RANAR DA ZAKAYI EXPIRE

Ya kai 'Dan Adam!! Ya kai wanda duniya take zugashi tana rudinsa!! Ya kai wanda dogon buri ya cika zuciyarka!!!

- Anya kana tuna ranar da zakayi expire kuwa? Wato ranar da zaka tashi daga aiki... Ranar da zaka bar duniya tare dukkan abinda ka mallaka..


- Kamar yadda Kowanne kayan kampani yake da expiry date ajikinsa, hakanan kaima kana da taka ranar tana nan arubuce awajen Ubangijinka.

- Watakil idan ta kusanto ya bayyana maka alamun zuwanta. Watakil kuma sai dai ta riskeki "Baghtatan" ba tare da wani kintsi ba!!.

- Kamar yadda mutane suke kyamar dukkan abinda yayi expire, to hakanan daga wannan ranar bayan sun binneka, iyalanka zasu kyamaceka.

Babu wanda zai yarda ya tayaka kwanciya acikin Qabarinka. Koda shi yana daga waje, kai kana ciki... Ba zai yarda ba.

- Wani ma tun daga addu'ar da yayi maka aranar, to ba zai Qara zama don yin addu'a agareka ba. Ba zai so yaji ambatonka ba.

- Da zarar sun dawo daga binneka zasu yi wanka su sanya kyawawan tufafi don karbar ta'aziyyar mutuwarka, Amma wannan ba zai hana su shagaltuwa da hirarrakin duniya awajen ba.

- Kafin kwana bakwai sun dena jin radadin mutuwarka, sun fara tunanin raba dukiyarka... Kowannensu yafi so nashi kason yafi tsoka.

- Idan sun karbi kasonsu, kowa zai bada himma ne wajen gyaran duniyarsa da wannan kudin ko dukiyar.. Babu wanda zai damu dakai ballantana ya juyar da nasa kason don ciyarwa ko sadaqah domin saukaka maka halin da kake ciki acikin Qabarinka!!

- Matanka kuwa, kafin kwana arba'in sun fara Qirga sauran kwanakin takabarsu, sun matsu su gama iddar takabarsu don saurin su samu wasu Mazajen.

- Duk soyayyar da matarka take yi maka ba zata so tayi shekara guda bayan rasuwarka ba tare da ta sake wani Mijin ba.. (sai dai in da larurar ciki, ko goyo).

- Kuma daga ranar da aka daura mata sabon aure, shikenan murna ta dawo sabuwa.. Daga ita har angonta ba lallai ne su rika son jin ambaton sunanka ba. Musamman atsakiyar lokacin amarcinsu.

- Gidanka kuwa, komai girmansa ba lallai ne iyalanka su amince abinneka acikinsa ba.. Idan ma aka binneka wani sai yayi shekaru bai leka wajen da kake ba, ballantana yayi maka addu'a.

- Motarka kuwa, komai kyawunta ba zasu yarda asanya gawarka acikinta ba. Don kar warin jikinka ya 'bata musu ita..

- Abokanka da 'Yan uwanka kuwa, kafin wata uku sun manta da iyalanka. Babu wanda zai rika hidimta musu don tausayinsu. Sai dai 'yan kadan.

Wallahi da ace za'a yi maka izini ka leko duniyar nan, kaga yadda gidanka zai koma bayan shekara guda da rasuwarka, da sai kasha mamaki.

To in dai haka duniyar nan take, da kayan cikinta, to mai zai rudeka har ka manta da biyayyar Ubangijinka??

Mai zai sa kabi shaitan da zuriyarka alhali shine babban makiyinka afili a bayyane?

Mai zai sa ka rika biye ma son zuciyarka, tunda ba zata amfaneka da komai ba!!

"YA KU WADANDA SUKAYI IMANI! KUJI TSORON ALLAH MUTUKAR JIN TSORONSA, KADA KU MUTU FACHE SAI KUNA MASU MIKA WUYA ZUWA GA ALLAH".

Comments