​MU KOMA GA ALLAH

Seeking forgiveness from Allaah is from the greatest of good deeds.”. Ya Allah... Forgive our sins, our indiscretions, our mistakes which we have done either deliberately or in innocence... Ya Allah forgive our past and guide use all in our future. Ameen..

😭😭😭
1 Dazaran katashi zaka bude Data don gani sakon duniya. Amma Sallar Asubah cikin Jam'i tagagareka. ​Mu koma ga Allah.​

2 Kana iya minti 90 cikin kallon ball idan anyi rashin sa'a atafi extra-time. Amma Sallar farilla tagagareka cikin Jam'i don kallon ball. ​Mu koma ga Allah.​


3 Kana iya haddace handout don ganin kaci jarrabawar duniya ta dan adam, Amma baka iya haddace surah daya ta Alqur'ani don guzurin lahira. ​Mu koma ga Allah.​

4 Kanada halin kyautar mota don neman suna, Amma baka da hannun kyautatawa gajiyayyu da marayu don neman lahirarka. ​Mu koma ga Allah.​

5 Kanada lokacin musu, Amma bakada lokacin yiwa Annabi salati. ​Mu koma ga Allah.​

6 Kanada kudin sayan mota da sutura ta alfarma, Amma sayan Sinsiya ta sharar dakin Allah tagagareka. ​Mu koma ga Allah.​

7 Kanada lokacin karanta jarida, Amma bakada lokacin karanta maganar mahaliccinka. ​Mu koma ga Allah.​

8 Kana iya kuka don Asarar abun duniya, Amma tuna azabar kabari yagagareka. ​Mu koma ga Allah.​

9 Kanada lokacin kallon season film, Amma sada zumunci tagagareka, don neman haye siradi. ​Mu koma ga Allah.​

10 Kanada lokacin zuwa ko inane don neman abun duniya, Amma neman ilimin sanin mahaliccinka yagagareka. ​Mu koma ga Allah.​

11 Kaine jagora wajen zalunci da cin dukiyar al'umma, Amma kiran sallah (Ladanci) Abun kunyane agareka. ​Mu koma ga Allah.​

12 Ka zabi rayuwar duniya fiyeda ta lahira, bayan bakasan yaushe zaka mutu ba. ​Mu koma ga Allah.​

​👉🏼NAZARI NA MUSAMMAN.​

1 Idan arziki ne yasanya kabijirewa mahaliccin ka, to yau ina ​Qarunah?.​

2 Idan zallan sabon Allah kakeji dashi da shagaltuwa, to yau ina ​Fir'aunah?.​

3 Idan zalunci kasa agaba to yau ina ​Hamana?.​

​👉🏼YAKAI DAN'WA AMUSULUNCI KASAKE TUNANI.​

1 Talauci baya hana dautar Allah. Tuna da tarihin ​Annabi muhammad (S.A.W).​

2 Idan hassada akema, Tuna da tarihin ​Annabi yusuf. (A.S)​

3 Idan radadin ciwo zai sakamanta da Allah tuna da tarihin ​Annabi Ayuba. (A.S)​

4 Idan zallan kinka ake kan gaskiya, tuna da tarihin ​Manzon Allah (S.A.W).​

5 Idan wani abune yadameka, Waraka na cikin ​Alqur'ani.​ Karanta kabarwa Allah komi.

Comments