kofar parlon yayi a hankali ya tura ya shiga, bbu kowa parlon sai Jasmine da plate din potatoe gabanta ta kifar kasa, mikewa tayi jin an bude kofa ta kalli kofar da sauri, ya tsaya ya rungume hannuwansa yana kallonta, a hankali ta shiga tahowa tana kallonsa itama har ta iso gabansa ta tsaya, murmushi ya sakar mata murya can kasa yace "Jewel!" Ita dai kallonsa kawai take, ya matso kusa da ita a hankali ya ja hancinta yace "Did you miss me" taba nasa hancin tayi a hankali ita ma, ya wara manyan idonsa yana 'yar dariya sai ga mama jummai ta sauko daga stairs rike da jakunkuna biyu, ai tana ganin El-ameen tayi still, ya kalleta ya kalli jakar da mamaki, lkci daya murmushin dake dauke fuskarsa ya bace yace "Ina kuma xaki da jaka mama?" Ae sai ta fashe da kuka tace "Yo naji Ahmad na cewa gobe xai kai ta asibiti ta xauna a can, a gida ma ana yi bata warke ba sai wani asibiti can, ku bar ni in je a mata na gargajiya mana tun da ba a dace da na baturen ba, don Allah ni a bar ni da ita xan kula da ita har Allah ya bata lafiyan. Idan ya so sai in baku addreshin kauyena, ku yarda da ni baxan cuce ta ba..." El-ameen kallonta kawai yake da mugun mamaki, yanxu da Allah bai kawo sa ba tafiya da ita kawai xata yi, karasowa parlon yayi yace "Ehh wannan kuma gaskiya ne mama kin kawo shawara me kyau, Amma bari muyi shawara da Junaid din koh" tana matsar kwalla tace "Toh" xaunawa yayi yana kallon Jasmine dake ta binsa kamar xata shige jikinsa, yayi murmushi ya xaunar da ita ya jawo ragowar potatoe din da ta xubar ya dau daya ya kai mata baki, ta bude bakin ya saka mata, kallon Mama jummai dake kallonsu tana 'yar murmushi yyi yace "Mama xaki d'an siyo mata fruits a bakin titi don Allah," tace "Toh" ya fiddo kudi ya mika mata yace "Na dubu xa ki ce a baki" karban kudin tayi ta fita sabe da gyalenta, jasmine ta bi ta da kallo, mikewa yayi ya isa kofa yana lekan ko ta tafi sannan ya juyo ya kusa cin karo da Jasmine da har ta biyosa, murmushi yayi ya isa gun jakunkunan da mama jummai ta sauko da, ya bude yaga wanda ke dauke da kayan Jasmine din, duddubawa yayi ya fiddo da hijab ya sa mata, sannan ya dauki jakunkunan biyu ya rike hannunta suka fita daga gidan ya kulle da key, yana rike da hannunta ya nufi gun mai gadi, yace "Kana ji na Usman, xa mu dan yi tafiya ne amma baxa mu dade ba" ya fiddo kudi aljihunsa ya mika masa yace "Ga kudin ka na wannan watan, yanxu xaka tafi xan kulle gidan ne, sai ka tsaya bakin gate har mama ta dawo ka bata Jakarta da kudin nan ita ma, da xaran mun dawo xan neme ka" Mai gadin da ko kadan bai ji dadi ba yace "Toh shikenan yallabai, Allah ya kiyaye hanya, ya dawo da ku lafiya" El-ameen yace "Ameen, d'an je ka canja min wutan gidan xuwa na gen" ba musu maigadin yaje yayi yanda yace masa gidan ya dawo ba wuta gaba daya, ya dawo shima ya hada nasa kayan, suka fito gaba daya, El-ameen ya kulle gidan yace "Don Allah ka jira har tsohuwar ta dawo ka bata hakkinta da kayanta," mai gadin yace "In'sha Allah yallabai" daga haka El-ameen ya nufi motarsa da ita da sauri yana rike da nata jakar kayan, ya bude front seat yasa ta shiga, ya ajiye jakar kayanta a bayan motar ya rufe, ya xaga ya shiga motar ya tada ya bar wajen, kafin ya isa titi ya ga Mama jummai na ta xabga uban sauri rike da ledan fruits, ta basa tausayi sosai, yasan tsakaninta da Allah take son yarinyar amma cutar dake damunta na asibiti ne ba na gargajiya ba, kuma tun da ta fara tunanin guduwa da ita wataran ko ba yanxu ba sai ta gudu da ita din, may be some other time xa su kuma nemanta, kallon jasmine yayi yaga yanda ta kafa ma glass din motar ido ko kiftawa bata yi tana kallon motoci dake tafiya kan titin kamar me son gano abu, yayi murmushi ya kamo hannunta yace "Jewel" kallonsa tayi da sauri, ya sakar mata murmushi, ta maida dubanta kan titi, sosai yake tausayinta don a yanxu dai bata da gata a duniya sai nasu, murmushi yayi tunawa da yayi axumi uku ya hau kansa fa. Tafiya kawai yake ba tare da yasan takamaiman inda xai kai ta ba ma, duk he's just confuse, yasan ko ya kira Junaid yanxu ma ba fitowa xai yi ba yana can Mumy ta gama basa abinci ta lullubesa yayi bacci, tsaki yayi yana girgixa kai.
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
29....
Parking yayi a gefen titi yana tunanin inda xai kai ta, gidan frnds dinsa masu mata? girgixa kai yayi don yasan ba lallai basu yi thinking negatively ba, Hotel? Ya girgixa kai coz it's not decent, to ina xai kai ta? Dafe kansa yayi cike da confusion, can ya dago ya juya yana kallonta ya ga ita ma shi take kallo, yayi murmushi a hankali yace "Ina xan kai ki jewel?" Dauke kanta tayi ta jinginar jikin glass din motar tana lekan waje, ya tada motar ya kuma hawa kan titi ya dinga driving din kamar bai son yi, cikin mintunan da basu wuce ashirin ba ya iso clinic, yayi parking a wajen da aka tanadar don ajiye mota, kalle kallen haraban hospital din ya dinga yi, ganin patients ne Kawai ya fito, ai tana ganin ya fita ta fasa ihu ita ma xata fito, ya juyo da sauri yace "Wait jewel yanzu xan bude maki" xagawa yayi daya side din ya bude motar ya fito da ita, kalle kalle ta shiga yi, ya rike hannunta ya shiga asibitin da sauri, bai saurari nurses din dake gaida sa ba ya haura sama da ita ya bude office dinsa suka shiga, key ya sa ma kofar sannan ya juya yana kallonta ya sauke ajiyar xuciya yace "We've got a good solution koh" kama hannunta yayi ya nufi bedroom din dake office din ya xaunar da ita kan gado yana kallonta, kwan kwasa office dinsa ya ji ana yi ya mike da sauri ya fita, mikewa tayi ita ma da saurinta ta bi bayansa, ganin ta biyosa yasa bai bude kofar ba yace "Who's there?" Muryar nurse yaji tace "ur attention is needed at the theatre sir" a fusace yace "Toh da ban xo ba fa" shiru tayi yyi tsaki ya kama hannun Jasmine ya maida ta dakin, xaunar da ita ya kuma yi a hankali yace "Look jewel, yanxun nan xan dawo kar ki bi ni plss" ya kusa second goma yana kallonta sannan ya mike a hankali xai fita ita ma ta tashi da sauri, yace "Ohhw ina xan kai ki jewel?" Fita yayi ta bi bayansa, ya isa show glass din dake office din me dauke da magunguna da ruwan allurori ya bude ya dauki wani kwalban allura ya rufe, syringe ya dauka ya juya suka kusa cin karo, yace "Sorry!" kama hannunta yyi suka koma dakin ya sa ta xauna, cikin few minutes ya hada alluran yayi mata a lap, 'yar kara kawai tayi masa tana bata fuska, yayi kasa da murya yace "Sorry jewel!" sun kusa minti goma xaune yana yi yana kallon agogo, yaji an kuma kwankwasa kofa, ya mike da sauri ita ma ta mike sai dai da ganinta kasan duk jikinta ya mutu, rike hannunta yayi ganin yanda take layi ya fito office din yace "Yes!" Muryar Abbansa yaji yace "S'ako na bai iso gare ka bane, ka wani garkame office kana ce min yes" xaro ido yayi yace "Ohh No, kaya nake canzawa ne Abba gani nan xuwa yanxu" Abba bai kuma cewa komai ba, hakan yasa ya kama hannunta suka koma dakin, kwantar da ita yayi ta lumshe ido, ya sauke ajiyar xuciya ya mike ya bude inda kayan shiga theatre dinsa suke, ya cire na jikinsa ya saka sannan ya lullubeta ya fito daga dakin ya rufe da key. Sha biyu saura ya fito daga theatre, yana komawa office ya bude dakin yaga bacci kawai take, toilet din dake nan ya shiga yayi wanka ya fito ya saka kananun kayansa ya fito office ya xauna ya kifa kansa kan table don bacci yake ji, wata nurse ta shigo rike da cup din coffee ta ajiye masa kan table tace "Sir" dagowa yayi yace "Thanks" har ta kai kofa xata fita yace "Nurse Sharifah" juyawa tayi ta dawo tace "Sir?" Yace "Nan sama kike ko k'asa yau?" Tace "a nan nake duty" yace "good, akwai patient a dakina, i want you to stay with her throughout the nyt, mental disorder gareta, in case xata farka cikin dare ki rakata restroom" shiru tayi tana kallonsa tsoro bayyane fuskarta, murmushi yayi yace "She won't hurt you, bata komai, just in case kar ta tashi ne yasa nace ki tsaya da ita" a hankali tace "Ohk sir... Let me explain to..." Katse ta yayi yace "No! Xan je in mata bayani" daga haka ya mike ya fita. Ta lallaba ta isa kofar dakin ta tura a hankali ta leka ta ganta tana bacci cikin bargo, a haka ya dawo office din yace "Ki shiga baxa ta maki komai ba nace" gyada masa kai tayi ta shiga dakin, ya dau coffee dinsa ya sha bayan ya huce sannan ya mike yayi kwanciyarsa kan kujeran dake office din. Can misalin Karfe uku ihunta ya farkar da shi ya mike da sauri ya nufi dakin dai dai lokacin da nurse din ma ta fito da gudu, shiga dakin yayi ya ganta tsaye sai ihu take, ya karasa da sauri ya rike hannunta yace "Jewel!" Tsit tayi tana kallonsa, ya sauke ajiyar xuciya ya xaunar da ita gefen gado, ya juya xai fita ta mike ta bi sa da sauri, nurse din na tsaye bakin kofar fita office har lokacin yace "Taho ki rakata restroom nace babu abinda xata maki" da kyar ta karaso ta shigo dakin, shi ya kaita toilet din, ya juya yana kallon Nurse din ta karaso a hankali ita ma ta shiga toilet din ya juya ya fita. Da asuba yana kwance idonsa lumshe bayan ya dawo daga mosque yaji mutum kusa da shi, bude ido yayi da sauri ya mike xaune yana kallonta, murmushi ya sakar mata yace "Good morning jewel" dagota yayi ya xaunar da ita gefensa, remote ya dauka ya kunna mata tv, wani kallo ta dinga yi ma TVn kamar idonta xai fito, dariya ta basa ya mike ya shiga daki yaga nurse din rakube kasan gado tana bacci, yace "Nurse Sharifa" mikewa tayi da sauri tana murxa ido duk da ganinta kasan a tsorace take, yayi murmushi yace "Kin yi sllh?" Tace "Yes sir" yace "Good" toothbrush da paste dinsa ya dauko ya mika mata yace "Xaki wanke mata baki" ta karba tana kallonsa, ya fito ya dagota taki tashi idonta kyar kan TV ko kiftawan kirki bata yi, dariya ta basa sosai ya kuma dagota ta fasa masa ihu har lokacin bata dauke idonta kan kallon ba, ya dau remote ya kashe tvn, sai a sannan ta juya ta kallesa, yayi murmushi ya dagata ta mike ya shiga daki da ita, kin yarda nurse din ta wanke mata baki tayi, hakan yasa ya wanke mata da kansa, ganin hadiye komai take yasa bai mata amfani da ruwan toilet din ba, ya fita ya dauko table water ya bude ya bata ta sha ya kama hannunta suka fita, ya kalli nurse din yace "Tea xaki je ki hado min plss" ba musu ta fita sai ga ta ta dawo da cup din tea ya karba yace "Thank you, kafin ki tafi ki dawo" tace "Ohk sir" sannan ta fita, jasmine ya shiga ba tean, ta sha kadan taki shan sauran da alama tea bai dameta ba, mikewa yayi ya tafi ya wanke bakinsa toilet, juyawan da xai yi ya ganta tsaye bayansa, murmushi yayi ya kama hannunta suka fito office, ya xaunar da ita sannan ya shanye sauran tea'n, TV ya kunna mata don yana son fita ya gaida Abbansa, ai ko ta nutsu sosai tana kallon mutanen dake yawo a tvn, ya mike a hankali yanda baxata lura ba ya fita ya haura last floor xuwa office din Abbansa, wani aikin Abban nasa yasa sa, ransa bai so ba amma bai yi musu ba ya shiga yi, yana cikin yi aka yi interrupting power, ya xaro ido sanin kila yanxu xata fara ihu, da sauri ya dinga signing files din, cikin minti sha biyar ya gama ya fice, ya sauka xuwa office dinsa, yana budewa yaga wayam daki ya nufa ya tura nan ma wayam, ya xaro ido ya shiga toilet nan ma bbu ita, wani mugun tashi hankalinsa yayi ya fito da sauri ya dinga dube dube ya sauko har downstairs yana kallon nurses din yace "wata patient bata sauko ba yanxu" bai jira cewarsu ba ya fita haraban asibitin da sauri, ya dinga dube dube bai ganta ba, gun masu gadi ya nufa da sauri ya tambayesu suka ce basu ga kowa ba, komawa reception yayi ya dinga yi ma nurses din masifa basu ga wata ta sauko ba yanxun nan, nan suka shiga dube dube su ma cikin ward,haka aka yi ta nemanta cikin asibitin har da likitoci da cleaners, wasu na tunanin anya kuwa Dr El-ameen dai dai kansa yake ganin yanda ya wani rikice nurse Sharifa ma duk hankalinta ya tashi barin da tasan ba mai hankali bace patient din, har Abba sai da ya sauko jin wai ana neman patient daga bakin wani likita, kallon d'an nasa kawai yake yana son sanin wace patient ce wannan wanda shi kadai yasan da ita a asibitin, Salatin da Dr Ibrahim wanda office dinsa ke kallon na El-ameen yayi ya ja hankalin nurses da wasu likitocin, da hanxari duk aka karasa wajen aka gansa tsaye bakin office din yana kallon ciki da mamaki, El-ameen ya karasa shima yana kallon office din, tsaye take a office din duk tayi kaca kaca da uban files din dake kan table dinsa, ta bude show glass duk ta watsar da magunguna da allurorin dake ciki, El-ameen ya d'an saci kallon Abbansa da ya rungume hannu yana kallon ikon Allah, daga likitocin har nurses din kallonta suke su kalli El-ameen, hakan ya bata tsoro sosai ganin yanda aka taru bakin kofar ana kallonta, ta fasa wani shegen ihu da karfi tana kallon El-ameen, sunkuyar da kansa yayi, ta dinga ihu can ta tafi bayan glass da gudu ta labe har lokacin ihu take, da kyar ya dago kai yana kallon Abbansa yace "Abba... Brain disorder gareta, I..I... She's under medication ne Abba, jiya da xan xo na taho da ita..." Wani mugun kallo Abba ke masa yace "Asibitina yayi kama da na mahaukata?" Sosa kai yayi xai yi magana Abba ya masa wani uban tsawa yace "Uwar ka xaka gaya min, wasu mahaukatan iyayen ne suka baka 'yar su ka sata under medication har kake yawo da ita?" Ya lumshe ido ya bude a hankali yace "No, A gida nake mata treatment din Abba, dama...dama akwai injection da nake mata da daddare ne to kuma ka kirani clinic shi yasa na taho da ita... Yanxu ma xan maida ta gidansu..." Abba yace "Amma arnaye ne iyayenta koh?" Shiru yayi bai ce komai ba, Strictly Abba yace "Ka maida masu 'yar su ka basu shawaran su kai ta asibiti, na kuma hanaka aikin nan daga yau, in ma kana son concentrating a field dinka na neurology ne yanxu you can go and apply for work a psychiatry ba ka dinga yawo da mahaukata ba har kana kawo min su asibiti suna min barna" daga haka Abba ya juya ya bar wajen, nurses din ma duk suka juya, jiki a sanyaye El-ameen ya karasa cikin office din ya kamo hannunta suka fita, sai wani shisshigewa jikinsa take a tsorace, likitocin dake gun suka bi sa da kallo, hijab dinta ya sa mata suka fita xuwa gun motarsa yasa ta shiga ya tada mota yyi warming ya bar haraban hospital din. Hotel ya nufa da ita don dat was the only option a lokacin, yana parking a haraban hotel din kiran Junaid ya shigo wayarsa, yayi mamakin ganin kiran don yasan bai xuwa can gidan da safe bare ace yaje ne ya gani a rufe, ya kalli agogo yaga bakwai da wani abu, daga kiran yayi daga daya bangaren Junaid yace "I saw ur text jiya, kuma I hail you da ka nuna kai babba ne" El-ameen yace "what's he talking about" Junaid yace "Really! There's no need of pretending, kana ina yanxu" El-ameen ya kalli inda yake sannan ya gaya masa, Junaid yace "Me kake a hotel" El-ameen yayi shiru sannan yace "Why are you even asking?" Junaid yace "Magana xa muyi, shud I come over..." El-ameen yace "aikin fa?" Junaid yace "Na dau hutun sati daya..." El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "Good! Taho ka same ni yanxu" daga haka ya katse wayar, junaid ya sauke ajiyar xuciya ya dafe kansa don maganar da faisal yayi masa jiya ya tsaya masa, so yake yaji mai El-ameen xai ce game da shawaran faisal, in har shima ya basa go ahead xai jaraba ya ga ko me yiwuwa ne.
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
30.....
Bude motar El-ameen yayi ya fito ya xaga ya fiddota yana rike da hannunta suka shiga reception din hotel din, babu wanda xai ganta yace mahaukaciya ce, xa a fi tunanin daga kauye ta fito duba da yanda take kalle kalle kamar idonta xai fito, tana kuma shisshige sa, daki yyi masu book aka basa makulli ya haura sama yana rike da hannunta, xaunar da ita yayi a dakin yana kallonta, tausayinta kawai yake a hankali yace "Allah ya baki lafiya jewel" ta dawo kusa da shi tana kallonsa, wayarsa ne ya soma ring ya dauka ganin Junaid ne ya d'aga ya gaya masa numbern room din da yake, cikin few minutes Junaid ya iso dakin ya murda kofa ya shigo, tsayawa yayi daga bakin kofa yana kallonsu da mamaki, El-ameen ya mike ya d'aga kafada yace "Ummi ta kusa gano abinda muke, so I had to take her away daga gidana" Junaid ya xaro ido yace "Da gaske?" El-ameen ya koma ya xauna yace "nafi tunanin gulma aka kai mata, nd I suspect that khadija" junaid ya girgixa kai yace "No! Khadija baxa taba exposing dinmu ba, kila dai kanwarka ce sumayya..." Kallonsa El-ameen ya tsaya yi yace "Sumayya kuma? Ae bata san komai ba" tabe baki Junaid yayi ya karaso dakin yana kallon Jasmine da ita ma idonta ke kansa, ya juya ya kalli El-ameen yace "Nan ku ka kwana kenan" El-ameen ya girgixa kai yace "Clinic, nd you know what sai da ta tona min asiri ta sa Abba ya ganta and he wasn't happy" Junaid bai ce komai ba ya xauna gefen gadon dakin, ta mike a hankali ta dawo kusa da shi ta tsaya tana kallonsa, ya d'an bude ido yana kallonta shima yace "Good morning!" El-ameen da ke kallonsu ya dauke kai yace "I heard you are taking her to Ogun state" Junaid yace "Yea but na canxa plan yanxu" El-ameen ya kallesa yace "To Which?" Junaid ya rufe ido na kusan second ashirin sannan ya bude a hankali yace "Faisal ya bani shawaran in aureta kawae, you know gidanmu an takura in fito da mata nan da few weeks, but kaga frnd ban san yarinyar nan ba, ban san daga inda ta fito ba, ban san meye sanadin haukatan ta ba, infact ban ma san ko matar aure bace, kana ganin shawaran faisal yayi, ya bani good reasons da yasa yace in aureta but am not even sure it will be possible ba lallai 'yan gidanmu su yarda ba" tunda ya fara magana El-ameen ke kallonsa ko kiftawa bai yi, Junaid ya kallesa jin bai ce komai ba yace "You are quite" El-ameen yayi saurin lumshe ido tara da yin wani murmushin da xa a iya kiransa da na karfin hali yace "Yea shawara ce mai kyau, may be xa a fi samun nutsuwa gun nema mata lafiya babu fargaba...." A hankali Junaid yace "Toh how xan kai ta gida a matsayin warce xan aura a haukace, kuma sai in ce ina iyayenta?" El-ameen yace "Ai tana da nutsuwa, shiryata kawai xa ayi ka hada ta da budurwa kamarta irin ace kawarta din nan ku je tare, bai fi kuyi xaman ten minutes ba ku fito just dat ka tabbatar kana kusa da ita kar ka bar wajen, matsalar da xa a samu a nan shine baxata yi magana ba but wannan ba komai bane Kawar sai tayi mata xa ayi tunanin kunya ne da ita, kuma ai gun Mumy kadai xaka kaita komai xai xo da sauki, iyaye kuma ba matsala bane xa mu san yanda xa muyi...." shiru El-ameen yayi xuciyarsa na bugawa ya rasa dalili, Junaid yace "Uhunn will this be possible kuwa?" El-ameen ya kallesa ya dan yi murmushi yace "idan Allah ya yarda" junaid ya lumshe ido yace "Toh Allah ya sa, idan Allah ya bata lafiya sai in sauwake mata ta nemi 'yan uwanta" kallonsa El-ameen yayi da sauri sai dai bai ce komai ba, Junaid yace "Toh ita mama dake kula da ita ina ka kaita?" El-ameen yace "Na sallameta" Junaid ya kallesa da sauri yace "ohh Why?" El-ameen yace "I had to, don Ummi ta tura a duba gidan" junaid ya girgixa kai yace "Toh yanxu ya za ayi da ita a nan?" El-ameen yace "I don't know" Junaid yace "Ka kira wannan nurse din na ranan mana" ba musu El-ameen ya fiddo wayarsa bayan sun gaisa ya gaya mata dalilin da ya kirata ya kuma gaya mata inda xata samesa, kafin awa daya ta iso gun, El-ameen yace "Ga kayanta nan xaki shiryata, you will be staying with her na 2 dayz plss..." Nurse din tace "But sir ina da duty a asibiti da daddare" kallon junaid El-Ameen yayi, jin bai ce komai ba yace "Ohk xa mu san yanda xa ayi xuwa ltr" Daga haka ya mike yace ma junaid xai tafi gida, Junaid yace "But am also leaving" kudi ya ciro a aljihunsa ya mika ma nurse din yace "Gashi ki siya maku abinda xa ku ci kar ki kuma bar ta ita kadai a daki" shi dai El-ameen fita kawai yayi, junaid ya bi bayansa, tana ganin haka ta mike da sauri xata bi su a rikice amma tuni suka rufe kofar, nurse din ta kamo hannunta sanin bata komai ta ja ta suka koma dakin. Umma ce xaune tare da Hajiya a parlon hajiyar, da ganinsu kasan abun duniya ya dame su, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah shi kyauta, amma ita suhaima don uwarta bata tabbatar da abu ba xata xo ta fadi yanxu da ta xo gidan nan ya xa muyi, ga shi matar nan ba mutunci ne da ita ba, mu dai Allah bai yiwo mu masu sa'a ba kila" Hajiya tace "Ae ni naji dadi da abun ya tsaya iya waya balki, sai kin ji maganganun da ta gayan wllh, wai in cire ido kan d'anta, maganganu dai bbu dadin ji, sai dai ban to fa ba don mu muka ja ma kanmu, uhum Allah shi kyauta dai, duk Suhaima ce ta ja mana" Umma tace "Xai kuma iya yiwuwa fa kawai rufa ma d'an nata da junaid din asiri tayi, wannan tattaccen d'an nata, kinsan kuma fa bakinsu daya da Amina" Hajiya tace "Ni wllh duk abun ya ishe ni, duk inda muka billo ba nasara wannan wace irin fitina ce, gashi ni gabana kullum cikin faduwa yake kar yace tsinannar Humainan nan yake so, kai ni na tabbata ma ita uwar xata ce ya fito da, kinga fa 'yan kwanaki suka rage wllh duk hankalina a tashe yake" Umma tayi tagumi tace "ga dukkan alama uwar nan tasa ba a xaune take ba ita ma abinda muke shi take yi, baki ga yau tun safe ta fita ba, ita da bata xuwa ko ina" Umma tace "Toh ke sai yau kika sani, ni ai tun ba yau ba nasan ita ma a tsaye take, bar ganinta haka green snake under the green grass ce wllh, amma dai akwai wani plan din da nake ta shiryawa a raina sai dai wllh ni kaina tsoronsa nake, amma hakan kadai shine mafita ba boka ba malam cikin kwanciyar hankali, sae dai kuma plan din na bukatan hadin kan mu ne, bbu bakin ciki ko nuna banbanci bare kyashi in suhaiman inma muhibbar" Hajiya tace "Haba balki, Ae mun xama daya wllh kawai gaya min wani plan ne wannan" shigowar motar junaid suka ji ko wannen su tayi shiru tana tabe baki, Umma tayi kwafa tace "ka kusa shigowa hannu yaro" Junaid na gama parking ya shiga part din Mumy, bbu kowa parlorn jin ana soye soye kitchen ya nufi kitchen din, Humainah ce kitchen din tana suyan nama, tana ganinsa ta hade rai ta dauke kai ta ci gaba da abinda take, karasowa kitchen din yayi ya rungume hannayensa yace "Fitsara kika koyo gidan Ayshan kenan?" Daure fuska tayi sosai ta kashe gas din ta rufe naman da ta soya ta juya xata fita ya fixgota ta fado jikinsa, 'yar kara tayi ya Rungumeta yana kallonta, tuni jikinta ya dau rawa ta fara turasa tana cewa "Meye haka ya Ahmad ka sake ni..." D'ago kanta yayi ta kasa kallon fuskarsa sai kokarin kwace kanta take, yayi murmushi murya can kasa yace "Ba fitsara ba!" Ta girgixa kai da sauri ba tare da ta bari sun hada ido ba tace "don Allah kayi hakuri ban gane kai bane, baxan kara ba" Muryar fatima da ya ji yasa ya saketa da sauri, ko second uku bata kara ba ta fice daga kitchen din tana tuntube, juyawa yayi shi ma ya fita yana mamakin hakan da yayi don bai taba shigen haka ba, mumynsa kadai yake runguma a rayuwarsa. Karfe hudu da wani abu yana kwance part dinsa kiran El-ameen ya shigo wayarsa, ya d'aga daga daya bangaren El-Ameen yace "ka dai ji abinda nurse din nan tace daxu, kuma baka kira kace ga yanda xa ayi ba, kai fa matsala gare ka" junaid ya d'an yi shiru sai kuma yace "Wllh ban san yanda xan ce xa ayi ba friend, baxai yiwu ka kaita ko gidan frnds dinka masu mata ba?" El-ameen yace "Kai ma ai naga kana da frnds din masu mata, ka kai ta mana" daga haka ya katse wayar, junaid ya tabe baki ya ajiye wayarsa ya koma ya kwanta, wata old time frnd El-ameen ya kira don xuwa tayi spend din daren da Jasmine ganin time na wucewa. Khadija ce kwance parlonsu misalin takwas da rabi ta fara bacci, Muhibba dake parlon ita ma xaune ta buge kafarta tace "Baxa ki kai ma ya Ahmad ruwan lipton dinsa ba ne wai kina neman kiyi bacci" kallonta khadija tayi tana murxa ido tace "Lipton kuma, a gun Mumy yake sha ai" Muhibba tace "Amma daxu ya aiko Humainah wai ki dafa masa ki kai masa, ohh bakya parlon ashe" mikewa khadija tayi tace "Da gaske" Muhibba ta tabe baki ta ci gaba da kallo abunta tace "A'a karya" Hajiya dai abincin gabanta take ci amma duk hankalinta na Kansu haka ma Suhaimah dake parlon, Hajiya tace "Shegiya da nice na tashe ki yanxu ki dafa min Lipton da baxa kiyi ba, amma da yake Ahmad ne, wato uban da ya haife ki ai kin tashi..." Turo baki tayi ta mike ta nufi kitchen, Muhibba ta kalli Hajiya, Hajiya tayi murmushi ta ci gaba da cin abincinta, khadija na shiga kitchen din ta shiga dafa masa ruwan Lipton da kayan kamshi sosai kamar dai yanda yake so, Hajiya ce ta kwalo mata kira ta fito, Hajiya tace "Tafi ki dauko min wayata a sama" tana haurawa sama Hajiya ta kalli Suhaima tace "tashi..." Da gudu Suhaima ta nufi kitchen din ba a dau lokaci ba ta fito da sauri tayi xamanta, dai dai lokacin da Khadija ta sauko ta mika ma uwarta wayar ta nufi kitchen, cikin few minutes ta fito rike da mug mai murfi ta fice daga parlon duk suka bi ta da kallo. Junaid na xaune parlor yana kallon kwallo sai dai duk sonsa da kwallo ranan baya masa dadi, gaba daya tunanin yanda xai fara kawo jasmine gun mumy ran lahadi kamar yanda El-Ameen ya basa shawara yake, kwankwasa kofa aka yi ya juya da sauri lokaci daya khadija ta bude ta shigo da sallama tace "Gashi yaya" kallonta ya tsaya yi kafin yace "What's that?" Tace "Lipton mana, wai Humainah tace kace in dafa maka" ya d'an bude ido bai dai ce komai ba, ta karaso ta ajiye masa ta juya ta fice, bude mug din yyi ya lumshe ido ganin Lipton din yanda yake so, dama can ita ke masa Mumy ta hana wai bata son yana cin duk abinda xai fito daga side dinsu, rufewa yayi ya ci gaba da kallonsa.
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
31.....
Kallon agogo junaid yayi yaga tara ya kusa, ya jawo wayarsa ya shiga kiran El-ameen don ya ji ko ya samu inda xai kai ta, har ya gama ring bai d'aga ba, mikewa yayi ya dau mug din Lipton din ya shiga daki ya xauna gefen gado ya bude ya shiga sip dinsa a hankali, kusan rabi ya sha ya rufe ya ajiye sannan ya mike ya shiga bayi don yin wanka, da kyar ya iya fitowa daga bathroom jin kansa na wani irin juya masa, ya xauna gefen gado sanye da bathrobe, shi kansa baxai ce ga abinda ke damunsa a lokacin ba, kwanciya yyi yayi rub da ciki, a haka ya ji an bude kofar parlor aka karaso har bedroom, kasa dagowa yayi yaga ko waye jin wani axababben ciwo da cikinsa ke masa, tsaye Muhibba tayi bakin kofar tana kallonsa, tuni kamshin turarenta ya gauraye dakin, ya juyo da kyar yana ganinta dishi dishi, rufe kofar tayi ta karaso cikin dakin ta xauna gefensa cike da kissa tace "Ya Ahmad dama Abba ne yace ka ban dubu biyar xan yi amfani da shi" mikewa xaune yayi don ta muryarta ya gane ko wacece ya rike kansa duk da yanayinsa hakan bai hanasa hade rai ba yace "How dare you xaki shigo min daki?" Mikewa tayi ta nufi kofa irin ta ga ko xae tsayar da ita, har ta isa bakin kofar bata ji yace komai ba sai komawa da yayi ya kwanta ya runtse ido, cije lebe tayi ta kuma dawowa ta hau kan gadon da damuwa kamar gaske ta dafa sa da duk hannunta biyu tace "Wai baka da lafiya ne ya Ahmad" ai bai san lokacin da ya fixgota ba ta fado kansa ya kankameta, wani murmushi tayi tana kallon kyakkyawan fuskarsa don har lokacin idonsa rufe suke, ta dake tace "Meye haka ya Ahmad, ka kyaleni" ko kadan bai jin abinda take cewa ba, lkci daya ya koma kamar mara hankali, wani farin ciki ya rufeta ba kadan ba ta sakar masa jiki, cikin mintuna kadan yanayinsa ya bata tsoro, tun tana daurewa har dai tsoron ya fara bayyana, gashi ba rikon wasa yayi mata ba, turasa ta fara yi a tsorace daga karshe tana neman kwace kanta duk da ba haka suka yi da su Umma ba, amma ta gama tsorata da shi gaba daya, kin saketa yyi ta saka kuka tace "Don Allah ya Ahmad kayi hakuri ina rokon ka" ko sanin abinda take cewa bai yi ba, ihu ta fasa a rikice tana turasa tana kwala ma Umma kira amma ya ki saketa, bude kofar dakin da aka yi lokaci daya da karan tarwatsewan bowl me dauke da fruit salad ne ya sa shi sakinta da sauri, ta ja bargo ta rufe jikinta tana kuka jikinta na rawa, shi ko dama bathrobe na jikinsa, kallonsu Humainah ta tsaya yi a bakin kofa jiki a sanyaye, ya sauko da kafafuwansa kasa ya rike kai xuciyarsa na bugawa ya dinga nanata innalillahi... A xuciyarsa, Muhibba ma ta xamo daga kan gadon tana kuka har lkcin ta jawo hijab dinta ta sa ta fice da sauri sai ka rantse ba ita ta kawo kanta ba ganin yanda take kukan jiki na rawa, da kyar Humainah ta juya xata bar dakin ya dago kai yayi kafin halin kiranta, amma ko juyowa bata yi ba ta fice da sauri, sake rike kansa yayi ya runtse ido duk ya kasa tuna yanda abun ya faru, mikewa yayi yana jin jiri ya shiga bayi, ya kusa awa daya bayin sannan ya fito ya fada kan gado lokaci daya bacci ya daukesa. Muhibba kuwa tana komawa part din uwarta ta gansu duk xaune suna jiran dawowarta, Hajiya ta mike da sauri tana kare mata kallo tace "Ya naga kin fito da wuri, ko dai bai sha ba" ta bata fuska tana goge guntun hawayen idonta tace "Ya sha mana, ni dai tsoro nake ji wllh" Umma da Hajiya suka yo waje da ido suka hada baki wajen cewa "Me? Kina nufin bai maki komai ba??" ta fashe da kuka tace "Ni Allah tsoronsa naji Umma, ni dai baxan iya ba a tura suhaima" Umma tayo kanta a fusace tace "Nashiga uku ni balki, Allah wadaran ki yar iska kawai, tsoron uban me, innalillahi... Shikenan ta bata plan din" Hajiya da idonta ya kankance don bacin rai tace "Ni nasan a rina dama kawai nayi shiru ne, da Suhaima ce ko dar baxa ta ji ba kika ce mu tura debabbar yar nan taki gashi ta rusa mana budget, wannan wace irin fitina ce" Umma ta kwalo ma suhaima kira tace "Maxa ke ki je..." Muhibba tace "Humainah fa ta shigo ta ganmu!" Juyawa suka yi da sauri Suna kallonta, Hajiya ta xaro ido tace "Allah?" Muhibba ta tabe baki tayi hanyar daki, Umma ta jabe kan kujera ta dafe kai tace "Allah ya tsine ma tsiya!" Tsaki Hajiya tayi ta fice daga part din kamar xata tashi sama. Ray din rana ne ya farkar da Junaid da safe, ya mike xaune da sauri yana kallon agogo yaga bakwai da kusan rabi, xaro ido yayi lokaci daya abinda ya faru jiya da daddare ya dawo masa gabansa ya fadi, kalle kallen dakin ya shiga yi yana tunanin what just came over him jiya, rike kansa dake sara masa yayi, ya mike tsaye da kyar ya shiga toilet, wanke baki yayi, yayi wanka snn ya dauro alwala ya fito, ya jima xaune kan pray mat bayan ya idar da sllh daga bisanni ya mike ya isa bakin kofa ya tattara pieces din bowl din jiya da Humainah ta fasa bakin kofar ya gyara wajen ya goge ya fitar da mug din Lipton din ma. Parlor ya fito ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido. Ganin har Karfe tara ya kusa ya sa ya mike a sanyaye ya fita ya nufi part din Mumy, kasa shiga parlon Mumy yayi don bai san da wani ido xai kalli Humainah ba, da kyar ya tura kofar daga karshe ya shiga, bbu kowa parlon sai kamshi me dadi dake tashi, ya karasa ciki jiki ba kwari ya xauna, Mumy ce ta fito daga daki tana kallonsa tace "Sai yanxu ka tashi?" Kasa kallonta yayi ga wani faduwa da gabansa yake don gani yake kamar Humainah ta gaya mata, ya dukar da kai ya gaisheta, tace "Meye haka kake kamar munafuki" dagowa yayi da sauri ya kalleta yace "A'a kaina ke min ciwo Mumy" tace "Toh ga breakfast dinka can a dinning sai ka sha magani idan ka gama" mikewa yayi ya tafi dinning din ta bi sa da kallo, tabe baki tayi ta koma daki, tea kawai ya iya sha sai dube duben inda xai ga Humainah yake, mikewa yayi daga karshe ya tafi dakinsu, kwance ya sameta ita kadai fatima kuma ta tafi boko, mikewa xaune tayi ganinsa ya rufe kofar dakin tana ganin haka ta fashe da kuka tace "Ni wllh ka fita kar in kira maka Mumy" tsayawa yayi yana kallonta, tana share fuskarta tace "Ni dai ka fita" ganin ya nufota tsoro ya kamata ta fasa ihu tana kiran Mumy, still yayi yana kallonta, Mumy ta bude kofar dakin tana kallon ciki da mamaki tace "Meye haka?" Ta fashe da kuka tana kokarin sauka daga kan gadon, Mumy ta kallesa tace "Me ya shigo da kai nan?" Rasa abun cewa yayi ya fara kame kame, can yace "Ni ban san..." Wani tsawa Mumy tayi masa tace "Get out!" Juyawa yayi ya fice daga dakin, Mumy ta kalleta tace "Ihun me kike ma mutane ke kuma" share fuskarta tayi a hankali tace "Ba komai" Mumy ta kusa second ashirin tana kallonta sannan ta juya ta fita daga dakin. Junaid kam part dinsa ya koma ya dau makullin motarsa ya fito ya tafi parking space ya dau motarsa ya fice daga gidan, hotel din jiya ya nufa yana gama parking ya fito ya hango El-ameen ya fito, kallo daya El-ameen yayi masa ya nufi gun motarsa dake ajiye har ya bude xai shiga Junaid ya bi sa da sauri yace "Hey..." Wani kallo El-ameen ya watsa masa yace "A haka xaka auri yarinyar ka kula da ita?" Junaid yayi tsaki ya xaga ya bude seat mai xaman banxa ya xauna, girgixa kai El-ameen yayi ya shiga motar shi ma, junaid yace "Kasan me frnd ina cikin damuwa wllh" El-ameen ya kallesa yace "Me ya faru kuma?" Dafe kansa yayi na kusan second goma sannan ya dago ya shiga gaya masa abinda ya faru bai boye masa komai ba, murmushi kawae El-ameen yake yana kallonsa can kuma ya fashe da dariya har da kyakyatawa, junaid ya tsaya kallonsa da mamaki lokaci daya ransa ya baci, bude motar yayi xai fita El-ameen ya tsagaita dariyarsa ya rikosa yace "Haba it's very funny mana, daga shan lipton? Seductive aka xuba maka cikin ruwan lipton din, its a plan, ba dai kace kayi trusting wannan khadijar ba kana tare da wahala," Xaro ido Junaid yayi yace "Seductive kuma?" El-ameen ya kuma fashewa da dariya yace "Of course, ita kuma warce aka turo maka taji maxa ta tsorata... Ohhh my God! Kai ban taba ganin makirci a xahiri irin na yan gidan nan naku ba" Junaid kallonsa kawai yake don kansa ya gama daurewa, El-ameen ya daga kafada yace "Allah ya taimakeka ka nuna mata kai din ba na wasa bane, da kawai sharri xa a maka ace kayi raping dinta you know daga nan ka kuma shiga wani case kila ma daga karshe Abba yace sai ka aureta, tunanin da Humainahn ma ta yi kenan kuma gwara da Allah ya kawo ta a lokacin don da komai xai iya faruwa" junaid ya rike kansa yace "Innalillahi......" El-ameen ya tabe baki yace "Allah ya kyauta! Ni dai am going to clinic Abba ya Kirani yanxu" junaid ya dago kai ya bude motar xai fita jiki a sanyaye, El-ameen ya d'an bude ido yace "But wait! ina xa ka yanxu? Uhn.... kar kuma pills din bai gama sakin ka ba kaje ka afka ma....." Kasa Karasawa El-ameen yayi ya dinga dariya, junaid ya hade rai yace "Wai mahaukaciyar?" Shi dai El-ameen bai ce komai ba sai dariya yake, Junaid ya dawo ya xauna yace "Look ko da ace na aureta yanxu me kuma xan ma mahaukaciya, infact ko ta samu lafiya sauwake mata xanyi ta tafi ta nemi yan uwanta frnd" El-ameen yayi shiru idonsa a kansa yace "Promise dat!" Shiru Junaid yayi shima yana kallonsa can yace "Promise what?" El-ameen yace "That tana samun lafiya xaka sauwake mata kuma baxa ka taba 'yar mutane ba" junaid bai ce komai ba can ya tabe baki yace "Do i need to, ba dai ni nayi niyyar yin hakan ba, ohk I promise" A hankali El-ameen yace "Kuma alkawari dai kaya ne" junaid ya masa wani kallo yace "Na fi ka sanin wannan" El-ameen yace "Good, yau Thursday sai ka fara shirye shiryen kai ta gidan ku on Sunday, I promise xan yi iya kan kokarina in ga everything goes smoothly" Junaid yace "But ni ban san wanda xai mata shiri me kyau ba irin na xamani" El-ameen yace "Ba sai kayi hiring a xo har hotel a mata ba" junaid yace "Ohk" bude motar junaid yayi ya fita ya nufi cikin hotel din El-ameen ya bi sa da kallo.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
32....
Yau ya kasance Saturday Junaid na xaune tare da El-ameen sai Jasmine da ake ma gyaran gashi cikin hotel room din, nurse din da ke kula da ita ma na xaune dakin, kyar El-ameen ya kafeta da ido yana kallon yanda kwararriyar hairdresser din ke mata gyaran dogon gashinta, da ta yi motsi xai xaro mata ido hakan yasa ta nutsu sosai duk da taki tsaida kan gu daya sai bin ta matar take, da ganinta kasan bata so, tsoron El-ameen dake gabanta yasa bata nuna hakan ba, shi kam Junaid wayarsa kawai yake dannawa, har bayan kusan minti talatin matar ta gama mata gyaran gashin, nurse din sai murmushi take tana kallon yanda gashin ke sheki ga tsayi, ita kanta hairdresser din sai kallon jasmine take da sha'awa bata taba kawowa mahaukaciya bace an dai ce mata bata da lafiya, El-ameen ya warce wayar hannun Junaid ganin bai ma san an gama ba, Junaid ya kallesa da sauri yace "What?" El-ameen yace "Your I don't care attitude xai kai ka ga halaka fa" Junaid ya hade rai yace "Shi gyaran gashin xan tsaya kallo kamar yanda ka ke kallo ko me?" Tsaki yayi ya mike yana kallon hairdresser din ya fiddo dubu biyar aljihunsa ya mika mata yace "Thanks madam" ta karba da hannu biyu tana murmushi tace "Baxa a mata kunshi ba?" Ya juya ya kalli El-ameen, El-ameen ya kauda kansa, d'aga kafada yayi yace "A'a no need" matar tayi masu sallama ta fita daga dakin da jakar kayan aikinta. Sai a sannan Junaid ya kalli kan jasmine dake xaune har lokacin bata tashi ba sbda El-ameen, kauda kai yayi ya koma ya xauna yana kallon El-ameen yace "Look frnd ni ban san da warce xan hada ta mu tafi ba fa gobe... Am confuse" El-ameen yace "Kai baka san da warce xaka hada ta ba sai ni?" Tsaki Junaid yayi yace "Ni matsalata da kai kenan, cikin nurses din clinic din ku babu sa'arta??" El-ameen yace "Babu!" Kallonsa kawai Junaid yake, El-ameen yace "Ba na ga kwanaki ka tsaya kula wata yarinya a mall ba har da karban numberta, just call her ka nemi favour wajenta, naga wayayya ce" Junaid yayi shiru yana kallonsa lokaci daya yana son tuno sunanta, can yace "Koh?" El-ameen ya d'aga kafada, Junaid yace "But ni ban taba kiranta ba fa, sai in ce mata me?" El-ameen yace "Ka fini sanin me xaka ce" Junaid ya dau wayarsa yana son tuna sunan da ya sa mata, can sunan ya fado masa yace "Yes Hafsat I think" numberta ya duba yayi dailing, bugu uku ta d'aga ya kalli El-ameen sannan ya mata sallama, amsawa tayi daga daya bangaren, yace "Hafsat?" Tace "yea" ya d'an shafa kansa yace "Ahmad Junaid, wanda kika ara ma motar ki kwanaki" tace "Ohk kwana biyu?" Yace "Alhmdllh, kina gida ne?" Tace "No ina school," yace "Which?" Tace "Al-qalam..." Yace "Alryt xan xo in same ki later, I will cal you idan na xo" tace "Ohk.." Sallama yayi mata ya katse wayar, El-ameen ya tabe baki ya mike ya karasa kusa da jasmine ya dagota sanin saboda shi ne taki tashi, ae da sauri ta mike ya dawo da ita kusa da su, ya dauki ragowar Irish dinta ya ajiye mata gabanta. Da yamma El-ameen na office Junaid ya xo ya samesa, ya ja kujera yace "Na je na sameta, i've explain everything to her and tace babu damuwa, gobe around Eleven xa mu tafi saboda sai ta fara xuwa makaranta" El-ameen ya tabe baki yace "Ohk" Junaid yace "I prefer ta sa hijab then veil" El-ameen yace "Ohk, sai ka je kasuwa ka siyo mata sabo har kasa milk colour tunda kalan gold ne kayan" Junaid yace "Ka raka ni mana..." El-ameen yace "as you can see am busy, idan tsoron mutanen kasuwan kake sai ka ba nurse din dake wajenta kudi taje ta siyo kai sai ka tsaya da ita kafin nurse din ta dawo" Junaid ya mike yace "Ohk" sannan ya juya ya fita, bin sa da kallo El-ameen yayi yana girgixa kai, can yayi murmushi ya ci gaba da abinda yake. Washegari lahadi junaid ya rasa me ke masa dadi, bai san yanda Mumy xata dauki jasmine a matsayin warce yake shirin aure ba idan aka gano bata da hankali, Karfe takwas da wani abu ya shigo parlon Mumy, Humainah ce ke ta goge goge a parlon, tana ganinsa tayi hanyar daki ya bi ta da kallo, tun daga incident din ranan take avoiding dinsa, dakin Mumy ya tafi ya sameta tana gyaran dakin, ya gaidata ta amsa tare da cewa "Jiya Karfe nawa ka dawo gidan nan?" Ya shafa kansa yace "Tara saura, naga kamar kin yi bacci ne shi yasa ban shigo ba" bata ce komai ba ya juya kamar munafuki ya fita, a tsatstsaye yayi breakfast ya fita xuwa gaida Abbansa, Hajiya ce parlon tana hada masa breakfast, ya xauna kasa ya gaida Abbansa sannan ya gaisheta, tayi murmushi tace "Lafiya lau Ahmad" ya kusa minti biyar xaune parlon jin Abba bai ce masa komai ba ya mike yayi masa sallama ya fita. Karfe goma saura Junaid ya shirya yayi ma Mumy sallama ya fita, Mumy dai jin sa kawai take da yace ranan xai kawo mata surkarta, yana fita gidan Hajjo ta diro da 'yar Jakarta babu notice. Junaid na isa hotel din ya tarar warce yayi hiring don gyara Jasmine har ta xo, El-ameen yayi tsaki ganinsa yace "Sai yanxu ka ga daman xuwa tata da kai" Junaid yace "Ehh" simple make up aka yi ma jasmine da kyar don har cixon me make-up din sai da tayi, wajen sa mata kaya ma a bayi sai da suka yi karamin yaki don sai da El-ameen ya mata jan ido ta tsaya, shi dai Junaid wayarsa kawai yake dannawa, sai da aka dau kusan awa daya wajen shiryata, tayi wani sanyayyan kyau, sai dai da ganinta kasan a takure take cikin kayan, da ta sa hannu xata cixge El-ameen xai mata wani irin kallo, lokaci lokaci Junaid kan sata kallonta, har matar ta gama ta sa mata hijab, tayi wani kara xata fixge El-ameen ya mata tsawa, sake hijab din tayi tana kallonsa, ya sakar mata wani lallausan murmushi, can Junaid ya mike ya fita daga dakin, waya El-ameen ya dauka ya dawo kusa da ita ya shiga daukan ta hoto sai kallon yanda wayar ke Haske take kamar idonta xai fito, wanda hakan ya kara mata kyau ba kadan ba, ya dauketa ya kusa goma, can ya dawo kusa da ita ya xauna ya matso da ita a hankali sannan ya masu selfie, mai make up dai sai kallonsu take da sha'awa don sun yi mata kyau sosai, bude kofa Junaid yayi El-ameen ya mike ya koma inda yake, Junaid ya ciro kudi ya mika ma matar tayi masa godiya ta fita, Junaid ya kalli El-ameen yace "Hafsat na jiranmu" El-ameen yace "Ohk Allah ya kiyaye hanya, no matter what kar ka yarda ka bar kusa da ita" Junaid yace "Ohk" dagota El-ameen yayi ya kama hannunta, kin tafiya tayi tana kallon flat shoe din kafarta, El-ameen ya jawota ta fasa ihu tana son cire takalmin, Junaid dai sai kallon ikon Allah yake, El-ameen yace "Baxa ta iya tafiya da takalmin ba kenan" dukawa yayi ya cire mata takalman ai ko sai gashi ta fara tafiya, Junaid ya xaro ido yace "Haka xa mu je ba takalmi?" El-ameen yace "Ae hijab din ya kai kasa sosai, bbu komai kawae ka ba Hafsat din ta rike mata, hope ka dai gaya mata brain disorder gare ta?" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Tabdi!" Daga haka ya juya ya fita, El-ameen yayi murmushi ya bi bayansa yana rike da hannunta, kallonsu kawai ake tun daga cikin hotel din har suka fito haraban hotel din, junaid na isa gun motarsa ya juya yana kallonsu, wani mugun faduwa gabansa yayi suna hada ido da ita, ya tsura masu ido su biyun, a hankali take tahowa kamar me tausayin kasa, El-ameen na rike da ita har suka iso gun motar ya bude front seat ya shigar da ita, junaid ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Jikina na bani baxa mu yi nasara ba..." El-ameen ya girgixa kai yace "No! Allah xai daura ka kansu, just pray before going in, nd ka nuna masu ba ta da lafiya ka taho da ita, kaga hakan baxae sa a takurata tayi magana ba, kuma duk me aka ajiye mata kayi saurin dauka ka bude ka bata, if not saukowa kasa xata yi ta xauna ta jawo gabanta, though in TV a kunne yake ma ba lallai ta lura da komai na parlon ba attention dinta gaba daya xata ba Tvn, idan kaga kallon xai yi yawa kawae ka kashe Tvn ma, don't force her on anything don sai ta iya maka ihu" a hankali junaid yace "Ohk!" El-ameen yayi murmushi ya gyada masa kai, juyawa junaid yayi ya bude mota ya shiga ya tada suka bar haraban hotel din, a hanya ya dau Hafsat kamar yanda suka shirya, sai kallonta Hafsat take gaban mota don ita bata ga alamar hauka tare da ita ba, junaid na kallonta ta madubi yace "Bata yi kama da mahaukaciya ba koh?" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba har suka iso gida, a parking lot ya ajiye motar, sai a sannan yaji gabansa na faduwa, ya juya yana kallon Hafsat yace "plss xaki kama hannunta..." Ta yi shiru sai kuma tace "Baxa ta min komai ba" ya gyada mata kai yace "Yea baxata maki komai ba" bude motar yayi ya fito ita ma ta fito, ya xaga xuwa daya side din ya bude ya fito da ita, kalle kalle kawai take idon nan Maa shaa Allah, Hafsat ta kasa karasowa don duk tsoro ya cika ta, Junaid yace "No plss kar ki sa a xargi abu, wllh baxata maki komai ba, xo ki riketa plss" da kyar ta karaso tana kallon Jasmine, yana d'aga kai yaga Umma da Hajiya xaune balcony as usual wani mugun bugu xuciyarsa yayi, ya dauke kai da sauri yana kiran Allah a xuciyarsa. Hafsat na mika hannu xata rike nata tayi bayan junaid da sauri, kiris ya rage xuciyarsa ya shige cikinsa don yayi xaton ihun nan nata xata yi, ganin yanda su Umma ke ta lekosu yasa kawai ya kama hannunta ya nufi part din Mumy, Hafsat ta bi bayansa da sauri.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_
33.....
Mikewa Hajiya tayi da sauri tana kallon kafar Jasmine tace "Balki tashi ki ga ikon Allah" da sauri Umma ma ta tashi ta bude baki tana kallon kafarta, a hankali Junaid ya tura kofar parlon ya shiga gabansa na faduwa, babu kowa parlon ya karasa ciki yana rike da hannunta har lokacin ya isa 3 sitter ya xaunar da ita shi ma ya xauna ya kalli Hafsat ya nuna mata gefen jasmine, ta karaso ta xauna suka sa ta tsakiya, kalle kallen parlon kawai jasmine ke yi, yana son xuwa ya sanar ma Mumy xuwansu amma yana tsoron kar ta bi sa, haka suka ta xama parlon, Hafsat dai sai kallonsa take ganin bai da niyar ta shi ya sanar da mutan gidan xuwansu, fatima ce ta fito parlon, ta d'an xaro ido ganinsa tace "Lah Ya Ahmad!" yace "Kira Mumy" kallon Hafsat tayi ta gaida ta, Hafsat ta amsa da murmushi, ta juya tana kallon Jasmine ita ma ta gaida ta, kallonta kawai Jasmine ke yi kmr idonta xa su yi magana, Junaid yace "Leave ki je kiyi abinda na sa ki" juyawa tayi ya bar parlon tana mamakin abinda yasa taki amsa gaisuwarta, Junaid ya kalli Hafsat da sauri yace "Tana fitowa sai ki gaisheta duk me xata ce kiyi ta bata amsa kawai" Hafsat ta gyada masa kai, ba a dau lokaci ba Mumy ta fito parlon, kwata kwata bata dauka da gaske Junaid yake ba, murmushi dauke fuskarta ta karaso tana kallonsu ta xauna tace "Sannun ku da xuwa" Hafsat tace "Yauwa Mama ina yini" tace "Lafiya lau, ya hanya" Hafsat tayi kasa da kai tace "Alhmdllh," ganin hankalin Mumy na kan Hafsat Junaid yyi saurin cewa "Tana gaishe ki Mumy" ya fadi hakan yana nuna Jasmine, Mumy ta kalli Jasmine don ita dai bata ji tace komai ba, ta dai yi murmushi tace "Lafiya lau, sannun ku da xuwa" Hafsat tayi saurin cewa "Yauwa Mama" Mumy ta kira fatima ta fito tace "Dauko masu ruwa fatima" kitchen ta shiga ta fito da tray ta nufi fridge ta bude ta fiddo ruwa da drink ta dawo parlon, kusa da Jasmine ta ajiye tray din ta kuma komawa kitchen ta dawo da snacks, Jasmine ta kalli Junaid da gabansa ke ta faduwa ta fara kokarin sauka kasa ai da sauri ya riketa yanda bbu wanda xai lura, ya jawo remote yayi powering tv, tvn na kawowa ta koma ta xauna tana kallo, sallaman su Umma da Hajiya yasa xuciyarsa kusan shigewa cikinsa, suka karaso parlon su Suhaima na biye da su a baya ko warce da murmushinta a fuska, Hajiya tace "Ashe bakuwar har ta iso ko a sanar da mu, sannun ku da xuwa," Mumy tace "Ae kuwa, da wai idan sun tashi tafiya xa su shiga su gaida ku" Umma tace "Allah sarki" Hafsat tace "Ina yinin ku" suka amsa mata a tare, Mumy dai sai kallon mamaki take ma jasmine dake ta kallo kamar her life depend on it ganin bata gaida su ba, Junaid ya lura da hakan hankalinsa ya tashi ba kadan ba, su kansu su Umma kallonta suke, Hajiya tace "Toh wai wacece surkuwar ta mu a ciki" Junaid na shirin cewa Hafsat ce, Hafsat ta riga sa ta hanyar nuna masu jasmine, ya xaro ido don shkkn tasa ta samesa, Umma tace "Ikon Allah, sannu Amaryar mu" nan ma dai ko dagowa Jasmine bata yi ba idonta na kan TV, Hajiya tace "Toh fah, anya amaryar nan na jin mu kuwa" Hafsat tayi saurin cewa "ba ma ta jin dadi ne muka fito..." Umma tace "Ikon Allah, ana burin auren lafiyayya shi kuma ra'ayinsa kenan bawan Allah, Allah sarki naga ma kamar ciwo gareta a kafa don bbu takalma ku ka shigo" lumshe ido Junaid yayi a hankali ya bude, shi kam ya shiga uku da matan ubansa, Mumy dai bata tanka su ba ta kalli fatima tace "Xubo masu abinci fatima" Guri Hajiya ta nema ta xauna tana cewa "Tun da baki gare mu bari mu xauna" Junaid ya watsa mata wani kallo ta gefen ido, Umma ma ta xauna tana cewa "Toh baxa a kai ta gun Hajja ba tun da tana nan..." Gaban Junaid yayi wani mugun faduwa jin sunan warce ta kira, Mumy tace "Xa su je" Hajiya tace "Ya kamata kam, ai da mun san da xuwansu da ko 'yar girki ne mun yi" kallonsu kawai Hafsat take ko ba a gaya mata ba tasan matan ubansa ne, Fatima ta fito daga kitchen rike da warmer din abinci da plates da spoon, Junaid ya kalli Mumy a hankali yace "Baxa su ci ba Mumy" Hajiya tace "Suka gaya maka? Ke xo ki ajiye masu" Ko kallonta bai yi ba, fatima dai ta dire abincin gabansu, a hankali Mumy tace "Xuba mana" Bude kofa aka yi Humainah da Khadija suka shigo Hajja na biye da su a baya tana cewa "Don jaraba mutum ya kwaso uban tafiya a rasa abinda xa a hada sa da sai wani tsinannen taliya can, tsiya dai a gidan Muhammadu ta kare..." Khadija na ganin Jasmine tayi still bakin kofa da mamaki, Humainah kam kallo daya ta masu ta nufi daki, Hajja ta karasa shigowa parlon tana bin kowa da kallo tace "Xaman me ake haka, me ya faru" Hajiya tayi murmushi tace "Kishiyar ki Ahmad ya kawo mana mu gaisa" Hajja ta washe hakora tace "Ikon Allah, tana ina" lumshe ido Junaid yayi ya jinginar da kansa jikin kujera don yasa tasa ta kare kawai, Umma tayi murmushi ta nuna mata jasmine tace "Ga ta can kamar bebiye ba uhm ba uhm uhm," Hajja ta karaso baki har kunne tace "Ke don baki da kunya har gida xaki xo kwacen miji, to ahir dinki ni da Amadi mutu karaba" shi dai Junaid har lokacin yaki bude ido, ji yake kamar yayi tsuntsu ya bar parlon, Hafsat ma duk ta rasa abun yi a lokacin, fatima ta bude kulan me dauke da hadadden spaghetti ta shiga xubawa, Hajja ta dunguri Jasmine tace "Ya hure maki kunnen kar ki gaisheni kenan koh, to ba karamin aiki na bane in kora ku ke da shi wllh" juyowa Jasmine tayi da sauri tana kallonta, wani kara da ya tsorata occupants din parlon ta saki da karfi, Hajja na tuntube tayi kofa da gudu tana salati a tsorace, fatima ma dake gabanta tuni ta rufa ma Hajja baya, Hajiya da Umma da su Suhaima duk aka mike a tsorace, Mumy ma ta mike tana kallon Junaid, juyowa Jasmine tayi ganin ta kora Hajja, idonta ya sauka kan spaghettin da fatima ta fara xubawa a plate, wani karan ta kuma saki a rikice ta daga kafarta tana matsawa kusa da Junaid kamar xata shige jikinsa tana kallon taliyar, ae sai ga Umma da Hajiya ma bakin kofa da gudu 'ya yansu na biye da su a baya, Mumy kanta barin wajen tayi, Khadija ta karaso da sauri ta dauke taliyar tunawa da tayi haka ta ma indomie ranan, Hajiya ta saki salati tana tafa hannu tace "Al-qur'an mahaukaciya ce" Hajja ta dafe kirji tace "Mahaukaciya kuma" Mikewa Junaid yayi ya dagota, da gudu Hajja tayi waje su Hajiya suka rufa mata baya da gudu su ma, Mumy tace "Ahmad" tsayawa yayi ya juyo a hankali yana kallonta, sake hannun Jasmine yayi ya karasa kusa da ita cikin sanyin murya yace "Na'am" jin bata amsa ba ya dago kai yana kallonta ganin yanayin fuskarta yasa jikinsa yayi sanyi sosai, strictly tace "Wacece yarinyar nan" kasa ce wa komai yayi ta masa wani tsawa tace "Ba magana nake maka ba" a hankali yace "Ita nake son aure, Mumy it's a long story... Am sorry i hide everything for you, tana da brain disorder ne, so..." Mari Mumy ta sauke masa, Humainah dake tsaye bakin kofar daki tana kallon duk abinda ke faruwa ta juya a hankali ta bar wajen, lumshe idonsa yayi ya bude, Hajiya na tafe hannun ta saki shewa tace "Maganar Suhaima dai ya tabbata...." Hajja ta leko parlon tace "Amma na tausaya ma gwalma'da'dden rayuwar ka Ahmad, ka rasa shegiyar da xa ka kawo mana matsayin surka sai mahaukaciya, to Allah sai ya mana hisabi da kai, kuma maxa ku kira min ubansa duk inda yake ya dawo yaga me ya haifa ma kansa..." Hafsat da tausayin Junaid ya rufeta ta juya ta nufi kofa, da sauri Suhaima ta fincikota tace "Ke kuma algunguma munafuka har da yi ma mahaukaciyar jagora koh....." Mari me lafiya Hafsat ta sauke mata, Hajja tace "Kambu Ramaa!" Tun kan ta rama Hafsat ta kuma sauke mata wani, Muhibba da Sadiya suka yi kanta, ta fixgi wani vase dake parlon tace "Duk yar iskar da ta matso kusa da ni wlh sai na buga mata kuma babu abinda xai faru don baku son wanene ubana ba, yau Allah ya ga dama kuma sai ya daura maku haukan nan, kuma mahaukaci ai mutum ne, ba sonku Allah ya fi yi a kanta ba da ya bar ku da hankalin ku, ku ba abun farin cikin ku bane d'an ku xai yi jihadi ma, ga dai gida kamar babba amma karami ne" jefar da vase din hannunta tayi ta fice daga parlon, Hajja tace "Kaji gantalalla k'awar mahaukaciya kawai, uban waye hamagon uban naki, to mu dai xuri'armu babu mahaukaci, ke ubanki yayi jihadin ya aureta mana yar buhu kawai" tuni Hafsat ta kusa gate abunta, Hajja ta fashe da kuka tace "Ni kuu kira min Muhammadu ya xo ya ga abun da muke gani, Ahmad ya cuce mu, ya xo ya ga sa6on da Ahmad ya tafka, amma duk laifin uwarsa ce wllh kuma mu dai Allah ya isa, ina laifin ka fiddo 'yar uwar ka Humainah a matsayin warce xaka aura, ko ka xabo cikin kannin nan naka Suhaima da Muhibba, toh ni ina ya samo mahaukaciyar ma tukun" Mumy da har idonta ya kawo ruwa ta kalli Junaid da kansa ke kasa tace "Maida ta inda ka daukota kuma minti talatin kawai na baka kaje ka dawo" juyawa yayi yana rike da ita ya nufi kofa, Hajja da su Hajiya da suka ji kamar suyi shewa ana rige rigen gudu aka bar bakin kofar. Junaid na ganin dishi dishi ya nufi mota da ita, driving kawai yake amma bai ma ganin gabansa da kyau ji yake kamar a sama yake tafiyar ma, ihun da jasmine tayi da karfi yasa idonsa ya bude sosai, sai a sannan yaga irin tukin da yake da ihun da jama'a ma suke yi, kokarin kauce ma babban motar da yake kokarin karo da yayi, amma hakan bai yiwu ba don sai da suka yi karo bayan haka ya juya kan motar yayi gefen titi yayi cikin jama'a nan ma yaje ya buge da pole, sama sama ya dinga jin abinda Jasmine ke cewa, iya karfinta take cewa Umminta.... Umminta, Wayyo Umminta.... daga haka bai sake jin komai ba kuma bai sake sanin abinda ke faruwa ba.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
34.....
El-ameen ne xaune cikin special ward
ya hade kai da gadon dake kusa da shi, bude kofar ward din aka yi ya dago da kyar, dai dai lokacin da Hajja ta karaso gun gadon da gudu ta daura hannu a ka ta saki wani uban ihu tana salati su Hajiya ma suka shigo ko wanne tana salati, mikewa El-ameen yyi ya fice daga ward din, ba a dau lokaci ba nurses har hudu suka shigo suka fitar da Hajja da su Hajiya, kuka Hajja take rusawa iya karfinta tana cewa "Ku gaya min ko mutuwa yayi don Allah, wayyo mahaukaciya ta cuce mu, kila yana tukin ta shake mana shi ya saki steering, wayyoo ni Dijee" Su Hajiya dai sai matsen kwalla ake kamar gaske, El-ameen ne ya xo wucewa Hajja ta bi sa da gudu tana cewa "Tsaya Aminu gaya min me ya samu Ahmad din, don Allah gaya min ya mutu ne? Wayyo an kassara Muhammadu don shi daya gare sa" Tafiya kawai El-Ameen yake tana binsa da gudu har ya isa ward din ya shiga ya rufe kofar yasa makulli, ta fashe da matsanancin kuka tace "Allah ya isa tsakani na da kai dan iska" A hankali El-ameen ya karasa gadon da Junaid ke kwance yana kallonsa, a shoulder dinsa yaji ciwo banda nan bbu wani waje kuma sai dai har lokacin he's unconscious, juyawa yayi yana kallon Jasmine dake kwance a wani gadon har lokacin ita ma bata farfado ba, ya xauna ya hade kai da gado, shine mutum na farko da aka fara kira aka sanar ma hatsarin wanda hakan na nuni da shine mutum na karshe da suka yi waya da Junaid din, bude kofar ward din aka yi Abbansa ya shigo da wata nurse biye da shi a baya da clinic tray, mikewa yayi Abba yace "Meye amfanin saka su gaban da ka xo kayi ga injections ba a gama ba....." Baya ya koma Abba ya dafa goshin Junaid ya kuma yi masa gwaje gwaje sannan ya juya ya koma gun jasmine, a forehead dinta ta ji ciwo sai kneel dinta daya, ita ma ya mata gwaje gwajen da xai yi ya juya yana kallon El-ameen yace "Ka karbi injections din hannunta ka masu, in ka gama ka xo office ka dau wanda xaka xuba a ruwa" daga haka ya juya ya fita, nurse din ta karaso ta mika masa tray din hannunta ya karba ta juya ta fita, Junaid ya fara yi ma sannan ya karasa gun Jasmine ya mata a lap. Kasa fita daga ward din yayi ya koma ya xauna duk jikinsa ba kwari, Abbansa ne ya kuma dawowa tare da Abban Junaid, Abba ya karasa gun gadon yana kallon Junaid da ganinsa kasan kawai yana boye tashin hankalinsa ne, Allah ya basa lafiya kadai yace ya juya ya fita Abban El-ameen ya bi sa a baya, El-ameen ya koma ya xauna, har bayan azahar babu wanda ya farka cikinsu, har lokacin kuma Hajja na asibitin tana rera kuka har an gaji an kyaleta, su Hajiya duk sun koma gida, kiran la'asar ya sa El-ameen ya fita daga ward din don xuwa yin sallah, yana fito ko minti biyar ba a yi ba jasmine ta bude idonta a hankali, bin dakin ta shiga yi da kallo a hankali har idonta ya sauka kan Junaid, kokarin mikewa xaune ta yi taji kamar an tsikara mata allura a kneel ga kuma drip din da ta gani jikinta, ta koma da sauri ta kwanta tana kallon drip din hannunta, fixgewa tayi ta ajiye, ta kusa minti bakwai xaune kamar me son tuno abu wanda hakan da take yi yasa kanta yayi mata wani mugun nauyi ga tsara mata da yake kamar xai tsage, kara tayi ta rike kan da hannu biyu taji abu kamar hula a xagaye mata, da sauri ta cire hannunta, bayan kusan minti biyu taji ciwon ya rage, saukowa ta shiga yi a hankali daga kan gadon, kamar me tsoron tiles din dakin ta dinga tafiya tana dingishi har ta isa gadon da Junaid ke kwance tana lekan fuskarsa, komawa baya tayi da sauri, sai kuma ta saka kuka tana yarfe hannu lokaci daya tana kare ma dakin kallo, a hankali tace "Ummi...." Sake lekan fuskarsa tayi ta kusa minti biyu idonta a kansa kafin ta juya a hankali ta bar wajen, muryoyi taji daga waje ta nufi wani kofa da ta gani da gudu ta bude ta shige ta fashe da kuka, ji tayi an bude kofa can waje tayi saurin jingina a jikin kofar bathroom din, kallon gadonta kawai El-ameen yake da mamaki, can ya juya ya kalli Junaid, da sauri ya nufi toilet tana jin ya murda ta juyo da sauri ta tura kofar da duk hannunta biyu, sau daya ya tura kofar ya bude ta koma baya da sauri tare da juya masa baya, kallonta ya tsaya yi da mamaki, a hankali yace "Jewel" xaro ido tayi zuciyarta na bugawa har lokacin kuma bata juyo ba, karasawa yayi ya dafata yace "Jewel" k'ara tayi da karfi yyi saurin juyo da ita yace "Hey It's me jewel" tsit tayi tana kallon fuskarsa xuciyarta na bugawa, murmushi ya sakar mata ya kama hannunta yace "Am glad you are fine!" fixge hannunta tayi da sauri ta fashe da kuka tace "Ummina!" Tana fadin haka ta sake juya masa baya tana rera kuka, still yayi na kusan second ashirin sautin xaxxakan muryarta na kai kawo a kunnensa, ya kifta ido ya kusa sau biyar, can ta juyo a hankali suna hada ido ta sunkuyar da kai ta raba ta gefensa xata fita yyi hanxarin tare hanyar, da kyar ya iya bude baki yace "Wait! Wait Ina...ina Ummin naki?" Kallonsa kawai take sai kuma a hankali ta buda masa hannu alamar bata sani ba, cikin sanyin murya yace "Baki sani ba?" Ta gyada masa kai hawaye ya gangaro fararen idonta, murmushi ne yayi slipnn lips dinsa a hankali yace "Ohh! Alhmdllh!" lokaci daya murmushin ya bace tunawa da yayi sai fa ya iya xama kuma tayi loosing memory ya girgixa kai da sauri yace "No! no gaya min ya sunanki?" Kallonsa kawai take yi, ya gyada mata kai yace "Yyees tell me, ya sunanki?..." Gefensa ta kuma rabawa xata fita ya rikota, ta juyo da sauri ta warce hannunta tana masa wani irin kallon da yasa hanjin cikinsa kadawa, komawa baya yayi da sauri ta fice daga toilet din ya bi ta da kallo xuciyarsa na bugawa.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
35.....
Da kyar El-ameen ya iya juyawa ya fita daga bathroom din, ya ganta tsaye kusa da kofa tana kokarin budewa, tsayawa yayi yana kallonta har ta bude xata fita yayi saurin cewa "Wait wait ina xa ki" ko kallonsa bata yi ba ta fice, xaro ido yayi ya juya yana kallon Junaid kamar idonsa biyu din nan, bayanta ya bi da sauri ya tarar har ta sauka stairs tun kan ta karasa shiga reception ya sha gabanta, xuciyarsa na bugawa ya dake yace "Look, kin ga baki da lafiya ina xa ki" shiru tayi tana kallonsa, ya kasa kallon cikin idonta, cikin sanyin murya yace "Kiyi hakuri ki bari ki kara samun lafiya sai a kai ki gidan ku kin ji?" Jin bata ce komai ba ya dago da kyar yana kallon kwayar idonta, hawaye ya gani fal idon, ya dauke kansa, a hankali yaji tace "Toh ina ne nan?" Ya kuma dagowa da sauri yana kallonta yace "Asibiti," maimaita abinda ya fada tayi a sanyaye ya gyada mata kai, tace "Meye hakan?" Buda ido yayi yana kallonta lokaci daya jikinsa yayi sanyi, ya girgixa kai da sauri yace "Ki gaya min sunan ki tukun!" Shiru tayi tana kallonsa, can tace "Suna?" Ya gyada mata kai, kafa masa ido tayi kamar dai tana son tuno sunan, a xuciyarsa ya dinga furta innalillahi, k'ara tayi ta dafe kanta xata durkusa, yayi saurin rikota ya dagata ya nufi sama da ita, addu'a ya dinga yi a xuciyarsa na cewar Allah yasa ba abinda yake tunani bane, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, gadon da take ya mayar da ita ta kwanta ta rufe ido, ya ja kujera ya xauna kusa da gadon yana kallonta, ta kusa minti biyar bata bude idon ba, can ta bude a hankali tana sauke ido kansa ta mike xaune da sauri tace "Ummina" gefen gadon ya xauna yace "Toh gaya min inda take in kai ki" ACn dake ward din ta tsura ma ido da ganinta kasan tunani take, wani karan ta kuma yi ta runtse ido ta dafe kanta, lumshe ido yayi shi ma ya dafe kai tausayinta na shigarta, a hankali ya dago yana kallonta cikin sanyayyan murya yace "Ki kwanta ki huta kin ji, anjima xa ki tuna inda Ummin ki take in kai ki" bude ido tayi tana kallonsa ya sakar mata murmushi ya gyada mata kai, komawa tayi ta kwanta, yace "Xa ki ci abinci" ta kallesa tace "Abinci?" Kamar me koyon word din tayi maganan, jiki a sanyaye ya mike ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, yana rufo kofar ta mike xaune tana kallon gadon da Junaid yake, saukowa tayi a hankali ta isa gun gadon ta duka tana lekan fuskarsa, ta kusa minti biyar tana kallonsa can ta kamo hannunsa a hankali murya can kasa tace "Daddy!" Mikewa tayi da sauri kamar warce ta tuno abu, runtse ido tayi ta dafe kanta hade da yin ihu, sosai kanta ke juya mata wanda hakan yasa ta fadi kan gadon, ta dau lokaci bata dago ba, can ta bude ido a hankali ta ganta kansa, xaro ido tayi ta mike da sauri tana kallon shoulder dinsa dake jini duk da bandage din dake nan alamar ta fama masa, kuka ta fashe da ta duka a hankali tana kallon shoulder din, bandage din dake kanta ta taba ta sa hannu biyu ta fixge da karfi har sai da ya fita ta matso kusa da shi ta duka ta daura bandage din kan kafadar nasa, bude kofa aka yi El-ameen ya shigo rike da plate da cup din tea, tsaye yayi bakin kofar yana kallonta ta juyo ita ma tana kallonsa ta nuna masa kafadar Junaid tace "Ciwo!" Tana fadin haka ta d'an bude ido tana kallon abinda ta kira da ciwo kamar me son gano abu, karasowa El-ameen yayi sanin she's trying hard ne ta tuna abu yace "yes ciwo ne, taho in sa maki wani bandage din you are bleeding" gadonta ya nufa, ta bi bayansa jiki a sanyaye, ya nuna mata inda xata xauna ta hau gadon ta xauna, ya ajiye plate din hannunsa ya dauko wani bandage din da plaster ya gabanta, runtse ido tayi tun kan ya taba kan, yana kallon fuskarta har ya gama sa mata bandage din, murya can kasa yace "Bude idon" a hankali ta bude tana kallonsa, ya mata murmushi ta sunkuyar da kanta, abincin ya bude ya dau spoon ya mika mata, ta karba tana kallon cokalin, yace "Eat" ganin yanda take kallon cokalin yasa ya karba ya debi abincin ya kai mata baki, ta bude bakin a hankali ya xuba mata, kallon yanda take tauna abincin yake, aka bude kofar ward din Abbansa ya shigo da wata nurse, ajiye spoon din yayi da sauri, Abba ya karaso yana kallonta yace "Maa sha Allah, Alhmdllh ashe ta farka baka sanar min ba, to ina 'yan uwan nata ita" rasa abun cewa El-ameen yayi, Abba dai sai kallonta yake ganin she looks familiar, lokaci daya ya tuna inda ya taba ganinta ya kalli El-ameen da sauri yace "Wannan ba mahaukaciyar nan bace da ka kawo min nan ranan, me ya hada ta da Ahmad?" El-ameen da xuciyarsa ke bugawa ya mike don ya ma rasa abun cewa, tsawa Abba yayi masa yace "Are you daft?" Da kyar yace "Abba ta samu lafiya ma, dama iyayenta, Abba gida...." Strictly Abba yace "Kana son ganin the odza side of me ko Ahmad?" Sunkuyar da kai yayi, Abba yace "Maxa fitar min da ita daga nan ka maida ta gun iyayenta, mutumin banxa kawai" juyawa Abba yayi ya bar wajen ya isa kusa da Junaid yyi gwaje gwajensa, ya jima yana kallonsa kafin ya kalli nurse din yace "We might need to diagnose his brain, ya dau lokaci bai farfado ba" daga haka ya juya ya fita nurse din ta bi bayansa, tun da El-ameen ya ji abinda Abba yace gabansa ya fadi ba kadan ba, ya karasa gadon da sauri yana kallon Junaid, kansa ya dafa na kusan minti uku sannan ya cire hannunsa a hankali cikin sanyin murya yace "Come back pls frnd, for the sake of ur patient...." Juyawa yayi yana kallonta ya ga hawaye idonta ya karasa da sauri yace "Me ya faru?" Ta fashe da kuka, shiru yayi yana kallonta don ya lura ba ko wani magana ma take ganewa ba, kamo hannunta yayi a hankali yace "Kiyi hakuri kin ji, xan kai ki gidan ku" ita dai kallonsa kawai take, tunanin inda xai kai ta yake, sanin in har Abba ya dawo ya kuma ganinta ransa xai baci, gashi bai son barin Junaid, murda kofar dakin aka yi, ya juya da sauri Mumy ta shigo tare da Humainah da fatima, jikinsa yayi sanyi ya sunkuyar da kai. Humainah ce tayi karfin halin karasawa kusa da gadon da Junaid yake ta durkusa ta fashe da kuka, fatima ta juya ta fice daga ward din, Mumy bata iya ta karaso cikin dakin ba, Humainah ta kamo hannunsa cikin rawar murya tace "plss ka tashi ya A.jay..." El-ameen ya karasa kusa da ita yace "He will be fine ki daina kuka kin ji" juyawa Mumy tayi ita ma ta fita daga dakin, Humainah ta kallesa hawaye na bin kuncinta tace "Toh me yasa har yanxu bai tashi ba" dagota yayi yace "Xai tashi nan da few minutes in'sha Allah" kallon jasmine dake ta kallonta tayi kawai ta juya ta fice daga ward din tana kuka sosai, juyawa yayi yana kallon Jasmine ya karasa kusa da ita, hawaye ne ya gangaro idonta a hankali tace "Yayanta ne?" Kallon mamaki yake mata don in tayi wani maganar kamar ba ita ba, gyada mata kai yayi yace "Ehh!" Daga haka ya xauna ya ci gaba da bata abincin, kadan ta ci ta dauke kai xai yi magana aka bude kofa mikewa yayi da sauri, gabansa ya fadi ganin Abba ne ya dawo, yace "Abba ynxu xan fita da ita wllh" wani kallo Abba yayi masa sannan ya nufi gadon da Junaid yake, wani ruwan ya sa masa ya juya yana kallon El-ameen yace "tana gama karban sauran treatment dinta gobe ka fitar min da ita a asibiti, don't let me repeat my self tomorrow" kai ya gyada da sauri yace "Yess sir" juyawa Abba yayi ya fice, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya ya xauna yayi tagumi, da dukkan alamu tayi loosing memory ko ba duka ba, kuma xai dauki months kafin ta dawo dai dai shima sai tana shan drugs ana kuma yi mata abubuwan da ya dace, in kuma Allah yasa tayi toxali da wani nata kila ya dawo gaba daya, a hankali ya daga kai yana kallonta ya ga ta jingina jikin gado idonta lumshe, mikewa yayi da sauri ya kwantar da ita ta bude ido ya sakar mata murmushi yace "Sleep jewel!" A hankali tace "Sleep" ya gyada mata kai daga haka ta lumshe idonta. Har sha biyun dare yana dakin, hankalinsa ya tashi sosai ganin Junaid bai farfado ba har lokacin, wata nurse ce ta xo tace Abba na kiransa ya mike ya fita jiki ba kwari, yana fita jasmine ta farka ta mike xaune da sauri tana kalle kalle a hankali tace "Ummina" ta kusa minti goma xauna ta ga Junaid na motsi, ido ta kafa masa, can ta sauko a hankali ta iso kusa da gadon ta duka tana kallonsa, a hankali ya bude idonsa ya shiga kalle kallen dakin idonsa ya sauka kanta, ta d'an koma baya tace "Sleep" kallonta kawai yake, ta d'an yi murmushi ta buda masa manyan idonta ta kuma cewa "Sleep"
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
36.....
A hankali ta koma baya jin bai ce komai ba har lokacin idonsa na kanta, ta d'an bata fuska ta juya masa baya dai dai shigowar El-ameen ward din, da sauri ya karaso gun gadon yana kallonsa ganin idonsa bude, murmushi ne yayi escaping lips dinsa yace "Ohh Captain! You are back" Lokaci daya murmushin ya bace ganin yanda Junaid ke kallonsa, dukawa yayi a hankali yace "Ahmad!" Nan ma dai kallonsa kawai Junaid ke yi, El-ameen ya girgixa kai da sauri yace "No plss say something frnd, kana ji na..." D'aga sa yayi xaune yace "Ahmad talk to me" dafe kai El-ameen yyi a xuciyarsa ya dinga furta innalillahi.... Jasmine ta matso kusa da shi a hankali tana kallonsa, Dagowa yayi da kyar ya kuma kallon Junaid yace "Captain!" Dukawa tayi kamar yanda yayi ita ma cikin sanyayyan muryarta tace "Captain!" El-ameen ya juya yana kallonta, ta buda masa ido tace "Captain" juyawa yayi ya maida dubansa ga Junaid yaga kallonta yake, mikewa El-ameen yayi jiki a sanyaye ya nufi kofa, jasmine ta bi sa da kallo har ya fita sannan ta juya tana kallon Junaid tace "Captain" kallonta kawai yake, ta matso kusa da shi tana kallon shoulder dinsa a hankali tace "Ciwo!" Sai kuma tayi murmushi tace "Yana ma zafi?" Kallonta Kawai har lokacin ko kiftawa bai yi, shiru tayi kamar me naxarin abinda ta fada can ta rike kanta ta sulale nan wajen tayi k'ara tana cewa Umminta dai dai shigowar El-ameen da Abbansa sai wani Dr faruqh, Junaid ya lumshe ido ya bude, El-ameen ya karasa da sauri ya dagota yana kallonta, Abba ya girgixa kai tare da yin kwafa yace "When I say tomorrow I mean tomorrow" a sanyaye El-ameen ya maida ta kan gadon da take ya kwantar da ita har lokacin ta ki bude ido, Abba dake ta kallon Junaid ya duka gabansa a hankali yace "Ahmad?" Junaid ya dago ya kallesa sannan ya maida kansa kasa yace "Na'am" Abba ya juya ya kalli El-ameen da ya xaro ido yana kallon Junaid, da sauri ya karaso har lokacin idonsa a kansa, Abba yyi murmushi yace "Alhmdllh! Ina ke maka ciwo yanzu?" Junaid yayi shiru, a hankali Abba ya kuma cewa "Ahmad" ya dago ya kallesa yace "Ba ko ina Abba" Abba yace "Are you sure?" Ya gyada masa kai, Abba yace "Maa sha Allah, Allah ya tsare gaba bari a kawo maka tea yanzu sai ka sha drugs" daga haka Abba ya juya ya fita, Dr faruqh yayi murmushi yace "Allah ya kara kiyayewa Captain Junaid" Junaid yace "Ameen" daga haka Faruqh ya juya ya fita, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "gaskiya kana da matsala junaid, ni meye nawa xa ka share ni" Junaid bai tanka sa ba ya sauka daga kan gadon ya nufi toilet, El-ameen ya bi sa da kallon mamaki, girgixa kai yayi ya juya yana kallon jasmine ya ga har ta fara bacci, ya karasa kusa da ita ya duka murya can kasa yace "Jewel" bude ido tayi tana kallonsa, ya mata murmushi yace "Sleep" cikin sanyin murya tace "Captain!" Yayi shiru yana kallonta kafin ya girgixa mata kai a hankali yace "Doctor!" Rufe idonta tayi bata sake budewa ba ya mike ya gyara mata kwanciya ya rufa mata bargon da ke kan gadon, junaid ya fito ya nufi gadon da yake, El-ameen ya bi sa da kallo yace "patient din ka ta samu lafiya" Ba tare da junaid ya kallesa ba yace "Naga alama" El-Ameen yayi murmushi yace "Hakan kuma ya faru ne ta dalilin accident din da ku ka yi, nd this clearly shows dat hatsari ne cause din haukanta, sai dai kuma ga dukkan alamu tayi loosing memory...." Wata nurse ce ta shigo da cup din tea ta karasa kusa da Junaid ta mika masa ya karba ya fara sha, ta ajiye magungunan hannunta ta gwada masa yanda xai sha ta bude fridge ta fiddo masa ruwa ta ajiye sannan ta fita, El-ameen yace "Ina magana xaka wani min shiru?" Junaid ya kallesa yace "Ai na ji ka, and am glad ta samu lafiya dama abinda nake so kenan, yanzu abinda ya rage shine in sama mata inda xata fara rayuwa har memoryn ta ya dawo....." El-ameen yace "inda xa ka sama mata kamar ina?" Junaid ya kallesa sannan yace "Inda xata xauna ta ci gaba da rayuwa nace" El-ameen yace "Toh ai ban gane irin gun da kake fadi bane" Junaid yace "Ko mama jumman nan sai in sa a nemo min in damka mata ita ta rike har tayi recalling abubuwa ta nemi iyayenta" El-ameen yace "Haba, she still need medication har ynxu fa....." Junaid ya kallesa yace "Nayi iya taimakon da xan mata a yanzu, idan mama jumman ma ta dauketa dole xan basu kudi that will be enough for der needs....." El-ameen yace "No plss ba sai an kai ta kauye ba, ka bari ka cike ladan ka kawai" Junaid yayi masa wani irin kallo yace "Bana ketare maganar mahaifiyata, tace in maida ta inda na samo ta and dat's wat am going to do..." Shiru El-ameen yayi na wani lokaci kafin yace "Amma baka mata adalci ba" Junaid yace "Look ka bar ni in ji da abinda ke damuna yanzu El-ameen, ban san da idon da xan kalli mahaifiyata ba, ban san ta wani sigar Abbana xai dauki batun nan ba, I've tried my best na mata iyakar abinda ya kamata tunda gashi ta dawo hankalinta...." El-ameen bai kuma cewa komai ba ya lumshe ido ya bude sannan ya fita daga ward din. Junaid ya jinginar da kansa jikin bango daga xaunen da yake ya lumshe ido, har kusan Karfe biyu El-ameen bai dawo dakin ba, ya juya yana kallon gadon da take kwance, saukowa yayi daga kan gadon da yake ya karasa nata gadon yana kallonta, lumshe ido yayi cikin sanyin murya yace "Na so taimakon da xan maki ya fi haka Jasmine, I can't help, baxan iya tsallake umarnin Mumyna ba, am very glad kin dawo mai hankali, nasan you will cope da new environment din da xa ki samu kanki har tunanin ki ya dawo" ya kusa minti goma kusa da ita kafin ya mike a sanyaye ya koma gadonsa. Ciwon kai bai bar sa ya runtsa ba har Karfe hudu, yana nan kwance aka bude kofar El-ameen ya shigo, lumshe ido yayi kamar me bacci, El-ameen ya karasa kusa da shi yana kallonsa, ya daura hannunsa kan forhead dinsa ya ji da dumi sosai, kallon magungunan da ke gefensa yayi da mamaki ganin bai sha ba, ya jima tsaye kansa kafin ya juya ya koma gun jasmine, kwata kwata daren kasa bacci yayi sbda tausayinta, da ya tuna abinda Abbansa yace kan gobe bai son ganinta asibitin sai jikinsa yayi sanyi, in kuma ya tuno furucin junaid ma sai yaji tausayinta sosai, dukawa yayi yana kallon fuskarta, yaga ta bude ido da sauri, komawa baya yayi ta mike xaune tana mitstsika ido tace saw "Captain!"
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
37/38
Murmushi El-ameen ya mata yace "Good morning" ita ma a hankali tace "Good morning!" Ya gyada mata kai yana murmushi har lokacin, duk abun nan da suke Junaid na kallonsu, yana ganin El-ameen xai juyo yayi saurin lumshe ido, El-ameen ya nufi kofa ta bi sa da kallo kafin ya fita tayi saurin cewa "Captain!" Juyawa yayi ya kalleta ya girgixa mata kai yana murmushi yace "No, Am doctor!" A hankali tace "Doctor?" Ya d'an bude ido yace "Yess" juyawa yayi ya fice. Saukowa tayi daga gadon ta nufi gadon Junaid ta duka tana kallon long eyelashes dinsa don har lokacin idonsa a lumshe yake, a hankali tace "Captain!" Ya bude ido da sauri yana kallonta, tayi murmushi tace "Good morning!" Mikewa xaune yayi ya mayar mata murmushin yace "Morning jasmine, how you?" A hankali tace "Am fine, and you?" Shiru tayi da sauri kamar me naxarin abinda tace, can ta runtse ido ta dafe kanta ta durkusa wajen, ya sauko da sauri yana kallonta, ta kusa minti biyar a haka shi dai bai dagota ba bai kuma san ma me xai ce mata ba, mikewa tayi a hankali tana rike da kan ta juya ta bar wajen ya bi ta da ido, xama tayi kan kujeran da ke kusa da gadonta ta kifa kanta ta inda ba ciwo, komawa yayi ya xauna har lokacin yana kallonta. El-ameen ne ya shigo dakin bayan an idar da sllhn Asuba, ya samu Junaid xaune kan darduma, ya ajiye ledan hannunsa ya ja kujera ya xauna yana kallonsa yace "Good morning captain, ya jikin?" Junaid yace "Alhmdllh" kallon magungunansa El-ameen yayi yace "Jiya baka sha drugs din ka ba ashe?" Junaid bai ce komai ba El-ameen ya tabe baki ya mike yana kallon jasmine dake xaune har lokacin kan kujera kanta kife kan gado, karasawa yayi yana kallonta ya ga bacci ma take a haka, ya dan duka yace "Hello!" Bude ido tayi da sauri tace "Hi" murmushi yayi yace "Good, tashi kiyi sllh" dago kai tayi da sauri tana kallonsa tace "Sallah?" Ya gyada mata kai, tayi shiru tana kallonsa kamar bata taba jin Kalmar ba, shi dai Junaid kallonsu kawai yake, El-ameen yace "Am coming" daga haka ya juya ya fita, ba a dau lokaci ba ya dawo tare da wata nurse rike da hijab, ya kalli nurse din yace "Ki rakata bayi, ki gwada mata yanda xata yi alwala" nurse din ta kalli jasmine sannan ta kallesa tace "Ban gane ba sir" Yace "Yes alwala xaki yi tana gani tana bin ki" nurse din ta kuma kallon jasmine dake kallonta ita ma ta ajiye hijab din hannunta tace "Toh sir" El-ameen ya kalli Jasmine yace "Tashi ki bita kiyi duk abinda tayi kin ji" mikewa tayi tana kallonsa ya gyada mata kai yace "Yes follow her" tace "I should follow her?" Murmushi yayi ganin yanda take catch up da sauri yace "Yes follow her" kamar me tausayin kasa haka ta dinga bin nurse din a baya har suka shiga toilet din, nurse din ta rufe kofar tana kallonta tace "Do you want to urinate?" Kallonta kawai Jasmine take kamar me naxarin word din, a hankali tace "Urinate?" Matar ta gyada mata kai, girgixa mata kai tayi, matar ta dau kettle daya ta mika mata ita ma ta dau daya tace "Kiyi duk yanda ki ka ga nayi" a hankali Jasmine ta durkusa tana kallon nurse din runtse ido tayi jin xafi a kneel dinta, nurse din dai sai kallonta take har ta bude idon, sannan ta yi bismilla ta fara alwalan tana kallonta, jasmine ta wanke hannunta ita ma kamar yanda ta ga nurse din ke yi, haka tayi ta kwaiwayon ta har suka kare alwalan nurse din ta fito tana biye da ita a baya, har lokacin junaid na xaune kan darduma, El-ameen ma na xaune yana jiran fitowar su, mikewa yayi yana kallon junaid yace "Pray mat malam" junaid ya tabe baki ya mike ya koma kan gado, El-ameen ya shimfida ya kuma dauko wani ya shimfida a baya, ya dau hijab ya mika mata yace "Ki saka" karba tayi tana kare ma Hijab din kallo, ya mata alama da tasa, kokarin sakawa ta shiga yi ta kasa don bata san ma yanda xata saka din ba, ya karaso yana murmushi ya karba ya saka mata, Junaid ya kauda kai hade da tabe baki, El-ameen ya nuna mata inda xata tsaya kan darduman yace "Kiyi duk yanda kika ga nayi" shiru tayi tana kallonsa, yace "Kin ji?" A hankali ta gyada masa kai, ya koma darduman gaba ya tada sllh, haka ta dinga binsa sllhn tana yin duk yanda taga yayi da kyar sbda kneel dinta, har suka idar ya juya yana kallonta, jini ya gani Hijab dinta ya dawo kusa da ita da sauri yace "Ohh!" Hannu yasa xai daga hijab din ta koma baya sauri tana masa wani kallo, komawa baya yayi cikin sanyin murya yace "Yi hakuri," mikewa yayi ya fita, ta juya tana kallon Junaid da ke kallonsu, dauke kanta tayi tana nan xaune har El-ameen ya dawo da nurse, nurse din ta duka kusa da jasmine tace "Sannu" daga hijab din tayi tana kallon kneel din, kayan aiki El-ameen ya miko mata nan ta fara gyara mata wajen, rufe idonta tayi da ganinta kasan daurewa kawai take, El-ameen ya durkusa kusa da ita yana mata sannu, har nurse din ta gama, a hankali ta bude idonta da ya kada, yace "Sannu" ta kallesa sannan ta sunkuyar da kanta, mikewa nurse din tayi ta fita da kayan aikin, tashi yyi ya dauke darduman da yake kai ita ma ta mike ta dauke dayan, Junaid ya dauke kai tun kan su kallo inda yake, ledan da El-ameen ya shigo da ya nufa ya bude ya fiddo da sabbin toothbrushes da toothpaste, ya ajiye ma junaid daya ya bude daya ya matsa toothpaste ya mika mata yace "Tafi ki wanke bakin ki" karasowa tayi ta karba tana kallonsa, murmushi yayi sanin bata gane ba kenan, yace "Follow me" da sauri tace "Follow her" dariya ta basa yace "No, follow me dai" daga haka ya shiga toilet ta bi bayansa, yana kallonta yayi mata alama da hannu da ta wanke baki da brush din, saka brush din tayi a baki ta tsaya, yace "Toh wanke bakin" tsotsan toothpaste din tayi ta cire brush din tana yamutse fuska, yace "No ba haka ba" ya mika mata hannu alamar ta basa ta mika masa ya kai brush din baki, nan ya shiga gwada mata yanda xata yi sannan ya mika mata, yanda taga yayi haka tayi yana kallonta har ta gama sannan ya nuna mata gun xuban ruwa yace "Wash ur mouth," karasawa tayi tana kallon wajen, yayi murmushi ya karaso ya bude mata ruwan ya tara da hannunsa ya kai bakinsa ya kuskure ya xubar sannan ya kalleta yace "Haka xa ki yi" tara hannunta tayi ita ma, ya tsura ma fararen hannun nata ido har ta kai ruwan baki ta kuskure kamar yanda ta ga yayi" murmushi ya mata yace "Good gal" juyawa yayi yace "Mu tafi" ta bi bayansa suka fito, bai yi mamakin rashin ganin junaid dakin ba, yana lafiya ma ya aka kare bare yanxu, kujera ya nuna mata ta xauna yace "Am coming" sannan ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita. Ba a dau lokaci ba ya dawo da bowl me dauke da apples, ya jawo table karami ya ajiye kusa da ita sannan ya daura bowl din kai yana kallonta yace "Eat" kallon bowl din kawai take, can ta sa hannu ta dau apple daya a hankali ta kai bakinta, bude kofa aka yi duk suka juya, gabansa ya fadi ganin Abbansa, Abba ya karaso dakin yana kallon gadon junaid yace "Where is my patient" El-ameen yayi saurin cewa "Ya d'an fita ne yanxu Abba" Abba yace "Ya fita da sassafen nan ya je ina?" El-ameen da gabansa ke faduwa yace "Ina jin ya fita ne, no cewa yayi xae fita ya sha iska" wani kallo Abba ke masa sannan ya kalli Jasmine dake kallonsa yace "Bana son in sake shigowa in ga yarinyar nan a nan Ahmad" kallon Abban nasa yayi a sanyaye yace "Toh Abba" Abba yace "Mutumin banxa kawai, kuma maxa kaje ka dubo min patient dina yanxu" daga haka ya juya ya fita, El-ameen ya juya yana kallon Jasmine, murmushin karfin hali ya sakar mata yace "Eat your apple" sunkuyar da kanta kawai tayi, ya juya a sanyaye ya fita daga dakin. Babu inda bai duba ba a asibitin amma bai ga junaid ba, abun yayi mugun basa mamaki kar dai gida ya wuce, dawowa sama yayi bai kuma yi gigin xuwa gaya ma Abba bai gansa ba don yasan baxai ji da dadi ba, office dinsa ya fara tafiya ya dau makullin motarsa sannan ya tafi ward din da jasmine take ya ganta har lokacin rike da apple din bata ci ba, ya karasa kusa da ita yace "Eat mana jasmine" bata kallesa ba ya kama hannunta xai dago ga ta fixge hannun tana masa wani kallon da ya fadar masa da gaba ya d'an koma baya a hankali yace "kiyi hakuri" ya gane bata son a taba ta kenan, mikewa tayi tsaye, ya fara tafiya yace "Mu je" har ya isa bakin kofa ya juyo yaga bata biyosa ba, yafito ta yayi sai gashi ta fara tahowa, Suna tafe yana juyowa yaga ko tana binsa har suka fito haraban hospital din ya nufi parking space da ita, gaban mota ya bude mata ya mata alamar ta shiga, still tayi tana kallon motar kamar warce ta tuno abu, can kuma ta kallesa kamar xata yi kuka, accident dinsu na jiya ne ya fado masa lokaci daya ya gane abinda yasa taki shiga, girgixa mata kai yayi yace "babu abinda xai faru jewel, shiga" kin shiga motar tayi still, ya xaga ya bude driver seat ya shiga ya tada motar kallonsa kawai take daga waje, can ta fara kalle kallen asibitin, a hankali ta shiga daga karshe yayi murmushi ya rufo motar, yana gama warming ya ja motar suka bar haraban asibitin bayan an bude masa gate, driving kawai yake ba tare da yasan inda xai kai ta ba, duk tausayinta ya cika shi, a hankali yace "Ina xan kai ki Jewel?" Kallonsa tayi ba tare da ta ce komai ba, Kanwar Abbansa ce ta fado masa kawai ya yanke shawarar kai ta can gidan, Karfe takwas da wani abu suka isa gidan, ya bude motar ya fito ya xaga ya bude mata ita ma ta fito, yana gaba tana biye da shi a baya suka shiga gidan, bbu kowa parlon ya nuna mata kujera ta xauna, cousin sis dinsa ta fito daga kitchen da mamaki take kallonsa tace "Toh fa, yaya daga ina haka?" Yayi murmushi yace "Gida, kira min Mumy" daki ta tafi tana cewa lallai yau akwai ruwa da kankara, Hajiya salmah Kanwar dad dinsa ta fito parlon tana kallonsa tace "Kayi batan hanya ne Ahmad?" Yayi murmushi yana shafa kai yace "A'a Mumy ina kwana" ta tabe baki ta amsa tana kallon Jasmine, sunkuyar da kai jasmine tayi, El-ameen yace "Mumy na xo neman alfarma ne a gun ki pls" tana kallonsa tace "Na me fa Ahmad" yayi kasa da murya ya shiga mata bayanin Jasmine, kallonsa take baki bude har ya kai karshe tace "Ehh lallai Ahmad, wato kai ne baka jin maganar naka iyayen koh, kai ne baka san darajar su ba, to wllh maxa ka maida masa ita shi da ya jajubo ta, maganar banxa kawai, shi me wayo yaji maganar tasa uwar sai kai ne da baka san darajan naka uban ba koh....." Mikewa El-ameen yayi bai kuma sauraranta ba, Jasmine na ganin ya tashi ita ma ta tashi da sauri, ya nufi kofa ta bi bayansa, small mum din tasa ta bi sa da harara tace "D'an rainin hankali kawai, mara wayo, kuma wllh sai na kira yaya na gaya masa yasan baka dauke sa bakin komai ba." Har ya fice daga parlon bai tanka ta ba.
Junaid na fita daga asibitin dama trekking yayi har ya isa bakin titi duk da jirin da yake gani ga wani ciwo da kansa yake masa da shoulder dinsa, singlet ne da jeans jikinsa. shi matsalar sa daya Mumy bai san ta inda xai soma bata hakuri ba, ya jima tsaye bakin titi wani tricycle ya tsaya yana tambayarsa ko tafiya ne, ya shiga ya gaya masa inda ya nufa, Suna isa gida ya fito yace masa yana xuwa, gun mai gadi ya karbi dari biyar ya basa sannan ya shiga gidan, Hajja ce ta fito daga side dinta rike da wani katon kwandon kwanuka ta xuba kulolin abinci har uku da flask sai cup ta daura a kai, xaro ido tayi ganinsa ta sauke kwandon da sauri cikin daga murya ta ce "Alhmdllh jama'an gida Bilki, Fatee da Amina ku fito gashi ya ji sauki ya dawo.... Amadina ya dawo, yaron kirki ya dawo...." Haka ta dinga yi kamar ta samu waka, Umma ce ta fara fitowa da sauri su Muhibba na biye da ita, sai Hajiya da khadija, fatima ma ta fito, da gudu khadija ta tafi ta rungumesa cike da murna, yake su Hajiya da Umma aka shiga yi ana gode Allah ana jajantawa, Shi dai junaid bai kallesu ba ya nufi part dinsa Hajja ta bi bayansa da sauri tana cewa "Amadina ya dawo, yaron kirki ya dawo" tun kan ta iso ya sa ma kofar key ya shige bedroom, ruwan xafi ya hada yayi wanka a toilet ya fito ya shirya, sai dai singlet kadai yasa da bakin jeans sbda kafadarsa, kwanciya yayi jin xaxxabi na neman rufesa, ko minti goma bai yi da kwanciya ba aka bubbuga kofar parlon ya mike da kyar ya bude, fatima ya gani tsaye, ta gaishesa ta masa ya jiki ya amsa sannan tace Abba na kiransa. Gyada mata kai yayi ta juya ta tafi, ya koma ya xauna parlon gabansa na faduwa ya kusa minti biyar sannan ya mike jiki ba kwari ya fita daga parlon ya tafi part din Abba, da kyar ya iya shiga parlon ganin dukka mutan gidan xaune da alaman shi ake jira, bai bari sun hada ido da kowa ba, kansa a kasa yayi surveying inda xai xauna ya xauna kawai, sai a sannan ya d'an dago kai yaga kusa da Humainah ya xauna, sunkuyar da kai yayi, banda kallonsa babu abinda ake yi a parlon, Mumy kadai ne bata ma kalli inda yake ba, Abba ya soma gaisarwa, sannan Hajja dake ta kallonsa baki har kunne, sai kuma Hajiya da Umma, bayan nan ya daga kai yana kallon Mumynsa cikin sanyin murya ya gaisheta, ta amsa ba tare da ta kallesa ba, Abba yace "Meye dalilin ka na baro asibiti ba a sallame ka ba?" Sunkuyar da kansa yayi bai ce komai ba, Abba ya girgixa kai yace "Toh ka kyauta, Ahmad ban yi mamakin abinda ka aikata jiya ba, don dama ni na dade da sanin kai ma mahaukaci ne, iyayen ka ne dai basu sani ba......" Hajja ta kyalkyale da dariya har da kwanciya tace "A'a Muhammadu wllh nima ina sane kawai dai ban taba fadi bane, tunda hannun ka baya rubewa ka yanke ka yar, amma Amadi kam mahaukaci ne" sunkuyar da kai junaid yayi, Hajiya da Umma sai danne dariyarsu suke, Humainah tayi murmushi ta sunkuyar da kai ita ma, Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya kyauta, amma kafin haukan naka ya xame mana bala'i na yanke shawarar yi ma aure nan da sati biyu kawai, ko kwandalar ka bana bukata xan maka komai, shi yasa ma nace xan maka aure, alkawari ne wannan na daukar ma kai na" dagowa yayi da sauri yana kallon Abba, su Hajiya duk aka kwalalo ido, Hajja tace "Atoh" kallon Mumy junaid yayi yaga idonta na kan TV, xufa ya dinga ji na keto masa, a hankali yace "Abba!" Abba ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu yace "No, ba shawarar ka nake nema ba, ba kuma xan maka abinda xai cutar da kai ba."
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
39.....
Junaid bai kuma cewa komai ba ya sunkuyar da kansa, Abba yace "Tashi kaje, idan lokaci yayi xaka san matar taka" da kyar Junaid ya mike ya nufi kofa ya fita daga parlon, part dinsa ya koma ya kwanta, lokaci daya yaji xaxxabi na neman rufesa, ya jima kwance kafin bacci ya daukesa. Driving kawai El-ameen ke yi ba tare da yasan inda xai kai ta ba, sai a lokacin ya fara daya sanin sallamar mama jummai da yanxu kawai sai ya kai su hotel, parking yayi gefen titi ya dafe kansa yana tunanin abun yi, can ya dago yana kallonta ya ga kallonsa take, murmushi ya sakar mata ta sauke idonta daga kansa, wayarsa ya ciro ya shiga neman number wata course mate dinsa kuma frnd dinsa a da, bugu uku ta daga suka gaisa, ya tambayeta oga da yara, daga daya bangaren tace "Suna nan qlau, kana duniya kuwa El-ameen, ko ma dai ce min xaka yi bikin ka ya kusa?" Dariya yayi yace "Haba dai d'an yaro da ni, aure ba yanxu ba sai na kara girma" dariyan tayi ita ma tace "Continue deceiving ur self, ga mu dai har mun kusa aurarwa," yace "Toh wa ya sani ko ni xa a ba wa ma," tace "Allah ya sauwake, me 'ya ta xata yi da sa'an ubanta" dariya yayi sosai yace "Ban dai xo da naira nace ina so bane, yanxu dai kina kt ne?" Tace "Ina nan ina xa ni," yace "Toh a gaya ma oga gani nan xuwa dai" tace "Sai kace gaske" yace "Allah kuwa, gani xuwa favour xan xo nema gun ku" tace "Toh sai ka xo, ina xuba ido" yace "Alryt tnx" daga haka ya katse wayar, juyawa yayi yana kallon Jasmine dake ta kallonsa, ya buda ido hade da mata murmushi, sunkuyar da kai tayi, ya ja motar suka bar wajen, cikin minti ashirin ya isa gidan Dr Sumayya, bakin gate yayi parking ya kirata, tana dagawa yace "Ga ni a waje" tace "Toh ka shigo mana" yace "Ohk" bude mota yayi ya fito ya xagaya ya bude mata ta fito ya rufe sannan yace "let go" a hankali tace "Ohk" wara ido yayi ya gyada mata kai yace "Good" daga haka ya fara tafiya ta bi bayansa, Dr Sumayya ce ta bude masu kofa tana murmushi tace "Sannu da xuwa Dr, ashe tare da bakuwa ku ke" yace "Exactly Mrs Sumayya" parlor suka shigo tace "Sannun ku da xuwa" xaunawa tayi suka kuma gaisawa, ya tambayeta yara tace sun tafi sch, yace "Maa sha Allah, bakuwata na kawo maki ta d'an yi kwana biyu" ta kalli Jasmine tace "Da gaske?" Yace "Serious" murmushi tayi tace "Ohh she's welcome, budurwar ka ce?" D'an wara ido yayi yace "No, no, xan ma iya cewa patient dita ce" Dr Sumayya ta kyalkyale da dariya tace "Ohhh I see" murmushi yayi yace "Ohhh serious" kallon Jasmine tayi tace "Sannu 'yan mata ina kwanan mu" El-ameen ya kalleta ya dawo gefenta yace "Tell her good morning jewel" kallon matar Jasmine tayi a hankali tace "Good morning" matar ta dan bude ido tana dariya tace "Toh fa" murmushi El-ameen yayi yace "She just recovered from posttraumatic stress disorder, and tayi loosing memory yanxu" Dr Sumayya jikinta yayi sanyi tace "Allahu Akbar, toh ina iyayenta" girgixa kai yayi yace "Its a long story Dr, bamu san iyayenta ba, Abokina Captain Junaid ne helper dinta, shi ya tsinto ta ya bada suggestion in mata treatment, gaba daya expenses din kuma shi yayi volunteer....." Dr Sumayya tace "Ahmad Junaid dai dana sani me ji da kan nan?" Dariya El-ameen yayi yace "Ohh Really? Toh shi!" Tace "Ikon Allah, ashe yana da mutunci da taimako" El-ameen yace "Sosai ma, don baku xauna da shi bane" Dr Sumayya tace "Kai amma yarinyar ta ban tausayi wllh, Allah sarki" El-ameen yace "Kwana biyu xata yi a nan, akwai d'an matsala ne kuma we are trying to fix it up, ki dinga bata pain relieving drugs sbda injury din kanta" Dr Sumayya tace "In'sha Allah" mikewa yayi yace "Ni xan koma office" tace "Toh shikenan take care!" Mikewa Jasmine ma tayi da sauri ya juya yana kallonta yace "You will stay with aunt kin ji...." Hawaye ne ya ziraro idonta, jikinsa yayi sanyi yace "No kar ki yi kuka I will be back soon" Dr Sumayya ta karaso ta kama hannunta tace "Kar ki damu xai dawo kin ji 'yan mata" El-ameen yayi murmushi ya juya ya nufi kofa, Dr Sumayya ta tafi daki da ita tana lallashinta. Junaid bai farka ba sai kusan Karfe uku na rana, ya mike xaune da kyar, rike kansa dake masa ciwo sosai yayi, can ya mike ya nufi toilet ya dauro alwala ya fito ya tada slln azahar, parlor ya fito bayan ya idar ya ga abinci ajiye parlon, sai a sannan ya fara jin yunwa don tun tea din da ya sha a asibiti jiya da daddare bai sake cin komai ba, xaunawa yayi ya bude food warmern, ya ga shinkafa ne da miya, ya dau plate ya dibi kadan ya fara ci, kwata kwata bai jin dadin abincin a bakinsa, spoon hudu yayi ya ajiye ya jinginar da kansa jikin kujera, kwankwasa kofar parlon aka yi ya juya yana kallon kofar kauda kai yayi dai dai lokacin da aka bude, colleagues dinsa na gun aiki ne har su hudu dukkansu sanye da uniform suka shigo parlon, ya d'an bude ido yana kallonsu har suka karaso parlon, daya daga cikinsu Captain Umar yace "Ohh ko mu koma ne A.jay" Murmushi yayi yana shafa kansa yace "Uhnn it's surprising, sannun ku da xuwa" xama suka yi gaba daya, nan suka gaisa, Daya daga cikin su yace "sai muka ji bad news Ahmad" junaid yayi murmushi, Capt Umar yace "Toh ya jikin?" "Jiki Alhmdllh, tun da gashi har na dawo gida" duk suka yi masa Allah ya sauwake, mikewa yayi ya nufi fridge din dake parlon ya bude ya kawo masu ruwa da drink ya ajiye masu, sun d'an taba hira na minti sha biyar suka ce masa xa su koma, fruits da drinks suka ajiye masa yayi masu godiya ya rakasu part din Mumy su gaida ta, da fara'a ta tarbe su basu jima ba suka mata sallama suka fito, Umma da Hajiya sai kallonsu suke daga balcony, shi kuma bai ce su gaida su ba, yi ma yayi kamar bai taba ganinsu ba, hakan yayi mugun kona masu rai, ya raka frnds din nasa har waje gun mota, sannan ya komo cikin gida, part din Mumy ya tafi, duk suka bi sa da kallo ko wanne da tunanin da take a ranta, yana shiga parlon Mumy Hajiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Yaro man kaza" Umma ta tabe baki tace "Ke yanxu kin yi farin ciki da hukuncin da Alhaji ya yanke kansa?" Hajiya tace "Ina fa nayi farin ciki, kika san warce xai aura masa? Kema dai kin san ba lallai ya xabi 'ya yanmu ba, na ma fi tunanin kila yace shegiyar Humainahn nan, kuma da mun shiga uku mun lalace..." Umma tace "Ba abun mu koma gun malam ba yanxu ya hada mu da k'ulli yace sai an barbada ko sai anyi wani abun daban asiri ya kuma tonuwa ga Hajja mayya a gida" Hajiya tace "Mu je ki ji ina da wata shawara Allah ya bamu sa'a wannan karan" mikewa Umma tayi da damuwa tace "Ameen" ta bi bayanta suka shiga parlor. Bedroom junaid ya shiga ganin Mumy bata parlor, ya karasa gabanta ya durkusa ba tare da ya bari sun hada ido ba, cikin sanyin murya yace "Don Allah kiyi hakuri Mumy, forgive me plss kar kiyi fushi da ni" jin bata tanka sa ba yasa ya dago yana kallonta, a hankali yace "Kin ji Mumy!" Tana kallonsa da kyau tace "Ka min wani abu ne?" Shiru yayi bai ce komai ba, tace "Toh baka min komai ba tashi ka fita" kasa tashi yayi, tace "Ka tashi na ce" a sanyaye ya mike ya fita daga dakin. Kallo daya yayi ma Humainah dake parlor ya nufi kofa ya fita, dai dai fitowar Hajja daga part din Abba, ya dauke kai kamar bai ganta ba xai wuce tace "Kai Amadi mu muka dauro maka hatsarin nan ne xaka wani dinga sha mana kamshi a gida don fitsara, to Allah shi kara, kuma ka tafi ka gaida ubanka Abubakar ya xo tun daga Abuja" yi yayi kamar bai san da shi take ba ya fara tafiya xuwa part dinsa, da karfi ta kwalo masa kira yanda tasan Abba xai ji cike da masifa tace "Ni din sa'ar uwar ka ce ina maka magana kake tafiya kake min tsaki, toh Muhammadu ka fito ka ga rashin kunyar da Amadi ke min gaban jama'a, don an maka gata an raba ka da gagarumar mahaukaciya sai ka dau gaba da 'yan gida..." Tsayawa yayi yana kallonta fuskar nan nasa a daure, tace "D'an banxa kawai, ka wuce ka gaida ubanka Abubakar nace" part din Abbansa ya tafi ta bi sa da harara, da sallama ya shiga parlon ya xauna kan carpet kansa a kasa ya gaida Small Abban nasa dad din Humainah, Alhaji Abubakar yace "Lafiya lau Ahmad ya jikin?" Junaid yace "Alhmdllh Abba ya hanya" "Hanya mun baro ta, ya aikin?" Cewar dad din Humainah yana kallonsa, Junaid yace "Alhmdllh" dad din Humainah yace "To Maa sha Allah" kallon Abbansa yayi yaga idonsa a kansa, yayi kasa da kai ya mike yayi musu sallama har ya kai bakin kofa Abba yace "Ka koma asibitin?" Girgixa kai Junaid yayi yace "Yanxu xan tafi Abba" Abba yace "Toh ka kira Abdul ya kai ka, ga makullin mota" komawa cikin parlon yayi ya dau makullin yayi masa godiya ya juya ya fita. shiryawa ya tafi yayi a part dinsa ya fito, sai da ya fara shiga ya gaya ma Mumy xai tafi asibiti snn ya fito ya tafi parking space ya dau motar Abbansa ya fita don xai iya driving din. Abban El-ameen ne ya duba sa da kansa a office dinsa, wani likita yayi masa allura ya basa drugs dinsa, ya kusa awa daya office din sannan dad din El-ameen yace xai iya tafiya ya dawo da daddare karban allura, godiya Junaid yayi masa ya mike ya fita daga office din, yana saukowa second floor ya tsaya yana kallon kofar office din El-ameen, karasawa yayi ya murda handle din door din ya tura, xaune ya gansa ya jinginar da kansa jikin kujerar da yake idonsa rufe, har ya karasa cikin office din bai sani ba, yayi knock din table din gabansa, da sauri El-ameen ya bude ido ya gyara xama, Junaid yace "Sleeping at work" El-ameen ya shafa kansa yace "Our run away patient" Junaid ya ja kujera ya xauna yana kallonsa yace "ka bani number mai gadin can gidan naka nasan baxai rasa sanin whereabout din mama jummai ba, El-ameen ya bude hannu yace " I don't have!" Junaid ya d'an bude ido yace "Da gaske?" El-ameen ya gyada masa kai, junaid yace "Toh yanxu ya xa muyi?" El-ameen yace "Na kai ta gidan old frnd dita Dr Sumayya" junaid yyi shiru kafin yace "har xuwa yaushe?" El-ameen yace "I told her kwanaki kadan xata yi, dama mijinta bai nan ne nasan xata rike ta but kasan halin su mata" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Or mu kai ta orphanage home kawai tunda dai hankalinta ya dawo" wani kallo El-ameen yayi masa yace "tunda ca tayi maka bata da iyaye ba, ko kuma ance maka manya suke dauka" Junaid yace "Toh yanxu kasan inda iyayen nata suke, ka sani ma ko suna da rai, kaga ni iya taimakon da nasan xan iya yi ma yarinyar nan kenan sbda parent dina, ba don su ba xan iya yi mata komai na taimako a rayuwa, I just can't keep on disobeying my mother, beside am getting married in 2wks time kamar yanda Abbana yace, to ya kake son inyi da 'yar mutane, ina xan kai ta idan ba orphanage home ba?" El-ameen ya lumshe ido ya bude hade da shafa kai yace "Aure xa a maka! Toh me xai hana ta xauna gidan ka tare da matar ka har memory dinta ya dawo junaid, last gatan da xaka yi ma baiwar Allahn nan kenan a rayuwa" junaid yayi shiru yana kallonsa can yace "Gidana kuma?" El-ameen yace "Yes, ko tare xaku tare da Mumy?" Murmushi junaid yayi yace "Idan matar bata yarda ba fa?" El-ameen ya hade rai yace "Gidan ubanta ne ko kanta xata xauna?" Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe idon yana naxarin shawarar El-ameen.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
40/41
Mikewa Junaid yayi yace "I will think about that!" Daga haka ya nufi kofa El-ameen ya bi sa da kallo har ya fita. A haraban hospital din suka hadu da faisal, faisal yace "Ohh my God, ashe abinda ya faru kenan captain shine ko ku sanar da ni kai da El-ameen? da Childishness din ku ne ya tashi da har gida xa ku xo ku sameni" junaid yayi murmushi yace "I thought ka sani ne ai," faisal yayi tsaki yace "Ta ina xan sani?" Daga haka ya bar sa nan tsaye ya shiga asibitin, murmushi junaid ya kuma yi ya shiga mota ya bar asibitin. Yana isa gida part dinsa ya tafi yayi alwala yayi sllhn asr sannan ya kwanta parlor, har ya fara bacci yaji an bude kofar parlon, bude ido yayi ya mike xaune da sauri, Humainah ce ta shigo parlon ta tsaya daga bakin kofa ta d'an hade rai tace "Xamu tafi tare da Hajja!" Yana kallonta yace "Ina xa ku" tace "Gidanmu!" Shiru yayi kafin yace "Ohk, yaushe xa ki dawo?" Ta tabe baki tace "Baxan sake dawowa ba, da kayana duka xan tafi ma" murmushi Junaid yayi yace "Ohk Allah raka taki gona" tace "Ameen" daga haka ta juya ta fice daga parlon, ya koma ya kwanta. Tana fita hajja ta shigo sabe da gyalenta da 'yar jakar da ta taho da shi, tace "Toh Amadi ni dai xan tafi sai kuma na dawo kai maka amarya ko kaki ko ka so sai in ga ta tsiya, idan har ynxu ra'ayin rayuwa da mahaukaciya kake to sai ka haukatar da warce za a kai maka hakan xai fi maka rufin asiri" daga haka ta juya ta fita ya bi ta da kallo hade da tabe baki, ranan da daddare Ummin El-ameen ta xo gidan, duk yanda ta so ya gaya mata ko El-ameen yasan komai kan xancen yarinya mahaukaciya kin gaya mata yayi yace babu ruwan El-ameen, ba don ta yarda ba ta kyalesa don tasan bakinsu daya, can tace "Na ji labarin aure xa ayi maka, saura abokin ka, shi wannan kauye ma xanje dauko masa mata wallahi xan basa mamaki," Dariya Junaid yayi yace "Kai Ummi, kauye kuma" bata tanka sa ba ta mike ta fice daga parlon. Shirye shiryen biki aka dinga yi gidansu Ahmad Junaid babu kama kafar yaro, cikin kankanin lokaci aka hada lefe akwati shidda, shi dai Junaid kallon ikon Allah kawai yake wai shi xa ayi ma aure, auren ma na dole kamar wani mace kuma har lokacin bai san matar ba dariya ma kawai abun ke basa, ana saura sati bikin ya dawo aiki da yamma yana kwance sai dai gaba daya tunaninsa na gun Jasmine yana son sanin halin da take ciki yana kuma son ganinta, kiran El-ameen ne ya shigo wayarsa ya daga, daga daya bangaren El-ameen yace "Uhm duk xumudin xama angon ne yasa ka mance da patient dinka captain?" Junaid yace "If that's what you are thinking...." El-ameen yace "Toh yayi kyau, amma idan baka manta the very first day da ka fara xuwa min da batun ta sai da na baka shawarar ka raba kanka ka ki, yanxu ka xo kayi abinda ya dame ka, ka bar ni da 'yar mutane, ko irin ka dinga kira ka tambayi lafiyarta babu, to Dr sumayya dai ina a week time xa su yi tafiya da mai gidanta wai..." Junaid yace "Yea! Then an min auren sai ta dawo gidana kamar yanda ka ce" El-ameen ya tabe baki ya katse wayar. Karfe biyar da wani abu Junaid ya shirya ya tafi part din Mumy yace mata xai dan fita, sabuwar motar da Abba ya basa ya dauka ya fita daga gidan, a hanya ya kira El-ameen, yana dagawa yace "Kana ina?" El-ameen yace "Me xan maka?" Tsaki Junaid yayi yace "Dalla ni ka gaya min" katse wayar El-ameen yayi, junaid yayi parking ya ji kamar ya juya, sai dai baxai iya ba sbda son ganin jasmine da yake, sake kiransa yayi yana dagawa yace "How dare you xaka katse min waya daga tambaya" El-ameen yace "Ashe ba dadi kai kake ma mutane, ni da ma kai ka haukacen wllh kayi loosing memory ko xaka rabu da wnn worst attitude din naka, gashi it's getting worst nowadayz, ni ina gida anything?" Katse wayar junaid yayi hade da yin kwafa, ya kusa minti goma xaune motar ya kuma yin wani kwafan ya ja motar ya nufi gidan nasu, Ummi dake parlor ya gaida tace "Ni ban ga kai da abokin naka kuna shirin bikin nan ba Ahmad" junaid yayi yake yana shafa kai yace "Ae abinda ya kawo ni kenan" Ummi tace "Toh yayi kyau, da an gama naka da sati biyu in an huta xan kai nasa lefen kauye" Junaid ya fashe da dariya yace "Wllh xan maki driving din" Ummi ta hade rai tace "Am serious, dan ma ka gaya masa nake gaya maka" dakin El-ameen ya nufa yana dariya, El-ameen ya tura laptop din gabansa yace "What is making him laugh" Junaid ya buda ido yace "Baka ji a bakin Captain ba, yanzu dai tashi ka kai ni in duba yarinyar nan tunda gori ka min daxu" El-ameen yace "As you can see am busy, sai dai in baka address" junaid yace "Ba fa dadewa xa mu yi ba" "yess! ko minti daya xa muyi" cewar El-ameen yana kallonsa da kyau. Junaid ya kusa minti goma tsaye yana kallonsa kafin ya juya ya fita daga dakin, El-ameen yace "Byee!" Da daddare yana kwance bedroom Humainah ta fado masa, tabe baki yayi ya dauki wayarsa ya shiga kiranta, sai da ya kusa katsewa ta daga yace "don ma kin samu na kira ki" tace "I didn't beg for ur call" shiru yayi sannan yayi murmushi yace "True! Yaushe xa ki dawo?" Tace "Ana saura kwana biyu bikin ka xamu dawo da Hajja" yace "Bikinsu dai" daga haka ya katse wayar, Har ya ajiye wayar ya tuna Hafsat, tun ranan da abun ya faru bata kira ba bai kirata ba, numberta ya duba ya shiga kiranta bugu uku ta daga ya mata sallama ta amsa daga daya side din hade da gaishesa, ya ce "Ya kike?" Tace "Qlau" rasa me xai sake ce mata yayi, can dai yace "Am sorry for what happened Hafsat," tace "Ohh ba komai, ya wuce ai" yace "To nagode" tace "welcome! But a ina ka san yarinyar?" D'an shiru yayi kafin yace "It's a long story" tace "really?" Yace "Yeah!" Labarin yanda ya fara ganin jasmine tun daga rana ta farko ya fara bata har xuwa ranan da ya kai ta gida gun parent dinsa da abinda ya faru bayan barinsu gida, Hafsat da duk jikinta yayi sanyi tace "Yanxu kana nufin ta dawo hankalinta?" Yace "Yea, amma tayi loosing memory" Cike da damuwa Hafsat tace "Allah sarki, to yanxu tana ina?" Ya lumshe ido ya bude yace "Tana gun frnd dina, buh am getting married in a week time sai ta dawo gidana har tayi regaining memory, Hafsat tace "Dat's nyc Allah ya sanya alkhairi, ya bada xaman lafiya," Yace "Ameen thank you" shiru tayi ya kalli agogo ya ga har sha daya ya wuce, yace "Xa ki kwanta koh?" Tace "Yeah" yace "Ohk good nyt, tnx a lot ki gaida mutan gida" tace "Ayt bye!" Daga haka ya katse wayar ya ajiye yayi addu'an kwanciya. Washegari da yamma junaid na kwance bayan ya dawo daga aiki El-ameen ya shigo parlon, kallo daya ya masa ya dauke kai, El-ameen na daga tsaye bakin kofa yace "In ka shirya ka taso mu tafi" ko kallonsa junaid bai yi ba, El-ameen yace "Ohk nayi tafiya ta" daga haka ya fice. Junaid ya mike ya shiga bedroom ya daura shirt dinsa ya dau Atm ya fita, a part din Mumy ya tarda El-ameen, ya jira har ya gama surutun sa snn yace "Mumy xa mu d'an fita yanxu mu dawo" Mumy tace "Toh Allah ya tsare" ya juya ya fita. A mota yayi ta jiran El-ameen har sai da yaga dama ya fito, El-ameen ya xaga daya side din ganin junaid a driver seat yana shiga junaid ya tada motar suka bar layin, tun a hanya El-ameen ya kira Dr sumayya ya sanar da ita xuwansu, a visitor parlor suka sauka dotan Dr Sumayya 'yar shekara sha uku ce ta kawo masu ruwa da drink ta xauna kusa da El-ameen tana ta basa labari, junaid dai makala earpiece yayi yana danna waya, bayan kusan minti biyar Dr Sumayya ta shigo parlon suka gaisa da El-ameen, El-ameen ya fixge wayar sai a sannan ya dago yana kallon Dr Sumayya yace "Ina yini!" Tace "Lafiya lau ya aiki," yace "Alhmdllh," mikewa tayi ta fita tana fita sistern ta warce xata yi mate din jasmine ta shigo parlon tare da jasmine din, xama tayi kan kujera ta nuna ma Jasmine gefenta ta xauna sannan ta gaida su El-ameen, ya amsa mata da murmushi yace "Ya sch?" Tace "Alhmdllh" kallon jasmine tayi tace "Baby baki ce masu ina yini ba" sunan da Dr Sumayya ke kiranta da shi kenan a sati daya da 'yan kwanakin da tayi a gidan, shine duk yan gidan ke kiranta da haka, shima El-Ameen dake yawan xuwa gidan sai ya dinga kiranta da haka, jasmine ta kalli farida sannan ta kalli El-ameen a hankali tace "Ina yini?" Murmushi kawai yayi mata ta sunkuyar da kai, Junaid dai sai kallonta yake ta gefen ido, El-ameen yace "Toh baki gaida wannan ba Baby" Ya fadi hakan yana nuna mata Junaid, kallonsa tayi tace "Ina yini?" Ya dago kai shi ma yana kallonta yace "Lafiya lau" daga haka ta sunkuyar da kai, El-ameen yace "Baby dawo ki xauna nan ki gaya min abubuwan da Farida ta koya maki yau" mikewa tayi ta dawo kusa da shi ta xauna kasa, Junaid ya kalli agogon wrist dinsa sannan ya ci gaba da danna wayarsa, El-ameen yace "Gaya min mana" dago kai tayi ta kallesa cikin sanyayyan muryarta tace "tace min girki ne abinda muka yi" dariya yayi yace "Da gaske, to me ku ka girka?" Ta kalli farida tace "Ya ma?" Dariya farida tayi tace "A'a tuna dai" shiru tayi kamar me naxarin sunan girkin, da sauri farida tace "Ohkk okk fried rice ne da coconut drink muka yi baby" tayi hakan ne don yanxun nan sai ta iya rike kai ta fara ihu hakan kuma zai ja Dr Sumayya ta bata mata rai, shi kansa El-ameen ya san in dai tayi stressing brain dinta wajen son tuno abu nan da nan kan xai fara mata ciwo, kuma yana daukan lokaci bai daina ba. Jasmine ta kallesa tace "Fried rice and coconut drink Mumy tace mu yi" yayi murmushi yace "Good kuma kin iya yanxu?" Girgixa masa kai tayi alamar A'a, zai yi magana junaid ya mike yace "Toh ni xan koma" El-ameen yace "ohK bani makullin motata" hade rai yayi yace "Xan yi amfani da shi ne" El-ameen ya mike ya warce makullin ya koma ya xauna, juyawa junaid yayi ya fice daga parlon. Da daddare yana kallon wani program khadija ta shigo parlon da sallama ta ajiye masa mug din hannunta, yana kallonta yace "Meye wannan?" Tace "Lipton mana" yace "Wa yace ki kawo min?" Tace "Ance kace wai in maka" yace "Ohk tnx" mikewa tayi ta fita, ya girgixa kai ya ci gaba da kallonsa, bayan kusan minti talatin yaji kamar motsi a balcony, mikewa yayi ya kashe wutan parlon ya rage na tv kadai ya dawo ya xauna, a hankali aka murda kofar parlon, ya jinginar da kansa jikin kujera idonsa na kan tv, Suhaima ce ta shigo parlon da hijab dinta har kasa, ta tsaya daga bakin kofar tana lekosa, shi dai bai juyo ba har lokacin, cikin sassarfa ta karaso cikin parlon ta na kallonsa tace "Ya Ahmad?" Bai tanka ta ba hakan yasa ta d'an yi murmushi ta xauna kusa da shi tace "Amm dama...." Mikewa yayi yana kallonta fuskar nan nasa kamar bai taba dariya ba yace "me ya shigo da ke nan?" Gabanta yayi mugun faduwa ta mike tace "Oh dama..." Juyawa tayi da sauri zata bar wajen ya fixgota, ya sauke mata wani mari me lafiya cikin tsawa yace "Nace me ya kawo ki nan" jikinta ya dau rawa tace "Wayyo kudi xa ka ban" wani marin da ya gigitata ya kuma kai mata, ya ja ta ya nufi daki da ita, kuka ta dinga yi a tsorace tana cewa "Kudi wllh na xo karba" belt ya dauka ta fasa ihu a rikice tana kiran Hajiyarsu, ya ja ta suka fito parlor ya xabga mata a jiki, wanda hakan sai da ya kusa sa ta sakin fitsari, dukanta yake kamar an aikosa, ta dinga ihu iya karfinta tana kiran Hajiya da Umma, Dama suna labe balcony, Hajiya ta saki murmushi haka ma Umma a tare suka ce "Alhmdllh" duk suka sauko compound din, sosai suke jin ihun Suhaima, Hajiya ta saki salati da karfi tana kwala ma suhaimar kira tana cewa "ina kike, me ya same ki" Umma ma ta dinga kwalo mata kira duk suka cika tsakar gidan da hayani, su khadija ne suka fara fiffitowa sannan fatima, Hajiya tuni ta nufi part din junaid har lokacin tana kwalo ma Suhaima kira, Abba ne ya fito shi ma jin hayaniya, Ya kalli Umma yace "Meye haka?" Umma tace "Yo ina muka sani Alhaji, ihunta kawai muke ta ji mun rasa inda take" Fitowa Mumy ma tayi jin abinda Umma tace, Tuni Hajiya ta isa kofar junaid ta shiga bubbuga kofar tana kiran Suhaima, bude kofar junaid yayi bayan ya lallasata iya son ransa da belt ya cillota waje ya kulle kofarsa, birgima ta dinga yi tana cewa "Wayyo Hajiyarmu bai sha ba" Hajiya da idanuwanta suka firfito ta dagota da sauri ta toshe bakinta a jikinta tace "Ba kya ji Suhaima kin tsokanesa kenan koh?" Abba ne ya karaso yana kallonsu yace "Meke faruwa ne wai?" Da sauri Hajiya tace "A'a ita ce bata ji Alhaji fitsara tayi masa daxu, mu je kawai maganinta kenan" Abba ya kwalo ma junaid kira Hajiya da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta tace "oh Alhaji don ya hukuntata shine wani abu, bata dawowa da wuri ne daga makaranta yayi mata magana tayi masa fitsara shine ya xaneta, ai ni ya min dai dai, mu je kawai Alhaji" Mumy ce ta karaso wajen Hajiya tace "Ohh Amina ku rabu da yaron nan, don ya doketa ya hukuntata shine me... Yanxu da fatima ce ai baxa ki ce komai ba" juyawa kawai Mumy tayi ta bar wajen, Abba ya girgixa kai shima ya koma part dinsa, Sumsum Hajiya ta ja Suhaima da ke kuka tana soshe soshen suka bar wajen, Umma ta hadiye yawu da kyar ita ma tayi part dinta. Wasa wasa har biki ya rage kwana biyu, banda shirye shirye babu abinda ake a gidan kamar irin shi ya zabi matar din nan, tuni 'yan uwa da abokan arxiki aka fara xuwa daga garurruwa daban daban, sai a lokacin Junaid abun ya fara damunsa on like before da lamarin ke basa dariya, babban damuwar tasa rashin sanin wacece iyayen sa suka xaba masa, babu yanda bai yi da Mumy ta gaya masa ba ita ma tace bata sani ba, Tashin hankali gun Umma da Hajiya baya faduwa don sun rasa abun yi, komai suka yi ba nasara ciki gashi basu san wacece shegiyar da xa a aura masa ba don basu ga alamar daya daga 'ya yansu bane, da yammacin ranan Hajja ta diro gidan, magiya junaid ya dinga mata kan ta gaya masa wacece matar tasa tace ubansa yayi kadan balle shi, sosai hankalinsa ya tashi, bayan magrib Abba yasa a kira sa, yana shiga parlon ya xauna Abba yace "Babu wani shirin da za kuyi ku, ko walima ne?" Ya gigixa kai yace "A'a Abba, walimar da xa ayi a nan gida ya isa" Abba yace "Toh shkkn, hakan it's Ohk" ranan kasa bacci junaid yayi har kusan karfe dayan dare, wayarsa ya jawo daga karshe ya shiga neman number Humainah don yasan baxa ta rasa sanin matar ba, har ya gama ringing bata daga ba ya sake kiranta sai gashi ta dauka, cikin sanyin murya yace "Kina ji na Humainah" "Um" kawai tace masa kamar anyi forcing dinta, ya lumshe ido ya bude yace "Plss nasan baxa ki rasa sanin warce xa a aura min ba, ki gaya min wacece plss" taki cewa komai na kusan second talatin har sai da yace "Hello" sannan tace "Ban sani ba nima" yace "Plss" kamar xata yi kuka tace "Ban sani ba," tsaki yayi ya katse wayar ya jefar. Washegari alhamis da asuba yayi shirin fita aiki ya fice ya bar masu gidan, haka ya wuni bai da sukuni ranar, yana barin gun aiki Clinic ya tafi gun El-ameen, da damuwa yace "Frnd har yanxu fa ban san wacece matar nn ba" El-ameen yayi murmushi yace "gobe idan mun kai ka xaka ganta, sbda son da Abba yake maka shi yasa yake son surprising naka" Junaid yace "Plss ka daina bata min rai more, what sort of surprise is this, and what if fitinanniya ce taki yarda da xaman yarinyar a gidan?" El-ameen ya hade rai yace "Sai ka korata nasu gidan don bata xo maka da gida ba, and tana tarewa gobe ita kuma xata tare ran lahadi don ranan Dr Sumayya xa su yi tafiya, tsaf ita ma kuma xa a gyara mata nata dakin" Junaid ya dafe kai yace "Ba haka ba frnd, kasan tana iya xuwa tayi reporting ma su Abba fa" El-ameen yace "Shit, gashi har xa a maka aure gobe baka xama mature person ba, ka ki girma har yanxu junaid, look yanxu you are going to leave a free.... When I say free I mean a free life, no more Mumy Mumy Mumy, you are going to head a family of ur own don haka ko wani decision kayi a gidan ka is right ba sai wanda parent dinka suka maka ba, from tomorrow you will be on ur own" junaid yace "Uhum?" Tsaki El-ameen yayi, can yayi kwafa yace "da rabon matar nan ta rainaka idan ta lura you don't have a say of ur own!" Mikewa Junaid yayi yace "Baka san ni ba kenan" daga haka ya fice daga office din.
42 MISSING
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
43.....
Washegari da ya kasance Friday tun sassafe El-ameen ya xo da leda me dauke da sabon dinkin dakakkiyar farar shadda me tsada sosai, dinkin yar ciki da babban riga, sai hula da takalma duk sabbi, tsokanarsa kawai yake yana dariya, shi dai Junaid wayarsa kawae yake dannawa daga kwancen da yake fuskar nan tasa babu yabo bbu fallasa, gefensa El-ameen ya zauna yace "Ko fa d'an gyaran fuska da gashi baka yi ba captain, haka xa mu kai ka?" Mikewa Junaid yayi xaune a fusace yace "look ka daina bata min rai Ahmad, bana son haka, it's not funny" El-ameen ya hade rai yace "Ka hayyako min kamar ni xan aurar da kai? Toh ni dai ban da ni a kai ka in har baxa ka tashi muje saloon ba" tashi daga xaunen junaid yayi fuskar nan tasa daure ya shige daki, El-ameen ya fashe da dariya yace "Oho dai, ana saukowa juma'a xa a daura..." Karfe tara fatima ta kawo breakfast parlon, El-ameen yace "Ina kawar ki Humainah?" Fatima ta ajiye abun hannunta ta gaishesa sannan tace "Tace anjima xa su taho da mamarta da na kirata" El-ameen yace "Toh idan kin koma ki ce ma Mumy Junaid na can yana ta kuka nayi lallashin duniyar nan yaki saurarata" fatima ta xaro ido lokaci daya ta fashe da dariya tace "Kai yaya" ya hade rai yace "Ba aiken ki nayi ba" juyawa tayi ta fita tana dariya. Karfe sha biyu da wani abu junaid ya shiga wanka, kan ya fito El-ameen har ya fito masa da sabbin kayan ya feshe su da uban turare, kallo daya junaid ya ma kayan ya nufi closet dinsa ya bude ya fito da wani blue shaddarsa, El-ameen yace "Ya haka ango ga sabon dinki nayi maka?" Ko kallonsa junaid bai yi ba ya ajiye kayan kan gadon ya xauna yana goge gashin kansa, tsaki El-ameen yayi ya mike ya dauke kayan ya mayar closet din ya sa key ya jefa makullin aljihunsa, kallonsa kawai junaid ke yi, can yace "You are provoking me El-ameen" El-ameen yayi dariya yace "oho dai tunda ba iya dukana xa ka yi ba, in baxa ka sa sabon dinkin ba ka tafi da singlet da short nicker gun daurin auren ma" yana murmushi ya fice masa daga dakin, Junaid ya fuxar da iska ya dafe kansa xuciyarsa na tafarfasa, ya kusa minti ashirin xaune sanin lokaci na wucewa ya mike yana kallon kayan da El-ameen ya ajiye masa, wani takaici ya rufesa, sai kace irin yana son auren, tsaki yayi ya fixgo rigar yana kallo, ya kusa wani minti goman tsaye ya sake jan tsaki ya xura rigar ya dau wandon ya sa, kayan suka haska sa sosai, da ganinsa ka ga Ango, toilet ya koma ya dauro alwala ya fito ya tafi gun hulunarsa ya dau daya ya gyara ya daura a kai ya dau takalminsa ma ya saka, ko agogo bae kalla ba bare ya fesa turare ya fice daga dakin rike da wayoyinsa. Kallonsa El-ameen ke yi daga sama xuwa kasa yace "Ina sabon takalmin da hular, kuma ina babban rigar?" Wani uban harara Junaid ya xabga masa yace "Baxan sa ba" El-ameen ya fashe da dariya yace "Oho dai bbu wanda zai ce wa ennan ma da ka sa ba sabo bane, nima bari in je inyi wankan in shirya as babban abokin ango" daga haka ya shige dakin, junaid ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, banda faduwa babu abinda gabansa yake wai shi xa a daura ma aure yau. Daya saura El-ameen ya fito daga dakin sanye da farar shaddar da ya dauka a closet din Junaid, shi ma yayi kyau har ya gaji, kallo daya Junaid yayi masa ya dauke kai, El-ameen ya xauna gefensa yana murmushi ya mika masa agogo yace "Here!" Dauke kai junaid yayi bai ce komai ba, El-ameen yace "Dama ka saki ranka ga su faisal nan xuwa, if not you will be the topic of discussion na cewa an maka auren dole, just pretend as if its nothing and you are happy..." Ko rufe baki El-ameen bai yi ba sai ga faisal da kusan abokansu har biyar, Junaid ya sauke ajiyar xuciya hade da sakar masu murmushi, tsokanansa suka shiga yi kamar shi ya kawo su, shi dai baya cewa komai sai murmushin da bai kai ciki ba, hotuna suka shiga yi gaba daya a parlon, daga bisanni suka fita don xuwa masallaci, sosai gidan ke cike da jama'a, Junaid yaji dama kawai ya gansa a waje ba sai ya bi ta compound ba, kallo aka bi sa da shi barin su Umma da bakin ciki ya cika su kamar su yi yaya, ko kayan arxiki basu saka ba ana xaune bakin murhu, El-ameen yace "Ya kamata ka je Mumy ta sa maka albarka kafin ka fita, sai ka ga anyi a sa'a" part din Mumy Junaid ya nufa, bai bi ta kan mutanen parlon ba ya shiga bedroom dinta ya sameta xaune tare da sisters dinta sai abokan arxiki, kallonsa take har ya iso gabanta ya durkusa cikin sanyin murya yace "Xa mu tafi masallaci Mumy" ta yi murmushi tace "Toh Allah ya tsare, yasa ayi a sa'a" ya sunkuyar da kai yace "Ameen" sai a sannan ya kalli Mutan dakin ya gaishesu ya mike ya nufi kofa, duk suka bi sa da kallon sha'awa ganin irin respect dinsa har ya fita, kanwarsa ce Aysha ta bi bayansa murmushi dauke fuskarta tace "Ya Ahmad" yace "Ya kike" tace "lafiya lau, tun jiya bamu hadu ba" yace "Eh ai kin san inda nake" daga haka ya ci gaba da tafiyarsa. Ana saukowa daga juma'ah aka daura aurensa da warce bai ma sha'awan sani yanxu kam a kan sadaki dubu dari biyu, bai wani tsaya gaishe gaishe ba ya xame ya bar wajen ba tare da El-ameen ma ya sani ba ya koma gida. Bayan isha junaid da El-ameen sai faisal na Parlor xaune Khadija ta shigo tace Abba na kiransa, mikewa yayi ya fita xuwa part din Abbansa, shi da Abban Humainah ne xaune parlon sai wani amininsa, Junaid ya samu waje ya xauna sannan ya gaishe su, nasiha suka yi masa banda Abbansa dake ta kallonsa, shi dai kansa na kasa, har suka kare cikin sanyin murya yayi masu godiya, Abbansa ya kara da cewa Allah yayi ma rayuwar aurensa albarka, yace "Ameen" Abokin Dad dinsa Alhaji Umar ne yace Ya tashi ya tafi don tuni aka kai masa matarsa, mikewa yayi bai ce komai ba ya fita daga parlon, part din Mumy ya tafi a sanyaye ya sameta ita da Ummin El-ameen a dakin, ya isa gabanta ya durkusa murya can kasa yace "Abba yace in tafi Mumy" Mumy tace "Toh Allah ya albarkaci rayuwar auren ka Ahmad, Allah ya baka xuri'a ma su yi maka biyayya kamar yanda kake min" kasa dago kansa yayi, lokaci daya idonsa ya kada, a hankali ya daura kansa kan kafarta cikin sanyin murya yace "Mumy ban san matar ba har yanxu" murmushi tayi ta dago kansa tana kallonsa sai dai bata ce komai ba, Ummi tace "kasan mahaifinka baxai maka xabin da xai cuce ka ba Ahmad, Allah ya baku xaman Lafiya, tashi ka je" mikewa yayi a hankali ya juya ya fita. Karfe tara saura suka bar gidan shi da El-ameen da faisal, xuwa yanxu kam sun daina tsokanarsa ganin yanayinsa, El-ameen ji yake kamar shi aka yi ma hakan yaji tausayinsa sosai, gun masu gasassun kaji El-ameen yayi parking ya fita ba a dau lokaci ba ya dawo rike da ledan kaji da drinks, tafiyar kusan minti talatin suka yi suka isa gidan Junaid, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya ya juya yana kallonsa bayan yayi parking a compound din, gidane duplex mai kyau da girman gaske, compound din ya kawatu da kayan shuke shuke iri iri ga haske ko ina kamar rana, faisal sai danne dariyarsa yake ganin yanda Junaid ya hade rai yana kallon gidan, El-ameen yace "Toh ni dai a nan xan bar ka, gobe da safe zan kawo maka motar ka" junaid ya kallesa yace "Haka koh?" El-ameen yace "Allah baxan shiga ba sai dai ko faisal" faisal yace "No, sai dai mu dawo ganin amarya gobe" El-ameen yace "Exactly" ficewa junaid yayi daga motar El-ameen yace "Wait ga kajin amarya baka dauka ba" ko saurarensa junaid bai yi ba ya nufi cikin gidan, El-ameen ya dauki ledojin ya bude motar ya fito yana dariya ya bi bayansa, tsaye ya gansa a parlor yana bin ko ina na parlon da kallo, kamshi me dadi ne ke tashi ta ko wani angle, komai na parlon brown nd milk, El-ameen ya karaso cikin parlon ya ajiye masa ledan a kasa yace "Sai da safe ango" junaid ya kallesa yace "Yanxu da gaske ba xa ka raka ni ba" El-ameen yace "Kila yanda gabana ke faduwa naka baya faduwa haka, I just can't, gobe dai xan dawo..." Daga haka ya fice daga parlon, Junaid ya sauke ajiyar xuciya ya kalli hanyar stairs, a hankali ya karasa ya haura sama, ya dde tsaye corridor din dakunan yana kallon kofar dakin da ya san tana ciki, karasawa yayi bakin kofar ya murda a hankali lokaci daya ya tura yana kallon cikin dakin, xaune ya ganta can karshen gado ta takure waje daya fuskarta rufe da babban veil, ya kusa minti biyu yana kallonta sannan ya karaso cikin dakin ya isa gabanta ya tsaya yana kare mata kallo yace "Ke kika ce ma iyayena kina so na?" Shiru bata ce komai ba, yace "Magana nake maki" Mikewa tayi xata bar wajen ya fixgota har sai da ta fado kansa fuskarsa daure yace "Ina maki magana xaki wuce" turasa tayi tace "Ni ka kyaleni, ko kuma kai kace kana so na ba" saketa yayi ya bude ido yana kallonta da mamaki, ta bude mayafin fuskarta ta hararesa ta bar wajen, rungume hannayensa yayi ya bi ta da kallo har ta xaga daya side din gadon ta xauna, murmushi kawai yayi ya fita daga dakin ya shiga nasa, wayarsa ya dauka ya shiga neman layin El-ameen, yana dagawa yace "Guess wacece amaryar" El-ameen yace "Uhun! Humainah!" Junaid yace "Ohh dama ka sani?" Dariya yayi yace "No! I only guessed" tsaki junaid yayi yace "Very funny wai Humainah, all the same xata yi girki dai ta gyara gida ta kula da jasmine, shikenan an wuce wajen" El-ameen ya xaro ido yace "Wacece jasmine kuma?" Shiru junaid yayi can yace "Sai da safe" daga haka ya ajiye wayar ya shiga cire kayan jikinsa, wanka yyi yayi alwala ya fito ya canxa xuwa jallabiya snn yayi shafa'i da wutr ya jima xaune kan darduma daga bisanni ya mike ya koma kan gado, har ya kwanta ya mike xaune, murmushi yayi da ya tuna wai fa Humainah ce matar da aka aura masa, wai Humainah, dariya ya fara yi, ita wannan har ta isa aure yarinyar da ko secondary bata kare ba, though yaji dadin da ya kasance ita ce don baxa ta wani bada wani matsala gun kawo jasmine gidan ba, tabe baki yayi ya mike ya fita ya koma dakinta, kwance ya sameta ta takure waje daya tana bacci, tabe baki yayi ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa can nesa da ita, ya kusa awa daya kwance kafin bacci ya daukesa, can cikin dare ya ji tana tashin sa, ya mike xaune ya kunna bedside lamp yana kallonta da kumburarrun idonta alamar ba kuka kadan tayi ba, yace "What?" Kamar xata yi kuka tace "Ni yunwa nake ji" ya kalli agogo ya ga sha biyu har ya gota yace "Yunwa? Baki ci abinci daga gidanku bane" tace "Eh ni ban ci ba" d'an tsaki ya ja yace "Toh ni yanxu ina xan samo maki abinci tsakar daren nan?" Tace "Ni dai wllh yunwa nake ji" ledan da El-ameen ya ajiye parlor ya tuna yace "Tafi parlor xa ki ga leda ki duba meye a ciki" ta xaro ido tace "Ni dai tsoro nake ji" ya hade rai yace "Xan fa kwada maki mari idan kina damuna ina bacci" ta fashe da kuka ta mike xaune, tsaki ya ja ya sauka daga kan gadon ita ma ta sauko ta bi bayansa da sauri, a tare suka sauko parlon ya kunna wuta ya dau ledan ya bude ya nufi kitchen ya dauki plate da wuka da fork sai cup ya fito, nan parlon ya dawo ya xauna kan rug ya fiddo kaza daya ya Yanyanka a plate yana kallonta yace "Ga shi" matsowa tayi a hankali ta dau daya ta fara ci, ya mike yace "Idan kin gama ki kashe wutan parlon" da sauri ita ma ta mike tace "Don Allah ka jira ni ya A.jay wllh tsoro nake ji" ya hade rai yace "Kina fa damuna" ta d'an marairaice ta koma ta xauna ta ci gaba da cin kazar, xaunawa yayi shi ma yace "Idan sha biyu da rabi yayi baki gama ba xan yi tafiyata" ta d'an hararesa bata ce komai ba, dauke kai yayi sai dai lokaci lokaci ya kan saci kallonta, suna hada ido yyi saurin cewa "Haka aka koya maki a gidan ku Idan xaki kwanta kar ki cire kayan da kika yini da?" Tace "Kai ma ai gidanku ne" bai kuma ce mata komai ba har ta gama, ta mike ta dau plate din tace "Raka ni kitchen" harararta yayi ta rama ta nufi kitchen, ya bi ta da kallo, tana fitowa ya mike ya kashe wutan parlon yyi hanyar stairs ta bi bayansa da sauri suka shiga dakin a tare, wutan dakin ta kunna yace "Meye haka?" Tace "Xan wanke baki mana" gado ya nufa yayi kwanciyarsa ta shiga toilet, ba a dau lokaci ba ta fito ta nufi closet ta bude ta fiddo doguwar riga da hijab ta koma bayin, tana fitowa tayi kwanciyarta nesa da shi ta juya masa baya, yace "Ke wa kika bar ma wuta a kunne?" Tace "Nafi son haka, ni bana son duhu" tsaki yayi ya mike ya tafi ya kashe wutan kan ya dawo har ta mirgino ta dawo gefensa, yayi kwanciyarsa hade da juya mata baya.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
44 & 45 .....
Da asuba Junaid ya dade xaune gefen gado daga bisanni ya mike, kallo daya ya ma Humaina dake bacci ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito har xai fita xuwa masallaci ya dawo ya isa kusa da gadon ya buga kafarta, bude ido tayi a hankali tana kallonsa ya juya ya fita daga dakin, ko da ya dawo daga masallaci samun ta yayi kwance tana bacci har lokacin, bayi ya shiga ya debo ruwa ya fito ya watsa mata, ta mike xaune da sauri tana kallonsa, yace "Sllh!" Daga haka ya fita daga dakin, tsaki tayi ta bi sa da harara ta sauka daga gadon ta shiga bayi. Tana idar da sllh tayi jigum kan darduma, can ta mike ta shiga gyaran bedroom din, tana gamawa ta shiga bayi ta wanke baki tayi wanka ta wanke bayin ta fito daure da towel, gaban mirror ta xauna ta gama shafe shafenta sannan ta shirya cikin Abaya baki da veil dinsa ta d'an gyara fuskarta ta koma gado ta xauna tayi tagumi. Bude kofar dakin aka yi fatima da khadija suka shigo, Humainah ta mike da sauri lokaci daya tayi murmushin jin dadin ganinsu, fatima tace "Uhum Amaryar yayarmu, Antynmu!" Hade rai tayi can ta fashe da kuka tace "Ni ba amaryarsa bace, ai Hajja tace sbda a raba sa da mahaukaciyar nan ne aka aura masa ni, amma da ya rabu da ita sai a sa ya sakeni in ci gaba da karatuna" innocently tayi maganar tana kallonsu, Khadija da fatima suka fashe da dariya barin khadija, juyawa Humainah tayi a sanyaye ta koma gefen gado ta xauna, hade kanta tayi da gwiwa tana kuka, fatima ta karasa kusa da ita da sauri tace "Toh ai ba mu ce ba haka bane ba fa Humainah" Humainah ta girgixa kai tana kuka tace "Ba wani nan nasan wayo aka min baxa a ce ya sakeni ba, yar yarinya da ni xan je ss3 za ayi ma aure bayan ku ba a maku ba....." Khadija ta xauna gefenta tace "Ni dai ba dariya nake maki ba, ba ruwana, ga abinci Mumy tace a kawo maki" Humainah ta dago kanta tana share hawayen idonta tace "Hajja fa?" Khadija tace "Ta ce anjima xata xo" Junaid ne ya shigo dakin ya tsaya daga bakin kofa yana kallonsu yace "A baki aka ce ku bata abincin?" Kallonsa suka yi gaba daya basu ce komai ba, ya nuna masu kofa duk suka mike, Humainah ta hade rai tana kallonsa tace "Ba yanxu xa su tafi ba toh" Ko kallonta bai yi ba, ganin su fatima sun nufi kofa kamar xata fashe da kuka tace "Don Allah kar ku tafi" murmushi fatima tayi ta raba ta gefen yayan nata ta fita khadija ta bi bayanta, kuka sosai Humainah ta shiga yi, ya karaso cikin dakin ya xauna d'an nesa da ita yace "baki san ke ba yarinya bace yanxu tun da har aka aurar da ke" hade rai tayi tana kallonsa tace "Ni dai yarinya ce" murmushi yayi yace "Toh naji! tsoron xama ke kadai kike a dakin da kike son su xauna da ke?" Ta kallesa hade da gyada masa kai, yace "Toh xan samo maki warce xata dinga taya ki xama ai kina so?" Tana kallonsa tace "Amma babba ce?" Ya girgixa mata kai yace "No yar yarinya ce kamar ki sai ta dinga taya ki xama kuna kwana ma tare" sosai ta hade rai tace "A'a bna so, xan iya xama ni kadai" shiru yayi yana kallonta, can yace "Saboda me?" Ta mike tace "Haka nan kawai, xan iya xama ni kadai abuna" daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, lumshe ido yayi ya bude yana naxarin abinda ta ce, Mikewa yayi shima ya fita daga dakin ya koma nasa. Karfe sha biyu saura aka danna bell downstairs, Junaid dake bedroom dinsa yana danne dannen waya ya mike ya fita, dai dai lokacin da Humainah ma ta fito, kallo daya yayi mata ya sauka ya je ya bude kofar, Hajja ce tsaye bakin kofar da Sadiya, ta washe hakora ganin Junaid tace "A'a ango, to gani na biyo ka don kayi amarya sai ka mance da uwar gida?" Juyawa yayi ya bar bakin kofar ya koma parlor, Hajja ta shigo tare da Sadiya da gudu Humainah ta sauko jin muryar Hajja ta rungumeta, Hajja tace "Lalala kinga yanda kika yi kyau kika yi fresh kuwa? Lallai Amadi ya iya kiwo daga jiya xuwa yau" hade rai Humainah tayi tace "Ni babu abinda ya ban na ci har yanxu" Hajja tace "Ehh amma ai kin kwan masa a gida" turo baki tayi ta tafi ta xauna, Hajja ta kalli Junaid tace "Banxa kai kuma ko ka kira ka mana godiya ka ga xukekkiyar amarya ba mahaukaciya ba" Kallonta kawai yake can ya tabe baki yace "Nii ban gode ba tun da ban ce ina so ba, kawai makala min aka yi" Humainah ta fashe da kuka tace "Hajja kin dai ji ko, ni dai tare xa mu koma don ni ma makala min aka yi ban ce ina so ba" Hajja ta hade rai tace "Kai kaga irin hada ta da Allah annabin da aka dinga yi don ta amince da gantalallen auren ka, banda kaddara me xata yi da kai Ahmad, kai da cikakken saiti baka da, wllh wllh 'yar nan tafi karfin ka, kawai ka kara gode ma Allah da ya sa aka baka ita" juyawa tayi tana kallon Humainah tace "ke kuma kar ki kuskura ki bari ya kwana dakin ki tunda haka yace, hanyar jirgi daban ta mota daban kin dai ji ni..." Humainah ta gyada mata kai tana goge hawayen idonta, Hajja ta nemi kujera ta xauna tana cewa "Banda walakanci an samu an lallaba yarinya da kyar ta amince ta rufa maka asiri ta aureka xaka dinga gaya mana magana, ko fa kwandalar ka bbu a bikin nan don tsiya.... Amma bari na fi ka iskanci sai ka xo ka durkusa kana rokona in ce mata ta so ka" girgixa kai Junaid yayi ya mike ya haura sama abun sa. Har Karfe uku Hajja na gidan ita dai Sadiya dama turo ta aka yi ta ga kwakwaf ta ga yanda gidan yake da abubuwan da aka xuba, tana gama abinda ya kawota ta kara gaba ta bar Hajja. Har dai bayan la'asar Hajja bata da niyar tafiya Junaid ya rasa me suke kullalawa a dakin gashi El-ameen ya ki xuwa saboda Hajjan, mikewa yayi ganin har biyar ya gota ya shiga dakin, suna ganinsa suka yi shiru, Hajja ta hade rai tace "To ya aka yi kuma?" Ya d'an shafa kansa yace "Kawu Abubakar ne ya kira wai yana ta jiran ki xai koma" mikewa Hajja tayi da sauri tana xuge yar purse dinta tace "Auu bawan Allah to bari in je" Humainah ta marairaice kamar xata yi kuka tace "Yanxu tafiya xa kiyi ki bar ni Hajja" Hajja ta hade rai ta kalli Junaid sai kuma ta duka kusa da ita murya can kasa tace "Kin dai ji abubuwan da na gaya maki dai koh?" Humainah ta gyada mata kai, Hajja ta mike tace "Ehh to ba dole in tafi ba Humainah, amma ina nan dawowa kila ma da kayana xan taho tunda ai jikokina ne ko na xauna bbu komai" daga haka ta nufi kofa tana cewa "Toh kai d'an ubanka xaka kai ni gidan ne ko in je in hau machine tunda Sadiya sun koma da driver" ficewa junaid yayi daga dakin ita ma ta fita tana cewa "Toh Humainah sai Allah ya sake dawo da ni" har gida Junaid ya ajiye Hajja sannan ya kira El-ameen yace "Toh ta tafi, am waiting for you" daga haka ya katse wayar ya kama hanyar gida. Kusan a tare suka iso gidan da El-ameen, El-ameen yayi parking ya fito yana murmushi yace "Daga ina haka ango?" Junaid yace "Nayi dropping dinta mana" bude motar El-ameen yayi ya shiga yana kallonsa yace "Tabdi gaskiya Humainah ta karbe ka, ka ga yanda ka kara kyau yau kuwa" girgixa kai Junaid yayi yace "Kaga ni mu yi maganar arxiki, kasan kuwa yarinyar nan tace ita bata son a kawo mata kowa gida?" El-ameen ya hade girar sama da ta kasa yace "Kamar ya? Kaga matsalar ka ko Ahmad, daga aure har yarinya xata fara raina ka tana fadin abinda xa ayi a gidan da wanda baxa ayi ba, gidan ta ne da har xata gaya maka abinda xa ayi? Kai wani irin Human being ne junaid" Shiru Junaid yayi yana kallonsa, can ya sauke ajiyar xuciya yace "Am afraid kar ta ce xata gaya ma su Mumy ne shi yasa ban ce komai ba" El-ameen yace "Tabdi! Yarinyar nan fa wllh sai kayi gaske da ita Idan ba haka ba second Mumy dinka xata xama, naga alamar fitinanniya ce, shikenan kai kuma ka xama abun tausayi baka da say a duniya sai na Mumy da wife, haba sai kace ba captain ba kawai ka cika ma kanka girman kai da miskilanci maimakon being ur own self, ita wannan har ta ma wuce ka bubbuge ta Idan tace xata kawo maka rainin hankali" girgixa kai junaid yayi hade da yin murmushi yace "Uhum lallai" horn ya danna aka bude gate ya shiga da motar yayi parking ya juya yana kallon El-ameen, El-ameen yace "Toh gobe dai Dr Sumayya xata yi tafiya ban kuma san inda xan kai patient dinka ba" junaid ya bude motar ya fita shima ya fito suka shiga cikin gidan. Parlor El-ameen ya xauna junaid ya haura sama ya sameta xaune ta kunna kayan kallon parlon, yace "Ki fito ku gaisa da abokina" Ta hade rai tace "Baxan fita ba ni indai wannan El-ameen din nan ne" juyawa yayi ya bar dakin ya koma parlo, El-ameen yace "Xuwa kayi kace ta sauko?" Junaid bai ce komai ba ya xauna, El-ameen yace "In dai nine ta rike gaisuwar ta, kaga ni kasan yanda xa ayi kafin gobe, yanxu clinic xan tafi" Junaid yace "Dama baka yi niyar xuwa yau ba kenan koh?" El-ameen yace "Da wata daban ce matar ba wannan fitsararrar ba" dariya junaid yayi ya mike ya rakasa har waje gun motarsa, Junaid yace "But ka gaya min yanda ya kamata inyi approaching dinta har ta amince" El-ameen yayi murmushi yace "Babu abinda ka iya a rayuwa sai sa uniform da yi ma Mumy biyayya kamar yaya, all the same xan kira ka later dai" daga haka ya shiga motarsa ya tada ya bar layin. Da daddare shinkafa da miyar da Mumy ta aiko masu ya diba ya ci, ya jima xaune parlor yana tunanin yanda xai shawo kan Humainah ta amince da xuwan jasmine gidan ganin har lokacin El-ameen bai kirasa ba, Karfe goma kiran El-Ameen ya shigo wayarsa ya daga, sun dade suna waya har kusan karfe sha daya daga karshe suka yi sallama Junaid ya ajiye wayar, murmushi kawai yake ba wai don yasan dalilin murmushin shi kansa ba, mikewa yyi ya haura sama ya shiga dakin sa, wanka yayi ya fito ya saka pyjamas dinsa ya xauna gefen gado har sha biyu yayi sannan ya mike ya fita daga dakin ya nufi nata, a hankali ya tura kofar ya shiga ya rufe, kwance ya sameta waje daya tana bacci tv a kunne ga remote kusa da ita alamar kallo take bacci ya dauketa, kashe wutan dakin yayi ya karaso ya xauna gefenta yana kallonta doguwar rigar bacci ne jikinta sai net da ta xura gashinta ciki, haka kawai ya ji gabansa na faduwa, a hankali ya kira sunanta, da sauri ta bude ido don ba wani nisa baccin nata yayi ba, ta mike xaune tana kallonsa, pillow ta jawo ta daura jikinta tace "Me ya faru?" Ya d'an bude ido yace "Magana xa muyi" kalle kallen inda hijab dinta yake ta shiga yi, can ta turo baki tace "Ina jin ka" mikewa yayi xai dawo kusa da ita, da sauri tace "A'ah a'ah ka tsaya a nan mana ai ina jinka" sunkuyar da kai yayi yana murmushi ya xauna, murya can kasa yace "Saboda me kika ce baki son warce xata taya ki xama?" Hade rai tayi tace "haka nan" a hankali yace "kinga Idan na fita aiki tun sassafe fa sai yamma nake dawowa, baxa ki iya xama ke kadai a babban gidan nan ba sbda in some cases sai ki ga akwai aljanai a babban gida haka" xaro ido tayi ta matso kusa da shi a hankali tace "Aljanai kuma Ya A jay?" Yace "Of course tunda sabon gida ne ba a taba rayuwa ciki ba" kamar xata yi kuka tace "Toh ai Abbana yace min xa ka sa ni school soon, kaga sai ka sama min from 7 to 6 kaga kenan tare xamu dinga dawowa gidan" ya d'an hade rai yace "Nan da sati biyu fa xan je Lagos inyi aiki a can to ke kadai xa ki xauna?" Tace "A'ah to ba sai in je gun su Mumy kafin ka dawo ba" dauke kai yayi can ya juyo yace "Toh Idan tare xamu lagos din fa, kenan Idan na tafi aiki ke kadai xaki yi ta xama can din ma" kamar xata yi kuka tace "Toh mai aiki xaka sama min kenan?" Ya girgixa mata kai yace "A'a ba mai aiki bace amma xata dinga taya ki aikin" hade rai tayi tace "Wai wacece ita ya Ahmad?" Kamo hannunta yayi a hankali yace "Idan ta xo xa ki ganta, nd you will like her, bata da matsala" fixge hannunta tayi tana komawa baya tace "Aljanan su cinye ni wllh kuma ni kar ka sake cewa wata xata taya ni xama xan gaya ka da su Mumy da....." jawota yayi jikinsa ba shiri tayi tsit ta fara turasa tace "Meye haka ya A jay" a hankali ya daura bakinsa kan wuyarta, lokaci daya ranan da ta gansa da Muhibba a daki ya fado mata, ta fasa ihu a tsorace tana kokarin kwace kanta tace "Don Allah ya Ahmad ka yi hakuri ka kyaleni bana so" murya can kasa yace "Meye ba kya so?" Da kyar muryarta na rawa tace "Toh to naji wacece xata taya ni xaman?" Dago kanta yayi yana kallonta, tsoro fal ya ga cikin idonta, yayi murmushi yace "Kin dai amince ta xo sai ki ganta" kai ta shiga gyada masa da sauri, a hankali ya saketa yace "Gobe da safe xa a kawo maki ita" komawa baya take tana gyada masa kai, yayi murmushi ya mike ya kashe kayan kallon dakin, kamar xata yi kuka ta isa gun bedside lamp da sauri ta kunna tace "Wayyo me yasa ka kashe" xagawa yayi daya side din ta bi sa da kallo yayi kwanciyarsa tare da juya mata baya, ajiyar xuciya ta sauke a hankali ita ma ta kwanta, juyowa yayi ta mike xaune da sauri kamar xata yi kuka, yace "Ki kashe wutan nan da kika kunna" girgixa masa kai tayi tace "Plss ya Ahmad bana son duhu" mikewa xaune yayi tana ganin haka ta kashe wutan da sauri tace "Oya yi hakuri kwanta na kashe" dariya ta basa ya koma yayi kwanciyarsa, bayan kusan minti ashirin yaji ta birgino a hankali gefensa ta kwanta. Da asuba ya tasheta yin sllh ya fita daga dakin xuwa nasa, yau ma kamar jiya daga gida aka kawo masu breakfast, tea kawai junaid ya sha yayi kwanciyarsa a parlor yana jiran xuwan El-ameen don ya kirasa yace suna hanya, Karfe goma saura El-ameen ya shigo compound din da motarsa, mikewa junaid yayi ya nufi kofa ya bude, El-ameen ne ya fara fitowa ya xaga ya bude mata side din da take ta fito, sanye take da atamfa da hijab dinta fari har kasa, kallonta junaid yake ko kiftawa bai yi, El-ameen ya rufe motar ya bude baya ya fiddo jakar kayanta yana kallonta yace "Mu je baby" kallon gidan take ba tare da ta yi motsi daga inda take ba, yayi murmushi ya shiga gaba ya fara tafiya, bin bayansa tayi kamar me tausayin kasa, ya juya yaga tana biye da shi ya ci gaba da tafiyarsa, kallonsu junaid yake har suka iso balcony ya lumshe ido ya bude ya basu hanya, El-ameen ya juya yana kallon Jasmine ya ga ta ki karasowa, yace "Come on mana" a hankali ta shiga tahowa Junaid ya bi ta da kallo har suka shiga parlon, juyawa yayi ya bi bayansu, El-ameen ya nuna mata kujera ta xauna bayan ya ajiye kayanta da ke hannunsa shi ma ya xauna yace "Baby ba ki gaishesa ba" ya fadi hakan yana nuna mata Junaid, kallon junaid tayi da fararen idonta a hankali tace "Ina kwana" kasa amsawa yayi ya d'an mata murmushi kawai, sosai haskenta ya kara fitowa da gani kasan ba karamin kulawa take samu gun Dr Sumayya ba, Humainah ce ta sauko parlon jin shigowar mota, kallonsu ta shiga yi da d'ad'd'aya da d'ad'd'aya daga inda take tsaye duk da ba ganin fuskokinsu take ba, El-Ameen ya hade rai, ta karaso cikin parlon idonta ya sauka kan jasmine still tayi gabanta yayi mugun faduwa tana kallonta, Junaid yace "Amm.... Kin ganta she will keep you accompany ana kiranta da Baby...." Wani kallo Humainah ke mata, can tayi dariyar rainin hankali tace "Ko kuma placenta ba!" Lokaci daya ta hade rai tace "Ita mahaukaciyar ce xata yi keep dina company??" Strictly El-ameen yace "Kar ki kuma kiranta da mahaukaciya" hararansa tayi tace "Toh ni dai baxa ta xauna gidan nan ba, kai ka yi auren ka kai ta gidan ka mana" sai kuma ta fashe da kuka ta haura sama da sauri, Junaid ya kalli El-ameen, El-ameen yayi tsaki yace "Wllh da ma bare kawai aka sama maka da wannan yar tashar! An hada ka da balaa'i kawai" junaid ya sauke ajiyar xuciya ya mike jiki ba kwari ya bi bayanta, a hankali Jasmine ta mike ta dawo kusa da El-ameen ta durkusa kusa da shi cikin sanyin murya tace "Uncle ni ka kai ni gida gun Mami" sunan da suke kiran Dr Sumayya da shi kenan, shiru El-ameen yayi yana kallonta, ta d'an taba hannunsa tace "Uncle!" Kifta ido yayi da sauri ya shafa kansa a hankali yace "Toh xan kai ki" xaunawa tayi nan kasa kusa da shi tana kallonsa murya can kasa tace "Uncle Meye meaning din mahaukaciya?" Shiru yayi nan ma yana kallonta, ta bude manyan idonta tace "Idan mun je gida in tambayi farida?" Murmushi ya mata hade da gyada mata kai.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
46.....
Kwance junaid ya sameta tana kuka a dakin, ya karasa ya xauna kusa da ita ya dago ta, turasa ta shiga yi cikin kuka take cewa "Ni ka kyaleni, ka kyaleni" a hankali yace "Listen to me plss Humainah, ba fa mahaukaciya bace" ta fashe da matsanancin kuka tace "Nace ka kyaleni ni dai" saketa yayi yana kallonta, ta koma ta kwanta tana ci gaba da kukanta, mikewa yayi ya fita daga dakin ya koma parlor, El-ameen dai kallonsa kawai yake bai ce komai ba, Junaid ya xauna ya shafa kansa yace "Shknn you can go Idan tafiya xaka yi" El-ameen yace "Toh gimbiyar taka ta yarda kar in tafi in bar yar mutane ta kasheta kana kallo" Junaid yace "In xaka tafi kayi tafiyar ka kawai" mikewa El-ameen yayi yana kallon Jasmine yace "Baby xaki tsaya nan har in dawo kin ji" kallonsa kawai take, ya durkusa kusa da ita yace "Kin ji?" Idonta ne ya cika da hawaye, a hankali El-ameen yace "Kuka kuma baby" shi dai junaid kallonsu kawai yake, El-ameen ya ciro handki ya mika mata yace "baxan dade ba xan dawo kin ji" karba tayi ya mike ya kalli Junaid sannan ya fita daga parlon. Kallonta kawai Junaid ke yi kanta a kasa tana fidgeting fingers dinta, can ya mike ya kullo kofar sannan ya dawo ya dau jakar kayanta yace "Tashi mu je" mikewa tayi a hankali tana kallonsa ya d'an mata murmushi yace "Follow me" daga haka ya nufi stairs ta bi bayansa, dakin dake kusa da na Humainah ya bude ya shiga ta tsaya daga bakin kofa tana kallon dakin, juyawa yayi yana kallonta yace "Shigo mana" a hankali ta shiga dakin ya rufe kofar, kan gado ya ajiye jakarta ya bude closet yace "Ki ajiye kayan ki duka a nan kin ji?" Sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, ya nuna mata kofar bayi yace "ga toilet nan" kallon kofar tayi ta gyada masa kai, yace "Are you hungry?" Girgixa masa kai tayi da ganinta kasan a tsorace take, yayi murmushi ya kunna mata tvn dakin yace "Ki xauna kiyi kallon ki toh" ta gyada masa kai ya juya ya fita daga dakin ya rufo mata kofar, da sauri ta mike ta nufi kofar ta bude, yana tsaye bakin kofar Humainah ya juyo yana kallonta, dawowa yyi yace "Ya aka yi?" Kamar xata yi kuka tace "ina jin tsoro" shiru yayi yana kallonta ta bude kofar sosai ta koma ta xauna a dakin, Dakin Humainah ya karasa ya bude ya shiga ya sameta har lokacin tana kuka ya rungume hannayensa yana kallonta, can ya karasa kusa da gadon ya xauna yace "Ke yanxu baxa a iya cin arxiki gun ki ba, baxa ki yi taimako ba, kwana biyu fa kawai xata yi ta bar gidan" ko kallonsa bata yi ba ya dagota ya rungumeta yace "plss mana, wllh xata bar maki gidan soon, she's not staying long" turasa tayi tace "Bana so, kuma ni ka rabu da ni" hade rai yayi ya saketa ya mike yace "Toh wai gidan ki ne nan din? Ko a kanki take xaune" dago kai tayi tana kallonsa, ya watsa mata wani kallo ya juya ya fice daga dakin, wani sabon kukan ta fashe da har da shessheka. Dakin sa ya koma ya kwanta yana tunanin anya decision din da yayi na kawo jasmine gidan yayi daidai kuwa, har aka kira Azahar yana kwance, mikewa yayi daga karshe ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito, nan dakin yayi sllh yana xaune kan darduma bayan ya idar aka danna bell din gidan, mikewa yayi ya fita har lokacin dakin da jasmine take a bude yake, parlor ya sauka ya bude kofa, fatima da khadija ne bakin kofar rike da flask din abinci, gaishesa suka yi ya karba yace "Mun gode, ku gaida mutan gidan," daga haka ya kulle kofar ya dawo cikin parlor, plate ya dauko a kitchen ya dibi couscous din dake cikin flask din ya bude na miya ya diba sannan ya rufe ya dau goran ruwa da cup da spoon ya haura sama, dakin da jasmine ke ciki ya shiga, kwance ya ganta a kasa ta takure waje daya tana bacci, ya shigo dakin ya ajiye abincin hannunsa yace "Jasmine" sau uku yana kiranta ganin bata tashi ba ya durkusa gabanta ya d'an taba ta, bude ido tayi ta mike xaune da sauri ganinsa, yayi mata murmushi ta sunkuyar da kai, yace "Me yasa baki kwanta kan gadon ba" shiru tayi bata ce komai ba, ya dauko darduma ya shimfida a kasa yace "Dawo nan" mikewa tayi ta xauna kan darduman ya ajiye mata abincin da ruwa a kai yace "ga abinci ki ci" kai ta gyada masa, yace "Toh ci mana" a hankali ta dau spoon din da dibi abincin ta kai baki tana kallonsa, murmushi ya mata yana kallon yanda take tauna abincin, yace "You like it?" Kai ta gyada masa, ya mike yace "Toh maxa ki cinye kafin in dawo" daga haka ya fita daga dakin ta bi sa da kallo. Ko da ya dawo xaune ya sameta ta tura abincin gabanta tayi jigum, ya karaso ya durkusa gabanta yace "Baki ci ba kuma" ta girgixa masa kai a hankali tace "Na ci" yace "No! kadan kika ci" spoon din ya dauka ya dibi abincin ya kai mata baki, a hankali ta bude bakin ya xuba mata, haka ya dinga bata har abincin yayi rabi ta kauda kai tace "Na koshi" ajiye spoon din yayi yana kallonta yace "Toh tashi ki je kiyi alwala ki xo kiyi sllh" mikewa tayi ta nufi toilet yace "Baki cire hijab din ki ba" dawowa tayi ta cire Hijab din ta ajiye, ya bi ta da kallo har ta shiga toilet din sai dai bata rufe kofar ba, mikewa yyi ya fita ya koma dakin sa. Lokaci lokaci ya kan lekota, tausayinta kawai yake ba kadan ba barin yanda ya lura duk a tsorace take, ana kiran sllh magrib ya shigo dakin bai ganta ba, kiranta ya shiga yi amma shiru ya juya ya fita ya sauko downstairs, kitchen ya sameta tana wanke d'an plates din da aka bata, ya tsaya bakin kofa yana kallonta, da sauri ta juyo a tsorace, wara ido yayi yace "Uhum!" A hankali tace "washing nake yi" murmushi yayi mata yana gyada mata kai, ta juya ta ci gaba da wanke plates din, yace "Me xa ki ci for Supper?" Ta juyo tace "Supper?" Ya gyada mata kai yace "Yea dinner" ta d'an langwabar da kai a hankali tace "na koshi" wara ido yayi yace "me kika ci?" juyawa tayi ta ci gaba da wanke wankenta. Har ta gama yana tsaye bakin kofar, ta juyo tana kallonsa, murmushi yayi mata ya fita daga kitchen din ta bi bayansa suka haura sama, yace "Tafi kiyi sllh" kai ta gyada masa ta shiga dakin da take, shi ma ya shiga nasa. Ana idar da sllh ya tafi siyo masu abinci, ajiye abincin yayi a parlor bayan ya dawo ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera, can ya mike ya shiga kitchen ya dauko plate ya dau take away daya ya juye ya sa spoon ya dau ruwa ya tafi sama, xaune ya sameta bakin kofar dakin tana ganinsa ta mike tsaye, yace "uhum!" a hankali tace "Tsoro nake ji" kallonta ya tsaya yi kafin ya shigo dakin ya ajiye mata abincin hannunsa yace "Toh xo ki ci abinci" ta karaso ta xauna inda ya ajiye mata abincin, bin sa da kallo tayi har ya fita sai dai bai rufe mata kofar ba. Har xai shiga dakinsa ya tsaya ya kalli dakin Humainah, karasawa yayi ya bude kofar, xaune ya ganta can karshen gado kanta hade da gwiwa, a hankali ya karasa kusa da ita ya xauna yace "Still crying?" Mikewa tayi xata bar wajen ya fixgota ya ce "Ina xa ki?" Ta fashe da kuka sosai, rungumeta yayi a hankali yace "Alryt am sorry, kiyi hakuri... She's going tomorrow tun da baki so" boye fuskarta tayi jikinsa tana kuka a hankali, yace "Toh ba nace kiyi hakuri gobe xata tafi ba" muryarta na rawa tace "Toh wacece ita" dago kanta yayi yana kallonta, can yace "Ohk I will tell who she is" janyeta yayi a jikinsa ya koma baya yana kallonta yace "Amma fa it's a long story" sunkuyar da kanta tayi, nan ya fara bata labarin ynda ya hadu da jasmine har xuwa wannan lokacin, kallonsa kawai take ko kiftawa bbu bata kuma ce komai ba, ya lumshe ido ya bude yace "Tana regaining memorynta Idan Allah ya yarda xa ta koma gun iyayenta, ita din abun tausayi ce, a yanxu bata da kowa sai mu da muka taimaketa" dauke kai Humainah tayi, ya matso kusa da ita yace "Baki ce komai ba" turo baki tayi tace "Toh ka kai ta gidansu El-ameen mana" murmushi yayi yace "In tambaye ki" ta dago kai tana kallonsa, yace "wai kishi na kike Humainah?" Hade rai tayi tace "Kamar ya? Sbda me xan yi kishin ka" yace "Toh me sa baki son ta xauna nan?" Tabe baki tayi tace "Ta xauna mana ni ina ruwana, kawae abinda na sani ka kai ni sch next week" murmushi yayi ya mike ya fita daga dakin, abinci ya dauko mata ya ajiye dakin yace "Ga abinci!" Ko kallonsa bata yi ba ya fita daga dakin. Karfe tara da wani abu ya mike daga kwancen da yake ya fita xuwa gun Jasmine, xaune ya sameta bakin kofa tayi jigum, ya d'an bude ido yace "kina nan har yanxu" mikewa tsaye tayi kamar xata yi kuka tace "Ni kadai xan yi bacci a nan?" Kallonta kawai yake ya ga hawaye idonta, girgixa mata kai yayi yace "A'a ba ke kadai xaki kwana ba, ina xuwa" daga haka ya fita ya shiga dakin Humainah, xaune ya sameta daure da towel gaban madubi, hade rai tayi tace "Kaya xan sa" yace "Uhm did I hold you?" Marairaice masa tayi tace "Ka fita plss" karasowa yayi kusa da ita ta mike da sauri, ya d'an bude ido yace "what?" Kamar xata yi kuka tace "Ka fita plss" yace "Alryt xan fita, amma abokiyar kwana xan kawo maki" kallonsa tayi da sauri tace "Kamar ya?" Yace "ku kwana tare da yarinyar plss" da mamaki take kallonsa tace "Mu kwana?" Matsowa yayi kusa da ita ta koma baya da sauri tace "Wayyo ya A jay ka fita plss" ya langwabar da kai yace "Toh in kawo maki ita?" Gyada masa kai tayi da sauri, yayi murmushi ya juya ya fita ta bi sa da kallo, tsaye ya samu Jasmine a daki tana ganinsa ta nufesa da sauri ta juya masa baya tace "Cire min abun" kallon Zip din kawai yake daga sama xuwa kasa na kusan minti daya, ta juyo a hankali tana kallonsa, kifta ido yayi da sauri yace "Na'am" a hankali tace "Ban iya cirewa ba, Mami da farida suke cire min" gyada mata kai ya shiga yi kamar kadangare, ta kuma juya masa baya, yayi baya da sauri yace "Ohk Ohk mu je a cire maki nima ban iya ba" daga haka ya nufi kofa ta bi bayansa, dakin Humainah ya shiga ita ma ta shiga, kallonta kawai Humainah ke yi daga sama xuwa kasa gabanta na faduwa, karasawa Jasmine tayi kusa da ita ta juya mata baya a hankali tace "ki cire mun abun" kallon Junaid Humainah tayi, ya gyada mata kai yace "Help her wai bata iya ba" da kyar Humainah ta daga hannu ta xuge mata Zip din, kokarin cire rigar ta shiga yi da sauri Junaid ya juya har yana buge kofa ya fita daga dakin, Jasmine ta kuma kallonta tace "Baki cire dayan ba" Humainah ta balle mata bra din ta koma gaban madubi, bin ta da kallo Jasmine tayi tace "Ina san inyi wanka" ko kallonta Humainah bata yi ba, Jasmine ta bi ta tace "Xan yi wanka" ba tare da Humainah ta kalleta ba ta nuna mata kofar bathroom, Jasmine ta nufi kofar ta bude ta shiga, a bude ta bar kofar, Humainah ta mike ta koma gefen gado ta xauna xuciyarta na bugawa, har Jasmine ta fito daure da towel dinta, ta gefen ido kawai Humainah ke kallonta, ta iso kusa da ita tace "cloth dina" Humainah ta hade rai tace "ki saka wanda kika cire mana" "toh" kawai jasmine tace ta tafi inda kayan da ta cire yake ta dauka ta sa ta kuma dawowa ta durkusa kusa da ita tace "Sa min" xuge mata Zip din Humainah tayi ta kwanta abunta, jasmine ta mike ganin ta kwanta ita ma ta kwanta nan kasa. Junaid na fitowa daga wanka ya dau wayarsa dake ring ya ga El-ameen ne ke kiransa, dagawa yayi El-ameen yace "Matar taka ta hakura dai koh?" Junaid yace "May be" El-ameen yace "Kasan me, bata yarda fa ta kwana ita kadai ya xa ayi gashi amarci ku ke ci...." Junaid yace "Ko kuma angwanci ba" El-ameen yace "Serious xata yi ta maku ihu ne cikin dare bata yarda ta kwanta ita kadai" junaid yace "ta gaya min, tana dakin Humainah yanxu ma" El-ameen yace "Ohk bata waya plss" Junaid yace "Kace mata me?" El-ameen yace "kai dai ka bata" shiru junaid yayi can yace "Naji" katse wayar yayi hade da yin tsaki ya saka jallabiyarsa ya fita daga dakin, da sallama ya tura kofar dakin Humainah ya d'an bude ido ganin jasmine kwance a kasa ya karasa ya durkusa kusa da ita yace "Me ya sa kika kwanta a nan" shiru tayi bata ce komai ba, ya kalli Humainah ya ga rufe idonta ma tayi, jasmine ya kuma kallo yace "Tashi ki hau gado" mikewa tayi ya nuna mata daya side din gadon ta xaga ta hau ta kwanta, a hankali ta matso kusa da Humainah shi dai kallonta kawai yake, wayar hannunsa ne ya fara ring ya kalli screen din, sai da ya kusa katsewa ya daga ya mika mata, karba tayi tana kallonsa yace "Kiyi magana" wayar ta kai kunnenta tace "Na'am" El-ameen yace "Baki yi bacci ba baby?" Ta kalli Junaid da ke kallonta ta sunkuyar da kai a hankali tace "Xan yi" juyawa junaid yayi ya fice daga dakin, "Kin ci abinci kuwa" tambayar da El-ameen yayi mata kenan ta gyada masa kai tace "Eh da afternoon ya bani wannan small rice da miya, na ci kadan Saboda ba dadi sai ya xo ya bani a baki" shiru El-ameen yayi bai ce komai ba, Humainah ta bude ido da sauri tana sauraren abinda take cewa gabanta na faduwa, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "Da ya baki a bakin sai kika ci?" Kai ta gyada masa tace "Eh da ya bani na ci, uncle he's kind, I like him just like Abba" mijin Dr Sumayya kenan, katse wayar El-ameen yayi, Humainah ta mike xaune xuciyarta na tafarfasa can ta mike ta fice daga dakin, da sauri Jasmine ta mike ta bi bayanta ita ma, dakin Junaid Humainah ta shiga ta gansa tsaye yana saka pyjamas dinsa, juyawa yayi yana kallonta ta xube wajen ta fashe da kuka sosai, karasowa yayi kusa da ita ya durkusa gabanta da mamaki yace "Me ya faru?" Jasmine ce ta shigo dakin ta karasa kusa da su a hankali ta durkusa ita ma tana kallon yanda Humainah ke kuka.
*Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
47.....
Dago kanta junaid yayi yana kallonta ganin ta ki yin shiru yace "Ohh Pls ki gaya min me ya faru mana, What happened?" Nan ma dai bata ce komai ba sai kuka, juyawa yayi ya kalli Jasmine dake durkushe kusa da su ita ma ya ga hawaye idonta, mikewa yayi ya fita xuwa dakin Humainah, a hankali Jasmine ta dawo kusa da ita cikin sanyin murya tace "Sorry Anty" kallo daya Humainah tayi mata ta mike tana goge hawayen da ya ki tsaya mata ta koma kan gado, junaid ya dawo dakin yana kallon Humainah yace "Wai don Allah kukan kike haka har yanzu?, are you even okay?" Ta hade rai ba tare da ta kallesa ba tace "Ni a nan xan kwana" daga haka tayi kwanciyarta ta juya baya, kallonta kawai Junaid ke yi, can ya juya ya kalli Jasmine da ke kallonta ita ma, karasawa yayi gun gadon a hankali ya xauna kusa da ita ya kai fuskarsa kusa da nata murya can kasa yace "Haba Humainah, toh ita fa" bata tanka sa ba sai rufe idonta da tayi, ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Humainah!" bude ido tayi ta wani hade rai tana kallonsa, ya marairaice mata yace "Ita ina xata kwana mana" ta fixge hannunta tace "Oho!" Daga haka ta kuma juya masa baya, ya kusa minti biyar yana kallonta kafin ya mike tsaye yana kallon Jasmine dake ta kallonsu, duk tausayinta ya cika sa, a hankali ya isa kusa da ita yace "Tashi mu je" mikewa tayi ita ma tana kallonsa ya fara tafiya ta bi bayansa, juyawa Humainah tayi da sauri tana kallonsu har suka fita ya rufe kofar ta mike xaune ta fara wani sabon kukan kai ka ce an mata mutuwa ne, dakin da Jasmine din take ya shiga tana biye da shi, ya xauna gefen gado, jasmine ta iso kusa da shi ta xauna kasa a hankali tana kallonsa tace "bata son in yi bacci da ita koh?" Girgixa mata kai yayi da sauri yace "No! she's sick ne" gadon ya nuna mata yace "Taso ki kwanta kiyi baccin ki" tace "Kai ma xa kayi bacci a nan?" shiru yayi bai ce komai ba ganin yanda take kallonsa ya gyada mata kai yace "Eh! Zo ki kwanta" mikewa tayi ta hau gadon ta kwanta, yana kallonta yace "kin iya addu'a ai koh?" Shiru tayi tana kallonsa can kuma a hankali tace "Bismeeka Allahumma Amootu Wa Ahya" murmushi yayi mata yana gyada kai yace "Jayyid! To yi baccin ki hakan ma yyi" tace "Kai baxa kayi baccin ba" yace "Xan yi mana, amma sai na gama kallo" yana magana ne yana powering tv, lumshe ido tayi ya d'an saci kallonta kafin ya maida dubansa kan tv, ya kusa awa daya xaune dakin yana yi yana kallonta har ya lura baccin ta yayi nisa, ya lumshe ido ya mike ya rufa mata duvet ya isa kofa ya bude a hankali ya fita ya bar kofar bude, dakin sa ya shiga ya rufe, kwance ya same Humainah idonta rufe, ya kashe wutan dakin ya karasa gadon ya kwanta. Kusa da ita ya dawo ya kamo hannunta murya can kasa yace "Humainah?" Shiru bata amsa ba, ya kai bakinsa dai dai fuskarta ya kuma kiranta a hankali, mirginawa tayi ta koma can karshen gadon ta juya masa baya, ya d'an tabe baki yayi kwanciyarsa ya lumshe ido. Kafin asuba ya je duba Jasmine ya fi sau biyar, yana dawowa daga masallaci bayan an idar da sllh ya shiga dakin ya tada ta, mikewa xaune tayi tana mitsika ido yace "tashi kiyi sllh" gyada masa kai tayi ta mike xata shiga toilet sai kuma ta juyo tace "Wanne?" Murmushi yayi yace "Asuba" juyawa tayi ta shiga toilet din, ya fita daga dakin, xaune ya tarda Humainah kan darduma, ya karaso ya xauna kusa da ita yana kallon yanda ta hade rai, yayi murmushi yace "Ba gaisuwa" dauke kai tayi tace "Ina kwana" ya juyo da fuskarta yana kallon idanuwanta da suka kumbura don kuka, ya langwabar da kai yace "Su Abba sun hada ni da aiki...." Mikewa ta shiga kokarin yi ya mayar da ita ta xauna ya kamo hannunta yace "Not until you tel me what ur problem is, jasmine or what?" bude kofar dakin aka yi duk suka juya da sauri, jasmine ta shigo dakin ta karaso inda suke ta duka kusa da junaid tana kallonsa tace "Nayi sallah, i want to brush my teeth" ya kusa second ashirin yana kallonta, Humainah ta janye hannunta daga nasa ta mike ta koma kan gado, gyada mata kai yayi da sauri yace "Alryt! Ohk" ya mike ya shiga bathroom, toothpaste da toothbrush sabbi ya fito da ya mika mata ta mike ta karba ta nufi kofa ya bita da kallo, har xata fita ta juyo tace "Xan yi wanka ma" ya d'an bude ido sai kuma yace "Ohk Ohk" ya koma bathroom ya fito mata da sabulu shower gel da sponge ya karasa ya mika mata ta karba tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Towel!" Juyawa yayi ya dauko mata towel dinsa ya dawo ya mika mata ta karba sannan ta juya ta fita, ajiyar xuciya ya sauke ya juya yana kallon Humainah da tayi kwanciyarta, karasawa gun gadon yayi yyi kwanciyarsa shi ma, tana ganin haka ta mike ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fice daga dakin. Karfe takwas da wani abu su fatima suka kawo breakfast, kamar jiya daga bakin kofar ya tsaida su ya karbi abincin hannunsu, khadija ta marairaice masa tace "Ya A jay xamu gaisa da Humainah mana" yace "Bacci take" Khadija ta turo baki ta juya haka ma fatima ya kulle kofar. Dawowa cikin parlon yayi yana kallon jasmine dake xaune kasan lallausan carpet din tsakar parlon, kusa da ita ya ajiye basket din abincin ya tafi kitchen ya dauko cup da spoon da plates sae kayan tea ya dawo parlon, tea ya fara hada mata, ita dai sai kallonsa take da sun hada ido xata sunkuyar da kai, har ya gama ya ajiye mata tean gabanta ya dibar mata potatoe da kwai da plantain ya ajiye mata yace "Gashi ki ci" girgixa masa kai tayi tace "Ni bana son milk" ya d'an bude ido yace "Uhhn!" Ta gyada masa kai, mikewa yayi ya tafi kitchen ya dauko wani cup din ya dawo ya hada mata Milo kadai ya ajiye mata, ta kalli potatoen gabanta a hankali tace "Ketchup" wara ido yayi yace "Uhun!" Ta kallesa ya mata murmushi yace "Tohm bari in je in siyo maki" daga haka ya rufe dankalin da tea ya mike ya tafi sama ya dauko makullin mota ya sauko parlon yace "ko xa ki bi ni?" Shiru tayi sai kuma tace "Ehh!" Komawa sama yayi ya dauko mata Hijab ta karba suka fita daga parlon, tara da wani abu suka dawo gidan da ketchup din, ya sake hada mata wani tean ya bata, kallon yanda take shan ketchup din yake yyi murmushi yace "You like it" ba tare da ta kallesa ba tace "Yes!" wani shayin ya hada ya dau dankali da kwai ya tafi sama, ya shiga dakin Humainah, xaune ya sameta kasan dakin ya karaso ya ajiye mata abincin hannunsa ya xauna yace "Ga breakfast" bata ko juyo ba bare ta kallesa, ya mike ya fita. Karfe sha daya da wani abu junaid na daki yana danna laptop aka danna bell downstairs, mikewa yayi ya fito ya duba dakin Jasmine don ganin ko ta tashi daga baccin da take yaga bata tashi ba, downstairs ya sauka ya bude kofa, gabansa ne ya fadi ganin Hajiya da Umma sai Aysha kanwarsa da su Muhibba da Suhaima, Hajiya na murmushi tace "Wannan kallo haka Ahmad ko mu koma ne" juyawa yayi ya bar bakin kofar ya dawo parlor duk suka shigo, Ya xauna ya gaida su bbu fara'a, duk suka amsa da yaken da bai kai ciki ba, Aysha ta gaida shi ya amsa ba tare da ya kalleta ba, haka ma su Suhaima Umma tace "Toh ina amaryar ko bata tashi ba" mikewa yayi ya haura sama, Hajiya ta saci kallon Umma, haka kawai gabansa ya dinga faduwa ya jawo kofar dakin da jasmine take a hankali don kar ta tashi ya rufe sannan ya shiga dakin Humainah, ganin idonta yasa jikinsa yayi sanyi, ya karasa kusa da ita ya xauna a hankali yace "What's the meaning of this Humainah! Me na maki kike ta kuka haka tun jiya, in dai yarinyar nan ne xata bar gidan soon" ko kallonsa bata yi ba, ya shafa kansa yace "Toh yanxu haka xa ki fita su Hajiya su ganki?" Jin taki cewa komai ya jawota jikinsa ta turasa ta fashe da kuka tace "Allah ni ka kyaleni, dama ni ba sonka nake ba kai ma kuma baka sona...." Yace "Ohk naji, fito ku gaisa da su Aysha" tace "Babu inda xan je" kallonta ya tsaya yyi, tayi kwanciyarta, ya kusa minti biyar xaune sannan ya mike ya fita daga dakin yana tunanin abinda xai ce masu har ya sauko parlor ya xauna, shafa kansa yayi yace "Bacci take, bata jin dadi ne" Hajiya tace "Allahu Akbar, baiwar Allah abun ka da rashin sabo" mikewa tayi tace "Bari inje dai in dubota" gabansa ne ya fadi sai dai bai dago ya kalleta ba, Umma ma ta mike tace "Mu je kam Hajiya, in ya kama aje asibiti ne sai a je" su Suhaima suka tashi wai su ma xa su, Hajiya tace "Kaji min fitsararru ku je kuyi me" ita dai Aysha bata ce komai ba har suka haura sama, Junaid ya ja tsaki ya mike ya fita xuwa balcony, Da sallama suka bude kofar suka shigo Humainah ta mike xaune da sauri tana goge fuskarta ganinsu, Umma tace "Allahu Akbar, sannu 'yar nan" Hajiya tace "Allah sarki, amma har da son jiki Humainah" ita dai bata ce masu komai ba, Umma tace "Ya jikin?" Ta sunkuyar da kai tace "Da sauki" Hajiya na kare ma dakin kallo ganin uban dukiyar da aka xuba tace "Wayyo sannu 'yar nan, kowa sai da yayi wannan experience din" bata sake cewa komai ba nan suka gama surutansu suka fita daga dakin ko Wanne da tunanin da yake a xuciya, sai da suka sauko sannan Aysha ta tafi dakin ita ma, Humainah na ganinta ta fashe da kuka, ta karasa da sauri tace "Meye haka Humainah" xaunawa kusa da ita tayi ta rungumeta tana lallashinta amma kamar tunxurata take kuma yi, Aysha tace "Wai kukan Meye haka kike?" Cikin kuka tace "Anty ni gida xan koma" Aysha ta d'an bude ido tace "Saboda me?" Kin cewa komai tayi, Aysha tace "Toh ni bari in tashi in tafi tunda baxa kiyi shirga ba" ta rikota da sauri tana kuka tace "Anty kin ga ya A jay baya kulani sai wannan yarinyar da ya kawo..." Da mamaki Aysha tace "Wace yarinya?" Tana goge fuskarta tace "ni ban san ta ba" da mamaki Aysha tace "tana ina?" Wasu sabbin hawayen na xuba idonta tace "Tana dayan dakin" kallonta Aysha take da mugun mamaki tace "Dayan dakin?" Humainah bata sake cewa komai ba ta hade kanta da gwiwa tana kuka, da kyar Aysha ta mike ta fita ta bude dakinsa bbu kowa dakin dake kusa da na Humainah ta dawo ta bude ta ganta kwance ta takure waje daya tana bacci, jikinta yayi sanyi sosai ta karasa cikin dakin tana kallonta, juyawa tayi ta fita daga dakin ta sauko downstairs, su Hajiya dake xaune sun debo ma Kansu kayan flour daga kitchen suna ci suna hira suka bi ta da kallo har ta fita, xaune taga junaid yana danna waya a balcony ta gansa, cikin sanyin murya tace "Ya A Jay xa mu yi magana" sai da ya ga dama sannan ya daga kai ya kalleta alamar yana ji, tace "Mu je daga can" tana fadin haka ta nufi parking space ya bi ta da kallo kafin ya mike ya bi bayanta, da damuwa sosai tace "Ya Ahmad wacece yarinyar nan?" Kallonta ya tsaya yi, can ya hade rai yace "Ina wasa da ke ne kike questioning dina?" Tayi kasa da murya a hankali tace "Ba haka ba yayana, ni ban san ka da irin haka ba, ka gaya min wacece ita kaga....." Yace "Allah xan bata maku rai daga ke har Humainahn, akwai wanda yayi contributing lokacin da nake gina gidana ne, ko a kanta yarinyar ke xaune?" Shiru Aysha tayi tana kallonsa da mugun mamaki tana tunanin anya shi ne kuwa, yaushe ma yake kula matan bare har ya daukota ya kawo ta gida, ko kadan bata kawo mahaukaciyar da ya kai gida kwanaki bace, kwafa yayi xai bar wajen tayi saurin cewa "Amma yaya shekaranjiya fa ku ka tare, bbu matar da xata samu nutsuwa....." Dawowa kusa da ita yayi fuskarsa daure yace "Allah xan mare ki, kuma kika kuskura kika fitar min da sirrin gida bbu ni bbu ke" daga haka ya juya ya bar ta wajen tsaye, jikinta yayi sanyi ba kadan ba lokaci daya ta ji mugun tsanar jasmine har cikin ranta, da kyar ta bi bayansa xuciyarta na tafarfasa ta shiga gidan, dakin Humainah ta koma ta xauna jiki ba kwari tace "Kiyi hakuri kin ji Humainah ban san lokacin da Ya Ahmad ya sauya hali ba haka, ni baxan iya cewa komai ba a nan amma in kinga xaki kira Mumy to ki kirata ki gaya mata ko Abba, don bamu san ma'anar xaman yarinyar ba" bude kofa aka yi duk suka juya, ya shigo ya nuna ma Aysha kofa, ta mike ta fita. Karasowa yayi kusa da gadon yana kallon Humainah strictly yace "Idan kina son mu xauna lafiya to ki daina interfering a kan duk abinda bai shafe ki ba, ki daina fitar min da sirrin gida, xaman da kike daban a gidan nan haka ita ma yarinyar xaman da take daban, be careful" daga haka ya juya ya fita daga dakin. Aysha bata sake shiga dakin Humainah ba har suka bar gidan, su Hajiya na lura da mood din Aysha amma ba daman tambayar me ya faru sai dai su ma plan din da suke daban a xuciyoyinsu.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
48.....
Sai kusan Azahar Jasmine ta tashi, tana ganin kofa rufe ta mike da sauri taje ta bude, fitowa Junaid yayi daga bedroom dinsa jin budewar kofar,ya rungume hannayensa yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi, yace "Kin tashi" ta gyada masa kai ta koma dakin, karasawa ciki yyi yace "Are you hungry?" Ta daga kai ta kallesa tace "ina son in yi girki" yace "girki?" Ta gyada masa kai yace "Uhnn! Toh xo mu je kiyi" gun kayanta ta nufa tace "in sa wani kayan" dariya ta basa ya bi ta da kallo har ta isa gun jakarta ta bude ta fiddo wata yar top fari mara nauyi da wando mai kamar 3qtr pink ta ajiye, xaro ido yayi yana kallonta, yaga ta fara kokarin cire doguwar rigar kantin jikinta, da sauri ya juya ya fita daga dakin ya sauka downstairs, tana gama canxa kayan ta dau net ta saka a kanta kamar yanda suke a gidan Dr Sumayya, ta fito dakin ta sauko kasa, buda ido yayi yana kallonta har ta karaso inda yake, can ya shafa kansa yace "No! Je Dauko hijab ki sa" shiru tayi bata ce komai ba, ya mata murmushi yace "Yes, je ki dauko" ta juya ta koma sai ga ta ta dawo da hijab, tausayinta kawai yake yanxu kam she don't know what's right or wrong kawai gata nan gata nan ne, kitchen ya nufa ta bi bayansa, sai da suka shiga ya kalleta yace "Me xa ki dafa?" Tayi shiru tana tunani can tace "Indomie and egg" yace "Ohk," ya fiddo mata da indomie biyu, da kwai uku, kamar me naxari tace "Onion, pepper, carrot....." Sai kuma tayi shiru idonta a kansa, murmushi yayi ya dauko mata ya ajiye, ta kalli indomien tace "Ga nawa, ga naka, ina na wancan Antyn" ta fadi haka tana nuna masa sama, shiru yayi bai ce komai ba, can ya dauko daya ya ajiye, kunna gas tayi ta dau tukunya ta xuba ruwa ta daura tace "Haka koh?" ya jingina jikin kofa ya rungume hannu yana kallonta, sosai yayi mamakin ganin yanda take hada girkin sai dai tana yi tana tsayawa kamar me naxari, cikin few minutes ta dafa indomien ta soya kwai ta xuba a plates uku duk ta sa fork, sai a sannan ta juya tana kallonsa yayi murmushi a hankali yace "Woaw! Sannu da kokari" ta wara masa manyan idonta tace "Uhm" kallonta kawai yake, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Yaushe Uncle xai xo?" Shiru yayi mata bai ce komai ba, ta matso kusa da shi tana kallonsa tace "When uncle xai xo?" Hade rai yayi ya dau plate din indomie daya ya mika mata yace "kai mata daki" ta karba tace "Ohk" sannan ta fita daga kitchen din ya bi ta da kallo, sama ta tafi ta tura kofar dakin a hankali ta shiga, xaune ta ganta kan darduma ta iso kusa da ita ta durkusa ta ajiye mata tace "Nayi girki" wani kallo Humainah ta watsa mata ta mike tace "Fice min a daki!" Jasmine ta mike tana kallonta, ta buga mata uban tsawa tace "Baxa ki dauka ki fita ba" dukawa Jasmine tayi a hankali ta dau indomien ta fita, ta koma downstairs kallonta junaid yake har ta karaso parlor ita ma tana kallonsa, hawaye ya gani idonta ya karba indomien ya ajiye ya xauna, ita ma ta xauna ya ajiye abincin gabanta yace "Ci abincin ki" ta goge hawayen idonta ta dau fork din a hankali ta fara cin indomien, duk ya lura ci kawai take ba don tana son ci ba, duk tausayinta ya cika sa. Tashi yayi ya tafi sama ya shiga dakinsa, wayarsa ya dauka ya ga mis calls din El-ameen, ya ajiye wayar ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito, har xai sauka downstairs sai kuma ya shiga dakin Humainah, ya hade rai yace "Don ta kawo maki abinci shine laifi har da yi mata tsawa?" Wani kallo tayi masa tace "Nayi, kar kuma ta sake xuwa inda nake kaje can ku karata" tana fadin haka ta fashe da kuka, ya karaso cikin dakin ya xauna kusa da ita yace "Haka kika ce?" Mikewa tayi xata bar wajen ya fixgota ta fado kansa, ya dago kanta ya hade goshinsu yace "Maimaita words din ki" yana ganin yanda kirjinta ke heaving, ya hade rai sosai yace "Maimaita nace" komawa baya take son yi amma ta kasa don ba rikon wasa yayi mata ba, shi kansa ji yayi xuciyarsa na bugawa, rufe ido tayi da kyar tace "Ni ka rabu dani, bana so...." Murmushi yayi ya lumshe ido ya hade bakinsu..... Still yayi da farko har lokacin bai bude ido ba haka ita ma, can ta fara turasa a tsorace, ya kwantar da ita a hankali ya shiga kissing dinta, sosai ta tsorata sai dai ta kasa kwace bakinta, da kyar ya saketa jin an tada sllh ya mike ya fita daga dakin, ta fashe da kuka ta boye fuskarta cikin pillow, bedroom dinsa ya nufa shiga toilet. Bai iya ya fito daga dakinsa ba sai da aka kira la'asar, ya sauko parlor don tafiya masallaci, xaune ya ga jasmine kan carpet a parlor ta daura kanta kan kujera idonta lumshe a haka, ya iso inda take ya d'an buga kujerar ta bude ido da sauri, murmushi ya mata yace "me sa baki tafi daki ki kwanta ba" a hankali tace "Tsoro nake ji ni kadai" ya durkusa kusa da ita yace "Tsoron me kike?" Kamar xata yi kuka tace "Nima ban sani ba" shiru yayi yana kallonta, hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Uncle baxai xo ba?" Nan ma dai shiru yayi bai ce komai ba, sunkuyar da kai tayi ganin haka, a hankali yace "Xai xo anjima, yanxu dai tashi ki shiga toilet ki yi alwala ki xo kiyi sllh, kin ma yi na daxu?" Girgixa masa kai tayi, yace "Toh da kin ji an kira sllh ki tafi kiyi alwala kiyi kin ji?" Ta gyada masa kai yace "Kin ma san me ake cewa idan ana sllhn ma?" Ta gyada masa kai, yace "Wa ya koya maki?" Tace "Mami da farida" yayi murmushi yace "Good tashi kije kiyi alwala sai kiyi na daxu da na yanxu" tayi narai narai da ido tace "Ina jin tsoro a sama" ya nuna mata bayin dake parlor yace "ae a can xaki je kiyi" mikewa tayi ta nufi toilet din, yace "Baki cire hijab ba" dawowa tayi xata cire ya tuna abinda ke jikinta da sauri yace "A'a a'a tafi kiyi haka kawai" ta juya ta tafi toilet din, sama ya koma ya dauko mata darduma ya shimfida mata sannan ya fita jin an tada sllh. Ko da ya dawo ya tarar bata idar ba ya xauna har ta gama, yana kallonta yace "kullum idan kinyi sllh ki yi addu'a kice Allah ya baki lafiya kinji" shiru tayi tana kallonsa ya mata murmushi yace "Kina jin yunwa?" Girgixa masa kai tayi yace toh bari in sa maki kallo, ta gyada masa kai yayi powering din tv ya mike ya haura sama. Haka tayi ta xama a parlon ita kadai har magrib, tana jin an kira sllh taje tayi alwala, ko da ya sauko tafiya masallaci samunta yayi har ta fara sllh, yayi murmushi ya fita. yana dawowa daga mosque ya ga motar El-ameen bakin gate yayi jim can ya juya xai shiga gate El-ameen ya danna masa horn, dawowa yayi don bai yi tunanin yana ciki ba, ya bude motar El-ameen yace "Why ain't you picking my cal?" Junaid ya daga kafada yace "Ban ma san ka kira ba" El-ameen bai ce komai ba ya bude motar ya fito rike da leda hannunsa, junaid ya nufi gate ya bi bayansa, sai da suka shiga gidan yace "Kasan yanxu sai da izinin ka xan dinga shigo maka gida..." Junaid bai ce komai ba har suka shiga parlor, jasmine dake xaune kan darduma tana ganin El-ameen ta mike da sauri tana kallonsa ya wara mata ido yace "uhmm!" da gudu ta karaso ta rungumesa tace "Uncle!" El-ameen ya d'an yi still, junaid kam hade rai yayi ya karasa shiga parlon ya xauna, a hankali El-ameen ya janyeta jikinsa yana murmushi yace "How are you" murya can kasa tace "am fyn, I missed you" gyada mata kai yayi ya nuna mata Junaid yace "He's always there for you also" ta kalli Junaid tayi shiru bata ce komai ba, kama hannunta El-ameen yayi suka karasa parlor ya xauna ita ma ta xauna, kusa da kunnensa ta kai bakinta tace "In je in kawo jakan?" Dariya yayi yace "Na me?" A hankali tace "Na cloth dina" yace "Wait tukun sai idan xa mu tafi" tace "Toh" duk wannan abinda suke junaid kan tv ya maida hankalinsa. El-ameen ya jawo ledan da ya shigo da ya bude ya dauko mata apple daya ya mika mata ta karba tace "Na gode" gyada mata kai yayi har ta fara ci ta mike ta isa kusa da Junaid ta durkusa tace "Uncle dina ya siya min apple xaka ci" ba tare da ya kalleta ba ya girgixa mata kai ta mike ta koma gun El-ameen ta xauna, in da sabo El-ameen ya saba da attitude din junaid, don haka bai damu da daure dauren fuskar da yake ba yace "Ina madam din taka" ba tare da Junaid ya kallesa ba yace "Tana daki" ko rufe baki bai yi ba sai ga ta ta sauko sanye da hijab dinta har kasa, tana ganinsu xaune parlon ta dauke kai ta nufi kitchen El-ameen ya bi ta da kallo ta gefen ido hade da tabe baki, Jasmine ta matso kusa da El-ameen a hankali murya can kasa kamar xata yi kuka tace "I don't like her" murmushi El-ameen yayi murya can kasa shi ma yace "Really! But why?" Cikin sanyin murya tace "She's mean!" Kallonsu kawai Junaid ke yi ta gefen ido, El-ameen dake lura da haka ya saka dariya yace "Malam da kawai ka juyo ka kallemu ka bar straining idonka" hade rai junaid yayi ya juya yana kallonsa, can ya mike ya haura sama, jasmine ta bi sa da kallo sannan ta kalli El-ameen tace "He's kind, I like him" El-ameen bai ce mata komai ba, Humainah ta fito daga kitchen rike da cup din tea, El-ameen ya bi ta da kallo can dai yace "Ina yini Humainah" ba tare da ta tsaya ba bare ta juyo tace "Lafiya lau" yayi murmushi yace "Ohh baxa ki tsaya mu gaisa ba, toh d'an dawo muyi wata magana da ke" ta juya ta kallesa yace "Minti uku kawai" fuskarta daure ta dawo parlon ta tsaya, yace "Toh xauna mana" ta xauna kujera ba tare da ta kallesa ba, yace "Kiyi hakuri nasa an kawo maki bakuwa may be ba da ixinin ki ba, ba dadewa xata yi ba gidan ki Idan Allah ya yarda, matar da ke rike da ita ne tayi tafiya shi yasa ta xo taya ki xama, Ina fatan kuma captain ya baki labarin ko wacece ita" Humainah bata ce komai ba ta dauke kai, El-ameen yace "pls ki tausaya mata marainiya ce ita a yanxu dai, akwai abubuwa da yawa da ta manta take bukatar a koya mata, plss help the innocent girl, take her as ur sis sai Allah ya baki lada!" Hawaye ya ga ni idonta, ya juya ya kalli Jasmine dake kallonsa yace "je ki kira min Captain" shiru tayi bata ce komai ba, can a hankali tace "Captain!" Ya gyada mata kai, ta d'an bude ido tace "Sleep Captain din nan?" Yace "Je kice masa ya xo" mikewa tayi ta tafi sama, El-ameen ya kalli Humainah yace "Ke dai baki son ta xauna kawai koh?" Ta goge idonta tace "Toh shine ni baxai kulani ba sai ita, komai yayi mata ni baxai min ba" sai ta fashe da kuka, duk da ta ba El-ameen dariya don yasan har da yarinta ya dai dake yace "Da gaske?" Cikin kuka tace "Ko da yaushe shi yake bata abinci ni baxai bani ba, sai yaje yayi ta xama da ita ko ya shiga dakin da take" shiru El-ameen yayi yana kallonta, can yace "Kiyi hakuri xan masa magana, but kema ki dinga yi masa biyayya banda tsiwa in har kina son ku xauna lafiya kamar masoya, in har kina masa haka ke ma xai dinga kyautata maki, baby kuma 'yan kwanaki xata yi ta tafi" kai kawai ta gyada masa tana goge fuskarta.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
49.....
Jasmine na haurawa sama ta bude kofar dakin Junaid ta shiga, xaune yake yana game da laptop, ya daga kai yana kallonta har ta karaso ta xauna kasa tana kallon game din tace "Irin na Saif" son din Dr Sumayya, jin Junaid bai ce komai ba ta daga kai tana kallonsa suka hada ido, sunkuyar da kai tayi, yace "Idan xaki shiga daki ki fara yin sallamah a amsa maki sannan ki shigo kin ji" dago kai tayi tana kallonsa da ganinta kasan bata gane abinda yake nufi ba, ya lumshe ido ya mike ya isa kusa da kofa ta bi sa da kallo, yana rike da kofar yace "before coming in, sai kin fara cewa Assalamu Alaikum, idan kika ji ance Wa'alaikis salam, sai ki shigo" shiru tayi tana kallonsa still, ya dawo dakin ya xauna yace "Say Assalamu alaikum!" Sunkuyar da kai tayi a hankali ta fadi, yace "Good, sai kinji ance maki wa'alaiki assalam sai ki shigo, tashi kije ki fadi in ji" mikewa tayi ta koma gun kofar ta tsaya a hankali tayi sallaman, girgixa mata kai yayi yace "No! Waje xaki ki tsaya ba nan ba" ta bude kofar ta fita tayi sallaman, ya amsa ta shigo kanta a kasa, kallonta kawai yake har ta iso inda yake bata dago ba, hawaye ya gani idonta, yace "Ohh kuka kike?" Bata ce komai ba kuma bata dago ba, ya d'an tabe baki yace "uncle din naki ya tafi kenan?" Ta girgixa masa kai hawaye na gangarowa daga idonta tace "Yace in kira Captain" kallonta kawai yake, cikin sanyin murya yace "Xauna" ta xauna kasa, yace "Kukan me kike?" Girgixa masa kai tayi bata ce komai ba, xai yi magana wayarsa ya soma ring, dauka yayi ya ga El-ameen ke kiransa ya ajiye wayar ya mike ya fita ta bi sa da kallo can ita ma ta mike ta bi bayansa. Tun daga stairs El-ameen ke kallonsa har ya sauko, ita dai Humainah kanta na kasa, Yana daga tsaye yace "Ya aka yi?" El-ameen yace "Am going" Junaid yace "Allah ya kiyaye hanya" jasmine na jin El-ameen yace going ta dawo kusa da shi da sauri ta durkusa tace "Uncle bag dina yana daki" ya langwabar da kai yace "Mami ai bata dawo ba baby, amma tace gobe xata dawo sai goben in xo in dauke ki koh" wani kuka ta fashe da tana kallonsa tace "Nooo" da mamaki yake kallonta ganin irin kukan da take, ta mike ta xauna kusa da shi ta kamo hannunsa tana kuka tace "Dont leave me plss Uncle, take me with you" ya girgixa mata kai yace "Toh ina xan kai ki baby mami bata nan, she's coming back tomorrow sai in xo in dauke ki" ta fashe da matsanancin kuka har da bubbuga kafa tace "Nooo!" juyawa junaid yayi xai koma sama El-ameen da ya ma rasa me xai ce mata yace "Dalla kai kuma meye haka Ahmad magana xa muyi" junaid ya wani hade rai yace "Ka fadi abinda xaka fadi mana" mikewa Jasmine tayi tana kuka har lokacin tace "I want to go and bring my bag..." El-ameen ya hade rai yace "I will flog you fa," cikin kuka tace "Nooo!" Humainah dai sai kallon ikon Allah take, El-ameen ya mike yace "You are telling me no koh, bari in nemo bulala yanxu, I will so flog you" dawowa kusa da shi tayi da sauri tana kuka tace "Plsss" ya nuna mata kujera yace "Toh xauna kar in mare ki yanxu, ki rufe min baki kuma" xaunawa tayi tana kokarin hadiye kukan, ya kalli junaid yace "Mu je" daga haka ya dau makullin motarsa da waya ya nufi kofa, ta mike da sauri ta fashe da wani sabon kukan tace "Uncle" ya hade rai yana kallonta yace "Koma ki xauna" komawa tayi ta xauna ya fita daga parlon, Junaid ya tabe baki ya bi bayansa, mikewa Humainah tayi ta haura sama, Jasmine ta dinga rusa kuka iya karfinta, sai da suka isa gun mota El-ameen yace "look junaid ka rage shige ma yarinyar nan tunda matar ka bata so, beside bai ma kamata ka fiffita ta kan matar ka ba, duka duka yaushe aka yi auren har xaka dinga shiga hakkinta haka, kawai yanxu a samo tsohuwar da xata dinga mata duk wasu abubuwan xai fi....." Katse sa Junaid yayi yana masa wani kallo yace "Abinda nayi niyyar yi kenan or you take her out from my house tunda yanxu kam kafi kowa son kula da ita da nema mata lafiya on like lokacin da take kan bola, ni sai in cire hannu ma in bar ka da ita tunda na mata mai wuyar, you can take her to wherever you wish for all I care Ahmad" daga haka ya juya ya bar wajen, El-ameen ya bi sa da kallon mamaki har ya shige gate ya kulle, juyawa yayi xuciyarsa na tafarfasa ya shiga motarsa ya bar layin. Ko da Junaid ya shigo parlon samunta yayi tana ta rusa kuka, ko kallonta bai yi ba ya haura sama. Har magrib Jasmine na parlon tana kuka, ya sauko ya fita xuwa masallaci ba tare da ya kalleta ba, sai da Humainah taji fitarsa sannan ta sauko parlon, daga bakin stairs ta tsaya ta dake tace "Xo mu tafi sama" ko kallonta Jasmine bata yi ba, ta karaso cikin parlon tace "Mu je" Jasmine tace "Am not going" juyawa Humainah tayi ta koma sama abun ta. Bakwai da wani abu Junaid ya shigo parlon rike da leda a hannunsa, ajiye ledan yayi yana kallon jasmine yace "Je dauko jakar taki in kai ki gun sa" kallonsa tayi kamar bata gane me yace ba, ya hade rai yace "I said go and bring your bag" mikewa tayi tana goge idonta ta tafi sama, ba a dau lokaci ba ta sauko rike da jakar tana kallonsa tace "Ban ga daya takalmin ba" kallonta kawai yake, ya dake yace "Ina xan kai ki?" Tace "Wajen uncle" yace "Toh mu je" kofa ta nufa tana cewa "Na bar ma Antyn nan daya takalmin" ya bi ta da ido har ta bude kofa xata fita yace "Kehh!" Juyowa tayi tana kallonsa ya karasa inda take tsaye ya hade rai yace "Daga yau kika sake kira min uncle a gidan nn sai na baki mari" kallonsa take irin bata gane ba din nan, ya duka dai dai fuskarta yace "From henceforth, I mean from now on kar ki sake kiran uncle a gidan nan" fixge jakar yayi ya jefar parlor ya kamo hannunta ya shigo da ita ya rufe kofar ya saketa ya haura sama. Xube wa wajen tayi ta dinga rusa kuka har da shessheka, tana nan xaune ya sauko xai tafi masallaci yin isha, bai ko kalleta ba ya fita daga parlon, ko da ya dawo kitchen ya shiga ya dauko plate ya debi abincin da ya siyo daxu ya haura sama ya shiga dakinsa, bai iya ya ci abincin ba ya ajiye kawai ya koma kan gado ya kwanta duk ya rasa me ke masa dadi, tv ya kunna shi ma haka ya dinga kallon absentminded, bude kofar dakin aka yi Humainah ta shigo, ta tsaya daga kusa da gadon tace "Ka bani waya xan kira Abbana" ba tare da ya kalleta ba yace "ban da kati" kallonsa ta tsaya yi, can ta juya ta fice. Lumshe ido yayi ya bude ya dau wayar ya shiga kiran El-ameen, El-ameen dake kwance daki yana danna waya ya tsura ma sunan dake kan screen din ido har ya katse, aka kuma bugowa nan ma har ya katse bai daga ba, bayan kusan minti biyu text ya shigo masa, bude content din yayi ya karanta kamar haka "Just want to say am sorry, i get I wasn't suppose to, but I dunno whatever happened wasn't right, am just trying to say sorry....." Screen d'in ya tsurawa ido har ya gama karanta text d'in snn ya ajiye wayar, indai Ahmad ne ya saba da halinshi na idc attitude, ajiye wayar yayi yaci gaba da abinda yakeyi, K'arfe take as Junaid ya fito, d'akin Humainah ya leqa yaga bata nan da alama toilet ta shiga, jan k'ofar yayi ya maida ya rufe ya sauk'o, kwance take k'asan tiles har ta gaji da kukan bacci ya soma d'aukarta, dab da ita ya k'araso ya k'urawa kyakkyawan fuskarta ido da Lashes d'inta suka kwanto kamar tayi fixing, sosai jikinshi yayi sanyi ganin har lokacin da d'an siririn hawaye shimfid'e a fuskan, a hankali yayi tapping jakarta da janyo ta mak'ale kamar wacce za a kwacewa yace "Jewel", a hankali ta bud'e idonta tana kallonshi, ya sunkuyo daidai fuskarta yace "Wake up", sai lokacin ta tashi da sauri tana k'are mishi kallo kamar yanzu ta soma ganinshi, tana son furta Uncle amma tana tsoro dan yayi warning d'inta da kada ta sake k'ira mishi wani Uncle, a hankali bakinta ke twitching hawaye na dad'a gangarowa idonta, ido ya rintse kawai ya kamo hannunta tareda janyota jikinshi ya rungume, ba shi ba har ita k'irjinta bugawa yakeyi, ido ta lumshe tana sauk'e ajjyar zuciya, cikin wata iriyar murya yace "am sorry Jasmine", itadai shiru kawai tayi tana sauraronshi, a hankali ya janyeta daga jikinshi ya d'ago hab'arta yace "am sorry okay?", yasa hannu ya share mata hawayen dake fuskarta, gaba d'ayanta yarinyar tausayi take bashi, mik'ewa yayi tareda kamo hannunta ya tayar da ita yace "Kinyi Sallah?", kai ta girgiza mishi yace "kiyi min magana, don't nod", a hankali tace "banyi ba", yace "Shiga kiyi alwala, I will b here waiting for you", ba musu tayi hanyan toilet d'in dake palo, saida taje bakin k'ofa snn ta sake juyowa taga ita yake kallo kamin ta shige toilet d'in, yana zaune ta fito ta d'auki hijab d'inta dake gefe ta saka, har ta idar da Sallah idonshi na kanta yana observing yanda take Sallahn, ta d'an jima zaune bayan ta idar snn ta kalleshi tace "Av prayed, nace Allah ya bani lafiya", kai ya kad'a yace "that's good, kullum ki dinga yin haka kinji?", tace "toh", ya mik'e yana maida wayarshi aljihu yace "zaki rakani?", kallonshi ta tsaya yi da manyan idonta kamar batasan mey yace ba saida yayi murmushi snn yace "I mean would you like to go out with me?" Har zatayi nodding kanta tayi maza tace "Toh", yace "Good saka Hijabinki mu tafi", tana gama sawa ta dubeshi da manyan milky eyes d'inta tace "Shoe d'ina ban ganshi ba kuma nace na barwa waccan Aunty", kallonta yayi kawai yace "muje, we will buy another one", lokaci lokaci yake juyowa ya kalleta yana driving, itakam kanta ta jingina jikin glass tana ta kallon garin, a Jifatu yayi parking, ce mata yayi ta zauna ta jirashi ya shiga ya gama siyayyan da zaiyi snn ya fito, takalmin da ya mik'a mata ta saka tana jin dad'i snn ya wuce dasu Royal Joint, a nan yayi musu order abinci suka wuce gida, hannunshi riqe da abincin da ya siyo ita kuma riqe da na shoe d'in da ya siya matan, suna shigowa gida daidai nan Humainah na sauk'owa kan bene, wani irin fad'uwa, da murna Jasmine ta kalli ledan shoes dake hannunta snn ta kalli Humainah dake tsaye tace "Aunty kinga new Shoe d'ina da wannan Uncle d'in ya bani, he is nice, kema kice mishi kinaso ya baki", Humainah dake tsaye gabanta na bugawa juyawa tayi ta koma d'aki, Jasmine ganin ta tafi yasa ta juyo da kallonta ga Junaid da yake kallon inda Humainah tabi, tace "Aunty nan ma A siya mata irin shoe d'ina", kallonta kawai yayi yace "Jeki d'auko plate", ledan da yake hannunta ta ajiye tayi kitchen, zaune ta tarar dashi yana danna waya, d'agowa yayi ya dubeta ganin ta tsaya mishi a ka yace "Sit down and serve yourself the food", zama tayi ta janyo leda d'aya ta bud'e ta shiga zuba fried rice d'in a plate ta fara ci, tashi yayi ya d'auki d'ayan ledan ya haura sama dashi, d'akin Humainah ya tura duk wutan d'akin kashe yake, kunnawa yayi ya k'arasa shigowa, a tsakiyan gadon ya ganta kwance ta dunqule waje d'aya, zama yayi bakin gadon bayan ya ajiye ledan hannunshi, sau biyu yana k'iranta yajita shiru, a hankali ya d'agota dan yasan ba bacci take ba, fuskarta da ya kumbura dan kuka ya k'urawa ido , hannu yasa ya shafi hawayen yana murzawa da d'an yatsanshi yace "Sana'ar da kika samu kenan yanzu?", turashi ta shiga yi daga jikinta, firmly ya riqeta, ganin ta kasa kwace kanta yasa ta fashewa da wani irin kuka tana sulalewa k'asa tace "ni ka sakeni ka fitamin daga d'aki", har ranshi yakejin kukan nata, d'agota ya sakeyi yace "Humainah mey ke damunki wai for crying out Loud?, me kike so?", shiru tayi mishi taqi cewa komai tana ci gaba da kukan, a hankali ta d'ago tana share hawayenta tace "Ka maidani gidanmu, inason ganin Abba na", wani irin kallo ya bita dashi
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
50.....
Washe gari ma kamar jiya haka suka wuni gidan, yana zaune d'akin Humainah da tayi kamar batasan da zamanshi ba,
Mikewa yayi ya fita daga dakin ya koma nasa, yana danna wayarsa yaji kamar ana sallama bakin kofa, tashi yayi ya isa gun kofar ya bude ya ganta tsaye, a hankali tace "Nace Assalamu Alaikum!" D'an murmushi yayi yace "Gud! Ya aka yi?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Kin gama cin abincin?" Gyada masa kai tayi yace "toh mu je" fitowa yayi daga dakin ya shiga wanda take ta bi bayansa, ya xauna gefen gado ta karaso ita ma ta xauna daga kasa inda yake, yace "No dawo ki kwanta kiyi bacci" tace "I've not bathed" mikewa yayi ya shiga toilet ya hada mata ruwa ya fito yace "Toh tafi kiyi" ta mike ta cire hijab ta shiga toilet din ya bi ta da kallo, fita yayi daga dakin jin kamar wayarsa na kara ya shiga nasa dakin, 1st love ya gani jikin screen din, ya dau wayar ya xauna sannan yayi picking hade da yin sallama, Mumy ta amsa ya gaisheta ba tare da ta amsa ba tace "Ina Humainah" kallon kofa yayi yace "tana daki Mumy" Mumy tace "Aysha tace kuka kawai yake?" Ya d'an bude ido yace "Mumy ai kinsan yanda take behaving ni ban san me ke damunta ba" Mumy tace "Kai mata wayar" yace "Toh, xan kira idan na kai mata" daga haka ya katse wayar, da kyar ya mike gabansa na faduwa ya fita daga dakin ya shiga nasa, kwance ya sameta ta lullube gaba daya da bargo, ya karasa ya xauna kusa da ita ya yaye bargon yace "Humainah ga Mumy" kin bude ido tayi ya dagota ta buge masa hannu tana turasa, yace "Mumy ce xata maki magana" tana bude idon hawaye suka biyo baya, ta fada jikinsa tana kuka a hankali, rasa me xai ce mata yayi, ya dago kanta yana kallon fuskarta, murya can kasa yace "Humainah!" Kallonsa tayi bata ce komai ba hawaye na bin kuncinta, wayarsa ne ya soma ringing ya dauka yana kallon Screen din, can ya kalleta yace "Mumy xata yi magana da ke, plss ki bar kukan nan" bata ce komai ba ya d'aga ya kai mata kunnenta, daga daya bangaren Mumy tace "Humainah!" A hankali tace "Na'am, ina yini Mumy" Mumy ta amsa tace "What's wrong with you kike kuka har yanxu?" Wasu hawayen ne suka xubo mata tace "Ba komai Mumy" Mumy tace "Ba komai kuma? Haka kawai kike kuka?" Shiru tayi bata ce komai ba, Mumy tace "Toh xan xo gobe" a hankali tace "Toh!" Mumy ta katse wayar, ya dago kanta da sauri yace "What did she say?" Komawa tayi ta kwanta tace "Nothing" ya dawo kusa da ita yace "Karya kike" k'in ce masa komai tayi, ya dagota yace "Baxa ki gaya min ba" turasa tayi tace "Let me" jawota jikinsa yayi yace "Ae sai kin gaya min" ta hade rai tace "Stop this, bana so" kallon bakinta kawai yake, ta fara kokarin sauka ya rikota, cike da masifa ta buge masa hannu xata yi magana ya dago kanta sai jin bakinsa cikin nata tayi, buda ido tayi tana kokarin turasa ta kasa ya kwantar da ita ya lumshe ido, tsorata tayi ganin ya fara wuce limit, lokaci daya ya kawar mata da tsoron ta sakar masa jiki kamar ba ita ba, yanda ya kwantar da kai ka rantse kace ba captain Junaid ba, murda kofar dakin aka yi, ya saketa da sauri ya koma baya ita kuma ta shige cikin bargo, Jasmine ce ta shigo dakin da hijab sai towel dake jikinta, kamar xata yi kuka tana kallonsa tace "Ni banga bag din kayana ba" kallonta kawai yake da rinannun idonsa, shiru tayi ita ma tana kallonsa, juyawa tayi ta fita ta tsaya daga bakin kofa a hankali tace "Assalamu Alaikum!" Lumshe ido yayi ya bude yana shafa kansa bai ce komai ba, sallaman ta kuma yi kamar xata yi kuka, amsawa yayi fuskarsa daure, ta shigo ta tsaya daga bakin kofa, sai dai ta kasa cewa komai ganin yanda ya tamke fuska, kallonta yayi yace "From now on idan kika sake shiga waje ba sallama I will slap you" hawaye ne ya cika idonta ta gyada masa kai ta juya a hankali ta fita, juyawa yayi yana kallon Humainah da tayi lamo cikin bargo, ya shafa kansa ya mike ya fita daga dakin ya shiga nasa, wanka ya shiga yayi, ya dauro alwala ya fito ya saka jallabiyarsa yayi shafa'i da wutr, yana xaune kan darduma har Karfe sha daya can ya mike ya fita daga dakin, tsaye yayi bakin kofa yana kallon dakin da Jasmine take don kofar a bude yake, ya karasa ya shiga dakin, kwance ya ganta daga gefe kusa da bakin kofar tana bacci har lokacin Hijab da towel ne jikinta, durkusawa yayi kusa da ita yana kallon fuskarta, ya lumshe ido ya bude murya can kasa yace "Jasmine" ganin bata motsa ba ya mike ya fita daga dakin ya sauka parlor ya dauko mata jakar kayanta ya dawo sama, ajiye jakar yayi ya bude ya fiddo mata doguwar riga ja mara nauyi, kiranta ya kuma yi a hankali bata tashi ba, ya d'an buga kafadar ta ta mike xaune da sauri tana mitsika ido tace "Uncle!" Ganinsa yasa tayi saurin cewa "Captain!" Bai ce komai ba ya mika mata rigar hannunsa yace "Tashi ki sa kayan ki" karban kayan tayi yana kallonta ta cire hijab din jikinta ta mike, dauke idonsa yayi daga kallon nata a nan wajen ta saka kayan da ya bata, ta dawo kusa da shi tace "Na sa" mikewa yayi ba tare da ya kalleta ba still ya nufi gado ya ce "Xo ki kwanta" tace "Kai ma xaka yi bacci nan koh?" Yace "Eh" karasowa tayi ta hau gadon ta kwanta har da matsa masa, lulluba mata bargo yayi ya xauna gefen gadon ya kunna Tv yace "Sai na gama kallo xan kwanta" har sha biyu bai ga alamar xata yi bacci ba, ya kalleta yace "Sleep mana" tace "Sleep captain" murmushi yayi ya gyada mata kai yace "Ke ki fara yi sai nima in yi" lumshe idonta tayi ya tsura mata ido yana kallo, bata sake bude idon ba kuma har daya saura, ya mike a hankali ya kashe Tvn, ya fita daga dakin ya bar kofar a bude ya shiga nasa dakin, kasa bacci yayi sai juye juye yake ya rasa dalili, daga baya dai ya gano dalilin ya kawar da shi daga ransa yayi forcing kansa yayi bacci. Washegari Monday yaji da ma kawai yayi resuming aiki duk da hutun sati biyu ya dauka but sbda Jasmine yasa bai yi haka ba, yana dawowa daga masallaci ya shiga dakin Humainah ya ganta xaune kan darduma, juyawa yayi ya fita dakin ya shiga wanda Jasmine take, har lokacin ya ga bata tashi ba, dukawa yayi dai dai fuskarta yace "Jasmine" ta bude ido da sauri mikewa yayi yace "Tashi kiyi sallah" ta gyada masa kai ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet. Ya juya ya fita daga dakin. Karfe takwas saura Humainah ta fito ta sauka downstairs ta shiga kitchen, tsaye tayi tana tunanin abinda xata hada for breakfast, can dai ta fiddo Irish ta fara ferewa, ko da junaid ya sauko don siyo masu breakfast yayi mamakin ganinta a kitchen, ya tsaya daga bakin kofar kitchen yana kallonta, yace "Gud morning" ba tare da ta kallesa ba tace "Ina kwana" murmushi yayi ya juya ya fita daga kitchen din. Yana xauna parlo Jasmine ta sauko da alamar tayi wanka don ta canxa kayan jikinta, kusa da shi ta durkusa tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Nayi wanka" ya gyada mata kai yana nuna mata kitchen yace "Tafi ki gaisheta ki taya ta aiki" tace "Toh" sannan ta mike ta nufi kitchen din ya bi ta da kallo ganin yanda take tafiya. Kallo daya Humainah tayi mata ta dauke Kai, ta karasa kusa da ita ta durkusa a hankali tace "Ina kwana" ba tare da ta kalleta ba tace "Lafiya lau" shiru Jasmine tayi can kuma tace "I want to help you" mika mata wukar Humainah tayi ta ta tafi gun gas xata kunna, jasmine ta dau dankalin daya ta rasa yanda xata fara fere shi, kallon Humainah dake kokarin dauko mai tayi sannan ta fara fere dankalin ihu ta fasa ta jefar da wukan jin wani xafi da ya ratsa taMikewa Junaid dake xaune parlor yayi yana kallon kofar kitchen din jin Ihun, Humainah ta ajiye man hannunta ta taho da sauri tana kallonta tace "Dama baki iya ba....." Jasmine ta fashe da kuka q rikice tana yarfe hannu ganin jini a hannunta, Shigowa kitchen din junaid yayi ya hade rai yana kallon Humainah, hade ran ita ma tayi ta juya ta koma ta ci gaba da aikinta, Jasmine ta karasa kusa da shi tana kuka tace "Captain kaga blood din" kama hannunta yayi suka fita daga kitchen din Humainah ta bi su da kallo ta gefen ido. Sama ya tafi da ita xuwa dakinsa ya sa ta xauna bakin gado ya dauko tissue yana goge mata jinin dake ta xuba, ganin yanda take kuka yasa yace "Sorry!" Ta fashe da wani sabon kukan tace "It's paining me" kallon yatsan nata yake, ido ya lumshe a hankali ya sunkuyo dai dai kan yatsan yana hura mata iska, itama lusmshe idon tayi tana jin d'umin iskar da yake hura mata, har ya d'ago idonta na a lumshe, cute face d'inta da eye lashes d'inta ke kwance ya k'urawa ido, a hankali itama ta bud'e manyan idanunta ta sauk'e kan face d'inshi, cikin wani irin murya yace "Does it still hurt?", a hankali ta gyad'a mishi kai, spirit d'in da ya saka jikin wool d'in ya d'auko yasa mata kan yatsan, ido ta rintse ta saki k'ara tareda k'ank'ame mishi hannu tana haawaye.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
51.....
Sake mata hannun yayi yana kallonta ganin yanda take kuka, ta girgixa masa kai tace "Bana so" ajiye Cotton wool din yayi yace "Ita ta yanka ki?" Girgixa masa kai ta kuma yi tana hawaye tace "Knife ta bani" bai kuma cewa komai ba ya mike xai fita, tace "Ka kira min uncle ya xo" juyawa yayi ya kalleta, tana hawaye tace "Call me Uncle" wani kallo ya mata ya fice daga dakin. Haka tayi ta xama ita kadai tana kuka tana yarfe hannu, da ta ga jinin ya fara xuba sai ta goge jikin farin bedsheet din, gajiya tayi da xaman ta mike ta fita daga dakin har lokacin tana hawaye, dakin da take ta shiga ta kwanta. Karfe tara Humainah ta shigo dakin rike da cup din tea da plate din potatoe da kwai ta ajiye mata, Jasmine ta mike da sauri tana kallonta da idonta da suka rine don kuka tace "Anty ki kira min uncle" tsayawa kallonta Humainah tayi, sai da ta sake maimaitawa sannan tace "Waye Uncle?" Jasmine ta goge hawayen idonta tace "Wannan uncle din nan nawa da ya tafi" shiru Humainah tayi can dai tace "Ohk" ta juya ta fita ta shiga dakin Junaid, wayarsa ta dauka ta fito ta dawo dakin da Jasmine take, number El-ameen ta dinga nema a wayar amma bata san da sunan da ya sa ba, call log ta shiga tana dubawa taga wani number da yasa My best, dialing tayi tana sa ran shi ne, bugu uku aka daga, daga daya bangaren El-ameen yace "ya?" Mika ma Jasmine wayar Humainah tayi, Jasmine ta karba tana kallon wayar, Humainah tace "Ki sa a kunne" Kai wa kunne tayi ta ji muryar El-ameen yana cewa "Captain" ta d'an bude ido tace "Uncle!" Shiru El-ameen yayi kafin a hankali yace "Baby" fashe wa da kuka tayi ya mike xaune daga kwancen da yake yace "Me ya faru baby" tana shessheka tace "I've hurt my self" yace "Where?" Tana kallon yatsan ta tace "My finger" yace "With what?" Ta kalli Humainah da ke ta kallonta tace "Knife" shiru yayi sannan a hankali yace "Sorry, an baki magani?" Ta girgixa masa kai tace "No, and it still hurt" yace "Ina Captain din?" Ta goge hawayen idonta tace "I don't know" yace "Toh wa ya baki waya?" Ta kalli Humainah tace "That Anty" yace "Where is she?" Pointing dinta tayi kamar yana gani tace "she's here" yace "Toh bata phone din" mikewa tayi ta mika ma Humainah wayar ta karba, El-ameen yace "Kin tashi lafiya?" Humainah tace "Alhmdllh" yace "Wai yankewa tayi?" Ta kalli Jasmine tace "Eh ta yanke ne" yace "Da girma wajen?" Ta kuma kallonta tace "Not dat deep amma jinin bai tsaya ba" El-ameen yace "Toh xan xo" daga haka ya katse wayar Humainah ta juya ta fita daga dakin, Jasmine ta fashe da kuka ganin hakan ta dinga rerawa. Goma saura El-ameen ya shigo gidan, junaid dake xaune balcony tun bayan fitarsa dakinsa ya dinga kallonsa har ya karaso balconyn, El-ameen ya ja kujera ya xauna yace "Next week xaka yi resume kenan" ba tare da Junaid ya kallesa ba yace "Seem so" El-ameen ya shafa kansa yace "Ashe baby yankewa tayi wai" kallonsa Junaid yayi da sauri, can ya kauda kai yace "Who's dat?" El-ameen yace "Ka fi ni saninta ai" junaid yace "Tun safe nake nan so I don't know" El-ameen yace "Ohk, can I go in?" Junaid yace "Da can tambayata kake idan xaka shiga?" Shiru El-ameen yayi bai ce komai ba, can ya fito da wayarsa sai kuma ya tuna bai da number Humainah, number Junaid din yayi dialing, Humainah dake ta masa dube dube a wayan dake cike da texts din mata yafi 50 a ciki sai dai duk bata ga wanda yake reply ba, whtspp ma haka sai dai yayi reply da sure! yeah! Lol! Ita dariya ma abun ya dinga bata, tana d'aga kiran El-ameen yace "Humainah bring her out ina waje" Humainah tace "Ohk" ta katse wayar ta ajiye ta fita ta shiga dakin Jasmine din, kwance ta ganta inda ta barta bacci ya dauketa, karasawa tayi ta shiga tashinta, Jasmine ta bude ido a hankali tana kallonta, Humainah tace "Uncle din ya xo" mikewa tayi da sauri daga kan gadon tana kallonta, Humainah tace "Yana waje" kofa ta nufa Humainah ta bi ta da kallo har ta fita, kalle kallen parlor ta shiga yi bata gansa ba, hakan yasa ta nufi balcony kamar xata yi kuka, ido hudu suka yi da shi, ta karasa kusa da shi da gudu ta duka kusa da shi tana kallonsa tace "Uncle ka xo" kallonta kawai junaid ke yi ta gefen ido, El-ameen dake kallon hannunta ya ga inda ta yanke yace "Yeah na xo" mika masa hannun tayi kamar xata yi kuka tace "Look" ya kama hannun yana kallon yatsan murya can kasa yace "Sorry, but me kike yi da wuka" ta kalli Junaid hawaye ya cika idonta sai dai bata ce komai ba, kallon Junaid din yayi shi ma ba tare da ya ce komai ba, ya mike ita ma ta tashi tsaye, gun mota ya nufa da ita junaid ya bi su da kallo, suna isa gun motar ta wara ido cike da murna tace "Uncle are we leaving, bari in dauko jakana da hijab" bai ce komai ba ya bude motar ya dauko plaster ya fito yace "Toh shiga" ba musu ta shiga ta xauna, ya yanki plastern ya kamo hannunta ya rufe gun da ta yanken, sai kallonsa take, yyi mata murmushi yace "Xai warke kin ji" kallonsa take kamar bata gane me yace ba, ya buda ido yace "It will heal" a hankali tace "Ohk!" Magani ya dauko a motar ya mika mata ta karba yace "You take one yanxu kinji?" Kai ta gyada masa, ya koma baya yace "Toh fito" kamar xata yi kuka tace "Are we not going" yace "Anjima ne ba yanxu ba" hawaye ne ya cika idonta ta fito daga motar, yayi murmushi yace "Anjiman ma baxan xo ba idan kika min kuka" share hawayen tayi a hankali tace "Na daina" wani chocolate ya dauko a motar ya mika mata yace "Toh gashi ki tafi" ta karba ta juya ta fara tafiya ya bi ta da ido, sai a snn junaid ya dauke ido daga kallonsu da yake, El-ameen ya xaga ya shiga motarsa yayi horn aka bude masa gate ya fice, tana share hawayen ta ta iso balcony din xata shiga ciki Junaid da ya wani hade rai yace "Come back here" dawowa tayi tana kallonsa, yace "Cire abun nan na hannun ki ki fita a nan" kallonsa take kamar bata gane me yace ba, ya mike yace "Nace ki cire" komawa baya tayi a d'an tsorace ta cire plastern ta jefar yace "Leave" parlon ta shiga ya koma ya xauna. Kuka tayi ba kadan ba a bedroom daga nan bacci ya dauketa. Sha daya saura junaid ya shiga parlor ya haura xuwa dakinsa, wanka yayi ya shirya ya fito yayi kwanciyarsa a parlor, can kuma ya mike ya koma sama, ya dde tsaye a corridor kafin ya tura kofar dakin da Jasmine take a hankali, kwance ya ganta tana bacci, ya shiga dakin ya karasa kan gadon ya durkusa yana kallonta, yatsanta ya kamo yana kallon inda ta yanken, ta bude ido a hankali, tana sauke idon kansa ta mike xaune da sauri, kamar bai son magana yace "Is it still paining you?" Girgixa masa kai tayi yace "Ohk! Sorry!" Ta gyada masa kai, yace "Toh kwanta" ba musu ta koma ta kwanta ya mike tsaye yana kallonta, wanda hakan yasa ta rufe ido da sauri. Kasa barin dakin yayi har bayan kusan minti goma ya ji an danna bell, ta bude ido tana kallonsa, murmushi yayi ya juya ya nufi kofa ya fita ya kulle sannan ya sauka downstairs, still yayi bakin kofa bayan ya bude yana kallon Mumynsa, ta hade rai tace "Meye haka?" Murmushi ya kirkira yana shafa kai yace "I i i was surprise ne" shigowa parlon tayi ya bi bayanta gabansa na faduwa. Tana xaunawa ya xube nan gabanta yace "Sannu da xuwa Mumy, ina yini?" Tace "Lafiya lau, ya kuke" yace "Alhmdllh wllh Mumy" yana yi ne yana kallon stairs kamar munafuki, can ya mike da sauri yace "Bari in kirata" ita dai bata ce komai ba ta bi sa da kallo don ko ba a gaya mata ba ta san bai da gaskiya wannan kame kamen, yana haura wa sama ya bude dakin Jasmine suka kusa cin karo tana kokarin fitowa, xaro ido yayi ya ja ta suka koma dakin yace "Ina xaki?" Tace "Ruwa" ya xaunar da ita xuciyarsa na bugawa yace "No xan kawo maki anjima, you know what kar ki sake ki fito yanxu kin ji koh?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Jasmine!" Tace "Uhm!" Yace "I said kar ki fito plss kin ji, kwanta kiyi baccin ki," toh kawai tace ta koma ta kwanta ya mike ya fita ya kulle dakin, dakin Humainah ya shiga ya duba ya ga ba ta, ya jima tsaye kafin ya juya ya fita ya koma parlor, xaune ya ganta kusa da Mumy kamar xata shige jikinta, Mumy na kallonsa tace "Da ina ka tafi" ya buda ido yace "Na je kiranta ban ganta ba Mumy" Mumy ta dauke kai tace "Kaji da abinda kake kullawa, kawai mutum ya maida kansa munafuki, ya dauko wasu halayyen da ba nasa ba" murmushi Humainah tayi don abun ya bata dariya ta mike ta tafi kitchen don dauko ma Mumy drinks, shi kam kasa karasawa cikin parlon yayi don gani yake kamar ta gano sa ne, tana kallonsa strictly tace "What are you up to Ahmad?" Kamar zai mata kuka yace "Nothing mum, just xuwa aikin da bana yi kwana biyu ne naji daban" hararan shi kawai take yayi murmushi ya karaso cikin parlon ya xauna gefenta ya mata side hug yace "I miss you Mumy, har xaxxabin rashin ki fa nake" kallonsa kawai take ganin yanda ya rame idanuwansa suka fito, ya langwabar da kai yace "Mumy" tace "Baka cin abinci ne?" Girgixa mata kai yayi yace "Ina ci Mumy, kewar ki ne kawai" tace "Toh ku koma can gidan" wara ido yayi yace "Koh Mumy? Toh xa mu koma" a zahirin gaskiya kawai ya fadi haka ne don xancen ya wuce kuma gaba daya hankalinsa na kan Jasmine, Humainah na shigowa parlon da drinks ya mike yace "ina xuwa Mumy" daga haka ya haura sama, a hankali ya bude dakin ya ganta xaune a kasa, ya karasa da sauri yana kallonta ya durkusa yace "Me kike a nan?" A hankali tace "Ruwa xan sha" yace "Yi hakuri bari in kawo maki yanxu" mikewa yayi ya fita ya shiga nasa dakin ya dauko goran ruwa ya fito ya dawo dakin, da kansa ya bata ta sha, yace "Toh koma kan gado" ta mike ta koma gadon.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
52___53
Jasmine ta bude ido tana kallon El-ameen tace "Uncle ya tafi" El-ameen bai ce komai ba sai kallon gate din gidansu da yake, can ya kalleta yace "Mu je" tafiya ya fara yi ta bi bayansa yana yi yana kallonta har suka iso titi, ya tsaida adai daita ya sa ta shiga sannan shi ma ya shiga, tara da 'Yan mintuna Mai adai daitan yayi parking bakin gate kamar yanda El-ameen ya umarce sa, fitowa yayi ita ma ta fito ya fiddo dari biyar ya mika masa sannan ya shiga gate din ta bi bayansa kamar xata yi kuka ganin inda suka dawo, junaid na tsaye balcony har suka iso, El-ameen ya kalli Jasmine yace "Tafi ki kwanta gobe xan xo in tafi da ke" kai ta gyada masa hawaye cike idonta tana kallonsa, gyada mata kai yayi yace "Yeah", daga ita har shi bbu wanda ya kalli junaid ta juya ta shiga parlon shima ya juya ya nufi gate, wani irin kallo junaid ya bi sa da shi har ya fita, sannan yayi tsaki ya juya ya shiga parlon, yana haurawa sama ya shiga dakinsa. Washegari Tuesday misalin sha biyu yana daki yana danne dannen laptop tun bayan da ya fita sallahn asuba bai kuma sauka parlor ba kuma idonsa biyu yana jin jasmine na ta sallama bakin kofa bai tanka ba, ita kuma bata shigo ba, muryoyin da yake ji parlor ya sa shi mikewa da sauri ya fita ya sauka downstairs, tsaye yayi bakin stairs din ya wani hade rai yana kallon wa enda ke parlon, Fatima ce da khadija sai Humainah, ga kuma jasmine dake xaune kan rug da plate din abinci gabanta, gaba daya kallonta suke barin fatima da idanuwanta suka kara girma don mamaki, kallo daya Humainah tayi masa ta dauke kai, fuska a daure ya karasa cikin parlon yana kallonsu khadija yace " With whose permission ku ka shigo min gida?" Khadija tace "Mumy ce tace mu xo mu taya...." Wani mugun kallon da yake mata yasa ta yin shiru ita ma ta hade rai, fatima kam dama bata dago kai ba, ya juya yana kallon Humainah yace "Kika bude masu kofa without permission dina koh?" Tabe baki tayi bata ce komai ba, kallonta ya tsaya yi na kusan second goma sannan ya juya yana kallon Jasmine da ta kasa cin indomien jin yana masifa, da ganinta kasan a tsorace take, tun kan yace komai muryarta na rawa tace "Ina jin yunwa ne shine na gaya ma Anty ta ban indomie" yace "Tashi ki bar parlon nan" mikewa tayi xata tafi sama ya dawo da ita yace "Dauki abincin" ta durkusa ta dauka ta wuce. Yana kallon kannin nasa yace "Kun san Allah if I shud hear a word daga bakin ku a kan komai na gidana xan maku abinda ban taba ba, nd I mean it" daga haka ya juya ya koma sama. Bayan Azahar su fatima suka bar gidan duk da ba haka Humainah ta so ba, sun dai samu ya basu kudin mota, sama ta haura bayan tafiyarsu ta shiga dakinta, bude kofar aka yi ta juya da sauri ta ga Jasmine, karasowa cikin dakin tayi hawaye cike idonta tana kallon Humainah a hankali tace "Anty cikina na min ciwo" ido Humainah ta xuba mata can tace "Kin ci abincin da na baki?" Girgixa kai tayi tace "Amai xan yi idan na ci" Humainah tace "A'a ki je ki ci dai....." Hawayen dake makale idonta ya gangaro tace "Anty ki kira min uncle in gaya masa" Humainah bata ce komai ba har sai da Jasmine tace "Kin ji" gado ta nuna mata tace "Toh xauna ina xuwa" Jasmine ta xauna ita kuma ta juya ta fita, dakin junaid ta shiga ta gansa kwance idonsa lumshe, lallabawa tayi ta karasa gun da wayarsa yake ta dauka ta fita, tana fita ya mike ya bi bayanta, tana tsaye dakinta tana kokarin dialing number El-ameen ya shigo, still tayi tana kallonsa sai kuma ta hade rai, kallo daya yayi ma jasmine ya fixge wayar yana kallon wanda take kira, da sauri ya katse yana mata mugun kallo yace "Kee!" Turo baki tayi tace "Toh ita ce tace in kira mata" juyawa yayi yana kallon Jasmine da tayi mugun tsorata, ya kuma kallon Humainah ya hade rai yace "Ki bar min irin haka a gidan nan, ke xata gaya ma ki kira mata shi... Are you on ur senses?" A hankali Jasmine ta mike xata fita ya fixgota, kuka ta saki tana kallonsa yace "Me xa ki ce masa?" Muryarta na rawa tace "That my tummy is aching" wani kallo yayi mata yace "Yayi abinda yafi aching din ma, fita daga nan" da sauri ta fita, shima ya juya ya fice, Humainah ta tabe baki ta rufe kofarta. Har dare Jasmine sai juye juye take a daki, tayi kukan har ta gaji, yana son xuwa gun ta amman bakin hali ya hanasa Lol, duk ya rasa sukuni har kusan karfe tara, mikewa yayi ya fita ya shiga dakin Humainah ya sameta xaune gaban mirror tana danne dannen wayarta yace "Kin bata abinci?" Ba tare da ta kallesa ba tace "yana kitchen ai" juyawa yayi ya fita xai koma dakinsa, tsaye yayi bakin kofarsa ya kasa shiga dakin yana kallon dakin da take, karasawa yayi ya tura kofar a hankali dai dai lokacin da ta mike xata bayi da saurinta, bin ta yayi da kallo sai kuma ya ga ta durkushe nan bakin kofar ta fara kwararo amai, shiga dakin yayi da sauri ya isa kusa da ita ya durkusa ya dagota yana kiranta, sosai ya ji jikinta yayi xafi, ta dago jajayen idonta tana kallonsa ta fashe da kuka tana rike da cikinta, ai bai san lokacin da ya hade ta da jikinsa ba, ba shiri ta hadiye kukan da take, xame jikinta tayi, ya mike da kyar yace "Am am sorry jasmine...." Kasa dagowa tayi sai hawaye, ya kama hannunta ta mike ta shiga bayi ta wanke bakinta ta fito ta kwanta, ya gyara gun aman ya dawo dakin yana kallon agogo, ya dawo kusa da ita yace tashi mu je asibiti, girgixa masa kai tayi da kyar tace "No ka kira uncle" hade rai yayi ya dau hijab dinta yace "tashi mu je nace" hawaye cike idonta ta mike xaune ta karba hijab din ta sa, kasa tashi tsaye tayi, hawaye na sakko mata tace "Baxan iya tashi ba captain" kallonta yake cike da tausayinta ya durkusa kusa da ita yace "Ina ke maki ciwo ne?" Cikinta ta nuna masa, sai kuma ta fashe da kuka ta koma ta kwanta, mikewa yayi ya fita xuwa dakin Humainah, har ta kwanta ya karasa ya kunna bedside lamp ta bude ido da sauri tana kallonsa ta mike xaune tace "Me ya faru?" Ya dan shafa kai yace "Plss asibiti xa ki raka mu in kai yarinyar nan amai take ta yi" hade rai tayi tace "Bacci ni xan yi, ka kira mata El-ameen mana" yace "No it's late yanxu kar a shiga hakinsa" wani kallo tayi masa tace "I see" ta koma xata kwanta ya rikota ta buge hannunsa tace "Leave me joor" rungumeta yayi yace "Haba wife taimako fa xa kiyi" turasa ta shiga yi tace "Ka rabu dani don Allah ni baccina xan yi" ganin kiss dinta yake son yi tace "Ohk naji naji, mu je" murmushi yayi ya saketa ta mike fuskarta daure ta dau hijab har kasa tasa ta fita ya bi bayanta, ba laifi ita ma ta tausaya ma Jasmine don da ganinta kasan tana jin jiki, tana rike da ita suka shiga motar, wani private hospital suka tafi, basu sha wahalan ganin likita ba, likitan na ta kallonsu har ya xaunar da ita sannan shi ma ya xauna, yayi murmushi yace "Couples?" Kallonta Junaid yayi da sauri ita ma ta kallesa suka hada ido ta dauke kai, ya dan wara ido yace "Ohh No! We are not" Likitan yace "Ohh sorry!" Murmushi kawai junaid yayi ya d'an saci kallonta, tambayoyi likitan ya fara mata junaid na bada amsa don kin cewa komai tayi, nan dai ya duba ta ya rubuta mata magunguna da allura sai test da ya rubuta xa a mata gobe da safe, malt junaid ya siya mata ta sha kafin a mata alluran sanin bata ci komai ba, fir taki yarda ayi mata tana kuka a rikice, junaid ya hade rai yace "Xaki sha mari fa, Meye a alluran" fixgota yayi ganin taki yin shirun, ya hade rai yana kallonta, da kyar ta yarda aka mata shima a cinya yana tsaye kanta, ta dinga ihu tana rusa kuka, yana rike da hannunta yana kallon yanda take kukan suka fito reception, dariya ma take basa, Humainah da dama bata bi su ba tana reception din xaune ta hade rai ganin yanda ya rike ta yana kallo, har suka shiga mota kuka jasmine take sosai, shi dai Junaid bai ce mata komai ba haka Humainah, ta gaji don kanta tayi shiru, suna isa guda Humainah ta bude motar ta fice, bin ta da kallo yyi sannan ya xaga ya bude motar ya ga shirun bacci tayi ashe, kiranta yayi murya can kasa ta bude ido a hankali yace "Fito" fitowa take son yi amma ta kasa, ta nuna masa cinyarta cikin tsarkewar murya tace "It's aching" kallon balcony yayi ya ga har Humainah ta shige, hannu ya mika mata ta kama sannan ya fito da ita, yana rike da ita suka shiga parlon, bai bari sun hada ido da Humainah dake parlon ba ya haura sama da ita, magungunanta ya bata ta karba ta sha yace "Toh kwanta ki yi bacci" girgixa masa kai tayi tace "Xan cire kaya" yace "Toh cire" mikewa tayi ta sauka ta cire hijab xata cire doguwar rigar jikinta yace "Noo tafi bayi ki cire" tace "Toh" sannan ta shiga bayin, kasa fita yayi daga dakin, har ta fito daga ita sai inner, xaro ido yayi ya kasa cewa komai bai kuma daina kallonta ba, tace "towel din...." Ai bai tsaya saurarenta ba ya fice daga dakin. Kayan baccinta ta dauka a closet ta sa sannan ta kwanta. Downstairs ya sauka ya kashe kayan wuta ya koma daki. Wanka yayi ya daura alwala ya shirya ya kwanta, sai dai ya kasa bacci har kusan sha biyu ya mike daga karshe ganin he's just deceiving his self ya fita, dakin Humainah ya shiga ya kunna wutan dakin, yayi mamakin ganinta xaune kan gado ta hade kai da gwiwa, dagowa tayi tana kallonsa da rinannun idonta, ya kashe wutan ya karasa da kyar ya xauna gefenta yace "What happened?" Sharesa tayi xata kwanta ya rikota ta fashe da kuka, ya rungumeta cikin sanyin murya yace "talk to me" turasa ta shiga yi ya ki saketa hakan yasa tayi lamo jikinsa hawaye na saukowa idonta, sun kusa minti goma a haka ya dago kanta yana kallonta da idonsa da suka kada murya can kasa yace "Kina da alwala?" Kin cewa komai tayi har sai da ya kirata, tace "na me?" Yace "Toh je kiyi" tace "Ni nayi" mikewa yayi yace "Ohk let pray" wani kallo take masa kafin tace "Na me?" yyi shiru yana kallonta, can ya mike ya hau darduman dake shimfide kasa yace "Am waiting" kin tashi tayi yace "Ke fa nake jira" da kyar ta sauka duk gabanta na faduwa ta dau hijab ta sa, raka'a biyu ya ja su, suna sallamewa ta mike ta haye kan gado ta shige cikin bargo ya bi ta da kallo, ya jima xaune kan darduman yana addu'o'i kafin ya mike ya dauke darduman ya nufi kan gadon ya xauna, cire bargon yayi ta mike xaune ta hade rai tace "Meye haka?" Ya hau gadon yana kallonta yace "Ina ruwana da ke kiyi baccin ki" kin kwanciya tayi da ganinta kasan a tsorace take, yayi murmushi ya kwanta ya juya mata baya, ta kusa minti biyar xaune kafin ta kwanta nesa da shi xata ja bargo ya koma kusa da ita ya jawota, ta fashe da kuka tace "Ya A.jay bacci fa xanyi plss" a hankali yace "Naji, yi baccin ki amma a jiki na" shiru tayi gabanta na faduwa can tace "Toh ni da bargo nake kwanciya" yace "Ga ki ga shi", bbu yanda ta iya haka ta kwanta ta rufa masu bargo tayi lamo ta rufe ido, sai da ya ga ta fara bacci ya cire bargon, ranan ta fadi ma 'yan garinsu bata taba tunanin haka Ya A.jayn yake ba, ba irin rokon da bata yi masa ba, bbu wanda bata kira masa ba barin Hajja amma duk a banxa abun ka da Novice da mai dacin ran tsiya, tuni baccin wahala da tashin sense yayi gaba da ita, shi kam rasa gane abinda yake ji game da ita a ransa yayi. Da asuba bayan ya dawo daga mosque duk ta daga masa hankali da kuka ita ya kira mata Mumy, ta kuma ki barin ya xo kusa da ita, ya ma rasa abinda xai yi, kyaleta yayi ya fita daga dakin, har xai shiga dakinsa sai kuma ya bude na Jasmine durkushe ya ganta can jikin gado tana kuka ya karasa ciki yana kallonta da mamaki yace "me ya faru kuma" kasa cewa komai tayi sai hawaye, ya durkusa kusa da ita da damuwa yana kallon idonta da ya kumbura don kuka yace "Cikin ne har yanxu?" Ta fashe da kuka ta kamo hannunsa tace "Captain it's still paining me, yana min ciwo sosai" ganin yanda ta rikice yasa hankalinsa ya tashi ya mike ya fita daga dakin ya shiga nasa ya dau wayarsa yayi dialing number El-ameen. Bugu daya ya daga, junaid yace "Pls come over yanxu" El-ameen dake kwance ya mike xaune yace "Me ya faru?" Junaid yace "Hurry up plss" El-ameen ya d'an bude ido yace "Toh fah" sai kuma yayi dariya yace "Kayi aika aika kenan, ba inda xan xo sai dai in turo maku nurse" Shiru junaid yayi d'an ya so ba shi dariya, yace "kaga bana son walakanci ina jiran ka" El-ameen yace "Allah ba da ni xa ayi wannan ba, me xan maku idan na xo?" Junaid yace "Ohk naji ka turo nurse din, but kai ma ka xo don baby ma bata da lafiya tun jiya" El-ameen ya mike tsaye yace "da gaske? Me ya sameta" Junaid ya katse wayar ya xauna ya shafa kansa, murmushi yayi yana mamakin sharp thinking irin na El-ameen, mikewa yayi da sauri ya fita ya koma dakin Jasmine, yanda ya bar ta haka ya sameta ya durkusa kusa da ita cike da tausayinta duk ta rasa inda xata sa kanta sai kuka take, da kyar tace "Captain ka ce Uncle ya xo plss" hade rai yayi yace "Baxan ce ba" kai ta gyada masa hawaye na sakko mata alamar to, can kuma cikin kuka tace "Ka ban Magani captain" hannunta ya kamo yace "Xa a kawo maki yanxu kin ji" ajiyar xuciya ya sauke jin shigowar motar El-ameen, bayan 3 mint ta fara kokarin mikewa tace "Uncle I want to ease my self" hade rai yayi jin tace uncle, ta mike da kyar tana duddukawa, mikewa yayi da sauri ganin abinda ke jikinta, ita ma ta kalli inda yake kallo, ai sai ta fasa ihu a tsorace tana kokarin daga rigar dai dai lokacin da El-ameen ya bude kofa ya shigo dakin, tana ganinsa ta kuma fashe wa da kuka tayi gunsa da sauri, shi ma kallon jikinta ya shiga yi, a rikice take cewa "Uncle kaga blood" xata daga rigar ya kama hannunta, ya d'an kalli Junaid ya ga shi yake kallo, a tare suka dauke kai, Junaid ya juya ya fice daga dakin, El-ameen ya kalleta da tausayi ganin yanda take kuka a hankali yace "Yi hakuri kin ji jewel" wayarsa ya ciro ya kira nurse daga clinic, ganin tsayuwar ke sa ta flow yace ta xauna taki, da kansa ya xaunar da ita ya durkusa gabanta.
[12/24/2017, 10:43] Khaleesat Haiydar: ? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
54......
Ko da nurse din ta xo kin bari El-ameen ya fita ya bar ta Jasmine tayi, ya fiddo wayarsa ya kira junaid har ya gama ringing bai daga ba, ya kuma kiransa nan ma no answer, kallon Jasmine da ke ta hawaye yayi yace "Nace maki am not going, yanxu xan dauko maki magani in dawo" tana girgixa kai tace "Noo" hade rai yayi yace "To bari in yi tafiyata..." Ta kamo hannunsa cikin kuka tace "Noo plss kar ka tafi" yace "Toh yanxu xan dawo" daga haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita, xaune ya ga junaid a balcony ga wayar a hannunsa, bai ce masa komai ba ya fita waje ya shigo da nurse din, ta gaida junaid ya amsa ba tare da ya kalleta ba suka shiga parlon tare da El-ameen, bai shiga dakin ba ya tura nurse din bayan ya mata bayani don yasan ba lallai ta yarda da nurse din ba idan ta gansa, tsaye yayi corridor din rooms din yana mamakin halin junaid, now a days the thing is just getting worst ma, tabe baki yayi yana nan tsaye har bayan kusan minti talatin nurse din ta fito tace "Dr bbu sanitary pad," shiru yayi sai kuma yace "then sai na je hospital don shaguna basu bude ba yanxu" tace "Ohk, ka taho da injection da drugs" yace "Ohk" ya juya ya sauka ita kuma ta koma dakin, da ido junaid ya bi sa har ya shiga motarsa ya bar gidan. Bakwai saura El-ameen ya dawo ya kira nurse din ta fito ya mika mata ledan hannunsa ta karba ta koma dakin, yana nan tsaye har ta kuma fitowa tace "Tayi bacci Dr" yace "Ohk shiga dakin can" ta kalli kofar dakin da ya nuna mata tace "In yi me?" Yace "Bata da lafiya ita ma ki duba ta" bude kofar tayi ta shiga da sallama, ta karasa gun gadon tana kallon Humainah da ke kwance cikin bargo tana bacci, yaye bargon tayi wanda hakan ya farkar da Humainah ta mike xaune da sauri tana kallon nurse din, Nurse din ta mata murmushi xata yi magana idonta ya sauka kan gadon, shiru tayi sai kuma ta juya ta nufi kofar da take tunanin bathroom ne, komawa Humainah tayi ta kwanta tana kokarin maida hawayen da ya cika idonta, ba a dau lokaci ba nurse din ta fito ta iso gun gadon tace "sannu sister tashi mu je bayi" bata mata musu ba ta cire bargon ta mike tsaye, kama hannunta nurse din tayi suka shiga bathroom din, Humainah ta kalleta cikin tsarkewar murya tace "Xan iya da kai na" nurse din tace "Toh shikenan" daga haka ta fito ta shiga gyaran dakin, tana nan har Humainah ta fito, nurse din ta tambayeta inda kayanta yake ta nuna mata ta bude ta fiddo mata da gown, cikin 'yan mintuna ta gama shirya wa nurse din sai kallonta take don tasan daurewa kawai take, darduma ta shimfida mata ta bata hijab ta karba ta hau kan darduman ta tada sallah, nurse din ta fita don xuwa hado mata tea tasha kafin ta bata Magani, da mamaki ta kalli El-ameen dake tsaye har lokacin a corridor tace "Kana nan har yanxu Dr, ai da ka xauna parlor" yace "Am okay, ya jikin nata?" Tace "Da sauki I want to go nd make a cup of tea for her" yace "Are you sure she's ohk?" Tace "Ka shiga ka duba Dr" yace "No ba sai na shiga ba, make the tea for her na taho mata da drugs" tace "Okay," sannan ta sauka, ba a dau lkci ba ta dawo da cup din tea din ta kai ma Humainah, ba laifi ta karba ta sha, nurse din ta fito El-ameen ya bata magungunan sannan ya sauka downstairs, parlor ya ga junaid kwance yana kallo, El-ameen bai bi ta kansa ba ya fita yayi xaman sa a balcony, nurse din na saukowa Junaid ya haura sama, kofar dakin da Jasmine take ya tura a hankali ya shiga ya tsaya daga bakin kofar yana kallonta, bacci ya ga take ya karasa kusa da gadon ya durkusa dai dai fuskarta yana kallonta, bude ido tayi a hankali ta mike xaune da sauri ganinsa, ya d'an koma baya yace "Cikin ya daina?" Kallon jikinta ta shiga yi, sai kuma ta gyada masa kai tace "Uncle ya tafi?" Hade rai yayi yace "Ban sani ba" tayi shiru bata ce komai ba, ya mike ya fice daga dakin, dakinsa ya shiga don yin wanka, Jasmine ta sauko daga kan gadon tana kalle kallen jikinta, a hankali ta dinga tafiya har ta fito ta sauko downstairs, hawaye ya cika idonta ganin bbu El-ameen, har xata koma sai kuma ta fita parlon, wara ido tayi ganinsa xaune yana danna waya, ta karasa da sauri ta durkusa kusa da shi tace "Uncle!" Yayi murmushi yace "Har kin tashi?" Gyada masa kai tayi, yace "Toh cikin ya daina?" Shiru tayi sai kuma a hankali tace "Eh ya daina, uncle wannan Antyn tace min am on my period, Meye wannan?" Ya d'an bude ido yace "Nima ban sani ba" shiru tayi sai kuma ta kalli jikinta a hankali tace "Uncle har yanxu fa yana yi" murmushi yayi yace "Xai daina, je ki duba min ko Anty ta tashi a sama" tace "toh" sannan ta mike ya bi ta da kallo har ta shiga parlon, dakin Humainah ta shiga ta ganta kwance tana kuka, karasa gun gadon tayi ta durkusa kamar ita ma xata yi kukan tace "Anty menene?" Shiru Humainah tayi mata, hakan yasa ta mike ta fita ta koma gun El-ameen, hawaye cike idonta tace "Uncle kuka take, she don't want to talk to me" yace "Captain din fa?" Tace "Yana dakinsa" mikewa El-ameen yayi ya shiga gidan ta bi bayansa, tsaye yayi bakin kofar Humainah yayi sallama har sau biyu bata amsa ba, Jasmine tace "Ka shiga tana ciki" bude kofar yayi ya mata alamar ta shiga, tana shiga ya bi bayanta, karasawa cikin dakin yayi ya tsaya d'an nesa da gadon yana kallonta yace "Ya jikin Humainah?" Mikewa xaune tayi amma ta kasa juyowa tace "Da sauki" yace "Ohk kiyi hakuri, Allah ya sauke kin ji" kai kawai ta gyada masa yace "Go to sleep xa ki ji sauki sosai" kwanciya tayi ya juya ya fita Jasmine ta bi bayansa, a hankali Jasmine ta kamo hannunsa tace "I hate that captain, he's so mean" bude ido El-ameen yayi, sai kuma ta sunkuyar da kai a hankali tace "Though I like him also, he's fine just like you" dariya El-ameen yayi yace "To naji tafi dakin ki" ta hade rai tace "Ina xa ka" yace "parlor" bude kofa aka yi duk suka juya Captain ya fito, suna hada ido da Jasmine ya watsa mata wani kallo a kan idon El-ameen kuma, xame hannunta tayi a hankali daga na El-ameen ta juya ta shiga daki, junaid yace "You are still around ashe, tot ka tafi" El-ameen bai tanka sa ba ya sauka kasa, junaid ya bude kofar Humainah ya shiga ya karasa gun gadon ya xauna yace "Good morning wife" rufe ido tayi da sauri, yayi murmushi xai dagota ta mike xaune sai kuma ta fashe da kuka, ya wara ido yace "Toh kuma, Allah ya baki hakuri just came to say ya jikin" daga haka ya mike ya fita, dakin Jasmine ya bude ya ganta xaune ta rungume hannayenta kiris ya rage ta fashe, yace "Ai kin iya dafa indomie koh?" Kai ta gyada masa a hankali, yace "Toh xo ki dafa mana" mikewa tayi ya juya ta bi bayansa, indomie hudu ya fiddo mata tace "Har da Anty?" Yace "Eh" kujera ya dauko ya xauna kitchen din yana kallon yanda xata yi girkin, har ta gama bayan kusan minti goma idonsa na kanta bai ma san ta gama ba, ta karasa kusa da shi ta duka a hankali tace "Captain!" Rufe ido yayi ya bude da sauri ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Jasmine" bude ido tayi a hankali tace "Na gama" mikewa yayi a hankali har lokacin yana rike da hannunta yace "Ohk dear, dauka daya ki kai ma Anty sai ki dauka kema ki ci" toh tace ya sake hannunta ya juya ya fita. Da yamma nurse Salima ta kuma dawowa duba Humainah da Jasmine kamar yanda El-ameen ya umarce ta. Da magrib junaid ya shirya ya tafi gida, gabansa sai faduwa yake don bai san yanda xa su kwashe da Mumy ba, part din Abbansa ya fara shiga don gaidasa, ya tarda Umma da Hajiya a parlon, xaunawa yayi kasa ya gaida Abba ya amsa yana tambayarsa gida, yace "Alhmdllh Abba" juyawa yayi yana kallon Su Umma ya gaida su, duk suka amsa masa da fara'ar da bai kai ciki ba ana tambayarsa amarya, Hajiya ta mike ta fice daga parlon bayan ta ma Abba sallama Umma ta bi bayanta, ya d'an jima xaune parlon Abba sannan ya mike yace masa xai je gun Mumy, kamar munafuki ya xauna kasa ya sunkuyar da kai yana gaida Mumy, ta amsa masa bbu yabo bbu fallasa, rasa abun cewa yayi haka ya karashi xaman sa Mumy nata harkan gabanta ya mike yace xai tafi tace "Allah ya tsare" ya fita parlon, bai yi mamakin ganin su Hajiya da Umma xaune a spot dinsu ba, ko sallama bai yi masu ba ya fice, Hajiya tayi murmushi tace "Komai dai ya kusa xuwa karshe in da rai da lafiya, sai mun cusa ma iyayenka tsanarka" gidansu El-ameen junaid ya nufa bayan ya bar gidan, yayi mamakin ganinsa xaune waje, ya xauna gefensa yace "kai kuma xaman waje ka fara yanxu kenan" El-ameen ya shafa kai yace "Yafi min alkhairi ne, kawai Ummi ta dau fushi da ni kan abinda bansan komai kai ba, ni wllh ban san kayan me take nufi ba" junaid yayi shiru can yace "Toh ka tambayi Abba mana," El-ameen yace "He also don't want to say anything about it to me" junaid yace "Toh tashi mu je mu samu ummin sai mu tambayeta" El-ameen yace "A'a ni baxan je ba, wannan Kanwar Abban nawa na ciki" mikewa Junaid yayi ya shiga gidan, Small mum din El-ameen ce xaune parlon da Ummi, Ummi ta hade rai ganinsa ya d'an shafa kai ya karaso ya xauna kasa kusa da Ummi ya gaida ta ta amsa bbu yabo bbu fallasa, ya gaida Anty dake parlon ita ma ta amsa masa haka, yana shafa kai yace "Ummi mu fa bamu san kayan me ake cewa ba" Anty tace "Eh ai baxa ku sani ba munafukai, irin yanda aka maka haka xa a masa shi ma kwanan nan" ko kallonta Junaid bai yi ba ya kalli Ummi ya marairaice yace "Allah Ummi ba mu sani ba" Ummi tace "kayan auren mutum ku ke hadawa a boye ko na me" junaid ya xaro ido yace "Kayan aure kuma Ummi, wani kayan auren?" Ummi ta tabe baki tace "Na sha gaya masa yanda aka yi maka a gida haka shi ma xa a masa yana xaton fadi nake kawai koh, to xaku sha mamaki daga kai har shi" junaid yayi shiru can yyi murmushi yace "toh ayi masa hakan kawai Ummi, don nima ina masa maganan aure baya saurarana, ni ba gashi ina xaune lafiya da matar ba" Ummi tace "To tafi daki ka ga kayan sun yi" junaid ya d'an bude ido yana kallonta, sai kuma ya mike ya nufi bedroom dinta, ko da ya fito dariya kawai yake yace "Wllh sun yi sosai Ummi, Allah ya saka da alkhairi" junaid bai ce ma El El-ameen komai ba da ya fito kawai dariya yake bakin rai, El-ameen yace "Meye haka?" Junaid yace "Nothing, na shawo kan Ummi ta hakura wllh" kallonsa kawai El-ameen yake bai ce komai ba.
Bayan kwana biyu da ya kama ran lahadi Humainah ce tsaye kitchen tana girkin lunch Jasmine na daga bakin kofar kitchen din tsaye duk ta cika ta da surutu ita dai aikinta take ba tare da ta tanka ta ba don da tace ta tafi xata dawo, junaid kuma na sama, danna bell aka yi Jasmine ta xaro ido tace "kila uncle koh Anty?" Humainah bata tanka ta ba ta fita daga kitchen din, jasmine ta bi bayanta da sauri, suka isa gun kofar a tare ta bude, wata yarinya da baxata wuce su ba ce tsaye bakin kofar Humainah sai kallonta take don bata santa ba, yarinyar tayi murmushi tace "Baki san ni ba koh, yi hakuri ruwan sha xa ki ban don Allah, na xo gidan aunt dina ne dake layin nan ne wllh wai ashe jiya da daddare suka yi tafiya da mijinta gashi duk na gaji bbu shagunan siyan ruwa nan kusa" Humainah tace "Ohk, shigo" yarinyar ta shigo tana bin ko ina na parlon da kallo ta samu kujera ta xauna, fridge Humainah taje ta dauko mata ruwa da drink ta ajiye mata, Yarinyar ta mata godiya tana murmushi Humainah ta koma kitchen, kallon Jasmine da ta xauna kasa kusa da ita tana kallonta yarinyar tayi tace "Sannu ya sunan ki?" Jasmine ta d'an wara ido tace "Uncle na kira na jewel, captain na kira na Jasmine, Mamina na kirana Baby" yarinyar dai sai kallonta take, Humainah dake kitchen tana jin su ta tabe baki ta ci gaba da girkinta, yarinyar tace "Waye captain, waye Uncle?" Jasmine xata yi magana suka ji taku stairs, shiru tayi tana kallon stairs din haka ma yarinyar har ya sauko, kallo daya yayi masu ya dauke kai, yarinyar tace "Ina kwana" ya ji bai ji ba ita dai bata sani ba don bai amsa ba ya shiga kitchen ya rufe kofar yana kallon Humainah yace "Wacece ta shigo min gida?" Humainah ta daure fuska tace "Ruwa xata sha" ya wani hade rai yace "Ruwa? Kika san daga inda take maxa fita ki sallameta kar ki sha mamaki" bata tanka sa ba ta ci gaba da girkinta, ya bude kofar ya fice, kallon Jasmine yayi yace "Come here" mikewa tayi ta bi bayansa don stairs ya nufa, yarinyar ta bi su da kallo, fitowa Humainah tayi ta xauna parlor ganin bata ga Jasmine parlon ba ta kalli stairs, yarinyar tace "Nagode kwarai 'yar uwa, ni sunana Hadiza" Humainah tace "Welcome" yarinyar ta mika mata waya tace "Sa min number ki mu dinga xumunci naga kina da kirki" Humainah ta karba ta sa mata number ta mika mata, yarinyar tace "Suna fa?" Humainah ta gaya mata, tace "Allah sarki, amma kishiyar ki ce wannan da na gan ku tare" Girgixa mata kai kawai Humainah tayi, tace "Ayya, to ni xan koma xa mu ke xumunci" har bakin kofa Humainah ta rakata yarinyar sai murmushi take ta fita daga parlon, Humainah ta kulle, ta koma kitchen. Da yamma misalin karfe shidda motar El-ameen ya shigo gidan, Junaid dake daki ya mike yana lekensa ta window don tun ranan basu sake haduwa ba, ko parking din arxiki bai yi ba ya fito da ganinsa kasan yana cikin tashin hankali, junaid ya fashe da dariya har da kyakyatawa ya sake curtain din ya koma kan gado ya dinga dariya, direct dakinsa El-ameen ya nufa don bbu kowa parlon, kwankwasa kofar yayi junaid ya mike xaune yace "Come in" ya tura kofar ya shiga yana kallon junaid dake ta kokarin danne dariyarsa, junaid ya mike tsaye yace "Ya aka yi na ganka haka besty, me ya faru" xaunawa kan gado El-ameen yayi ya rike kai, Junaid ya xauna gefensa yace "Talk to me mana" El-ameen ya dago da kyar yace "Kaga abinda su ummi ke shirin min sai kace wani mace, wllh not me" junaid yace "Me xa a maka?" El-ameen yace "Wai aure!" Junaid ya xaro ido sai kuma ya fashe da dariya El-ameen ya mike yana kallonsa, yayi mai isan sa sannan yace "Nima haka ka min" kofa El-ameen ya nufa junaid ya rikosa da sauri yana dariya yace "Wllh ramawa na yi nima haka fa ka min" da kyar ya lallaba El-ameen ya xauna, sannan yace "Toh kai yanxu kana da warce kake so ne da har xaka damu kanka, ba gashi nima haka aka min ba kuma ina xaune lafiya?" Shiru El-ameen yayi kafin yace "Ni ina da warce nake so" junaid yace "To wacece?" Da kamar baxai ce komai ba sai kuma ya shafa kansa a hankali yace "Baby!" Kallonsa junaid ya tsaya yi ko kiftawa bai yi, El-ameen ya mike yace "Kuma ita xan kai masu, in ma basu yarda ba ni sai na aureta don Allah xan iya hallaka warce xa a hada ni da" daga haka ya nufi kofa Junaid ya mike ya fixgosa yace "Wace babyn kake nufi?" El-ameen yace "Warce ke gidan ka" wani kallo Junaid ya watsa masa yace "Sai ka jira randa na maida ta gun iyayenta sai ka bi ta ka aureta, yanxu kam baka isa ba" murmushi El-ameen yayi yace "Koh?"
*Haske Writers association*??
[12/25/2017, 22:31] Khaleesat Haiydar: ? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
55.....
Wani kallo junaid ke masa ya sake sa ya koma baya yace "Yess! Me ya hana ka son auren nata lokacin da take hauka? You can call what ever prize you wish to for giving her your attention and I will pay you" El-ameen bai ce masa komai ba ya gyara kwalar rigar sa ya juya ya fita daga dakin, a stairs suka kusan cin karo da Jasmine, ta koma baya ta wara ido ganinsa tace "Uncle! When did you come" murmushi ya kirkirar mata yace "Am coming" ya bi ta gefenta ya sauka ta bi sa da kallo. Tana jin fitar motarsa ta bata fuska tayi daki da sauri xata fara kuka. Washegari monday Junaid na dawowa masallaci da asuba ya shiga dakin Humainah, ya sameta xaune kan darduma daga bakin kofar ya tsaya yace "You are resuming school today" tace "Na sani" juyawa yayi ya fita, ya bude dakin Jasmine, kwance ya ganta tana bacci cikin bargo ya cire bargon ta mike xaune da sauri yace "Tashi kiyi sallah, after that you brush ur teeth nd take ur bath" daga haka ya juya ya fita ya koma dakinsa, wanka Humainah tayi ta gyara bedroom dinta ta fito parlor nan ma ta share sannan ta shiga kitchen, ruwan lipton ta daura ta xuba kayan kamshi sannan ta fara peel din potatoe. Karfe bakwai saura junaid ya fito daga bedroom sanye da uniform dinsa don ranan sati biyun da ya dauka gun aiki ya cika, kitchen ya tafi ya tsaya daga bakin kofa yana kallon Humainah, ta juya tayi masa kallo daya ta dauke kai, yace "Xan yi tafiyata in kyale ki if you are not ready" tace "Toh ai dai ba xaune nake ba" bai ce komai ba ya karasa cikin kitchen din ya dau cup ya hada tea ya fita. Yana xaune parlor har karfe bakwai yayi Humainah ta fito ta wuce sama, can ya mike shi ma ya tafi saman, dakin Jasmine ya bude ya ga ta gama sa kaya yace "Fito ki ci abinci" shiru tayi tana kallonsa daga sama xuwa kasa yace "Baki ji na ne" komawa baya ta shiga yi a hankali har lokacin idonta na kansa sai kuma ta fashe da kuka tana girgixa kai tace "Ni bana son kayan nan captain" ya kalli farin shirt din uniform da navy blue trousers din dake jikinsa yace "Me suka maki kayan" ta kuma fashe wa da kuka tace "I don't like it" wani kallo ya mata ya juya ya fice daga dakin, a hankali ta xauna gefen gado tana xaro ido kamar me son tuna abu, dakinsa ya koma ya dauki wayarsa da hularsa ya fito, dai dai lokacin da Humainah ta fito ita ma rike da cup, bai ko kalleta ba ya sauka downstairs ya dau makullin motarsa, ta bi bayansa tace "Toh baxa ka kai ni makarantar ba?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Sai kuma gobe am late" daga haka ya fice daga parlon ta bi sa da kallo kamar xata fashe da kuka, ajiye cup din hannunta tayi a parlon ta koma sama hawaye cike idonta. Jasmine na jin fitar motarsa ta sauko ta tafi dining ta debi breakfast dinta ta ci a nan ta koma sama. Da yamma misalin karfe hudu saura Humainah na dakinta bayan ta daura girki a kitchen ta ji an danna bell, mikewa tayi ta fito dai dai lokacin da Jasmine ma ta fito, ko kallonta bata yi ba ta sauka, bude kofar parlon tayi ta ga yarinyar jiya a tsaye, murmushi yarinyar tayi tace "Kin gan ni kuma koh, daxu aunt dina ta dawo na taho, yanxu ma gida xan koma nace bari in shigo mu gaisa" Humainah ta d'an yi murmushi ita ma tace "Toh sannu da xuwa" hanya ta bata ta shigo ta xauna parlon, yau ma kamar jiya ruwa ta kawo mata, yarinyar sai hira take mata kamar sun dde da sanin juna, ita dai Humainah duk ta kasa sakewa, Jasmine ta shigo parlon tana kallon Humainah tace "Anty ki kira min Uncle" Humainah tace "Bani da waya" Jasmine tayi shiru bata ce komai ba, sai kuma ta juya ta koma sama, yarinyar da ta kira kanta da hadiza tace "Amma wacece yarinyar nan?" Humainah tace "Kanwar mijina ce" Hadiza tace "ohh, Allah sarki, amma basa kama ko dai 'yar uwar na family kike nufi" a takaice Humainah tace "Eh!" Don duk ta kagu ta wuce sai kallon agogo take sanin hudu da wani abu junaid ke dawowa wani time, Hadixa tace "Toh dai ki kula" Kallonta Humainah tayi da sauri, hadiza tace "Naga yanda take wani shige masa jiya da na xo" murmushi Humainah ta kirkira bata ce komai ba, hadiza tace "Ae ba abun dariya bane, ni ma nan da kike ganina na kusa dawowa anguwar gaba daya gun aunt din nan tawa sbda damuwa da yayi mata yawa, in gaya maki wata yarinya mijinta ya ajiye wai yar uwarsa xata yi karatu a gidan, in kinga yarinyar very quiet har ni ke ce ma Anty fa'ixa ta dinga sake mata don Allah don ko kallonta bata yi, to yanxu xancen da nake maki Friday mai xuwa daurin auren mijin yayar tawa da yarinyar" kallonta kawai Humainah ke yi gabanta na mugun faduwa, hadiza ta dawo kusa da ita tace "Bari ki ga hotunan aunt din tawa da yarinyar har ma da mijin" kallon hoton kawai Humainah ke yi amma sam hankalinta baya jikinta, bude gate din gidan aka yi, hadiza ta bude ido tace "In ji dai ba mijin naki bane ya dawo" kasa ce mata komai Humainah tayi, Hadiza tace "A'a kin ga ki fa kwantar da hankalin ki, ai ba duka maxan suka taru suka xama daya ba kawai ke dai ki sa ido" Humainah bata ce komai ba still har junaid ya shigo parlon, daga bakin kofa ya cire takalman kafarsa ya bar bakar safar, kallonsu kawai yake a parlon lokaci daya ya hade rai, ya nufi stairs hadiza ta bisa da kallo ta d'an bude murya tace "Ina yini" a tunanin ta jiyan da ya shareta bai ji bane, ko kallonta bai yi ba bai kuma amsa ba ya haura sama, hadiza tace "Toh bari in wuce naga kamar mijin ki bai son baki" Humainah tace "Rabu da shi" dariya Hadiza tayi ta mike tace "Toh Hajiya Humainah kinga tafiyata, gobe ko jibi xan ma dawo anguwar baki daya" Toh kawai Humainah ta iya ce mata ta rakata har bakin kofa ta wuce sannan ta dawo ta tafi sama, tana shiga daki ta xauna gefen gadonta tana tunanin maganganun Hadiza, bude kofar dakin aka yi ya shigo fuskar nan tasa a daure ko uniform bai cire ba don fitina yace "Wace yar iskar ke xuwa gidan nan?" Ko kallonsa bata yi ba ta dauke kai, ya karasa ya fixgota yace "keh! Baxa ki gaya min wacece ita ba?" Fixge hannunta tayi tace "Mutum ce kuma ai ka gane ma idonka" yace "Koh? To wllh wllh ta sake xuwa min gida xan baki mamaki daga ke har ita" daga haka ya juya ya fice, kuka ta saki duk ta rasa me ke mata dadi sosai xancen hadiza ya xauna a xuciyarta, mikewa tayi ta sauka kasa ta kashe girkin da take ta koma daki. Har bayan magrib junaid na xaune daki duk abinda ya ma El-ameen jiya ya tsaya masa ya rasa yanda xai yi, ta yaya ma xai ce yana son Jasmine, wani irin so ma yake nufi, mikewa yayi daga karshe ya dau makullin motarsa ya fita, ana kiran isha ya isa gidansu El-ameen, sai da yayi sllh a masallaci sannan ya shiga gidan, xaune ya samesa a daki da faisal, faisal na ganin junaid ya bude ido yace "Captain junaid, ashe ana ganin ka" murmushi junaid yayi ya xauna yace "Kai ma ai ba ganin naka ake ba" hira suka d'an yi da faisal, shi dai El-ameen wayarsa kawai yake dannawa, daga bisanni faisal yayi masu sallama yace xai tafi clinic ya fita, Junaid ya kalli El-ameen da ya ki kallon inda yake yace "Har da wani pretending baka gan ni ba?" Ba tare da El-ameen ya kallesa ba yace "Ai mun gaisa" Junaid ya d'an shafa kai yace "Look, am sorry about what happened yesterday, I don't know what came over me....." Katse sa El-ameen yayi yace "It's ohk, I also don't know what came over me, i was just confused, I couldn't help it... May be dat was y I uttered those words" shiru junaid yayi yana kallonsa ganin he was so serious, El-ameen yace "Yess!" Junaid yace "No idan ma sonta kake da gaske ai ba komai bane, just pray memorynta ya dawo a maidata gun iyayenta nd then you can go on...." Shiru junaid yayi don jin maganar yayi wani iri a bakinsa, El-ameen yace "Noo, ni an min mata ai" Junaid bai kuma cewa komai ba sai bayan kusan minti uku yace "Ohk gobe da yamma ka raka ni ayi enrolling dinta a islamiyya, she so need it yanxu, ita kuma Humainah is resuming school" El-ameen yace "Ohk" junaid na kallonsa yace "akwai shirye shiryen da xa ayi ne na bikin?" No kawai El-ameen yace masa. Washegari Tuesday junaid bai bari Humainah ta je school ba don bai son barin Jasmine ita kadai a gida sai sunyi registering dinta a islamiyya, haka Humainah tayi ta kumbure kumburenta ya wuce aiki abun sa, kwata kwata ranan bata sake ma Jasmine ba, sai taji ina ma Hadiza xata xo ranan ma amma har Junaid ya dawo bata xo, bai damu da girkin da bata yi ba don sai ya ci abinci yake dawowa, Karfe biyar saura ya shiga dakin Jasmine ya ganta kwance tayi jigum, tana ganinsa ta mike xaune yace "Sa hijab din ki ki fito" ba musu tai yanda yace ta fito parlor, sai ga Humainah ma ta sauko ta tsaya bakin stairs tana kallonsu ta wani hade rai, Ko kallonta junaid bai yi ba yana kallon Jasmine yace "Mu je" ta bi bayansa xa su fita Humainah ta rufe kofar tana masa wani kallo sai kuma ta fashe da kuka tace "Ni wllh xan hada ka da Abba na gaji haka kuma" Jasmine dai sai kallonta take, junaid ya fixgota yace "rashin kunyar ki ta da ne xai dawo koh?" Bai jira cewarta ba ya turata one side ya kama hannun Jasmine suka fita ta fashe da kuka sosai ta haura sama da sauri, Junaid ya kira El-ameen ya fi sau biyu kafin ya daga, bai damu da hakan ba ya gaya masa islamiyyan da xai taho ya samesu, ya fi minti talatin yana jiransa kafin ya xo, a tare suka shiga babban makarantar suka yi duk abinda ya dace junaid ya bada kudi, aji hudu aka sa ta bayan yayi bayanin ailment dinta, shi dai El-ameen kallonsu kawai yake, suna fitowa makarantar xa su shiga mota junaid ya hango Hafsat sanye da uniform din makarantar da hijab, tuni El-ameen ya shige mota Jasmine ma ta bude bayan motar ta shiga tana kallonsa, Hafsat bata lura da Junaid ba xata wuce yace "Hafsat!" Juyowa tayi da sauri tana kallonsa, murmushi yayi yace "kwana biyu" dawowa tayi ita ma tayi murmushin tace "Alhmdllh" yace "Nan kike knn" kai ta gyada masa, ganin duk tayi wani iri yana kallonta yace "Baki da lafiya amma koh?" Murmushi ta kirkira tace "Am getting married ne" ya d'an bude ido yace "Ohh really, when?" kamar baxa ta ce komai sai kuma tace "Friday" Junaid yace "Toh Allah ya sanya alkhairi, but shine bbu gayyata" bata ce komai ba, ganin kamar bata son maganan yasa yayi mata sallama tayi wucewarta ya shiga mota
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
56.....
Kallo daya junaid yayi masu ya tada motar ya ja suka bar wajen, yana jin Jasmine tace "Uncle why didn't you want to talk to me?" Ba tare da El-ameen ya kalleta ba yace "Am meditating!" Ta wara ido tace "Ohh What's that?" Da Hannu ya mata alamar da tayi shiru, tayi shiru tana kallonsa, ganin junaid gidansa ya nufa El-ameen yace "Hey drop me, gida xan tafi" junaid bai ce komai ba yayi parking ya bude motar ya fita ya daga ma Jasmine hannu ta hade rai tana kallonsa, murmushi yayi ya rufe motar junaid ya ja motar ya kama hanyar gida. Yana gama parking ta bude motar ta fice ta nufi parlor, daki ta shige ta sa key ta fashe da kuka. Washegari karfe bakwai da minti goma duk suka bar gidan, farin riga ne jikinsa sai wandon uniform don bai son ya ji Jasmine tace bata son kayan, ita dai Humainah ko kallonsa bata yi ba ta wani hade rai gaban mota, jasmine ya fara ajiyewa islamiyya, sannan ya tafi da Humainah makarantar da tace take so na su fatima, yana gama parking ya dau shirt din uniform dinsa ya sa sannan ya bude motar ya fita ta bi bayansa, nan take ya biya komai ya fice ya nufi office abun sa. Da yamma yana barin gun aiki Jasmine ya fara xuwa dauka don hudu suke tashi, da fara'arta ta karaso gun motar, kamar daxu da safe bbu uniform jikinsa sai wandon, ta wara masa ido tace "Captain nayi frnds guda uku, kuma suna koya min karatu I like them" kai kawai ya gyada mata ta bude motar xata shiga yace "Koma baya" ba musu ta rufe ta koma baya, ya ja motar ya kama hanyar gida, bai yi mamakin ganin Humainah ta dawo ba, Jasmine ta durkusa kusa da ita a parlor don xaune take tana cin abinci, ai ko ta wani hade rai, Jasmine tace "Anty nayi frnds uku" banxa da ita Humainah tayi, Junaid na kallon Jasmine yace "Tashi ki tafi sama" mikewa tayi, ta yi yanda yace mata. Shirye shiryen biki ake tayi gidansu El-ameen, har ya fi junaid shiga damuwa amma ko a jikin umminsa da Abba, ana saura kwana biyu daurin auren Junaid ya je gidan don har lokacin bai kirasa ba, kallon arxiki El-ameen bai masa ba, shi ko bai damu ba ya dinga danna waya abun sa, ana kiran magrib ya bar gidan. Ran saturday misalin karfe sha daya junaid na tsaye bedroom dinsa sanye da farar shadda yana kokarin saka wristwatch, Humainah ta shigo dakin, sanye take da riga da skirt Holland da ya mata kyau ba kadan ba, ta madubi yake kallonta har ta karaso cikin dakin tace "Ina son xuwa gida yau ya Ahmad" juyawa yayi ya kalleta ya dauke kai ya gama sa agogon sannan yace "Gun Daurin aure xan tafi yanxu, sai ki jira next time" tace "Amma nasan hanya na ga" yace "toh ko kin je wa xa ki samu a gidan bayan duk biki xa su" tace "Ehh nima sai in bisu ae" shareta yayi don bai son barin Jasmine kadai a gidan ne, tace "Ka ji?" Ya hade rai yace "ki jira ran lahadi in kai ki don't disturb me plss" kallonsa ta tsaya yi hawaye ya cika idonta, ya dau makullin motarsa ya fita ya bar ta nan tsaye, dakin Jasmine ya shiga ya ganta xaune kan darduma da Qur'ani gabanta, sosai take catch up, amma da ganin ta kasan ta san su a da ne shi yasa, ya durkusa gabanta yana kallonta a hankali yace "Mu'allima Jasmine!" Dago manyan idonta tayi ta kallesa sai kuma tayi murmushi ta rufe fuska, murya can kasa tace "Captain kayi kyau" yace "Uhnn koh?" Ta gyada masa kai yace "Uncle din ki xai yi aure yau, can xan je" ta xaro ido tace "Toh ni baxan je ba? kuma ni bai gaya min ba" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Langwabar da kai yayi yace "Maza kadai ke xuwa ai" shiru tayi bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace "gobe sai na kai ki gidan ki ga amaryar" kai ta masa nodding a hankali tace "Toh" ya dago chin dinta yace "Tea'n ya ishe ki?" Tace "Uhm na koshi" yace "Ohk," sannan ya mike ya daga mata hannu ya nufi kofa, bin sa da kallo tayi har ya isa kofa, a hankali tace "Kayi kyau" juyowa yayi da sauri sai kuma yayi murmushi yace "Ae kin gaya min" sunkuyar da kai tayi ya juya ya fita, har xai sauka sai kuma ya shiga dakin Humainah, xaune ya ganta ta hade kai da gwiwa, ya karasa kan gadon ya dagota ya ga kuka take, xaunawa yayi gefenta ya jawota jikinsa yace "Toh ba nace maki ran Sunday xan kai ki ba" ta fashe da wani sabon kukan, ya rungumeta yace "Toh yi hakuri, da yamma sai in kai ki by then su ma sun koma gida" shiru tayi bata ce komai ba, yace "kin ji" dago kai tayi tana kallonsa, ya buda mata ido ya ciro wayarsa ya shiga daukarsu hotuna, mikewa yayi daga karshe yace "sai na dawo" daga haka ya fita daga dakin, direct gun daurin auren ya tafi, El-ameen yi yayi kamar bai taba saninsa ba, shi kam ko a jikinsa don dariya ma yake basa, nan dai aka daura auren a kan sadaki dubu dari biyu, ko minti biyar Junaid bai kara ba ya bar wajen ya tafi gida abun sa. Misalin karfe biyar aka danna bell, Humainah dake kitchen tana girka supper ta fito da sauri tana kallon kofar, karasawa tayi tun kan junaid ya fito ta bude kofar ta ga hadiza tsaye, sosai gabanta ya fadi, hadiza tace "Gida ni kadai nace bari in yo nan!" Humainah ta kirkiri murmushi tace "Shigo mana" shigowa hadiza tayi Humainah tace "Mu je daki" ba musu Hadiza ta bi bayanta, Humainah dake ta addu'ar kar junaid ya fito ta bude dakinta da sauri ta shiga hadiza ta bi bayanta, hadiza tace "Ko dai mijin ki na nan ne" Humainah tayi murmushi tace "Yana nan" Hadiza tace "Atoh bari in tafi, amma shi bai xuwa gun aiki ne...." Humainah tayi dariya tace "No kiyi xaman ki ai ba shigowa xae yi ba, karfe hudu xuwa biyar yake dawowa daga aiki" Hadiza ta xauna gefe tace "Mijin naki ne naga bai fiye son mutane ba" Humainah ta yi yake tace "Bari in duba girki a kitchen" daga haka ta fita daga dakin. Dakin Junaid ta nufa ta tura a hankali ta gansa xaune yana kallo a laptop, xata rufe kofar yace "Who rang the bell?" Rasa abinda xata ce tayi, ta bude hannu alamar bata sani ba ta juya ta fita, kitchen ta koma don ci gaba da girkinta ta ga Jasmine tsaye tana juya miyan, wani kallo ta watsa mata tace "Wa ya sa ki?" Jasmine ta ajiye cokalin hannunta tace "Taya ki nake" Humainah tace "Fita!" Ba musu ta fita dai dai lkcn da aka danna kararrawan parlor, kallon kofar tayi ta karasa ta bude, su uku ne tsaye bakin kofar ta tsaya kallonsu, daya daga cikinsu yayi murmushi yace "Hi, Ahmad na nan?" Ta d'an bude ido tace "Waye shi?" Na gefensa yace "Junaid!" Ta kuma bude ido tace "Waye shi?" Kallonta suka tsaya yi gaba daya, ta girgixa kai tace "A'a mu bamu da Ahmad junaid a gidan nan, Captain kawai muke da" xaro ido suka yi gaba daya suka fara dariya, murmushi tayi ita ma tana kallonsu, daya yace "Toh ina captain din?" Tace "Bari in kira sa" Juyawa tayi ta gansa bakin stairs a tsaye ya hade rai yana kallonta, ta juya ta kalli kofar kitchen taga Humainah ma tsaye tana kallonta, karasowa captain yayi parlon yana kallon colleagues din nasa, Capt Umar yace "Ehh lallai kam captain kadai gare su a gidan, dubi wani kallo da yake ma mutane" murmushi junaid ya kirkira yace "Sannun ku da xuwa, ku karaso mana" Capt kb yace "the great Aj, bamu gan ka gun daurin auren aminin naka ba" junaid ya bude ido yace "ohh! Ae kam na je, kawai dai na bar gun da wuri ne" karasawa cikin parlon suka yi duk suka xauna, Tuni Humainah ta koma kitchen ta ci gaba da aikinta, Gaisawa junaid yayi da frnds din nasa, har lokacin Jasmine bata bar parlon ba duk da satan kallonta da yake yana hararanta, durkusawa tayi kusa da shi tace "Captain in kawo masu ruwa?" Kai kawai ya gyada mata ba tare da ya kalleta ba, Ta mike ta nufi kitchen, Capt Mk yace "Sistern ka ce amma wannan" kai junaid ya gyada ba tare da ya kallesa ba, Capt kb yace "Ahhh toh ni dai ina ciki, har ta fi ka kyau wllh, ina kama kafa ni dai yaya Ahmad" dariya sauran suka yi, Capt Mk ya hade rai yace "Ae don ta min ne shi yasa na tambayi ko kanwar sa ce...." Dariya Capt Umar yake yana kallonsu duka yace "Toh duk na riga ku wllh, tana bude kofar ta min, na dai yi shiru ne kawai" Sosai junaid ya daure fuska bai ce komai ba, Capt Mk yace "Toh pa, ya da hada rai Ahmad ko dai ba blood sis bace?" Wara ido junaid yyi yace "Kai haba blood one kuwa, irin ni babban yaya din nan shi yasa na daure fuska duk ku gama haukan ku....." dariya suka yi gaba daya, jasmine ta shigo parlon da goran ruwa guda uku a hannu duk ta mimmika masu, tace "Anty baxa ta bar ni in shiga kitchen in dauko cups ba" Kb yace "Gaskiya Anty bata kyauta ba, toh ya sunan ki?" Ta kalli junaid da ke kallon wani gun daban tayi dariya ta xauna tace "Ka ga Captain yana ce min Jasmine, Uncle na ce min jewel, mamina na ce min Baby" kb yace "Waow that's nyc, i will call you jewel also!" Ta kalli junaid xata yi magana ya mata wani mugun harara, mikewa tayi da sauri tace "In tafi Captain?" Yace "Ehh" juyawa tayi ta tafi sama, duk su ka bi ta da kallo, Mk yace "Uhmm! But ya aka yi ban santa ba Aj, fatima da khadija kawai na sani" Junaid yace "Ehh ba tare mu ke da ita ba" Humainah ce ta fito daga kitchen ta karaso cikin parlon ta tsaya daga bayan kujera ta gaida su, da fara'a suka amsa mata suna tsokanarta ta kara gaba abunta, dakinta ta shiga ta ga hadiza xaune har lokacin, ita har ta ma mance da ita, rufe kofar tayi tace "Kiyi hakuri girki nake ne" hadiza tace "Ba komai, nima nasan aunt dina kila ta dawo yanxu, tafiya xan yi" Humainah tace "Ki jira ki ci abinci mana, baki yayi a parlon yanxu xa su tafi" xaunawa Humainah tayi Hadiza ta fara mata hira ita dai sai uhn uhn take don bata son junaid ya ji muryarsu, shidda saura junaid ya raka frnds din nasa har bakin mota yayi masu godiya yace "Kun dai ki cin abinci" Mk yace "Kai kuma ka ki barin mu yi sallama da jewel, ni dai ina nan dawowa gobe" KB yace "kai ka ma kai shi har gobe, bayan isha ni ina nan xuwa" dariya suka yi gaba daya banda Junaid da yace "Ai duk kuna da 'yan mata na ga" sun kusa minti sha biyar tsaye daga bisanni suka wuce ya koma ciki, Tuni Humainah ta sauka kasa ta debo ma Hadiza abinci jin fitarsu, yana haurowa sama dakin Jasmine ya bude, ya ganta tsaye bakin window tana kallon waje, hade rai yayi yace "From henceforth aka sake ring din bell kika sauka kika bude kofa I will slappp you, wani ya saki ne?" Kallonsa ta tsaya yi, hadiza dake jin duk abinda yace ta kalli Humainah murya can kasa tace "Toh fah" Jasmine kam bata ce komai ba sai kallonsa take kamar bata gane me yace ba din nan, ya karaso cikin dakin a fusace yana mata mugun kallo yace "Kin ji abinda nace?" Girgixa masa kai tayi da sauri, ya dawo kusa da ita strictly yace "Nace daga yau kar ki kuma fitowa parlor idan aka ring din bell, kuma na sake ganin kin tsaya magana da maxa har kina gaya masu sunan ki sai na maki mari!" Sunkuyar da kai tayi cikin tsawa yace "Kin ji?" Ta gyada masa kai hawaye cike idonta, juyawa yyi ya fice daga dakin. Hadiza tace "Toh fah, don Allah ki gaya min yanda kuke da yarinyar nan" Humainah ta tabe baki kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Yar uwarsa ce" hadiza tace "Tabdi toh Meye kuma na hanata magana da maxa, aurenta shi xai yi ko me?" Hade rai Humainah tayi bata ce komai ba, Hadiza tace "Toh ae ba xancen hade rai bane, wllh ki sa ido kar abinda ya samu yayata ya same ki, abu na biyu kuma na ga bbu wani interaction mai karfi tsakanin ki da mijin ki, anya kuwa?" Shiru Humainah tayi bata ce komai ba, Hadiza tace "Tabdi, to auren dole aka maku ne, yo ko da auren dolen ne ma ke ba mace bace baki san yanda xa ki ja mijin ki jiki ba, ai kam xa ki tsaya kallon ruwa...." Ita dai Humainah har lokacin bata ce komai ba, Hadiza tace "Ya ina magana xa ki share ni, ni tun randa na ganki naji Allah ya dora min san ki banda haka wannan ai ba hurumin da xan shiga bane, batun gaskiya Humainah da sake a xaman auren ki, ga mijin ki hadadde me kyau da shi xa ki tsaya wasa wata ta kwace maki, lallai ma" mikewa tayi tace "Kin ga tafiyata abincin ma ya ishe ni" Humainah da duk jikinta ya mutu tace "A'a don Allah ki kara..." Hadiza tace "Tafiya xan yi" daga haka ta nufi kofa fuu irin tayi fushi din nan ita, Humainah ta bi ta da sauri don ita tsoronta kar junaid ma ya ganta, tuni hadiza ta fice daga gidan gaba daya, Humainah ta sauke ajiyar xuciya tana naxarin maganganun ta, xama tayi bakin gado tayi tagumi hawaye ya cika idonta, to ita ta ma san yanda xata yi da junaid, da kyar ta iya mikewa ta shiga bayi ta dauro alwala don yin magrib, ta jima xaune kan darduma daga bisanni ta mike ta fita daga dakin ta sauka kasa, kitchen ta tafi ta hada masa abincinsa a tray, ta gama xata fita Jasmine ta shigo kitchen din ta tsaya daga bakin kofa tace "Anty abinci na" ba tare da Humainah ta kalleta ba tace "Ban yi da ke ba, ki shiga ki dafa" Jasmine tace "Na'am" juyawa Humainah tayi ta fice daga kitchen din ta bar ta nan tsaye. Junaid na waya Humainah ta shigo dakin, ta ajiye abinci har lokacin bata mike daga durkushen da tayi ba, yana gama wayar ya juya yana kallonta ya d'an bude ido yace "Uhun! Yau kuma" hade rai tayi, yayi murmushi yace "Toh na gode, kin ba Jasmine na ta?" Kallonsa kawai take, can ta tabe baki tace "Kace da magrib xaka kai ni gida" yace "Ohh shi sa aka kawo min abinci, to ni gidansu El-ameen xan tafi yanxu" kuka ta fashe da tana kallonsa, ya sauko kasa ya dawo kusa da ita shi ma ya durkusa ya fara kwaikwayonta, duka ta shiga kai masa tana cewa "Ni ka kyaleni bana so" dariya yayi yace "Sai in dawo captain din yanxu, ni kike duka" dagota yayi suka koma kan gado yace "Gobe lahadi kin ga sai in kai ki tun asuba sai sha biyun dare xan je daukan ki" ta tsaida kukan tace "Kace Allah" yace "Sai na ce?" Shiru tayi tana kallonsa, ya ja hancinta yace "Allah" murmushi tayi ta fada kansa tace "Toh na gode" can kuma ta mike ya bi ta da kallo har ta fita, abincin ya bude ya ga tuwon shinkafa ne da miyar vegetable..... " ya dau plate da spoon ya dibi kadan ya ci snn ya rufe ya mike, wanka ya shiga ya fito ya shirya don xuwa gidansu El-ameen duk ya kagu yaga matar aminin nasa, dakin Jasmine ya shiga ya ganta xaune kasa ta daura kanta kan gado, yace "Kin ci abinci?" Ta girgixa masa kai, yace "Bata baki bane?" Ta sake girgixa masa kai, shiru yayi sannan yace "Je daki na ki dauki nawa" tace "Toh" sannan ta mike ta fita ta shiga dakinsa bude abincin tayi da miya sai kuma ta dawo tace "Dukka xan dauka?" Yace "Ehh" komawa tayi sai ga ta ta dawo da tray din, murmushi yayi ya juya ya fita daga dakin.
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
57.....
Junaid na fita gidan ya kira wayar Faisal, yana dagawa yace "Ya? ku na ina yanxu?" Faisal yace "Kai kam sam baka da kirki captain" junaid yace "That's constant ai...." Faisal yace "Toh yayi kyau muna shirin kai ango..." Dariya junaid yayi yace "Ohk toh gani nan xuwa kar rashin kirkin yayi yawa koh?" daga haka ya katse wayar ya dau hanyar gidansu El-ameen, El-ameen na cin abinci a dakinsa Junaid ya shigo, junaid yace "Tab har daman cin abinci ka samu kenan, ni tym din nawa ina na samu wannan daman....." Ko kallonsa El-ameen bai yi ba ya hade rai, dariya sosai Junaid yayi yace "Harara a duhu kawai kake yi" Dr faruq yace "Ni na ma yi xaton tafiya kayi Ahmad, bikin aminin naka guda ace baka kusa" Junaid ya shafa kansa yace "Daxun nan na dawo bana nan" faisal yace "ga alama mun gani" murmushi junaid yayi bai kuma cewa komai ba, ya mike ya bude closet din El-ameen ya fiddo wani dakakken shadda sky blue ya ajiye masa ya koma gun huluna ya fiddo wanda xai shiga da kayan ya ajiye masa, ya dauki agogo me tsada cikin agogunansa ya daura kan kayan yana murmushi yace "Ka tashi ka shirya time na wucewa" wani kallo El-ameen yayi masa ya ci gaba da cin abincinsa, can ya ajiye abincin ya mike yana kallonsu faisal yace "Ku tashi mu je" daga haka ya nufi kofa Junaid ya fixgosa yace "Ka ma isa, da wannan kayan da kke yawo tun safe xa mu kai ka" dariya faruqh yayi yace "Gaskiya ne wnn kuma, go nd change frnd" duk yanda suka yi da El-ameen kin canxa kayan yayi, sai da wani abokinsa Dr Lawal ya sa baki, sosai kayan suka yi masa kyau don bai taba sa su ba ma, junaid sai dariya yake har su faruqh suka dinga mamaki wai ashe dai yana interacting haka da mutane shidai baice musu komai ba, Karfe takwas da rabi suka bar gidan bayan El-ameen ya sallami parent dinsa, karfe tara da kusan rabi suka isa gidan nasa, junaid ya kashe mota don shi ke driving din ya juya yana kallon El-ameen murmushi dauke fuskarsa yace "Toh gashi mun kawo ka frnd, mu iyakar mu kenan, Allah ya bada xaman lafiya.." Kallonsa kawai El-ameen ke yi, faisal yayi dariya yace "Ya ka yi shiru ango" faruqh yace "Manta da su, har ciki xa mu raka ka Dr" daga haka ya bude motar ya fita Lawal ma ya fita yana dariya yace "Fadi kawai suke, but har ciki za mu raka ka, ai dole mu bada amanarka" bude motar El-ameen ma yayi ya fita ya nufi gate din, Junaid ya dinga dariya har ya shiga da su faruqh, ya juya ya kalli faisal yace "Ba don halinsa ba mu shiga faisal" faisal yace "A'a ku shiga ku fito ina nan" daga haka Junaid ya bude motar ya fita ya shiga gidan shi ma, duk xama suka yi a parlor har El-ameen aka rasa wanda xai haura sama, junaid yace "Wai tsoro ku ke ko me, to ni bari in je in sauko da ita" daga haka ya nufi sama, El-ameen ya mike ya bi bayansa, bakin kofar dakin ya ga junaid tsaye kam, abun ya ba sa dariya yana isa bakin kofar ya tura sa cikin dakin, tana xaune gefen gado fuskarta a rufe, da sauri junaid ya juya ya fito yana kallon El-ameen yace "Meye haka kuma" El-ameen ya janyesa daga bakin kofar ya shiga dakin, bin sa junaid yayi yana shafa kai, har gabanta ya isa ya tsaya, ita dai bata dago ba har lkcn kanta a rufe, fixge mayafin El-ameen yayi, junaid ya fixgosa dan kada yayi b'aramb'arama, ita ko ta rufe fuskarta da kafarta da sauri, El-ameen yace "A ina kika san ni da har kika ce kina son aurena?" Mikewa tayi tsaye tace "I shud be asking you your silly ques.....!" shiru tayi tana kallonsa, can ta juya ta kalli junaid da ya xaro ido yana kallonta, shi kansa El-ameen din kallon mamaki yake mata, ta sulale kasa ta fashe da kuka tana kallonsu, Juyawa El-ameen yayi kamar xai tashi sama ya fice daga dakin, Junaid ya bi sa da kallo, can ya kalleta yace "Hafsat!" Ta daga kai tana kallonsa, rasa abinda xai ce mata yayi, can ya dau stool din dake gaban mirror ya xauna yana kallonta yace "Did you know him?" Girgixa kanta tayi hawaye na sakko mata, yace "Then how's this, I mean did it all happen?!" Share hawayenta ta shiga yi a hankali tace "Ni ban san sa ba, Abbansa ne abokin dad dina I think, kawai ni dai Abbana yace min he's getting me married, that's all I know...." Junaid yayi shiru kafin yace "But kinsan yan gidansu?" Gyada masa kai tayi tace "Eh nasan Ummi da Sumayya" yace "Shine dai baki sani ba kenan?" Kai ta gyada masa nan ma, junaid yayi murmushi yace "Ki kwantar da hankalin ki, Ahmad is my frnd, a childhood frnd, he will be of a good husband idan kin masa biyayya, just ki cire a ran ki cewar ba a son ranki aka yi auren nan ba, ki bi mijin ki, you will like him, infact love him ma dai" ita dai bata dago ba bata kuma ce komai ba, ya dade xaune yana bata magana masu kwantar da hankali, daga bisanni yace "Kin ji Hafsat?" Hawaye na bin kuncinta ta gyada masa kai alamar toh, yayi murmushi ya mike yace "Toh Allah bada xaman lafiya" daga haka ya fita, El-ameen kadai ya gani xaune parlor, El-ameen na ganinsa ya mike ya nufesa yace "Da kai aka hada baki aka min auren nan koh Ahmad" Junaid yace "Toh ya xa kayi da ni" daga haka ya nufi kofa El-ameen ya bi sa da kallo har ya fita. Ko da junaid ya koma gida dakin Jasmine ya fara shiga yaga har tayi bacci, rage Acn dakin yayi ya sa mata blanket ya dawo dai dai kanta ya durkusa yana kallon fuskarta murya can kasa yace "Good nyt dear" ya fad'a tare da lumshe idonshi yana bud'esu a hankali, mikewa yayi ya kashe wutan dakin ya fita, dakinsa ya shiga yayi wanka ya canxa xuwa pyjamas dinsa, ya jima xaune gefen gado daga karshe ya fita ya shiga dakin Humainah. Washegari da safe yana xaune parlor yana kallon wani movie Humainah kuma na kitchen tana hada breakfast Jasmine ta shigo parlon sanye da kayan islamiyya, kallonta kawai yake har ta karaso kusa da shi ta durkusa tace "ina kwana" kallon kofar kitchen yayi sannan ya kalleta yace "Sai yanxu kika tashi?" Girgixa masa Kai tayi tace "Wanka nayi" ido ya tsura mata ta mike xata tafi, a hankali yace "Jasmine" dawowa tayi ta durkusa tace "Na'am" yace "How was ur nyt?" Tace "Alhmdllh" yace "baxa ki islamiyya ba yau!" Ta kallesa da sauri tace "fashi?" Shiru yayi kafin yace "Yes for only today xa mu fita ne" tace "Toh" sannan ta mike ta nufi sama ya bi ta da ido. Karfe goma da wani abu Humainah ta gama shirinta ta shiga dakin junaid, ta hade rai ganin bacci ma yake, ta karasa gun gadon tace "Ya Ajay" a hankali ya bude ido yana kallonta ta hade rai sosai tace "Na fa gama" jawota yayi ta fada kansa yace "So early, nifa bacci nakeji?" ya fad'i yana lumshe ido, Ta turo baki tace "Dubi agogo fa" ya kalli agogon yace "Toh ai jiya da daddare ni ban yi bacci ba" kwace kanta tayi tace "Ni na hanaka" rikota yayi yace "Eh mana" murmushi kawai tayi tace "Ni dai ka tashi ka shirya ya Ajay" yace "Toh naji hada min ruwan wanka" mikewa tayi ta shiga bathroom din, ba a dau lokaci ba ta fito tace "Na hada" yace "Toh mu je ki min" ficewa tayi daga dakin da sauri, yayi dariya yace "Ashe bbu inda xan kai ki kuwa" sha biyu saura Junaid ya fito bayan ya shirya cikin kananun kaya, ya shiga dakinta ya ganta xaune gaban mirror yace "Toh mu je" ta mike cike da jin dadi ta dau hijab dinta da hand bag suka fita, sai da ya ga ta sauka downstairs sannan ya shiga dakin Jasmine ya sameta tana bacci, tada ta yayi ta mike xaune tana kallonsa yace "Kafin in dawo ki shirya kin ji" kai ta gyada masa ya juya ya fita, ana kiran azahar ya isa gida Humainah ta fice da sauri daga motar bayan yayi parking ta nufi cikin gidan, tabe baki yayi ya bude motar ya fito yayi part din Mumy shi ma, ko minti goma cikakke bai yi gidan ba don duk hankalinsa na kan Jasmine dake gida ita kadai, Mumy na lura da shi ita dai bata ce komai ba har ya bar gidan, Humainah duk ta ji kamar ta bi sa tunawa da tayi gida xai koma. Yana isa sai da yayi sllh sannan ya shiga gidan, ya kusa minti biyar a parlor kafin ya haura sama har xai shiga dakinsa sai kuma ya bude dakinta, durkushe ya ganta a dakin daure da towel alamar fitowarta daga wanka kenan, tana ganinsa tace "Captain Kaga towel din ya rike earring din, yaki ya cire" kin karasawa yayi dakin har sai da ta kuma kiransa, ya karaso ya durkusa shima ya shiga kokarin cire mata dan kunnen daga jikin tawul din, haka kawai hannunsa ke rawa ta daga ido tana kallonsa tace "Captain" bai ce komai ba ya kuma kasa cirewa, rike hannunsa tayi tace "Are you sick" bai kalleta ba bai kuma ce komai ba, hakan yasa ta cire dan kunnen gaba daya daga kunnenta, sai a snn ya daga ido yana kallonta, tace "Na cire" mikewa yayi ya fice daga dakin. Tana gama shiryawa ta sauko parlor ta gansa kwance idonsa lumshe, daga bayan kujeran ta tsaya tace "Captain na gama" bude ido yayi yana kallonta ya mike xaune, makullin motarsa ya dauka yace "Toh mu je" gaba ta shiga ya bi bayanta har suka fita parlon ya rufe. Front seat ya bude mata ta shiga sannan ya xaga ya bude maxaunin driver ya shiga ya tada motar, sai da suka dau hanya sannan tace "Captain ina xa mu?" Bai tanka ta ba hakan yasa tayi shiru bata kuma cewa komai ba, tafiyar kusan minti ashirin suka yi yayi horn bakin gate aka bude gate din ya shiga yayi parking, kallonta yayi ta sunkuyar da kai, ya bude motar ya fita yace "Come down" bude motar tayi ita ma ta fito ya shiga gaba ta bi bayansa, ring din bell yayi ba a dau lokaci ba aka bude, murmushi tayi ta basu hanya tace "Sannun ku da xuwa...." Junaid ya shiga parlon yace "Yauwa amarya, yana ciki kuwa" shiru Hafsat tayi bata ce komai ba, Jasmine ta hangosa tsaye bakin stairs ta wara ido tace "Uncle!" Da gudu ta karasa cikin parlon daga Junaid har Hafsat suka bi ta da kallo, tana isa gun stairs din ta rungume sa, murmushi El-ameen yayi ya janyeta jikinsa, Hafsat ta kalli junaid da ya dauke kai, ita ma ta sunkuyar da kai, kama hannunts El-ameen yayi suka dawo parlon tace "Uncle ban san nan captain xai kawo ni ba" junaid ya fiddo waya kamar xai yi kira ya juya ya fice daga parlon, Jasmine tace "kuma Uncle yace min kayi aure da gaske ne?" Wara ido yayi yace "uhn! He's lying" ta langwabar da kai tace "Ohh captain! Why him" Juyawa tayi ta kalli Hafsat dake tsaye har lkcn bakin kofa ta matsa kusa da shi a hankali tace "Who's she?" Satan kallon Hafsat yayi yace "My sister" mikewa tayi tace "Ohk let me greet her" kafin yace komai har ta isa gun Hafsat tace "Anty ina yini?" Hafsat ta d'an yi murmushi tace "Lafiya lau, sannu da xuwa" Jasmine na murmushi tace "Ke sistern uncle ce koh?" Kai Hafsat ta gyada mata, El-ameen ya mike yace "Xo ki xauna in kawo maki drink ko baki so" dawowa parlon tayi tace "Ina so uncle" fridge ya nufa Hafsat kuma ta nufi kitchen, hollandia drink ya dauko mata da goran ruwa daya sai glass cup ya dawo kusa da ita ya xauna ya bude drink din ya xuba mata ya sha kadan ya bata ta wara ido ta karba tace "Thank you uncle" Hafsat ta fito daga kitchen rike da food warmers da plate a tray ta shigo parlon ta durkusa nan kusa da su tace "Ga abinci!" Jasmine ta kalli El-ameen, bude abincin Hafsat tayi ta dibar mata ta sa spoon ta mika mata, karba Jasmine tayi tace "Na gode Anty" murmushi Hafsat tayi mata ta mike ta bar wajen, Jasmine ta sauko kasa tana kallon El-ameen tace "I like her!" Murmushi yayi ya shafa kai bai ce komai ba, spoon din ta dauka ta fara cin abincin tace "Uhnn akwai dadi" El-ameen ya karbi spoon din ya debi abincin shi ma ya ci, mikewa Jasmine tayi da sauri ya kalleta yace "What?" Ta xaro ido tace "Ina captain toh?" Kofa ta nufa da sauri El-ameen ya bi ta da kallo, tana fita ta gansa xaune waje, tace "Baka shigo ba captain" mikewa yayi yana mata wani kallo yace "ina takalmin ki?" Kallon parlor tayi yace "Tafi ki dauko...." Ta marairaice tace "Are we going?" Wani mugun kallo yake mata xai yi magana El-ameen ya fito, kamar xata yi kuka tace "Uncle wai tafiya xa mu yi" El-ameen yace "A'a mu je ki ci abincin ki" juyawa tayi ta koma parlon, El-ameen ya d'aga ma junaid hannu yana murmushi yace "In xaka shigo ka shigo malam" daga haka ya koma parlon, xaunawa Junaid yayi ya dafe kansa, can ya mike ya sauka daga balcony din ya nufi motarsa ya shiga ya danna horn mai gadi ya bude masa gate ya fice daga gidan, Jasmine tace "Uncle ya tafi" El-ameen yace "Ci abincin ki" a hankali tace "Toh" ta ci gaba da cin abincin ta, yana nan xaune har ta gama ta mike tace "Na gama uncle ka tafi da ni gida" shiru yayi yana kallonta, ta koma ta xauna ta marairaice tace "Ka ji?" Yace "Nan ba gida bane?" Bin parlon tayi da kallo a hankali tace "Gidan Captain xaka kai ni" hade rai yayi yace "ina aiki a sama sai na gama" daga haka ya haura sama ya bar ta wajen, mikewa tayi ta bi sa da kallo kamar xata yi kuka, ko minti biyar ba ayi da tafiyarsa sama ba, Hafsat ta sauko tace "Har kin gama" gyada mata kai tayi, Hafsat tace "Toh taho mu je sama" ba musu Jasmine ta nufi stairs suka haura sama a tare Hafsat ta shiga da ita dakinta ta nuna mata gado ta xauna, sannan ta kunna mata kallo. Har bayan la'asar Jasmine na dakin tayi rub da ciki kan gado tana kallo, Hafsat kuma na ta danne danne a laptop aka bude kofar dakin duk suka juya kallonsa, karasowa cikin dakin yayi yana kallon Jasmine yace "Kin yi sllh" gyada mata kai yayi, ya d'an saci kallon Hafsat suka hada ido ya dauke kai da sauri, Jasmine tace "Anty ce kawai ya rage tayi sallah"
*Haske writers association*
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
58__59
Kallon Hafsat da ta dauke kai El-ameen yayi, sannan ya juya ya fita daga dakin, Hafsat tace "Is there any need of you telling him I've not prayed?" Jasmine ta wara ido tace "Ohk sorry" murmushi Hafsat tayi ta ci gaba da danna laptop dinta, dab da magrib aka danna bell Jasmine ta mike Hafsat tace "Ina xa ki?" Jasmine tace "To open the door" Hafsat tace "No! Ur uncle will do that" komawa tayi ta xauna har aka kira sallah Hafsat tace taje tayi alwala. Karfe bakwai da rabi El-ameen ya shigo dakin ya ajiye basket din abincin hannunsa ya fita, Hafsat ta mike ta dauko abincin ta bude ta dibar ma Jasmine ta bata, har kusan karfe goma suna zaune dakin Jasmine tace "Baxa mu je muyi ma uncle hira ba?" Hafsat tace "Je ki samesa a parlor" mikewa tayi xata fita Hafsat tace "Tafi da plates din ki kai kitchen daga nan" dawowa tayi ta dauka sannan ta fita, yana xaune parlor yana kallon news ya bi ta da kallo har ts shiga kitchen din ta fito ta karaso cikin parlon ta xauna kasa kusa da shi tace "Uncle ka ci abinci?" Girgixa mata kai yayi tace "Why?" Yace "Ba a bani ba ai" mikewa tayi yace "Ina xa ki?" Tace "Ina xuwa" dakin Hafsat ta koma ta langwabar da kai tace "Anty Uncle yace yunwa yake ji ki kawo masa abinci" daga haka ta juya ta fita daga dakin, El-ameen yace "Me kika je yi?" Tace "Nace Anty ta kawo maka abinci?" Ya hade rai yace "Did I send you?" Girgixa masa kai tayi, sai ga Hafsat ta fito, kitchen ta shiga ta dau plate da spoon ta fito ta koma daki, El-ameen ya tabe baki ya ci gaba da kallonsa, ba a dau lkci ba Hafsat ta fito rike da plate din abinci ta shiga kitchen ta daura kan tray ta sa ruwa da cup ta fito parlon ta durkusa ta ajiye kusa da shi sannan ta mike ta bar wajen, sai da ya ji ta shi ga daki snn ya dau abincin ya fara ci, Jasmine tace "Har yanxu captain baxai xo ba?" El-ameen ya ajiye plate din hannunsa yace "I will knock fa idan kina damuna da captain ni nace kar ya xo?" Shiru tayi tana kallonsa, a hankali tace "Sorry!" Daukar abincin sa yayi ya ci gaba da ci. Yana gamawa yace "Tashi ki tafi dakinta ki kwanta, am also going to bed" mikewa tayi ta fara tafiya, yace "Baby!" Kin juyowa tayi har sai da ya kuma kiranta, ta juya a hankali ya ga hawaye idonta, buda ido yayi yace "Crying?" Ta girgixa masa kai, ya kwantar da murya yace "toh gaya min kukan da kike?" Shiru tayi yace "Am waiting fah!" A hankali tace "Captain ya...." Mikewa yayi yace "Get away!" Ta juya da sauri ta tafi dakin Hafsat, kuka ta fashe da Hafsat na kallonta tace "what happened?" Tana share hawayenta tace "He shouted at me" Hafsat tace "Ohk sorry, tafi kiyi wanka ga kaya na fito maki da" bathroom ta nufa a sanyaye Hafsat ta bi ta da kallo. Tana fitowa ta saka rigar da Hafsat ta fito mata da tayi kwanciyarta. Da asuba El-ameen yayi masu knocking kofa, Hafsat ta kalli agogo don dama tuni ta tashi, biyar da minti arba'in ne, jin ya kuma knocking ta mike ta nufi kofar ta bude, kallo daya yayi mata ya juya ya bar wajen ta koma ciki ta tada Jasmine tace "Tashi kiyi sllh." Throughout ranan Jasmine a dakin Hafsat ta yini, Hafsat nata bata labarai, duk El-ameen na jinsu. A kwana biyun da Jasmine tayi gidan ba karamin sabo tayi da Hafsat ba, komai tare suke sai kayi tunanin sun dade da sanin juna, sosai Hafsat ke sonta ga tausayinta da take, duk abubuwan da tasan ya kamata gwada mata take, hakan yasa El-ameen ya d'an fara sake mata ganin yanda take kula da ita, ita kam ko a jikinta don sau dayawa idan yayi mata magana bata ma sanin da ita yake. Ran thursday da yamma suna kitchen su biyu suna girki shi kuma yana parlor aka danna bell, mikewa yayi ya isa gun kofar ya bude, Junaid ya gani tsaye, El-ameen ya shafa kai yana murmushi yace "Sai yau" Junaid bai ce komai ba ya shigo parlon, sai dai bai xauna ba yace "Tana ina?" El-ameen yace "Wa?" Junaid yace "Warce na kawo!" El-ameen xai yi magana sai ga ta ta fito daga kitchen, ta wara ido ganin junaid tace "Captain!" Karasowa tayi inda suke ta nufesa da fara'arta sai kuma ta ja ta tsaya ta fara dariya tana rufe baki tace "I missed you!" Ba yabo ba fallasa yace "Tafi ki dauko Hijab din ki" kallon El-ameen tayi sai kuma ta marairaice tace "Noo! I want to stay here Captain plss" ya wani hade rai yace "I will slap you ke da staying din" ta kalli El-ameen kamar xata yi kuka, El-ameen yace "Ae nan da can duk daya ne naga" Junaid yace "No ba daya bane" El-ameen yace "Why?" Yace "Coz a can tana xuwa makaranta...." Bai rufe baki ba tace "Toh ka kawo min kayan makarantar sai in dinga xuwa a nan ma" wani mugun kallo junaid ke mata kafin yace komai ta fashe da kuka sosai tace "This Aunt is kind, but the other one is otherwise I want to stay here plss captain!" Me El-ameen xai yi ban da dariya, cikin kuka tace "Uncle its not funny, I don't like her, I prefer staying here plss" sakin baki junaid yayi yana kallonta, El-ameen na dariya yace "Gud nd fyn tafi gun kind aunt din ki" juyawa tayi da sauri ta nufi kitchen, El-ameen ya kalli Junaid ya d'aga kafada yace "Ka kawo mata kayan makarantar ta" wani kallo Junaid yyi masa ya juya ya fice daga parlon. Washegari da safe Jasmine na kitchen da Hafsat suna girka breakfast aka danna bell, Jasmine xata fita Hafsat tace "Ina za ki?" Tace "In bude kofa" Hafsat tace "Ci gaba da aikin ki" El-ameen ne ya bude kofar, wanda ke tsaye gun ya rusuna ya gaishesa sannan yace "Captain ne ya aiko ni in dauko bakuwar da ke gidan nan, driver ne ni" El-ameen ya shafa kai yace "Kaje kace masa nace bata tashi ba" da ladabi drivern yace "Toh sir" daga haka ya juya ya bar bakin kofar, El-ameen ya rufe kofar, Jasmine dake tsaye kofar kitchen ta fito da sauri tace "Who's he uncle?" Kallonta yake daga sama xuwa kasa, sleeping gown red colour ne jikinta da ya haska farar fatar ta, ta bude ido tace "Uncle" kifta ido yayi ya karaso kusa da ita a hankali yace "Me kika ce" ta ce "Waye shi?" Murmushi yayi ya kamo hannunta ya kai bakinsa kusa da kunnenta, ta xaro ido xata koma baya taji ta jikinsa, runtse ido tayi tace "Uncle!" Ido hudu yayi da Hafsat dake kallonsu, ta juya da sauri ta koma kitchen, sake ta El-ameen yayi ya koma baya, ta turo baki tana kallonsa tace "What's that?" shafa kansa yayi ya juya ya koma daki. ta juya ta shiga kitchen tana kallon Hafsat dake soyen dankali tace "Anty!" Hafsat ta kalleta tace "Ya aka yi" shiru tayi bata ce komai ba, Hafsat ta nuna mata ruwan lipton dake tafasa kan gas ckr tace "Ki juye a flask" kai ta gyada mata ta dau flask da cup ta nufi gun gas din, tara saura suka gama, ta dibar ma El-ameen nasa ta daura a tray tana kallon Jasmine tace "Kai masa!" Shiru Jasmine tayi sai kuma ta dauka ta fita, sau biyu tana sallama ya amsa ta tura kofar ta shiga ta karasa kusa da shi ta ajiye trayn, kallonta kawai yake ta mike tace "Ga breakfast mun yi" sauke idonsa yayi yace "toh xauna mu ci" ta wara ido tace "Ni da Anty xa mu ci" ya hade rai yace "Xauna na ce" murmushi tayi ta xauna ya mike ya dauko darduma ya shimfida ya daura tray din kai ya xauna yace "Toh dawo nan" dawowo kan darduman tayi ya hada tea a cup ya bude warmer din potatoe da kwai da plantain ya dau plate ya diba yana kallonta yace "Start!" Langwabar da kai tayi tace "Toh Anty fah?" Yace "Xata ci nata ai" daukar fork din tayi ta fara cin potatoe din sannan ta mika masa, idonsa na kanta ya karba shi ma ya ci ya kuma mika mata, girgixa kai tayi tace "I will use my hand" ya lumshe ido yace "Okay" kasa cin dankalin tayi ganin yanda yake kallonta, ya buda ido a hankali yace "Eat mana" sunkuyar da kai tayi sai kuma ta mike tace "Am coming" yace "Sit!" Kamar xata yi kuka tace "Uncle am coming" yace "Ina xa ki?" Ta sauke idonta kasa tace "ina son xan dauko hijab dina am feeling cold" murmushi yayi yace "Uhun?" Ta turo baki tace "Yes" yace "Toh tafi, kar ki dawo kuma" shiru tayi tana kallonsa, yace "Tafi" mikewa tayi xata fita yace "Xo ki dauki abincin ki" ta juya tana kallonsa can tace "Why?" Yace "Am ohk" ta bata fuska tace "Toh ai baka ci ba" ya tsuke fuska yace "Na koshi" turo baki tayi tace "Baka koshi ba joor" xaro mata ido yayi yace "Xo ki dauka na ce" karasowa tayi a sanyaye ta durkusa xata dauka tray din ya fixgota ya xaunar gefensa yana kallonta yace "What are you wearing hijab for?" Kamar xata yi kuka tace "You are looking at my body" xaro ido yayi ya fara dariya yace "How?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "What's there idan na kalle ki?" Gyara xama tayi tana kallonsa tace "But you are not my muharram!" Da mamaki ya dinga kallonta, tal langwabar da Kai ita ma tana kallonsa, sauke idonsa yayi daga kallonta yace "Who told you that?" Shiru tayi sai kuma tace "Mu'allim!" Tabe baki yayi yace "Shi kuma captain muharramin ki ne kenan?" Tace "Yes, coz he's my family, my elder brother" kallonta kawai yake can yace "Who told you that?" Tace "I know!" Yace "Then who am I to you?" Ta kallesa tace "you are captain's frnd, nd... You are our family frnd" wani kallo yake mata kafin yace "Toh tashi ki tafi" ta mike ta nufi kofa ya bi ta da ido, tsaki yayi ya mike ya shiga bathroom. Dakin Hafsat ta shiga ta ganta xaune gaban mirror tayi tagumi ta karaso ta xauna tace "Aunty what's wrong with you?" Kallonta Hafsat tayi tace "Nothing, ur breakfast is downstairs" Jasmine ta bata fuska tace "No kalli idon ki, are you crying?" Girgixa mata kai Hafsat tayi tace "Ba komai" a sanyaye Jasmine ta mike ta fita daga dakin ta koma dakin El-ameen, yana bathroom ta nemi waje ta xauna har ya fito bayan kusan minti ashirin daure da tawul, mikewa tayi ta karasa kusa da shi a hankali tace "Uncle may be Aunty is sick, she's crying" hade rai yayi yace "you are not my muharrama, how dare you come into my room just like that without permission?" Ta buda ido tace "Ohh, I....." Yace "Leave now" juyawa tayi a sanyaye ta fita daga dakin, nan corridor ta sulale ta fara kuka, ya gama shirinsa ya fito, kallo daya ya mata ya shiga dakin Hafsat ta mike ta bi bayansa, kwance ya ganta kan gado kamar me bacci, Ya tsaya daga bakin gadon yana kallonta, Jasmine ta karasa ta xauna gefenta tace "Anty na kira maki uncle xai duba ki, he's a doctor...." Bude ido Hafsat tayi ta mike xaune ganinsa, ba yabo ba fallasa yace "What's wrong with you?" Shiru Hafsat tayi, Jasmine ta matso kusa da ita tace "He said what's wrong with you" Hafsat tace "Nothing" Jasmine ta hade rai tace "And you were crying mana" El-ameen ya tabe baki ya cire bargon da ta rufe da shi tana ganin haka ta fara kokarin komawa baya ya riketa ya daura hannunsa a forehead dinta, saketa yayi ya juya ya fita, Jasmine ta bi bayansa da sauri suka shiga har dakinsa, gaban mirror ya nufa ita ma haka ta tsaya daga bayansa tace "Uncle me ye ke damunta?" Banxa yayi mata ta kuma tambayar ya juyo ya fixgota yace "Am not ur muharram ko kin manta ne!" Shiru tayi ta bata fuska, kawai gani tayi ya rungumeta ta xaro ido tace "Uncle!" Bakinsa ya kai kunnenta yace "And Captain isn't ur muharram also...." Jikinta ya dau rawa ya saketa ya fice daga dakin. Fitowa ita ma tayi ta shige wani daki ta fara kuka, har rana bata fito ba, karfe uku tayi wanka ta sa hijab dinta ta fita ta nufi gate, tafiya kawai take har ta iso main road, tsaye tayi tana kalle kallen ababen hawa dake wucewa, ko sanin yanda xata ce su tsaya bata yi ba, can dai tayi deciding ta jira motar captain, ta kusa minti sha biyar tsaye sai wasa da hijab take wani mota yayi parking gefenta ta bi motar da ido, wani ne ya fito ya kusa minti uki tsaye kafin ya karaso kusa da ita yana kallonta ya rungume hannu yace "Good afternoon!" Dauke kai tayi ta turo baki, ya karyar da kai yace "naga alamar kina jiran driver ne koh?" Kallonsa tayi tace "No motar captain nake jira in gani" ya dan wara manyan idonsa yace "Kike jira ki gani?" Tace "Eh" yace "Ohk yace maki yana xuwa ne?" Girgixa masa kai tayi, ya d'an yi shiru kafin yace "Toh ki kirasa" tace "Bana da waya" yace "Toh ga ta wa" tace "Bana da number" murmushi yayi yana kallonta yace "Ohh dat's good, to in yi dropping din ki?" Kallonsa tayi tace "Toh" sannan ta nufi gaban motar, bin ta yayi da kallo har ta bude ta shiga, ya xaga shi ma ya shiga, sai da ya hau kan titi sannan yace "Ina ne gidan ku" buda hannu tayi tace "Nima ban sani ba" kallonta yayi da sauri yace "Baki sani ba?" Kamar xata yi kuka tace "Ehh amma kamar ta can captain ya biyo, sai yayi corner" waje ya samu yayi parking don kansa ya fara rikicewa yana kallonta yace "Ya sunan ki!" Langwabar da kai tayi ta wara ido tace "Jasmine, jewel baby!" Kallonta yake ko kiftawa bai yi, can yace "Daga ina kike yanxu?" Kamar xata yi kuka tace "Uncle ne yayi min ihu ya koreni, shine xan je gidan Captain" jinginar da kansa yayi jikin kujerar motar yace "Toh fah! Amma ba garin nan kike ba koh?" Tace "Ehh Mami na ta tafi UK in ji uncle a can muke sai muka xo nan yace min?" Xaro ido yayi yace "Toh yanxu ina xan kai ki?" Tace "Mu bi ta can kila xa mu ga gidan" tada motar yayi ya bi inda tace, tafiya kawai suke da sun yi nisa sai tace ba nan bane, duk ta daure masa kai nan ya fara tunanin anya bata da disorder kuwa, fashe masa da kuka tayi daga karshe wai ita sai ya kai ta gida, can dai ya fara tunanin anya ma ba aljana ya dauko ba, dafe kansa yayi yace "Look Jasmine ni ban san gidan ku ba wllh, ya sunan brother din naki?" Tace "Sunansa captain!" Yace "Real name dinsa fa nace?" Tace "Ehh" Bude motar yayi ya fita da nufin tambayar ko akwai wani captain a anguwar, ita ma ta fito da sauri ta fashe da wani kuka tace "ni dai ka kai ni gidanmu plss" da damuwa yace "Wait! idan na maida ki inda na dauko ki xa ki gane gidan?" Make kafada tayi tace "Ni baxan gane ba gidan captain dina xa ka kai ni" xaro ido yayi yana salati a xuciyarsa, tana share hawayen fuskarta tace "Ka ji?" Hannunta ta ji an kama ta juya da sauri lokaci daya ta warce hannun, wata mata ta gani tsaye tana kallonta baki bude, a d'an tsorace ta koma kusa da shi, matar ta saki salati tace 'yar nan! Ashe Allah xae kuma hada mu" Jasmine ta turo baki tana komawa baya, shi kam kallon tsohuwar yayi yace "Yauwa mama kin san ta?" Washe baki tayi tace "Wllh na santa, kwarai kuwa na santa"
? *Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
60.....
Kallon mama jummai kawai yake, can ya girgixa kai yace "Toh yanxu ya xan yi da ita?" Da sauri tace "Ka bani ita in tafi da ita nasan inda xan samo su" Jasmine ta saki wani kara da ya tsorata mama jummai tace "Nooo I don't know herrr" ta fad'a tareda k'ura mishi ido tana kallonshi, tada motar kawai yayi ya fara tafiya, suka yi tafiyar kusan minti sha biyar ya isa wani babban gida yayi parking gaban gate ya juya yana kallon mama jummai yace "Idan kin samo yan uwan nata ki kawo su nan, gidan iyayena ne nan din" shiru mama jummai tayi ya d'an yi murmushi yace "Ehh" tace "A'a kaga ni dai duniya bbu gaskiya yanxu, ina iyayen naka?" Wayarsa ya dauka ya yi dialing number ya kai kunne, bayan few seconds yace "Farida ku fito ke da Ramla" daga haka ya katse wayar, ba a dau lkci ba wasu yan mata da baxa su wuce Jasmine ba suka fito, yace "Toh kin gani mama, kanne na ne wa ennan" daga haka ya bude motar ya fita ya xaga ya bude side din Jasmine ita ma ta fito tana kallon Mama Jummai k'asa k'asa, yana kallon kanninsa yace "Ku tafi da ita ciki" Farida dake ta kallonta tace toh, ta fara tafiya haka Ramla ta bi bayansu, mama jummai ta fito a sanyaye, ya fiddo dubu biyu ya mika mata yace "Kiyi kudin mota" godiya tayi ta fara tafiya tana waige waigen gidan, ya koma motar aka bude masa gate ya shiga yayi parking, da sallama ya tura kofar babban parlon gidan, durkushe ya ga jasmine jikin kujera kannin nasa na kusa da ita, xaune a kan kujera mahaifiyarsa ce sai stepmother dinsa dake parlon ita ma, Mahaifinsa ma na parlon xaune sanye da farin glass dinsa ga laptop gabansa kan centre table, karasowa yayi ya xauna daga gefen mum dinsa a kasa, mahaifiyar tasa Hajiya Mariya tace "Wacece wannan Abdul?" Sosa kai ya shiga yi a hankali yace "Hajiya bakuwa ce...." Wani kallo take masa tace "Bakuwa daga ina?" Rasa abinda xai ce mata yayi can yace "Mance gidansu tayi wai" wani kallo yan parlon suka shiga yi masa, Dad dinsa ma ya dago for the 1st tym yana kallon abinda ke faruwa, Hajiya ta daka masa tsawa tace "Waye abokin wasan ka a nan?" Yace "Hajiya ga ki ga ta ki tambayeta ni wllh bn santa ba ma, taimakon ta kawai nayi" Hajiya ta kalleta tace "Ke daga ina kike" Jasmine ta sauke idonta daga kallon da take ma Hajiyar a hankali tace "Gidan uncle?" Hajiya tace "Xa ki ina?" Ta dago manyan idonta tace "Captain!" Hajiya tace "ikon Allah, to daga wani garin kika xo?" Shiru tayi sai kuma tayi maza tace "UK" duk suka buda ido suna kallonta, stepmum dinsa Hajiya karima tace "Ina kenan a UK?" Buda musu hannu Jasmine tayi alamar bata sani ba, Hajiya ta kallesa ta juya xuwa harshen fullanci tace Maxa ya tafi da ita station right away, marairaice mata yayi yace "Ammi taimako...." Harara ta watsa masa tace "Xan saba maka wllh" Dad dake ta kallon Jasmine yace "Ke Ramla ku tafi da ita daki" mikewa suka yi gaba daya suka bar parlon, Abdul ya kalli Mum dinsa da ta hade rai sosai ya mike kansa a kasa ya bar parlon. Karfe bakwai da kusan rabi El-ameen ya shigo parlor junaid na bin bayansa, duk da ganinsu kasan ba karamin gajiya suka yi ba, ganin hanyar daki El-ameen ya nufa junaid ya fixgosa a fusace yace "Look am tired of this game ka gaya min inda yar mutane take Ahmad...." Juyawa El-ameen yayi yace "plss don't make me loose my temper..." Daga haka ya bar sa gun tsaye, dakin Hafsat ya shiga ya ganta xaune kan pray mat ya hade rai yace "Wai ma kina me ta fita gidan nan baki sani ba" kallonsa tayi tace "Ba tare ku ke da ita a daki ba, ta ina xan san ta fita ko bata fita ba" kallonta ya tsaya yi can ya fice daga dakin, bedroom dinsa ya shiga ya xauna gefen gado ya rike kansa. Jasmine ce xaune ita kadai dakin bayan isha, tun xuwanta gidan take xaune ita kadai a dakin sai dai su shigo su yi abinda ya kawo su su fita, Farida ce ta shigo mata da abinci ta fita, kamar xata yi kuka ta jawo abincin ta bude tana kallo, cokali ta dauka ta fara ci don dama yunwa take ji, bude kofar dakin aka yi wani guy da baxai wuce 33 ba ya shigo dakin har xai fita ganin ba kowa sai kuma ya dawo yana kallonta, bata sake kallonsa ba ta ci gaba da cin abincinta, farida ce ta shigo dakin ya kalleta yace "Who's she?" Tace "Ya Abdul brought her" yace "Abdul?" juyawa yayi ya fice daga dakin ya tafi dakin kanin nasa, Abdul dake xaune dakin yana kallo a system yace "Ka dawo bro?" yace "Yea, wace yarinyar!" Abdul ya ci gaba da kallonsa a laptop yace "Amm, i just saw her on the way... No I helped her wai ta mance gidansu," wani kallo yake masa kafin ya juya ya fita, ya koma dakin da Jasmine take, cikin dakin ya karasa yana kallonta yace "daga ina kike?" Kallonsa tayi ta ajiye spoon din hannunta tace "Daga gidan uncle" yace "xa ki ina?" Tace "Gidan Captain!" yace "Toh me ya kawo ki nan?" Ta kalli kofar dakin tace "Wani mutum ne" yace "A ina ya gan ki?" Xata yi magana Abdul ya shigo dakin, yana kallon yayansa, Jasmine tace "Ga shi nan" Yayan nasa me suna Aliyu yace "I gat you will one day bring what will lead you to ur grave Abdul, you saw a gal like this on the road, she lied to you, you picked her up nd brought her home ryt?" mikewa Jasmine tayi kamar xata yi kuka tace "Am not lying, am not a liar..." Aliyu ya kalleta yace "I see, to wacece ke?" Tace "I am Jasmine" yace "Ur family?" Tace "They are in UK" yace "Where in UK?" Ta langwabar da kai tace "I don't know!" Tabe baki yayi ya juya zai fita ta kalli Abdul tace "I don't like him..." Juyowa yayi yana kallonta yayi murmushi ya fita, Abdul ya sauke ajiyar xuciya yace "Ki ci abincin ki" ta koma ta xauna shi ma ya fita. Sha daya saura Ramla da farida suka shigo dakin suka shiga shirin kwanciya, ita dai Jasmine na xaune kan carpet har lokacin, Ramla ta nuna mata gado tace "Ki kwanta in xa kiyi bacci" daga haka ta shiga bathroom neman bathromm dan tanason tayi wanka amma babu k'ofa, bude kofar aka yi Aliyu ya shigo dakin, ya karaso ya durkusa kusa da ita yana kallonta yace "Ki ka ce baki so na?" Ta kallesa tace "Yess" yace "Why?" Ta ce "I don't know" kamar wacce tayi tunani sai kuma tace "Okayy you are mean" giranshi d'aya ya d'age yana examining fuskarta yace "Ohkk...?, have you eaten?" Gyada masa kai tayi yace "Kin yi sllh?" Ta girgixa masa kai yace "Why?" Tace "No bathroom no toilet" murmushi yayi ya nuna mata kofar bayin yace "There it is" tace "Someone went in " yace "Ohk idan ta fito sai ki shiga" mikewa yayi yace "Good nyt," daga haka ya fita daga dakin. Washegari da safe Jasmine na xaune bayan tayi wanka da ruwan da Ramla ta hada mata Aliyu ya shigo dakin, yana kallonta daga bakin kofar yace "Come down for breakfast" mikewa tayi ya juya ya fita ta bi bayansa, a bakin stairs yace "you make sure you greet everyone out there" tace "toh" xaune duk yan gidan suke a dinning, duk aka xuba mata ido ta kasa ci gaba da tafiya, juyawa yayi ganin ta tsaya yace "Taho" karasowa tayi har dinning din ya nuna mata kujera ta xauna, sai hararansa Hajiyarsa take da step mum dinsa, shi dai Abdul kansa na kasa, gaishesu tayi gaba daya stepmum dinsu kadai ta amsa, Aliyu yasa Ramla ta yi serving dinta yace "Eat" ba musu ta fara cin chips and Egg da soup, shi ma ya hada tea ya fara sha, ko minti goma yan gidan basu kara dining din ba duk suka mike banda Abdul, can dai shima ya mike ya fita waje, ta kalli Aliyu tace "They all don't want me to stay with them ryt?" bai ce mata komai ba ya ci gaba da shan tea dinsa, kallonsa kawai take hakan yasa ya ajiye cup din yana kallonta shi ma yace "Ya aka yi?" yar dariya tayi tace "You are fyn, just like my captain and uncle" ya buda ido yace "Really?" Kallon wayarsa da yayi vibrate tayi daga gefensu ta dauka tace "Your phone!" Bai ce komai ba ya ci gaba da shan tean sa, ta dawo kujerar dake kusa da nashi ta mika masa wayar tace "Sa min pictures in gani" karba yayi yana kallon kwayar idonta ta sunkuyar da kanta, mika mata wayar yayi bayan ya shiga gallery yace "Take Jasmine!" Karba tayi ta koma inda take tana kallon hotunan, har lokacin idonsa na kanta, can yace "When did you come to Nigeria?" Ta kallesa snn ta ci gaba da kallon hotunan tace "Last month" yace "And baki san gidanku ba har yanxu?" Mikewa tayi da sauri tana wara manyan idonta tace "Uncle!" Gunsa ta koma har tana tuntube tace "Look kun yi hoto da uncle dina" karban wayar yayi da sauri ya ga hotonsa ne da abokinsa Dr El-ameen wanda suka yi just last week ranan daurin auren El-ameen din, ya kalleta yace "You know him?" Gyada masa kai tayi da sauri tace "Yess he's my uncle" ajiye wayar yayi yace "Da gaske?" Tace "Yes, call him to pick me plss" kamar xata yi kuka ta kare maganar, shiru yayi yana kallonta, tace "plssss nah, am missing him" ajiyar xuciya ya sauke, ya dau wayar ya nemo number El-ameen, bugu uku El-ameen dake station da junaid ya dauka, Aliyu yasa a hands free yace "Assalamu alaikum, Where are you Ahmad?" El-ameen yace "Ya aka yi Aliyu?" Jasmine ta wara ido xata yi magana Aliyu ya daura hannu a lips dinsa alamar tayi shiru, yace "Kana dai ina yanxu?" El-ameen yace "Am very busy frnd!" Aliyu yace "me kake yi?" El-ameen yace "Bari dai xa mu yi waya anjima" Aliyu yace "Wait...." El-ameen yace "Kaga am in station yanxu, am not my self, a sister of mine is missing tun jiya" Aliyu ya lumshe ido ya bude yace "Jasmine?" Mikewa El-ameen yayi daga xaunen da yake yace "Exactly, you know anything about it?" Aliyu yace "Come over yanxu..." Kallon junaid El-ameen yayi yace "It seems he knows her whereabout" mikewa Junaid yayi fuskar nan tasa a daure ya fice daga station din, El-ameen ya sallami yan sandan ya bi bayansa da sauri, shi yayi driving din har ya isa gidansu Aliyu, parking yayi daga waje ya kira sa, Aliyu na dagawa El-ameen yace "ga mu a waje" Aliyu yace "Ka shigo mana" El-ameen ya kalli Junaid ya bude motar ya fita shi ma ya bi bayansa, har lokacin Jasmine na xaune parlo da Aliyu El-ameen ya bude kofar parlon, suka shigo tare da Junaid, mikewa Jasmine tayi da sauri ganinsu ta wara ido, da gudu ta nufesu idonta har ya fara cikowa, sai dai idonta na kan captain dake kallonta ko kiftawa bai yi, bata san lokacin da ta nufesa ba ta rungumesa tace "Captain!" Wajen seconds goma bai ce komai ba yana jin yanda ta rirriqeshi duk k'arfinta kamar za a rabasu kamin ya janyeta daga jikinsa a hankali, juyawa tayi da sauri ta kalli El-ameen tace "Uncle" xata rungumesa shi ma ya matsa daga wajen ya hade rai, shi dai Aliyu kallonsu kawai yake, murmushi ta kirkira tana kallon El-ameen a hankali tace "Uncle!" Kallo daya Junaid ya ma Aliyu ya kama hannunta ya nufi kofa, ta xaro ido tana kallonsa, bin sa da kallon mamaki suka yi su ma, Jasmine tace "Captain plss wait let me say goodbye to my new friends, they helped me...." Tuni ya fice da ita daga parlon, ta juya kamar xata yi kuka tana kallon Aliyu da ya bi ta da ido ta daga masa hannu, titi junaid ya nufa da ita don makullin motar na gun El-ameen, ya tsare me adai daita, yasa ta shiga shi ma ya shiga. Xaunawa El-ameen yayi a parlon xuciyarsa na tafarfasa, Aliyu ma ya xauna yace "Who's that barbarian?"El-ameen ya girgixa kai yace "Rabu da shi, where did you get her?" Aliyu ya dau wayarsa ya kira Abdul cikin yan mintuna ya shigo parlon, gaida El-ameen yayi ya xauna yana kallon yayansa, Aliyu yace "Where did you say you picked the gal!" Bayanin inda ya ganta Abdul yayi, El-ameen yace "Ohh amazing, tnx very much bro you helped us gaskiya" Abdul yayi murmushi yace "But how did you get to know tana nan" Bayanin yanda aka yi taga hoton El-ameen a wayarsa Aliyu yayi masu, El-ameen ya wara ido yace "Ikon Allah, but please don't tell Hajiya anything about cewar na santa...." Aliyu yace "Why?" El-ameen ya shafa kansa yace "Kawai ku dai kar ku ce komai" Abdul yace "tana ina?" El-ameen yace "Abokina ya tafi da ita" Abdul ya mike yace "Ohh without even a goodbye!" daga haka ya fita daga parlon. Aliyu yace "Don Allah ya ku ke da yarinyar?" El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "It's a long story...." Labarin jewel ya fara basa tun daga farko har ixuwa yanxu, Aliyu da tausayinta ya cikasa sosai, duk jikinsa yayi sanyi yace "Allah Sarki! Dat's so sad" El-ameen ya gyada kai yace "Yea it is" Aliyu ya had'e rai yace "Toh shine zai wani dinga nuna isa a kanta don kawai shine silar tsinto ta" El-Ameen ya tabe baki baki yace "Haka nan yake", tsaki Aliyu yayi yace "Ni ko xan nuna masa helping her doesn't mean yafi kowa authority a kanta" El-Ameen yayi dariya yace "Toh a ina xaka kuma ganinsa", kwafa Aliyu yace "Just watch and see what I do".
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
61__62
Fitowa Junaid yayi daga napep din yana kallon Jasmine da ta tsuke baki yace "Sauko kar in baki knock" kamar xata yi kuka ta sauko ya ciro kudi ya mika ma mai adai daitan ya kama hannunta ya nufi gate, Humainah ce xaune parlor da Hadiza suna ta hira, yayi tsaye bakin kofa yana kallon hadiza, jasmine ta karasa cikin parlon ta tafi gun Humainah ta durkusa tace "Anty na dawo" ko kallonta Humainah bata yi ba, junaid yace "Tashi ki wuce daki" mikewa tayi ta nufi stairs ya bi bayanta, Hadiza ta mike tace "Tabdin, kinga tafiya ta Humainah, sai mun hadu gobe" Humainah bata ce komai ba har ta fita, can ts mike ta tafi sama ita ma, dakinsa ta shiga ta ga baya nan, ta fito ta shiga dakin da tasan Jasmine na ciki, tsaye ta ganshi a dakin, kallo daya ya mata ya maida dubansa ga Jasmine yace "Ina jin ki" kmr xata yi kuka tace "Shine sai ne sai na sa hijab na fita naje main road ina jiran motar ka, sai baka xo ba, shine sai wani mutum yace in shiga motarsa na shiga" wani kallo ya watsa mata yace "Daga yanxu na sake jin sunan Uncle a bakin ki sai na fasa bakin" juyawa yayi ya fice daga dakin, Humainah ta bi bayansa har cikin dakinsa tace "Bari ka ji, ni yarinyar nan baxa ta kuma xama min a gida ba wllh, It's either ta bar min gida ko kuma inyi reporting dinka...." Bata rufe baki ba ya fixgota da shirin watsa mata mari sai kuma ya fasa, yana huci ya jefar da ita kan gado yace "Don uwar ki a kanki take xaune?" Mikewa xaune tayi tace "Uwata?" Sai kuma ta fashe da kuka tana kallonsa tace "Uwata ka xaga ya Ahmad" juyawa yayi ya fice daga dakin ya koma downstairs. Bayan magrib ya tafi siyo masu abinci don har lokacin Humainah na aikin kuka a daki, tana jin fitarsa ta dau hijab dinta da jaka ta fice daga gidan, Jasmine ya fara kai ma abinci da ya dawo ya sameta tana bacci ya tada ta tayi sllh ya ajiye abincin ya fita, har xai shiga dakinsa sai kuma ya tsaya, ya kusa minti biyar tsaye kafin ya shiga dakin Humainah, ganin bata ciki ya ajiye ledan hannunsa xai fita sai kuma ya nufi bathroom ya bude, juyawa yayi ya fita da sauri ya tafi gun mai gadi, mai gadin na ganinsa ya mike tsaye, yace "Yaushe ta fita?" Mai gadin yace "Bayan fitar ka, tace kati xata siyo" junaid bai ce komai ba ya nufi motarsa ya bude ya shiga ya fice daga gidan, cikin minti sha biyar ya isa gida yayi parking a waje, lokaci daya gabansa ya fara faduwa, da kyar ya ja kafa ya shiga compound din, ya kusa minti uku tsaye balconyn Mumy kafin ya tura kofar a hankali ya shiga, ido hudu suka yi da Mumy dake xaune parlon sai Aysha dake parlon ita ma, jikinsa yayi sanyi ganin Humainah xaune parlon kan carpet kusa da Mumy, Mumy bata kuma kallon inda yake ba har ya karaso parlon ya durkusa nan kasa da kyar yace "Ina yini Mumy" kallonsa tayi tace "Uhn Ahmad kenan, ita Humainahr ce ta xama abar walakantawar ka yanxu, har ka kalleta ka xagi Uwarta da ke kabari sbda ka isa koh?" Sauke idonsa yayi a hankali daga kallonta, Mumy tace "Tunda har ka iya bude baki ka xagi uwarta nima xaka iya xagina, infact nima ka xaga..." Da kyar yace "Don Allah kiyi hakuri Mumy, wllh sharrin shaidan ne I didn't....." Tsawa ta daka masa tace "Rufe min baki" ya sunkuyar da kansa, ta kalli Humainah da har lokacin take hawaye tace "Kema rama ki ce masa uwarsa" kallon Mumy tayi, Mumy tace "Ehh kice masa uwar sa shi ma" ta kallesa ta ga shima kallonta yake, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, shi ma yyi murmushin ya sauke kansa, Mumy tace "Fice min a parlor" mikewa yayi ya fita daga dakin, Aysha tace "Me ya hada ku Humainah?" Shiru tayi bata ce komai ba, can ta kalli Mumy, Mumy ta mike ta bar parlon, Aysha ta dawo kusa da ita tace "Tell kar ki ji komai kin ji sis, me ya hada ku?" Kuka ta saki a hankali tace "Aunty kin ga fa har yanxu yarinyar tana nan gidan....." Hade kanta tayi da kujera ta kasa ci gaba, Aysha tayi shiru tana kallonta da tausayi, can ta dago tana share hawayen idonta tace "Amma Anty kar ki gaya ma Mumy" Aysha bata iya ta ce komai ba, ta mike ta fita daga parlon, tsaye ta gansa a balcony ta karasa kusa da shi tace "Ya Ahmad?" Juyawa yayi yana kallonta yace "What did she tell mum?" Girgixa kai tayi tace "Bata ce komai ba, amma ya Ahmad kai ma kasan baka kyauta mata kuma Allah...." Hannu ya daga xai wanka mata mari ta bar wajen yace "Xan baki mamaki idan baki fita sabgata ba wllh" juyawa tayi ta koma parlor, ido hudu yayi da Hajiya dake tsakar gida for the 5th time ya sauke kai, tace "Ina yini Ahmad" kallonta yayi fuska daure yace "Ina yini" tayi wani murmushi ta ci gaba da abinda take, jasmine ce ta fado masa ya shiga parlor yaga ba kowa ya nufi bedroom, xaune ya ganta ita da Aysha, Aysha na ganinsa ta mike ya bi ta da harara har ta fita, ya dawo kusa da Humainah ya xauna yace "Ohk, Alryt! Am sorry, tashi mu tafi gida" ta hade rai sosai tace "Bbu inda xan je" yace "Koh?" Juyawa tayi xata kwanta ya fixgota, ta shiga turasa ya hade ta da jikinsa, kasa kwace kanta tayi, ta fashe da kuka tace "Allah ni ka kyaleni...." Bai bari ta rufe baki ba ya hade bakinsu, sai da ya gaji don kansa ya kyaleta, xata kwanta ya dauketa ya mike, bude ido tayi da sauri tace "Meye haka?" Bai saurareta ba ya fita daga dakin, rufe fuskarta tayi da sauri a jikinsa tana cewa "Na shiga uku" Aysha dake parlor ta bi su da ido, har ya fita parlon, xaro ido Hajiya tayi tana kallonsu ta dau waya da sauri tana kiran Umma, Umma na dagawa tace "Bilki fito fito ki ga ikon Allah, fito waje yanxun nan" da gudu umma ta fito daga part dinta, ta bude baki tana kallonsu ita ma, lamo Humainah tayi a jikinsa har suka fita gate, Umma ta yi side din Hajiya da sauri tace "kinga tsiya koh? Kar dai ace wannan karan ma aikin banxa muke, wllh kila ciki ne da ita ma laulayi take" Hajiya da bata samu bakin cewa komai ba ta rafka tagumi, Umma tace "Kinyi shiru" Hajiya ta sauke wani shegen ajiyar xuciya ta mike tace "Mu je ciki balki" ba musu Umma ta bi bayanta. Junaid na gama parking a gida har bedroom ya kai ta, yana ajiye ta ya fice daga dakin ya shiga dakin da Jasmine take, kwance ya ganta ta takure waje daya, ya durkusa kusa da ita yace "Jasmine!" Bude ido tayi a hankali, tana ganinsa ta mike xaune yace "Me ya faru?" A hankali tace "My head is aching" abincin da ya ajiye mata ya jawo ya bude ya ga bata ci ba, yace "Me yasa baki ci ba?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya bude take away din ya dau spoon ya sa mata a ciki ya mika mata ta karba, yace "Eat" ba musu ta fara cin abincin yana kallonta, da ta dago ido sai taga kallonta yake, ganin irin kallon yasa ta matso kusa da shi a hankali tace "Captain!" Ko kadan bata ga alamar yasan tana yi ba, ta kirasa yayi sau biyu kafin ta dafa hannunsa, kifta idon yayi da sauri yace "Jasmine!" Langwabar da kai tayi tace "You are looking at me" sauke idonsa yayi kasa, kamar xata yi kuka ta sauko kasa ta durkusa kusa da shi tace "Did I wrong you again?" Murmushi ne yayi escaping lips dinsa yace "No!" Mikewa tayi ta koma kan gadon ya bi ta da kallo ta xauna ta ci gaba da cin abincinta, ya tashi ya fita daga dakin ya koma nasa, sha daya da wani abu ya sake dawowa dakin, kwance ya ganta ya karasa kusa da gadon ya durkusa ya ga bacci take, ya cire bargon jikinta yana kallonta, sleeping gown ne jikinta, ya dinga kallonta, lumshe ido yayi ya daura lips dinsa a goshinta ya gangaro a hankali har xuwa kan lips dinta, bude ido tayi da sauri ya koma baya, ta mike xaune tana kallonsa, kasa motsi yayi a gun bai kuma bari sun hada ido ba can ya mike da kyar ya fice daga dakin, ya koma nasa, ya kusa minti talatin xaune kafin ya mike ya fita ya shiga dakin Humainah, kwance ya ganta cikin bargo ya karasa gadon ya xauna ya cire bargon, ta bude ido tana kallonsa, shiga yayi cikin bargon ta mike xaune xata sauka ya jawota jikinsa ya kashe wutan dakin. Washegari da safe karfe bakwai ya gama shirin fita aiki, kasa shiga dakin Jasmine yayi, Humainah ta gama shirin makaranta ita ma bayan ta hada breakfast don tun asuba da suka tashi bata koma ba, yana xaune parlor rike da cup din tea ya kalli Humainah da saukowarta kenan yace "Tafi kice mata ta shirya driver xai xo kai ta makaranta" yi tayi kamar bata ji sa ba ta ci gaba da goge takalminta, yace "Humainah!" Ta daga kai tana kallonsa, repeating kansa yayi ta hade rai tace "Takalmi na nake polish" yace "Kawo in maki ki tafi" tabe baki tayi ta ajiye takalmin ta haura sama, samunta tayi ta fito daga wanka daure da towel, tana mata wani kallo tace "Ki shirya wai" daga haka ta fita, shi ya ajiye Humainah, Jasmine kuma driver ya ajiye ta. Tun daga lokacin da Junaid ya taho da Jasmine El-ameen bai sake bi ta kansu ba duk da yana son ganin Jasmine amma yaki xuwa gidan, ba karamin takura masa Aliyu yayi a kan ya nuna masa gidan junaid ba ya dinga kakkauce masa don yasan ko kadan bai da mutunci, Jasmine kam tun bata damuwa da abinda Humainah ke mata har ta fara damuwa don da tayi mata abu sai ta fara kuka, duk ran da hadiza ke gidan kuwa bata da kwanciyar hankali don ita tsoronta ma take ko da yaushe cikin tsangwamarta suke, tana son ganin Uncle dinta ta tambayesa yaushe Maminta xata dawo amma har ranan bata gansa ya xo ba, gashi tana tsoron tambayar captain shi, shi ma captain din ba sosai take ganinsa ba don tun bayan incident din daren ranan bai barin su hadu sai tayi bacci, duk dare kafin ya kwanta sai ya shiga to make sure she's fyn, a haka ta cika wata daya a gidan, ranan wani lahadi tana sharan parlor don yanxu kusan ita take duka aikin gidan idan captain baya nan taji an danna bell, ajiye broom din tayi ta mike da kyar don tun jiya cikinta ke mata ciwo, karasawa gun kofar tayi ta bude xaro ido tayi tace "Aunty!" Sai ta rungumeta ta saka kuka tace "plss go with me aunty" Hafsat dake kallonta ganin yanda ta rame tausayinta ya cika ta tace "Ohk I will dear" kallonta kawai El-ameen yake, tana daga kai ta gansa ta karasa da gudu ta rungumesa hawaye na sauko mata tace "Don Allah Uncle ka tafi da ni kar ka bar ni" janyeta yayi jikinsa ya gyada mata kai kawai, Hafsat ta karasa cikin parlon, El-ameen ya kama hannunta suka shiga, kasa ta xauna kusa da shi tana kallonsa tace "In dauko kayana?" Yace "Captain fah?" Bude hannu tayi tace "Ban sani ba nima" xai yi magana aka bude kofar Junaid ya shigo, ya d'an yi mamakin ganinsu ya karasa cikin parlon suka gaisa da Hafsat, ya xauna yana kallon El-ameen da ya hade rai yace "Welcome Doctor"
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
63.....
El-ameen yace "Thank you" mikewa yayi yana Satan kallon Jasmine da ta sunkuyar da Kai ya haura sama, ba a dau lokaci ba Humainah ta sauko ta shigo parlon ta gaida su ta tafi kitchen ta dauko drinks ta ajiye sannan ta xauna parlon, mikewa El-ameen yayi Jasmine ma ta mike da sauri tana kallonsa tace "Ina xa ka uncle?" Yace "Mu je" binsa tayi suka fita Humainah da Hafsat duk suka bi su da kallo, garden ya tafi da ita ya xauna ta xauna gabansa yace "What's wrong with you?" Hawaye ne ya cika idonta a hankali tace "I want to go to Mami...." Sai kuma ta fashe da kuka, ya kamo hannunta yana kallonta yace "An maki wani abu ne?" Hawaye na bin kuncinta tace "She don't like me, frnd dinta ma bata sona they are always shouting at me and calling me a mad girl...." Wani kukan ta kuma fashe wa da, cikin sanyin murya yace "Kiyi hakuri" kai kawai ta gyada masa, yace "And what did captain say about it" ta girgixa Kai tace "He's always at work...." Dago kanta yayi yana kallon kyakkyawan fuskarta, ya sa yatsa yana goge mata hawayen da ya ki tsaya mata a hankali yace "It's ohk jewel" muryarta na rawa tace "Are you going with me plss?" fuskarsa ya kai kusa da nata ya had'e goshinsu yace "Toh ba ke kika gudu ba baby" tace "I won't do that again plss" kallon yanda dan karamin bakinta ke motsi ya dinga yi, tace "Plss ka tafi da ni uncle they don't like me, they are always calling me mad...." Lumshe ido yayi ya hade bakinsu, tayi still a wajen, lokaci daya jikinta ya dau rawa, takun da yaji yasa shi saurin cire bakinsa ya saketa amma tuni ya iso wajen don a kan idonsa yayi hakan, tsaye yayi gun kamar an dasa shi xuciyarsa na bugawa yana kallonsu, El-ameen ya mike shi ma idonsa kansa, karasowa yayi yace "Xo ki wuce" ba musu ta mike ya bar wajen da sauri da ganinta kasan a mugun tsorace take, takawa yayi har gaban El-ameen yana kallonsa cikin kaushin murya yace "Daga yau kar ka kuma shigo min gida Ahmad, this shud be ur last plss, idan ba haka ba duk me na maka kai ka ja ma kanka, i dont want to see you in my home any longer, to hell with the goddamn friendship" har wani rawa jikinsa yake yana maganan lokaci daya idonsa ya kada yayi jajur, ya juya yana huci ya bar wajen, El-ameen ya shafa kansa ya ciro wayarsa ya kira Hafsat ta fito su wuce. Sama junaid ya nufa ya bude kofar dakin da take, xaune ya ganta kasa ta takure gu daya, tana ganinsa ta mike, ya karasa kusa da ita ya fixgota lokaci daya ya kifa mata wani wawan mari da yayi mugun gigitata don sai da ta fadi, bin ta yayi ya dago fuskarsa a daure cikin kak'k'ausar murya yace "You allowed him kissed you?" Kasa bude idonta tayi sai wani rawa da jikinta yake, ji yayi kamar xuciyarsa na shirin buga wa ya jefar da ita ya fice da sauri, ta kusa minti goma kafin ta iya bude idonta da kyar, ji tayi gaba daya dakin na juya mata ga wani axababben ciwo da kanta ke mata, ta rike kan tana son mikewa ta xube gun daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba.
Har after asr Junaid na balcony xaune ya jinginar da kansa jikin kujera idonsa lumshe, bude idon yayi a hankali jin kamar ana amai, ya mike ya shiga parlon, Humainah ya gani durkushe a bakin kofar toilet din dake parlon, da kamar xai koma sai kuma ya karasa, amai take sosai yana kallonta har ta gama ta mike ta nufi stairs da sauri da ganinta ta galabaita ba kadan ba, juyawa yayi ya koma balcony yayi xamansa. Sai da aka yi magrib ya shiga gida bayan ya siyo masu take away, ya jima tsaye corridor kafin ya tura kofar dakin Jasmine kwance ya ganta a kasa, ta bude idonta da yayi mata nauyi da kyar ga kadawa da suka yi, wani ja na musamman lips dinta suka yi da ganinta kasan ba karamin kuka ta sha ba, karasawa yayi dakin ta mike xaune da sauri ganin sa, ya ajiye ledan abincin ya fita, dakinsa ya koma ya hade kai da bango wani mugun tausayinta na ratsa shi, ya nufi gado ya shige cikin bargo. Har tsakar dare bai iya ya rintsa ba, aman da Humainah ke tayi yasa shi mikewa ya fita ya shiga dakinta ya sameta durkushe a bathroom, yace "What's wrong with you?" Kasa ce masa komai tayi ta mike ta koma kan gado ya juya ya fita. Washegari yana dawowa daga mosque dakin Jasmine ya shiga xaune ya ganta kan praying mat ya juya ya fita, ganin yanda Humainah ke amai yasa shi tafiya asibiti da ita da safe, kallon likitan dake masa bayani kawai yake har likitan ya kai aya, da mamaki likitan yace "Ain't you happy Mr Ahmad Junaid?" Junaid ya d'an yi murmushi yace "Ohh I am... Of course I am thanks Dr" murmushi likitan yayi yace "Congrat once more Mr Ahmad" mikewa Junaid yayi yana d'an murmushi, karfe sha daya na safen suka iso gida bayan an bata magunguna da allurai, har ya gama parking bacci take ya juya yana kallonta, murmushi yayi ya fito ya xaga ya bude motar ya dauketa ya tafi cikin gidan. Murmushi El-ameen yayi ya yagi memon dake kan table dinsa ya dau pen yayi rubutu ya tura gaban Aliyu dake xaune gabansa, dauka Aliyu yayi yana karanta content din yace "Uhn don Allah da gaske?" El-ameen ya daga kafada yace "Yea! Dat's the address, you can do what ever you wish provided you won't harm the girl" mikewa Aliyu yayi yace "Thank you" daga haka ya fice daga office din. Bayan sati daya Jasmine na daki xaune da yamma tayi tagumi da ganinta kasan tana cikin damuwa ga yunwar da take ji tana kuma tsoron fita, tura kofar dakinta aka yi ta mike da sauri don a tunaninta junaid ne duk da rabon da ya shigo dakinta tun ranan da ya shigo ya ajiye mata abinci bayan ya mareta, Hadiza ce ta shigo dakin tace "Ke don ubanki baxa ki fito kiyi gyaran gidan ba, kina ganin me gidan bata da lafiya sai dai ki wani kume a daki" kofa Jasmine ta nufa ta fita hadiza ta bi ta da harara, gyare gyare kawai take a parlon Humainah kuma na kwance tana shan kankana, hantaran ta hadiza ta dinga yi komai tayi tace bai yi dai dai ba, Humainah da hayaniyar ma ba son shi take ba tace "Ke xo dauke bowl din nan ki bar min parlor dallah, katuwa da ke bbu abinda kika iya sai dai a baki ki ci mahaukaciya kawai" karasawa Jasmine tayi da sauri ta durkusa ta dauki daya daga babban bowl din Hadiza ta daka mata tsawan da ya firgitata ta sake bowl din ya tarwatse ta mike tsaye da sauri, mikewa Humainah tayi tace "Kan uba shi bowl din nawa kika fasa...." Karasowa Hadiza tayi ta sauke mata wani wawan mari har biyu kamar an aikota sannan ta turata kasa a kan idon junaid da ya shigo parlon tana cewa "wato har yanxu haukan bai bar ki ba kenan, jaka mara asali" still Humainah tayi ganin Junaid, Hadiza na ganinsa ita ma ta kame wajen, gun Humainah ya nufa bai yi wata wata ba ya dauke ta da tagwayen mari, ai tuni Hadiza ta fice daga parlon tana tuntube, wani kara Humainah tayi ta durkushe wajen tana rike da kuncinta, ya kalli Jasmine dake durkushe kasa ta rike kanta, ya durkusa ya dagata ya nufi sama da ita, ba karamin wahala ta basa ba kafin ta cire hannayenta biyu daga rikon da tayi ma kanta kuka kawai take tana cewa kanta, kasa bude idon tayi ta rike hannunsa cikin kuka tace "I can't open my eyes captain, kai na na min ciwo sosai" bai san lokacin da ya rungumeta ba idonsa ya kada sosai, sun kusa minti sha biyar kafin ya mike ya sa mata hijab dinta ganin taki bude idon ya fita xuwa asibiti da ita. Sai kusan magrib suka dawo gida yana rike da hannunta suka shiga parlor har lokacin bata yarda ta bude ido ba babu yanda likitan basu yi da ita ba, duk ta daga ma junaid hankali, kwantar da ita yayi kan kujera bayan ya bata malt dinta ta karasa shanyewa ya bata magunguna ta sha, xaunawa yayi gefenta ya rike kansa, wayarsa dake kan kujera ya fara ring ya dago da kyar ya dauka yana kallon screen din, gabansa ya fadi ganin kiran Abbansa, mikewa yyi ita ma ta mike xaune da sauri tana laluba sa tace "No don't leave me Plss captain" komawa yayi ya xauna cikin sanyin murya yace "toh bude idon sai in tafi da ke" muryar ta na rawa tace "Baxan iya ba, it's paining me" dafe kansa yayi can ya dago ya daga kiran Abbansa, daga daya side din Abba yace "Ka taho gida" ajiye wayar yayi don dama he was expecting that, ya dagota ya kama hannunta suka fita, yana gama parking a kofar gidansu yace "Yanxu xan fito kin ji Jasmine" kai ta gyada masa idonta rufe, ya bude motar ya fita ya rufe, ko ba a gaya masa ba yasan Humainah ta tafi gida, part din Mumy ya nufa ya tura kofar ya shiga, Abbansa na xaune parlon sai Mumy, Humainah kuma na xaune kasa kusa da Mumy sanye da hijab har kasa ta sunkuyar da kai, karasawa yayi cikin parlon kansa a kasa ya durkusa ya xauna kan rug ya gaida Abba, kallonsa kawai Abba yake, ya dago da kyar yana kallon Mumy yaga ita ma kallonsa take ya sunkuyar da kansa, Abba yace "Ahmad!" Ba tare da ya dago ba yace "Na'am" Mikewa Humainah tayi da sauri tayi hanyar toilet sai amai, bin bayanta Mumy tayi ta dafa ta tana kallonta, sannu ta dinga mata ta dagota bayan ta gama, da kyar tace "xan kwanta Mumy" Kama hannunta Mumy tayi ta kai ta bedroom dinta ta kwanta nan da nan ta fara bacci, Mumy ta kusa minti biyar a tsaye tana kallonta kafin ta juya ta fita, xaunawa tayi a inda take Abba yace "Bata da lafiya ne?" Mumy tace "Eh ta kwanta ma" yace "Toh koh a tafi asibiti!" Mumy tace "Bari ta tashi dai" kallon junaid da kansa ke kasa Abba yayi yace "You slapped her ryt?" Shiru yayi bai ce komai ba Abba yayi masa tsawa yace "Ba magana nake maka ba?" Gyada kai yayi yace "Eh Abba" Abba yace "Good!"
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
64__65
Tashi ka je, k'asa tashi yayi Abba yace "Baxa ka bar min parlor ba?" A hankali yace "Abba kayi hakuri don Allah, sharrin...." Mikewa Abba yayi yace "you are stupid, get away" mikewa yayi da kyar ya fita daga parlon, ya nufi gate, yana bude motar Jasmine dake xaune yanda ya bar ta har lkcn idonta rufe tace "Captain!" Ba tare da ya kalleta ba bai kuma ce komai ba ya tada motar, kiransa ta kuma yi bae tanka ta ba ya ja motar, laluba sa ta shiga yi, ya kama hannunta yana driving da hannu daya yace "Open ur eyez!" Ta girgixa kai tace "It's hurting me" bai kuma cewa komai ba har suka isa gida, kallon b'akin motar dake Parke daga gefen flowers din da ya xagaye frontage din gidan ya dinga yi, mai gadi na bude masa gate ya sauke glass yace "Waye yayi parking can?" Mai gadin ya kalli motar yace "ca yayi wani yake jira a can gidan yallabai" junaid bai kuma cewa komai ba ya sake kallon motar sannan ya ja motarsa ya shiga compound, yana gama parking ya juya yana kallonta yace "Jasmine open those eyez idan ba haka ba xan yi tafiya ta in bar ki" da sauri ta kamo hannunsa kamar xata yi kuka tace "yana min ciwo captain, don't leave me plss, ka kira uncle kace ya kawo min Magani" wani kallo yake mata kamar tana ganinsa, can ya janye hannunsa xai sauka ta rikosa da sauri tace "No plss" hade rai yayi yace "toh ba sai na fita ba sannan xan fito da ke" a hankali ta sakesa ya fita ya xaga ya bude side din da take ya kama hannunta ta sauko ya rufe motar suka nufi cikin gidan, parlor ya xaunar da ita ya koma wani kujerar ya xauna ya dau remote yayi powering tv, a hankali tace "Captain!" Ya kalleta bai ce komai bs, kuma kiransa tayi yace "Yess!" Tace "kar ka tafi ka barni" dauke kai yayi bai tanka ta ba ya maida dubansa gun tv, can ya mike ya shiga toilet din dake parlon ya dauro alwala ya fito, nan parlon yayi don har anyi isha a mosque, yana idar wa ya koma ya xauna ya ci gaba da kallonsa, kiransa tayi ya juya ya kalleta yace "What?" A hankali tace "I want to ease my self" kallonta kawai yake har sai da ta kuma kiransa yace "Toh ki bude idonki ki je kiyi mana" girgixa masa kai tayi tace "Yana min ciwo ne" bai kuma cewa komai ba ita ma tayi shiru, har bayan kusan minti goma tausayinta ya ji ya mike da kyar ya karasa kusa da ita yace "Stand up" mikewa tayi ya kama hannunta ya nufi toilet da ita nan bakin kofar ya bar ta yace "Go in" daga haka ya juya ya dawo parlor, ba a dau lokaci ba ta fito tana kiransa yace "What?" Tana lalube ta shigo parlon ta xauna, sun fi awa daya xaune ganin yanda tayi lamo jikin kujerar kmr me bacci yace "Me xa ki ci?" Da sauri ta bude ido alamar baccin ya fara daukarta, ya mike yana kallonta ya karaso kusa da ita ya durkusa yana kallon idanuwanta da suka yi ja sosai yace "Good you open the eyez, ya daina ciwo yanxu" shiru tayi sai kuma tace "Yana min" yace "Me xa ki ci?" Bata ce komai ba ta yi kasa da kanta yace "Xa ki sha tea nd bread?" Ta kallesa tace "No! Only tea" mikewa yayi ya nufi kitchen ba a dau lokaci ba ya dawo rike da cup din tea, ya mika mata ta karba tace "Thank you!" Komawa yayi ya xauna, tana gama shan tean ya sa ta taje tayi alwala tayi sllh. Karfe goma saura ganin ta fara bacci yace "Go to bed if you are sleepy" mikewa tayi ta nufi stairs ya bi ta da kallo. Washegari da asuba ya kwankwasa mata kofa, cire bargon jikinta tayi ta xauna tana murxa ido, can ta sauka daga kan gadon ta nufi kofar ta bude, kallonta yake daga sama har kasa, yar rigar bacci ne jikinta tace "Captain" ya sauke idonsa yace "It's time for prayer," har ya juya xai tafi ya kuma juyowa yace "kina gama sllh ki shirya for islamiyya" ta gyada masa Kai ya juya ya bar bakin kofar, yana xaune parlor shirye cikin uniform rike da cup din coffee Jasmine ta sauko, kallon agogo yayi yaga Karfe bakwai saura minti goma yace "Tafi ki dafa indomie" tace "Toh" ta nufi kitchen, bin ta yayi da kallo yace "Come here" ta juyo ta dawo inda yake ta tsugunna tace "Na'am" yace "Baki iya gaisuwa ba" kallonsa kawai take wanda hakan ya sa shi dauke kai, a hankali tace "Good morning captain" ajiye cup din hannunsa yayi ba tare da ya kalleta ba ya mike yace "Morning" tashi tayi ita ma tana kallon white uniform din jikinsa tace "You've not buttoned all the buttons captain" kokarin barin wajen yake ta shiga gabansa tace "Let me help you" da sauri ya koma baya ya hade rai yace "No! I will do that my self" daga haka ya nufi stairs, ta bi sa da kallo. El-ameen ne xaune a study room dinsa earpiece makale a kunnensa yana duba wani littafi, aka turo kofar dakin hade da sallama ya daga kai ya mata kallo daya ya maida dubansa kan littafin gabansa, karasowa tayi tace "You have a visitor!" Yace "Who?" Tace "Yana parlor" rufe littafin gabansa yayi yace "Alryt!" Ta juya ta fita, ya mike ya fita xuwa bedroom dinsa, jallabiya ya daura kan kananun kayan jikinsa ya sauko parlor, Aliyu ne xaune parlon, El-ameen yace "uhn! Ashe ka san gidana Dr" Aliyu ya kallesa yace "No! da map na xo" El-ameen yayi murmushi yace "Da alama" karasowa yayi ya xauna yace "Toh ya aka yi Dr, don nasan ba haka nan ka xo ba" Aliyu yace "It's private, let move out" El-ameen yace "Uhm toh mu nawa ne a parlon?" Mikewa Aliyu yayi ya nufi kofa El-ameen yayi murmushi ya bi bayansa. Bayan kwana uku Humainah na xaune kasa a parlor ta daura kai kan kujera duk ta rame ba kadan ba don ba karamin wahala take sha ba, Mumy ce xaune daga gefenta da sisternta Anty Nafee sai Abba dake parlon shi ma, Anty nafisat tace "Wai baxa kiyi magana ba Humainah, Meye haka kike yi" ta fashe da kuka tace "Ni ba abinda ya hadamu Mumy, ni ban masa komai ba" shiru duk suka yi suna kallonta, hawaye ne ya shiga sauko mata, Mumy ta jinginar da kanta jikin kujera a sanyaye, she's just imagining anya Ahmad dinta ne kuwa, Ahmad din da ta yarda da tarbiyar da tayi masa, Ahmad da tayi raise da hannunta, Ahmad da ko kadan bai son bacin ranta, wai yau har kwana biyar bai sake waiwayo gidan ba, girgixa kai tayi ta lumshe ido, mikewa Humainah tayi da sauri Anty nafisat ta bi bayanta, bedroom ta kai ta bayan ta gama aman, ta kwantar da ita sannan ta xauna gefenta tace "Humainah idan ma baxa ki iya gaya ma su Mumy abinda ya hada ku da Ahmad ba ni ki gaya min, take me as ur mum kin ji" girgixa kai tayi tace "Ba abinda ya hadamu Aunty" sai kuma ta fashe da kuka, Anty nafisat tayi shiru tana kallonta cike da tausayinta. Junaid na xaune parlor da evening yana kallon wani program though absentminded, duk ya rasa dalilin da yasa ba shi da rest of mind daga jiya, haka kawai sai ya ji gabansa ya fadi, gashi yana son xuwa gida amma ya kasa, ko kadan bai son xamansa da Jasmine su biyu kadai, har aka kira magrib yana xaune parlon, can ya mike ya je yayi alwala ya wuce masallaci, yana dawowa sama ya tafi ya sameta xaune kan darduma, daga bakin kofar ya tsaya yace "Me za ki ci?" Ta d'an bude ido tace "Potatoe nd ketchup!" Tabe baki yayi ya juya ya fita ya dau makullin motarsa. Sha biyu saura na dare yana kwance idonsa biyu sai dai ya kashe wutan dakin yana son yin bacci amma ya kasa, murda kofa dakin aka yi jasmine ta shigo da sallama, ya mike xaune ya kunna bedside lamp yace "What's it?" Karasowa take son yi yace "Tsaya nan, nd what did you want?" Tsayawa tayi tace "Cikina ke man ciwo" yace "Go nd sleep gobe xan baki Magani, stop disturbing me" a hankali tace "Ohk" ta juya ta fita, ya sauke ajiyar xuciya ya koma ya kwanta, har daya bai yi bacci ba yana son dubata amma ya ki xuwa daga karshe ya mike ya dauro alwala ya shimfida darduma. Yana xaune cikin mota idonsa a kanta ko kiftawa bai yi har ta karaso gun motar, sanye take da hijab dinta har kasa ta bude front seat ta shiga tana kallonsa tace "Na gama" bai ce komai ba ya ja motar suka bar gidan, sai da suka dau hanya sannan yace "Cikin ya daina ciwon ne?" Girgixa masa kai tayi tace "Yana yi har yanxu" bai kuma cewa komai ba har suka iso wani gida bayan tafiyar kusan minti ashirin, kallonta yayi ita ma haka, ya dauke kansa ya bude motar xai fita tace "Where is this captain?" Juyowa yayi yace "You wait for me, ba dadewa xan yi ba!" "toh" kawai tace ya fita ya kulle motar ya shiga gidan. Tsakar gida ne babba me dauke da sashi daban daban, xaune a tsakar gidan wata 'yar dattijuwa ce da yara mata biyu da baxa su wuce sha takwas ba, tana ganinsa tace "Ikon Allah, Ahmad ne a gidan namu yau!" Tana magana ne tana kokarin bude masa wani tabarma ya xauna, D'an murmushi yayi ya xauna kan tabarmar yace "Ni ne Hajiya, ina yini?" Da fara'a tace "Lafiya lau Ahmad, ya gida ya su Amina?" Yace "duk lafiya lau" gaishesa yan matan suka yi ya amsa hade da tambayar su makaranta, Hajiya tace "Toh ina amaryar taka, ai ya kamata ka kawo min ita mu gaisa ko Ahmad" ya shafa kai yace "Xan kawo ta Hajiya" Hajiya tace "Toh muna xuba ido" yace "Baba na ciki kuwa?" Tace "Ehh bai jima da shigowa ba ma, tashi ka je" mikewa yayi ya nufi babban parlon gidan, da sallama ya shiga ya samesa xaune kan babban darduma a kishingide, dattijon na ganinsa yace "Ikon Allah, Ahmad!" Karasowa Junaid yayi kansa a kasa ya xauna hade da yi masa sallama ya gaishesa, da fara'a dattijon ya amsa masa yana tambayarsa gida da Abbansa, junaid yace "Duk suna lafiya Baba" Dattijon yace "toh ya aka yi, ko Muhammad ne ya aiko ka?" Girgixa kai yayi yace "Shawara na xo nema gun ka baba" Gyara xama dattijon yayi yace "Toh bismillah, ina jin ka Ahmad" shiru Junaid yayi na d'an lokaci kafin ya fara basa labarin Jasmine tun daga lokacin da ya ganta har xuwa yanxu, kallonsa kawai dattijon ke yi, can yayi murmushi yace "Ahmad kenan, to amma meye ka boye ma iyayenka wnn aikin ladan da kayi, ai abun su yi alfahari da kai ne wannan" girgixa kai yayi yace "A'a ba lallai su fahimce ni ba ma" shiru dattijon yayi sannan ya sauke ajiyar xuciya yace "Ikon Allah, to tana ina yarinyar?" Junaid yace "Gidana take" "tare da matar ka?" Ya tambayesa yana kallonsa, shiru yayi kafin yace "Ehh!" Dattijon yace "Amma da amincewar matar taka kuwa" shiru junaid yayi nan ma, can kuma yace "A'a" dattijon yace "Toh maido ta nan Sa'adatu ta rike ta har Allah ya bata lafiya ya bayyana danginta" kallonsa junaid yayi da sauri, can ya sunkuyar da kai, dattijon yace "Hakan yayi maka?" Gyada masa kai kawai yayi yace "Nagode Baba" ya ciro kudi aljihunsa ya ajiye masa dattijon yace "A'a je ka da abun ka Ahmad, duk lokacin da ka taso takanas don gaida ni xan karba" murmushi junaid yayi yace "Kayi hakuri baba, abubuwa ne suka yi yawa" dattijon yace "Allah kuwa" duk yanda junaid ya so tsohon ya amshi alkhairin kin karba yayi, haka yayi masa sallama ya fita bayan ya kuma jad'd'ad'a masa ya kawo Jasmine kar ya shiga hakkin matarsa, jinsa kawai junaid yayi ya fice daga parlon, yaran gidan ya bai ma kudin hannunsa yayi ma babarsu sallama ya fita, Malam tukur malamin mahaifinsa ne tun fil'azal, kusan gun sa junaid ya sauke littattafen addini da dama hakan yasa yake girmama tsohon. Bacci ya tarda Jasmine ke yi a motar bai tasheta ba ya tada motar ya bar layin bayan ya kwantar mata da kujerar. Yana xaune shi daya parlor ya jinginar da kansa jikin kujera, gaba daya hankalinsa yayi gun mumynsa a lokacin, dama akwai tym din da xai xo ya dade haka bai je inda take ba without any reason, lumshe ido yayi duk ya rasa abun da ke damunsa yanxu, gashi ko kadan shawarar da Malam Tukur ya basa bai masa ba, muryar Jasmine yaji tace "Captain!" Ya bude ido da sauri yana kallonta tace "Anty baxa ta dawo ba?" Hade rai yayi yace "leave!" Da sallama El-ameen ya shiga parlon, Mumy dake xaune da fatima suka amsa masa ya karasa cikin parlon ya gaida Mumy da fara'a bayan ya xauna, da murmushi ta amsa masa tana kallonsa, fatima ta gaishesa ya amsa hade da tambayarta sch, kallon Humainah dake kwance yayi kan yace komai ta gaishesa, ya amsa da murmushi lkci daya ya gano ba ita daya bace, ya kusa minti sha biyar parlon kafin Mumy tace "kana ji na Ahmad?" Ya kalleta yace "Ina ji Mumy" kasa cewa komai tayi da ganinta kasan there is something eating her in, gashi duk ta rame, sunkuyar da kansa yayi ko bata fadi ba yasan kan junaid ta kirasa, a hankali yace "Mumy kin yi shiru" cikin sanyin murya tace "I don't know what has come over ur frnd...." Kallonta yayi yace "Me ya faru Mumy?" Tuni idonta ya kada ta kasa ci gaba, jikinsa yayi sanyi ya kasa cewa komai kuma, bude kofar aka yi Abba ya shigo yana ganin El-ameen yace "Good u are here" xaunawa yayi ya fiddo wayarsa yyi danne danne ya kara kunne, junaid dake durkushe a lokacin kusa da Jasmine dake juye juye wai cikinta na ciwo ya kalli screen din wayar hannunsa gabansa ya fadi ganin Abbansa ne, da kyar ya d'aga daga daya bangaren Abba yace "Ka taho ina jiran ka yanxu" daga haka ya katse, bbu tunanin da junaid bai yi ba daga karshe dai ya mike bayan ya lullube Jasmine ya fita, xuciyarsa na raya masa Humainah ta fadi abu kenan a gida, cikin yan mintuna ya isa gida, yayi part din Mumy jiki ba kwari, bai yi tunanin Abba na can ba, yana bude kofar yayi still ta dalilin ido hudu da suka yi da Abban nasa, da kyar ya karaso parlon yayi ma El-ameen kallo daya ya dauke kai gabansa na faduwa, kasa kallon inda Mumy take yyi, ga Anty Nafisa ma dake parlon sai Aysha da Humainah dake jikinta, ya xauna ya gaida Abba, yaji no answer, a sanyaye ya gaida Mumy nan ma no answer, bai kuma gaida kowa parlon ba, cikin kaushin murya Abba yace "Ahmad!" Da kyar ya dago kai ya kallesa, Abba yace "Bani takardar Humainah!" Kallonsa kawai yake kamar bai fahimce sa ba, Abba ya mike yace "Ni kake ma wannan kallon?" Sunkuyar da kai yayi, A nutse Abba yace "Bani takardarta nace" junaid ya lumshe ido ya bude yace "Abba ni bbu abinda ya hada mu......" Bai rufe baki ba Abba ya sauke masa mari yace "You are very stupid ka bani abinda na tambayeka ko sai na saba maka" shiru yayi na d'an lokaci sai kuma yace "Babu takarda hannuna" Abba ya kalli Aysha yace "Ke tafi nemo min takarda" da kyar ta mike jiki a sanyaye ta shiga daki, ba a dau lokaci ba ta dawo rike da takarda Abba ya karba ya mika masa, karba yayi ya ciro pen din dake aljihunsa duk aka xuba masa ido a parlon barin Mumy da ko kiftawa bata yi, Humainah kam jikin kujera ta rufe fuskarta hawaye na sakko mata, cikin 'yan mintuna ya gama rubutunsa a jikin takardan ya mika ma Abba ba tare da ya bari sun hada ido ba, wani kallo El-ameen ke ma junaid yana son assuring kansa ba saki ya rubuta ba, Abba ya kusa minti uku idonsa na kan takardan kafin yayi wani murmushi ya mika ma Mumy da tuni hawaye ya cika idonta, ajiye takardar tayi don baxata iya gani ba, Anty Nafisat ta dauka da sauri cikin few seconds ta gama karanta takardan, mikewa tayi lokaci daya idonta ya canxa launi tace "Ehh lallai ka xama dan iska Ahmad, sakin ka rubuta da gaske?? Ashe kai mara imani ne?" Hannu Abba ya daga mata sannan ya kalli Junaid yace "Tashi ka tafi" mikewa yayi kansa a kasa ya nufi kofa, Mumy ta fashe da kuka haka ma Aysha, Humainah kam kin dago kanta tayi, El-ameen ya mike da sauri ya bi bayansa, karo junaid ya kusa ci da Umma da Hajiya dake labe balcony, bai ko bi ta kansu ba ya sauka, taku daya biyu yayi still yana kallon Hadiza dake tsaye balcony din Hajiya lokaci daya ya ganeta, tana ganinsa tayi saurin shigewa parlor ta rufe kofa, ji yayi kansa na juya masa, kan kace me har ya fice daga compound din ya isa gun motarsa, fixgosa El-ameen dake biye da shi yayi yace "Sakin ta kayi Ahmad?" Wani kallo Junaid yayi masa yace "Ehh" murmushin takaici El-ameen yayi yace "Good!" Junaid ya shige motarsa ya tada ya bar layin.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
66__67
Ko parking din arxiki bai yi ba ya shige cikin gida ya nufi dakinsa direct ya kwanta xuciyarsa na bugawa, har aka kira magrib yana kwance can ya mike yayi alwala ya fita xuwa Masallaci, sai da ya dawo ya shiga dakin Jasmine yaga bacci take, tashinta yayi ta bude ido a hankali, kallonta ya tsaya yi, ta mike xaune tace "Captain" kifta idonsa yayi yace "Cikin ya daina?" Ta gyada masa kai yace "Me xa ki ci?" Cikin sanyin murya tace "am not hungry" mikewa yayi yace "toh kiyi sallah" daga nan ya fita daga dakin. Har kusan daya na dare junaid bai yi bacci ba yana dai kwance, mikewa xaune yayi jin kamar an bude kofar parlor ya kalli agogo, jasmine? Toh ina za ta? ya mike tsaye ya nufi kofa da sauri ya fita, dai dai lokacin da haske ya gauraye downstairs, still yayi a gun, can kuma ya bude kofar dakinta, ga mamakinsa sai ya ganta kwance, kansa ya daure ba kadan ba don ya kulle kofar ai, karasawa dakin yayi da hanxari gun gadon ya cire bargon jikinta ta bude ido a tsorace, dagota yayi tace "Captain" bai saurareta ba ya fice ya koma dakinsa yana rike da hannunta ya rufe kofar da key, tace "What's that captain?" Wani kallo ya mata ba shiri tayi tsit, ya bude closet dinsa ya binciko pistol dinsa har biyu, xaro ido tayi a tsorace tana komawa baya tace "Captain!" Ya kalli kofa jin ana haurowa sama, da sauri ta dawo bayansa ita ma tana kallon kofar a mugun tsorace, hannunta ya rike gam har lokacin idonsa na kan kofar, xaro ido yayi ya ganin key din hannunsa ya nufi kofar da sauri da nufin sakalawaa yaji an riga sa slotting key, baya ya koma yana kallon kofar yana kiran Allah a xuciyarsa har aka bude, su uku ne ko wannensu sanye da bakar facemask, yayi ma biyu pointing din duka bindigan hannunsa, rungumesa Jasmine tayi ta baya ta runtse ido ta fasa ihu jikinta na rawa tace "Captain! Who are theyyy" Baya ya dinga komawa tana jikinsa, daya daga cikinsu ya karaso yayi pointing ma Jasmine bindigar hannun sa yace "Her life or you drop ur weapon" sauran ma duk suka karaso suka yi yanda yayi, ba karamin tashi hankalin Junaid yayi ba, lumshe ido yayi a hankali ya sake pistols din hannunsa ya rungumeta gam, cikin dakiyar murya yace "What did you want from me?" Dariya duk suka yi daya daga cikinsu yace "Money, cars, houses, infact everything" yana rungume da ita ya nufi inda atm dinsa yake ya dauka ya jefa masu ya fadi pin, ya kuma dauka makullin motocinsa har biyu ya jefa masu, da na gidansa daya, cikin dakiyar murya yace "What again?" Wani dariya duk suka yi, daya daga cikinsu ya tako har gabansa yana kallonsa, sake kankame Jasmine yayi a karo na farko xuciyarsa ya soma bugawa, ita ko ko ina na jikinta rawa yake sai kiransa take tana kuka, hannu mutumin yasa a aljihu ya ciro wani abu fari a leda ya jefar fuskar Junaid, daya daga cikinsu ya fixge Jasmine, daga nan suka fice daga dakin gaba daya taku daya biyu junaid yayi da niyar binsu ya xube nan gun, duk kokarin da yayi na son mikewa hakan bai yiwu ba, wani juyi yaji kansa yana yi, da kyar ya iya mika hannunsa ya jawo wayarsa dake gefen gado, number El-ameen yake son nemowa amma ya kasa, cikin ikon Allah ya fiddo lambar, ji yayi kamar numfashinsa na neman daukewa, wayar ya xame daga hannunsa shi ma ya kuma faduwa nan kasa, a hankali idonsa ya fara rufewa daga haka bai kuma sanin abinda ke faruwa ba, El-ameen dake xaune da laptop gabansa ya kalli agogo jin ringing din wayarsa, mikewa yayi ya dauko wayar daga charging da yake, tsayawa kallon screen din wayar yayi ganin number junaid, da kamar baxai dauka ba sai kuma ya tabe baki ya daga, shiru yayi bai ce komai, jin shirun yayi yawa yace "Ya aka yi, mistake i guess, ryt?" Jin ba ace komai ba ya kalli screen din yaga ba a katse ba, mayarwa yayi kunnensa yace "Hellow?" Tabe baki yayi ya katse wayar, har xai ajiye sai kuma ya kuma kiransa, har ya gama ring ba a dauka ba, ajiye wayar yayi ya koma ya xauna sai dai haka kawai hankalinsa yaki kwanciya. Kuka kawai Jasmine take tana kiran Captain har suka sa ta bayan motar, babu wanda ya ce mata komai har suka iso wani gida bayan tafiyar kusan minti talatin drivern yayi horn a bakin wani babban gate, ba a dau lokaci ba aka bude gate din, a parking space suka yi park din motar drivern motar ya fito kafin sauran su fito, nan take suka cire mask din fuskarsu daya daga cikinsu na kallon Jasmine yace "Fito!" Ta fashe da wani sabon kuka tace "Nooo!" Hade rai suka yi gaba daya mai tukin motar ya fito da bindigar aljihunsa yace "C'mon fito malama" ihu ta fasa a tsorace, ya fixgota yana nuna mata bindigan ba shiri tayi tsit ko ina na jikinta na rawa, yana kallon sauran dake tsaye yace "Sai mun hadu gobe you can go with the car" daga haka ya tasa ta gaba xuwa balcony, suna shiga parlon ta durkushe kasa tana bin ko ina na parlon da kallo, kamar me counting stairs din ya dinga saukowa yana kallonta, hade rai yayi yace "Amma na ce you guyz shouldn't scare her fa Salim" Wanda ya kira da Salim ya xauna saman kujera yace "We didn't" mikewa Jasmine tayi da sauri tana kallon stairs din jin muryarsa, ya sakar mata murmushi ya buda manyan idonsa yace "Jewel!" Da gudu ta karasa kusa da inda yake sai kuma ta ja ta tsaya ta fashe da kuka tana kallonsa, Yace "Amma ba mu yi haka da ku ba salim" mikewa salim din yayi yace "What did you expect idan bata yi kuka ba toh? Were you expecting her to be laughing bayan mun dauketa daga gida?" Daga haka ya shiga daki dake parlon, Aliyu ya d'an bude ido yace "Sorry jewel, they didn't mean to hurt you" hade rai tayi tace "Why am I here?" Bai ce komai ba ya karasa cikin parlon ya xauna. Washegari da safe El-ameen ya gama shirin fita office Hafsat ta shigo dakin tace "Breakfast fah?" Kallonta yayi yace "Sai na fita office" tace "Ohk" ta juya ta fita, mikewa yayi ya dau wayarsa har xai sa a aljihu junaid ya fado masa ya shiga kiransa, har ya gama katse wa ba a dauka ba, tsaki yayi ya dau brief case dinsa xai fita wayar ya fara ring ya duba yaga Aliyu ne, dagawa yayi, daga daya bangaren Aliyu yace "Good morning" El-ameen yace "Morning Dr, ya gida" Aliyu yace "Alhmdllh, ga ni ga Jewel!" El-ameen ya xaro ido yace "Jewel kuma?" Kallon Jasmine dake xaune ta takure waje daya Aliyu yayi ya mika mata wayar yace "Ur uncle" kin karba tayi ta fashe da kuka a hankali tace "Ka kai ni wajen captain plss" Katse wayar El-ameen yayi ya fice ya dau motarsa a parking space ya bar compound din, cikin 'yan mintuna ya isa gidan Junaid, bedroom ya nufa direct, ya kusa second goma tsaye bakin kofa yana kallon hodar dake xube a kasa ko ba a gaya masa ba yasan ta meye, ya ciro handkerchief ya rufe hancinsa ya karasa cikin dakin ya durkusa kusa da shi yana kallonsa, mikewa yayi ya fice daga dakin ya fiddo wayarsa ya shiga kiran Aliyu, bugu biyu ya daga, a fusace yace "Was that the deal, don me xa kasa ayi masa haka...." Dariya Aliyu yayi yace "Girman kansa nake son sauke masa, kuma da ca suka yi ya basu ita cikin lamana ba yarda xai yi ba" daga haka ya katse wayar, dafe kai El-ameen yayi can ya juya ya koma dakin. Abban El-ameen ne tsaye kan Junaid yana kallonsa, awan sa kusan hudu kenan hospital din still unconscious, El-ameen ma na jingine daga jikin bango tun safe bai bar dakin ba yana tare da shi, dad din nasa ya kallesa yace "Wai an sani ma kuwa a can gidansu?" El-ameen ya girgixa kai, Dad yace "Why? You mean baka kira su ba har yanxu" yace "Xan kira yanxu Dad, bana son daga masu hankali ne" Dad din yace "No call them right away! Kuma ka sake masa alluran" daga haka ya juya ya fita, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya ya ja kujera ya xauna ya dau wayarsa ya shiga kiran Abban Junaid, bugu uku ya daga, ya gaishesa da ladabi yace "Abba dama Ahmad ne ke asibiti tun safe....." Bai kai karshe ba Abba ya katse sa ta hanyar cewa "Allah ya sauke, ka kira uwarsa" daga haka ya katse wayar, El-ameen ya tsura ma wayar ido, lumshe ido yayi yana addu'ar Allah yasa ya farfado kafin yamma. K'in sakin jiki Jasmine tayi duk kuwa da Kanwar Aliyun dake gidan, hatta abinci taki ci, banda kuka babu abinda take ita ya kai ta gidan Captain, bayan la'asar gari yayi sanyi Aliyu yace "Toh tashi in kai ki" mikewa tayi tana share fuskarta ya fara tafiya ta bi bayansa, Ramla da duk xaman gidan ya isheta ta bi su da kallo, wata kofa ya bude ya fita tana biye da shi a baya, babban garden ne sosai ga carpet grasses Kore shar shimfide a ko ina na garden din, sannan ga babban swimming pool xagaye daga gefe, tsuntsaye ke ta shawagin su a wajen gwanin sha'awa, kare idonta ta shiga yi tace "Ohhsh, My head is aching, I can't follow here" ya kalleta yace "This is the only road" tana kare fuskarta ta shiga takowa a hankali, xaunawa yayi ya nuna mata gefensa yace "Sit" ta ki xama tace "Noo mu wuce plss, I don't like here, it's making me dizzy" hade rai yayi yace "Sai in kira dog yanxu idan baki xauna ba" da sauri ta xauna tana rurrufe idonta, a hankali yace "Open ur eyez!" Girgixa kai tayi kmr xata yi kuka tace "It's aching me" yace "Ki bude a hankali" a hankali ta shiga bude idon ta shiga bin ko ina na garden din da kallo, yace "What did you see?" Shiru tayi sai kuma murya can kasa tace "Green grasses!" Yace "No! Look deep, I mean don't blink your eyez nd tell me what you see" shiru tayi bata ce komai ba idonta na kan koren ciyayin ko kiftawa bata yi, a hankali ya mike ya juya ya bar gun ya koma cikin gida. Sai kusan Magrib ya koma garden din ya ganta kwance tana bacci, durkusawa yayi kusa da ita a hankali yace "Jasmeen" firgit ta farka tace "Ummana" sai kuma ta mike tsaye da sauri, rike kanta tayi tace "Wayyo Kai na" mikewa yayi ya komawa baya yana kallonta ganin faduwa xata yi, kasa tabata yayi har ta kai kasa, sannan ya durkusa har lokacin idonsa a kanta, ta kusa minti biyar bata dago ba, can ta dago a hankali idonta ya kada sosai ba kadan ba, da kyar tace "Ka kai ni wajen captain pls, I want to go to him" yace "Toh bari in baki Magani sai in kai ki" mikewa yayi ita ma ta mike da kyar, kasa tafiya tayi ganin faduwa xata yi ya juya da sauri ya koma cikin gidan ya kira Ramla ta fito ta kamata suka shiga cikin gidan, tea me kauri ya hada mata ya tilasta ta ta sha, sannan ya bata Magunguna tana sha bacci ya dauketa, Ramla ce ta rufa mata bargo ya mike yana kallonta yace "You stay with her kar ki bar ta ita kadai" kai ta gyada masa ya juya ya fita daga dakin.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
68__69
Har washe gari Junaid na kwance unconscious, duk wani taimako Dad d'in El-Ameen saida ya tabbatar sun bashi amma ko kadan baya responding to treatment, El-Ameen gaba daya hankalinshi ya tashi duk tausayinshi ya cikashi, Har lokacin babu wanda ya lek'o daga gidansu Junaid, a bangaren Jasmine kuwa kuka ta dinga yi ita a kaita gidan captain, shareta Aliyu yayi da farka can kuma yace "Toh tashi" mik'ewa tayi ta nufi gun slippers d'inta xata sa, kamar wacce ta tuna wani abin ta juyo tana kallonshi tace "Are you sure you are taking me to captain?" murmushi yayi ba tare da ya kalleta ba ya kad'a kai yace "Yes Jewel, amma zaki dena wannan kukan and clean your face" Kamin ya gama magana ta shiga share hawayen dake fuskanta tace "Av cleaned it" yace "Good", daga haka yayi gaba ta biyoshi a baya, hanyan da yabi jiya shi taga yabi yauma, yana bud'e k'aramin k'ofar garden d'in ta had'e rai taja ta tsaya daga wajen, juyowa yayi ya yaga ta had'e rai, murmushi yayi ya dawo gabanta yana kallon kyakkyar fuskarta da manyan idanunta da hawaye ya cika zubowansu any moment yace "Don't you want to see Captain?", kamar bataji mey yace mata ba tayi shiru tana kallon k'ofan, ganin baza tace komai ba yasa yace "He said we should wait for him there", ya fad'a yana nuna mata garden d'in da yatsanshi, yaci gaba "Captain is waiting for you in there", kamin ya rufe baki ta maza ta k'araso ta sa kai cikin garden d'in, murmurshi kawai yayi tareda shafa fuskarshi ya biyota a baya, waige waige ta dingayi ko zata ga Captain amma bata ganshi ba, ta juyo da idonta da suka kuma cikowa zatayi k'ofan taga ya shigo, hawayen na k'arasa gangarowa tace "You said he is waiting for me in here", ya girgiza kai yace "Erhm No, he said we should wait for him here, he is coming to pick you ltr" jiki a sanyaye batace komai ba ta koma kan bench d'in ta zauna tareda kifa kanta kan cinyoyinta, daga gefenta ya samu waje ya zauna, yace "Jewel!" Kin dagowa tayi, kamar bai son magana yace "Tell me what you see in here" dago kanta tayi ya nuna mata carpet grass dake shimfide yace "Me kika ga" shiru tayi bata ce komai ba tana bin ko ina na garden din da kallo, mikewa yayi ba tare da ya bari ta lura ba ya bar gun. Da rana El-Ameen na zaune d'akin Junaid yayi xurfi a tunanin da yake, kamar daga sama yajiyo muryan Junaid na ce mishi "Where is she? Where is Jasmine?", Da hanzari ya mike ya iso gaban gadon yana kallonsa, dukawa yayi murmushi yayi escaping lips dinsa yace "Ahmad how you feeling now?" Dauke kai Junaid yyi ya shiga k'ok'arin mik'ewa yaji kanshi na wani mugun sara mishi komawa yyi ya kwanta ya lumshe ido hade da dafe kai yace "Where is she?, I need to get to her, she is in trouble" da kyar yayi maganan yana kokarin sake tasowa, wani sarawa da kanshi yayi yasa yayi maza ya koma ya kwanta, El-ameen ya rik'o shi yace "Ahmad stop proving stubborn, you are still weak", Junaid yace "No! Help me get up pls, she's in trouble frnd!" rasa me zai ce masa El-ameen yayi, duk yaji tausayinshi ba kad'an ba, bai kuma ce masa komai ba ya koma ya xauna don yasan ba lallai ya iya mikewa ba, Allura kawai ya had'a daga karshe ganin Junaid ba shiru xai yi ba yayi mishi, a hankali ya dinga lumshe ido har bacci ya d'aukeshi, Yana fara bacci El-ameen ya k'ira wasu nurses d'in yace su kula da shi yanzu zaije ya dawo, ya jadadda musu da he should be under well supervision yanxun nan zaije ya dawo, a risine suka amsa mishi daga haka ya d'auki key yayi waje, kai tsaye gidansu Junaid ya nufa, daga bakin gate ya tsaya ya shiga k'iran Khadeejah a waya, tana d'auka yace "Ina bakin gate Khadeejah, ki fito yanzu", bata fi 5mins ba ta fito tunanin Yayanta duk ya cikata, da kanshi yasa hannu ya bud'e mata k'ofa tana shiga yaja motar, jikinta duk a sanyaye tace "Yaa El ina wuni", amsa mata yayi ba tare da ya kalleta ba tace "Ya jikin Yaa Aj?" ta k'arasa maganan kaman zatayi kuka, saida ya kalleta kamin ya maida kallonshi kan driving din da yakeyi yace "Wajenshi zamu yanzu", bata sake cewa komai, yace "me ya hana ku xuwa?" Hawaye ne ya gangaro mata tace "Abba!" yace "Mumy fa?" Tace "Tana gida" bai kuma cewa komai ba har suka isa asibitin ta biyoshi a baya bayan sun fito motan, shi ya fara shiga d'akin, zaune ya tadda nurses din kan sofa dake d'akin, suna ganinshi suka mik'e ya tambayesu ko sunga wani movement bayan fitanshi suka ce a'a, daga haka ya sallamesu sukayi Waje, Khadeejah da har ta k'arasa gaban gadon idonta cike da hawaye ta durkusa tana kallon yayan nata, kuka ta shiga yi, El-ameen yace "Ba abinda na kira ki kiyi ba kenan" da kyar ta tsaida kukan nata tana share hawayen fuskarta tace "Yaa El wai su waye suka mishi haka, kuma ba a sansu ba?" El-ameen yayi mata assuring murmushi yace "Kiyi mishi addu'a kawai, he will be fine", ta kad'a mishi kai, karasowa yayi ya shiga Examining Junaid yana gamawa ya fita. Wajen hud'u da wani abu Khadeejah na zaune Junaid ya farka, da saurinta ta isa wajenshi ta zauna kan kujera kamar zatayi kuka tace "Yaa Aj ya jikinka?", bai bata amsa ba ya shiga kokarin mikewa xaune yace "Mumy fah?" A hankali tace "tana gida" komawa yyi ya kwanta yace "Humainah?" kai ta kad'a tace "um tana gida", daga haka babu wanda ya sake magana cikinsu, kiran da Hajiya tayi mata yasa ta koma gida ba don ta so ba. Da daddare Junaid na kan gado idanunshi lumshe sai dai ba bacci yake ba shi daya yasan abinda yake ji a lokacin, bude kofar dakin aka yi duk da yana son bude ido amma ya kasa, Humainah ce ta shigo dakin, ta kusa minti biyu tsaye bakin kofar kafin ta karaso a sanyaye ta isa gabanshi ta durk'usa, lkci daya hawaye ya cika Idonta, da kyar ya bude idanunshi ya sauk'e kanta jin motsin mutum kusa dashi, sunkuyar da kanta tayi hawayen da ke makale idonta ya gangaro, ya lumshe ido a hankali ya kamo hannunta ya rik'e cikin nashi dan bazai iya kallonta ba, kuka ta fashe da sosai, cikin sanyin murya yace "Am.. Am sorry, for everything" bata iya ta ce masa komai ba sai kukan da take yana son lallashinta amma ya kasa, bude kofa aka yi El-ameen ya shigo, jim yayi ganinta, can ya karaso ciki tun kan yace komai ta mike ta fice daga dakin da sauri. Washegari da safe junaid na bacci El-ameen ya fita, gidan Aliyu ya nufa yana gama parking a waje ya shiga gidan, bin compound din yayi da kallo ganin bai ga motar Aliyu ba, ya bude kofar parlor ya tsaya yana bin ko ina da kallo, Jasmine ce ta leko daga kitchen tana ganinshi ta fito a guje tayi inda yake ta wara ido tace "Uncle!" Gira ya daga mata yace "Uhmm" bata fuska tayi tace "plsss take me away from here, take me to Captain, kallon stairs yayi yace " Dauko hijab din ki" da sauri ta tafi dauko hijab din, ya fita ta bi bayansa. Asibiti ya koma da ita dan ya gaji da tambayarta da junaid ke jefo masa a ko da yaushe, tana biye da shi a baya suka shiga ward din, idon junaid biyu a lokacin don Dad din El-ameen bai dade da fita ba, ido ya kafe su da har suka karasa shigowa dakin, El-ameen i xamansa kan kujera yana kallonsa, gadon ta nufa tana kallon ruwan hannunsa ta durkusa kusa da shi kamar xata yi kuka tace "Whats wrong with you captain, are you sick?" Kallonta kawai yake kamar bai gane me take nufi ba, ganin bai ce komai ba yasa tace "Aren't you happy am back Captain....? Talk to me plss" hawaye ne ya taru idonta ganin yaki cewa komai still, ta juya tana kallon El-ameen, tabe baki yayi ya mike ya fice daga dakin. kamar jira Junaid yake ya fita yana fita ya fixge drip d'in dake hannunshi ya mik'e tsaye da k'yar, ji yayi jiri na neman k'ada shi hakan yasa ya dafa kanshi ya jingina da bangon, tana ganin haka ta mik'e da sauri tazo gabanshi tana kokarin rik'eshi tace "Captain you didn't tell, are you sick?", makullin motar da El-ameen ya ajiye kan table ya d'auka yace "Let's go" xaro ido tayi tace "You are sick Captain, you can't even stand right lemme call Uncle for you", ganin zata b'ata mishi lokaci ya samu da k'yar yayi regaining balance d'inshi ya jefa mata wani kallo ya kamo hannunta suka fice daga d'akin, haka ya dinga tafiya da k'yar har suka iso gun mota, Jasmine sai ce mishi takeyi "Captain ina xa mu tafi" bai tanka mata ba, ganin yanda yake tafiya tace "Kafar ka ne ke ciwo" motar yasa ta shiga, ya shiga shima ya tada suka bar asibitin, El-ameen da ya fito da sauri dan ya koma d'aki bai gansu ba a kan idonshi motar tabar premises din asibitin, driving kawai Junaid yake ba tare da yasan me yakeyi ba, Roughly yake driving d'in kamar wani mai tseran formular, he just want to take her away, Jasmine na ganin irin driving d'in da yakeyi lokaci d'aya ta rikice ta shiga k'iran sunansa, sosai take ihu da ya rikita Junaid d'in shima lokaci d'aya yayi loosing control d'inshi motar ta kufce daga hannunshi, har lokacin babu abinda jasmeen take banda ihu, rintse ido kawai Junaid yayi dan shima yana jiran hukuncin Allah a kansu, da k'arfi yaji sunyi hitting wani abu da yasa kanshi yin baya, yakai 5mins zaune idonshi rintse, a hankali ya samu ya bud'e idonshi ya sauk'e kan Jasmine, kallonshi kawai takeyi da wasu irin expressions shimfid'e fuskarta, ganin irin kallon da take mishi yasa ya kawo hannu zai tab'ata to check if she is fine, gani yayi tayi Luuu zata fad'a baya yayi maza ya rikota, wani irin skipping heart d'inshi yayi ganin yanda ta sakar masa jiki bata motsi, Sosai ya rud'e ganin suma tayi, bai damu da mutanen da suka tarar mai jikin mota ba don ba ma jin abinda suke cewa yake ba, da k'yar ya samu ya kwantar da ita daga gefe ya shiga k'ok'arin tada motar, Luckily ya samu yayi igniting motar tareda yin reverse, ikon Allah kawai ya maidasu asibitin, ko gama parking baiyi ba ya fito daga cikin motar, jingina yayi jikin motar jin yana neman faduwa, El-ameen dake tsaye har lokacin inda yake cos he was still surprise, ya karaso gun motar yana kallonsa yana son gano abinda yasa ya dawo. Kin ce masa komai Junaid yayi, can ya nufi cikin asibitin ya bar sa nan tsaye, bude motar El-ameen yayi ya ja baya da mamaki ganinta a kwance, bin junaid yayi da kallo kafin ya matso kusa da ita ya kai hannu kan fuskarta breathing d'inta yaji na hitching sama sama, reception ya nufa da sauri sai ga shi da nurses da stretcher, bedroom dinsa na office ya kwantar da ita ya fiddo oxygen bag cikin wani wardrobe daidai bakinta ya jona tube snn ya koma ya kunna socket d'in da Oxygen d'in ke jone, kan sofa El-ameen ya koma ya zauna ya da rik'e kanshi da duka hannayenshi biyu yana jin yanda kan ke sara mishi sbd stress amma bashida strength d'in koda nemawa kanshi magani, mikewa yayi a fusace ya fita nemo junaid, tsaye ya gansa daga waje ya karasa kusa da shi ya fixgosa yace "What happened to her?" Kallonsa kawai Junaid yake da wani expression a fuskarsa don a tunaninsa abu ne ya sameta, turasa yayi ya shiga office din da sauri ya nufi bedroom direct, lumshe ido yayi xuciyarsa na bugawa ya durkusa kusa da ita cikin sanyin murya yace "Am sorry jasmine, am sorry" ya kusa minti uku kafin ya bude ido ya zuba mata yana kallon yadda breathing d'inta ke dawowa dai dai a hankali, duk sai ya nemi ciwon kai da dizziness din da yake ji ya rasa, Shigowa El-ameen yayi dakin yace "Yea ka kasheta kawai kowa ma ya huta Ahmad, just kill her" ko kallonsa junaid bai yi ba idonsa a kanta, a hankali ta bude ido ta sauke kansa, lumshe ido yayi yana hamdala a xuciyarsa, ta kusa minti daya tana kallonsa kafin ta mike zaune da sauri tana bin ko ina na dakin da kallo, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya shi ma, kallon El-ameen ma tayi sannan ta sake kallon junaid, kusa da Ita El-ameen ya dawo ya cire oxygen din yace "Baby are you okay?" Jin bata ce komai ba ya kai hannu xai dafa goshinta ta koma baya da sauri tana masa wani irin kallo, Kallon junaid yayi junaid ma ya kallesa, ta shiga kokarin sauka daga kan gadon junaid ya mike yace "Where are you going to?" Ko kallonsa bata sake yi ba ta nufi kofa da sauri, bin ta junaid yayi ya wani fixgota yace "keee" tana juyowa bai ankara ba sai ji yayi ta sauke masa mari, a hankali ya saketa yana kallonta, ta fashe da kuka ta durkushe wajen tace "Where is this?"
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
70.....
Still junaid yayi yana kallonta ko kiftawa bai yi, El-ameen ya karaso shi ma idonsa a kanta ya durkusa kusa da ita ya dake yace "Why did you slap him?" Mikewa tayi da sauri tace "How dare him touch me, who is he?" Kasa cewa komai El-ameen yayi ya hadiye yawu da kyar ya mike yana kallon junaid da ya kasa daina kallonta, kofa ta nufa El-ameen yayi saurin bin ta yace "Wait! Ina xa ki" kokarin bude kofar take ta kasa, can ta fashe da kuka ta juyo tana kallonsu tace "Where is this plss, me nake yi a nan?" El-ameen ya sauke ajiyar xuciya a hankali ya juya ya kalli junaid, juyawa junaid yayi ya shige bedroom yayi banging kofar, bin bayansa yayi da sauri, junaid ya xauna gefen gado, El-ameen ya karasa kusa da shi yana kallonsa, murmushi ne yayi escaping lips dinsa yace "Frnd it seems ta dawo hankalinta fa, from all indication her memory is back, ohh God! Isn't it amazing frnd?" ko kallonsa junaid bai yi ba, hakan yasa ya hade rai, can ya juya ya fice, jingine ya ganta jikin bango tana bin ko Ina na office din da kallo, tana ganinsa ta fashe da kuka tace "Tell me where is this plss, ina Usman? What are we doing here?" Tausayinta ya ji sosai cikin sanyayyan murya yace "kin ga baki da lafiya ne shi yasa kika ga kan ki a nan, I am Dr El-ameen Umar, i....." Tsaida kukan tayi da sauri tace "Me ya sameni?" Shiru yayi yana kallonta, kallon jikinta ta shiga yi tace "Get me out of here plss, where is my driver?" Rungume hannayensa yayi yace "He went to call ur parent!" Ta buda ido tace "My parent? Stop kidding me pls, where is usman, and???" Langwabar da kai yayi yace "this is katsina! Where are you from" xaro manyan fareren idonta tayi tace "What? Katsina??" Gyada mata kai yayi yace "Yea, sit in gaya maki abinda ya kawo ki nan" wani kallo ta watsa masa Calmly tace "No! Just get me outta here" kallonta yake da expression din da xa a iya kira da na mamaki, is she this rude? Hannunta ta daga tace "Before the count of 5, I want to see me out of here!" Xaro ido yayi yace "If not?" Wani mugun kallo take masa tace "Are you daring me?" Xai yi magana junaid ya fito daga bedroom ya nufi kofar office din ya bude, ya juya yana kallonta fuskar nan tasa a murtuke yace "Get out!" daga sama har kasa take kallonsa tace "Or?" Ji yayi kamar ya kifa mata mari, ya dake yace "I throw you out" wani tsaki me lafiya ta ja tana hararansa tace "Kayi kadan!" Bai san lokacin da ya daga hannu ba sai ji yayi El-ameen ya rikesa yace "meye haka captain! What are you doing" bai jira cewarsa ba ya shige bedroom dashi ya kullo kofar, junaid da tunda yake mace bata samu fuskar da xata yi masa kallon banxa ba ya hade fist dinsa lokaci daya idonsa ya kada, xuciyarsa na bugawa yace "I regret everything Ahmad, a kan wannan brat din nayi ruin din relationship dina da parent dina, is this who she is...." El-ameen ya lumshe ido ya bude yace "No! Consider her plss, never judge a book by just it cover..." Xaunawa junaid yayi ya rike kai xuciyarsa na tafarfasa, El-ameen ya juya ya fito daga dakin, tsaye ya ganta ta wani hade rai, tana ganin El-ameen tace "Did he try slapping me?" El-ameen yace "No he didn't" tace "Good, get me out of here" El-ameen ya ja kujera ya xauna yace "Since you don't want to cooperate, its unfortunate to say, drivern ki da kike tambaya is late, you two had an accident shekaranjiya, and you were unconscious tun lokacin sae yau kika farfado, here is katsina state" kallonsa take da mugun shock, can ta sulale gun tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un....." Ta maimaita hakan yayi sau biyar, can ta fashe da kuka sosai tace "Me muka xo yi katsina..." Mikewa tayi a rude tace "Oh my God, Where is my farida..." Shiru yayi yana kallonta, da gudu ta isa kusa da shi ta kamo hannunsa tace "Plss tell me Dr, where is my sister, my sister...." Kasa cewa komai yayi sai kallonta da yake da tausayi, ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Ka min magana Dr, Ina kanwata" jin yaki cewa komai ta fada kansa tana kuka sosai, dagowa tayi da sauri tana kallonsa kamar me naxari, ta wara ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Dr Ummi fa, where is she, ina take ita?" Dafa shoulder dinta yayi don ya ma rasa amsan da xai bata, ya zaunar da ita yace "Look, sun tafi gida....." Wani kara tayi ta kamo hannunsa tace "Nooo, kar ka ce min haka Dr, we were all together, where is the car...." Kuka ta fashe da sosai, sai a sannan ya fara da ya sanin ce mata drivernta ya rasu, kwantar da murya yayi yace "Kinga sisters dinki are all fine, sun je gida fadi ma parent dinku ne, but if you can't wait for the arrival of ur parent ki gaya mana garin ku sai a kai ki yau din nan" har wani rawa jikinta yake tace "I am from bauchi" yace "Where in bauchi?" Sake hannunsa tayi ta koma baya hawaye na sauko mata tace "idan mun je nasan hanya, plss a kai ni yanxu" shiru yayi yana kallonta, ya daga kai jin an bude kofar bedroom, Junaid ne ya fito bai ko kallesu ba ya nufi kofar ya bude ya fice, El-ameen ya mike da sauri ya bi bayansa, har ya fara sauka stairs ya dafosa yace "Ahmad, she said she's from bauchi" Junaid ya juyo ya dake yace "So?" El-ameen yace "Yaushe xa a maidata gida?" Cire hannunsa yayi daga shoulder dinsa yace "Am going no where!" El-ameen ya buda ido yace "Baka cika ladan ka ba kenan" tafiya ya ci gaba da yi yace "Na bar maka" El-ameen ya bi sa da kallo har ya sauka sannan yace "uhm wnn ne kuma baka isa ba" daga haka ya juya ya koma office, kuka sosai ya sameta tana yi, ya durkusa kusa da ita yace "na fa ce maki yan uwanki na gida" mikewa tayi da sauri tace "Yanxu xa mu tafi plss?" Ya langwabar da kai yace "Ni ban iya tuki ba, wanda ya iya kuma kin maresa, nd you were rude to him, kuma shi ya kawo ki asibitin nan" mikewa tayi da sauri tace "ka kai ni motor park kawai, I will be okay, you help me thank him" daga haka ta nufi kofa da sauri bin bayanta yayi ya sha gabanta yace "Dama ta haka ake biyan good deed baiwar Allah?" Wani kallo tayi masa tace "Toh me yake bukata, money?? or what!"
BN SAMU 71 ba
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
72......
Sakin baki El-ameen yayi yana kallonta, can yace "Can you pay him?" Tace "Yea of course" murmushi yayi ya ma rasa me xai ce mata ya juya ya koma ya xauna, bin bayansa tayi ta hade rai sosai tace "nace ka bude min kofa in fita, let me out pls" girgixa kai yayi yace "I know no where here, wanda kika mara shi ne d'an garin and shi ya kawo ki nan unconscious, he paid for everything pertaining to ur bill and was with you till today that you recovered...." Shiru tayi tana kallonsa, can ta sauke ido a hankali tace "Does that call for his touching me, he touched my body, why did he? he shudnt have...." Shiru tayi can ta dafe kanta tace "Ohk am, I am sorry, I.. I am sorry" taso wa yayi yace "Very good of you, yanxu dole sai mun je gidansu ki basa hakuri sannan sai ya maida ki gida koh" shiru tayi can ta turo baki tace "Do I have to?" Yace "Of course yes!" A hankali tace "But he's so rude" dariya ta basa yace "And you were rude to him also!" Girgixa kai tayi tace "No I wasn't" xai yi magana aka kwankwasa kofa, mikewa yayi ya kalleta ya nuna mata kujera yace "Sit, let me check who's at the door" ba musu ta xauna, ya karasa gun kofar ya bude, wata nurse ce tsaye tace "Good morning sir, ur attention is being needed...." Yace "Alryt, ohk" daga haka ya rufe kofar ya dawo yana kallonta yace "Ohk, Ya sunan ki?" Da kamar baxata ce komai ba, sai kuma ta d'an kallesa a takaice tace "Zahrah!" Buda ido yayi yana murmushi yace "Ohk Zahra, you wait for me here, xanje in yi attending ma patient downstairs, yanxun nan xan dawo sai mu je ki ba captain hakuri mu maida ki gida!" Tace "Who's that?" Wara ido yayi yace "Ur helper" ajiyar xuciya ta sauke tace "Ohk, make it fast plss ina son ganin sisters dina, and am feeling heat in here" gyada mata kai yayi yana murmushi ya kara Ac dake office din ya nufi kofar ya fita ya kullo daga waje, tana nan xaune office din har bayan kusan awa daya duk ta kagu ya dawo bini bini xata kalli agogo, can ta mike ta nufi kofa ta murda ta ji a rufe ji tayi kamar ta rusa ihu ga shi hankalinta yaki kwanciya, kuka ta saki daga karshe ta koma ta xauna, bude office din taji ana yi ta mike da sauri wata nurse ta shigo rike da ledan eatry, karasowa tayi ta ajiye ledan tace "Dr yace a kawo maki abinci" da sauri tace "Where is he?" Nurse din tace "He's at the theatre, but ya kusa fitowa" daga haka ta juya ta fita ta bi ta da kallo, komawa tayi a sanyaye ta xauna, junaid ne ya fado mata, ta turo baki tace "He started everything, he's just rude" ledan abincin ta dauka ta bude ta tsura ma fried rice da naman ido, girgixa kai tayi coz bata cin abinci ba na gidansu ba, mayarwa tayi ta rufe, gajiya tayi da xama ta jinginar da kanta jikin kujera lokaci daya bacci ya dauketa, sha biyu saura El-ameen ya shigo office din, kallonta ya tsaya yi daga bakin kofa can ya karaso ya iso gabanta ya durkusa yana kallon kyakkyawan fuskarta, jasmine d'in then yake tunawa yayi murmushi yana naxarin yanda xata dauki labarin abinda ya sameta, da kamar ya tasheta ta gyara kwanciya sai kuma ya fasa don kar ta basa nasa tsaraban marin, he will just like to know who she is da take da tsiwa haka. Mikewa yayi ya shiga bedroom don yin wanka. Ko da ya fito daga dakin masallaci ya fita yin sllhn Azahar, yana dawowa ya sameta har lokacin tana bacci, kujerar ya shiga bugawa a hankali ta bude ido da sauri ya koma baya yace "Amm tashi kiyi sllh" gyara xaman ta tayi tana masa wani kallo tace "You kept me waiting" yace "Sorry plss" mikewa tayi ya nuna mata daki yace "Akwai toilet a ciki" bata ce komai ba ta shiga bedroom din, ba a dau lokaci ba ta fito yace "me yasa baki ci abincin fa?" Girgixa kai tayi tace "Abincin gidanmu kawai nake ci" xaro ido yayi yana kallonta, sosai ta basa dariya sai dai ya dake bai yi ba, kallon jikinta tayi tace "But..." Sai kuma tayi shiru, yace "But what?" A hankali tace "Ba kayan nan ne jikina ba" murmushi yayi yace "Yea, nurses ne suka canxa maki, you have being here for three dayz," kan ta ce komai ya mike da sauri ya dauko hijab dinta dake daki ya mika mata, karba tayi ya shimfida mata darduma tace "Idan na gama xa mu wuce koh?" Kai ya gyada mata, ta hau darduman ta tada sllh, kallonta kawai yake har ta idar, ta jima xaune kan darduman kafin ta mike ta dauke tana kallonsa tace "Na gama" mikewa yayi ya mika mata makullin motarsa yace "Go out, look for parking space and wait for me there" karba tayi ta fita, bayan kusan minti biyar ya bi bayanta, tsaye ya ganta a gun ya karasa ya karba makullin sannan ya nufi gun motarsa tana biye da shi, front seat ta bude ta shiga bayan ya tada motar, cikin minti sha biyar suka isa gidan junaid, kallonta yayi xai yi magana tace "Call him fast plss" buda ido yayi yace "No, we are going in" hade rai tayi tace "No ni baxan shiga ba," kallonta ya tsaya yi yace "Why?" Tace "I just can't, pls ni dai ka taimaka ka ban kudin transport in fita in nemi park idan naje gida in'sha Allah I am sending you back ur money, give me ur account number" xaro ido tayi tace "Ohh My phone??" Lokaci daya ya ji ransa ya baci, ya tsura mata ido yana kallo, how can she be this rude, who is she da xata dinga fadin kudi haka, cire glass din idonsa yayi yace "Amma hakan bai dace da ke ba Zahrah...." Wani kallo ta watsa masa tace "I just want to be home" bude motar yayi ya fice ya bar ta, bin sa tayi da kallo can ta bude motar ta fita ta bi bayansa, a hankali ya murda kofar parlon ya shiga, kwance ya ga junaid kan doguwar kujera idonsa lumshe, ya juya ya kalleta ya ga ita ma leko sa take, karasawa yayi parlon ta bi bayansa, dukawa yayi kusa da shi yana kallonsa, lokaci daya ya bude idonsa da ya kada yana kallonsa, El-ameen yace "Sleeping?" Bai jira cewarsa ba ya dafa kansa ya ji xafi, mikewa xaune junaid yayi ya rike kansa cikin sanyin murya yace "I regret everything frnd, you told me this from the very beginning, I..." El-ameen yace "Don't say that man, One never knows where his or her reward lies...." Girgixa kai junaid yayi xuciyarsa na bugawa yace "Allah am regretting" Zahrah da ke tsaye daga bakin kofa ta karaso cikin parlon kamar me tausayin kasa, kallonta El-ameen yayi don yasan junaid bai san tare suke ba, durkusawa tayi d'an nesa da su tana kallon Junaid, cikin sanyayyan muryarta tace "I..i am sorry!" Dago kai yayi da sauri yana kallonta, ta sunkuyar dai kai tace "Kayi hakuri, but you started it 1st" wani kallo ya jefa mata, ta turo baki ta mike tana kallon El-ameen tace "Is that all?" Murmushi El-ameen yayi yace "toh bai ji abinda kika ce ba" Kallon junaid tayi tace "I said am sorry" da kamar baxai ce komai ba, sai kuma ya mike yace "Sorry for ur self" daga haka ya nufi stairs, xaro ido tayi ta bi sa da kallo har ya haura sama, ta kalli El-ameen tace "You see! He's just rude" murmushi El-ameen yayi yace "And you too!" Tabe baki tayi tace "Dan Allah ka kai ni park xan gane hanya" kamar xata yi kuka ta kare maganar, El-ameen yace "Ohk, xauna ina xuwa" sama ya tafi, ta dinga bin parlon da kallo, babban hotonsa dake manne parlon yana sanye da uniform hannunsa rike da hula ta tsura ma ido, can ta karasa gun hoton tana kallo kamar me naxari, Tsaye El-ameen ya same junaid a daki yace "Look junaid Kaga dai ta baka hakuri, plss ka sa lokacin da xa ka kaita gida I will escort you" girgixa kai yayi yace "Ni babu inda xan je" hade rai El-ameen yayi yace "Stop this Malam, it's ur responsibility naga...." Xaunawa junaid yayi yace "Leave me plss Ahmad, am going no where, ka bar ni in fara tunanin yanda xan gyara duk abinda na bata a kan yarinyar nan, you can take her home frnd duk daya ne" tausayinsa El-ameen ya ji, bai kuma cewa komai ba ya juya ya fita, tsaye ya ganta bakin kofa ta wani hade rai, El-ameen bai kalleta ba ya fita ta bi bayansa, suna tafiya tace "baxai kai ni gidan ba koh?" El-ameen yace "Yess" tsaki tayi tace "Da na sani baxan xo basa hakurin bama" El-ameen bai tanka ta ba ya shiga mota ita ma ta shiga, sai da suka kama hanya sannan tace "Toh ina xa mu yanxu" bai kulata ba har ya iso gidansa, parking yayi ya fita ita ma ta fito a fusace tace "What's this please" da kamar baxai ce komai ba sai kuma ya kalleta yace "sai na shirya xan tafi dake ai koh? I have to fuel my car and put things in order, so dole sai na xo gida" tace "Ohk" cikin gidan ya nufa ta bi sa, Hafsat na kitchen jin shigowarsu parlor ta fito, Sannu da xuwa tayi masa ya amsa ya tafi sama, ta karasa kusa da Zahrah tana murmushi tace "Welcome Jewel" kallonta kawai Zahrah take irin kallon mamakin nan da yayi kama da na rainin hankali, still Hafsat tayi tana kallonta, El-ameen ya sauko yace "Hey, Meet my wife Hafsat!" Murmushi Zahrah tayi tace "Ohh sorry, it's nyc meeting you sis Hafsat!" Kasa cewa komai Hafsat tayi El-ameen yayi murmushi yace mata xa muyi waya anjima, daga haka ya fita Zahrah tace ma Hafsat sai anjima ta fita ita ma. Sai da suka dau hanya tace "Why was she staring at me that way?" Da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Coz you look new to her, and perhaps rude" xaro ido tayi tace "Did she know me before?" Gyada mata kai yayi yace "Yeah" tabe baki tayi ta maida kanta jikin kujera tace "I've never come across a being like her all my life" murmushi yayi ya kalli agogon hannunsa yaga daya da wani abu, yace "Kika ce bauchi koh?" Kai ta gyada masa yace "Where in bauchi?" Ta kada kai tace "Idan mun je xan gane hanya" bai kuma cewa komai ba ya dau wayarsa yayi dialing number Dad dinsa yana dagawa yace masa xai d'an je Kano wani aiki ya dawo, suna gama waya ya kira Ummi ma ya gaya mata haka, ajiye wayar yayi ya maida hankalinsa kan driving din da yake, ba su yi nisa da fara tafiya ba tace "Am Hungry!" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ke da baki cin abinci idan ba na gidan ku ba" tace "Ohh yes, soft drink kawai nake so yanxu" murmushi yayi yace "Toh shi daga gidan ku aka yo shi kenan" bata kuma ce masa komai ba, yayi parking ya fita wani shopping mall ya siyo mata drink da snack, karba tayi tace "Thank you" karfe hudu saura suka shigo Kano, ya kalleta yace "Where is this?" Bude hannu tayi alamar bata sani ba, yace "Kano!" Ana kiraye kirayen isha suka shigo bauchi, yace "kin san ina ne nan?" Gyada masa kai tayi yace "Toh mun yi sauri ko ba mu yi ba?" Hannu ta buda masa alamar bata sani ba, yace "Uhm to wani anguwa ku ke?" Tace "Kawai ka dinga tafiya xan dinga nuna maka" yace "Ohk"
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
73.....
A bangaren Junaid kuwa suna barin gidan yayi kwanciyarsa, duk ya rasa me ke masa dadi, har magrib yana daki ga wani xaxxabi da yake ji, sllh yayi ya dau makullin motarsa ya fita, gida ya nufa duk jikinsa a sanyaye, he regret ever meeting her, he regret helping her, he regret all that have happened, parking yayi kofar gidan ya kasa fitowa, ya hade kansa da steering, ya kusa minti sha biyar kafin ya fito jiki ba kwari ya shiga compound din, tafiya yake kamar bai son yi don bai ma san me xai fara ce ma Mumynsa ba, bai san ta inda xai fara ba, why did all this happen to him? Shi kuma irin tasa kaddarar kenan, shafa kansa yayi ranan da ya fara ganin Zahrah ya fado masa, murmushin takaici yayi, yayi saurin kauda tunanin, ido hudu yayi da Hadiza da ke tsaye sakale da jakarta alamar tafiya xata yi ga nikab a hannunta, Umma da Hajiya ma na tsaye balcony din, suna hangosa Umma tayi mata alamar da ta shiga parlor, da sauri ta shiga ta kullo kofa, girgixa Kai yayi nufi balcony din, Umma da Hajiya aka kafa masa ido da mamaki don a tunanin su gaishesu xai xo yi, ko kallonsu bai yi ba ya bude kofar ya shige parlon, Hajiya ta xaro ido tace "Ikon Allah Meye haka Ahmad?" Hadiza dake tsaye parlon ta xaro ido ganinsa, bai yi wata wata ba ya fincikota ya kai mata naushi a baki, wani kara tayi Umma da Hajiya da tuni suka shigo parlon suka shiga salati suna tambayar yana da hankali kuwa, ko sauraransu bai yi ba ya fixgota ya fito da ita tsakar gidan, dukanta ya shiga yi yana ball da ita kamar an aikosa, ta dinga ihu tana cewa a taimaketa, tuni 'yan matan gidan suka fiffito, Mumy ma ta fito, su Hajjo da aka diro daxu ma aka fito, Hajiya da ko ina na jikinta rawa yake ta dinga jan Junaid murya can kasa tana cewa "In ma laifi tayi maka kayi hakuri Ahmad.... Ka rufa mata asiri" ko saurarenta bai yi ba bugunta kawai yake kamar an aikosa, a fusace Hajja ta karaso ta fixgoxa ta sauke masa mari tace "Don uwar ka Amina dama shirin tafiya gidan ka nake yanxu, ban taba tunanin cewar da mahaukaci Muhammadu xai hada jikata ba, ita Humainahr ka sakar min, tsabar haukan naka ya girmama har gida kake xuwa jibgan mutane yanxu" kokarin gudu Hadiza take ya wani fixgota ya kuma sauke mata mari, Abba ne ya shigo compound din daga masallaci, ya tsaya da mamaki yana kallon tsakar gidan, Junaid da ban da tafasa babu abinda xuciyarsa yake ya fara waige waigen inda xai ga Humainah, ganin bata compound din ya ja Hadiza har part din Mumy duk aka bi sa da ido ya shiga har parlor da ita, salati Umma ta dinga yi tana cewa anya Ahmad lafiyarsa kuwa, ku ceci 'yar mutane don Allah, fitowar Humainah kenan daga daki ya jefar mata da Hadiza nan gabanta yana kallonta sannan ya juya ya fice daga parlon, kallon mamaki Humainah ke mata, tuni duk aka shigo parlon, Abba kam dama part dinsa kawai ya nufa, Hadiza da ko ina na jikinta rawa yake ta mike da sauri xata fita, Humainah ta rikota tace "Me ya kawo ki nan?" Juyawa tayi tana waigen inda xata ga su Umma, Hajjo tace "Ina kika santa?" Hawaye ne ya cika idonta tace "Ita ta ja min komai, ni ban santa ba...." Hajjo tace "yo ni daxu tare muka shigo gidan nan da ita, ita ce ma ta shigo min da kayana daga adai daita kuma tace min Ita 'yar wan Bilki ce, me ta maki?" Kuka sosai Humainah ta fara ta durkushe gun tace "Ita ce silar komai, ita ke xuwa gidana kullum...." Salati Hajja ta saki tace "Ita ta sa ya sake ki kenan?" Humainah ta gyada kai hawaye na sauko mata, Hajja ta cakumo Hadiza tace "Ni dama nasan ba yin kan jikana bane wannan, nasan baxai aikata haka a banxa ba, to ko ki fadi wanda ke tura ki gidan ta ko in xuba maki fetur yanxu in babbakaki" juyawa Umma tayi ta fice daga parlon Hajiya ta bi bayanta da sauri, Hajja ta kwada mata mari tace "Baxa kiyi magana ba" Mumy da duk jikinta yayi sanyi ta karaso tace "Ki yi hakuri Hajja ki sake ta...." Wani kallo Hajja ta watsa mata tace "Ke ja can dalla" shaketa Hajja ta yi tace "Baxa kiyi magana ba?" Hadiza ta fashe da kuka tace "Ni Umma ce da Hajiya suke tura ni" salati Hajja ta saki tace "Suke tura ki kije kiyi me?" Shiru Hadiza tayi Hajja ta ja ta xuwa gun tv tana neman wayar wuta tace "Toh xa ki ga ikon Allah idan ba ki bude baki kin ban labari ba" juyawa Humainah tayi hawaye na bin kuncinta ta koma daki, Hadiza da tayi mugun tsorata jikinta na rawa tana hawaye tace "Wllh tura ni suke in je in dinga xugata" Hajja ta saketa tana tafa hannu tace "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, dama su suka kashe ma jikata aure, to su ma na su na rawa yanxu, ina Muhammadu" daga haka ta fice daga parlon kamar xata tashi, jigum Mumy tayi tana kallon Hadiza dake ta waige waige kamar munafuka, can kuma ta fice da gudu daga parlon. Tafiya kawai El-ameen ke yi a hankali, haka kawai gabansa ke faduwa ganin anguwar da ta nuna masa wai nan xa su bi, tafiya me nisa suka yi tace "Here!" Juyawa yayi da sauri yana kallonta yace "Where?" Nuna masa babban entrance din tayi tana bin ko ina da kallo ganin canji da dama tace "there!" Kasa daina kallonta yayi tace "Just horn, sai ka sauke glass xan masu magana" girgixa kai yayi yace "Wai gidan sarautan nan?" Kallonsa ta tsaya yi kafin tace "Eh gidanmu ne!" Dauke kai yayi can ya juyo yace "Kina nufin ur father is a king?" Bude motar ta shiga kokarin yi tace "Yeah my father is a king" danna horn yayi kamar yanda tace har lokacin idonsa na kanta, ita ko sai kalle kalle take fuskarta dauke da mamaki ganin changes da dama, wasu dogarai ne suka fito suna kallon motar, karasowa suka yi ta sauke glass tana kallonsu, ganin bata gane ko daya daga cikinsu ba ta bude motar ta fito tace "Ku bude mana hanya" daya daga cikinsu yace "Daga ina?" Fitowa El-ameen yayi yace "Baki daga katsina" bude masu hanyar aka yi, ya koma mota ita ma haka, ya ja motar ya shiga ciki, tafiya mai tsayi suka yi kafin su kai wani gate, kallon El-ameen tayi kamar xata yi magana sai kuma ta fasa, wasu guards suka karaso gun motar, sauke glass tayi daya daga cikinsu yace "Daga ina?" kallonsa kawai take don shi ma bata san sa ba, toh yaushe aka canxa guards din bakin gate kuma, a takaice tace "Bude mana gate" El-ameen yace "Sorry, baki daga katsina, mai martaba na sane da xuwan mu" komawa yayi aka bude gate din ya ja motar xuwa babban haraban palace din, juyowa tayi da sauri ta kallesa tace "Everywhere looks strange" kashe motar yayi yace "How strange" a hankali tace "Naga changes da yawa ne"
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
74.....
Bude motar tayi ta sauka, shi ma ya sauko, har ta nufi kofar shiga fada sai kuma ta juyo tana kallonsa tace "Ni xan bi ta baya, may be Abbana na tare da baki, you follow there" girgixa kai yayi yace "No i will wait out here" tabe baki tayi ta juya ta dau wata hanyar daban ya bi ta da ido har ta bace masa, ajiyar xuciya ya sauke ya koma can inda wasu bishiya ke a jere ya ja daya daga fararen kujerun dake gun ya xauna, wayarsa ya ciro ya shiga kiran layin Junaid, bugu uku ya daga, El-ameen yace "Amm muna bauchi Man" Junaid dake xaune laptop gabansa yace "Ohk, it's good" Shiru El-ameen yayi kafin yace "Guess what frnd?" ajiye laptop din yyi a gefensa yace "Not in the mood" Murmushi El-ameen yayi yace "Ohk Gudnyt" katse wayar junaid ya jefar da wayar hannunsa ya mike ya fice daga dakin. A hankali Zahrah ta tura kofar ta shiga babban parlon da nan ne masaukin manyan baki a fadan, bbu kowa parlon, ta dinga bin parlon da kallo ganin shi ma ya canxa mata, hanyar da xai sada ta da bangaren Ummanta ta nufa da sauri, lokaci daya taji gabanta na faduwa, jakadiyar Umma ce mutum ta farko da ta fara haduwa da a hanya, wara manyan idonta tayi ta karasa da sauri tace "Baaba na dawo, ina ummana, ina su Ummi.....!" Wani kara jakadiyar tayi a gigice ta saki kayan hannunta ta juya da gudu ta bar gun tana salati, still Zahrah tayi ta bi ta da kallon mamaki, kan kace me sai ga ma'aikatan fadan sun bubbullo jin ihun jakadiya, sai dai duk wanda yayi tozali da ita sai ya bar gun a guje, duk ko ina ya hargitse, ita dai tana tsaye kamar warce aka dasa a gun cike da mamaki, a hankali ta shiga bin jikinta da kallo ko wani abu ne jikin nata, bata gama recover ba sai da yayanta ya shigo parlon taga yana mata wani kallo, da sauri ta nufesa ta ga ya juya ya bar gun, sosai jikinta yayi sanyi ta ji kafafuwanta sun kasa daukarta, Umma ce ta fito da stepmum dinta, sai dai ga mugun mamakinta sai gani tayi ita duk sun yi still a position dinsu suna kallonta ko kiftawa babu, Ummi ce ta shigo ita ma suna ido hudu ta fasa wani kara a rikice ta juya da gudu ta bar gun, juyawa Zahrah tayi da sauri hawaye cike idonta ta fita da gudu, a hankali Umma ta sulale gun ta fadi kasa a sume, rikicewa jakadiyar ta da sauran ma'aikatan dake gun suka yi suka yo kanta, Zahrah na fita dama inda ta hango El-ameen ta nufa tana isa gunsa ta xube gun ta fashe da kuka sosai tace "Why is everybody running away from me, mene a jikina da suke gudu plss tell me" shiru yayi yana kallonta, sai ya ji tausayinta, a hankali yace "Bbu abinda ke jikin ki, they are just surprise ne...." Girgixa kai tayi cikin kuka tace "Noo, what are they surprise at, do I look new? Tell me plss, dukkansu guduna suke yi" lumshe ido yayi yace "Kila basu yi xaton ganin ki yanxu bane" buda ido tayi tace "Why is that?" Takun da suka ji yasa su juyawa gaba daya, Mai martaba ne tafe da dogaransa a baya, mikewa tayi da sauri ta nufesa da sauri tace "Abba!" Kallonta kawae yake, ta fashe da kuka ta tafi da gudu ta rungumesa cikin kuka tace "Abba ni ce pa Fatima" daura fuskarsa yayi a kanta cikin sanyin murya yace "Fatima!" Rungumesa tayi sosai, hawaye na sakko mata tace "Abba kila su Umma basu gane ni bane koh?" Kasa ce mata komai yayi, El-ameen dai sai kallonsa yake yaji tausayinsa ba kadan ba, dago kai sarkin yayi yana kallonsa, mikewa yayi ya karasa inda suke ya sunkuyar da kai yace "Barka dai mai martaba, ga Zahrah na maido gida, Allah ya kiyaye gaba" kallonsa kawai sarkin yake, El-ameen yace "Na bar ku lafiya" juyawa Zahrah tayi tana kallonsa, Sarki ya taka ya isa har gabansa, hannunsa ya kama ya nufi fada da shi, tsaye duk occupant din masauratan suke ko wanne a tsorace, Mai martaba da har lokacin bai sake El-ameen ba ya nufi babban parlonsa da shi, Zahrah dai na biye da shi a baya kamar xata shige jikinsa ganin wani kallo da ake mata duk inda suka wuce, xaunawa sarki yayi ya nuna ma El-ameen kujera ya xauna, ya kusa minti biyar bai ce komai ba, Zahrah dake xaune kusa da Abban ta sai jiran jin me xai ce take, hawaye ne ya sakko idonta tunawa da tayi da irin kallon da ake mata, ta daura kanta kan kafar Abban nata muryarta na rawa tace "Abba na canxa ne wai, me yasa ake guduna?" Da kyar me martaba ya saita kansa, yana rike da hannunta yace "Baki canja ba mamata" kallon El-ameen yayi yace "Bawan Allah, a ina ka ga Fatima?" Shiru El-ameen yayi kamar baxae ce komai ba, sarki dai sai kallonsa yake, sunkuyar da kai yayi yace "Bani na ganta ba ranka ya dade...." Sarki yace "Waye shi?" Dago kai yayi yace "Aminina ne, shi ne silar komai" Sarki yace "Kana da masaniyar inda ya ganta, kuma yana ina?" El-ameen yace "Ehh nasan inda ya ganta, yana katsina yanxu haka,!" Sarki yace "Ina ya ganta" kallonta El-ameen yayi yaga yanda ta kafa masa ido tana jiran jin me xai ce, lumshe ido yayi ya bude ya kalli Sarkin yace "Tana da matsala ne a lokacin" sarkin yace "Wani irin matsala?" El-ameen yace "Ehh toh, A lokacin ta samu matsalar kwakwalwa" mikewa tayi tana kallon El-ameen, sarkin ma kallonsa yake ko kiftawa bai yi, da kyar yace "Matsalar kwakwalwa?" El-ameen ya gyada kai yace "ehh, Ban mancewa dawowarsa Egypt kenan ya taso xae xo guna da yamma ya ganta gefen titi a halin Hauka....." Labarin yanda Junaid ya ganta, da irin tausayinta da yaji El-ameen ya shiga ba sarkin, bai boye masa komai ba har lokacin da junaid din ya nemi shi ma ya taimaka ya nuna shi bbu ruwansa, da yanda dai ya amince daga karshe, kuma bbu abinda ya rage tun daga hidimar da Junaid yayi da ita na Magani abinci sutura, nemo me kula da ita da yayi, har da irin matsalar da ya shiga gun iyayensa ta dalilin ta, da challenges din rayuwa da ya dinga fuskanta, duk da haka kuma bai taba gujenta ba, bai kuma fasa yi mata duk abubuwan da ya dace ba, har gidansu da ya kaita da niyar aurenta lokacin da iyayensa suka takurasa yayi aure, da dai yanda abubuwa suka gudana a lokacin, hatsarin da suka yi da ya maido mata da hankali sai dai kuma tayi loosing memory, da aurensa da Humainah da sakinta da yayi kan Zahrahn, kai bbu abinda ya boye ma sarkin har xuwansu bauchi sai dai bai fadi tijaran da Zaharar tayi masa ba, rike kai sarkin yayi don tuni idonsa ya canxa launi, Zahrah kam hawaye ne kawai ke saukowa idonta jikinta yayi mugun sanyi, tuni ta kasa ci gaba da tsayuwa ta durkushe wajen ta fashe da kuka sosai, da kyar sarkin ya iya dago kansa daga karshe, ya goge idonsa da Handkerchief din hannunsa cike da karfin hali yace "Shekara daya da watanni biyar kenan rabon mu da fatima, tun da suka yi hatsari a hanyar Kano, and....." Kasa ci gaba yayi ya mike yace "Gobe da safe xa mu tafi katsinan" daga haka ya dau hanyar da xai sada sa da Bedroom dinsa, kallon El-ameen kawae take, can ta mike a hankali ta isa gabansa ta durkusa wasu sabbin hawayen na sauko mata cikin sanyin murya tace "Will he ever forgive me?" Kallonta El-ameen yake, yayi murmushi bai ce komai ba, ta fashe da kuka sosai tace "Don Allah ka gaya min xae iya yafe min....." Saukowa El-ameen yayi yace "He will in'sha Allah" tana share hawayen da ya ki tsaya mata tace "toh Meye sunansa?" Yana kallon kwayar idonta yace *Captain Ahmad Junaid* a hankali tace "Ahmad Junaid" gyada mata kai yayi yana murmushi ta sauke idonta kasa.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
75.....
Washegari da ya kasance litinin misalin karfe takwas na safe Zahrah ta fito daga part din mai martaba bayan ya bata umarnin da ta tafi ta gaida Ummanta da stepmum dinta kilishi, bata yarda ta kwana ko ina ba sai gun sa tunda shi kadai ne bai gujeta ba, kuma ga bakin da suka dinga tururuwan xuwa ganinta tun a daren jiyan hakan yasa tayi xamanta gun Abbanta, a nan part din nasa tayi shiryawarta ta saka kayan da jakadiyar Umma ta kawo mata da safen, bangaren Ummanta ta nufa fuskarta rufe da hular alkyabbar jikinta don bata son kallon da ake mata, xuciyarta fal tunanin Junaid ta dinga tafiya a hankali, ta rasa dalilin da ya tsaya mata a rai haka, har mafarkinsa sae da tayi daren jiya, gashi ko ganesa ta tabbatar baxa tayi a hanya ba da xa su hadu, bata damu da mutanen da ta dinga wucewa ba wasu na gaisheta wasu na mata sannu da xuwa har ta iso bangaren Umma, xaune ta sameta parlor ga baki da dama xaxxaune parlon, da ganinta kasan har lokacin bata yi recover daga shock din jiya ba, a sanyaye Zahrah ta karasa har tsakar parlon ta duka ta gaida mutanen dake ta kallonta ko wannensu ya amsa mata cike da fara'a, karasawa tayi gaban Ummanta ita ma ta gaisheta, amsa mata tayi cikin sanyin murya tana kallonta, kasa ci gaba da tsayawa gun Zahrah tayi, ganin Umma taki sakewa da ita, ta mike kawai ta fice hawaye cike idonta, bangaren Kilishi ta nufa nan ma baki ta samu fal a parlon, ba laifi kilishi ta ja ta jikinta hawaye na sakko mata tace "Sannu Zahrah, Allah ubangiji ya kara mana tsawon rai mai amfani...." Rungumeta Zahrah tayi tana kuka, nan ta dinga lallashinta tace "Gode ma Allah xatayi da bawan Allahn da ta dalilin sa ta dawo gida yanxu" jikinta ya kuma yin sanyi sosai ta ji banda taga junaid bbu abinda ke damunta yanxu, mikewa tayi tana share hawayen ta, Ummi ta gani tsaye ita ma tana hawayen, da sauri ummin ta karaso ta rungumeta tace "I missed you sweet sis...." Zahrah bata iya cewa komai ba sae hawaye, janye jikinta tayi ta fita daga parlon, a hanya ta hadu da yayanta tana ganinsa xata canxa hanya ya janyota ya rungumeta, rufe fuskarta tayi a kirjinsa, a sanyaye yace "Welcome back Lil sis, ba gudun ki muke ba, it's just....." Girgixa kai yayi lokaci daya idonsa ya kada yace "We missed you Zahrah" bata iya ta ce komai ba sai kai da ta gyada masa kawai, yace "Baki je gun bakon da ku ka xo tare ba" goge fuskarta tayi tace "yanxu xan je" saketa yayi yace "Yea ki tafi yanxu, nima daga can nake" gyada masa kai tayi ta nufi bangaren saukan baki inda El-ameen yake, Xaune ta gansa parlor yana waya, ta nemi gefe ta xauna sai kallonsa take, yana gama wayar tayi saurin dauke idonta daga kansa, ya d'an bude ido yace "Good morning princess" d'an murmushi tayi tace "Good morning" yana murmushin shi ma yace "How you!" Ba tare da ta kallesa ba tace "Am good," yace 'Happy to be home ryt?" Lumshe ido tayi ta bude ta gyada masa kai, yace "My wife said I shud send her regards" kallonsa tayi tana murmushi tace "Am grateful" yace "In the next 1hr xa mu kama hanyar katsina" da sauri tace "Amma ai da ni xa a je koh?" Yace "No I don't think so...." Bata fuska tayi tace "Nima nace xan je" dariya yayi yace "Ohk ohk!" Shiru tayi sai kuma tace "Nuna min hoton matar ka" da mamaki ya kalleta yace "Really" bai jira cewarta ba ya dauko wayarsa ya bude ya shiga gallery ya nemo hoton Hafsat ya mika mata, mikewa tayi ta karasa kusa da shi ta karbi wayar ta dawo ta xauna, kallonta kawai take sannan ta kallesa tace "She's... She's beautiful!" Murmushi yayi yace "Ohh tnxx" kallon hotunan ta shiga yi, can ta mike da sauri tace "Ohh this is me" mikewa yayi ya koma kusa da ita yana kallon wayar ya ga hoto ne da yayi masu ita da Hafsat, gyada mata kai yayi yace "Yea, ke da Hafsat" a sanyaye ta ci gaba da kallon hotunan taga duk hotunanta ya fi yawa a wayar, ajiye wayar tayi ta koma ta xauna ta lumshe ido, yana kallonta yace "What?" Bude ido tayi ta girgixa masa kai cikin sanyin murya tace "Have you taken breakfast?" Gyada mata kai yayi yace "Yea" bata kuma cewa komai ba can kuma tace "Ban san sunanka ba!" Wara ido yayi yace "I am El-ameen Ahmad..." Gyada kai tayi tace "You have the name of my dad" murmushi yayi yana kallonta, ta mike tace "Xan je gun Abba yanxu" bin ta yayi da kallo har ta fita. Karfe goma saura sarki da tawagarsa suka shirya tsaf domin tafiya kt, shiga ce yayi na alfarma irin ta sarauta, da farko bai amince Zahrah ta bi su ba sbda b'akin dake ta xuwa masarautan dominta amma yayanta na sa baki sarki ya amince su je tare, don har da shi xa'a, rungume yayan nata tayi tace "Thanks bro" Ummanta ta tafi tayi ma sallama sai a sannan Umma ta rungume 'yar tata ta fashe da kuka, jikin Zahrah yayi sanyi ita ma hawayen ya shiga sakko mata da kyar ta fita daga dakin ta je yi ma step mum dinta sallama, Ummi ta gani ita ma ta shirya tsaf, Ummi na ganinta tace "Zahrah tare xa mu je fah" Kilishi ta kalleta tace "Mai martaba ne yace tare xa ku" bata fuska tayi tace "Yanxu xanje in gaya masa, Mumy bana son ta kara tafiya ita kadai ne...." Kilishi tayi murmushi tace "Toh Allah yasa ya amince" daga haka Ummi ta kama hannun 'yar uwar tata suka fita, basu sha wahalan shawo kan Abbansu ba ya amince xa ta bi su, motoci biyar ne xa a tafi katsinan da, mai martaba kuma flight xai bi da Zahrah da El-ameen da Ummi, Abdul kuma xae bi tawagar Abbansa ta mota sai su hade a masarautan kano daga can kuma su dau hanyar katsina.
Karfe daya motocin tawagar sarki El-ameen suka iso masarautan Kano, ko minti talatin basu kara a Kano ba suka dau hanyar katsina, Zahrah da Ummi suka shiga mota daya da Mahaifinsu, El-ameen bai yarda ya shiga motar sarki da ya sa masa takwara ba ya hau motar gaba, uku da wani abu suka shiga garin kt, duk da El-ameen ya san ba lallai junaid na gidansu ba, can ya sa suka nufa gaba daya, hudu da minti goma suka iso kofar gidansu Junaid, El-ameen ne ya fara fitowa, sannan dogarawan sarki, kafin sarki ma ya fito tare da aminansa, Sarki na kallon El-ameen yace "Masallaci mafi kusa, xa muyi la'asar!" Masallacin kofar gidan ya shiga da su bayan sun daura alwala, su Zahrah dai na mota a xaune, hudu da minti ashirin duk suka fiffito daga mosque din, Sarki yace "Shiga kayi mana sallama da masu gidan, El-ameen ya shiga compound din, bbu kowa tsakar gidan sai Khadija dake xaune balcony din Mumy, ya karasa har inda take, ta gaishesa da fara'ar yake, amsa kafin yace "junaid fa?" Ta girgixa kai tace "yana can gidansa!" Yace "Abba fah?" Ta kalli bangaren Abba tace "Yana ciki, amma yana da baki" El-ameen yace "Su waye?" Tace "Hajja na ciki, kawu Abbakar ma na ciki sai Abokansa biyu" ya d'an bude ido yace "Meeting din me ake" shiru tayi bata ce komai ba, a hankali yace "Junaid koh?" Gyada masa kai tayi, yace "Su Hajiya fah?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Mumy fa?" Kallon kofar parlon tayi tace "Tana ciki" yace "Ohk pls ki gaya min taron me ake a parlon" ta tabe baki tace "Humainah ce ta gaya ma Hajja abinda ya sa ya saketa daxu da safe" El-ameen ya d'an bude ido yace "Ta basu labarin mahaukaciya kenan" gyada masa kai Khadija tayi, El-ameen yace "Toh me Abba yace?" Hawaye ya cika idonta taki cewa komai, ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh bai xo ba junaid din" hawaye na sakko mata tace "Tun daxu ake kiransa ya ki ya xo" El-ameen bai kuma cewa komai ba ya nufi parlon Mumy, xaune ya ganta da ganinta ba karamin kuka ta ci ba, kasa karasawa yayi cikin parlon ya juya ya fita kawai, kofar gida ya koma ya ba sarki hakuri sannan ya ce su shigo, Fitowa Zahrah tayi da 'yar uwarta suna daga gefen mahaifinsu suka shiga gidan, har parlon Abba yayi musu iso, tuni Khadija ta mike tana kallon ikon Allah ganin jama'ar dake shigowa gidan, El-ameen ne ya fara shiga parlon da sallama ya gaida Abba da ladabi, Hajja tace "Alhmdllh kun ga babban munafukin abokin nasa nan, ae wllh sai Allah ya mana hisabi da ku...." El-ameen bai ko kalleta ba yana kallon Abba yace "Abba baki kayi daga masarautan Bauchi, mai martaba sarkin bauchi ne da kansa" Abba da ya wani xaro ido tun kan yace komai Sarki El-ameen ya shigo parlon da sallama Aminansa biyu da Zahrah da Ummi ma suka shigo sai Abdul sauran dogarawan sarki suka yi cirko cirko bakin kofa, da farko tsaye sarkin yayi ganin yanda ake kallonsa da mamaki barin Abba ya sa shi samun kujera ya xauna, parking Junaid yayi kofar gida ya tsura ma manyan motocin dake Parke a jere ido, mamaki ne ya cika sa sosai lokaci daya yaji gabansa ya fadi ya bude motar ya fita da sauri ya shiga cikin gidan, uniform ne jikinsa sai hula dake kansa, ko lura da dogarawan da suka cika compound din bai yi ba, shi dai burinsa ya ga Mumynsa, hankalinsa bai gama tashi ba sai da ya ga jerin takalma dake kofar parlon Abba, da part din Mumy xa shi kawai ya fasa ya nufi parlon Abba da sauri ya shiga.
76......
Tsaye yayi bakin kofa yana bin kowa na parlon da kallo irin na mamaki, ido hudu suka yi da Zahrah dake kallonsa ko kiftawa babu, hade rai yayi ya juya xai fita El-ameen dake tsaye har lokacin ya kama hannunsa yana kallon Sarki da shi kansa kallon Junaid yake yace "Ahmad junaid kenan, kuma dominsa ku ka taho katsina." Mikewa Hajja tayi da sauri tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Me yayi? Yaron da ko hanyar bauchi na san ko xa a kashe sa bai sani ba, ashe kai mugu ne Aminu ba mu sani ba..... Meye hadin jikana da masarautar Bauchi can kace ko ina?" Abokin Abba ne yace "A'a Hajja ba tashin hankali bane, ae ba mu jira mun ji me ke tafe da su ba, kuma ko gaisawa fa ba a yi ba, sannan ance sarki ne nan gabanmu ba fa waxiri ba....." Wani kallo ta watsa masa A fusace tace "Yo ni ina ruwana da sarautarsa, ka gan ni nan ban tsoron kowa sai Allah, kuma bbu irin fitintinun da ban gani ba a duniya, ya fadi me jikana yayi masa in ji, Ahmad da ko titin da xai kai sa Bauchi bai sani ba" Abba dai kasa cewa komai yayi, don shima jiran jin me only son din nasa yayi kawai yake, Sarki kam banda murmushi babu abinda yake sai dai ba lallai ka gane murmushin ma yake ba sbda turban din kansa, Aminin sa da shi ma ya samu gu ya xauna gefensa cikin kaushin murya yace "Mind you all, ba fa karamin mutum bane xaune a gaban ku, sannan mu alkhairi ne ya kawo mu in'sha Allah, Mai martaba sarkin bauchi kenan da kansa don haka a samu nutsuwa don Allah....." Hajja tace "Ina xa mu samu nutsuwa ba ku fadi me ke tafe da ku ba, ni dai nasan Ahmad ko cinnaka baxae iya kashe wa ba...." Sarki ya kalli Junaid yace "Toh karaso ka xauna Ahmad" tsaye junaid yayi kamar baxai karasa parlon ba gashi gabansa sae faduwa yake ya rasa dalili, sarkin bauchi kuma, is she related to the royal family? Abba ne yace "Ka kasa tahowa ke nan?" Da kyar ya d'aga kafa ya karaso ya xauna nan tsakar parlon Hajja ta xauna gefensa tace "Kwantar da hankalin ka Amadi bbu wanda ya isa ya cutar da kai matukar ina raye a doron kasa, su fadi me kayi in ji" tana magana ne tana matsar kwalla, Abba ya kalli El-ameen yace "Tafi ka kira Amina" juyawa yayi ya fita ba a dau lokaci ba ya dawo parlon tare da Mumy, k'in xama Mumy tayi ta kalli junaid ta kalli Sarki sannan Abba, Sarki ya kalli Zahrah da ke xaune daga kasa kusa da shi, sannan ya kalli Junaid yace "Kasan yarinyar nan?" Junaid ya daga kai yana kallon kwayar idonta, Sunkuyar da kai tayi da sauri ta dalilin faduwa da gabanta yayi, sai da sarkin ya kuma nanata tambayar sannan ya gyada kai kawai, Hajja da ko k'adan bata gane Zahrah ba ta yo waje da ido tace "A ina ka santa don ubanka?" Kallonsa kawai sarkin ke yi, a ransa kuwa tunani yake anya shi din El-ameen ya basa labari jiya, da irin fadin ran nan ya taimaki 'yar sa kenan, A fili kuwa cewa yayi "Toh a ina ka santa Ahmad?" Kallon El-ameen Junaid yayi yace "Shi ma ai ya santa, ya ma fi ni saninta" Hajja ta mike tace "Atoh a hankali gaskiya dai xata bayyana don ni nasan jikana bai santa ba sai dai abokinsa" Aminin sarki ne yace "Ahmad kake koh? Toh kasani ba karamin mutum bane nan gaban ka, am repeating this, you go straight to the point and answer his questions right away, takanas ya taso tun daga bauchi domin ka don haka kar ka maida mu kananan mutane" Mumy ji tayi ta kasa tsayuwar ma, da kyar ta samu waje ta xauna tana kallon ikon Allah, Junaid kam dama ba direction dinsu yake kallo ba, Sarki ya nisa yace "Ahmad, ni ne Mahaifin Zahrah, ka kuma min abinda har karshen rayuwata baxan taba mancewa da kai ba, ka dawo min da farin cikina ka fitar da ni kunci lokaci daya, ashe har yanxu akwai sauran mutanen kirki a duniya? ashe akwai masu xuciya irin taka a duniya, kaf rayuwata ban taba jin na kaunaci mutum kamar yanda naji kaunar ka daga jiya ba, da kai na kwana a raina jiya Ahmad....." Hajja sai wuwwulla ido take tana jiran jin me yayi ma sarkin, Sarki yace "Xan so ka ban labarin yanda ka ga Zahrah har ixuwa jiya Ahmad" k'in dagowa Junaid yayi da farko can ya dago suka hada ido da sarkin sai yaga yayi masa kwarjini, da kyar ya iya cewa "Nayi xaton El-ameen ya fadi maku ranka shi dade" Sarki yayi murmushi yace "Ehh, amma xan so sake jin labarin daga bakin ka" Junaid ya shafa kansa ya kalli Abba dake kallonsa, sannan ya dauke kai, xaunawa Hajja tayi tana jiran jin labari ita ma, Kamar baxae ce komai ba sai kuma cikin sanyin murya yace "It all happened on a faithful tuesday evening....." Lumshe ido yayi ya bude ya shiga ga bada labarin tun daga ranan da ya fara ganin Zahrah a gefen titi, bbu abinda ya canxa daga wanda El-ameen ya fadi ma sarkin jiya, yanda ya kama mata gida da farko daga karshe kuma suka koma gidan El-ameen, irin hidima da wahalhalun da suka yi shi da El-ameen a kanta, da yanda suka boye ma iyayensu, mama jummai da suka dauko.... kai bbu abinda ya boye har gida da ya kawota da nufin aurenta da yanda iyayensa suka gane ba mai hankali bace..... Bbu wanda jikinsa bai yi sanyi ba a parlon, Hajja ta rushe da kuka tace "Ae dama nasan jikana yaron kirki ne, Allahu Akbar, xaka aikata fiye da haka ma don k'akan ka ka gado " sunkuyar da Kai Junaid yayi ya kasa ci gaba don dama yanda yake bada labarin kamar bai son yi, Aminin sarki ne yayi Encouraging dinsa da ya ci gaba don sarkin kasa cewa komai yayi banda ido da ya tsura masa, Zahrah kam banda kuka babu abinda take jikinta yayi sanyi ba kadan ba, ita kanta Mumy hawayen ne ke sakko mata, cikin sanyin murya junaid ya ci gaba yace "I had to take her away..... muka bar gidan and....." shiru yayi kafin ya fadi yanda suka yi hatsari bayan barinsu gidan wanda shi ne dalilin dawowan hankalinta sai dai kuma tayi losing memory ta mance komai, bai boye yanda ya janye jikinsa daga lokacin bisa umarnin da iyayensa suka basa, ya fadi yanda ya bar ta da El-ameen bai kuma bi ta kanta ba, El-ameen kuma ya kai ta gidan Course mate dinsa tayi kusan wata biyu a can, a watannin ta biyu a gidan sau daya yace yaje daga nan kuma bai sake komawa ba, har aka yi aurensa da Humainah, ya fadi shawarar da El-ameen ya basa da yanda ya amince ya maidata gidansa da xama gaba daya ya kuma sa ta a islamiyya, bai boye irin matsalolin da suka dinga fuskanta da Humainah a kanta, ya kuma fadi dalilin sa na sakin Humainah, bai rufa komai ba kan irin xaman da suka yi da Zahrahn bayan barin Humainah gidan har ya kai karshen labarin da fadin dalilin dawowar memory dinta, sai da idon kowa ya kawo a parlon, ya kusa minti biyar kansa a kasa kafin ya dago a hankali, hawaye ne cike idonsa ya mike ya isa gun Mumy ya durkusa ya daura kansa a kafarta a sanyaye yace "Ki gafarceni Mumy, nasan nayi disobeying din ki, na kuma boye maki abinda nayi which I wasn't suppose to ko da kuwa baxa kiyi supporting dina ba shi yasa komai bai tafi min dai dai ba, forgive me plss Mumy....." Hawaye kawai Mumy take bata iya ta ce masa komai ba, ya mike ya isa gun Abbansa shi ma ya durkusa gabansa hawaye na sakko masa yace "Ka yafe min Abba, I know I... I failed you....."Jin Abba bai ce komai ba yasa shi mikewa a sanyaye, tashi sarki yayi ya taka har gabansa ya dafa sa sai kuma ya rungumesa yace "They will all forgive you in'sha Allah son, sannan ina me umartarka da ka mayar da matarka ka nemi gafararta....." Daga haka ya sake sa ya isa gaban Abba yace "Ina neman alfarmar ku yafe ma Ahmad duk abinda ya maku a kan Zahrah...." Murmushi Abba yayi ya mike yace "Bai min komai ba mai martaba, Allah ya basa ladan abinda yayi, ina alfahari da kasancewarsa d'ana, yasan ba lallai in sauraresa ba a lokacin shi yasa yayi komai gaban kansa, Allah ya biyasu gaba daya da abokin nasa, is good thing sun riketa amana, ta kuma samu lafiya ta dalilin su, I am proud of them....." Mikewa Mumy tayi a sanyaye xata fita Sarki yace "Toh Hajiya bamu ji kin ce kin yafe masa ba, ina nema masa wannan alfarmar don Allah" murmushi kawai tayi, Hajja da baki ya ki rufuwa tace "Yo wa ya sani ko bakin ciki take masa kamar yanda matan ubansa ke masa, ni dama tun ran da Amadi ya kawo yarinyar gidan na daura ido na kanta na ji ta kwanta min toh tunda yan gida suka ce mahaukaciya ce basu san xance ba ina ni ina magana ace don ba ni na haifesa ba" kallonta kawai junaid yake haka ma El-ameen dake murmushi, sarki yayi murmushi shi ma yace "Da fatan mun kafa xumunci kenan har illah maa'sha Allah" Hajja ta mike da sauri tace "toh ni makka xaka kai ni, shekarana uku rabona da can wllh" 'yar dariya sarkin yayi yace "Kina da kujeru biyar wannan shekarar Idan Allah ya yarda" shewa tayi tace "Allah yayi maka albarka...... Sai mu je tare da Humainah da kawayena Uku" kofa junaid ya nufa xai fita daga parlon sarki ya kirasa, juyowa yayi yana kallonsa, sarkin yace "Ina gayyatar ka masarautar mu tare da El-ameen, ur labours will not go in vain" Shiru Junaid ya d'an yi sai kuma yayi kasa da kai yace "Sai na dau excuse gun aiki idan Allah ya yrda" Kai kawai sarkin ya gyada masa, Satan kallon Zahrah yayi ya juya ya fice, kamar warce aka tsikara ta mike ta bi bayansa da sauri.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By Khaleesat Haiydar_???
77......
Bin bayansa Zahrah tayi, ya ki tsayawa ita ma bata ce ya tsayan ba ya nufi part din Mumy, yana bude kofar ta ja ta tsaya tace "Amm... Ahmad Junaid!" Lokaci daya ya juyo ya sauke idonsa kanta yace "Yess!" Wani mugun kwarjini ya mata ta kasa cewa komai sae kallonsa take, daga kasa har sama ya kalleta sannan ya juya yayi shigewarsa parlor, still tayi gun kamar warce ruwa ya cinye, duk wannan abun El-ameen na tsaye balcony yana kallonsu, juyawa tayi suka hada ido da shi, hawaye ne ya ciko mata ta sauka daga balcony din da sauri ta nufi gunsa tana kallonsa lokaci daya hawayen idonta ya silalo tace "kaga abinda yayi min koh?" Murmushi El-ameen yayi ya buda ido yace "Yea! Haka nan yake! but idan ya sauko xa ki ga he is the sweetest guy you never expect.... He's still angry at you ne shi yasa" a sanyaye tace "But he shud have listen to me..... He's a sadist I notice" dariya sosai El-ameen yayi ta turo baki, tace "I just have to make him forgive me before leaving that's all!" El-ameen ya d'age gira yace "Go in ki samesa...." Shiru tayi sai kuma a hankali tace "In je?" Gyada mata kai yayi ta juya ta koma part din Mumy, tafiyarta kawai yake kallo har ta isa kofa ta murda a hankali ta tura ta shiga, durkushe ta gansa a parlon kusa Humainah dake kwance kan doguwar kujera idonta lumshe, tsaye tayi bakin kofar ta kasa karasowa, kallo daya yayi mata ya dauke kai, Dakewa tayi ta karaso parlon cikin rashin kuxari, dai dai lokacin da Humainah ta mike xaune da sauri, ya mike ya xauna gefenta yana kallonta ganin yanda ta rame, hannunta ya rike kamar bai son magana don bakinsa kadai yayi motsi yace "What wife!" Ta dafe kanta bata ce komai ba, can ta d'ago da kyar tace "Amai nake ji" mikewa yayi ya daga ta suka bar parlon, ita ko lura da Zahrah da tayi still tana kallon ikon Allah bata yi ba har ya shiga da ita daki, Zahrah taji ta ma kasa tsayuwar, tunda take bata taba jin abinda ta ji a lokacin a xuciyarta ba, kawai ji tayi hawaye ya cika idonta, ta juya da sauri har tana neman faduwa ta fice daga parlon. Bata ko kalli El-ameen dake tsaye har lokacin ba ta tafi can karkashin bishiya tayi xamanta gun ta fashe da kuka, juyawa El-ameen yayi ya koma parlon Abba, drinks ne da ruwa gabansu mai martaba kuma ga dukkan alamu hajja ce ta debo masu, yana shiga tace "yauwa tafi ka kira Amadin su yi sallama da Sarkin wai xa su koma" fita ya kuma yi ya tafi part din Mumy, khadija da fatima ne parlon don dama suna ganin shigowar junaid suka shiga daki, amsa gaisuwar fatima yayi yace "Ina Junaid din?" Khadija tace "Yana daki" yace "Tafi ki ce masa Abba na kiransa" mikewa tayi shi kuma ya juya ya fita, ba a dau lokaci ba Junaid ya fito ya karasa gun El-ameen, El-ameen yace "Hope ka saurareta dai yanxu?" Girgixa kai yayi yace "Bani da lokacin ta, bana kuma bukatan godiyar da xata min ko hakurin da xa ta ban, don Allah nayi mata ba don ita ba wllh" Murmushi El-ameen yayi yace "Gaskiya ne" Junaid ya shiga parlon Abba, nan dai suka yi sallama da mai martaba dake sauraren xuwansa da El-ameen nan da kwana biyu, Zahrah na ganin fitowar Abbanta ta mike ta nufi gate da sauri, Ummi ta bi bayanta ganin mood dinta, Abdul ma bin ta yayi da kallo, har bakin mota Hajja da su Abba suka raka mai martaba, sai surutu take masa kamar irin ta san sa da can, junaid dai na biye da su a baya, lokaci lokaci mai martaba kan juyo ya kallesa, ita ko Zahrah can wani mota ta tafi ta tsaya a baya Ummi sai tambayarta take meyasa mood dinta ya canxa amma ta ki cewa komai, a hankali junaid ya dinga bin wajen da kallo ganin bai ganta ba, har cikin motar dake gabansu sai da ya kalla bbu ita, El-ameen dai na tsaye rungume da hannayensa yana kallonsa, tsaf ya gane me yake nema, kawai yayi murmushi, Mai martaba kansa sauraren Hajja kawai yake amma rashin ganinta ya sa ya fara waige waige shi ma, can dai yace "Ina Zahrahn ta xo ta shiga mota" Ummi ce tace "Toh kinji Abba na neman ki ma, ki taho mu je" ba musu Zahrah ta fito daga bayan motar sai dai duk jikinta a sanyaye, satan kallonta Junaid ya dinga yi har ta iso gun motar da suka taho da, Hajja ta jawota ta rungume tace "Kice ma Uwar ki ina nan xuwa, xata yi babbar bakuwa don tare xamu taho da su Amadi, Allah ya maki albarka ni dama tun farkon ganin ki kika kwanta min don akwai ni da tausayi" kai kawai Zahrah ta gyada mata ta bude bayan mota ta shiga Ummi ma ta shiga, junaid bai fasa mata kallon sata ba, ita ko bata ko kalli su waye a tsaye gun ba, tana shiga motar ta rufe ido, bata kuma bude ba sai da taji tashin motar da fatan kai wa gida lafiya da su Hajja keyi masu, ta kalli tagar motar suka yi ido hudu da junaid, dauke kai tayi da sauri, can kuma ta kalli El-ameen dake kallonta shi ma, d'an murmushi ta kirkira ta daga masa hannu a hankali, shi ma ya mayar mata da murmushin, driver ya ja motar suka dau hanyar fita daga layin. Tuni su Abba suka shiga gida, Hajja dai har lokacin bata fasa daga ma motocin da har sun bar layin hannu ba baki a wangale, El-ameen yace "Toh ae sai ki sauke hannun haka" juyowa tayi da sauri tace "Kaga ikon Allah ko Aminu, ashe dama tsinannun matan Muhammadu ne ke tare mana hanyar arxiki a gidan nan, yo gashi suna barin gidan sai ga sarki sukutum ya kwaso kafafuwa ya xo ganin jikana...." El-ameen yayi dariya yace "Toh jikan naki dai ba mutumin kirki bane don walakanci ya ma yarinyar daga ta bi sa tayi masa godiya kin dai san hali..." Tsuke fuska tayi ta kalli Junaid dake tsaye da sauri tace "Wato don ubanka ni xaka ma bakin ciki koh? Toh Allah ya isa idan aka hanani kujerun makka nah, kai baka yi murnar ta dalilin ka sarki ya shigo gidan ubanka ba, kasan alkhairin da yake shirin yi ma xuri'ar mu.... Ka xata sarauta abar wasa ce... Toh gobe gobe ka shirya mu je ka bata hakuri, kasan alkhairin da ubanta ke shirin maka...." Junaid da takaici ya ishe sa yace "Bana bukatar komansu don ni sbda Allah nayi, mahaifina na da rufin asiri dai dai gwargwado, nima ina da nawa rufin asirin don haka babu abinsu da xae rude ni, ke dai ki je a kai ki makkan....." Bude baki Hajja tayi tana kallonsa cike da masifa can ta gyada kai tace "Shegiya nake idan ban je na ce ma Ubanka mari ka sharara mata ba" daga haka ta shige gate fuu, El-ameen ya fashe da dariya, junaid ya hade rai sosai yace "Ka bar min irin wannan abun Ahmad bana so" El-ameen ya tabe baki yace "Haka kawai mutum ya daura ma kansa wani hali da baxai fishesa ba a rayuwa, to riban me ka ci don ka walakantata Ahmad, ka dai san tafi karfin ka...." A fusace Junaid yace "Ni dai na fi karfinta don bata ma gabana, don Allah nayi abinda nayi" dariya El-ameen yayi yace "Shi yasa naga ka dage sai satan kallonta kake...." Daga haka ya daga kafa ya shiga gidan ya bar sa nan tsaye.
*Captain Ahmad Junaid*?
_By khaleesat Haiydar_???
78.....
Ranan laraba da safe misalin goma su Junaid suka yi set off din xuwa bauchi sai dai ta plane don yace baxae iya xaman mota ba, shi ma din ba karamin takurasa Abba yayi ba kafin ya amince xai je don da ca yayi shi baxae je ba don sbda Allah yayi abinda yayi, xuwa lokacin dae ba laifi Mumy na amsa gaisuwarsa sae dai ba kamar da ba hakan yasa duk ya ji ba dadi, tun ranan litinin yake gidan, ko yaje aiki nan yake dawowa da yamma, tausayin Humainah yake sosai hakan yasa ko da yaushe yana kusa da ita, part dinsa ya mayar da ita daga karshe ita dai Mumy nata ido, duk da luran da yayi su Umma basa gidan haka ma Suhaima da Muhibba ko sau daya bai taba tambayar inda suke ba, harkokin gabansa kawai yake, Hajja dake ta shiri tun daga ranan litinin din tana jiran ranan jumma'a da Abba yace za su je bauchi da su Junaid bata san har sun tafi ba safiyar laraban, suna cikin taxi da xai kai su Airport wayar El-ameen ya fara ringing, cirowa yayi yaga Aliyu ne ke kiransa, shi har ya ma mance da shi, d'an murmushi yayi ya daga kiran, daga daya bangaren Aliyu yace "Masu Jasmine/jewel/baby!" Murmushi El-ameen yayi yace "Yea, mara mutunci da abokina bai dawo sense dinsa ba sai dai ka ga sammaci wllh" dariya Aliyu yayi yace "Ae nasan ya dawo ne, bayan ka xo ka dauketa ka mayar masa ae magana ta kare" El-ameen yace "Exactly, kuma albishirin ka, ita ma ta dawo, ka dai gane me nake nufi..." Aliyu yace "Ohh really, dama na ga alama soon xata dawo.... But what brought her back!" El-ameen yace "That's a long story, yanxu ina hanyar bauchi ne" Aliyu yace "me xaka yi bauchi" El-ameen ya saci kallon junaid dake kallonsa yace "Ohk! Let's chat!" Daga haka ya katse wayar, wani uban tsaki Junaid ya ja ya dauke kansa, El-ameen yayi dariya, junaid bai kuma kallon inda yake ba har suka isa airport. sha daya suka sauka bauchi, El-ameen ya tare masu taxi duk suka shiga baya ya fadi ma me taxin inda xai kai su, Sai a sannan ya juya yana kallon junaid yace "ka cika umarnin da sarki ya baka kuwa?" Junaid ya kallesa yana jiran jin umarnin me, ganin El-ameen bai kuma cewa komai ba har bayan kusan minti biyar yace "Wani umarnin?" El-ameen yace "Ashe kana da baki" dauke kai Junaid yyi, El-ameen yace "Na mayar da Humainah da yace kayi!" Shiru Junaid yayi masa na kusan minti sha biyar kafin ya juya ya kallesa yace "Ehh" ko kallonsa El-ameen bai yi ba idonsa na kan titi, murmushi Junaid yayi ya shafa kai, sha biyu saura suka isa masarautan, El-ameen ya fito daga taxin haka ma Junaid dake bin ko ina da kallo, Kudi El-ameen ya ciro ya ba mai taxin sannan ya nufi Entrance din masarautan junaid ya bi bayansa, gaba dayansu dakakkiyar Shadda ce jikinsu, shi El-ameen ruwan hoda, shi kuma junaid fari, yana biye da shi ne yana danna waya, tafiya sosai suka yi kafin su iso main Entrance din da xai kai su har palace din, fixgosa Junaid yayi ganin tafiyarsa kawai yake yace "Meye xaka wani dinga wucewa kana kyaleni a baya, ko na ce ma nasan hanya ne" kallon mamaki El-ameen yayi masa kafin ya duka yace "To hau!" Junaid bai san lokacin da ya fara dariya ba yace "Ka ji dan iska, kai har xaka iya goya ni?" Murmushi El-ameen yayi ya mike don ko ba komai ya sa shi dariya baxae shiga yana murtuke ma mutane fuska ba, a tare suka jera suna tafiya, Junaid yace "Wani disc ne na gani daxu a hannun ka a plane" El-ameen yace "Na ban mamaki ne" Abdul dake tsaye da abokansa biyu gun mota da alamar xa su fita ne ya hangosu ya karaso da sauri yace "Ohh baki gare mu haka... Welcome to you guyz, sannun ku da xuwa" hannu ya basu gaba daya biyun sannan yayi masu jagora har xuwa fada, ganin Abbansa na da baki ya nufi part dinsa da su, suna shiga parlonsa Junaid ya nemi gu ya xauna ya cire hular kansa, Abdul yace "Amma flight ku ka biyo koh?" El-ameen yace "Eh my oga at the top yace bai iya xaman mota ba sbda kura" dariya Abdul yayi yana kallon Junaid, junaid yayi murmushi yace "Manta da shi basir gare sa bai iya xaman mota shi yasa muka biyo jirgi" dariya suka dinga yi gaba daya, El-ameen ya jefa masa hular kansa yace "Kaji sharri...." Drinks kala kala da kayan marmari Abdul ya dire masu ya xauna yace "Toh ya mutan gidan, ya muka baro ku?" El-ameen ne kadai ya amsa don shi junaid kallonsa kawai yake ganin ba kaman wasa suke da kanwarsa ba, waya Abdul ya dauka ya ce bari in kira maku mutuniyar ku gaisa kafin Abba ya sallami b'akinsa, yana kara wayar a kunne bayan ta daga yace "Lil sis, ki taho ina jiran ki part dina" daga haka ya katse wayar, bayan kusan minti goma sai ga ta ta shigo parlon, wani alkybba dake daukar ido ne jikinta har yana jan kasa, shi kansa takalmin kafarta abun kallo ne, hular kanta ya rufe kusan rabin fuskarta, tana ganin mutane xaune parlon ta turo baki ta nufi bedroom don ta gaji da gaishe gaishe, Abdul yace "Ina kuma xa ki bakin ki ne fa" daga kai tayi da sauri ta maida hular saman kanta, ido hudu suka yi da junaid ya kasa dauke idonsa kanta, tayi saurin kauda idonta ta kalli El-ameen dake kallonta shi ma ko kiftawa babu, wani kyalli take gaba dayanta, tayi wani kyau na musamman duk da ba make-up bane fuskarta, murmushi tayi da ya bayyana fararen hakoranta ta karasa gun El-ameen ta durkusa nan kasa cikin sanyayyen muryarta tace "Welcome!" Kai kawai ya iya gyada mata, Abdul kuma yayi excusing kansa ya fita, da kyar El-ameen ya samo abun cewa yace "Ya gidan, ya su mama!" Ta langwabar da kai tace "Taso mu je ku gaisa da su" Junaid dai danna wayarsa kawai yake, El-ameen yace "Baku gaisa da captain ba?" Gefenta ta d'an kalla tace "Ohk, sannu da xuwa" daga haka ta mike tace "Mu je gun Ummata" mikewa El-ameen yayi
ya dau Apple daya ya kalli junaid yace "taso mu je muyi gaisuwa frnd" junaid yi yayi kamar bai ji sa ba, Zahrah tuni ta nufi kofa ta fita abunta, warce wayar El-ameen yayi yace "kaga ka ajiye halin nan naka aside har mu bar garin nan, in girman kai ne da ji da kai toh gidansa ka xo, bbu wanda xaka nuna ma a nan sai dai ma ka kara course wajen su" mikewa junaid yayi yace "Dama don ku ci min mutunci yasa kuka dage sai na xo garin nan, how dare her xata shigo ta ki gaisheni tana min kallon rainin wayo, da ana rubuta hali a goshi wllh da ban fara ko da kallon inda take ba bare har na tausaya mata" yar dariya El-ameen yayi yace "Yau kuma ba don Allah kayi ba kenan......" Wani tafarfasa xuciyar junaid yake, El-ameen ya tabe baki yace "If you like kar ka fito muyi me ya kawo mu bar garin nan" daga haka yayi ficewarsa ya barsa gun tsaye, tsaye ya ga Zahrahn tana jiransu ga dukkan alama taji abinda suka ce, murmushi ya mata yana fatan Allah yasa ba jin dai tayi ba. Ta mayar masa da murmushin tayi gaba tana cewa "Kila yana da matsalar kunne ne, shi ya hanasa jin sannun da nayi masa," da sauri El-ameen ya kalli bayansa ya ga ko yana gun, ya ga ko fitowa bai yi ba, can ko sai ga shi ya fito, Tana gaba El-ameen na biye da ita a baya shi kuma junaid na bayan El-ameen, bangaren Kilishi ta fara kai su, sosai tayi farin cikin ganinsu, ta sa aka cika su da kayan ciye ciye da sha, Shi dai junaid idonsa na kan makeken plasman parlon dake cike da kayan alatu, ganin yaki taba komai tace "Kai ya sunanka, ko kai ne takwaran mai martaba?" Girgixa kai yayi yace "A'a, Ahmad" tace "Babana ne ma ashe, to baka ci komai ba.... Ba a mana haka fa" da ganin murmushin da yayi kai kan ka kasan kirkira yayi, ya dau slice din kankana ya Kai baki yana tauna da kyar, ta gefen ido Zahrah ke kallonsa can ta tabe baki hade da murguda bakin, El-ameen kuma hararansa kawai yake ta gefen ido, ita ko Kilishi sai kallonsa take haka nan taji ya burgeta, jikinsa ne ya basa kowa kallonsa yake ya ki daga kai ya kuma daukar apple ya kai baki ya gutsura a hankali, Zahrah tace "Mumy bari in kai su gun Umma" Kilishi tace "Toh maxa ku je Zahrah" mikewa tayi tana kallon El-ameen tace "Mu je" mikewa yayi shi ma yayi mata sallama tace "A'a mai gida ai xaku dawo" kallon Junaid tayi tace "Toh tashi ku je babana" d'an murmushi yayi ya mike yace "Sai mun dawo" daga haka suka fita gaba daya daga parlon, a tare suke tafiya da El-ameen suna hira jefi jefi, El-ameen yace "Yayanki ne Abdul din nan koh?" Ta gyada kai tace "Yea, stepbrother nah" ya wara ido yace "Waow, mum dinsa ce kenan wannan!" Ta gyada kai tace "Ehh shi da Ummi" yace "Ayya, amma kina da kanni ko yayyi the same mum kuwa" girgixa kai tayi tace "I am the only one gun Ummata" kallonta yake da mamaki, yaji tausayin mahaifiyarta sosai, ko ya tayi da Allah ya rabata da only child dinta, junaid dai distance me d'an tsayi ya bari tsakaninsu yana biye da su hakan kuma bai hanasa jin hiran tasu ba, daya daga masu girke girken fadan ne ta washe baki ganin Zahrah tace "Gimbiya ban ganki kitchen yau ba" d'an murmushi tayi ta tsaya har ma'aikaciyar ta karaso kusa da ita, El-ameen ya ci gaba da tafiya, Zahrah na kallonta tace "Ina ciwon kai ne shi yasa... Ya aiki?" Matar tace "Alhmdllh, b'aki kika yi?" Kada mata kai tayi dai dai lokacin da Junaid ya karaso ya wuce su, ta bi sa da wani kallo kafin ta tabe baki tace "Da rana xan shigo kitchen Karima" daga haka ta nufi El-ameen dake tsaye wani stairs yana jiranta, ita kuma matar ta bi ta da kirari, ta gefen ido junaid dake tsaye gefen El-ameen ke satan kallonta har ya ga ta kusa isowa, El-ameen na ganinta ya ci gaba da tafiya, shi kuma yana ganin xata wuce sa ya sa mata kafa, ko lura bata yi ba sai ji tayi ta tafi luu xata fadi, tayi k'ara a tsorace tana neman regaining balance, bai san lokacin da yayi saurin tarota ba ta fado jikinsa, still tayi da farko sai kuma ta dago kai da sauri suka yi ido hudu, kasa motsi tayi ta kuma kasa dauke idonta cikin nasa, shi ma kallonta kawai yake gabansa na faduwa, bakinsa ta ga yana motsi a hankali ta sauke idonta kai underneath his breathe taji yace "Jas...jasminee!" Gaba daya ta shagala da kallonsa, shi ya fara dawowa hankalinsa ya saketa da sauri, sai a sannan ta koma baya duk ta daburce, a tare suka juya da sauri kallon El-ameen suka ga gun wayam babu shi.
*Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
79
Da sauri ta sauka ta bi bayansa, junaid ya bi ta da kallo har lokacin xuciyarsa bai bar bugawa ba, da kamar ya koma part din Abdul sai kuma kawai ya bi bayanta, ji yayi gaba daya yaji haushin kansa, ya ja tsaki ya ci gaba da tafiya kamar bai son yi, tsaye Zahrah taga El-ameen da wasu dogarawa suna hira, ta kasa karasawa gun, juyawa yayi suna hada ido ya sakar mata murmushi, kasa mayar masa tayi, yace "ban san hanya ba, I've to wait for you....." Karasowa tayi da kyar ba tare da ta ce komai ba ta ci gaba da tafiya, bai bari suka hada ido da junaid dake tahowa ba ya daga ma dogarawan hannu ya bi bayanta, tafiya kawai take amma ji take kamar xata harde ta fadi kasa, duk yana lura da ita hakan yasa ya karasa suka jera da ita yace "Masarautan nan naku da girma sosai" ta gefen ido ta kallesa tace "Yyeah!" Rasa abun cewa yayi shi ma can kuma yace "But kin gama sec sch kuwa?" Shiru tayi sai kuma ta gyada masa kai tace "Ehh!" Yace "Dat's good" junaid dai na biye da su a baya, wata hanya daban ta dauka suka haura bene sannan ta bude wata babban kofa ta juya tana kallonsu, suna hada ido da El-ameen ta sauke idonta kasa ta ci gaba da tafiya, tsarin gun kamar na Kilishi da suka baro, babu kowa babban parlon sai jakadiya da wata me goge goge, Ta nuna masu kujera, jakadiya ta bi ta da kirari kafin tayi masu sannu da xuwa, El-ameen ne kadai ya amsa mata yana murmushi, Bedroom din Umma Zahrah ta nufa ba a dau lokaci ba sai ga ta sun fito da Umman, murmushi ne shimfide fuskarta har ta karaso parlon tana kallonsu gaba daya tace "Sannun ku da xuwa...." Sakkowa El-ameen yayi har kasa Junaid ya bi sa da ido kafin shima yayi kasa da kansa ya sauka, suka gaisheta gaba daya, tana murmushi har lokacin ta amsa, tuni jakadiya ta cike gabansu da kayan marmari da shaye shaye, Umma tace "To waye Ahmad waye takwaran mai martaba" El-ameen yayi murmushi yace "Ni ne El-ameen...." Ta kalli junaid cikin sanyin murya tace "Kai ne Ahmad kenan" kai ya gyada mata ba tare da ya dago ba, a sanyaye tace "Allah ya albarkaci rayuwar ku, yasa ku gama da iyayen ku da duniya lafiya....." El-ameen yayi saurin cewa "Ameen Umma mun gode" Umma ta kalli Zahrah tace "Kin kai su gun Kilishi?" Ta gyada kai tace "Can muka fara xuwa" Umma tace "To Maa sha Allah" ba su wani dade part din Umma ba ta dalilin bakin da tayi, Zahrah ta nufi fada gun Abbanta da su, sai dai wannan karan sauri kawai take bata bari sun jera da El-ameen din ba, bai takurata ba ya jira junaid, junaid na isa gunsa yace "ya kuma ku ka raba tafiyar?" Murmushi yyi yace "Yea hakan yafi don ni ba runguma bane iyakar abinda zan mata idan na kasa jure shariyarta gare ni" Wani kallo Junaid ke yi masa kafin yace komai El-ameen yayi dariya yayi gaba ya bar sa nan, suna shiga fada ta juya ta bar su tare da Abbanta. Da rana Umma ta takurata ta kai masu lunch tace ai masu aiki xa su kai masu, Mikewa tayi d'aga karshe dai ta fita nemo Ummi ta rakata. Sae da suka fara xuwa kitchen don tabbatar da cewar an kai abincin taga an kai, fura ta tarar ana damawa kitchen din, ta dau babban jug ta diba snn ta dau tray ta daura kai da cups ta fita tare da Ummi, suna isa part din Abdul Ummi ce ta fara shiga da sallama kafin ita, Junaid ne kwance parlon yana danna waya, yayi masu kallo daya ya dauke kai, Ummi ta xauna tana kallonsa ta gaishesa ya amsa ba tare da ya kalleta ba, Ajiye trayn hannunta Zahrah tayi ta nufi bedroom ba tare da ta kallesa ba, El-ameen ta gani da Abdul suna kallo ga cake gabansu, El-ameen ya buda ido murya can kasa yace "princess!" Tace "Uhm, kun yi lunch?" Hararata Abdul yayi yace "Basu yi ba" 'yar dariya tayi ta kalli El-ameen dake kallonta, can ta karasa ciki ta xauna kusa da Abdul ta kai bakinta kusa da kunnensa kamar me rada tace "Why is he alone?" Abdul ya kalleta yace "Ahmad?" Satan kallon El-ameen tayi sai kuma ta dauke kai da sauri, Abdul yace "He said he's more comfortable there" da sauri tace "Alryt, ohk" sai kuma ta kalli El-ameen tace "Ga fura na kawo maku fa" ba tare da ya kalleta ba yace "Toh mun gode" mikewa tayi ta fita daga bedroom din, xaune ta samu Ummi har lokacin idonta na kan Junaid, "ki tashi mu je" ta fadi haka bayan ta dauke kai daga kallonta, shi dai idonsa na kan waya, Ummi ta mike tace "Ohk furan xa a xuba masu ne?" Da sauri Zahrah tace "Noo!" Sai kuma ta nufi tray din da ta dire daga gefensa ta durkusa ta dau cups din ta xuba furan ciki ta ajiye tana kallonsa fuskarta daure, kara wayarsa yayi a kunne ya mike xaune ya sakko da fararen kafafuwansa kasa kamar wanda aka tilasta yayi magana yace "kina ji na?" Kasa daina kallonsa Zahrah tayi, ya shafa kansa yace "Have you eaten?" Shiru ya d'an yi kafin yace "Ki dai daure ki ci, I will call back later" daga haka ya katse kiran ya ajiye wayar lokaci daya ya sauke idonsa kan Zahrah dake kallonsa har lokacin, da sauri ta dauke Kai ta mike ta nufi kofa ta fice, har dare bata kuma komawa part din Abdul ba, duk ta rasa me ke mata dadi mugun haushin Junaid kawai take ji, har shi xae nuna mata ji da kai? mikewa tayi daga karshe ta fice ta nufi bangaren Abdul, El-ameen da Junaid ne parlon wannan karan, kmr daxu kwance Junaid yake waya na kare a kunnensa, Bata ko kalli inda yake ba ta karasa gun El-ameen dake kallon wani movie ta xauna kusa da shi tayi fari da ido tace "Are you okay? Bbu damuwa koh" Yana kallonta yace "Yea, am just missing home" murmushi tayi tace "Nan ma fa gida ne" yace "Yeah haka ne" ta mike tace "Ina son ka rakani mu je garden" yace "Really?" Ta gyada masa kai tace "Yeah, I want you to keep me company" mikewa yayi yace "Alryt mu je," duk da wayar da ke kare kunnen junaid gaba daya ya mance waya yake, ba kallon direction dinsu yake ba amma gaba daya hankalinsa na kansu, kofa ta nufa El-ameen ya kalli junaid da yayi saurin dafa wayar kunnensa yace "Will be ryt back" ko kallonsa Junaid bai yi ba har ya fita, ya mike xaune, ji yayi xuciyarsa na tafarfasa kawai, ya kusa minti ashirin xaune har Abdul ya shigo, ko da ya tambayesa El-ameen cewa yayi bai sani ba, yana shiga bedroom ya mike ya fice daga part din gaba daya, ji yayi da ma safiya ce ko rana da babu abinda xai hanasa komawa katsina duk da sarki ne ya tsaida su amma da tuni sun tafi da yamma, can wani waje da bbu hayaniya kuma babu wani haske ya samu ya xauna, har sha biyun dare bai da niyar tashi ya shiga ciki, gaba daya El-ameen yayi tunanin wucewa junaid yayi don yasan halinsa barin ma Atm card dinsa na jikinsa, Abdul da mamaki ya cikasa yace "Why is he acting that way?" El-ameen yace "That's he's hobby" Abdul bai san lokacin da ya fashe da dariya ba, El-ameen yace "Yeah, an only son, mumy's pet" Zahrah dake tsaye ta tabe baki ta juya ta fita daga parlon sai dai duk jikinta yayi sanyi, kasa komawa part dinta tayi hakan yasa ta bi hanyar da tasan baxa a ganta ba ta fita waje, tafiya kawai take ba don tasan ina ma xata ba kuma meye ta fito yi, bata yi wani nisa da tafiyan ba tayi ido hudu da shi har lokacin yana xaune ya xuba ma taurari ido kamar me kirgan su, rasa abinda xata yi tayi a lokacin, ci gaba da tafiya xata yi ko juyawa xata yi ta koma, Dakewa tayi ta tsaya inda take, can ta karaso fuskar nan nata daure tana kallonsa tace "Don me xaka wani fito nan cikin dare ka ba mutum wahalan nemanka when I am suppose to be in bed" wani kallo ya watsa mata ta gefen ido ya ci gaba da kallon sky abun sa, fixge wayar hannunsa tayi tace "Malam magana nake maka fah?" Sai a sannan ya kuma kallonta suka yi ido hudu gabanta ne ya fadi sosai, ya mike ya warce wayarsa yace "Gadina aka baki ne?" Wani kallo tayi masa tace "Ehh sbda ta dalilina ka xo garin nan....." Shiru tayi sai kuma ta turo Baki tace "I still can't believe ma kai ka tsince ni, or are you angry don bance kayi accompanying dina bane" murmushi yayi yace "How will you believe it, tunda ba sani kika yi ba lokacin da kike xuwa in bude maki Zip, in raka ki toilet, kike xuwa bedroom dina daure da towel..... Infact har lokacin da nake taimaka maki idan kina menses....." Xaro ido tayi, tayi wani kara tace "Nooo...." Ya gyada kai yace "Yesss! Har lokacin da......" juyawa tayi da gudu ta bar gun, bai san lokacin da ya fara dariya ba har da xama. Washegari kasa fitowa Zahrah tayi, kenan idan haka ne kila har nakedness dinta ya taba gani, har da kukanta da tayi wnn tunanin, sai da Umma ta bata rai sannan ta mike ta fita xuwa gaida su da safen, hijab tasa tsabar bata jin xata iya kallon junaid, tana shiga parlon ko ta gansa shi kadai xaune yana shan tea, kin dago kanta tayi ta kuma kasa karasawa can bedroom, kallonta kawai yake yana kokarin boye murmushin fuskarsa, juyawa tayi xata fita ya mike tana ganin haka ta kwasa da gudu, wani dariya ya taho masa bai san lokacin da ya fashe da dariyar ba, Abdul da El-ameen suka fito da sauri, buda baki Abdul yayi ganin ashe yana iya dariya haka, El-ameen kam karyar da kai yayi ya rungume hannu yana jinjina abinda ya ba junaid dariya haka, da kyar ya tsaida dariyar ya daga kai yana kallonsu, Abdul yayi murmushi yace "Ohh that's more beautiful of you captain" El-ameen ya tabe baki yace "Ko xa mu iya sanin abinda ya baka dariya haka Ahmad, na tabbata mu sai mun yi fiye da wanda kayi" shafa kai junaid yayi yana murmushi yace "Bana son ku haukace da dariyar just let it" El-ameen ya daga kafada yace "Lallai kam" daga haka ya juya ya koma dakin, Abdul ya karasa ya xauna gefensa yace "Gist me more about ur self captain...." Murmushi junaid yayi yana kallonsa. Karfe sha daya junaid ya gaji da xama don Abdul da El-ameen sun fita, bbu kuma yanda basu yi da shi ya bi su ba yace A'a baxae je ba, suka yi tafiyarsu suka barsa, dama bayan azahar xasu gana da wasu yan uwan mai martaba kafin su kama hanyar kt ranan, mikewa yayi ya fita yana rike da wayarsa, tafiya sosai yayi ya ga wani waje kamar gun shakatawa ga tsuntsaye sai shawagi suke, carpet grass ne shimfide gun, shiga yayi ta wani babban kofa ya dinga tafiya yana bin ko ina na wajen da kallo, wasu kuyangu guda uku ya gani suna tahowa ya bi su da kallo kafin yace "Ana shigowa nan kuwa" a tare suka gyada masa kai, daya daga cikinsu tace "Sai dai Gimbiya na nan ita ma!" Yace "Wace gimbiyar?" Tace "Gimbiya Zahrah" bai ce komai ba yayi gaba abunsa, xaune take ita kadai tana kallon cartoon da laptop din dake ajiye gabanta ta xauna kan kafafuwanta, gefenta kuma bowl ne me dauke da kayan itatuwa, juyawa tayi jin taku bayanta, suna hada ido ta mike da sauri har tana ball da bowl din fruits din gabanta, ta kuma juyawa da shirin gudu tayi karo da laptop dake ajiye, tsallakesa tayi ta bi wani hanyar da gudu, bin ta yayi da kallo kafin ya tabe baki ya xauna ya daga laptop din, ya dau apple daya ya shiga ci ya canxa cartoon din xuwa something meaningful yana kallo yana murmushi. Da yamma misalin hudu da wani abu junaid da El-ameen ne xaune a fadar me martaba dake dauke da mutane da dama tun daga waziri, advisern sarki har xuwa kasa, sannan ga 'yan uwansa da abokan arxiki, kanninsa mata da maza, Abdul na xaune daga gefen Abbansa, Ummi na xaune daga daya bangaren sa, Umma da Kilishi ma duk suna fadan xaune, Zahrah ce karshen shigowa ta nufi gun Ummanta ta xauna gefenta, kallon Junaid kawai sarki yake, can kuma sai ya kalli El-ameen, bayan kusan minti biyu na silence sarki yayi gyaran murya yace "Ahmad!" Dago kai junaid yayi yana kallonsa, Sarki yace "Nasan ba lallai in iya biyan ka abinda ka min ba amma ka fadi duk abinda kake so nan duniya in dai bai saba ma shari'a ba nayi maka alkawarin yi ma shi idan Allah ya yarda," shiru junaid yayi, can ya dago ya kalli Zahrah da idonta ke kansa suna hada ido ta dauke kai, kallon El-ameen yayi yaga wani gu daban yake kallo, can ya girgixa Kai yace "Bana bukatan komai mai martaba, I helped her for Allah's own sake" kallonsa kawai Sarki ke yi, can ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh shknn, Allah ya albarkaci rayuwar ka Ahmad" cikin sanyin murya junaid yace Ameen, sarki yayi murmushi ya juya yana kallon El-ameen yace "Kai fa takwara na?" Kallon junaid El-ameen yayi suka hada ido junaid ya sauke kansa kasa, Zahrah ma idonta na kan El-ameen gabanta na faduwa, haka kawai junaid ma ya ji gabansa na faduwa, bayan kusan second ashirin El-ameen yace "Ina son ka min alfarmar bani aurenta, na kuma yi maka alkawarin xan rike ta da amana...." Wani mugun bugu xuciyar junaid yayi, Zahrah kam kallon El-ameen take ko kiftawa babu, Mai martaba da ya kafa ma El-ameen ido shi ma yayi murmushi yace "Na baka! Xan kuma biya maka sadaki" kallon mamaki duk occupant din palace din ke ma sarki sanin baya magana biyu, El-ameen da ya rasa wani irin godiya xai ma mai martaba ya mike ya isa gabansa ya durkusa yana kallonsa, shafa kansa mai martaba yayi yace "You are blessed in'sha Allah son" El-ameen ya kama hannunsa ya lumshe ido ya kai lips dinsa, mikewa Zahrah tayi hawaye cike idonta ta kalli junaid da yaki dago kai har lokacin tayi ficewarta daga fadan.
*Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
80......
Ko k'adan Junaid bai kuma gane abubuwan da sarki ke cewa ba a wajen gashi bai yarda ya dago kai ba, mikewar da El-ameen yayi ya sa shi mikewa shi ma, kiran sunansa da ya ji anyi ya sa shi juyawa yaga sarki ne ya kirasa, sarki na kallonsa yace "Allah ya tsare hanya, ina kuma sauraron xuwar kakar ka" da kyar ya iya amsa masa yana kirkirar murmushi sannan ya juya ya fita, tun a hanya ya dake yayi patting shoulder din El-ameen yana murmushin karfin hali yace "Congrat frnd!" Kasa ce masa komai El-ameen yayi yana kallonsa, suna isa part din Abdul junaid bai ko kalli kayayyakin sawan da Abdul ya jido masu a boutique jiya ba, atm dinsa ya dauka da waya xai fita, wani abokin Abdul yace "Baxa ka canxa kaya ba Captain, Abdul din da xai kai ku airport ma bai gama shiri ba" cike da karfin hali junaid yace "Yeah, ina waje nan...." Daga haka ya nufi door, El-ameen dake tsaye ya bi sa da ido, a hanya Junaid ya hadu da Abdul, Abdul yace "A'a ina xa ka captain" junaid ya kirkiri murmushi yace "Ina jiran ku a waje" hannunsa Abdul ya kama yace "Noo baka isa ba, sai ka sake wanka ka canxa kaya" duk yanda Junaid ya so Abdul ya kyalesa kin saurarensa yayi har sai da ya mayar da shi part dinsa, dole yayi wanka ya canxa kaya, duk suka shirya, Abdul ya tafi da su xuwa gun Mum dinsa suka yi mata sallama ta hadasu da turarruka masu tsadan gaske, sannan ya kai su part din Umma, ita kadai ce xaune parlor da jakadiyarta, tana ganinsu ta saki fuska nan suka yi mata sallama ta dinga sa masu albarka, shi dai Junaid kansa na kasa, tsaraba sosai ta hada masu su biyun su kai ma Mum dinsu, El-ameen yayi mata godiya, shi ma junaid da kansa ke kasa yayi godiyar, Abdul yace "Umma ina Zahrahn fah?" Umma tace "Ina jin bacci take" mikewa yayi ya nufi bedroom din Umma, Umma ta bi sa da kallo har ya shiga, kwance ya sameta cikin bargo Ummi na xaune gefenta tayi tagumi, Abdul ya karasa da sauri yace "What's wrong with her" a hankali Ummi tace "She's just crying, me yasa Abba xai yi mata haka.... In ma haka ne ba sai ya basu kudi me yawa ba, ina jinin sarauta da auren....." Wani kallo ya watsa mata ya cire bargon yana kallon Zahrah, mikewa xaune tayi ta fashe da kuka tana kallonsa, ya xauna yace "Look ki hadiye kukan nan ki min magana, aurensa ne baki so?" Shiru tayi bata ce komai ba sai hawaye, yace "Ki min magana mana" girgixa kai tayi a hankali tace "A'a...." Yace "Baki son auren?" Tana goge fuskarta tace "Ni baxan iya cewa bana so ba, they helped me and...." Ya mike yace "Good you know that! Kina hauka ma duk sun xauna da ke da amana bare aure, yarima kamar ki kike so ko wa?" Girgixa kai tayi yace "to yanxu tashi ki wanke fuska ki taho kuyi sallama da su" mikewa tayi da kyar tayi yanda yace mata ta daura alkyabbarta ta rufe kusan rabin fuskarta ta bi sa suka fita tare da Ummi, sosai Umma taji dadin ganin ta fito don bata yi tunanin xata fito ba a yanda ta dinga kuka, har mota ta rakasu Ummi na rike da hannunta, shi dai Junaid yana gaba sai dai yayi murmushi idan aka ce wani abu, Ummi tace "Ya Abdul mu raka ka airport din plss?" Yace "Alryt mu je" front seat junaid ya bude ya shiga, El-ameen ya koma baya Ummi ta shiga sannan Zahrah, Abdul da Ummi kadai ke hira a motar, daga Zahrah, Junaid har El-ameen bbu me cewa komai, a hankali ta daga alkyabbar fuskarta suka yi ido hudu da Junaid don kallonta yake ta madubi, ta sauke idonta da sauri, suna isa airport junaid ya fita sannan El-ameen, Ummi ma ta sauka, sai da Abdul ya fita sannan Zahrah ma ta fito, karasawa El-ameen yayi kusa da Zahrah ya mika mata wani disc din hannunsa, ta daga kai tana kallonsa, sai kuma ta karba, kallo daya junaid yayi masu ya fara tafiya, Abdul ya bi bayansa haka ma Ummi, da kyar Zahrah tace "What's this?" Ya rungume hannayensa yace "Throw back! That period I do call you jewel, while captain call you Jasmine," ganin kallon da take masa na rashin fahimta yayi murmushi yace "Rayuwar ki na kwanakin baya ne..... Watch it.. You might like it" shiru tayi tana kallonsa, ya gyada mata kai assuringly, a hankali ta sauke kanta kasa yace "Let go" ba musu ta bi bayansa tana jujjuya disc din hannunta, xaune suka tarda su junaid, ta xauna gefen Ummi, El-ameen kuma ya tsaya suna jiran a kira su, lokaci lokaci ta kan juya ta kalli junaid kuma duk kallon da xata yi masa sai sun hada ido alamar shi ma kallon nata yake, can dai ya mike yace ma Abdul xai siyo ruwa ya bar wajen, bai kuma dawo ba sai da aka fara announcing jirginsu ne next din tashi, hannu kawai ya daga ma su Abdul ya shiga tafiyarsa, bin sa da ido Zahrah tayi, can ta kalli El-ameen dake kallonta ta d'aga masa hannu ta juya da sauri ta bar gun. Har suka sauka kt bbu wanda yace komai tsakanin junaid da El-ameen, taxi El-ameen ya tsayar masu ya kallesa alamar ya shiga, a karo na farko junaid yayi magana yace "Ae tafiyar mu ba daya bace, ka tafi xan samu wani" kallonsa kawai El-ameen yake can kuma ya shiga taxin da kayan tsarabarsu ya fadi ma driver din inda xa shi drivern ya ja motar suka bar junaid tsaye, kalle kallen inda zai xauna ta dalilin jirin da yake gani junaid ya shiga yi, can ya samu dakali ya xauna ya rike kansa, ya kusa minti goma xaune kafin ya mike da kyar daga karshe ya samu wani taxin ya shiga. Biyar saura ya shiga gida har lokacin yana ganin jiri, part din Mumy ya nufa, bbu kowa parlon ya shiga bedroom dinta, xaune ya sameta Hisnul Muslim a hannunta, kallonsa ta shiga yi har ya karaso gabanta ya durkusa ya daura kansa kan kafarta, ita dai kallonsa kawai take, dumin da taji a kafarta ya sa ta dago kansa tana kallo, hawaye ta gani fuskarsa, da mamaki tace "Me ya faru?" Kasa ce mata komai yayi sai hawaye, nan da nan hankalinta ya tashi tace "Ahmad!" Mayar da kansa yayi kafarta ta sauko kasa hankalinta ya tashi sosai tace "Talk to me son, me ya faru" rasa abun da xai ce mata yayi kawai ya rungumeta cikin sanyayyan muryarsa yace "Nothing mum, just forgive me plss" ji tayi hankalinta ya kwanta, a sanyaye tace "I've done that since son" a hankali ya xame jikinsa kansa a kasa yace "Nagode mum" daga haka ya mike ya fita daga dakin ya koma part dinsa yana shiga ya rufe kofar yasa makulli ya hade kansa da kofar wasu sabbin hawayen na xubo masa, ya kusa minti talatin tsaye kawai kuma ya bude kofar ya fice, can gidansa ya nufa cikin a dai daita, yana sauka ya ba sa kudin sa ya shiga gidan, ya kusa minti goma tsaye parlor sannan ya haura sama, dakin da Zahrah take ya fara budewa, hular ta ne kwance kan gado da ribbon sai zaninta, gadon na nan yanda yake tun daren da ya shigo ya tada ta bayan yaji an shigo gidan, karasawa cikin dakin yayi a sanyaye ya dau hular da ribbon yana kallo, juyawa yayi yana kallon takalminta dake ajiye a kasa daga kusa da gadon, ya kalli gaban mirror dake dauke da kayan shafanta, sai Qur'aninta dake ajiye daga gefe, xaunawa yayi gefen gadon ya lumshe ido ya rike kansa da yayi masa nauyi. A can masarautan bauchi kuwa tunda Zahrah suka dawo take kuka a dakinta bayan ta kulle kanta, bbu wanda ta saurara ta bude kofar har kusan goma na dare, mikewa tayi xaune da sauri tana kallon disc din da El-ameen ya bata da ta ajiye gefenta, dauka tayi ta mike ta nufi inda laptop dinta ke ajiye ta dauka ta dawo ta xauna gefen gado ta bude ta kunna.
*Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
81
Still Zahrah tayi ganin kanta xaune a wani parlor kasan rug, doguwar riga ce jikinta da hula a kanta, Junaid ta gani tsaye parlon yana danna waya can ya karaso ya xauna kujera, gani tayi ta juya tana kallonsa, shi ma kallon nata yake can ya ci gaba da dannar wayarsa, wata dattijuwa ce ta shigo parlon tana isowa gabanta ta xauna ta ajiye plate din hannunta me dauke da potatoe da ketchup, dattijuwar ta dau potatoe daya ta dangwala da ketchup din ta kai mata baki, taga ta karbe daga hannunta tana jujjuyawa can ta Kai baki ta lashe sannan ta mayar mata, tuni hawaye ya cika idon Zahrah, Junaid dai kallonsu kawai taga yake, dattijuwar ta jawo ta jikinta ita ko tayi lamo, saukowa junaid yayi ya dau dankalin ya kai mata baki ta kauda kai da sauri ta dinga shigewa jikin dattijuwar, ya tabe baki ya ajiye, Suna ta xaune a haka sai ga El-ameen ya shigo parlon, kallonsa kawai Zahrah take ko kiftawa bbu, farar 3 qtr ne jikinsa sai blue polo kallo daya yayi ma junaid ya karaso ya durkusa gabansu ita da dattijuwar ya ajiye ledan hannunsa, ba a dau lkci ba dattijuwar ta mike bayan ta xaunar da ita ta bar wajen, taga El-ameen ya xauna gabanta ya dago kanta yana kallon fuskarta ita ma kallon nasa take, Junaid dai bai ko kallesu ba waya kawai yake kallo, murmushi me kyau El-ameen ya mata taga ya lakaci hancinta ita dai idonta na kansa, dankali ya dauka ya dangwali ketchup ya kai mata baki ta kauda kai, hade rai taga yyi ya rike kanta ya kai dankalin bakinta, a hankali ta ga ta fito da harshe ta lashe ketchup din, dariya ta ga ya fara yi yana kallon junaid da yaki kallon inda suke, Zahrah bata san lokacin da tayi murmushi ba hawaye na sakko mata, taga ya kuma dangwala ya kai mata ta lashe, xaro ido tayi ta rike breathe ganin ya kai dankalin baki, sai kuma ya kalli Junaid da sauri yaga ba kallonsu yake ba, sosai jikinta yayi sanyi ta kasa daina kallonsa wasu sabbin hawayen na xubo mata, gani tayi junaid ya mike ya fice daga parlon, El-ameen ya jawo ledan da ya shigo da ya bude ya fiddo da magunguna da hollandia yoghurt, ya jawo cup din dake wajen ya bude drink din ya xuba ciki sannan ya dauka ya kai mata baki ba musu taga ta bude bakin tana sha har ta kauda kanta daga karshe, kadan ya sha ya ajiye cup din ya mike ya bar wajen, gani tayi ta jawo cup din ta juya upside down, drink din ya malale a gun har a jikinta, El-ameen ya karaso wajen yana kallonta, can ya hade rai ya durkusa ya ja hancinta, hannu tasa ita ma tayi yanda yayi sai kuma ta ja nasa hancin shi ma, murmushi Zahrah tayi ta lumshe ido, can ta bude a hankali, magani taga ya kada a cup ya kai bakinta, ba musu ta bude ya juye mata, ta shiga yamutse baki ya ciro handkerchief a aljihunsa ya goge mata bakin ya mayar sannan ya mike, Datijjuwar daxu ta ga ta dawo, shi kuma ya bar parlon, dattijuwar ta daga ta bayan ta dauke cups din gun suka bar parlon. Haka Zahrah ta dinga kallon irin rayuwar da tayi a baya, duk jikinta yayi sanyi sosai banda hawaye bbu abinda take, wani gun tayi murmushi wani kuma tayi dariya, tunanin da me xata biya dattijuwar nan ta dinga yi, har inda take xata so a kai ta, wani tausayin El-ameen ta ji dinga ji har cikin ranta, ashe haka yayi hidima da ita, ta ga dai kafin ta ga kanta tare da Junaid sau daya ta ganta da El-ameen sau goma, kuma taga junaid da ya shigo bai wuce minti biyar sai taga ya fita kuma kullum fuska a daure barin idan El-ameen na gun, a wani gu ne ma da El-ameen baya parlon taga ya xauna gabanta har ya dago kanta yana kallonta, can kuma ya mike ya koma kujera, gajiya Zahrah tayi daga karshe ta kashe laptop din ta koma ta kwanta a sanyaye, kasa bacci tayi daren ranan tunanin El-ameen take? na junaid ne? Duk ta kasa tantancewa da kyar ta samu bacci ya dauketa sai dai har asuba mafarkan junaid kawai take, tana idar da sllh bayan ta tafi ta gaida Abbanta da Umma ta tafi bangaren Kilishi ita ma ta gaida ta, Ummi ta shiga nema ta ganta bedroom din Kilishi ta ja ta suka fita ta koma part dinta da ita, Ummi tace "Ohh sis bacci fa xan koma" suna shiga bedroom Zahrah ta xaunar da ita ta ciro laptop dinta dake charge ta ajiye gaban Ummi tace "Idan kin gama kallon nan akwai tambayar da xan maki" daga haka ta kunna mata ta fice daga dakin, da farko Ummi kamar ta kashe laptop din tayi kwanciyarta sai dai hango yar uwarta da tayi a xaune ya sa ta bude ido daga nan kuma ta maida hankalinta gaba daya kai. Takwas saura Ummi ta fito parlor ta samu Zahrah kwance idonta lumshe alamar bacci take, jiki a sanyaye ta karasa ta xauna kusa da ita ta dafa ta cikin sarkewar Murya tace "Sister!" Bude ido Zahrah tayi da sauri tace "Ahmad!" Sai kuma ta maxa ta mike xaune tana kalle kalle, kallonta kawai Ummi ke yi, murya can kasa tace "Ahmad?" Zahrah da duk ta daburce lokaci daya tace "Ohh, Ummi, kin gama kallon ne" Ummi ta share hawayen fuskarta tana murmushi tace "Yeah and I love it Zahrah, I love it... Xan kai ma su Abba su ma su kalla...." Tana magana ne hawaye na xubo mata, Zahrah da ita ma hawayen ya cika idonta a hankali tace "but ina son in maki tambaya!" Ummi ta kalleta tayi mata murmushi tace "Ina jin ki My sis" Zahrah ta sauke idonta kasa tace "Between the two of them, waye ya ci ace baxan mance ba har karshen rayuwata, nd who deserve me?" Kallonta kawai Ummi ke yi, can tayi murmushi a hankali tace "My Dad! El-ameen... He soo deserve you sis, he gave you all his time, he took care of you, bai kyamace ki ba, bai kuma taba gajiya da ke ba....." Kuka sosai Zahrah ta shiga yi tana kallon yar uwarta, Ummi da jikinta yayi sanyi tayi shiru tana kallon ta ita ma, cikin rawar Murya Zahrah tace "Toh shi Ahmad fah?" Ummi ta sauke idonta kasa a hankali tace "Yeah yayi maki kokari sosai shi ma, just that na lura shi ba mai son hayaniya bane, sannan miskiline, kuma na lura bai son yanda El-ameen ke yi maki, sai naga ma kamar kishi yake duk da baya cewa komai, indai El-ameen na parlon naga baya xama sai kawai ya fita, idan kuma ku biyu ne kadai ya kan xauna kusa da ke, sai dai kuma baki saki jiki da shi yanda kika yi da El-ameen ba, bai kuma san ma yanda xai kula da ke ba" Zahrah ta jinginar da kanta jikin kujera ta lumshe ido, Ummi ta kamo hannunta tace "El-ameen na son ki sosai Zahrah, duk da halin da kike ciki bai kyamace ki ba don har abinda kika kai baki yana ci....." Zahrah ta bude ido tana kallonta, murmushi ta kirkira tace "Yeah na gani" Ummi tayi murmushin ita ma ta mike ta dau Laptop din ta fice tana cewa "I just love this sweet sis, xan kai ma Abbanmu...." kuka sosai Zahrah ta fashe da bayan fitar yar uwarta, ita kanta ta rasa kukan me take ta mike da gudu ta shiga bedroom ta fada kan gado ta dinga rera kukan. Da kyar Junaid ya iya fita masallaci sallahn asuba, yana dawowa kuma yayi kwanciyarsa nan parlor kan kujera don bai jin xai iya fita aiki, ya rasa gane xaxxabin me ke son rufe sa, mikewa yayi daga karshe ya koma sama yayi wanka ko xai iya xuwa aikin, kamar kar ya fito ya ji wani sanyi na shigarsa duk da ba da ruwan sanyi yayi Wankan ba ma, ya dade kwance cikin bargo kafin ya mike ya shirya cikin kananun kaya ya dau makullin motarsa ya fita, gida ya nufa yana gama parking ya fito ya tafi bangaren Mumy kansa na sara masa, fatima ce xaune parlor da Humainah da khadija, bai iya ya amsa gaisuwar da suke masa ba ya shiga dakin Mumy, bbu kowa dakin ya kwanta kan gadon, bai yi minti biyar da kwanciya ba Mumy ta shigo, tsaye tayi bakin kofar tana kallonsa can ta karaso kusa da gadon tace "Ahmad!" Bude ido yayi yana kallonta, hannu ta daura forehead dinsa tace "Are you sick?" Mayar da idonsa yayi ya lumshe yace "Just headache mum" mikewa tayi ta fita sai ga ta ta dawo da cup din tea tace "Tashi ka sha shayin sai in baka Magani" ba musu ya mike xaune ya karba cup din ya shiga shan tea din, kadan ya rage ya ajiye, Mumy ta dauko masa paracetamol da ruwa a cup ta mika masa, ya karba ya hadiye maganin, tsaye tayi tana kallonsa don ta ma yi mamakin da ya karba maganin, mikewa yayi da sauri tace "You better don't do that...." Tsayawa yayi da farko yana yamutse fuska ta galla masa harara, sai kuma ya shige bathroom sai amai, tana nan tsaye har ya fito, bai bari sun hada ido ba ya koma ya kwanta ya lumshe ido, tace "Sai ka tashi mu tafi asibiti, saura in mun je ka gudo" girgixa Kai yayi cikin sanyin murya yace "Wllh bacci nake ji Mumy jiya ban yi bacci ba, idan na tashi sai mu je" ta kusa minti biyar tsaye tana kallonsa bata ce komai ba, har ta ga alamar bacci ya fara daukarda, karasawa tayi ta dau wayarsa ta sa masa a silent ta ajiye sannan ta fita. Sai kusan karfe sha biyu junaid ya farka da wani matsanancin ciwon kai, da kyar ya mike xaune, El-ameen ya gani dakin xaune yana hada drip ga injections a gefe guda, El-ameen ya sakar masa murmushi ya mike yace "You are awake!" Dauke kai junaid yayi yana kokarin mikewa, El-ameen ya xauna ya riko hannunsa yace "What's wrong with you, lafiya muka rabu jiya fa?" Junaid ya dake yace "ce maka aka yi bani da lafiya?" El-ameen yace "Yeah, Zahrah ma na son gaishe ka wai, I told her you are sick" daga haka ya jawo wayarsa, wani kallo junaid ke yi masa xuciyarsa na tafarfasa.
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
82.....
El-ameen ya gama danne dannensa ya Kai wayar kunne bayan few seconds yace "Hello Zahrah, here is the captain" daga haka ya mika ma junaid wayar yana kallonsa, kin kallon inda yake junaid yayi, har sai da yace "Ahmad!" Sai a sannan junaid ya kallesa yace "Did I told you am sick?" El-ameen yace "Yeah! I know you are okay, but karbi wayar...." Wani kallo junaid ke yi masa kafin ya karbi wayar ya kai kunne, gabansa ya fadi sosai jin muryarta da ya daki ear dinsa tace "Hello!" Dakewa yayi yace "Yeah, ina ji" shiru tayi shi ma haka, bayan kusan second ashirin ya kalli screen din wayar ya ga ba a kashe ba, mayarwa yayi kunnensa ya hade rai yace "Hello!" Tace "Yeah! Ina ji nima" tsaki ya ja ya katse wayar ya jefar kan gado ya juya yana kallon El-ameen yace "Kaga ka bar ja min raini gun yarinyar nan plss, ku je can ku karata ka daina sako ni a abun ku...." Murmushi El-ameen yayi yace "Alryt.... Yanxu dai bari in sa maka ruwan nan in maka allura am leaving" a fusace junaid yace "Wai ca nayi maka bani da lafiya ne, let me plss" mikewa yayi ya shige toilet ya kulle ya hade kansa da kofa, Murmushi El-ameen yayi ya fita ba a dau lokaci ba ya dawo tare da Mumy, tana kallon kofar toilet din tace "Ahmad!" Sai da ta kuma kiransa sannan ya amsa a hankali, strictly tace "Come out" ba musu ya fito jiki ba kwari ya karasa kan gadon, Mumy na tsaye El-ameen ya sa masa drip din sai a snn ta juya ta fita, El-ameen yayi 'yar dariya yace "Gaskiya ne Mumy's boy" ko kallonsa Junaid bai yi ba ya koma ya kwanta kan gado, El-ameen ya dau makullin motarsa da waya ya fita, lumshe ido Junaid yayi xuciyarsa na bugawa, bayan minti goma da fitar El-ameen aka bude kofar dakin, Humainah ce ta shigo ya bude ido yana kallonta, karasowa tayi kusa da gadon ta durkusa tana kallonsa tace "Baka da lafiya ne?" Chin dinta ya dago yana kallon fuskarta yace "How are you feeling now" a hankali tace "Alhmdllh" yace "Kina cin abinci yanxu?" Girgixa masa kai tayi ta kwantar da kanta kan gado har lokacin tana kallonsa tace "Only tea" gefensa ya nuna mata, ba musu ta mike ta dawo kusa da shi, ya daura hannu kan tummy dinta yace "Ya babyn?" Hannu ta buda masa alamar bata sani ba, yayi murmushi tayi kwanciyarta gefensa, komawa yayi shi ma ya kwanta tare da lumshe ido. Sha daya saura aka buda kofar dakin Hajjo ta shigo, fashe wa da kuka tayi sosai ta karaso kusa da gadon tace "Ya baxa ka kwanta ciwo ba ka yaudare ni ka ci amanata Ahmad, har ni xaka dinga ma bakin ciki, to dadin abun dai ni ba talaka bace, kuma dukiya me uban yawa mijina ya mutu ya bar min wanda ko da xanje makka sau dari baxa su girgixa ba, ku abun duniya ya tsole ma ido kai da uban ka" tana kai wa nan ta nufi kofa fuu, junaid ya bita da kallo har ta fita, Humainah kam murmushi tayi ta koma ta kwanta. Da yamma junaid na kwance duk ya rasa me ke masa dadi so yake kawai ruwan ya kare ya cire ya fita daga gidan ko xai ji dadi, ba don Mumy ba da tuni ya tuge drip din, Humainah na kwance nesa da shi tayi bacci tun daxu, bude kofa aka yi El-ameen da Aliyu suka shigo dakin, kallonsu kawai yake Aliyu ya karaso shi ma yana kallonsa yace "Baka ji dadi ba ashe" junaid bai ce komai ba, Aliyu ya kara da cewa Allah ya sauwake" sai a sannan yace "Ameen thank you" El-ameen yace "My frnd Dr Aliyu hope ka gane sa" Junaid bai ce komai ba ya nuna ma Aliyu kujera ya xauna, Aliyu yace "Am ohk here" El-ameen yace "How are you feeling now Ahmad?" Dakewa junaid yyi yace "Naji sauki ka cire min ynxu" El-ameen yace "No! Sai ya kare, am coming back later" Junaid ji yayi kamar ya shakesa sai dai bai ce komai ba, El-ameen yace "Idan kaji sauki in shaa Allah xuwa gobe xa ka rakani bauchi, sarki na nemana" duk da faduwar da gaban junaid yayi bai nuna ba yace "baxan iya barin aikina in je bauchi ba" El-ameen yace "Alryt, Aliyu sai ya rakani," daga haka ya juya ya nufi kofa yace "Sai na dawo ltr" ba tare da Aliyu ya kuma kallon Junaid ba yace "Allah ya kara afuwa" daga haka ya fita shi ma, mikewa xaune junaid yayi ya dafa kansa. A can bauchi kuwa Zahrah duk ta daga ma mahaifanta hankali ita fa sai an kai ta gun dattijuwar matar nan duk inda take, da farko lallabata mai martaba ya dinga yi yace ta bari xa a nemo matar a kawo ta masarautan ganin ba hakura zata yi ba yasa yace a kira masa El-ameen. Washegari El-ameen ya dau hanyar bauchi tare da Aliyu, haka kawai yaji gabansa na faduwa, addu'a ya dinga yi a xuciyarsa Allah yasa ba fasa basa auren mai martaba yyi ba, Aliyu dai sai dariya yake masa yace "Ana xaune kalau xaka jajibo ma kanka aure, auren ma daga gidan sarauta.... Tab xaka sha takaici kuwa" murmushi El-ameen yayi yace "Can xa a sha takaici ba ni ba" Aliyu yace "Ni dai don kawai ina son ganin babe din ne shi yasa xan bi ka amma bbu ruwana da neman aurenka, ni bayan Hafsat nake" El-ameen bai tanka sa ba ya kuma cewa "Toh wai yasan kana da mata kuwa?" Gyada kai El-ameen yayi yace "Yeah, I told him everything" Aliyu ya xaro ido lkci daya ya fara dariya yace "Ni i thought gidan sarauta basa bada 'ya yansu wa mai mata, Toh did your parent know about this?" El-ameen ya masa wani kallo yace "Yeah i told my dad, nd stop dusturbing me plss" Aliyu yace "Toh me yace?" El-ameen bai sake tanka sa ba har suka isa bauchi, sun jima hotel din da suka yi lodge kafin su tafi can masarautan don Aliyu yace baxai sauka gidan mutane ba, babu bata lokaci aka gabatar da su gaban mai martaba, El-ameen dai har lokacin gabansa bai bar dukan uku uku ba, duk ya kagu yaji kiran me sarki yayi masa, bayan gaisuwa sarki yace "Ina Ahmad din?" El-ameen yace "Ba tare muka taho ba, baya jin dadi" Sarki yayi masa addu'ar samun sauki, bayan few seconds yayi gyaran murya yace "Al-ameen!" Kallonsa El-ameen yayi ya kasa amsawa, Sarki ya ci gaba da cewa "Na yarda da kai na aminta da kai yasa xan hada ka da Zahrah da yar uwarta ka kai su duk inda matar nan me kula da ita take, kwana biyu kacal xasu yi a katsina idan ka tashi dawo da su kuma har da dattijuwar nan xa ku dawo" wani boyayyen ajiyar xuciya El-ameen ya sauke a hankali yace "In'sha Allah ran ka shi dade...." Daga haka ya sallamesu suka bar fadan, Wazirin sarki dake fadan yace "Is this a good decision kuwa, in suka sauka katsinan ina xai ajiye su, its not safe tafiyar su su kadai, i think gwara Abdul ya bi su" Sarki yayi murmushi yace "Da tuni sun cutar min da Zahrah" Aliyu sai dariya yake bayan sun fita yace "Tun ba ayi aure ba ka fara xama masinja, anya abun nan xai yiwu kuwa Dr...." Murmushi El-ameen yayi yace "Xa dai su xama masinja can..." Washegari da safe suka kuma daukar hanyar kt tare da Zahrah da Ummi, Zahrah dai sai kallon Aliyu take lkci lkci a jirgi, yana lura da haka can dai yace "Ya dai 'yan mata da kallo haka?" Tabe baki tayi tace "Just that you look familiar, nothing else...." Ya wara ido yace "Really? A ina kika san ni toh?" Shiru tayi kafin tace "I think... Ohk sorry it might be a dream" yana gyada Kai yace "That's woaw, a ina kika gan ni a dream din?" Kallon El-ameen dake ta kallonsu tayi tace "Wani waje, I think it's a garden... Ohh I really can't remember, yes a garden..." murmushi sosai Aliyu yayi yana gyada kai yace "It's a pleasure meeting u in dream land" bata kuma tanka sa ba ta dauke kai. Suna sauka kt El-ameen ya tare masu taxi, sun dau hanya Zahrah tace "Ina xa mu yanxu?" Kallonta yayi yace "My home, Hafsat will be glad to see you" girgixa kai tayi tace "Noo! Kai ni gun Granny din Ahmad Junaid" kallonta El-ameen ya tsaya yi, can ya lumshe ido yace "Ohk, Alryt" daga haka ya fadi ma me taxin inda xai kai su, Aliyu yace "Bari in sauka nan, kar ya rainani idan ya sake ganina gidansu" murmushi kawai El-ameen yayi yasa mai taxin yayi parking Aliyu ya sauka, El-ameen yace "Thanks frnd sai mun yi waya" d'aga ma Zahrah da Ummi hannu Aliyu yayi ya bar wajen. Suna isa kofar gidansu Junaid El-ameen ya fara fitowa sannan Ummi da Zahrah, ya ba mai taxin kudi ya kallesu yayi murmushi yace "Mu je" bin bayansa suka yi ya nufi gate. Part din Hajja ya nufa da su, khadija ce kwance parlon da Rahma mikewa xaune suka yi gaba daya suna kallonsu barin Khadija dake ta kallon Zahrah, El-ameen yace "Hajja fah?" Rahma xata yi magana sai ga Hajja ta fito cike da masifa jin muryar El-ameen, sororo ta tsaya tana kallon Zahrah, El-ameen yace "Kin yi bakuwa Hajja..." Wani shewa tayi ta karaso ta rungumeta tace "Ikon Allah, dama idan Allah ya so ka da arxiki duk nacin mahassadi sai dai ya mutu don sai kayi arxikin nan, sannu yar sarki jikar sarki, kiri kiri suka gudu suka bar ni sai gashi kin xo daukata..." El-ameen yayi murmushi ya nuna ma Ummi dake ta kallon ikon Allah kujera ta xauna, ya kalli Zahrah yace "Xan dawo da dare" daga haka ya fice daga parlon, Hajja ta rasa inda xata sa Zahrah da yar uwarta kawo wancan kawo wannan duk ta cikasu da kayan ciye ciye, Su khadija suka xama 'yan kallo, hannun Zahrah ta kama daga karshe tace "Mu je ki gaida Amina ita daya ce mata a gidan yanxu, kinsan sauran duk nasa an mayar da su gida, sbda jikokina da suka sa ma ido barin Ahmad" Ita dai Zahrah bin ta kawai take har suka shigo parlon Mumy, nan gabanta ya shiga faduwa, Fatima ce ke shara a parlon, Hajja tace "Ke ina uwar ki?" Fatima na kallon Zahrah tace "yanxu ta fita kasuwa...." Hajja tace "Toh dama wa xai aike ku ya sha takaici duk baku da amfani ai, Ahmad din na ciki har yanxu?" Girgixa kai fatima tayi tace "Yana bangaren sa" kama hannun Zahrah Hajja ta kuma yi suka fita tana cewa "Mu je ki gaida sa ba lafiya, kinsan Allah baya kyale ma ci amana da mai bakin ciki.... Toh abinda ya samu Amadi kenan" d'an murmushi Zahrah tayi duk da bata gane inda xancen Hajja ya dosa ba, bbu kowa parlon junaid haka yasa ta kuma jan ta har bedroom, ita dai gabanta ya ki daina faduwa tana biye da ita, yana xaune gefen gado idonsa na kan abinda Humainah take, sanye yake da 3qtr da singlet fari, kana ganinsa kasan har lokacin he's not his self, Humainah kuma na durkushe gabansa tana xuba masa pepper soup din kayan ciki da Mumy tayi masa, juyawa suka yi gaba daya suna kallon bakin kofar, Hajja ta washe baki tace "Amadiii...." Kallon mamaki kawai yake ma Zahrah ko kiftawa babu gani yake kamar mafarki yake, ita kanta kallonsa take ta kasa karasowa, Hajja ta janyo ta hakan yasa ta saurin dauke kai daga kallonsa Hajja tace "Mai martaba ne ya turo ta ta gaisheni...." Humainah da tayi ma Zahrah kallo daya bata kuma dago kanta ba, xuba pepper soup din kawai take ba tare da tasan abinda take ba ga wani bugu da xuciyarta yake, Can ta mike bayan ta rufe kulan xata fita Hajja ta fixgota tace "Keee baxa ku gaisa ba, me sunata kenan fatima, ita ce wanda yayanki ya ceci rayuwarta tana ganiyar hauka, baki ganeta bne..." Humainah da xuciyarta ke bugawa har lokacin ta kalli Zahrah a karo na biyu, ita kanta Zahrah kallonta take, Hajja ta kalli Zahrah tace "Kin ga matarsa kenan, ita ma jikata ce, na ma fi sonta a kan sa wllh, xan iya komai a kanta, sunanta Humainah" kasa cewa komai Zahrah tayi, ita kanta xuciyarta bugawa yake, Da kyar dai ta bude baki tace "Sannu!" Ba karamin Dakewa Humainah tayi ba na ganin ta bata amsa tace "Yauwa!" Daga haka ta fice daga dakin, Zahrah taji duk jikinta yayi sanyi, a ranta kuwa tunani take ashe akwai warce xata fi ta kyau, kallon junaid tayi taga har lokacin idonsa na kanta, ta sunkuyar da kai da sauri, Hajja da baki ya ki rufuwa tace "Toh ki karasa ki masa sannu man, amanata ya ci Allah ya kamasa kin san gudu suka yi basu je da ni ba, daxu da asuba ina idar da sllh na daga hannu biyu nace Allah na yafe masa, kila shi yasa kika gansa a haka yanxu" murmushi Zahrah ta kirkira tana jan kafa ta karasa gaban gadon da kyar tace "Ya jikin?" Bai ce komai ba bai kuma fasa kallonta ba irin kallon da na kasa fassarawa, ji tayi kafafuwanta sun gaza daukarta, ta kasa ci gaba da kallonsa, ta durkushe wajen.
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
83......
Hade rai Hajja tayi tana kallon Junaid tace "Ya haka tana gaishe ka kayi mata shiru?" Bai tanka ta ba ya dauke kansa daga kallon Zahrah da yake, Hajja tace "Ae ko a haka xaka kare, wawa ne kadai ke hali irin naka" Shi dai bai kalli inda take ba bare ta sa ran amsa, mikewa Zahrah tayi jiki a sanyaye Hajja tace "Rabu da Gantalalle" daga haka ta kama hannun Zahrah suka fita, murmushi yayi ya bi kofar da ido, can ya dauke kai ya lumshe ido ya bude, mikewa yayi ya koma parlor ya xauna. Har yamma Humainah bata koma part din Junaid ba shi ma kuma bai fito ba duk da xaman part din nasa ya ishesa, Zahrah kam na bangaren Hajja dake ta jan ta jiki kamar ta maida ta ciki, su khadija sai kallon ikon Allah suke, ko ta kan Ummi bata wani bi sai Zahrah. Bayan la'asar junaid na dawowa masallaci ya shiga part din Mumy, bbu kowa parlon ya nufi bedroom din Humainah da fatima, Humainah kadai ce xaune dakin, ya karasa yana kallonta yace "Why did you leave daxu?" Sosai ta hade rai bata ce komai ba, ya rungume hannayensa yace "Baki gane ta bane?" Kamar jira take ta fashe da kuka, ya bude ido yana kallonta, tayi mai isarta tayi shiru, yace "Ina Mumy?" Kin cewa komai tayi har sai da ya kuma tambayarta, muryarta na rawa tace "Tana gun Hajja" juyawa yayi ya fita daga dakin. A hanya ya hadu da Mumy xata koma part dinta, tace "Ya jikin!" Yace "Alhmdllh Mum" tace "Ashe bakuwa aka yi" kai kawai ya gyada mata tace "Toh da kyau, El-ameen din fa" girgixa mata Kai yayi yace "Ban sani ba Mumy" daga haka ta karasa part dinta, shi kuma ya nufi bangaren Hajja, Zahrah na xaune parlor Hajja kuma ana kitchen da fatima tana gwada mata ynda xata yi ma kajin da Mumy ta Kai masu, Ummi kuma na can daki ta gaji da hayaniyar Hajja tayi kwanciyarta, Zahrah bata ko kalli inda Junaid yake ba har ya karaso ya xauna yana kallonta ta gefen ido, jikinta ne ya bata kallonta yake ta mike xata bar parlon ya fixgota har sai da ta kusa faduwa, xaro ido tayi tana kallonsa cike da masifa sai dai kuma ta kasa masifar, bude kofar parlon aka yi ya sake hannunta, El-ameen ya shigo da sallama, sai ga Hafsat ma ta shigo parlon, kallonsu kawai junaid yake haka ma Zahrah, El-ameen yayi murmushi yayi xamansa kan kujera Hafsat ma ta xauna tana kallon junaid murmushi dauke fuskarta tace "Ina yini Captain!" Murmushin ya mayar mata yace "Lafiya lau, ya kike Hafsat" tace "Alhmdllh" Zahrah dai na tsaye har lokacin sai satan kallon Hafsat take, El-ameen yace "Meet Hafsat Zahrah, ae kin santa" sai a sannan ta kirkiri murmushi ta xauna tana kallon Hafsat tace "Sannu!" Hafsat ta mayar da murmushin tace "Yauwa, ya hanya!" Ba tare da ta kalleta ba Zahrah tace "Alhmdllh!" Hajja ce ta fito daga kitchen tana kallonsu El-ameen tace "Yaushe wa ennan suka shigo" Hafsat ta sauka har kasa ta gaida ta, Hajja ta washe baki tace "Sannu 'yar nan, ko sanin ki bn yi ba sai yau, ya gidan?" Hafsat tace "Alhmdllh" Hajja tace "Kema kin xo ganin bakuwa yar sarki kenan?" mikewa Junaid yayi ya fita daga parlon. Bai sake haduwa da Zahrah ba har washegari da yamma, yana son xuwa amma ya hana kansa fita, da yamman ranan kuma El-ameen ya kawo mama jummai gidan bayan wahalar da ya sha na nemanta, Zahrah na dakin Hajja, Hajja ta aiki khadija ta kirata bayan El-ameen yayi mata bayanin wacece mama jummai, tsaye Zahrah tayi bakin kofa tana kallon mama jummai dake rakube waje daya parlon, da gudu ta karaso ta rungume ta hawaye cike idonta cikin sanyin murya tace "Mama!" buda baki mama jummai tayi tana kallonta da mamaki, can ita ma ta rungumeta tace "Allah Akbar, kaddai ace min yar nan ta warke?" Hajja tace "Kaji wani mugun alkaba'i ko, yo so kike kiyi ta ganinta a haukace 'yar nan? Toh hankalinta daya da naki yanxu dai..." Mama jummai dake kallon Hajja tace "Ayya hajia, ae ni nama fi kowa son ganin warkewarta, ban kuma yi tunanin xan sake haduwa da ita a duniya ba...." Sai kuma ta fashe da kuka ta kuma rungume Zahrah tace "Allah sarki ne, Allah Akbar" Hajja ma ta fashe da kuka tace "Ae ni xan gaya maki wannan, sannan ina me maki albishir da cewa kin haye, ba ke ba wankau da talauchi har abada... Yar sarki sukutum ce nan kike gani jikin ki, yanxu haka kafar ki kafarta har masarautan su, wato da baki rike ta da kyau kin kula da ita tsakani da Allah ba da sunan ki asararriya yanxu, nasan har sai kin gaji da hawa jirgi xuwa makka...." Washegari da ya kama asabar su Zahrah na ta shirin komawa Bauchi har da Hajja da ta hada kayanta jaka guda, shi dai Abba bai ce mata komai ba amma da ganinsa kasan bbu yanda ya iya da ita ne, Mumy ce tayi karfin halin yi mata magana cewa bai kamata ba, nan ta balbaleta wai bakin cikin ita ma xata mata, ko a jikin junaid da in ma kayanta gaba daya xata dauka ta koma bauchi bbu abinda ya sha masa kai don abinda ya damesa a xuciya kadai ya ishesa, Karfe goma El-ameen ya iso gidan, part din Junaid ya nufa ya samesa parlor, tsaye yayi daga bakin kofa yace "Yah! Xaka rakamu bauchin ne yau?" Junaid ya kallesa yace "A wani dalili?" El-ameen yace "A dalilin tare xa mu da hajja" Junaid bai kuma tanka sa ba sae kwafa da yayi, El-ameen ya daga kafada ya juya ya fita, har part din Mumy hajja ta kai Zahrah su yi sallama da Humainah, dakin Mumy suka sameta Humainah ta hade rai sosai, tun bayan haduwarsu ranan da Zahrah ta xo gidan basu sake haduwa ba, Zahrah na tsaye daga bakin kofa tace "Allah ya kara lafiya" Humainah ta mayar mata da Amin ba tare da ta kalli inda take ba, Hajja tace "Kin san kowa da irin nasa laulayin, ita masifa ya daura mata... Mu je kawai" kallonta Zahrah ta kuma yi jin abinda Hajja tace sai kuma ta dauke kai ta fita. El-ameen ya jima tare da mai martaba bayan sun isa bauchi, ko da ya fito airport ya nufa don yana da aiki. Bayan sati biyu Junaid ya dawo daga aiki da yamma suka shigo gida kusan tare da El-ameen dake motarsa shi ma, El-ameen bai wani yi parking ba ya fito yana kallon motar junaid da ya nufi parking space, junaid ya fito El-ameen ya karasa kusa da shi yana kallonsa ganin kamar ba shi ba, can dai yace "Abba na ciki kuwa Captain" junaid yace "Ban sani ba nima, any problem" El-ameen yace "Then let me check" bin sa da kallo junaid yayi kafin ya nufi n bangaren Mumy ya gaisheta, ya tafi nasa part din. Bakwai saura junaid ya fito don xuwa masallaci dai dai lokacin da Abba ya fito tare da El-ameen, kallon mamaki junaid ke masa don bai san yana nan har lokacin ba, tunanin abinda xai kawo sa gun Abba har ya dade haka ya dinga yi amma ya kasa gano komai, ya dai nufi gun Abba ya gaida sa daga haka suka nufi masallaci gaba daya. Ko da suka dawo daga masallaci El-ameen sallama kawai yayi ma Abba ya shiga motarsa ya bar gidan, kasa daurewa junaid yayi bayan isha ya dau makullin motarsa ya tafi can gidan El-ameen, Hafsat ce ta bude kofar ganinsa tace "Sannu da xuwa captain, you came to our home today" murmushi yayi yace "Lallai kam, yana ciki?" Tace "Ehh yana ciki bismillah" hanya ta basa ya karasa xai xauna parlor tace "Yana sama ae" yace "Yi masa magana pls" tace "Study room dinsa fa yake" mikewa yayi yace "Ohk" daga haka ya haura sama, xaune ya samesa yana duba wani littafi gaba daya hankalinsa na kai, wanda hakan yasa bai dago ba don a tunaninsa Hafsat ce ta shigo, karasawa Junaid yayi, El-ameen ya dago da sauri jin turarensa, kallon mamaki yayi masa sai dai bai ce komai ba, Junaid ya xauna yace "Me ya kawo ka gidanmu daxu?" El-ameen ya buda ido yace "Yeah, Nasan ba don Allah ka taso ka taho gidana ba," sai kuma yayi murmushi yana girgixa Kai yace "it's very unfortunate Zahrah ta bata frndship dinmu, a da sati baya karewa ba tare da ka xo inda nake sau uku ba ko sau hudu, sauran kwanaki kuma ni xan je but yanxu....." Junaid ya d'an yi murmushi yace "Ae kai ma ba xuwa kake ba" El-ameen bae tanka sa ba ya ci gaba da duba littafin gabansa, junaid yace "I asked you a question..." El-ameen yace "Nothing, naje ne ya shigar min gaba gun neman auren Zahrah, as in shine waliyyina" Junaid da ya ji wani abu ya tsaya masa a xuciya ya dake yace "Why him?" El-ameen yace "Coz dad dina yace bbu ruwansa da batun auren...." Junaid ya hadiye wani abu da kyar yace "and what did he said about it?" El-ameen ya matsar da littafin gabansa yace "Yace babu damuwa idan har hakan baxae bata ma dad dina rai ba.. Nd I told him shi ma ya turo ni gunsa" mikewa junaid yayi kansa na juyawa ya kalli agogon hannunsa yace "Ohk, all good, it's getting late xan koma" El-ameen yace "Toh baka tambaye ni yaushe ne daurin auren ba?" Junaid yaji gabansa yayi mugun faduwa ya koma ya xauna xuciyarsa na bugawa sosai yace "When?" El-ameen yace "This Friday!" Kasa cewa komai Junaid yayi, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, bude kofa aka yi Hafsat ta shigo ta dire masu babban tray mai dauke da warmers din abinci ta fita sai ga ta ta dawo da wani tray mai dauke da ruwa da drinks sai cup ta fita, El-ameen yace "Mu ci abinci frnd..." Junaid yace "No! No, am ohk" El-ameen yace "Alryt then, you wait muyi shawaran abubuwan da xa ayi na bikin it's just 4 dayz left" Kallonsa kawai Junaid yake, El-ameen ya dau table water daya ya bude ya sha kadan yace "Yeah, though sarkin yace baya bukatan komai namu, amma dai mu ma mun san abubuwan da ya kamata, so ya kaga ya kamata mu yi" mikewa junaid yayi yace "Look, ka kira Faisal or Aliyu am not good at that" daga haka ya fice daga parlon, El-ameen ya bi sa da kallo yana murmushi.
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
84.....
Washegari ba karamin farin ciki junaid yayi ba ta dalilin lagos da xasu wani aiki da wasu daga cikin colleagues dinsa, kwana biyar xa su yi a can, yana dawowa da yamma ya jima part dinsa kwance kafin ya mike ya tafi gun Mumy tana kitchen ya sameta ya jingina jikin kofa bayan ya gaisheta yace "Mumy gobe xan je lagos aiki..." Kallonsa tayi tace "lagos?" Ya gyada mata kai yace "Ehh amma ba ni kadai ba, kwana biyar xuwa sati daya xa muyi" Mumy tace "Toh Allah ya tsare, ka fadi ma Abban ku?" Girgixa kai yayi yace "Anjima xan gaya masa" Tace "Toh shikenan, gobe Hajja ma xata dawo" yace "Ohk, ni da safe xan tafi ba lallai mu hadu ba" juyawa yayi ya fita daga kitchen din, har ya nufi kofa sai kuma ya dawo ya shiga dakin su fatima. Kasa bacci yayi daren ranan, sarai yasan me ke damun xuciyarsa amma ya dinga kokarin karyata hakan, tsaki ya ja daga karshe ya mike ya shiga toilet ya dauro alwala ya fita. Da safe ya gama shirinsa tsaf, kananun kaya kawai ya diba sai uniforms dinsa, ya nufi part din Mumy yayi mata sallama, tayi masa addu'ar Allah ya kai su lafiya ya tsare su, ya mike ya shiga bedroom din da Humainah take, bai fi 7 minutes ba ya fito ya dau jakarsa ya fita daga parlon, khadija ce ta rakasa har bakin gate bayan ta karbi jakarsa don driver din Abba ne xai tafi da shi gun aiki daga can sun wuce lagos, karban jakar yayi yana kallonta kmr baxae ce komai ba sai kuma yace "Su Hajiya fa?" Shiru tayi tana kallonsa, ya bude mota yace "Alryt, sai mun yi waya lil sis bye!" D'aga masa hannu tayi har motar ya bar layin. Da yamma junaid suka sauka lagos, Apartment din abokinsa Capt kabir ya sauka a barrack dinsu, wanka kawai yayi ya sauya uniform din jikinsa ya dau makullin motar kabir bbu yanda kabir bai yi da shi ya ci abinci ba ya ki, ya fita da mota duk da bbu takamaiman inda za shi, damuwa ne kawai yayi masa yawa, bai dawo gidan ba sai bayan magrib, Kabir dake xaune parlor da wasu abokansa biyu ya bisa da kallo don hannu kawai ya daga masu ya shiga bedroom, mikewa Kabir yayi ya bi bayansa, kwance ya samesa dakin yana kallonsa yace "Are you okay junaid?" Junaid yace "Yeah, just stress sai slight headache" kahir yace "Alryt Allah ya sauke, ga abinci na siyo ka ci ka sha Magani" junaid yace "Na ci abinci, drugs kuma ba sai na sha ba, idan nayi bacci xai min sauki" kabir yace "Toh shkkn" daga haka ya juya ya fita. Washegari da ciwon kai sosai junaid ya tashi, ko Kabir bai bari ya kula da halin da yake ciki ba, ya shirya cikin uniform dinsa ya daure ya sha tea kadan, Kabir yace "Ga makullin bike, don in ka fita da mota yanxu da matsala" junaid ya karbi makullin yace "No hold up No Lagos" dariya Kabir yayi yace "Exactly!" Junaid yace "Baka duty da safe ne?" Kabir yace "Yea, sai evening" Junaid yayi murmushi yace "Jin dadi" daga haka ya nufi kofa ya fita. Gaba daya a harbor ranan junaid was just absentminded, ga ciwon kansa sai karuwa yake duk ya kagu karfe hudu yayi ya gansa a gida. Biyar saura ya isa gida ko uniform bai cire ba ya haye gado dai dai lokacin da wayarsa ya dau ruri, jawo wayar yayi da kyar yana kallon screen din da kamar ya ajiye sai kuma ya daga ya kai kunne, El-ameen yace "Ashe kana lag!" Junaid yace "Yeah...." El-ameen yace "Shine bbu notice, beside you know it's not possible bikina ace baka nan, haka ka kin wnn wlkcnin lokacin da aka aura min Hafsat....." Katse sa junaid yayi yace "I will be back on Friday!" El-ameen yace "Uhm, now you are talking, har na kai mana dinki...." Lumshe ido junaid yayi trying to be calm yace "Alryt, but am busy yanxu, I want to hang up...." El-ameen yace "Ohk.... Xan kira anjima in fadi maka decision din da muka yanke da su Aliyu, i.e how everything is gonna be" Gyada masa kai kawai Junaid ya iya yi ya katse kiran ya jefar da wayar nan kan gado yayi rub da ciki ya runtse ido. A kwana biyun da junaid yayi a Lagos kowa ya gansa yasan ba karamin abu bane ke damunsa, duk ya rame ga shi ko abinci bai iya ci, bbu yanda Kabir bai yi da shi ya fadi me ke damunsa ba sai dai yace zazzabi ne, ranan laraba ikon Allah kadai ya maidosa gida daga gun aiki, Kabir dake ta shirin fita aiki ya bi sa da kallo har ya shiga daki sannan ya bisa yace "Kaga kar ma ka fara kwanciya ka taso mu tafi asibiti or I call ur mum in gaya mata" junaid bai yi masa musu ba don shi daya yasan yanda yake ji a lokacin, Kabir bai bari ya cire uniform ba suka fita xuwa NNRH dake nan barrack din, bayan sun ga likita aka yi admitting dinsa nan take, malt kawai ya iya sha a cikin abubuwan da Kabir ya siyo masa bayan an sa masa ruwa, ya kalli Kabir dake tsaye yana kallonsa yace "Don't worry frnd ka tafi aiki I will be ohk, bacci ma xan yi yanxu" sai da Kabir ya ga baccin xai yi da gaske sannan ya dau makullinsa ya fita. Washegari da safe junaid na bacci Kabir ya shigo ward din, yaga sabon ruwa ne ma aka sa masa, xaunawa yayi gefensa dai dai lokacin da wayar Junaid dake kan gadon yayi haske ta dalilin kiransa da aka yi don a cylnt wayar yake, My best ya gani jikin screen, da kamar baxae daga ba sai kuma ya dauka don yasan baxai wuce abokin da ya san sa da shi ba wato El-ameen, El-ameen na jin muryar Kabir bayan sun gaisa yace "Ahmad din fa?" Kabir yace "Ba ya jin dadi tun jiya, har ma anyi admitting dinsa clinic" El-ameen yace "Subhanallah! Ya jikin nasa yanxu?" Kabir yace "Alhmdllh, he's sleeping" El-ameen yace "Toh Allah ya sauwake, but a barrack din ku ya sauka?" Kabir yace "Yeah nan ya sauka" El-ameen yace "Alryt xan kira later" daga haka ya katse wayar, sai a sannan ya ga uban missed calls din dake wayar, ajiyewa yayi ya koma kujera ya xauna. Karfe uku junaid na xaune har lokacin da ruwa a hannunsa, shi ji yayi kamar ma kara masa ciwon ake, gashi ya kasa cin komai sai ruwa da yake sha, kabir da bai jima da shigowa ba yace "Ka dai kira gun aiki ka fadi dalilin absence dinka" kai kawai junaid ya iya daga masa, Kabir yace "Toh meyasa baka son a fadi ma su Mumy?" Shiru junaid yayi masa idonsa lumshe, kabir ya dau wayar Junaid din ta dalilin kiran da ya shigo, El-ameen ne ke kira ya kalli Junaid yace "Xa ka iya daukan kiran, it's ur frnd?" Junaid ya bude ido yana kallon wayar girgixa masa kai yayi, hakan yasa shi ya daga, bayan sun gaisa El-ameen yace "Wai jikin nasa har yanxu?" Kabir yace "Yea, muna hospital dai" El-ameen yace "Alryt! Clinic din cikin barracks din?" Kabir yace "Yeah Nnrh!" El-ameen yace "Toh Ga shi kayi ma security din ku na gate magana, I am at the gate" da mamaki Kabir yace "Kana Lagos ne dama?" El-ameen yace "Nop, I just landed" daga haka ya mika wayar, Kabir yayi masu magana sannan El-ameen ya shiga barrack din. Cikin mintunan da basu wuce 7 ba El-ameen ya isa hospital din snn ya kira Kabir ya fito ya shiga da shi, rungume hannu El-ameen yayi yana kallon Junaid can yace "Sannu, were you sick ne dama" Junaid ya kallesa yace "Am feeling much better yanxu" El-ameen yace "To ina drugs din da suka baka?" Kabir ne ya dauka ya mika masa yayi dariya yace "Kaddai ka xo ka nuna masu kai likita ne a nan fah, Kaga kai ba uniform gare ka ba" murmushi El-ameen yayi yace "Niii! Ae ko xan yi magana sai mun fita" dariya sosai kabir yayi, El-ameen ya ja kujera ya xauna yana kare ma ward din kallo, Junaid yace "Ya hanya!" Mamaki ne ya kama El-ameen ya kallesa yace "Ohh Alhmdllh! Yaushe xa su sallameka?" Girgixa kai yayi yace bai sani ba, El-ameen bai kuma cewa komai ba, ana yin La'asar Kabir ya bar clinic din don xuwa gun aiki, Washegari Friday da safe aka sallamesu daga hospital bayan ya tabbatar masu he's very okay, ko kadan El-ameen bai gaya masa ranan ne daurin aure ba duk da yasan ya sani, karfe tara ya shirya ya tafi can gun da suka xo yin aiki don shaida masu ranan xai koma kt, goma saura ya dawo ya tadda El-ameen kadai parlor yana waya, bedroom ya shiga ya hada kayansa ya fito, El-ameen da har ya gama wayar yace "Are we good to go?" Kai kawai Junaid ya gyada masa, yace "Toh baxa kuyi sallama da kabir din ba?" Junaid yace "mun yi waya da shi ya tafi ikj ba lallai xa mu hadu ba...." El-ameen yace "Ohk" daga haka ya mike ya karba jakar Junaid suka fita, junaid ya kulle masa apartment din ya ba neighbor dinsa key din, bike suka dauka xuwa airport road, bayan sun isa suka dau cab xuwa cikin airport din, El-ameen dai na ta lura da shi don ko ba a fadi masa ba yasan daurewa kawai yake, sai da suka hau jirgi Junaid ya dake yana kallonsa yace "Thought yau ne daurin auren?" El-ameen yace "Yeah! After juma'at prayer, xa ma ka iya xuwa kuwa" junaid yace "No!" Suna isa kt Junaid ya nufi gida shi ma El-ameen ya nufi nasa gidan. Part din Mumy junaid ya shiga ganin bbu kowa parlor sai tv dake kunne ya shiga dakin Mumy, xaune ya ganta a daki ya karaso ya durkusa ya gaisheta, bbu yabo bbu fallasa ta amsa tace "Ahmad ashe kai ka haifi kanka ban sani ba?" Kallonta yayi da mamaki jin abinda tace, tace "Leave immediately" kasa daina kallonta yayi lokaci daya yana tunanin me kuma yayi, da kyar yace "Mumy wani abun ya faru ne kuma?" Wani kallo ta watsa masa tace "Ka fita nace" mikewa yayi da kyar ya fita daga dakin, bedroom din su Humainah ya shiga, kwance take tana ganinsa ta mike xaune, ya karasa gadon jiki ba kwari ta mike tsaye, xai yi magana ta dakatar da shi tace "Ya Ahmad ni dai ka sake ni gaba daya bana auren kuma, idan kuma ba haka ba xan xubar da cikin nn wllh" kallonta kawai yake da manyan idonsa, can ya tabe baki ya juya ya fita daga dakin, ta fashe da kuka sosai ta sulale nan kasa ta hade kanta da gwiwa, tafiya kawai junaid yake yana son gane ma'anar abinda Mumy ta fadi masa, Muryar Hajja ne ya dakatar da shi jin irin kiran da take masa ba kakkautawa ya juya yana kallonta da mamaki, karasowa tayi fuskar nan nata a murtuke tace "Wato ai gwara kwadayina a kan taka Ahmad, tsabar naka kwadayin ya shahara 'yar gaba daya kake son aurewa kayi ma jikata kishiya, kishiyar ma jinin sarauta, dama ga Ka da taka sarautan da ka lak'a6a ma kanka tun ba yau ba, ita kuma ta xo da ta gidansu ku taru ku sa ma jikata hawan jini ta mutu in shiga uku, to ubanka yayi kadan bare kai, ban yarda da auren nan ba kuma baxa ayi ba, su rike kujerun jirginsu can baxa a je ba...."
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
85.....
Kallon Hajja kawai junaid yake don ya kasa fahimtar inda xancenta ya dosa duk ta cikasa da hayaniyar dake baraxanar haddasa masa ciwon kai, Muryar kawunsa yaji na kiransa ya juya yana kallonsa yayi masa alama da ya xo, part din Abbansa ya nufa ta bi sa tana ci gaba da xaxxaga masa bala'i shi dai bai tanka ba, bai same su parlor ba ya karasa har bedroom, hajja tayi tsaye nn parlon tana ta ci gaba da bala'i ta inda take shiga ba ta nn take fita, xaune ya samu Abbansa da frnds dinsa biyu sai kawunsa, Kawunsa wato Abban Humainah ne yace "Ahmad!" Ya dago a hankali yana dubansa amma ya kasa cewa komai. Kawun yace "Na'am mahaifin yarinyar nan ya bukaci da ka aureta, don me da ku ka dawo baka sanar ma iyayenka komai ba sai abokin ka ne ke fadi ma Abbanka few dayz back....." Kasa cewa komai Junaid yayi sai dai kansa yayi mugun daurewa, Abbansa dai sai kallonsa yake, Alhaji umar yace "Kayi shiru Ahmad, gaskiya ne Kai mijin mace hudu ne bbu wanda xai hanaka kara aure tunda kana da halin yin hakan sai dai kawai Kayi kokarin xamo me adalci tsakaninsu, amma meye na boye ma iyayenka, da nufin ka yau sai ka taho kace a tashi aje maka daurin aure, Babanka yayi ta xuba maka ido amma shiru baka ce masa komai ba...." Alhaji Habib yayi dariya yace "Kar fa ku ga laifinsa, that's what it takes to be a 1st child, wauta ne kawai irin tasa" Kawunsa yayi murmushi yace "Gaskiya ne, to Allah ya sanya alkhairi Ahmad, ae kai din mijin mata hudu ne, Allah ya baka ikon adalci" ae sai kawai Junaid ya sunkuyar da kai ya ma rasa gane wani yanayin yake ciki, yanxu ana nufin shi xa'a aura ma Zahrah, amma ai basu yi haka da kowa ba, how is this? No ya ma san kawai basu fahimce xancen bane amma da abokin sa xa ayi auren, Muryar Abokin Abbansa yaji yana ce masa ya tashi ya je, dagowa yayi da sauri cikin sanyayyen murya yace "Kuyi hakuri Abba, ni....." Kasa ci gaba yyi don bai ma san abinda xai ce ba, cewa xai yi shi bai sani ba ko kuwa ce musu xai yi ba fa da shi xa a daura auren ba, Abban Humainah yace "Tashi kaje, Allah yayi maka albarka... Ya baka ikon adalci tsakaninsu" mikewa yayi da kyar ya fita daga dakin cike da confusion to yaga ae ba fa da shi xa ayi auren ba, how is all this???? Ko kallon Hajja da ta cika parlor da muryarta bai yi ba ya fice daga parlon, ya tafi part dinsa ya dau makullin mota ya fito ya dau motarsa sai gidan El-ameen, Hafsat dake ta mopping din Balcony ta gaishesa da fara'a tace masa yana sama a study room, yana haurawa sama ya bude kofar dakin, Xaune ya samesa idonsa lumshe ya karasa gabansa yana kallonsa, bude ido El-ameen yayi ya gyara xama ganinsa yace "Yahh, xaka iya xuwa kuwa?" Junaid yace "Ahmad I don't get what my parent are telling!" El-ameen ya shafa kansa yana murmushi yace "Wai na auren ku da Zahrah?" Buda ido junaid yayi yace "Aurena da Zahrah kuma?" El-ameen yace "Yeah" xaunawa junaid yayi jin ya kasa ci gaba da tsayuwar yace "You are getting me confuse, wace Zahran...." Murmushi El-ameen ya kuma yi yace "To ya na iya maka frnd? Ban son wani abu ya sameka mu rasa ka a kan Zahrah, ni na nema maka aurenta, isn't it nyc..... Nasan yea you are in love with her..... Son da kake mata ya take nawa so I have no option then to let go, ita ma na ga tana son ka sosai shi yasa nayi haka from the beginning, nasan dai yanxu no more love sickness nd the rest, just that kar ku cuci Humainah....." Tuni idon Junaid ya kada ya kasa ce masa komai yana kallonsa, El-ameen ya dunkule hannunsa ya kamo na Junaid ya kai masa knuckle yana murmushi yace "Chop knuckle frnd" Ana saukowa juma'a aka daure auren Capt Ahmad Junaid da Princess Zahrah El-ameen Moddibo a kan sadaki 1m wanda mahaifinta ne ya bayar, daurin auren nan ya samu halartan dubban mutane da 'yan gidan masarautu da dama daga ko ina na states din Kasar duk ta dalilin Sarki El-ameen Moddibo, masarautan bauchi ya xamo bbu masaka tsinke tsabar jama'a, kusan duk manyan da suka xo daurin auren mamakin mijin Zahrah suka dinga yi ganin shi ba basarake ba, shi ba yarima ba, shi ba jinin sarauta ba, shi ba kowa ba just a mere military personnel with CLASS, ba karamin alfahari sarki El-ameen yake da junaid ba da ya xamo sirkinsa, Junaid ya gaisa da mutane da dama sunfi dari kowa son ganinsa yake ta dalilin yanda sirkinsa wato sarki ke koda sa gaban abokansa sarakai da manyan kasa, baka taba fadin yanayin da Junaid yake ciki a lkcn sai dai kawai kaga yayi murmushi wani lokacin wanda iyakarsa lips, gam yake rike da hannun El-ameen dake gefensa don bai son su rabu, Su Abba basu suka bar bauchi ba sai kusan magrib don ba karamin walima aka shirya ba, xuwa bayan isha masarautan bauchi yayi tsit baka taba cewa anyi komai ciki don tuni aka tsaftace ko ina, Junaid dake xaune daki na musamman da aka basu shi da El-ameen, Aliyu, faisal da wasu frnds dinsa biyu, ya rike kansa har lokacin don ya kasa gaskata da shi fa aka daura auren nan yau, El-ameen ya dawo gefensa yace "Toh programs kusan goma ne fa gabanmu Mr man!" Dagowa yayi da sauri yana kallonsa, El-ameen yayi dariya yace "Atoh, gwara ka bar rike kai this is just the beginning, Abdul yace ka shirya xaka gun Zahrah, wato xaka je ganin amaryar ka....." Da 'yar dariya El-ameen ya kare xancen daga haka ya shiga bathroom don watsa ruwa, Aliyu dake ta danna waya yace "Duk karya ce!" Faisal ya kallesa ya danne dariyarsa yace "Meye karyar?" Aliyu yace "Wannan ji da kan da miskilancin wani mana" dariya sosai Faisal da sauran frnds din Captain suka dinga yi, shi dai Junaid bai tanka kowa ba, El-ameen na fitowa ya shiga toilet din shima, wani kaya irin ta sarauta lafiyayye El-ameen ya ajiye masa gefen gado bayan ya fito yace "Wai kayan da xaka sa kenan suka ce" Junaid da har lokacin bai iya hada ido da abokin nasa ya shiga jujjuya kayan, can ya mike ya tabe baki yace "No, bai yi min ba" dariya sosai El-ameen yayi su Aliyu na tayasa wanda hakan yayi mugun kona ran Junaid, Aliyu yace "Ae ko ka ki malam dole haka xaka sa, coz that's the rule tunda gidan sarauta kayi auren" sai a snn Junaid ya kalli El-ameen ya hade rai sosai yace "Nooo, bbu wanda xae dinga kafa min rule, snn bbu wanda ya isa yyi forcing dina...." Aliyu ya fashe da dariya yace "Duk karya ce wnn" El-ameen da ya kasa daina dariya yace "See you. Ka dinga bin rules kenan har sai an kai maka matar ka can gidan ka" Junaid bai tanka sa ba xai dau kayansa ya sa El-ameen ya kwace kayan yace "Kasan Allah kar fa ka dinga mana taurin kai nan" faisal yace "Look Capt you just have to obey before complaining as a good militant, idan ka bar nan naga bbu wanda xai bi ka yace ga yanda xaka yi koh?" Daukan kayan Junaid yayi ya fita parlor don sa wa, Aliyu ya fashe da dariya yace "Wato abun sai da lallaba," ko da Junaid ya dawo dakin duk kallonsa suka tsaya yi don sak yarima ya dawo, yayi kyau ba kadan ba, Aliyu yace "Uhm yarima junaid, ka hadu" junaid bai tanka sa ba, misalin karfe tara da wani abu aka doka sallama can parlor El-ameen ya fita, wata yar dattijuwa ce tsaye ta duka har kasa ta gaishesa tace "Ance in yi ma ango iso har gun Gimbiya Zahrah" El-ameen ya juya ya koma daki yace "Toh an xo daukar ka Capt, if you like go nd misbehave mu dai muna nan" sae da junaid ya ga dama sannan ya mike ya fita, dattijuwar na gaba yana biye da ita a baya, haka kawai yaji gabansa ke faduwa, tafiya me nisa suka yi har suka iso wani babban kofa ta bude kofar suka shiga wani parlor me girman gaske xama yayi parlon ita kuma ta karasa ta bude wani kofa ta shiga ciki, ba a dau lokaci ba ta fito ta risina tace "xaka iya shiga ranka shi dade" mikewa yayi ya nufi dakin har lokacin gabansa bai bar faduwa ba, yana shiga dakin wani sanyayyen kamshi ya doki hancinsa bai san lokacin da ya rufe kofar ba ya juyo ya sauke idonsa kanta.
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
86___87
Ya kusa minti biyar tsaye bai karasa cikin dakin ba, tun da ya kalleta sau daya bai sake kallon inda take ba, xaune take kan hadadden Royal bed din dake dakin ta daura har kafafuwanta kan gadon, har wani daukar ido take tayi wani kyau na musamman, hannunta da ya sha hyena na rike da waya tana ta danne danne, ko sau daya bata kalli inda yake ba, can dai ya karasa gadon cikin takunsa na kasaita ya xauna ya fiddo da tasa wayar yana dannawa, ajiye wayar hannunta tayi ta mike ta nufi gaban mirror, bin ta da ido yayi bayan ta wuce sa, lokaci daya gabansa ya shiga bugawa, wani ubansun fitted gown ne jikinta gold colour yana jan kasa, kasa daina kallonta yayi har sai da yaga xata juyo sannan ya dauke kansa, wucesa ta kuma yi hannunta rike da laptop, ta koma kan gadon ta xauna ta kunna laptop din, tabe baki yayi lkci daya yayi d'an murmushi yace "Za ki iya da halina" kallonsa tayi a karo na farko tace "Nima xaka iya da nawa halin?" D'ago kai yayi ya kalleta ta gyada masa kai tace "Yeah!" Murmushi yayi yace "Ke har kina da halin da baxan iya da shi ba" murmushi ita ma tayi tace "Toh nima baka da halin da baxan iya da shi ba...." Gyada kai yayi har lokacin murmushi dauke fuskarsa sai dai bai ce komai ba, sun kusa minti sha biyar xaune bbu wanda yace komai, ita dai sai danna laptop take, satan kallonta yayi dai dai lkcn da ita ma ta dago suka hada ido, ji yyi dama hakan bai faru ba, ya wayance da sauri yace "Amm, lastly xa ki iya da halin matata" jingina tayi jikin gadon ta matsar da laptop din gabanta ta tabe baki tace "Bata da halin da xai daga min hankali, sae ma dai ita ce baxata iya da nawa halin ba" mikewa tayi ta hade rai lokaci daya tace "Kar ka kaga ka sameni kusan a banxa ka dauke ni for granted, ka xo kana gaya min magana yanda ka ga dama, you know who I am, kuma ni ba don ina sonka na yrda da auren ka ba sai don kawai in maka halaccin abinda ka min, in kuma yi ma Abbana biyayya, banda haka nafi class din ka, snn ni ba gidanka xan xauna da matar ka ba, Abbana zai siya min gidan da xan xauna, nafi karfin xama tare da ku....." Tunda ta fara magana yake kallonta da mamaki, furucinta na karshe yasa ya mike yana mata wani kallo yace "Who are you? A princess? Just that????" Dariya yayi wanda hakan ya kara fito da ainahin kyansa, ta tsaya kallonsa ko kiftawa bbu, ashe yana dariya dai, ya shafa kansa yana kallonta daga sama har kasa murmushi dauke a lips dinsa yace "Ba ki da gun xama da ya wuce gidana tare da matata, idan an siya maki gidan sai ki ajiye shi aside kiyi xaman auren da ya kai ki kt a gidana!" Kallonsa take tana huci tace "Baxan xauna gidan ka ba, nafi karfin xama tare da matar ka, my dad will get me a house......" D'aga kafada yayi yace "Toh xan ga ko kece mijin...." Shiru yayi sai kuma ya juya yana mamakin kansa anya ma tunda yake ya taba tsayawa yana exchanging words da namiji dan uwansa bare mace, abinda bai taba ba kenan duk tsawon rayuwarsa, juyawa ya kuma yi yana kallonta, tabe baki tayi hade da murguda baki tace "Sai mu gani ai ko ni xan xauna gidan ka" bai tanka ta ba ya koma ya xauna cike da jin haushin kansa kulatan da yyi tun farko ya kalli makeken agogon dake manne bangon dakin ya ga goma saura yan mintuna dai dai lokacin da dattijuwar daxu ta rafka sallama can parlor, mikewa yayi ya nufi kofa ya fita, wnn karan su biyu ne, suka duka har kasa tana masa sannu da fitowa, kai kawai ya gyada masu ya fice daga parlon, ko da ya koma inda aka saukesu bai ko kalli su El-ameen da Aliyu dake xolayarsa ba ya shige bedroom. A kwanaki ukun da suka gabata ba karamin Buduri aka sha a masarautan bauchi ba sai ka rantse baxa a mutu ba, safe, rana, dare sae an samu wani program da aka ce xa ayi kuma duk ba na wasa ba, kudi kam sun yi kuka ba kadan ba wanda hakan xai tabbatar maka da cewa ba karamar yar gata bace Zahrah, abun mamaki ya dinga ba junaid don ko kadan bbu abinda ya burgesa a shagalullukan da aka yi duk ya kagu a kyalesa ya bar garin, sai dai fa shi kansa yasan jin sa yake daban idan ya tuna Jasmine matarsa ce ynxu. Ranan talata aka yi program din karshe da suka kira shi da farewell princess Zahrah, shi dai Junaid na xaune gun ne idonsa a kan wayarsa da yake ta dannawa, yawan ci gun duk 'ya 'yan sarakai ne, princesses din sun gama yrda cewa mijin Zahrah duk da he's not from royal home is just classic, cute and very handsome bbu warce xata ce taga dariyarsa tun fara events har xuwa ranan sai dai murmushi da iyakarsa lips, da ganinsa kasan baya son hayaniya, har wani farin ciki Zahrah take idan yace baxai xo gun event ba tsabar haushin kallon da taga mata ke masa, don a duk events din da aka yi guda uku kadai ya yrda da kyar aka yi da shi sai wnn na karshen, sai ka rantse El-ameen ne angon don yawanci shi kedaukan post din Junaid, duk da Junaid waya kawae yake dannawa amma hankalinsa gaba daya na kan Zahrah as in kyan da tayi na musamman ne ranan, sae wani sheki take cikin lafiyayyen sliver gown me adon stones din dake jikinta, satan kallonta kawai yake wanda duk El-ameen na lura da shi yana dariya, sai kusan magrib aka tashi taron. Bayan isha mai martaba yasa aka kira masa Junaid, Junaid ya nemi gu ya xauna a babban parlon sarkin kansa a kasa, mai martaba yace "Dama ina son sanar da kai nasa a nema min gida a can katsina da Zahrah xata xauna, hakan ya maka ko" Junaid ya d'ago yana kallonsa, duk da yanda ransa ya bace bai nuna ba, cike da ladabi yace "Ae ina da nawa gidan ranka shi dade" Sarki yace "Eh nasan da haka Ahmad, amma ina ga hakan xae fi gwara tayi xamanta a nata gidan....." Mamaki ne ya cika junaid, yayi shiru na kusan minti daya kafin yace "Amma bana son rabasu da 'yar uwarta ranka shi dade.... Nafi son su xauna tare" sarki yace "A'a ina jin xaman su daban daban xai fi...." Junaid ya kuma kallonsa yana kokarin danne bacin ransa yace "I think it's not proper ita kadai ta xauna gida...." Mai martaba yace "Hakan yasa xan tura mata bayin da za su xauna da ita, in kuma hadasu da jakadu biyu" Junaid bai kuma cewa komai ba, sarki yace "Hope it's ohk...." Dakewa junaid yayi yace "Toh xan so ace gidana aka fara kai ta kafin ta tare can gidan" Sarki ya d'an yi shiru sai kuma yace "Ohk, but baxata wuce kwana biyu gidan naka ba" Junaid ya gyada masa kai yace "In'sha Allah" Sarki yace "Toh bbu damuwa" junaid bai jima parlon ba ya mike ya fice bayan sarkin ya basa shawarwari masu ma'ana, takaici ya ishesa lkci daya maganan Aliyu ya fado masa da yake cewa ae an fara kafa masa rule kenan tunda 'yar gidan sarauta ya aura, wani tsaki ya ja a xuciyarsa yace ba shi Ahmad din ba knn. Washegari misalin sha daya suka dau hanyar kt, sai ka rantse kace maida masauratan bauchi xa ayi katsina gaba dayanta Tsabar tawagar da aka yi don kai Zahrah gidan mijinta, Kai da gani kasan Gimbiya xa a kai daki, direct gida Junaid ya nufa don bai ma son yaje can gidan kansa ya fashe, bbu kowa gidan sai Hajja, Humainah da Mumy sai wasu frnds din Mumy wa enda basu je can tarban amarya ba, duk sisters din Mumy na can gidan da su fatima, bbu wani wanda ya amsa gaisuwarsa da mutunci ya nufi bangaren sa kawae, Hajja ce ta bisa har bedroom yana kokarin cire kayan jikinsa tace "Wato munafukin sarkin nn dan ya toshe bakina shi ne har da wani yi ma Humainah kayan daki da lefe irin ta yar sa koh, to yyi a banxa don ni bbu ruwana da wnn, kuma idan baka yi hankali ba sai nasa an ma uwarka kishiya kai ma irin yanda ka yi ma jikata," Murmushi junaid yayi yace "Toh ai ba haramun bane" daga haka ya shige toilet ya bar ta nn tsaye. Sai kusan yamma El-ameen ya zo gidan da Aliyu. Karfe shidda da wani abu Abba yasa a kira masa Humainah, tana isa parlon ta nemi jikin kujera ta xauna daga kasa, kallonta kawai Abba yake cike da tausayinta, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Abba ga ni" ya nisa yace "Kina jina Daughter" kai kawai ta gyada masa yace "Kiyi hakuri kin ji, matukar ina raye baxan taba bari Ahmad ya kuma walakanta ki ba, ki dauka auren ki da shi kaddara ce don biyayya kika mana, promise me ba ke xaki xamo tsilar ko wani tashin hankali da xae faru a gidan auren ku ba, you promise me xa ki xamo mai kauda kai a komai...." Hawaye ne ke sauko mata tace "I promise Abba" maganganu masu kwantar da hankali Abba ya dinga mata, wayarsa ya dauka daga karshe ya kira Junaid yace ya samesa parlonsa, ba a dau lokaci ba Junaid ya iso parlon, kallo daya ya masu bai kuma dago kai ba har ya nemi waje ya xauna daga kasa shi ma, kallon Humainah Abba yayi yace "Tashi ki je ki shirya ku wuce gida" ba musu ta mike Junaid ya bi ta da kallo har ta fita, Abba ya juya yana kallonsa yace "In ma kun cuceta kai da Allah, kuma I assure you baxae bar ku ba, more especially kai, I won't say anything more than this, tashi ka je" kasa cewa komai Junaid yayi bai kuma iya ya dago kansa ba, can dai ya mike yace "Nagode Abba" daga haka ya fita daga parlon ya tafi bangaren sa, bai tarda su El-ameen ba wanda hakan ya tabbatar masa da cewa wucewa suka yi, ya gama shirinsa ya fito, ya jima tsaye yana jiran fitowar Humainah ganin bata fito ba ya shiga ciki, bedroom dinsu ya shiga ya sameta xaune kasa ta hade kai da gwiwa, karasawa yayi dakin ya isa kusa da ita ya durkusa yana kallonta murya can kasa yace "Humainah!" K'in dago kanta tayi hakan yasa ya dago yana kallon fuskarta da ya wanke da hawaye, finger dinsa yasa yana share mata hawayen kmr me rada yace "Am...am sorry wife.... You.... have a special place in my heart!" Dago idanuwanta da suka rine tayi tana kallonsa, ya sakar mata wani lallausan murmushi ya lumshe ido ya kai mata light kiss a lips dinta, kasa kallonsa tayi ya mike ya daga ta ya dau hijab dinta ya mika mata ta karba ta sa, ya dau karamar jakarta yana rike da hannunta suka fita, dakin Mumy ya nufa da ita, Mumy dake xaune da frnd dinta tayi masu kallo daya ta dauke kai, durkusawa yayi nan gabanta, Humainah ma ta durkusa yace "Mumy xa mu tafi" sai a snn ta kalle su tace "Allah ya kiyaye hanya!" Mikewa yayi suka fita daga dakin Hajiya Karima na masu Addu'ar xaman lafiya, ana kiraye kirayen Magrib suka isa gida, su sisters din Mumy na gidan har lkcn da wa enda suka kawo amarya su kusan bakwai, junaid dai na dawowa daga masallaci ya shige bedroom dinsa ya sa key, sai da 'yan uwan Mumy suka yi magrib a gidan snn suka fara shirin tafiya, sai kuma da suka tabbatar Humainah ta kwantar da hankalinta snn suka je suka ma Zahrah da mutanen dake dakinta sallama suka tafi. Humainah na ganin sun tafi ta fito daga bedroom dinta don ko kadan abinda Abban Zahrah yasa aka mata bai burgeta ba, wani dakin daban ta bude ta shiga tayi kwanciyarta. Zahrah kam bacci ta dinga yi a daki don tunda suka isa kt take mitan ciwon kai, yan uwanta nata harkokin gabansu a makeken dakin, da ganin yanda suke abubuwa kaga jinin sarauta, bayan Isha junaid ya bude dakinsa ya sauka downstairs, ya jima xaune parlor kafin ya koma sama ya nufi dakin Humainah ganin bata ciki ya fito ya kwankwasa wanda Zahrah ke ciki hade da yin sallama, sai da aka amsa masa sannan ya bude kofar ya shiga, wani arnen kamshi ne ke tashi a dakin, ya duka har kasa ya gaishesu, suka amsa masa ba duka ba, daga nan kuma ya rasa abinda xai ce, Kanwar mai martaba tace "Mun yi xaton kamata yayi ace tun da muka iso garin nan ka xo duba mu, ga Fatimar can tana fama da ciwon kai, ae ba haka ake ba, muna sauka sai ka taho ganin yanda muka isa" bai dago ba bare ta sa ran amsa, sistern Kilishi tace "Kila haka suke abubuwansu" mikewa yayi har lokacin bai kalli kowa ba yace "Bari a samo mata Magani" daga haka ya fita. Bayan kusan minti goma sha biyar ya dawo dakin ya mika ma Ummi dake dakin maganin ba tare da ya hada ido da kowa ba yace "Amm akwai bedrooms dake a gyare....." Wata kawar Umma tace "Ae baxa mu bari ta kwana ita daya bane, nn ya wadatar!" Bai ce komai ba ya juya ya fita. Dakinsa ya shiga ya dau wayarsa ya shiga kiran El-ameen, bugu uku ya dauka tare da cewa "Angon Zahrah!" Shiru Junaid ya d'an yi kafin yace "Baxa ka xo ba kenan?" El-ameen yace "In xo in maka me?" Junaid yace "Just come over plss" El-ameen yace "Alryt, amma sai Hafsat tayi bacci" Junaid ya d'an bude ido yace "Ohh tsoron ta kake?" Dariya El-ameen yayi yace "Eh mana, in kuma bata yi ba sai gobe" murmushi Junaid yayi yace "Toh shknn sha xaman ka tare da Hafsat, goben sai kaxo" El-ameen yace "Ya ma fi komai sauki, a gaida min amarya" Junaid yace "Uhmm, good nyt!" Daga haka ya katse wayar ya ajiye, Sha biyu saura ya fita ya shiga dakin Humainah yaga bata nan still, mamaki ne ya kamasa ya karasa ya tura bathroom nn ba yaga bbu ita, fitowa yayi ya bude dakin kusa da wnn ya sameta kwance tana bacci, karasawa yayi ya xauna gefen gadon yana kallonta, can ya daga kafada shi ma yyi kwanciyarsa dakin. Washegari da safe Humainah ta sauka kitchen don hada breakfast, shi kuma sai da yyi wanka ya shirya snn ya fito ya shiga dakin da su Zahrah suke, yau ma ba duka suka amsa gaisuwarsa ba, yayi ficewarsa daga dakin addu'arsa kawai kada su kara ko da awa biyu a gidan, hakan ko aka yi don ko break din basu yi na kirki ba suka fara shirin tafiya, Humainah dai faram faram tayi masu ta shiga dakinta, da suka Tashi tafiya dubu dari uku Junaid ya basu suka ki amsa cike da gadara, bai sake bin ta kansu ba ya maida kudin sa, Airport ma yace xai kai su suka ce aa, Kanwar Abba ce ta sake jaddada masa cewa gobe fa xai kai Zahrah can gidanta don gobe bayinta xa su iso, su ma baxa su iya xama a garin har gobe bane shi yasa xa su koma, toh kawai yace masu duk suka bar gidan. Bayan tafiyar su da minti talatin ya mike ya haura sama xuwa dakin Zahrah, a hankali ya tura kofar dakin ya ganta xaune ta hade kai da gwiwa, kallonta ya tsaya yi can kuma ya karasa ciki ya xauna gefen gado, ita dai bata dago ba, ba tare da ya kalleta ba yace "Hope xa ki iya fitowa in maki introducing matata" dagowa tayi da sauri tana kallonsa tace "Nop, just get me out if this house ka kai ni gidana!" Ta gefen ido ys kalleta yace "Dama kina da gidan da ya wuce wnn?" Tace "Yess gidan da Abbana ya siya min!" Murmushi yayi yace "Idan ba haka ba ki min me?" Wani kallo ta watsa masa tace "Idan ba haka ba in kura Abbana in sanar da shi yanxu" juyawa yayi yana kallonta yaga iPhone din dake gefenta ya mike ya isa gabanta, ita dai kallonsa kawae take, ya dau wayar yace "Toh na raba ki da rike waya a gidana!" Mikewa tayi da sauri tace "Ae ba kai ka siya min wayan ba naga dai...." Wani kallo yake mata kawai ya nufi bathroom binsa da kallo tayi na kusan minti daya can ta mike da sauri jin kamar ruwa yake tarawa, tsaye ta gansa hannunsa rike da wayar dayan kuma sim card dinta, juyawa yayi ya kalleta kafin ya jefa wayar cikin ruwa, sim din kuma ya balla yace "Ba gidana xa a dinga kafa min sharadi ba!" Wani kara tayi ta karaso da sauri ta fixgosa tace "How dare....." Kasa ci gaba tayi sbda kallon cikin ido da yayi mata, ta fashe da kuka ta juya da sauri ta fita. Juyawa yayi shi ma ya fita bai ko kalleta ba ya fice daga dakin sai dai can kasar xuciyarsa ji yyi kmr an buga masa guduma kukanta dake dukan ears dinsa, kasa shiga dakinsa yayi, can kawai ya juya ya koma dakin nata.
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
87___88
Durkushe ya ganta a dakin tana kuka, tana ganinsa ta hadiye kukan ta hade rai sosai, hade rai shi ma yayi yace "Did you just say something?" Mikewa tayi tana masa wani kallo tace "We the royal blood don't say things twice...." Dariya sosai ta basa, sai dai ya dake bai yi ba ya Karasa gabanta yana kallonta, ko dar bata nuna ba duk da a tsorace take ganin yanda fuskarsa ke a daure, wani murmushi yyi yace "Mind you gidan Capt Ahmad ne nn ba so called royal home din ku ba" tabe baki tayi ta juya masa baya tace "I don't care where I am, I Still remain who I am..." kallonta ya shiga yi daga sama har kasa can ya gyada kai yana murmushi ya juya ya fita. Da rana El-ameen ya xo gidan, suna xaune parlor da Junaid ganin bai ga Zahrah ba sai Humainah dake kitchen, yace "Captain rowar ganin amaryar ake min" Junaid ya mike yace "Noo Not at all..." Daga haka ya haura sama ya tura kofar bedroom dinta, xaune ya sameta tana ganinsa tayi saurin goge hawayen fuskarta ta dauke kai, daga nn bakin kofa yace "ki fito ku gaisa da El-ameen.... Miss Royal being" wani kallo ta masa sai kuma ta mike ta dau hijab ta saka tayi ficewarta daga dakin ta bar sa tsaye, da murmushi fuskarta suka gaisa da El-ameen sai dai bata yrda sun hada ido ba, El-ameen na ganinta yasan kuka tayi, kallon Junaid da ya tsiri danna waya yyi sai dai bai ce komai ba, ita kuma ta mike, da har xata koma sama sai kuma ta nufi kitchen, Humainah dake hada stew ta kalleta ta dauke kai ta dalilin faduwa da gabanta yayi, Zahrah ta dake tace "Sannu da aiki" Humainah tace "Yauwa, thanks" kallon kayan lambun dake ajiye kitchen din Zahrah tayi ta karasa ta dauka ta nufi washing basin ta shiga wanke su, ita dai Humainah bata ce komai ba sai satan kallonta take, har ta gama wanke su ta dauki chopping board da wuka ta shiga yankasu, bayan kusan minti goma Zahrah tace "Ki ara min wayar ki" Humainah tace "Yana daki" har suka gama aikin bbu wanda ya sake cewa komai, ko da Zahrah ta dawo parlor bata ga El-ameen ba alamar ya wuce, sama ta nufa Junaid ya bi ta da kallo don yyi mamakin kitchen da ta shiga, can Humainah ma ta fito ta nufi sama ita ma ya bi ta da ido can ya mike ya bi bayanta, Zahrah na haura wa sama dakin da tasan na Humainah ne ta bude ta shiga, can kan gado ta ga wayar ta dauka ta xauna gefen gado, Humainah ta shigo dakin, sosai tayi mamakin ganinta xaune dakin, bata ce komai ba ta tafi gaban mirror, Bude kofar aka yi Junaid ma ya shigo, still yyi bakin kofa yana kallon Zahrah, kallo daya tayi masa ta dauke kai, ta mika ma Humainah wayar tace "bude min pattern" Humainah ta karba Junaid ya fixge wayar hannunta yana kallon Zahrah yace "Wa xa ki kira?" Ba tare da ta damu ba tace "Abbana" juyawa yayi ya fice da wayar, tabe baki tayi ta kalli Humainah ta mike ta nufi kofa, Humainah ta bi ta da kallo har ta fita ta juyo tace "Idan kin xuba abinci ki kira ni, we don't eat alone at home" daga haka ta fita, mamakinta sosai Humainah ta dinga yi, tana xuba abincin kuwa ta dawo sama ta bude kofar dakinta ta kirata, mikewa Zahrah tayi ta fito suka sauka kasa a tare, nan kan carpet Humainah ta ajiye masu abincin, Zahrah ta xauna ta tankwashe kafa ta dau spoon ta fara cin abincin, xaunawa Humainah tayi ita ma ta dau cokalin ba tare da ta kalleta ba ta shiga cin abincin, Zahrah ta d'an kalleta tace "How month pregnant are you?" Kallon mamaki Humainah tayi mata da kmr baxata tanka ta ba sai kuma tace "five" Zahrah ta langwabar da Kai tace "Ohk.... But me yasa mijin ki yake behaving yanda yake yi?" Humainah bata kalleta ba bare ta sa ran amsa, aka bude kofar parlorn Junaid ya shigo don dama yana waje, kallon mamaki yake masu can ya karaso parlon ya xauna yana kallon Humainah yace "Did you cook with me" kan tace komai Zahrah ta amshe tace "Of course No, not with her condition, just go get something outside to take!" Kallon Zahrah kawai yake can ya mike ya nufi stairs sai a snn yayi murmushi ya haura sama. Da daddare Zahrah na fitowa daga wanka ta xauna gaban mirror don yi shafe shafenta aka bude kofar dakin, duk da ynda gabanta ya fadi hakan bai sa ta juyo ba sai shafa lotion dinta take, tsaye yyi bakin kofar yana kallonta, ta gama shafanta ta mike ta nufi kan gado don daukar sleeping wear dinta, bin ta yyi da ido har ta dau kayan, ganin cire towel din xata yi yasa shi juyawa ya fice daga dakin ya rufo, murmushi tayi a xuciyarta tace you should have stay, tana gama shirya wa ta fito ta shiga dakin Humainah, Humainah dake kwance don ta gaji bayan dinner da ta girka ta bi ta da kallo, kwata kwata ta ki sakewa da ita, Zahrah ta xauna kan gadon ta dau remote tace "I hate staying alone... We don't do that at home" powering din Tv tayi ita dai Humainah bata ce mata komai ba. Daga karshe rufe ido ma tayi kmr ta fara bacci, xaman kusan minti talatin Zahrah tayi can tayi kwanciyarta kan gadon, bude ido Humainah tayi da sauri tana kallonta, ta gyada kai tace "Yeah, I am spending the nyt here" Humainah bata ce komai ba ta rufe idonta kuma, Zahrah ta gyara kwanciyarta ta ja duvet ta ci gaba da kallonta, bude kofar dakin aka yi Junaid ya shigo, ya buda ido yana kallon Zahrah, ko kallonsa bata yi ba idonta na kan tv, Humainah dai tayi kmr bacci take, juyawa yyi kawai ya fita daga dakin. Washegari da asuba Humainah ce ta fara tashi ta tada ta, sllh tayi ta fita ta bar ta dakin ta tafi kitchen, tana fita Junaid ya shigo, ya hade rai yana kallon Zahrah da ke kan darduma yace "Me ya shigo dake dakin matata, don ki koya mata girman Kai da unnecessary Royalism din ki koh?" Bata ko kallesa ba bare ya sa ran samun amsa, sosai hakan ya kona masa rai ya daka mata tsawa yace "Ba magana nake maki ba kika kyaleni" nn ma dai ko kallon gefen da yake bata yi ba, juyawa yyi ya fice daga dakin xuciyarsa na tafasa, sai a snn ta kalli bakin kofar ta gefen ido ta mike, ita ma ta fita ta shiga bedroom dinta tayi wanka ta shirya cikin wani lace mara nauyi da ya amsheta sosai, gyara dogon gashinta tayi ta daure a baya ta bar dankwalin a kafada ta sauka, ba wani aiki ta taya Humainah ba sai tambayoyi da ta isheta da shi kmr yar jarida, Humainah ta jera komai kan dining Zahrah ta xauna tana kkrin daukan cup tace "Yanxu sai ki je kiyi wanka kiyi kwalliya wa mijin ki..." Humainah bata ko kalleta ba ta wuce sama, tana tafiya sai ga junaid ya sauko cikin shirin Uniform, har ya karaso dining din idonsa na kanta, shayin ta kawai take sha, ya ja kujera ya xauna ya hade rai yace "A royal Home din ku ba'a koya maki gaisuwa ba ne koh" bata dago kai ba bare ta tanka sa sosai haka ya kona masa rai, sai a snn yasan ashe shariya na da ciwo, wani tsawa ya mata yace "Kee!" Dago manyan idonta tayi ta hade rai tana kallonsa can ta mike ta kwabar da cup din tean hannunta ta nufi sama kmr xata tashi sama, bin ta da kallo yyi baki bude, tunda yake shi mace bata taba yi masa haka ba, fasa breakfast din ma yyi gaba daya ya koma sama ya dau wayarsa da car key ya bar gidan. Sai wajen biyar ya dawo gida har lokacin ransa ba dadi, xaune suke parlor tana gyara Humainah gashi, ya wani hade rai yace "Duk ku bar parlon nn Immediately" ba tare da Zahrah ta kallesa ba tana ci gaba da combing gashin Humainah tace "And may we know y?" Karasawa parlon yyi cikin tsawa yace "ku bar min parlor nace" Zahrah ta yatsine fuska ta kwashi kayan gyaran gashin tace "it doesn't call for shouting! Maman baby tashi mu je" Humainah ta tabe baki ta tafi sama, Zahrah ta bi bayanta, xaunawa yyi kan kujera yana tunanin hukuncin da xai dauka kan Zahrah bai taba tunanin shariya da daukan kai na da ciwo ba sai ynxu, ranan ma tare Zahrah ta kwana da Humainah, shi dai bai ce masu komai ba, washegari ya gama shirin fita aiki ya sauko downstairs ya samesu tare suna breakfast, yana kallon Zahrah yace "Royal being, har yanxu bayin na ki basu iso bane ko dama kawai fadi aka yi" ko kallon inda yake bata yi bare ta tanka sai cin potatoe da ketchup dinta take, tsaye yyi yana kallonta, can yace "I can see you are deaf..." mikewa tayi irin ya takurata din nn a fusace ta yi hanyar stairs, bin ta yyi ya fixgota ya hadata da jikinsa kan yace komai cike da tsiwa tace "Me yasa ka fiye takura ne Mr man, get away from my life, i hate disturbance, I don't want...." Bai bari ta kai karshe ba sai jin kiss tayi, Humainah dake kallonsu dama dauke kai tayi ta ci gaba da jujjuya potatoe din gabanta, turata yayi yana mata wani kallo sai kuma ya juya ya nufi kofa da sauri, bin sa da kallo tayi a tsorace, can ta saci kallon Humainah sai kuma ta tafi sama da sauri, Junaid ya kusa minti goma xaune cikin motar kafin ya tada motar ya bar gidan. Har rana Zahrah bata fito ba, wajajen Karfe uku ganin ta fara jin yunwa ta fito daga dakin, bbu kowa parlon ta shiga kitchen ta hada tea ta fito ta dawo sama dai dai lokacin da Humainah ta fito daga dakinta, har Zahrah xata mata magana sai taga ta wani hade rai kmr bata ganta ba ta sauka kasa, Zahrah ta juya ido hade da tabe baki ta shige dakin ta. Da yamma kusan a tare Junaid ya shigo gidan da Hajja, ya wani hade rai ganinta, ita din ma ko amsa gaisuwarsa bata yi ba ta shige parlor tana kwala ma Humainah kira, Humainah dake kwance daki ta fito da sauri jin muryar Hajja, rungumeta tayi cike da jin ddin ganinta, Hajja ta turata tana kallonta daga sama har kasa tace "Ramar meye wnn Humainah, daina baki abinci yyi don yyi aure ko yaya?" Humainah tayi 'yar dariya tace "Ni ba Ramar da nayi Hajja" Hajja ta kalli sama murya can kasa tace "Yar sarkin na sama koh?" Humainah ta gyada mata kai kawai, Hajja ta tabe baki tace "Xata ci ubanta, ko da kuwa shugaban kasa ne uban nata...." Shigowar Junaid ya sa tayi shiru ta balla masa harara, dai dai lokacin da Zahrah ta sauko jin muryar Hajja, hajja ta tsuke fuska sosai, daga inda take tsaye ta gaida ta Hajja ta saki salati tana tafe hannu tace "Yanxu 'yar nn kya gaida Uwar da ta haifi uwar ki a tsaye?" Kallonta kawae Zahrah take, Hajja tace "Toh wnn ba dab'iar arxiki bane, don da Humainah ce ko kaffara baxan yi ba baxa ta yi haka ba, ba fa masarauta kike ba yanxu!" Wani kallo junaid yake ma Hajja don ji yyi kmr ya shaketa, Zahrah ta juya ta koma sama, bin bayanta yayi Hajja tace "Munafuki, hbayaala har ta fara girki ta basa yaci ne?" Humainah dai bata ce komai ba Hajja ta ce "Toh shi ma xae ci uban nasa ne" tsaye Junaid ya ganta gaban mirror, da kmr baxae karasa ba sai kuma ya karasa kusa datace ita, juyo da ita yyi yana kallonta yace "Me yasa kika gaisheta a tsaye!" Bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, tambayar ya kuma maimaitawa nn ma dai shiru kke ji, a fusace yace "Don me xan dinga maki magana kina share ni" ga mamakinsa har lkcn bata kalli inda yake ba, ya fixgota yace "Wllh na sake maki magana kika share ni I will..." kallon mamaki yake mata ganin bama ta da niyar kallonsa, can ya juya fita. Har dare Hajja bata bar gidan ba tana dakin Humainah, Junaid ya samu Humainah dake kitchen tana xuba ma Hajja abinci yace "Zahrah ta ci abincin?" Bata kallesa ba tace "I don't know!" Ficewa yayi daga kitchen din ya koma sama ya shiga dakinta, xaune ya sameta ya karasa kusa da ita yana kallonta kana ganinta kasan tayi kuka, bai san lokacin da ya durkusa gabanta ba ya kamo hannunta yace "Zahrah!" Kallonsa tayi bata ce komai ba, ya matsa hannunta a hankali, sauke idonta tayi kasa, can underneath his breathe yace "My arrogant princess!" Bata dago ba bare tace komai ba, ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Meye amfanin miskilanci da girman kai Jasmine!"
*Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
89.....
Zahrah ta kalli cikin idonsa tace "Who's Jasmine?" A hankali yace "You!" Dauke kai tayi ya mike ya dawo gefenta ya xauna yace "Baki bani amsar tambayata ba" shiru tayi bata ce komai ba, matse mata hannu yyi ta wurga masa wani kallo tace "Stop that" yyi d'an murmushi yace "Nasan abinda zan maki ki sauke girman kan nn naki...." Fixge hannunta tayi ta mike ta nufi toilet tace "You can't change who I am, beside you are more arrogant" daga haka ta shige toilet ta rufe, mikewa yyi ya fita daga dakin yana murmushi har lkcn, sai bayan ya fita ya dinga mamakin kansa, then what just came over him, karfe goma saura Zahrah ta shirya cikin kayan bacci ta fita daga dakinta, dakin Humainah ta tura ta shiga, suna xaune kasa ta gansu, Humainah ta daura kanta kan kafar Hajja, magana suke amma suna ganinta suka yi shiru, ko a jikinta ta karasa ta xauna gefen gado ta kalli hajja tace "Sannu da hutawa!" A dakile Hajja tace "Yauwa!" Daga nn Zahrah ta maida dubanta kan tv, Hajja ta kalli Humainah kmr xata yi magana sai kuma tayi shiru ta kyabe baki, Humainah ta d'an kalli Zahrah tace "Abincin ki downstairs" ba tare da Zahrah ta kalleta ba tace "Am not hungry" Hajja ta galla ma Humainah harara ta hade rai, har kusan sha daya Zahrah na dakin ita dai bata ce masu ba suma haka, tun da ta shigo kuma sun ki yin hirar da suke, can dai ta kalli Hajja tace "Sai da safe" da sauri Hajja tace "Ehh Allah ba mu alkhairi" ba sai Hajja ta ga tana kkrin kwanciya kan gado ba, ta yo waje da ido tace "Mai xan gani haka?" Humainah da ta danne dariyar da ya kusa taho mata tace "Nan xata kwanta mana" Zahrah ta kalli Hajja tace "Bacci xan yi a nn" Hajja ta wage baki tana mata kallon mamaki can dai tace "Su wa kika bar ma dakin naki ne" Zahrah tace "A nn nake kwana" Hajja ta kalli Humainah tace "Wai?" Humainah ts gyada mata kai, Zahrah ko tayi kwanciyarta, can dai Hajja ta rufe baki tace "Wai tun da aka kawo ta nn take kwanan maki?" Humainah tace "Uhm" Hajja tace "Tabdi, toh me salubabben yace?" Humainah tayi yar dariya tace "Ba ruwansa" Hajja tace "Toh Allah ya sauwake maku gaba daya" tuni Zahrah ta ja bargo, Hajja da ta kasa daina mamaki tace "Wai meye haka nake gani, to ni ina xan kwanta?" Humainah tace "Ki tafi dakinsa ku kwanta" dai dai nn Junaid ya shigo dakin, yayi mamakin ganin Zahrah kwance dakin, Hajja tace "Yanda yake wawa haka ya samo mata duk wawaye, banda haka ni ko a tarihi ban taba jin kalan abinda nake gani a dakin nn ba, toh shigowa Kayi Kai ma ka kwanta a tsakiyarsu ko ko?" Mikewa Humainah tayi ta dinga dariya, Junaid dai sai kallonta yake don har ya mance rabon da ya ga tana dariya haka, dauke kai yyi yana murmushi can dai ya kalli Hajja yace "Toh yau kinga hakan a gidan Ahmad Junaid" wani kallo ta wurga masa tace "Yi man shiru, gantalalle har kullum wautan yan fari ba cika ka xai yi ba, dama Kai kace ta dinga xuwa kwana nn?" Junaid ya kalli Humainah yace "You leave the room for them nd come to my room" daga haka ya juya ya fita, a fusace Hajja tace "Ka xagi Muhammadu wllh, ke kuma uwar me yace?" Humainah tayi murmushi tace "Yace kije dakinsa ki kwanta" duka take shirin kai mata ta mike da sauri ta fita daga dakin, daga nn bata sake ganin Humainah ba tayi jiran tayi jiran har ta gaji, kwafa Hajja tayi tace "Lallai yaran nn, dakin mijinta ta tafi ashe" kallon Zahrah da tayi bacci tuni kan gado tayi, sai kuma ta fara mamaki, taga dai ko kwana hudu ba ayi da tarewarta tabe baki tayi ganin ta kasa gano komai ta mike ta dau bargo ta shimfida a kasa da pillow, can misalin biyu Zahrah ta farka mikewa xaune tayi ita kadai ce kan gadon, can ta kalli Hajja dake ta sharar bacci a kasa, sauke kafafuwanta kasa tayi ta mike ta xaga inda take ta durkusa ta shiga tada ta, bude ido Hajja tayi tana salati, Zahrah tace "Akwai sanyi kasa meyasa baki hau gado ba" Hajja tace "Kai ai sai jikina yyi ciwo, nn ya ishe ni" Zahrah tace "Toh" mikewa xaune Hajja tayi tace "Toh ae gwara da kika tada ni, xan yi tsayuwar dare dama" Zahrah tace "Ina take ita?" Hajja ta tabe baki tace "Ae kya bar ni budurwa" daga haka ta mike tana salati ta shiga bayi, mikewa Zahrah tayi ta koma tayi kwanciyarta, da asuba hajja ce ta tada ta tayi sllh, tana idarwa tana daga kan darduman ta gaida Hajja dake ta jan carbi, Hajja ta amsa tace "Kin tashi lafiya?" Zahrah ta gyada mata kai, Hajja tace "Amma kina da ciwon baki koh? Naga kmr magana na maki wahala?" Murmushi Zahrah tayi, Hajja tace "Toh ae ba abun dariya bane sai in sa a sama maki Magani...." Zahrah tace "A'a lafiyata lau!" Hajja tace "Tohhh! Kuna waya da mutan gidan ku?" Girgixa kai Zahrah tayi, Hajja tace "Sbda me" Zahrah tace "Ba waya" Hajja tace "Baki xo da waya bane dama?" Girgixa kai kawai Zahrah tayi, Hajja tace "Toh Allah ya kyauta" daga haka bata sake cewa komai ba, can Hajja tace "Dawo nn in maki tambaya" mikewa Zahrah tayi ta koma kusa da ita ta xauna, murya can kasa Hajja tace "Halan gudun mijin ki kike?" Girgixa kai Zahrah tayi ba tare da ta kalleta ba, Hajja tace "Anya? Toh wace gulmar ta kawo ki nn jiya Idan ba gudunsa kike ba?" Zahrah tayi murmushi ta girgixa mata kai, Hajja tace "Ke ki fa bude baki ki min magana" a hankali tace "Ni dama a nn nake kwana" Hajja tace "Toh har ya maki kwanakin ki bakwai ne?" Kai Zahrah ta gyada mata, Hajja tace "Karya kike" murmushi Zahrah tayi ta mike tace "Zan je kitchen" daga haka ta fita Hajja ta bi ta da kallo tace "Ikon Allah yau naga halitta" Breakfast Zahrah ta shiga kitchen tana hadawa, cikin minti arba'ain ta gama soye soyen, ta kuma dafa hadadden lipton mai kamshi ta kuma dau nama a deep freezer ta gyara tayi pepper soup da shi, bakwai da kusan rabi ta kai ma Hajja nata, Hajja dake kan darduma har lkcn tace "Ahhh, Dama kuna girki 'ya yan gidan sarauta, to wa ya koya maki girkin?" Murmushi Zahrah tayi ta ajiye mata ta hada mata tea snn ta mike tace "Zan yi wanka" daga haka ta fita ta koma dakinta, ta fito daga wanka tana gyara gashinta aka bude kofar dakin, juyawa tayi, tayi masa kallo daya ta dauke kanta, sanye yake da uniform, hannunsa rike da hularsa ya karaso cikin dakin har ya iso bayanta yace "Ashe an koya maki girki gidan ku" bata ko kallesa ba bare yasa ran samun amsa, kwace comb din hannunta yayi, ta jawo mai xata shafa ya karbe man, wani man ta kuma dauka ya kwace duk ya jefar da su kan gado, tana son tashi amma ta kasa sbda tawul kadai ta daura, gashi yana bayanta, ta madubi yake kallonta shi ma ya hade rai yanda tayi, "Pls ka daina shiga rayuwata Ahmad" bai san lkcn da murmushi yayi escaping lips dinsa ba yace "Ohh really kinsan sunana ashe" mikewa tayi kafin ta bar gun ya rikota, turasa take son yi amma ta kasa, kawai ta saki kuka, buda ido yayi yace "Kuka?" Ganin yanda take kukan sai ya tuno masa da lokacin da take da disorder, ya ji duk jikinsa yyi sanyi, ya kamo hannunta suka koma gefen gado ya xaunar da ita cikin sanyin murya yace "Ohk ohk... Am... am sorry princess, am sorry Jasmine" ganin taki daina kukan bai san lkcn da ya rungumeta ba ya lumshe ido a hankali yace "I said am sorry xan bar shiga rayuwar ki...." A hankali ta tsaida kukan nata, dogon gashinta ya kama ta fixge gashin a hannunsa, murmushi yayi murya can kasa yace "Jasmine dita ta da ba haka take ba, she alwayz wants to be with her Captain, always happy when ever she see's her captain, she alwayz want to do everything with her captain, she's timid, she's alwayz afraid, she's innocent, the sweetest of all, she's alwayz happy and free, she was never arrogant, she don't have I don't care altitude, she never say who she is, she's full of respect, and the amazing of all, she changed me to what I am today, she....." Shiru yayi ta dalilin dago kai da tayi tana kallonsa da manyan idonta, lallausan murmushi ya sakar mata yace "Yeah, I want you to go back to ur former self..." Agogo da yayi stuck din karfe takwas ya sa shi bude ido yana kallon wristwatch dinsa yace "You made me late for work...." Bai karasa ba sai ji tayi ya fara kiss dinta, don kansa ya mike ya fice daga dakin daga karshe, haka ta bisa da kallo har lkcn ta kasa motsi inda take. Da kyar ta mike bayan ta ji fitar motarsa ta shirya cikin atamfa riga da skirt tana xaune gaban mirror tana sa xobunayen zinari guda biyu da ta fito da daga kayan lefenta Hajja ta shigo dakin, tace "Har yanxu wanka yar nn" kallonta tayi tace "Na gama kaya nake sa wa" Hajja tace "Ashe komai iri daya ne na dakunan naku" Zahrah ta gyada mata kai, Hajja tace "Toh taho ki hada min ruwan wanka wancan so mijin na can dakinsa tana sharbar bacci" mikewa Zahrah tayi tace "Toh bari in hada maki a nan" Hajja tace "Toh hada, ko kefa da kike bude baki kike magana yanxu" murmushi Zahrah tayi ta shiga bathroom dinta, ba a dau lokaci ba ta fito tace "Ga ruwan can na hada" Hajja tace "To tafi ki bude jakata xaki ga wani sabon atamfa duk yafi sauran sabonta ki dauko min, nima kwalliya zan yi yanda kika yi kar ina ji ina gani ki raba ni da Amadi in shiga uku" Dariya Zahrah tayi tace "Kai!" Daga haka ta fice daga dakin, Hajja tace "Ashe dai kina dariya 'yar ayi" ko da Humainah ta fito misalin Karfe goma Hajja na dakin Zahrah har lokacin ta cikata da labaran duniya, ita dai Zahrah ta tallabi kuncinta ne tana kallonta, wani lbrin yasa ta fashe da dariya, wani kuma ta xaro ido wani kuma ta bata fuska, sha daya ta shigo dakin ita ma ta xauna tana kallon Hajja tace "Ina kwana Hajja" Hajja tace "Ahh lafiya lau so miji, sai yanxu kika tashi?" Zahrah ta sunkuyar da Kai kar tayi dariyar da ya taho mata, Humainah ta turo baki tace "Ehh" Hajja tace "Toh Allah ya kiyaye, kun gaisa da takwarar tawa" Humainah ta d'an kalli Zahrah tace "Kin tashi lafiya" Zahrah tace "Alhmdllh" nan dai Hajja ta ci gaba da labaranta masu kai da marasu Kai, gyangyadin da ta dinga yi tana labarin yasa Zahrah ta sauko mata da pillow tace "Toh ki kwanta sai ki ci gaba da labarin" ai ko tana kwanciya ta bingire da bacci, Humainah tayi murmushi ta mike ta fita don daura lunch, bayan kusan minti talatin da fitan ta Zahrah ta mike ta fita don taya ta. Da yamma tun kan Junaid ya dawo Hajja ta hada kayanta wai yana dawowa xai maida ta gida, Humainah tace "Dama ba sati daya kika xo mana ba hajja?" Hajja tace "Ba gantalalliya nake ba ai" Zahrah tace "Toh ki Bari gobe alhamis mana" Hajja tace "Toh ai ba yar iska nake ba" dariya suka yi gaba daya banda ita dake ta faman xuge jaka, tana gamawa tace "Toh dai ayi xama na Allah da annabi banda munafurci da munafukin kishi mara ma'ana, ku dau kan ku kamr yan uwan juna, ke Zahrah ki bar gudun mijin ki, ke kuma Humainah in ma ta shigo dakin ki ki korata idan ba son amshe kwananta kike son yi ba, ni har kishiyata ta rasu sau biyar muka taba dambe da ita, cacan baki kuwa mun yi yafi sau hamsin, Amma lafiya muka xauna bbu tashin hankali shi yasa ku ka gan ni da kyau yanxu, shi kuma salubabben mijin naku xai dawo ya sameni" dai dai nan aka bude gate Hajja tace "Toh Alhmdllh gashi can ma," Junaid na shigowa Hajja tace "Taho ka xauna nn, nasan sokanci baxai bari Ka hada su kayi masu magana kamar yanda nayi yanxu ba"
*Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
90____91
Har bayan 2 dayz Junaid bai kuma kallon inda wives din nasa suke ba, yana dawowa daga aiki baya fitowa daga bedroom dinsa, su ma ko damuwa ba su nuna sun yi ba barin Zahrah, yanda suke abubuwan su sai ka rantse ba kishiyoyi bane duk da ba wai wani magana can suke ba amma ko da yaushe suna tare, nace to ko don basa nuna sun damu da mijin kamar yanda shima yake nuna bai damu da su bane oho, gwara Humainah idan sun hada ido tana gaishesa duk da baya bin ta kan gaisuwar nata, Zahrah kam ko kallo bai isheta ba, wani takaici yake ji har cikin ransa, kuma ya rasa abinda yasa yake jin haushin halin ko in kula da suke nuna masu, ranan asabar yana kwance daki kawai ya mike ya fita, downstairs ya sauka jin kamar girki ake don a tunaninsa Humainah ce, Zahrah ya gani kitchen din tana juye dafaffen shinkafa a warmer, kallo daya yyi mata ya fice ita ko duk da taji alamar shi ne bata ko dago kanta ba, sama ya koma ya bude kofar dakin Humainah ya sameta kwance, tana ganinsa ta mike xaune, xaunawa yyi gefen gadon yana kallonta yace "Irin kema kin tsiri wani hali da ba naki ba yanxu koh?" Bata ce komai ba ya hade rai yace "Magana nake maki malama" turo baki tayi tace "Toh me nayi?" Yace "Bbu ruwana da abinda kika yi, just that daga yau idan Zahrah ta shiga dakin ki just leave the room for her nd come to my room, nd daga yau kika sake min gaisuwar rainin wayo a parlor xaki sha mamaki, infact bedroom dina xaki dinga xuwa gaisheni daga yanxu, and... I don't care altitude din da kika tsira ma ya tsaya iya idan bana gidan nn, duk girkin da xa ayi ki tabbatar kin kai min bedroom....." Kallonsa take kawae, can tace "Ae bni kadai bace matar ka naga" mikewa yyi strictly yace "Ke kadai nasa hakan, if you want to dare me just ignore any of this instructions" daga haka ya fice daga dakin ta bi sa da kallo. Zahrah na gama girki Humainah ta sauka ta dibar masa nasa, ita dai Zahrah bata ce komai ba, bedroom dinsa ta kai masa tana ajiyewa xata fita yace "Come back here" hade rai tayi ta dawo ya nuna mata kan gado yace "Sit" karasawa tayi ta xauna, bai wani ci abincin ba ya sha ruwa ya tura ya ci gaba da kallonsa a system, gajiya Humainah tayi da xama ta mike yace "Ina xa ki" tace "Jirana fa take mu ci abinci" yace "ta ci ita kadai, ga wannan idan yunwa kike ji ki ci" tsaye tayi tana kallonsa ganin bai kuma kallon inda take ba ta koma ta xauna, can dai ta gaji da xaman ta kwanta lkci daya bacci ya dauketa. Har yamma bai bari ta fito daga dakin ba, wayarsa dake ring ya sa shi mikewa ganin bata da niyar dauko masa ya dau wayar, kallon screen din kawai yake ganin yayan Zahrah ne Abdul, can ya daga kiran ya koma ya xauna, gaisawa suka yi Abdul din yace "Captain ya Lil sis dita.... Her phone is not going through!" Mikewa junaid yayi yace "Ohk bari in kai mata" daga haka ya fita daga dakin ya shiga nata, xaune ya ganta kan gado hannunta rike da novel, karasawa yyi kusa da ita ya mika mata wayar, bata dago ba bare ta karba, wani kallo ya dinga yi mata, can dai ya dake yace "Take this" nn ma taki dagowa, katse kiran yayi yace "Ba magana nake maki ba?" Mikewa tayi ta sauka daga kan gadon xata fita daga dakin ya fixgota, wani tsawa tayi masa a fusace tace "Stay away from me Ahmad!" Runtse ido yyi jin tsawar har tsakiyar kansa, bai san lkcin da ya saketa ba ya fice daga dakin ya shiga nasa ya dau makullin motarsa ya fito ya koma dakin har lkcn tana tsaye, hijab dinta ya dauka ya kama hannunta ya nufi kofa ta shiga kokarin fixge hannun tace "Let me, just go away from my life...." ganin xata bata masa lokaci ya dauketa ya fice daga dakin bai dire ta ba sai cikin mota, ya kulle ya xaga ya shiga ya tada motar ya bar gidan, bai damu da haukan da ta dinga masa bayan motar ba ya dinga driving dinsa, tafiyar kusan minti talatin suka yi taga yayi parking, bude motar yayi ya fito ya xaga ya bude side din da take ya fito da ita, taku daya biyu ya cikata yana mata wani kallo, kalle kallen wajen ta dinga yi ganin duk bola ne, ya dawo gabanta ya tsaya yace "Kin ga nan?" Kallonsa kawai take bata ce komai ba, yace "Toh a nan na dauke ki bbu kyan gani da hannuna, kuma a lokacin da kowa ke kyamatar ki baki da wani sauran gata a duniya kina tsaka da hauka, wanda da a lkcn royal family dinki sun ganki a hakan ba lallai su taba ki ba sai dai su sa a dauko masu ke, kuma har duniya ta nade bbu wanda xae taba maki abinda na maki... Har ni xa ki ce ina shiga rayuwar ki, har na xaki wani dinga daga ma kai ke ga ki royal blood" Kallonsa kawae take hawaye cike idonta, can ta fashe da kuka sosai ta durkushe wajen, jikinsa yayi sanyi yana kallonta, bai san lkcn da ya durkusa gabanta ba shi ma ya dago kanta yace "Look I never mean to hurt you Zahrah just that...." Ganin yanda take kallonsa hawaye na sauko mata kawai ya mike ya daga ta suka koma mota, har suka isa gida bbu wanda yace komai cikinsu, yana parking ta bude mota ta fita tayi cikin gida ya fito ya bi bayanta, tuni ta shige daki ta sa key ta dinga rusa kuka, jin kofar a rufe yasa ya koma bedroom dinsa ya dau spare key ya fito ya bude dakin, ji yayi duk ya tsani kansa ganin yanda take kuka, ya karasa kusa da ita a sanyaye ya durkusa ya dago kanta yana kallonta, rungumeta yayi a hankali yace "Am sorry Jasmine.... I shouldn't have done that, forgive me pls" ita dai bata ce komai ba sai kuka, bai sake cewa komai ba, amma sun kusa minti talatin a haka jin ta daina kukan ya dago kanta yaga idonta lumshe, janyeta yyi jikinsa ya kwantar da ita ya mike ya fita daga dakin don lkcn magrib yayi. Ko da ya dawo masallaci dakin Humainah ya shiga ya ganta xaune kan darduma juyawa yayi ya koma dakinsa ya dau wayarsa mis cals din Abdul ya gani ya dauka ya kirasa ya basa hakuri snn yace bari ya kai mata, xaune ya tarda ita kan darduma ya karasa gabanta ya durkusa ya mika mata wayar, karba tayi tana kallon screen din can ta kai kunne a hankali tace "Brotherna!" Murmushi tayi ta gaishesa sai kuma ta koma harshen fullanci, kallonta kawai Junaid yake har dai suka gama wayar ta mika masa, karba yayi yana murmushi yace "thought xa ki ce masa cikin ruwa na jefa maki wayar, sai kuma naji kin ce yana gu na!" Kallonsa tayi da sauri sai kuma ta sunkuyar da kai, ya wara ido yace "You thought bana ji koh?" Bata ce komai ba yace "Don't worry I will get you a new phone princess" mikewa yyi ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, tun daga lkcn Zahrah ta d'an sauya in dai yyi mata magana ko yayane xata amsa masa, ta kuma fara gaishesa, sai dai miskilanci nan na nan, a haka har tayi sati uku gidan har lokacin kuma tare da Humainah suke kwanciya, shi dariya ma take basa, sau dayawa Humainah kan barta ita kadai dakin ta tafi dakinsa amma hakan bai sa ta daina shigowa da daddare ta kwanta ba, kwata kwata Zahrah bata nuna masu wai tana kishi, duk da irin abubuwan da yake ma Humainah a gabanta don ma Humainahn bata yarda wani lokacin don nauyinta take ji ganin shirunta yyi yawa kuma ko sau daya baxa ka ga alamar tayi fushi ba, amma fa ba haka abun yake gun Zahrah ba a can kasan ranta, so tari sai ta shiga daki xata fara kuka tayi mai isarta ta fito kuma kamar ba komai, mamakinta Junaid yake ganin yanda ko sau daya bata taba nuna ta damu da komai ba, ya rasa yanda xae yi kuma ta saki jiki da shi, bai son El-ameen yyi masa dariya shi yasa bai gaya masa komai ba, Yau da ya kasan ce Sunday duk suna parlor da daddare shi yana kwance yana kallo, lkci lkci ya ke kallon Zahrah dake xaune tare da Humainah suna cin abinci sai dai ita ba wani ci take ba jujjuyawa kawae take tana kallon ita ma, da ganinta kasan duk jikinta a sanyaye yake don actress din film din mahaukaciya ce, Humainah ma kallon take tana cin abinci, kawai gani suka yi ta sake spoon din ta mike ta wuce sama, Humainah ta kallesa, ya mike ya bi bayanta, xaune ya ganta daki tana ganinsa ta fashe da kuka, sosai ta basa dariya ya xauna gefenta ya kamo hannunta yace "What's wrong princess?" Kanta ta daura kan shoulder dinsa tana ci gaba da kuka, bakinsa ya kai kunnenta murya can kasa yace "Film din nan ne ya sa ki kuka?" A hankali ta gyada masa kai, yayi murmushi ya dago kanta yana kallon kwayar idonta, sauke nata idon tayi don baxata iya ci gaba da kallonsa ba, can kasan breathe dinsa yace "My princess, My Jasmine!" Ta kallesa kamar baxata ce komai ba sai kuma a hankali tace "My prince, My Hero"

assalamu alaikum, dan Allah a taimaka a karasa mana novel dinnan na captain junaid. tun 9 march, ba a kara updating ba
ReplyDeleteSannu Kowa,
DeleteSunana Mista, Rugare Sim. Ina zaune a Holland kuma ni mai farin ciki ne yau? kuma na gaya wa kaina cewa duk wani mai ba da bashi wanda zai tseratar da ni da iyalina daga mummunan halinmu, zan koma ga duk mutumin da ke neman bashi a kansa, ya ba ni farin ciki a gare ni da iyalina, na kasance ina buƙatar aro na € 300,000.00 don fara rayuwata gaba daya kamar ni uba daya ne da yara 2 Na hadu da wannan mai gaskiya kuma Allah yana tsoron mai bada rancen da zai taimake ni da rancen € 300,000.00, shi mutum ne mai tsoron Allah, idan kana bukatar aro Kuma za ku biya bashin don Allah ku kira shi ku gaya masa cewa (Mr, Rugare Sim) yana nuna muku shi. Tuntuɓi Mista, Mohamed Careen ta imel: (arabloanfirmserves@gmail.com)
MAGANAR BAYANIN AIKIN LATSA
Sunan rana......
Suna na tsakiya .....
2) Jinsi: .........
3) Bukatar Lamuni: .........
4) Tsawon Lamuni: .........
5) Kasa: .........
6) Adireshin Gida: .........
7) Lambar Waya: .........
8) Adireshin Imel ..........
9) Gashi na wata-wata: …………… ..
10) Aiki: ...........................
11) Wanne rukunin yanar gizo kuka kasance game da shi …………… ..
Godiya da kuma mafi kyawun gaisuwa.
Email arabloanfirmserves@gmail.com
domin samun littafain hausa ziyarci wannan shafi www.share4world.com.ng
ReplyDeleteMany thanks pls continuation of captain Ahmad junaid
ReplyDeletehttp://myjobpaid.com/?userid=343323
ReplyDeletehello 4 letest hausa novels complete visite www.hausabook.com
ReplyDeleteassakamu alaikum gaskiya yakamata akarasa mana wannan littafin dan Allah
ReplyDeleteSalamu alaikum Please continuation of the novel,its very interesting
ReplyDeleteHakkin mallakar hotoPR NIGERIA An sake gurfanar da shugaban kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta ‘yan Shi’a (IMN) Sheikh Ibrahim el-Zakzaky a gaban
ReplyDeleteSo sad the novel is not complete pls try and make it complete pls
ReplyDeleteThis comment has been removed by the author.
ReplyDeleteYana Beauty Salon & Spa offers full range of beauty services. Addison, Farmers Branch TX, Dallas, TX 75244. Reasonable prices. Discounts. Hair salon spa, Hair color, Facial, Waxing...
ReplyDeletevisit here : hair salon yana
Perfect
ReplyDeleteinteresting information and the article is really helpful. We also have an amazing article at mobile number tracker
ReplyDeletePlease the continue please
ReplyDeleteYayi
ReplyDeleteSlm
ReplyDeleteKhadeejat
ReplyDelete