Ballagar Mace (complete)


Tunda na jefa k'afata a cikin gidan na ke ta Karo
da kwanika, ga sunan birjik a tsakar gidan, ba
wanki, tamkar kwanikan da mutanen gari suka
ci abinci, saboda tsananin yawansu,kuma abun
da ya dad'a d'auremun kai, gurin da aka zuba
kwanukan kwata_kwata bai yi kama da wurin
wanke_wanke ba, cikin 2mints na k'arewa gidan
kallo.

Madaidaicin gida ne, wanda kana shigowa za ka
tarar da parking space wanda aqalla ya ci
motoci hud'u, sai parlour d'auke da 4 bedrooms,
kitchen, toilet and store.
Sai da muka shiga parlourn, na lek'a kitchen sai
na ga ashe kusan duk kayan kitchen d'in ne a
waje ba wanki.
Na juya na kalli sister maryam da muka je tare,
na ce
"an ya kuwa nan ne gidan amarya da ko wata
bata yi a gidan miji ba??
Maryam ta ce "nan ne don nan ta kwatanta mun
da ta shiga lokacin ba kya nan".
Ban gama mamaki ba kuwa sai ga ta ta fito,
tana washe ba ki, ta ce "maman Twins ashe ke
ce a gidan na mu, ku shigo mana"
Murmushi na yi, na ce "eh Amarya, ai sister na
ta ce kin zo har sau biyu ba ki same ni ba shi
yasa na ce bari na lek'o".
Soshe_soshe ta fara kamar wadda ba ta yi
wanka ba, tana fad'in "eh wallahi, zaman ne
mutum d'aya ba dadi, shi yasa na ke so mu
saba dake, tunda ni dai anguwar nan ban San
kowa ba, kad'aici duk ya dameni, kin ga na yi
kallon har na gaji, haka ma chat, don haka nake
so na dan samu wurin zagawa, ta k'arashe
maganar da sakin wata dariya.
Kallon_kallo muka tsaya yi da maryam, sannan
cikin yak'e na ce
"haka ne gaskiya"
Sai kuma ta mik'e tana fad'in bari ta kawo
mana ruwa, tafiyarta ta ba mu daman k'are ma
parlourn kallo, ga parlor har parlour, amma
rashin gyara yana barazanar hana a ga kyan
parlourn, don TV kawai za ki kalla ki san
parlourn yana buk'atar gyara, don k'urar da ke
jjkinta tsaf zan rubuta sunayen writters da muke
da su a jiki a kuma ga ne.
Ga shi tunda muka shigo wani bala'in zarni ke
tashi, daga cikin kujerun da muke zaune, abin ya
matuk'ar ba ni mamaki abinda ya kawo zarni
d'akin amarya.
Bayan ta kawo mana ruwa muka d'an ta6a hira
da ita, muka ce za mu tafi, ta ce
"to shike nan na gode, sai na shigo"
Na bita da to, sai da za mu fita na hango mage
a cikin flowers d'in da ke harabar gidan, cikin
raina na ce tabbas zarnin da muka ji, na fitsarin
mage ne, don rashin kula har ta bari mage ta
rik'a shiga d'aki tana lafta mata fitsari, haka
muka kuma tsallake kwanikan nan muka wuce,
ina tunanin ita kuwa tana aikin meye har
wanke_wanke ya tarar mata haka kamar tun da
aka kawo ta ba ta ta6a wanke kwanika ba , don
set d'in warmers ga su nan kala_kala banda
pots, plates, spoons, knives da sauran kayan
amfani duk baja_baja kamar ana gwanjon su.
Bayan mun iso gida na kalli maryam na ce
"gaskiya matar nan akwai gyara a lamuranta,
kalli fa gidanta tun kafin ta kai wata biyu da
aure, ai dole na cigaba da bibiyarta don ganin
irin annakiyar da zata yi, saboda na d'aukowa
readers rahoto".....
Mum Twins 😍
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ◾BALLAGAZAR
MACE ◾3&4
©MRS SAIF
®NWA
Wacece Nadeeya ???
Nadeeya 'ya ce a wurin Alhaji Sani Haruna,
asalin su' yan garin dutsen jahar jigawa ne,
domin dukkan su a can aka haifesu, su goma cif,
mama Haleema ta haifa, su takwas ne mata, sai
maza biyu, su ne manya.
Nadeeya ita ce ta bakwai a gidan, mahaifinsu
yana da kud'i dai_dai gwargwado, don ba abun
da baya musu na buk'atar su.
Mutum ne shi mai son farantawa iyali, don duk
abinda ake ya yi, za ka gan shi a gurinsu, daga
kan sutura kayan kyale_kyale ne, da na gyaran
gida ne duk a wurin su za ka fara gani, sai dai
kash!!! Maman su muguwar k'azama ce,da ko
inkula akan komai, domin ko 'ya' yan ta, bata
basu cikakkiyar kulawa,bare har su samu
kyakkyawar tarbiyya, shi yasa suka taso da
baud'add'un halaye duk abinda suka ga dama
shi suke yi,Nadeeya ga azababben son yawon
tsiya, barin ma aka ce biki, anan kuwa ko za a
kasheta sai ta je matuqar ta san da bikin,baya
da k'azanta da ta zama kamar gadon gidan su,
don kusan dukkansu suna da wannan halin.
Don ma sun samu uba mai kashe musu, don duk
abinda ya samo zai kawo gida, amma ina nan
da nan abubuwa suke lalacewa da an kawo
saboda rashin gyara, gida ga shi k'ato, ya kuma
k'eru, amma daud'a duk ta kashe gidan, idan ka
shiga gidan kamar shek'ar karnuka, don maman
su ba ta iya komai sai dai ta saka 'yar aiki, gata
da 'ya'ya mata Allah ya ba ta, amma ba ta saka
su sai dai su ci su yi kallo, idan lokacin barci ya
yi su je su kwanta.
Ga shi' yar aiki d'aya ta ke d'auka duk girman
gidan, ita za ta yi komai, don akwai ta da son
kud'i, ba ta son ta d'auki 'yan aiki da yawa ta
san za su ci kud'i da yawa, shi yasa da sun fara
sun ga baza su iya ba, sai su gudu.
Daga k'arshe ta hak'ura da maganar ' yan aikin,
sai su ke damalmalaya ita da sakarkarun 'ya'
yan ta, aikuwa a lokacin ne k'azanta ta samu
gindin zama a gidan, don sai rana ta kusa
fad'uwa suke fara shirin share_sharen gida,
wanke_wanke kuwa sai dai duk wanda zai yi
amfani da kwano ya je ya wanke da kan shi.
Shi kam mopping ba a ma maganarsa, don sai a
yi wata gidan bai samu arzik'in mopping ba.
Don idan ki na taka tiles d'in gidan, sai ki rantse
gam aka zuba, saboda dank'o, don sai ki na
d'aga k'afarki da k'arfi, gudun mannewa a jiki.
A unguwar ma idan ba ki ce gidan k'azamai ba,
baza a gane gidan su Nadeeya ki ke nufi ba, tun
mai gidan yana fad'a har ya saduda ya hak'ura,
shi ma ya bi.
(kun san idan mace k'azama ce, ko da mijinta
yana da tsafta sai ki ga a hankali ya fara
rikidewa shima yana zama k'azami)kafin daga
bisani Allah ya masa rasuwa, a lokacin Nadeeya
na ss1.
To daga nan fa sai al'amura suka dad'a
ta6arbarewa, don mai hana su wasu abubuwan
ba ransa, sai abinda mama ta zartar ita kuma
dama ga ta sai a hankali.
Dama hausawa sun ce
"Da na gaba ake gane zurfin ruwa,"
Saboda haka k'azantar Nadeeya da duk wata
ta6ara mai license ce, don tun daga gida ta
debo ta, ku dai ku biyo ni don Jin irin tata
annnakiyar, don bahaushe ya ce
"gado fi ya ke"
Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪4&5
©MRS SAIF
®NWA
Misalin k'arfe 6 na yamma Faruk ya dawo daga
aiki, ransa a matukar 6ace ya shiga parlourn
gidan, akan kujera ya tarar da ita tana shan
fruits, duk ta yi kaca_kaca da 6awon kankana da
lemo, don gida biyu ta raba kankanar sai ta
d'auki 6ari d'aya ta kafa kai tana sha.
Wata naunanniyyar ajiyar zuciya ya sauke, ganin
da ya yi ita kanta ba abinda ya chanza a jikinta,
don tun shekaran jiya ta saka kayan jikinta,
amma har yau ta kasa cireshi, wani d'an
k'aramin tsaki ya ja, da niyyar ratsewa ta gaban
ta ya wuce d'akin sa.
Hakan ya yi dai_dai dawowar nadeeya daga
duniyar da ta lula ta shan kankana, juyowa ta yi
tana kallonsa tare da fad'in "Faruk har ka dawo
ke nan, ta fad'a tare da washe baki.
Kai kawai ya gyda mata ya k'arasa shigewa
d'akin sa, baki ta ta6e tare da fad'in" mutum
sai shegen miskilancin tsiya maganar ma
wahalar yi take masa".
Faruk kuwa yana shiga d'aki kayan sa, ya tu6e,
ya shiga wanka, bayan ya gama ya d'oro
alwalar magrib, farar jallabiya sol ya saka,
sannan ya feshe jikinsa da perfumes d'in sa
masu dadin k'amshi.
Parlourn dai ya kuma komawa, still tana nan
yadda ya bar ta, sai remote da ta d'auka tana
canja channel, kuma yanzu ta gama shan
kankana, ayaba take ci.
Neman guri ya yi ya zauna a d'aya daga cikin
kujerun parlourn, duk da bai Jin dadin yanayin
tsamin dake ta shi daga cikin parlourn, amma
haka ya daure ya zauna.
Ganin ya zauna ya sa Nadeeya Jin dad'i, don
akwai ta da d'an banzan surutu, don dai Faruk
ba ya sakar mata fuska ne, da ya sha hira.
Sai da ta gutsiri kusan rabin ayaba ta saka a
bakinta sannan ta juyo tana shirin masa
magana, hannu ya d'aga mata tare da mikewa
tsaye yana fad'in "masallaci zan je yanzu, sai
dai ki bari sai na dawo, kafin nan kin cinye
abinda ya ke bakin ki". Don ya tabbatar idan ya
cigaba da kallon yadda bakinta ya dame da
ayaba hakan zai iya barazanar sa shi tashin
zuciya, wanda zai iya kai shi da yin amai, don
dai Faruk akwai shi da k'yank'yami tun yana
yaro, hakan yasa ya dade yana neman macen da
ta dace da ra'ayinsa amma Ummansa ta yi
gajen hak'uri ta had'a shi da 'yar aminiyarta,
wadda bai da tabbacin yadda yarinyar take, tun
da ba a gari d'aya suke ba.Su Faruk suna kano,
su kuma su Nadeeya' yan jigawa ne, kuma ita
umman Faruk ba zuwa take yi ba, ummansu
Nadeeya ce ke yawan zuwa, ko idan an yi hutu
ta turo su Nadeeya.
Dan k'awancen na su dad'add'e ne, ya samo
asali tun lokacin da suke boarding school na
dala,
Da yake masu son xumunci ne sai ba su watsar
ba,amma Faruk kam bai ma ta6a zuwa jigawan
ba, sai ranar d'aurin aurensu.
Don ko lokacin da aka saka bikinsu, ba wani
zuwa gurin ta ya ke yi ba, sa dai ya yi ta tura
musu kud'i hakan ya saka ba su damu da sai
ya zo ba. Nadeeyan ce ma mai damuwa don
gaskiya tana tsananin son Faruk, sai dai kash
bata san hanyoyin da zata bi don shawo kansa
ba, a maimaikon haka sai ta sa a ranta ai da an
kawota gidan sa shi kenan dole ya sauko ya bi
ta, sai dai abinda ya ba ta mamaki ko bayan
aurensu ba ta chanza zani ba.
Don haka ta tattara shi ta watsar, sabgar gaban
ta kawai take yi, a cewar ta burin ta ya riga ya
cika tun da ta aure shi.
Da wannan tunanin ya fice daga gidan ba ki
d'aya, zuciyarsa cunkushe da tunanin wannan
wace irin mace ce????
Aure ko wata 3 bai yi ba, amma ya fara Karo da
matsaloli, gaskiya Nadeeya kwata_kwata ba ta
dace da shi ba, don ta ko'ina ba ta yi kala da
matar da ya ke muradin aure ba.
Don aurenta ya d'auke sa, a matsayin k'addara
ce kawai, don akwai shi da biyayyar iyaye
musamman mahaifiyyarsa da ita kadai ta rage
masa sai k'anwarsa....
Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪6&7
©MRS SAIF
®NWA
Bayan sun idar da sallah, ya fi k'arfin 30mnts
yana zaune a parlor yana jiran Nadeeya ta kawo
masa abincinsa, amma shiru ka ke ji, sai da ya
lek'a d'akinta don ya sanarda ita ta kawo masa
abinci, tunda ita kwata_kwata ba ta san abinda
ya da ce.
Turus ya yi bayan shigar sa d'akin , yana duban
abinda ke gabanta, taliya ce a gabanta wacce
ake kira shar6u take kwasa, kusan rabinta duk
ruwa ne, ga shi ta kwasota za ta kai baki ruwan
taliyar har yana tsiyaya ta tsintsiyar hannunta.
Bud'e ido yayi yana kallonta, tare da fad'in
"amma ni dai ba wannan abincin ki ka dafa da ni
ba ko"???
Ita ma kallon nasa ta yi, tana cewa"au dama
har wani dafa abinci ake kashi_kashi???
Ta cigaba da fad'in" tab! Wai aiki, don yau ka ji
dad'i ma ban yi tazarce ba, don na ji ina son cin
jaloup d'in taliya, shi yasa kk wannan maganar."
Dafe kan sa yayi, yana fad'in "yanzu kina nufin
wannan k'azamain abincin zan ci "???
K'ara sul6ar taliyar ta yi, sannan ta ce" ni fa
ban ce dole ba, idan ka ga xa ka iya ka ci, idan
ba za ka iya ci ba, ka bar shi ba dole."
Kamar zai yi magana, kawai sai ya shareta ya
fito daga d'akin.
Kitchen ya nufa ya hada tea ya sha don yunwa
ce fal cikinsa, don yau bai samu ya ci abinci a
office ba, saboda ayyukan da suka saka shi a
gaba.
Tun asuba da ya tashi bai koma barci ba, don
da wuri yake son fita, don haka da kan shi ya
shiga kitchen ya d'ora ruwan zafi, don ya tashi
Nadeeya ya kai so uku ta k'i tashi, tea dai ya
kuma had'awa ya sha, a ransa yana cewa "shi
bai ga amfanin auren da ya yi ba , har gwanda
lokacin da yana gidansu sau dubu."
Har ya kusa gama shiri sannan ya jiyo,, katuwar
hammar Nadeeya alamun ta tashi, k'amshin
turarensa ne da ya cika gidan ya tabbatar mata
da ya gama shiri don haka cikin azama ta diro
daga kan gado ta yo waje, dai_dai lokacin Faruk
ya fito sak'ale da jakarsa alamun ya gama shiri
zai fita.
Kallo d'aya ya mata ya d'auke kan sa duk ta yi
wani dagaje_dagaje da ita kamar wadda aka
k'wato a bakin kura, gashin kan ta duk ya wani
cukurkud'e, haka idonta duk kwantsa ya cikasa,
bakin ta taf yawun barci take shirin yi masa
magana, da sauri Faruk ya k'ara wuta zuwa
k'ofar fita, yana fad'in "akwai kudi na nan na
ajiye miki akan stool, ko da za ki yi wani
amfanin".
Yana k'arasa maganar ya fice da sauri, don
baya son cigaba da kallon yanayin da take ciki,
don hakan yana haddasa masa tashin
zuciya...........
Maman Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪8_10
©MRS SAIF
®NWA
Dama ita Nadeeya saurin da take yi, don ta
kar6i kud'i ne, kafin ya fita, don haka Jin ya
ajiye mata kud'in ya sa, ta shige toilet ba tare
da ta kuma bi ta kansa ba.
Faruk kuwa driving ya ke, amma hankalinsa
gaba d'aya baya kai, yana can yana tunanin
halin da ya tsince kansa, a zuciyarsa yana cewa
"wai yanzu a haka rayuwarsa zata cigaba da
tafiya da wannan yarinyar"????
Tambayar da yake ta nanatawa a zuciyarsa
kenan, sai dai kash ya kasa samo amsar
tambayarsa, tunawa da yayi yanda mahaifiyarsa
ke son aurensa da Nadeeyar , yasan ko giyar
wake ya sha ba zai tinkareta da maganar
rabuwa da Nadeeya ba.
A haka ya yi ta sak'a da warwara har ya iso
office d'in su, don haka ya yi parking ya fito da
zummar shiga ciki.
Nadeeya kuwa bayan ta gama dak'ilanta, fitowa
ta yi ta chanza kaya don a cewarta sanyi ya yi
yawa ba zata iya wanka ba, kayan ma da ta
chanza don tana son fita ne, da zaga mak'ota
ne, don gaskiya ta gaji da zaman gida, tunda ta
ga maman Twins ta su bata zo d'aya ba, don da
ta shiga gidanta za ta fara kawo mata zancen
girki, ko gyaran gida ko jiki, ita kam
kwata_kwata basa cikin tsarinta, don haka ta
yanke shawarar watsar da ita kawai ta nemi
wata mak'ociyar, wadda ta su zata zo d'aya.
Haka Nadeeya ta fara shiga gidajen mak'ota
daga wannan gida zuwa wancan, har ta fad'a
gidan maman Nabeela, tun daga k'ofar gida take
jiyo shewa da raha na mata, tamkar gidan biki,
da sauri ta kutsa kan ta cikin gidan tare da
sallama, kusan a tare suka amsa mata sallamar.
Sannan wata mata dake zaune a tsakiya (wadda
ga dukkan alamu ita ce mai gidan) ta ce "ah!
Sannu da zuwa bak'uwa muka yi"???
Gyd'a kai, Nadeeya ta yi tare da cewa"eh, ai ni
ce amaryar can gidan mai red d'in gate, na kusa
da gidan Maman Twins".
Gaba d'aya suka d'auki gud'a suna cewa"ki ce
amaryar ce "???
Mai gidan ta amshe da cewa"ai mun yi fushi sai
yau ki ka shigo mana, ta k'arasa maganar cikin
sigar zolaya".
Wata dariya Nadeeya ta saki don ganin cewa
lallai yanzu ta samu abokan sha'ani don daga
ganin su za a daki chafta da su, sannan ta ce "a
yi mun afuwa yanzu ai gani na zo".
Dariyar dai suka kuma yi, sannan aka bata wurin
zama ta zauna, aka cigaba da hira, wadda hirar
ta su, duk akan maganin mata ne, daga
maganar sa mai gida tsalle, sai sa mai gida ihu,
sa mai gida kururuwa, kai har da sa mai gida
hauka lol, ga sunan dai birjik, dama Nadeeya ta
samu abinda take so, anan aka yi mata tallan
wasu, ta kwasa, don kud'in da ta fito da shi sai
da ya k'are tas, har sai da aka biyota bashi.
12 na rana matan suka fara watsewa, don
komawa gida, daga wadda za ta ce, ba ta yi
wanke_wanke ba, sai wadda zata ce yaranta sun
kusan dawowa daga school ga shi ko girki ba ta
d'ora ba. Wata ma ko tsinke ba ta d'aga a cikin
gidan na ta ba, amma ta fito yawon mak'ota,
irin su Nadeeya kenan.
A gaban idonta matan nan suka watse duka,
maimaikon ta yi haramar tafiya ita ma, ai sai ta
gyara zama, su ka d'auki wani sabon shafin
hira, suna hirar matar(wadda ake kira da
maman Nabeela) na kiciniyar d'ora girki.
Idan ka gansu da Nadeeya sai ka rantse da
Allah sun shekara a tare, saboda sabon da suka
yi lokaci d'aya.
************
Nadeeya ba ta bar gidan ba sai bayan la'asar,
don anan ta ci abinci rana.
Faruk kuwa 5pm ya yi shirin barin office, direct
gidan su ya nufa, don yana son ganin ummansa
da 'yar k'anwarsa Fateema.
Waye Faruk?????
Umar Faruk Sadauki, shine cikakken sunansa,
mahaifinsa haifaffen garin kura ne ta cikin jahar
Zamfara, wanda aka fi sani da Aliyu Sadauki, ya
dawo kano da zama ne sanadiyyar kasuwanci,
inda anan Allah ya hada shi da matarsa wato
mahaifiyarsu Faruk hajiya Aysha, sun yi auren
so da k'auna, sun kuma yi zaman Jin dad'i,
wanda Allah ya azurta su da yara biyu rak,
Umarul Faruk da Fateema Zahra, kafin daga
bisani Allah ya kar6i ran Alhaji Aliyu.
A lokacin Faruk yana level 3 a university,
Fateema kuwa tana j.s.s 2, saboda haka
ummansu ta cigaba da kulawa da su har zuwa
lokacin da Faruk ya gama karatu ya fara aiki,
wannan kenan......
Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪11&12
©MRS SAIF
®NWA
Da sallamarsa ya shiga parlourn gidan, da sauri
fateema ta taso tana masa sannu da zuwa, tare
da fad'in "bro jiya throughout ban ganka ba mun
yi missing d'in ka fa ".
Murmushi ya k'ara fad'ad'awa a fuskarsa,
sannan ya rik'o hannunta yana cewa "I miss yhu
more lil sister, nd ina Umma ta shiga ne, ban ji
motsinta ba".
Fateema ta ce "yanzun ta shiga d'aki, ina
tunanin wanka ta shiga don ba ta dad'e da
dawowa daga unguwa ba".
Faruk ya ce "ok, sannan ya nemi d'aya daga
cikin kujerun parlourn ya zauna.
Bayan 10mnts Umma ta fito tana fad'in" Faruk
kai ne da yamman nan"???
Sosa kai ya yi, sannan ya ce "eh, umma ina
wuni"???
Lafiya Lau, ya Nadeeya take???
Sai da Faruk ya d'an 6ata fuska sannan ya ce"
lafiya".
Umma ta dad'e tana nazarin halin da yake ciki
kwana biyu, don duk ta ga ya chanza, ta san
tabbas akwai abinda ke damunsa, da ta fiso sai
ya fad'a da bakinsa, amma zuwa yanzu ta san
ba lallai ya fad'a mata abinda ke damunsa ba,
don ta san halin Faruk sarai.
Maganarsa ce ta dawo da umma daga tunanin
da take yi, yana cewa "wai umma mai ku ka
dafa ne yau"???
D'an zaro ido ta yi tana cewa, haba Faruk idan
ka cika cikin ka, anan ka je gida ba ka ci abinci
ba, Nadeeya ba zata ji dad'i ba fa????
Ka san matan yanzu wayau ne da su, basa so
su ga mazajensu na cin wani abinci idan ba na
su ba".
Mere baki ya yi, a ransa yana cewa wadda ta
san kanta ba, amma wannan BALLAGAZAR
MACEN, ai ba ta san da haka ba.
Shirun da umma ta ji yayi ne, yasa ta ce "Faruk
anya babu matsala a zaman na ku kuwa???
Shiru ya kuma yi, don har ga Allah shi ba
mutum ba ne mai kai k'orafi ba, amma yasan
tunda har ta tambaya to dole ya gaya mata,
idan ba haka damuwa zata saka a ranta.
Don haka nan take ya juyewa umma abinda ya
ke faruwa, duk da ba ta ji dadin abinda ya fad'a
ba, amma sai ta ce "Faruk na san halinka yanzu
haka, ba ka tsaya ka yi mata bayanin abinda ba
ka so ba da wanda ka ke so ba ".
*************
Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ce
"haba umma, yanzu a ce har tsabtar jikin ta sai
na gaya mata ta yi, na d'auka duk a gidansu za
a sanarda ita komai ai".
Girgiza kai umma ta yi, tare da cewa
"abinda na ke nufi, ba ka zaunar da ita ka gaya
mata irin abincin da ka ke son ci ba, tunda a
maganarka ka nuna ra'ayinta kawai take bi
wajen girka abincin".
Kallon umma ya yi sosai sannan ya ce
"umma ni fa yanzu ba ma ta abinci na ke yi ba,
ta tsaftar jikinta da ta gidan na ke yi, yanzu
haka zancen da na ke miki akwai kwanikan da
sun fi sati ba su ga wanki ba, parlourn mu kuwa
bana Jin tana sharewa bare mopping."
Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪13
©MRS SAIF
®NWA
Ajiyar zuciya umma ta sauke tare da fad'in
"bari zan je gidan na sameta na nuna mata duk
abinda ya dace, tunda ka ga bata da kowa a
garin nan, ni ce a matsayin mahaifiyarta, amma
na yi mamakin faruwar haka, don na san
Nadeeya akwai hankali".
Hmm! Kawai Faruk ya ce don yasan umma ba
ta ta6a ganin laifin Nadeeya, mik'ewa ya yi da
zummar zuwa masallaci don ya ji ana ta k'wala
kiran sallar magrib, sannan ya ce da fateema ta
had'a masa kayan abinci kafin ya dawo.
Yana dawowa ya tarar da lafiyayyen tuwon
shinkafa da miyar egusi, wacce ta wadatu da
kifi, ai kuwa nan Faruk ya gyara zama ya
kwashi girki, yana korawa da mango juice.
********
K'arfe tara ta gama shirinta na shiga mak'ota
duk da yau ta tsaya ta yi picking ledojin dake a
zube a parlourn, sannan ta yi k'arfin halin
kakka6o kujerun parlourn, don duk k'ura ta cika
su, kasancewar hazon da ake yi kwana biya,
maimakon ta share sai ta bar k'urar duk ta
bazu kan tiles d'in da ke parlourn da kan center
carpet.
Mayafinta ta jawo ta nufi hanyar fita, sai dai
kafin ta k'arasa sai ta jiyo kamar ana buga
k'ofa, K'arasawa ta yi tare da fad'in
"waye????
Muryar umma ta jiyo tana cewa bud'e
Nadeeya."
Da sauri ta bud'e k'ofar, sannan ta zube har
k'asa tana gaisheta, d'ago ta, ta yi tare da
rungumeta tana fad'in "lafiya Lau 'ya ta, sannan
suka nufi ciki.
Nadeeya ta rasa inda zata saka umma da
Fateema don murna, ta kwaso wancan ta
d'auka wannan, duk ciki kuwa babu wanda ta
girka da kanta, don duk drinks d'in kwali ne da
snacks d'in da Faruk ke ajiyewa,tunda ba iya
cin abincita ya ke yi ba.
Murmushi kawai umma ke yi ta ce
"Nadeeya bar shi haka kin ga yanzu safiya ce,
sai da muka yi breakfast muka fito, daga nan
ma asibiti zan wuce na ga likita, saboda ciwon
k'afar nan ya matsa mun".
Duk da umma ta sha mamakin ganin yadda
gidan ya fara dafewa, amma hakan bai sa ta
nunawa Nadeeya wani abu ba, anan dai ta yi
mata nasiha da muhimmacin kula da miji da
kuma tsafta.
Sannan kuma ta ce Fateema, ta tsaya ta taya
aiki, zuwa anjima idan Faruk ya dawo ya mai da
ta gida.
Ai kuwa fateema ta sha aiki ba na wasa ba, don
har d'akin Faruk sai da ta gyara, duk da yana
d'an gyara abinsa da kansa amma ba kamar
gyaran mace ba.
Har da turaren wuta ta kunna, tunda ga sunan a
cikin show glass d'in ta birjik, amma ba ta
sawa, a salima, Nadeeya ta d'auka don kwalliya
kawai ake jerasu.
Ita kanta Nadeeyar sai da gidan ya burgeta, sai
sannu take wa fateema.
Fateema kam murmushin yak'e take yi, don can
k'asan zuciyarta tana mamakin Nadeeya mace
har mace amma sai imani, don idan ka kalli
Nadeeya dole ka sakata a jerin kyawawan mata,
don fara ce sol sai dai, rashin sanin ciwon kai,
da kuma rashin gyara ya na nema ya maida
mata farar fatarta zuwa bak'a.
Faruk tun cilla k'afarsa cikin gidan, ya ji wani
sauyi ya ziyarci sassan jikinsa, K'arasawa
parlou ya yi anan ya yi tozali da kyakkyawar
k'anwarsa,tana masa sannu da zuwa da
murmushi d'auke a fuskarsa ya ce
"Fatee, ke ce a gidan na mu"???
Ta ce
"yeah ai na dad'e ma bro".
Faruk ya ce
"I see! Ga gida nan sai k'amshi ya ke yi.
Bai k'ara shan mamaki ba sai da Nadeeya ta
fito sanye da atamfar super Toronto red, d'inkin
ya amshi jikinta, duk da Faruk ba wani son
Nadeeya ya ke yi ba, amma sai ya ga ta yi
masa kyau sosai.
Fateema kallon yayan na ta, take yi cike da
jindad'i, don ta ga ya yaba da wankan
Nadeeyar, shi yasa ta takurata,sai ta yi wanka
ta chanza kayan jikinta, sannan ta feshe mata
jiki da turaruka kala_kala, har kwalliya da daurin
d'an kwali duk fateema ce ta yi mata.
Bayan sun ci abincin, wanda shi kan sa abincin
Fateema ce ta girka, Faruk ya yi shirin mai da
ita gida, Nadeeya ta nace sai ta bi su,Faruk bai
yi musu ba suka tafi tare.
10pm suka dawo dukansu a gajiye suke, don
haka agurguje suka yi shirin barci, kaitsaye
bedroom d'in su suka wuce, dama su Nadeeya
an d'irki maganin mata an yi tatil,don haka na
kwashi takarduna da alk'alamina na yi waje, don
ban sani ba ko sa mai gida hauka ta sha, kar ta
rutsa da ni....... Lox
Maman Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪14&15
©MRS SAIF
®NWA
Cikin farin ciki Faruk yau ya tashi, don jiya
barcin dad'i ya yi, don bai ji wannan tsamin da
hamami ba, a jikin Nadeeya komai lafiya suka yi
suka gama, don haka da wuri ya shirya ya fice
office, bai tsaya jiran Nadeeya ba, don sallar
asuba ma, da k'yar ta tashi ta yi.
Don shi kam yanzu ya saba shiryawa kan shi
komai, don idan ya tsaya jiran Nadeeya makara
kawai zai yi a banza.
Nadeeya kuwa ungulu ce ta koma gidanta na
tsamiya, don dama ita ba tama fuskanci inda
maganar Umma ta dosa ba, don ta d'auka irin
nasihohin da akewa amare ne, umma ta zo ta yi
mata na ta, domin tun a dutse gwaggoninta sun
mata, ta kuma ji amma ita kam har ga Allah ba
ta san ana amfani da su ba, don tun tasowarta
ta kan ga ana yiwa amarya wannan k'us_k'us
d'in, da ta kira shi marar amfani. (kun ji fa......
Anan ina kira da 'yan uwana mata musamman '
yan mata,masu shirin aure, irin nasihohin nan da
ake wa amare kafin akai su d'akin aurensu,
yana da kyau ki rik'e su, don akwai hikima a
cikinsu, amma fa wadanda ake wa hud'ubar
arziki).
Taran safiya bai k'arasa ba, Nadeeya ta yi
hanyar zuwa gidan maman Nabeela don k'afarta
har k'aik'ayi take mata don jiya ba ta je ba, an
sha hira ba ita.
*****
Anan aka sha hira, daga bisani aka yi zancen
bikin k'anwar d'aya daga cikin mak'ociyar su,
anan fa Nadeeya aka yi uwa aka makar6iya, an
ji zancen biki, har da cewa a kawo mata anko
zata yi, a cewarta za ta fi jindadin zuwa.
K'arfe 2 ta bar gidan don tana so ta dawo gida
ta had'a kud'in ankon sannan ta ba da d'inki ko
express ne a mata tunda ta ji an ce bikin wani
sati ne.
Sai da ta fara zuwa gurin mai kayan miya ta
siya, kafin nan sai da suka yi daru da shi don
duk wanda ya saka mata bai mata ba sai ta
zare shi, ta ce ya chanza mata,
wai bata son gwalagwaji. Tun yana mata
kawaici don ya ga matar aure ce, har suka fara
sa'insa da shi, daga k'arshe ta tattara kayan
miyarta ta yi gaba.
Daga nan ta wuce wurin mai nama, don kura ce
duk neman dake cikin Freezer d'in su ta soye ta
cinye.
Malam nama nake so cewar Nadeeya"
Mai nama yace "
na nawa ki ke so"???
Nadeeya ta ce
" na 1k".
Cewa ya yi to, sannan ya fara yanko tsoka yana
had'awa da k'ashi.
Sai ko Nadeeya ta ce
"Malam ni fa bana so da k'ashi".
Juyowa ya yi, yana dubanta sannan ya ce
"ni kam bana sai da na sai na had'a da k'ashi".
Tabd'i Nadeeya ta ce
"Ai ni kuwa bana buk'atar kashi, ya ya ke nan??
Mik'o mata kud'in ta ya yi tare da fad'in
"sai ki kara gaba, don ko uwata da k'ashi take
miya".
Maimakon Nadeeya ta k'yale shi, ta wuce
abinta, ai sai ta ce
"yo ni ina ruwana dan uwarka tana miya da
k'ashi, sai aka ce Maka ni ita ce"??
Kuturu da kud'in sa, alkaki sai na k'asan
kwano,ta k'arashe maganar tare da murgud'a
baki.
A zafafe mutum ya yi cikinta kamar zai daketa,
yana fad'in
"ni za ki zaga, nan take ya hau d'ura mata
ashar, nan fa rikici ya kaure, suka hau
d'ure_d'uren ashar, kan ka ce me mutane sun
fara taruwa, dak'yar abokan sana'arsa suka ja
shi, ita kuma Nadeeya ta kwashi ledar kayan
miyan ta sai gida, naman da ba ta siya ba
kenan.
Koda ta koma gida damuwa ce fal cikinta, ga shi
ba ta siye naman ba, yanzu haka zata yi girkin
ba nama, ga yunwa sai nuk'urk'usarta take yi,
don yau ba ta tsaya cin abinci a gidan maman
Nabeela ba.
Don haka ta yanke shawarar d'ora farar shinkafa
ta ci da mai da yaji, don haka ta kuma rufe gida
ta je neman barkono, ba ita dai ta gama dafa
farar shinkafa da dakan ya ji sai bayan la'asar,
don haka ta ce ta huta a ci har dare.
Shi kan sa mai gidan mai da yaji zai ci idan ya
dawo a tunanin Nadeeya ke nan, ba ta san
Faruk ko abinci ya fiye ya ji ba ci yake ba, bare
tsurar farar shinkafa......
Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: [8/10, 10:42 AM]
Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪16
©MRS SAIF
®NWA
Bayan ya dawo ya yi wanka ya huta, ya buk'aci
Nadeeya ta kawo masa abincinsa, nan da nan
kuwa ta tashi bazar_bazar ta nufi kitchen, ba
jimawa kuwa, ta kwaso kayan abincin ta dire a
gabansa.
Shinkafar ya fara bud'ewa sannan ya ce
"Ai ba ki kawo miya ba."
Sai kuwa Nadeeya ta ce
"au ba ka ga yaji a leda ba, sannan ga mai nan
a waccen robar".
Juyowa Faruk ya yi yana kallonta ya ce
"uhhm! Sai yaya!"???
Sai ko Nadeeya ta ce
"sai ci".
Tsaki ya ja, sannan ya ce
"wai don Allah me ke damunki ???
Ta yaya za ki kawo mun, mai da yaji da
daddaren na ci?? Gaskiya ya kamata ki gyara".
Nadeeya shiru kawai ta yi tana harare_harare.
Mik'ewa ya yi, yana cewa ki samu wani abun ki
kawo mun na samu na ci amma ba wannan ba".
Ta ce
"kamar me kenan??
Yace
"ke ba mace ba ce???
ai kin san abinda ya dace a ce na samu na d'an
ci kafin na kwanta".
Dogon tunani Faruk ya saka Nadeeya, amma a
iya tunaninta, ba ta gano abinda za ta kawo
masa ba, don gaskiya ita kam yanzu ba za ta
iya wani d'ore_d'oren girki ba.
Don haka ta je ta ce masa ita gaskiya ba ta san
abinda zata kawo masa.
Ce da ita kawai ya yi ta je ta kawo masa fresh
milk da cake, don yasan ko ta kuma yin wani
girkin ba lallai ya iya ci ba.
Ko da kuwa ta dawo fresh milk kawai ne a
hannunta, ta fara magana tare da sosa kai
"Ai......da dama ina so na gaya Maka kusan
komai ya k'are fa".
Kallonta Faruk ya ke yi tare da nazarin
maganarta, ya ce
"wai kina nufin komai ya k'are"???
Gyd'a kai ta yi, tare da cewa
"har kayan abinci, suma sun kusa k'arewa".
Don kuwa kullum za ta yi girki da yawa take
girkawa, har yau ta kasa kwatanta dai_dai
cikinsu, ko na ce cikinta,tunda kusan ita kadai
ke ci, sai dai ta dafa da yawa, idan ta samu
almajirai ta basu idan ba ta samu ba ta zuba a
shara, shi yasa tun daga wajen gidan bolar su
ke wari.
Da hannu Faruk ya mata inkiya ta tafi kawai,
sannan ya dafe goshinsa da hannu,, yana
jimamin hali irin na Nadeeya.
Daga k'arashe ya zari key d'in motarsa ya nufi
eatery, duk da shi ba gwanin cin abinci a eatery
ba ne, tun yana saurayi, don ummansa ta
k'ware a girke_girken da ya ke so.
Sai ga shi yanzu da aurensa zai fara bibiyar
wurin cin abinci sanadin BALLAGAZAR MACE.....
Mum Twins 😘
[8/10, 10:42 AM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪17
©MRS SAIF
®NWA
Washe gari kuwa wuraren 12 na rana ya dawo
gidan don kawo kayan abinci, sai dai ko da ya
dawo Nadeeya ba ta nan an fita gantali, don
haka sai da ya kirata a waya, sannan ta zo.
Ai kuwa Faruk ya nuna mata 6acin ransa don
kuwa ba ya son yawo, don ya tsani gantalin da
mata ke yi a wasu unguwanni.
Sai ka ga mace ba za ta zauna a gidanta ba, sai
dai kullum tana garari a cikin unguwa bata gidan
waccan ba ta gidan wannan daga nan sai
tsegumi ya yawaita.
To shi kam ba zai d'aukan mata yawo ba.
Don haka yace da ita kada ta sake fita ba tare
da izininsa ba.
Nadeeya kad'a kai kawai ta yi, amma ba mu sa
ni ba ko ta ji???
Sai dai mu jira amsa nan gaba.
Bayan ta shige cikin gidan ne, ya bud'e boot ya
fara fitowa da kayan da ya siyo, yana ajiyewa a
parlor buhun shinkafa ne da cartons na taliya da
macaroni su sugar milk, drinks da dai sauran
kayan amfanin gida.
Ya d'auko ledar kajin da ya siyo da kifi, yana
mitar cewa dole ma ya samu yaron da zai rik'a
taya shi wani aikin, don yanzu ko shigo da
kayan nan aiki ne, ga shi yanzu sai ya je zai
kuma d'ibansu zuwa store.
Maganar zucin da yake yi ne ta tsaya cak,
sakamakon K'arasawa da yayi cikin parlourn,
mamaki ne k'arara a fuskarsa, wai ana nufin
Nadeeya har ta kwashe kayan da ya shigo da su
har da buhun shinkafa????
Kallon da ta ga yana mata ta d'auka ta birge shi
ne, abinda ta yi, shi yasa sai wani d'ashe baki
take.
Zubewa ya yi a kujera yana tunanin wannan
wace irin mace ce, komai na ta sangangan
kamar namiji, shi da yake son mace mai aji, da
yauk'i, wacce ta amsa sunan mace..
*******
Furzar da wata iska yayi, ya had'a hannayensa
ya murza sannan ya mik'e tare da fad'in
"bari na koma office, akwai ayyukan da na
baro".
Bai tsaya jiran mai za ta ce ba ya fice abinsa.
Ita kuwa mere baki ta yi ta fara magana
k'asa_k'asa
"umma ta gaida aysha mutum komai aka yi ba a
burgeshi".
Faruk kuwa bayan ya isa office ya ji yau, yana
sha'awar cin farfesun kifi don yana son shi
sosai, da ya yanke shawarar idan ya tashi aiki
ya fara zuwa gun cin abinci ya ci sannan ya
wuce gida, sai dai ya tuna da Maganar umma
akan ya rik'a bata dama tana masa irin girkin da
ya ke so.
Don haka ya kira Nadeeya a waya ya shaida
mata abinda ya ke so ta dafa masa.
Bari mu ji yanda girkin Nadeeya zai kaya
lol............. Dama macaroni ta yi niyyar dafawa
da miya, ta d'ora ruwan zafi kenan Faruk ya
kirata, don haka ta ce hutarere ba sai ta yi miya
ba, sa ta yi farfesun kifin tunda miya ai duk miya
ce, a ci da macaronin.
Kifin kuwa wanke shi kawai ta yi sama_sama,
ba maganar ko d'an lemon tsami ta saka wurin
wankin don ya kashe k'arnin, haka ta watsa shi
a tukunya ta had'a kayan miyanta ta yi blending
har da tomoto ta watsa, ba a maganar a soya
kifin kafin had'a farfesun, bare maganar wani
kayan k'amshi, gaba d'aya ta had'a komai da
komai ta d'ora.
Bayan ya dawo Nadeeya sai wani yak'e baki
take yi ita a lallai yau ya bata aiki ta yi, tasan
dole yau ta burge shi. Don haka nan da nan aka
kawo masa abinci.
Yana bud'ewa kuwa wani k'arni ya dake
hancinsa, kamar ya maida ya rufe sai dai ya ce
bari dai ya ci ya ji, don kar ya sare mata guiwa,
tun da ya d'auko salar tsokar kifin ya ke Jin
wani santsi a jikinta, duk da haka ya daure ya
tura baki, ai kuwa da sauri ya mike yana kakarin
amai ya nufi toilet, nan ya fara kwara amai, don
bacin kifin da ya ci, har d'an abinda ke cikinsa
duk ya amayar, dawowa parlourn ya yi ya
zauna.
Nadeeya ta kalle shi cike da tsiwa ta ce
"yanzu abincin nawa muninsa har yakai ya saka
ka amai???? "
Kallonta ya yi a kasalance ya ce" ki fara ci ki ji
kafin ki yi k'orafi.
Tace
"ci na nawa kuma???
Ai wanda na ci ya fi wanda na kawo Maka
yawa.
Kalon ban yarda da abinda kika ce ba ya watsa
mata.
Ganin haka yasa ta d'auko kwanon farfesun ta
ajiye ta zauna ta fara kwasa har romon, ita ke
sha Faruk ke ya tsine fuksa, daga k'arashe ya
tashi, ya bar wurin, yana matukar mamakin
Nadeeya tabbas ta wuce duk tunaninsa, ta wuce
mazaunin inda ya ajiyeta.
Don shi a tunaninsa d'an Adam ba zai iya cin
wannan farfesun da ta yi ba , yanda ya ji shi a
bakinsa sai wani mugun santsi kamar an sa
sabulu ga shi bai dahu ba, sai zallan zak'in farin
magi ke ta shi.....
Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪18
©MRS SAIF
®NWA
Washe gari, ko da Faruk ya tashi ransa duk ba
dad'i, haka dai ya shirya zuwa aiki, don ko d'an
ruwan tean da ya saba sha yau bai sha ba, sai
wurin 12 ya samu sukunin zuwa pizza hot, ya
d'an samu abinda ya saka a tunbinsa, don ji
yayi har ya fara Jin wani jiri_jiri, saboda yunwa.
Dan haka da ya tashi daga office, sai da ya fara
zuwa gidansu ya ci abinci sannan ya wuce gida,
ummansu tana ta tambayarsa lafiya ta ga duk
ya fad'a, bai ce da ita komai ba illah ba ya
jindadi kwana biyu.
Ta masa Allah ya sawwak'e, sannan ya fito
daga gidan.
Nadeeya kuwa tana can tana sak'a da warwara,
ta yanda zata 6ullowa Faruk ya barta ta je biki,
don gobe ne kamu, don haka ta yanke shawarar
zuwa ta gaya masa.
Ko da ta shiga d'akin sa yana zaune yana wani
aiki a laptop d'in sa.
Sallama ta yi sannan ta nemi wuri ta zauna,
sallamar kawai ya amsa mata, ba tare da ya
kalleta ba. Sai kuma ta fara magana
"Faruk dama ina so na gaya maka gobe akwai
bikin da za mu je".
Kallonta ya yi yana mamakin bikin wa za ta je,
tunda yasan ba ta da kowa a kano duk danginta
suna dutse. Don haka ya mai da hankalinsa ga
laptop d'in dake gabansa yace "bikin wa
kenan'????
Gyara zama Nadeeya ta yi, sannan cikin inda
inda ta ce
" eh.... ai dama akwai wata mak'ociyar mu ce,
za a yi bikin k'anwarta".
Bai d'auke kan sa daga aikin da yake yi ba, ya
fara magana
"anan kusa da mu ne za a yi bikin???
Sai kuwa ta amshe cikin zumud'i don ta ga
alamar kamar zai barta, ta ce
"Ai yayar amaryar ce a layin su maman Nabeela,
nan k'asan layin mu suke, amma a gidan
iyayensu da ke kurna za a yi komai na bikin".
What!! Faruk ya fad'a sannan ya ce
"kin san nisan da ke akwai daga nan zuwa
kurna kuwa???
Turo baki ta yi tare da cewa
"ni ina zan sa ni, ni kawai izini na ke buk'ata,
gobe mu je ka ga na gano daga can".
Kaitsaye Faruk ya ce
"ba za ta je ba".
Dan zaro ido ta yi ta ce
"ba zan je ba????
Gyd'a mata kai ya yi alamar haka ya ke nufi.
K'wafa ta yi, sannan ta mik'e ta fita tare da Jan
k'ofar d'akin da k'arfi ji kake garam!!
Rufe laptop d'in ya yi, ya jingina bayansa da
kujerar da yake kai, sannan ya lumshe ido yana
tunanin matsaloli irin na Nadeeya.
Nadeeya kuwa ta k'udirci aniyar ko za a mutu,
sai ta je bikin nan, don ba za ta yi anko a banza
ba,tunda yanzu idan ya fita tun safe sai wurin
9pm ya ke dawowa, don haka har ta je ta dawo
bai dawo ba.
Ba ta san ita ce silar saka Faruk dadewa bai
dawo ba, don idan ya tashi daga aiki sai ya fara
zuwa gidan abinci ya ci, ko gidan su, ko
abokanansa su ja shi zuwa na su gidan
musamman aminin sa Abbas, don matar sa tana
da hankali yana sha'awar yanayin zaman su.
K'arfe biyun rana suka isa gidan bikin, Nadeeya
an sha anko ta fito cas kamar ba ita ce
k'azamar nan ba. Ai kuwa Nadeeya ta kira
wannan fitar da farar tafiya don ta had'u da
friends d'in ta da suka yi secondry school tare
dama su 'yan Kano, amma GGSS Darki suka yi
dake jigawa.
Nadeeya ce ta fara shaida su, cikin tsananin
farin ciki ta nufi kujerun da suke zaune tana
cewa
"wai Samee da Zee na ke gani ko ido na ne???
Cikin mamakin Jin an kira sunan su, suka jiyo a
tare, ido suka zaro tare da fad'in " Nadeeya!!"
Nadeeya kuwa sai murmushi ake zabgawa,
sannan d'aya daga cikin su mai amsa sunan
Zee, wadda daga gani tafi d'ayar felek'e da iyayi
ta ce
"it's been far too long, kamar ba ke a duniya, ko
neman mutane ba kya yi, ga shi muna yawan
zuwa dutse, don dai ba mu da adress d'in ki ne
da kin gan mu".
Kujerar da ke gefensu ta ja ta zauna, sannan ta
ce
ai kar ku damu don kuwa yanzu muna tare
domin nima na zama 'yar kano, don aure ya riga
ya kawo ni da zama".
Shewa suka yi sannan suka ce
"a lallai kuwa muna tare".
Anan dai suka yi exchanging contact, tare da
yiwa Nadeeya alk'awarin zuwa, tunda ba su da
wani nesa a tsakaninsu.
Faruk kuwa bayan ya tashi daga aiki, haka
kurum, yau ya ji baya son zuwa ko ina, don haka
ya d'au hanyar gidansa, sai dai ya tsaya 212
Bakery ya siye bread na breakfast da cakes
varieties ya wuce gida.
6:30pm ya shigo gidan, bayan yayi parking ne,
ya k'arasa k'ofar parlourn yana knocking amma
shiru ba alaman za a bud'e masa, mota ya
koma ya d'auko extra key da ke hannunsa ya
bud'e, yana cewa a ransa yanzu haka barci take
yi.
Sai dai har yayi wanka ya shirya bai ji alamunta
ba, don haka ya yanke shawarar lek'awa
d'akinta ya gani ko lafiya, tura k'ofar d'akin ya
yi ya shiga, sai da wayam bata ciki, sai wani
uban hamami dake welcoming nasa, wani dogon
numfashi ya ja, don ganin d'akin a hargitse
kamar na tsohuwar mahaukaciya, ko ina kaya ne
a zube, still d'akin ya ke bi da ido, don shi rabon
da ya shigo d'akin nata har ya manta, to mai
zai zo ya yi???
Bayan ko d'akinsa ta shiga Allah Allah ya ke yi
ta fito, don ji yake duk shak'ar d'akin nasa ya
chanza.
Ya fi 3mnts a tsaye, sannan ya yanke shawarar
lek'awa toilet, sai dai tura kan sa ke da wuya
cuki toilet d'in ya banko k'ofar tare da toshe
hanci, sai da ya fito parlour ya saki numfashi
tare da zubewa kan kujera, don yasan tabbas ta
je bikin da ya hana ta zuwa, idan kuwa haka ne
lallai yau zata ga 6acin ransa....
Mum Twins 😘
[10/16, 4:22 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪19&20
©MRS SAIF
®NWA
Wayarsa ya ciro daga aljihunsa, ya danna kira a
no Nadeeya, dai dai lokacin su Nadeeya na
ak'ilun neman adaidaita, ta ji wayarta na
ringing, sunan da ta ga ya bayyana kan screen
d'in wayar ya sa ta ji cikinta ya murd'a, don duk
tsiwarta tana Jin shakkar Faruk.
Kasa d'auka ta yi, har wayar ta tsinke, bai dad'e
da tsinkewa ba, wani kiran ya shigo, gabanta ne
fa ya shiga dukan uku_uku don dai ta tabbatar
da Faruk ya dawo gida, tunda ta ga kira haka a
jere.
Sai a kira na uku, Hafsat (wadda ake bikin
k'anwarta tata ta ce da Nadeeya,
"ki d'auka mana sai kiranki ake yi, yanzu haka
mai gidan ne, ai sai ki gaya masa wahalar abun
hawa ake yi, har yanzu muna tsaye a titi ba mu
samu ba".
Ajiyar zuciya Nadeeya ta sauke, a ranta ta ce
"don ba ki san ba da saninsa na fito ba shi yasa
ki ke wannan maganar".
Faruk kuwa ya cika yayi fam, wato wayar ma
bata da lokacin d'agawa???
Har ya je sallah ya dawo ba alamar Nadeeya,
don haka ya sake kiran wayarta, cikin k'arfin hali
Nadeeya ta d'aga ta ce
"hel..... Faruk ya katseta a zafafe da fad'in
"ki tsaya a gidan bikin, ba na buk'atar
dawowarki", daga haka bai kuma cewa komai
ba, ya katse wayar.
******
Nadeeya ta yi sakato da waya a hannunta, a
ranta ta ce
"yanzu ya zan yi???
Da daddaren nan dai ko giyar wake na sha
bazan nufi dutse ba, sannan tunda ya ce kar na
nufi gidansa gwanda kar na koma, don dama ba
na gabansa, kar ya je ya mun wulaqancin da ko
kare ba zai ci ba.
Don haka ta yanke shawarar wucewa gidan su
Faruk d'in, sai dai ta san a Rijiyar zaki suke,
amma ba ta san yadda zata kwatantawa mai
adaidaita sahu ba, tunda ita ba 'yar gari ba ce,
kuma duk zuwanta gidan tare da Faruk ne.
Tana cikin wannan tunanin, suka samu adaidaita
sahu, abokanan tafiyarta, sai kiranta suke yi ta
zo, su tafi, anan ta kwashe abinda y faru ta
sanar musu.
Hafsat ce ta ce "
Ayya! Nadeeya kin yi shirme ni na d'auka da
izininsa ki ka zo,kin...... D'ayar matar da suke
tare ta katseta ta hanyar cewa
" hafsat ki zo mu tafi mu kam, kin san dai da
k'yar mu ka samu waanna adaidantan, ga shi
yana maganar zai tafi idan ba mu tashi tafiya
ba".
Ba ta sake cewa k'ala ba Hafsan,ita ma ta shige
cikin adaidaita, ya ja suka tafi, suka bar na
Nadeeya a titi ita kad'ai.
Ta fi k'arfin 15mnts a tsaye, tana tunanin abun
yi, daga baya ta yanke shawarar kiran Fateema
k'anwar Faruk, bayan ta kirata ne, take
tambayarta kwatancen gidansu, nan da nan
fateeman ta sanar da ita, amma sai da ta
tambaye ta ko lafiya???
Nadeeya ta ce
"lafiya k'alaau, kawai mun zo biki ne, na ke son
k'arasowa na gaishe da Umma".
Duk da k'asan zuciyar Fateema ba ta yarda da
maganarta ba, amma sai ta ce da ita "toh,Allah
ya kawo ki lafiya".
Cikin sa a ta samu keke napep, nan da nan ya
kawo ta, da yake gidan na su ba 6oyayye ba ne
har k'ofar gida ya ajiye ta.
Bayan sun gaisa da umma ne, take tambayarta
ina Faruk, nan da nan ta juyewa Umma abinda
ya faru.
Cikin mamaki umma ta ce
" gaskiya ba ki kyauta ba, Nadeeya ai ita mace
da biyyayya aka san ta, shi kuma Faruk ya biye
miki da ba ki yi hankali zuwa nan ba ki ka ce
garinku za ki wuce da daddaren nan ai da abu
bai yi dad'i ba".
Umma har ta d'auki waya za ta kira Faruk sai
dai ta ce bari ta bar shi sai da safe, tunda ya
saba zuwa gaishe ta kullum, sa yi maganar idan
ya zo.
Don haka ta ce da Fateema ta kai Nadeeya ta yi
wanka ta bata wani kayan marar nauyi ta
chanza sai ta zo ta ci abinci, ta kwanta ta huta.
Nadeeya kuwa cewa ta ke a ranta ita ba wani
wanka da zata yi don sanyi take ji, yaushe ta yi
wankan da har zata kuma yin wani.
Bayan sun shiga d'akin Fateema ne, take mata
maganar wankan, sai ko ta ce
"gaskiya ita ba wankan da zata yi, don sanyi
take ji"
Fateema ta ce
"Ai da ruwan d'imi ne".
Ta ce ita fa baza ta yi ba, sanin hali yasa
Fateema ta shareta da zancen.
Abincin ma da aka kawo mata tsakura ta yi,
sannan ta yi sallah ta nemi lafiyayyen gadon
Fateema ta haye sai barci.
Ko da Fateema ta shigo ta tarar tana ta sharar
barci, sai dai ta k'udundune da blanket kamar
marar lafiya, K'arasawa ta yi bakin gadon da
niyyar rage mata bargon, sai dai zafin da ta ji
jikin ta ya yi, ya bata mamaki har d'an karkarwa
take yi alamun zazz6i ya ci k'arfin ta, da sauri
fateema ta janyota jikin ta, tana tunanin to
dama bata da lafiya ne, ko kuma yanzu ciwon
ya sameta.......????
Afuwan please! posting sai Monday kuma, ina
da uzuri ❤❤👌🏻
Maman Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [8/13, 9:06 AM]
Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪21
©MRS SAIF
®NWA
Girgiza kanta ta fara tana fad'in
"Aunty Nadeeya ba ki da lafiya ne??? Na ji jikin
ki zafi rau". Da k'yar Nadeeya ta iya bud'e
idonta ta ce
"eh, dama tun kafin ta fito daga gida, ta ji kanta
yana mata ciwo, daurewa kawai ta yi ta fito".
Sannu"Fateema ta fad'a tare da ajiye kanta
akan pillow ta yo hanyar fita don sanarda
Umma, da sauri ta k'arasa wurin da umma ke
zaune tana fad'in
"Umma ashe Aunty Nadeeya ba ta da lafiya, ba
ki ji yanda jikinta ya yi zafi ba ".
Subhannal! Umma ta ce tare da mikewa tsaye,
mu je na ganta".
Ko da suka shiga d'akin itama Umma ta yi
mamakin ganin Nadeeya a halin da ta sameta,
ta yi ta mata tambayoyin abinda ya kawo mata
ciwon nan take, abinda ta gayawa Fateema shi
ta kuma maimaitawa Umma.
Saboda haka Umma ta ce
"Fateema ta mik'o mata phone d'in ta dake
parlour, da sauri ta hau neman no Faruk, bayan
ta kawo mata wayar.
Sai dai an yi rashin sa'a don abu d'aya ake
gaya mata, number'n is switched off".
Don shi kam Faruk tunda suka gama waya da
Nadeeya ya kashe wayarsa ya saka charging,
bayan ya gama abinda ya ke yi, yayi
kwanciyarsa don shi kam har ya manta da
maganar wata Nadeeya.
Agogon da ke manne a d'akin Umma ta d'aga
kai ta kalla, 10:30pm a fili ta ce
"gaskiya dare ya yi, ban son driving d'in dare, da
mun je asibiti, amma bari a mik'o miki magani
ki sha Insha Allah gobe da sassafe sai mu wuce
asibiti".
*******
Haka aka yi kuwa, tun da safe suka yi shirin
zuwa asibiti, don ko tabi kan Faruk Umma ba ta
yi, suka yi tafiyarsu, sai Fateema da suka bari a
gida, ita ma idan ta gama shirinta makaranta za
ta wuce.
Sai yamma liki's Faruk ya zo gidan, lokacin su
Umma sun dad'e da dawowa daga asibiti.
Nadeeya na kwance akan doguwar kujera, yayin
da ta yi matashi da cinyar Umma, sallamar
Faruk ta dira cikin kunnuwansu.
Annurin da ya shigo da shi akan fuskarsa 6at ya
6ace, ganin Nadeeya Kane_kane a cikin gidansu,
don shi har ga Allah ya gaji, da halin Nadeeya,
don shi bai ga amfanin aurenta ba, gwanda
mishi zaman sa ba aure,don bai ga abinda auren
Nadeeyan ya tsinana masa ba.
Umma ce ta katse masa tunani ta hanyar fad'in
"UmarulFaruk tunanin meye ka ke yi ne haka,
duk ka wani 6ata fuska kai da ya kamata ace,
yau d'in nan kana cikin tsananin farin ciki", ta
k'arashe maganar tare da sakin murmushin Jin
dad'i.
Cikin rashin fahimtar in da zancen Umma ya
dosa Faruk ya ce "Umma wani farin ciki kuma,
Allah abinda yarinyar nan take yi kwata-kwata
ba ta kyautawa yanzu ya kamata a...... Umma
ta katse shi ta hanyar d'aga masa hannu.
Murmushin ne dai d'auke a fuskarta ta ce
" ya kamata ka tsaya ka ji albishir d'in da nake
tafe da shi kafin, ka fara k'orafi".
Wuri ya samu ya zauna, sannan ya ce to Umma
ina Jin ki.
Umma ta ce
"tun safe muka je asibiti don Nadeeya tunda ta
zo jiya bata da lafiya, amma Alhamdulillah
rashin lafiyan da ake buk'ata ne, don gwajin
farko ya nuna Nadeeya na d'auke da juna biyu!"
Zaro manyan idanunsa waje ya yi tare da
mikewa tsaye ya K'arasa wurin da Umma ke
zaune ya dafa gwiwowinta ya ce
"Umma da gaske Nadeeya ciki gareta??
Umma cikin zolaya ta ce
"a'a wasa na ke, don sanin yadda Faruk ke da
masifan son yara".
Nan da nan kuwa ya 6ata fuska, har sai da
Umma ta ji tausayinsa ta ce
"ta ce da gaske ne fa Faruk, nan da wata
bakwai ka sa ran d'aukan baby in Allah ya
yarda".
Wani irin farin ciki marar misaltuwa ya mamaye
zuciyar Faruk, ji yake kamar ya d'auki Nadeeya
ya goya don murna.
Sai kuma ya zubawa Nadeeya ido yana tunani
"a ransa da gaske Nadeeya na d'auke da gudan
jininsa bai ta6a Jin son Nadeeya ko na second
ba, amma yau sai ya ji ta samu wata martaba a
zuciyarsa...
Mum Twins 😘
[8/15, 8:06 AM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪22
©MRS SAIF
®NWA
Anan dai Umma ta yanke shawarar Nadeeya za
ta zauna da su, har ta k'ara warwarewa, shi kan
sa Faruk ya amince da hakan, sai dai ya ce
Fateema ta je ta gyara masa gidan, don gaskiya
baya Jin dad'in zaman gidan a yadda ya ke.
Haka aka yi kuwa don dai sai da Nadeeya, ta yi
3wks a gidan su Faruk zuwa lokacin ta warke
ras, sai dai ita kan ta Umma d'an zaman da
suka yi ta fahimce Nadeeya ba k'aramar
k'azama ba ce.
Don haka tayi ta mata nasiha akan tsafta, amma
ina wanda ya yi nisa baya Jin kira.
A satin ne kuma ta koma gidanta, k'azanta ta
kuwa sabon shafi fal ta bud'e, don irin cikin nan
ne mai sa zubar da yawu ke gareta, don haka
duk inda ta samu watsarwa take yi, idan ta yi
abin arziki ta zuba aleda, amma fa ledar duk
inda aka ga dama ajiyeta ake yi daga nan ta
tsiyaye guri duk ya dame.
******
Saboda haka Faruk bai ta6a shiga tashin hankali
ba irin na wannan lokacin ba, gaba d'aya ya ji
ya tsani gidan da duk abinda ke cikin sa, ga shi
yana samun k'arin girma da d'aukaka kullum a
wurin aikinsu saboda k'wazonsa,don yanzu haka
ya siye wani makeken fili a ring road har ya fara
gini ya watsar don be ga amfanin saka mace irin
Nadeeya a gida mai kyau ba, domin akan
matsalar Nadeeya gaba d'aya ya rasa
nutsuwarsa,kullum cikin tunanin mafita yake,
abokanansa da dama sun ba shi shawarar ya
k'ara aure sai dai gaskiya shi ba shi da ra'ayin
mata biyu, don haka yanzu idan ya fita tun
sassafe baya dawowa sai kwanciyar barci, don
abinci kam ya yafe cin sa a gidan tuni.
Don haka duk wani eatery sabo da tsoho in dai a
garin kano yake,Faruk ya San da zaman sa.
Wata ranar laraba Nadeeya ta tashi da rashin
lafiya, don haka Faruk ya tsaya tare da ita bai
fita ba, don yanzu duk abinda take yi lalla6ata
yake don yana matukar tausaya mata albarcin
d'an sa dake jikinta.
Nadeeya sai wani narkewa take yi, ita a dole ga
mai ciki, ranar Faruk shi ya yi aikin gidan kaf, ya
gyara ko ina tsaf abinci ne dai ya fita ya siyo
musu.
Ko da ya dawo ya tarar da Nadeeya ta yi
bak'i,k'awayentan nan da suka hadu gidan biki,
don haka kallo d'aya ya musu ya shige kitchen
domin ajiye ledojin da ya shigo da su, don ya
tsane duk wani abu da ya shafi Nadeeya,
musamman wadan nan 'yan matan daga gani ba
su da wata cikakkiyar tarbiyya tun daga yanayin
kayan da suka saka.
Su kuwa su zee tun da suka d'ora k'wayar idon
su akan Faruk suka dask'are anan, musamman
Zainab da da k'yar ta hado wani yawu ta
had'iye, body language sukai using tsakaninsu,
nan take na ga sun mik'e suna sa6a bags d'in
su tare da ce wa Nadeeya
"mu za mu tafi sai mun kuma dawowa kenan"
Itama Nadeeyar mikewar to yi tana fad'in
"haba sameera da zainab, tun yanzu na d'auka
sai dare, a tare suka had'a baki suna cewa
"haba mun ce fa za mu dawo, dawowa ta
musamman ma kuwa".
Yak'e baki Nadeeya ta yi alamun ta ji dad'i
sannan ta ce
"Allah ya kai mu".
Suka bi ta da "ameen".
Bayan sun fito duban junansu suka yi tare da
had'a baki za su yi magana, sai samee ta yi
shiru ta ce
"fara fad'an taki maganar tukun".
Zee ta ce
"me za ta ce illah guy d'in can ya tafi da
imaninta,don ta ga maza kala - kala, amma
gaskiya Faruk na musamman ne kyansa da
yanayinsa duka sun mata, ta k'arashe maganar
da cewa
"Samee ni fa ya mun 100%,I really luv him with
ol my heart, kin san na dad'e ina mafarkin
samun namiji irin shi."
Kallon ta samee take yi sosai duk da bata yi
mamakin kalamanta ba, tunda ta san halin
k'awarta ta ba tun yau ba da son auren
kyakkyawan miji, mai kuma ganin gabansa tar,
duk da ita ba wani kyau ne da ita ba.
Amma sai ta ce
"yanzu kina ganin ba matsala zee??? Wata kila
yana son matar sa, ba lallai ki samu shiga ba".
Wata dariya Zee ta tintsire da ita sannan ta ce
"sai ka ce ba ki sanni be, nd then ki kalli mace
kamar jaka a gida, kin san Allah ban yi zaton
mijin ta yana nan ba, a yanayin da muka tarar
da ita".
Samee ta kar6e da cewa
"ba ke kadai ba, gaskiya yana k'ok'ari,d'an
zaman da na yi kusa da ita da k'yar na ke iya
had'iye yawu"
Zee ta cigaba "yanda kika san mushe haka take
bugawa, kin ga kuwa k'wace goriba a hannu
kuturu ai ba zai yi wahala ba...
Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪23
©MRS SAIF
®NWA
Ba a rufa sati da zuwan su ba, su ka kuma
dawowa sai dai sun yi rashin sa'a don ba su
samu Faruk a gida ba, amma da yake 'yan
duniya ne sai da suka yi dabara da suka samu
cikakken bayani akan sa, daga gurin
Nadeeya,don har phone number d'in sa sai da
suka sata a wayar Nadeeya.
Bayan sun yi nasarar gano yana aiki ne a federal
character, branch d'in su dake Bello road, don
haka zee ta ci alwashin daga nan, can za ta
nufa.
Faruk yana tsaka da aiki, sai ya ji an ce wai ya
yi bak'i, ya yi zaton abokan huld'arsu ne, don
haka kaitsaye ya ce
"ace su shigo".
Amma a mamakinsa sai ya ga mata, don haka
kallo d'aya ya musu ya d'auke kan sa, don shi
ya manta in da ya ta6a ganin fuskokinsu, a
dak'ile ya ce
"me ke tafe da ku ne"??
Zee ce ta tashi don K'arasawa zuwa inda Faruk
yake zaune sai wani karairaya take, ko ina na
jikinta motsi yake, saboda yanayin salon tafiyar
da take yi, ga shi wani riga da wando ne a
jikinta duk sun dameta, gaban rigar kusan a
bud'e yake, kan ta kuwa ya sha kitson
attachment wanda ya sauka har gadon bayanta.
Sauke k'wayar idonsa ya yi akan tulin files da ke
gabansa, da zummar cigaba da aikinsa, don
kallonta ba k'aramin k'ona masa rai ya ke yi ba,
don shi tun da suka shigo ya ji ya tsanesu, don
sun fi masa kama da karuwan gida.
Maganar zee ce ta dawo da shi daga tunanin da
ya ke, ta ce
"Alh Faruk ba ka gane mu ba ne"??
Faruk ya ce ban ma sanku ba,"
Zee ta ce a ranta "daga gani wannan shugaban
Jin kai ne, amma a fili sai ta ce
" k'awayen Nadeeya ne, da muka je gidan ku
last Wednesday, dama mun yo hanyar nan ne
muka ce bari mu zo mu gaisheka". Ta k'arashe
maganar tare da kashe masa ido d'aya.
Faruk ya ce
"na gode amma don Allah kar ku kuma zuwa
don da mata ta ku ke da alak'a ba ni ba",duk da
a ransa tambayoyine birjik yake da su, ta yaya
suka samu address na gurin aikin sa, kuma me
suka zo yi,duk da sun ce wai gaishe shi suka zo
yi, yasan sarai ba haka yake a zuciyarsu ba,
amma saboda baya son magana ta tsawaita a
tsakanin su yasa kawai ya shanye
tambayoyinsa.
Zee har ta bud'e baki za ta ce wani abu ya
d'aga mata hannu, sannan ya nuna mata k'ofa
alamar su fita, cikin k'unan rai samee ta mik'e,
don ita takaici bai barta, ta ce k'ala ba,da sauri
ta nufi k'ofa yayin da zee ta biyo bayan ta.
******
A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah, don yau
ne Nadeeya ta haifi santalelen
yaronta,kyakkyawan gaske, ga shi k'ato, Faruk
kam yau kamar ya taka rawa yake ji,don farin
ciki, in banda hamdala ba abinda ke fita daga
bakin sa.
Ranar suna yaro ya ci suna Muhammad amma
ana kiransa da Ansar, an sha shagalin suna, don
'yan uwan Nadeeya kaf ba wanda bai zo daga
dutse ba.
An yi taron suna an waste lafiya an bar mai jego
da d'an ta, sai wata tsohuwa da zata zauna da
ita zuwa lokacin da za su yi arba'in.
Sai da suka yi wata biyu cif tsohuwar ta
gangama yana ta-yana ta, ta yi gaba, aka bar
Nadeeya daga ita sai halinta. Don kuwa
k'azanta yanzu ne ta samu wurin zama, don
daga ita har yaron na ta, ba sa shak'uwa don
wani irin k'arni ke tashi a jikinsu.
Saboda idan Nadeeya ta saka bra sai ta yi sati
bata chanza ba, wanka kuwa tun da ta gama na
jego sai ranar da ta ga dama take yi har ta
yaron ba kullum ta ke masa ba, ga shi irin yaran
nan masu tumbud'i, ga shi Faruk yana masifar
son ya ga yaronsa a jikinsa duk likacinta da ya
ke gida, amma ina da ya d'auki yaron wani
k'arni ke dira cikin hancinsa, a dole yake ajiye
shi ya riga masa wasa daga nesa.
Faruk bai k'ara sanin yana cikin babbar matsala
ba sai da ta haihun nan, don yanzu tsakanin sa
da Nadeeya sai kallo daga nesa, don ko
mu'amular auratayya ba ta shiga tsakanin su.
Akwai wata rana lokacin ba su dade da yin
arba'in ba, ta d'irki magungunan mata kamar
hauka, wai ita alallai tana yiwa mai gida gyara,
don haka kan wani lokaci ta hau network mijinta
kawai take buk'ata, don haka Faruk bai dade da
dawowa ba ta kai tallan kanta.
Haka Faruk ya daure da niyyar faranta mata rai,
tun da shi kansa yana buk'atar matarsa.
Amma cusa kan sa da yayi jikin Nadeeya shi ya
yi sanadiyyar tarwatsa duk wani tanadin da ya
yi, tuni ya saketa ta yi baya, shi kuma ya dafe
kansa da duka hannayensa bai an karaba ya ji
hawayena na biyo kumatunsa na takaici da
tsantsar rashin sanin abun yi, amma dai ya saka
a ransa dole ya nemi mafita, tun kafin annakiyar
Nadeeya ta kai shi k'asa........
Mum Twins 😘
Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪24&25
©MRS SAIF
®NWA
Kwanaki sai dad'a shud'ewa suke yi, amma
Faruk ya kasa samun mafita, don duk ta inda ya
6ullowa ummansa ta k'i ganin laifin Nadeeya
kullum magana d'aya take nanata masa,shi ne
ya yi hak'uri dole wata rana zata chanza, duk da
ita kan ta ta sha mata fad'a akan hakan amma
ba a samu wani chanji ba.
Yanzu ga shi kusan watan Ansar takwas da
haihuwa amma kullum abubuwa sai dad'a
ta6ar6arewa suke yi ta 6angaren Nadeeya, ga
matsalar k'awarta zee kullum ba ta da aiki sai
na kiransa a waya, da bibiyar wurin aikinsa.
Wata siririyar ajiyar zuciya ya sauke tare da
fad'in "ya Allah ga ni gareka,, a matsayina na
bawanka mai rauni kai ka fi sanin daidai, ya
mad'aukakin sarki ya Allah ka kawo mun mafita
mafi alkhairi a gareni".
Daidai lokacin ne kuma ya lura da ya kauacewa
hanyar da ya ke son bi, sakamakon dogon
tunani da ya je, shi da zai karya kwana ya shiga
Jan bulo, bai yi aune ba sai ya gan shi kan
gwarzo road sosai don ya yi nisa sosai daga
kwanar da ya kamata ya shiga.
Da kamar ya yi u-turn ya dawo, sai kuma ya
samu zuciyarsa da kimsa masa kawai ya
k'arasa BUK ko Fateema ta gama lectures ya
d'aukota, sai su taho gida tare.
Straight gate d'in shiga makarantar ya nufa,
parking ya yi daidai faculty of science, sannan
ya fito daga motar tare da wayarsa a hannu don
kiran Fateema ya ji ko ta gama lectures tunda
ya ga yamma ta yi.
Kansa a sunkuye yake, yana lalabin number'n
tilon k'anwarsa, ta k'asa idonsa ya yi arba da
wata kyakkyawar k'afa mai d'auke da zara-
zaran yatsu da suka sha jan lallen saajan, d'an
mutsutstsuka idonsa Faruk ya yi don ya
tabbatar da k'afa ce, ko kuma idonsa ke masa
gizo, don k'afar ta fi masa kama da zane ko
hoto, don ganin k'afar ya yi tamkar ba a taka
k'asa da ita.
Sanyayyen k'amshin turaren 2U ya dake
hancinsa hakan ya tabbatar masa mai k'afar
tana kusa da shi.
A hankali Faruk ya d'aga idonsa, cikin d'auken
ganin fuskar wacce ta mallaki wannan tsaleliyar
k'afar.
Karaf! Idanunsu suka hadu lokaci d'aya, da sauri
yarinyar ta kawar da fuskarta gefe.
********
Shi kam Faruk ya kasa daina kallonta, for the
first time da ya tsaya k'arewa mace kallo a
rayuwar sa, yarinya ce wadda shekarunta ba za
su wuce 20_21yrs ba, za a iya kiranta da fara
amma ba gau ba, sai dai yanayin kyan skin d'in
ta shi ke Jan hankalin mutane, sai idanunta
masu fizgar hankalin mai kallonsu , tana da
hanci dai dai da d'an k'aramin bakinta, za mu
iya kiranta da doguwa, wadda tsayinta ya yi dai
dai da dirin jikinta.
Sanye take da Arabian gown coffee colour,mai
d'auke da adon yellow, yayin da ta yane kan ta
da yellow veil, fuskan nan fayau ba wani
tarkacen kwalliya sai lipstick da ta zizara a lips
d'in ta sai kwalli da ta saka a idonsa wanda shi
ke k'ara tona asirin kyaan idanun na ta, ta cikin
farin glasses da ta mak'ala a idonta, wanda ga
dukkan alamu medical ne.
Tuni Faruk ya daskare a wurin, har ta zo ta
ratsa ta gefensa da niyyar wucewa, salon tafiyar
ta, shi ya k'ara kambamamata a zuciyar Faruk,
yanda ta ke taku cike da nutsuwa da hankali,
tamkar ba za ta, taka k'asa ba, wanda wasu za
su iya kiransa da yanga, amma samsam a wurin
ta abun ba haka ba ne, it's just her nature,
saboda tun kafin ta zama cikakkiyar budurwa
haka tafiyarta take.
Bai an kara ba sai Jin muryar Fateema ya yi
tana fad'in
"friendy kin gaji da jirana ko"???
Murmushi yarinyar ta saki, wanda ya k'ara
bayyanar da asalin madarar kyaun da take da
shi, tare da cewa "haba friendy sai fa da na ce
ki hak'ura ki bar mata buk d'in gobe kya kar6a
ki ka k'i ji, bacin kin san maryam da naci". Ta
k'ara she maganar fuskarta d'auke da wani
Murmushin.
Faruk dake gefe yana kallonsu, sai ya ji kamar
kar ta daina magana, don ji yayi kamar tana rera
wata daddad'ar wak'a yanda salon maganar ta
ta ke fita, dafe ha6arsa ya yi tare da ce wa
"ya ILLah!me yasa yarinyar nan komai ta yi
burge ni take yi, duk da ya riga ya gama
yarjewa kan sa ya fad'a dumu - dumu cikin
k'aunarta.
Ajiyar zuciyarsa, ta yi dai dai da fara tafiyar su
don barin gurin gaba d'aya, da saurinsa ya ce
"Fateema"!!
Cikin mamaki Fateema ta jiyo don Jin muryar,
yayanta da hanzarinta ta k'arasa gurin da ya ke
tsaye tare da cewa
"what a wonderful surprise! Bro kwata_kwata
ban lura da kai ba."
Murmushi Faruk ya yi sannan ya ce ni kai na, na
san da haka, don na dad'e a tsaye ina kallonku
ke da k'awarki, amma ba ki lura da ni ba".
Cikin murna ta koma in da k'awarta ta ke tsaye
ta Jawo hannunta tana fad'in
"bro meet my eponym, sweetest,finest friend".
Ido Faruk ya d'an zaro alamun mamaki ya ce
"wow! Yhu mean Fateema is her name too"????
Gyad'a kai Fateema ta yi cike da k'warin gwiwa
alamar hakan take nufi.
K'arasawa Fateeman ta yi gun faruk tana gaishe
shi, tare da fad'in "ya Faruk, am I right???
Yes! Yes!! Faruk ya fad'a cike da jindad'i, yana
tunanin ashe ma ta san shi, har faty k'anwarsa
sai da ta fuskanci hakan.
Ta ce
" bro ai ba ka san wani abu ba duk wan da ya
zauna tare da ni ko na second ne sai ya san ya
Faruk a bakina".
Murmushi Faruk ya ke yi yana Gyad'a kai cike
da gamsuwa da maganar k'anwar tasa.
Sai kuma ya ce "ku zo mu tafi ko, kun ga
yamma sai dad'a yi take yi".
Fateema ta ce ai kuwa dai bro, sai mu fara
sauke friendy a gida sai mu wuce ko"???
Sosai ma kuwa Faruk ya fad'a tare da satan
kallon Fateeman.
Dan basarwa ta yi kamar ba ta ji abinda suke
cewa ba, sai da faty ta ce da ita
"friendy mu je ko???
Fateema ta ce
"namesake ku yi tafiyar ku kawai na gode, ina
ga yaya mus'ab yana hanya za mu tafi tare da
shi".
6ata rai teema ta yi ta ce
"haba ta yaya ki kasan yana hanya bacin ban ji
kun yi waya ba".
Har fateema xa ta ce wani abu, sai faty ta
katseta da cewa
"to wallahi sai kin shiga shi kenan"
Dariya suka yi gaba d'ayan su, saboda fateema
tasan halin k'awarta ta idan ba haka ta mata
ba, ba lallai ta shi ga ba.
Faruk haka kurum ya tsince kansa cikin farin ciki
yayin da ya ke driving, ji yake kamar kar yakai
Fateema gida, su yi ta zaman su a haka suna
zaga gari, sai dai k'asan zuciyarsa yana
mamakin yadda soyayyar yarinyar ta kama shi
lokaci d'aya...
Ku yi hak'uri rashin posting jiya yarona ne, ba
lafiya amma insha Allah idan na samu kai na, za
ku kuma jina ❤👌🏻
Maman Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪26&27
©Mrs Saif
Bayan sun ajiye teema a gidansu ne, Faruk ke ce
da Fateema "dama k'awarki ce amma ban ta6a
saninta ba"???
Faty tace" ah, ai da yake gaskiya ba ta cika
yawo ba, daga gida sai school, amma Umma
tasanta, don mun ta6a zuwa sau d'aya da ita ta
gaisheta, kuma ina yawan ma Umman hirarta".
Murmushi ya ke yi sosai ya ce
"k'anwata a tsakanin mu ba 6oyeye, so zan
gaya miki iya gaskiya ta, ina son k'awarki, ban
ta6a tunanin k'arin aure ba, a nan kusa ba, duk
rashin cikar da burina bai yi ba ta fuskar auren,
sai dai ganin k'awarki nan da na yi, na ji ina son
k'arin aure nan ba da jimawa ba, fatana Allah ya
sa wani bai riga ni ba".
Ya k'arasa fad'ar maganar da tausayawa kan
sa, idan har fateema tana da wanda take so to
lailai ya San ya rasa farin cikin rayuwarsa.
Ihun murnar da faty ta saki, shi ya dawo da
Faruk daga duniyar tunani, tace "yaya ni dai a
iya sani na friendy bata kula kowa, don a cewar
ta 6ata lokaci ne, don ita yanzu karatu ta sa a
gaba, ka ga kuwa na samu damar kafa
gwamnatin yaya na, hankali kwance".
Damk'e hannunta Faruk ya yi sosai cikin farin
ciki ya ke fad'in "thank you so much k'anwata,
I'm proud of you, don na tabbatar da cewa farin
ciki na shi ne na ki".
*********
Fateema tun jiya ta matsu gari ya waye ta je
skul ta fesawa Teema abun da ya faru, saboda
haka da wur_wuri yau ta shirya ta nufi
makaranta, har Umma tana ce da ita ki ka ce
yau sai 9 ku ke da lecture, na ga yanzu ko 7 bai
yi ba ki na neman fita"???
Sai da ta rataya Jakarta ta ke cewa
"Umma akwai abinda ya taso ne daga baya, shi
yasa zan fita yanzu".
Addu'ar dawowa lafiya Umma ta bi ta da
ita,sannan ta sa kai ta fice daga gidan.
Teema ba ta isa makarantar ba sai after 8, cikin
zumud'i fateema ta je tarota, ba a d'au dogon
lokaci ba ta fesa mata abinda ke cin zuciyarta
tun jiya.
Murmushi Fateema ta yi tare da cewa
"haba namesake ke fa kin san alk'awarin da na
d'auka na ba zan kula ko wani namiji ba, har sai
na kammala karatuna,kuma ke kika k'arfafa
mun gwiwa, amma yanzu ki zo da maganar ya
Faruk"????
D'an 6ata rai faty ta yi tare cewa
"haba friendy yanzu me ye matsalan yayana,
wallahi idan ki ka aure ya Faruk za ki ji dad'i,
don na fahimci yana matuk'ar son ki, don ni tun
tasowata ban ta6a ji ya ce yana son wata mace
ba, sai akan ki, kin ga bai kamata ki watsa
masa k'asa a ido ba."
Girgiza kai Fateema ta yi tace "ba ki fahimce ni
ba ne, ni fa karatuna ne ba zan ajiye ba, na yi
aure yanzu, don na san ina amincewa zai fara
maganar aure".
Murmushi faty ta yi, don a maganar da suka yi
da fateema ta fahimci tana son yayanta, kawai
dai ita ta d'auka karatu da aure babban aiki ne
shi yasa ta k'i amincewa, don ta tabbatar da
zancen wani ta kawo mata a cikin samarin da
ke nacin son ta da yanzu sun yi fad'a.
Don haka ta cigaba da nuna mata karatu da
aure ba matsala ba ne, kawai ta sawa zuciyarta
za ta iya kawai, sai Allah ya taimaketa, ba ta
gushe tana bata baki ba, har sai da ta ga ta
d'an sauko daga dokin nak'in da ta hau.
Yau kamar yadda ya saba a lokutan baya, k'arfe
6 na yamma ya shigo gidan d'auke da sallama a
bakinsa, tsayawa ya yi ya d'an kalleta ya wuce,
don inda sabo ya saba, zaune ta ke tana feeding
Ansar, amma gaba d'aya boobs d'in ta a bud'e
suke, ta yanda idan yaron ya sha wannan, sai
ya juyo ya sha wannan tamkar dai akuya na
shayar da d'anta.
********
70:30pm Faruk ya fito cikin shirin sa, da wani
tsadaden yadi golden colour wanda aka yiwa
ado da zare golden brown, yadin shara-shara ne
ta yanda za ka iya hango farar vest d'in sa ta
ciki, sai hular da ya kafa akan sa itama golden
brown, takalmin da ya saka yayi daidai da
kayan, yayi kyau sosai kamar wani sabon ango,
k'amshin turaren da ya zuba ne ya tilasta
Nadeeya lek'owa ta ga ko lafiya, don gaba d'aya
gidan ya k'amshashe kamar wurin kamun
amarya.
Ganin yanda ya yi masifar kyau, yasa ta ji wani
abu ya tokare mata mak'ooshi, wanda ba komai
ba ne, illa kishi, don haka ta sha gabansa tare
da rike k'ugu sannan ta ce
"ina zuwa da daddaren nan"????
Ido cikin ido Faruk ya kalleta ya ce
"zance".
Me ka ce"??? Nadeeya ta tambaya cikin k'araji.
Faruk ya ce
"sarai kin ji abunda na ce, don haka I can't
repeat myself".
Sai kuwa ta yi bakin kofa da sauri ta saka key
ta zare key'n ta cusa cikin zaninta, wanda garin
sauri har d'ankwalinta yana fad'uwa, hakan
kuma shi ya tona asirin cukurkud'ad'en gashin
kan ta wanda ya fi wata ba kitso ba kuma
gyara.
Kallonta Faruk ya yi, ya ce
"wai me ki ke yi haka??? Hauka ko kishi???
Ai duk macen da ta san kanta ba za ta tsaya ta
zama BALLAGAZA ba, irin yadda ki ka yi, har
hakan ya zama sanadin hango wata da na yi,
wadda nake fatan ita ce zata zamemun warkar
cutukan da ke, ki ka sa mun, ki godewa Allah da
nine mijinki, da wani ne, da tuni kin manta da
kin bar gidan, ko ya zama rik'akk'en d'an bariki,
ya kuma kwaso cuta ya ya6a miki".
Yana gama fad'ar haka ya janyota, gaba d'aya
zanin jikinta ya warware, ya ciro key d'in,
sannan ya mika mata, zaninta ya bud'e k'ofar
ya fice daga gidan gaba d'aya.
Nadeeya kuwa dask'arewa ta yi a wurin don
mamakin kalaman Faruk, kafin daga bisani ta
zube a wurin, sannan ta saki wani irin kuka har
da dukan bango kamar mahaukaciya sabon
kamu....
Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [8/23, 3:44 PM]
Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪28-30
©MRS SAIF
Cikin d'an k'ank'anin lokaci soyayya da
shak'uwa ta shiga tsakanin Faruk da Fateema,
ta yanda in dai suna tare da junansu ba sa
kallon kowa sai kan su, soyayya tsaftatatciya
mai cike da ganin k'ima da daraja juna.
Ba a d'auki wani dogon lokaci ba, Faruk ya
bijirowa Fateema da maganar aure, don baya
son dogon zance a yanzu ya fi buk'atar a ce
Teeman ta zama mallakinsa, Umma ce ta so ba
shi matsala, don cewa ta yi bata amince ya
k'ara aure yanzu ba, dududu auren nasa da ko
shekara biyu bai kai ba har zai tattago wani
auren.
Amma cikin taimakon Allah Faruk ya shawo
kanta har ta amince, a dole ita ma Fateema ta
amince aka saka ranar aurensu nan da wata uku
masu zuwa, don ta gaji da magiyar da Faruk ke
mata akan ta taimaka masa ta amince, uwa uba
ga shi Faruk ya samu kar6uwa gurin iyayenta,
don ta so ta kaucewa buk'atarsa don ta fiso ta
d'an yi nisa a karatun ta, in son samu ne ma ta
gama, amma k'ememe Abban ta ya amince da
buk'atar Faruk.
Don haka itama ta watsar da makamanta, ta
amince ta kar6i Maganar auren da hannu biyu,
don ummyn ta ta sha gaya mata karatu baya
hana aure.
Sai dai damuwarta d'aya da Faruk ya sanarda
ita yana da mata, don ko a labari faty bata ta6a
gaya mata yana da mata ba, tambayoyi ne birjik
a ranta, to me zai saka shi k'arin aure da wuri
haka, ga fargaba da ta cika zuciyarta, kar ta je
ta tarar da matarsa ta fi k'arfin ajinta, don
Faruk bai gaya mata komai ba dangane da
abinda ya shafi Nadeeya.
Bare faty da Umma ta mata kashen kada ta
sake ta sanar da Fateeman halin Nadeeya, don a
cewar Umman ba k'aramin raini zai jawo mata
ba.
*******
Fateema ce kwance a kan gadon d'akin ta ta yi
rigingine tana kallon fan da ke juyawa, wanda a
zahirin gaskiya ba ita take kallo ba, idonta ne
kawai akanta amma zuciyarta ta tafi bulayi
wata duniyar.
Sallama Ummy (mahaifiyar Fateeman) ta yi tare
da k'urawa 'yar tata ido wadda har a lokacin
bata san ta shigo ba.
Zama Ummy ta yi akan gadon tare da janwo
fateema zuwa jikinta, cikin sigar rarrashi Ummy
ta fara magana
"haba mamana me ke damunki haka???
Na shigo ina ta magana hankalinki kwata -
kwata baya tare da ke, na fuskanci kwana biyu
ki na cikin damuwa gaya mun meye damuwarki
kin ji mamana " ta k'arashe maganar tare da
shafa dogon gashin Fateeman wanda ya sha
gyara, ya kwanta luf zuwa gadon bayanta.
Gyara kwanciyarta ta yi akan cinyar Ummy ta
ce" Ummy ni fa kishiya ce bana so??
Ta k'arasa maganar da d'an turo baki.
Murmushi Ummy ta yi tare da d'an zaro
idanunta waje ta ce
"haba Azzarah a irin tarbiyyar da na ba ki ai bai
kamata ki ji tsoron kishiya ba, sanin kan ki ne,
tun kafin ki kai haka nake koyar da ke, duk wasu
dabaru na zamantakewa a gidan miji,don haka ki
daina Jin shakkar zama da kishiya in dai kin bi
kan turbar da na d'oraki, duka lamuranki ki
mik'awa Allah shi zai ji6inci lamarinki.
Ummy ta dad'e tana yiwa Fateema nasiha,
yanda zata bi mijinta har ma da abokiyar
zamanta don Ummy ba ta da duhun kai irin na
wasu iyayen, ita ke gayawa Fateema duk abinda
ya kamata ta sa ni, matukar shekarunta sun kai
ga matsayin sanin abun.
Tabbas Fateema ta ji ta samu kwanciyar hankali
da kuma k'warin guiwa, shi yasa take matukar
son Ummyn ta don tun tasowarta, ita ce
k'awarta kuma mahaifiya don duk matsalar da
ta shiga ita take fara gayawa cikin yardar Allah
ummy za ta lalubo mata mafita cikin sauk'i.
Dama hausawa sun ce duk abinda babba ya
hango yaro ko ya hau rimi......
Let us look back .... Fateema haifaffiyar garin
Kano ce, mahaifanta uwa da uba, fulanin garin
Garko ne, su shida ne ras a gurin iyayensu, guda
biyar duk maza ne, sai a haihuwa ta shida aka
haifi Fateema wadda ta ci sunan mahaifiyar
Ummy, shi yasa sun fi kiranta da Azzarah
musamman Abbansu, Ummy kuma ta fi ce mata
Mamana, sauran yayanta kuwa sun fi ce da ita
Fateema ko AZZARAH, shi yasa duk wanda aka
gaya mata amsawa take yi.
Fateema ta taso cikin kulawa ta iyaye da yayye
dukansu k'aunarta suke yi kamar su had'iyeta
musamman Abba,ko don ta kasance ita d'aya ce
a cikinsu??? domin ba don Ummy a tsaye take
ba, da shagwa6awar da Abba zai yiwa Fateema
sai ta zarce misali, to da ta ga za a kwacewa
daidai za ta yi magana, don ita har ga Allah
tana son 'yar ta samu cikakkiyar tarbiyya,
wadda take burin ta zama mace tagari a gidan
aurenta anan gaba, wacce ko wani miji ke burin
samu.
Don haka soyayyarta ba ta hana ta yi mata
fad'a idan ta yi ba daidai ba, ta kuma nuna
mata tsananin 6acin ranta gudun k'ara afkuwar
hakan anan gaba........
[8/23, 4:52 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪
©MRS SAIF
Don haka fateema ta taso da nutsuwa da
hankali, sam bata da rawarka irin na wasu 'yan
matan wannan lokacin, komai nata mai san yi
ne wannan kenan...
****
Faruk kuwa tun bayan, saka ranar auren su da
Fateema, ya tashi maganar ginin gidansa da ya
fara ya ajiye, don shiri sosai yake wa bikin,
tamkar shine na farko duk da ya ce, wannan
bikin ya fi masa na farko sau dubu.
Nadeeya kuwa tun da ta fuskanci da gaske
Faruk aure yake shirin yi, ta ce
"ita ba za ta iya zama da kishiya ba, sai dai ya
za6a ko ita ko amarya, kun ji fa... Ni dai a nawa
hangen sai nake ganin ai sai macen da ta amsa
sunan ta na mace a gun miji take ba da wani
options a bi ta kanta ba irin su Nadeeya ba...
Lolx.
Kallon uku saura kwata Faruk ya bita da shi,
sannan ya yi wani malalacin murmushi ya ce
"wato har wani xa6i ki ke ba ni?? Amma da a ce
ke mai tunani ce da baza ki ba ni wani za6i ba,
don kin san bazan za6eki ba, don haka abinda
zan iya cewa dake, idan kin ga za ki iya zama ki
zauna idan ba za ki iya ba, ban d'aure ki ba, it's
up to you."
Wata k'atuwar k'wafa Nadeeya ta saki sannan
ta shige d'akinta tana had'a kayanta tana kuka,
don ta sha alwashin daga nan sai dutse, don ko
gidan su Faruk ba za ta biya ba, don ita kanta
Umman haushinta take ji.
Trolley d'in ta jawo zuwa parlour da niyyar
ratsawa ta gefen Faruk ta wuce.
Sai Faruk ya ce da ita
"Ansar kuma fa, na ga kina neman shigewa ki
bar shi".
Kallon banza ta watsa masa, sannan ta ce
"Ai ka san da shi na zo, da zan tafi da shi, kai
dai da ka ke da jarabar son 'ya' ya sai ka rik'e
abunka don ni ko ba shi, zan iya rayuwa".
Daga haka ba ta k'ara ko kqllama d'aya ba ta ja
trolley d'in ta tai gaba.
Tsayawa ya yi rungume da Ansar a jikin sa
yana tunanin hali irin na Nadeeya, ya d'auki
kusan 5mnts a haka, daga k'arshe ya ga hakan
ba zai fitar da shi ba, ya nufi toilet da yaron,
wanka ya masa ya shiga d'akin Nadeeya don
d'auko masa kayan sawa, sai dai kaf kayan sun
yi daud'a, ya rasa mai zai yi, sai can ya tuna da
bai dad'e da siyo masa wasu sabbin kaya ba ya
manta bai bawa Nadeeya ba, don haka ya koma
d'akin sa ya d'auko set d'aya a ciki ya saka
masa, sannan shi ma ya shirya, ya rufe gidan ya
nufi motorsa rungume da Ansar a k'irjinsa.
Kaitsaye gidan su yana nufa don ba shi da wani
za6i da ya wuce ya kai shi can...
Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪31
©MRS SAIF
Umma na kwance a d'aki ta d'an kishingid'a ta
jiyo sallamar Faruk da sauri ta yo parlour tare
da fad'in "muryar wa na ke ji da safen nan
kamar Faruk"??
Sosa k'eya ya yi tare da cewa" ni ne Umma, an
tashi lafiya"?
Lafiya qalau Umma ta ce "tare da kai hannu ta
kar6i Ansar, sannan ta ce" ina maman ta sa, ba
ta fito daga mota ba ne"??
Hannu ya sa ya shafo sumar kansa, sannan ya
ce wallahi Umma da ma a.... Sai kuma ya yi
shiru, cikin zaro ido waje Umma ta mik'e tana
cewa "dama me, mai ya samu Nadeeyan, na ji
ka fara magana ka yi shiru".
Kwantar da muryar sa ya yi, ya ce "ba abinda
ya same ta Umma, kawai dai ta kasa fahimta ta
ne akan zancen auren nan, shi yasa yau tun
safe ta shirya ta wuce dutse, don ta ce sai dai
na za6a ko ita ko amarya".
Ajiyar numfashi Umma ta sauke tare da cewa
"kai kuma sai ka ce da ita ka za6i amarya ko"??
Sosa kai ya yi tare da fad'in" Umma ni fa ta
kasa fahimta ta na ne kawai, amma ba nufi na
wu......"yi mun shiru ni na nemi mafia, dama
idan dai namiji ya so k'arin aure ai dole ta gida
ta yi hak'uri, bare Nadeeya da take a lanjare".
Umma ke fad'in haka ta hanyar katse maganar
Faruk.
Waya ta d'auka ta kira layin Nadeeya sai dai
number'n x not reachable, don haka ta lalubo
number'n maman Nadeeyar itama x switched
off. Wulli ta yi da wayar kan kujera tana kallon
Faruk ta ce ga shi wayoyin na su duk ba sa
shiga".
Murmushi Faruk ya yi tare da fad'in "Umma ki
daina wahalar da kan ki, ita ce mai dawowa da
kanta, duk wannan na san barazana ce".
Harararsa Umma ta yi sannan ta ce "wato na
k'yaleta tunda kai ba ka da hasara wani auren
za ka yi, ni kuma ka lalata mun dangantaka ta
da aminiyata, ko da yanzu za ta dawo, dole na
cigaba da bibiyarta ita da mahaifiyarta, don
gudun samun matsala, idan ka kawo tsiya
yanzun za ka ajiye duk abinda ka ke yi mu yi
shirin zuwa dutsen".
Ai ba shiri Faruk ya tsuke bakinsa, don idan
umma ta ce a je dutse yau, ai duk ta rusa masa
schedule d'in sa na yau. Saboda haka ya ce
"Umma ki yi hak'uri don Allah, bari na ajiye
Ansar na wuce wurin aiki nan ma ba dadewa
zan yi ba zan nemi excuse na je duba aikin ginin
da ake yi".
Sai da ta kara waya a kunnenta don k'ara
neman layin maman Nadeeya, ta ce masa Allah
ya taimaka, amma Ansar yana cin abinci kuwa??
Faruk ya ce "sosai ba abinda baya ci".
Umma ta ce "oho! To ai da sauk'i, kasan yaran
yanzu sai su k'i bawa yara abincin mu na asali
sai na gwangwanaye, sai ka ga yaro ya fi
shekara amma baya iya cin abincin gargajiya".
Dariya Faruk ya yi ya ce
"Umma sai na dawo ina makara ".
Umma ta ce to, Allah ya kiyaye hanya".
Ya ce "ameen tare da ficewa daga parlourn.
*****
DUTSE
Nadeeya ce zaune ta yi jugum, tana tunanin
wannan wacce irin masifa ce, gidan aure ba
dad'i ta zo gidan su don ta ji sanyi nan ma ta
tarar da wata masifar, ba ta k'arasa tunanin da
take yi ba ta tsinkayo muryar mamansu tana
cigaba da fad'in
"to don ma ki ji na gaya miki, ba ki da wurin
zama a gidan nan, idan dai ba so kuke ku kashe
ni da raina ba,ga yayyanki can guda biyu watan
da ya wuce duk aka sako su, har an fara
zund'en mu a unguwa, a haka ke ma ki ke so ki
kashe na ki auren ku zo duk mu zauna taron
zawarawa, to ahir ki fita a idona, tun muna mu
biyu ki kwashi kayanki k koma".
Kuka sosai Nadeeya ke yi tana yiwa mama
magiya akan ta k'yaleta ta zauna, amma
k'ememe maman ta k'i.
Cikin kuka Nadeeya ke cewa "haba mama yanzu
ina komawa kano a yau ai zai zamemun abin
gori har zuwa k'arshen rayuta, a ce gidan na mu
ma sun kasa rik'eni sun koroni".
Cikin tsawa mama ta ce
"su fad'i ko ma meye amma ba zan goyi bayan
ki kashe aurenki, ki zo gida ki zauna ba".
Amma mama ai kya bar ni ko zuwa sati ne na yi
kafin na...... Ringing phone d'in ta shi ya katse
maganar da take yi, ganin sunan Umma ne ya
saka ta daidaita nutsuwarta kafin ta d'aga.
Bayan sun gama gaisawa ne, ta ce ta bawa
mama wayar, ba musu ta mik'a mata, sun dad'e
suna tattaunawa kafin daga bisani su yi
sallama.
Juyo da dubanta ta yi ga Nadeeya ta ce "kin ci
arzikin sirikarki, da ta biyo sawu don ko ba
komai nasan maganar aurenki tana nan, tunda
tana ta ba da hak'uri ga shi ta ce a jira Faruk
zai zo da kan sa ya tafi da ke".
Wata k'atuwar ajiyar zuciya Nadeeya ta sauke
don ko ba komai ta ji kashi hamsin a cikin d'ari
na daga damuwarta ya yaye....
Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [8/26/16, 9:53 AM]
phatyma▪BALLAGAZAR MACE ▪32&33
©MRS SAIF
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, yau bikin
Fateema da Faruk ya rage saura 3wks, shiri
sosai suke yi ta 6angarorin guda biyu.
Yayin da Faruk ya gama gininsa tsaf, gida ya
tsaru ba'a magana.
Fateema kuwa har an fara mata gyaran jiki don
musamman Ummy ta d'auko mai gyaran jiki 'yar
Maiduguri, cikin' yan kwanakin da aka fara mata
gyaran ta koma tamkar wata tauraruwa, lungu
da sak'o duk gyara ake mata don matar ta san
aikinta sosai.
Nadeeya na gefe, duk takaici ya cikata, don tun
dawowarta ta rasa yanda zata 6ullowa lamarin,
musamman yadda ta ga Faruk na masifar rawar
kai akan auren, har mamaki ta ke yi kamar ba
Faruk d'in da ta sa ni ba,dama akwai macen da
zai rik'a rawar kai akan aurenta, idan har ta
kwatanta da lokacin bikin su yanda ya nuna
ko'in kula akan auren a wancan lokacin lallai
tana son ta ga wannan yarinyar ta ga da me ta
fita,yake wannan uban rawan jiki akanta.
A zaune take parlour ta rafka uban tagumi,
yayin da ta saka TV a gaba kamar mai kallo,
amma sam zuciyarta ba ta kai, tunanin mafita
kawai take duk da ta san ba makawa sai an yi
auren, sallamar da maman Deedat(mak'ociyarta)
ta yi ne ya katse mata tunani.
Tace "lafiya maman Ansar ina ta sallama amma
sai yanzu ki ka jiyo ni"???
Hmm! Bari ke dai, ina cikin wani yanayi ne shi
yasa kwata_kwata ban ji motsin shigowarki ba,
cewar Nadeeya.
Maman Deedat ta ce" Subhannallah! Me ya faru
ne"??
Murmushin yak'e Nadeeya ta yi, tare da cewa
"akan zancen auren nan mana, yanzu haka
dududu bikin bai kai wata d'aya ba".
Neman wuri ta yi ta zauna sannan ta fara
magana da cewa "maman Ansar na sha gaya
miki abinda ki ke yi ba kya kyautawa, yanzu don
Allah kalleki kalli gidanki, ta yaya namiji zai
shigo ya tarar da matarsa a haka ki ce zai samu
farin ciki, ki na ganin dai wasu mazan ki'ris su
ke nema, su k'aro aure, amma ke tsakani da
Allah Faruk ya baki lokaci amma kin k'i ki
gyara, to ya kike so yayi
Idan bai k'ara aure ba, sanin kan ki ne ya.... A
zafafe Nadeeya ta d'aga mata hannu tana fad'in
"ya ishe ni haka, ke wace da har za ki shigo har
cikin gidana ki ce za ki ci mun mutunci, to
wallahi kin yi kad'an, kaitsaye ke ma ki fito ki ce
mun k'azama, kamar yadda wasu suka saba
fad'a, ya fi wannan lunku - lunkun da kike yi".
Maman Deedat ta ce "ni fa shawara ce na ke
ba..." ki rik'e abar ki bana so, taso ki fice mun
daga gida", cewar Nadeeya.
Ba musu maman Deedat ta shure takalminta ta
fita.
Nadeeya sai wani cika take tana batsewa ita
alallai an 6ata mata rai, Ansar ta sa6a a baya
ta saka hijabinta, ta kulle gidan ta nufi hanyar
gidan maman Nabeela.
*******
Kallo d'aya maman Nabeela ta mata ta fuskanci
damuwa tattare da ita, da sauri ta nufo inda ta
ja birki ta tsaya zo ta tana fad'in "aminiya me
ya sameki na ga ranki a 6ace"??
Tsaki Nadeeya ta ja, sannan ta ce" kin san dai
damuwata ba sai na kuma maimaita miki ba, to
wata aka kuma dora mun akan wata , yanzun
maman Deedat ta bar gidana, wai har ni za ta
kalli tsabar idona ta ce wa k'azama".
Shiru maman Nabeela ta yi, don ko ita har ga
Allah tana son ta yiwa Nadeeya magana akan
wasu halayenta ta daina musamman k'azantar
ta tayi yawa, amma tana tsoron ta fara gaba da
ita, tunda ta ga duk wanda suka yi gigin nuna
mata hakan sun dawo abokan gabarta.
Yana ga Kin yi shiru, cewar Nadeeya,
murmushin da bai kai ciki ba, maman Nabeela ta
saki tare da cewa "uhmm! Ai mutane ba a iya
musu, kana barci ne ana Maka minshari".
Wata doguwar k'wafa Nadeeya ta ja, wanda ya
yi daidai ta shigowar mai kayan Mata.
Ta ce "lafiya kuwa na ganku kowa fuska a
murtuk'e"??
Anan suka kwashe duk abinda ake ciki suka
gaya mata wata dariya ta saki, sannan ta je
gurin da Nadeeya ke zaune ta dafa kafad'arta ta
ce 'yar uwa kwantar da hankalinki, in dai za ki
saki kud'i zan had'a miki magungunan da sai
kin sha mamaki a gun mijinki, don kuwa idan
har kika yi amfani da su, zai manta da duk
wata' ya mace sai ke, za ki zama super star a
wurin sa,kishiya sai ta tattara kayanta da kan
ta, ta bar miki gidanki don baza ta jure
wulak'ancin da zai rik'a mata ba, don yanda
kika san kaza wadda ta sha maggi da sauran
sinadaran d'and'ano haka za ki koma, ita kuma
yanda ki ka san kazar da aka dafa da zallar
ruwa ba tare da an gwaraya shi da ko d'an
gishiri ba, haka zata zama a gunshi, amma fa
akwai tsada sai dai za ki ga aiki da cikawa".
Wani murmushi Nadeeya ta saki na jindad'i ta
ce
"kud'i ba matsala ba ne ko nawa ne zan ba da,
don na mallaki mijina ni kad'ai, domin bai dad'e
da ba ni kud'in kayan fad'ar kishiya ba, don da
ya ce zai had'o mun kaya na ce bana so ya ba
ni kud'in domin ina da kaya, yanzu haka zancen
da na ke yi akwai kaya tun na lefena wanda ban
ta6a sakawa ba, to me zan yi da wasu, tunda ni
ba wani bari na fita yake yi ba, bare idan zan
fita na saka, don haka na ce gwanda ya bani
kud'in, yanzu ba ga shi kud'in zai mun amfani
ba".
Sosai kuwa mai magani ta fad'a tare da cigaba
da cewa "gwara ki gyara jikinki, yanda za ki
kaucewa duk wani SABON SALO IRIN NA D'A
NAMIJI (Lubiee's buk),da zai bijiro miki da shi
lokacin da amaryarsa ta tare".
Ni kam (Mum Twins) na ce anya kuwa maganar,
mai maganin mata haka ne???
Don dai na san kaucewa duk wani Salo irin na
d'a na miji hanyoyi ne da dama, ba wai sai ta
hanyar d'irkar maganin mata kawai ba.
Shewa suka saki don Jin furucin mai maganin
mata tare da cewa "gaskiya maganarki haka
yake, don wasu mazan zuma ne a sha zak'i a
kuma sha harbi lolz......
Sai Monday kuma, ku yi mun uzuri please ❤👌🏻
Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [8/29, 11:57 AM]
Phatyma: [8/29,16,11:32 AM] Phatyma:
▪BALLAGAZAR MACE ▪34
©MRS SAIF
Yau ta kasance ranar alhamis, kuma yau ne aka
fara gudanar da shagalin biki, a yau d'in ne a ke
saran yin kamu da k'arfe 4:00pm.
Faty ana can ana faman shiri, kamar ta cire
kanta don murna da zumud'i, ku kuwa ba dole
ba, ita ce babbar k'awar amarya kuma k'anwar
ango tilo, don haka ita abubuwan ma har sun
mata yawa, bata nan bata can.
****AMNEEF PALACE a k'arfe hud'u da mintuna
arba'in, Wurin ya cika ya kuma tsaru ba k'arya,
duk mutanen dake gurin suna dakon zuwan
amarya ne,yayin da Ali jita da muk'arabansa ke
cashewa a tsakiyar filin gurin da wak'ar AURE.
5:5pm convoy na motocin amarya suka danno
kai harabar wurin, nan da nan MC ya fara
sanarwa ga amarya nan, cikin k'warewa a
harkar suka chanza salon wak'ar zuwa ta
bikin... Mai taken :Alk'wari ya cika auren so
k'auna tsakanin Faruk da Fateema.
Hankalin kowa ya raja'a ga hanyar shigowa
wurin, don bawa idonsa abinci, 'yan mata
amarya ne a gaba don haka su suka fara
shigowa ciki kuwa har da fatyma, ta sha kyau
har ba a magana, cikin wani lace dark green,
mai adon orange riga da skirt ne, d'inkin ya
zauna das a jikinta, komai orange colour ta yi
amfani da shi ta yi kyau sosai.
K'arasowar amarya ne ya sa na manta kyan da
faty ta yi, wohoho! Ku zo ku ga amarya yanda
madarar kyau ke zuba, Abun ba a cewa komai
sai dai na ce Masha'Allah TubarakallAllah! Don
amarya Teema ta yi kyau tamkar ka sureta ka
gudu.
Su Nadeeya ma ba a bar su a baya ba don sun
zo ita da gayyar mutanen dutse, da mak'otanta
irin su maman Nabeela, itama ta yi kyau sosai,
sai dai ganin Teema yasa ta raina kanta, don
nan da nan zuciyarta ta cunkushe da wani
azababben kishi, wanda take ji kamar ta je ta
shak'e teeman sai dai ba hali, daga k'arshe ma
ji take kamar ta yi tafiyarta ta bar wurin don duk
mutanen dake gurin haushin su take ji, amma a
dole ta cize ta daure ta zauna har zuwa lokacin
da za a tashi gudun tsegumin mutane.
An ci an sha an kuma yi lafiya an gama lafiya,
k'arfe takwas na dare aka watse ko wa ya nemi
hanyar da zata sada shi da mazauninsa.
[8/29,16,11:32 AM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪35
©Mrs Saif
K'arfe goman dare Faruk ya nufi tamfatsetsen
gidansa, wanda suka koma shi da uwargida
Nadeeya, kafin isowar amaryarsa Teema, duk da
bai so hakan ba shi yaso ne sai an kawo
Fateema sannan Nadeeya ta tare Umma ta ce
"sam ba ta san da haka ba, idan ya yi haka
tamkar ya ciwa Nadeeya mutunci ne.
Amma duk da haka sai da yasa Umma ta nemo
masa 'yan aiki dattijuwa d'aya da yarinya, duk
da kowa da part d'in sa amma gaskiya shi ya
tsorata da k'azantar Nadeeya, duk da kwana
hud'u kachal za su yi a gidan Teemansa ta tare,
amma ji yake kamar zata chanza kalar gidan
kafin lokacin, don da yana da dama har ita
kanta da ya chanza tunaninta kafin dawowarsu,
don tsohon gidansu gaba d'aya ta gama
condemning nasa.
Gama tunaninsa ya yi daidai da k'arasowarsa
gate d'in gidan, horn ya dannawa mai gadin,
cikin azama ya ja gate d'in, Farouq ya danna
hancin motarsa zuwa wurin da aka tanada don
motoci.
Bayan ya yi parking kaitsaye main parlourn
gidan ya nufa, sai dai wayam ba kowa a ciki sai
TV da ke 6a6atu ita kad'ai, juyawa yayi da
dubun sa 6angaren dama inda part d'in Nadeeya
ya ke, anan ya jiyo tashin hayaniyarsu ita da
'yan uwanta, da alama ba a parlourn ta suke ba,
suna can cikin d'aki ne, don maganar ta su can
nesa yake jiyo su.
Don haka ya sauke k'wayar idonsa a part d'in
Fateema wanda ke kulle, murmushi ya yi, kafin
daga bisani ya haura sama don zuwa nashi part
d'in.
Kayan jikinsa ya fara ragewa sannan ya shiga
toilet ya yi wanka, sannan ya samawa kansa
kaya marasa nauyi, dama ya ciko cikinsa daga
gidan abokinsa Abbas, don haka bai ma yi
yunk'urin kiran Nadeeya ba, don ko ya kirata ba
lallai ta zo ba, domin fushi take yi da shi ba na
wasa ba,idan kuwa ta zo yasan ba za su rabu
cikin arzik'i ba, don haka ya shareta.
Wayarsa ya janyo ya danna kira a lambar
Fateema, a lokacin Fateema na zaune ta saka
wata k'atuwar gora mai d'auke da ingantaccen
tsimi a gaba, tana faman ya tsine fuska, tana
cewa "Ummy ni dai na gaji da shan wad'an nan
kayan kusan sati nawa ina fama da su", ta
k'arashe maganar tare da kwa6e fuska kamar
zata yi kuka.
Ummy har za ta yi magna sai wata yarinya ta
shigo da gudu tana cewa "Aunty Fateema ana ta
kiranki a waya, ga shi har ta kuma tsinkewa".
Kar6ar wayar Fateema ta yi ganin sunan Farouq
da ta yi saving da QALBY ya bayyana a fuskar
wayar d'auke da 3 missed calls, ya saka ta wani
tattausan murmushi tare da mik'ewa.
Ummy ta ce
"ina zuwa kuma ??? kin bar abun na ki anan".
Dawowa Fateema ta yi tare ta d'aukan goran da
cup, ta fita don itama ana so ne ana kaiwa
kasuwa don sarai ta san mazan yanzu sai ana
had'awa da 'yan sinadarai musamman ita mai
kishiya.
Side d'in Abbanta ta nufa don gidan na su cike
yake da'yan uwansu wanda suka zo don biki
musamman mutanen Garko,don har d'akinta
cike yake taf da' yan mata.
Guest room dake part d'in Abba ta bud'e ta
shiga, daidai lokacin kiran Farouq ya kuma
shigowa wayarta, don ji yake idan bai ji
muryarta yau d'in nan ba, ba zai iya barci ba.
Can k'asan murya ta ce
"hello"
Wani sanyi Farouq ya ji tare da fad'in "Fatyna
wai ina ki ka shiga tun d'azu na ke kira ba ki yi
picking ba"??
Cikin siririyar muryarta ta fara fad'in" na ajiyeta
a parlor ne, ni kuma ina d'akin Ummy".
Ajiyan zuciya Farouq ya yi, sannan ya ce "please
Teemana ki rik'a yawo da phone d'in ki,, kin san
fa yau kusan sati kenan ban ganki ba, kin hana
ni ganin kyakkyawar fuskarki wai sai ranar da za
a kawoki sannan zan kuma ganinki, amma ai ya
kamata ko muryar ki na rik'a ji akai-akai ko na
samu sauk'i".
[8/29, 12:09 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪36
©Mrs Saif
Murmusawa ta yi tamkar yana gabanta, ta
dad'a kashe murya ta ce "haba Qalby dududu
kwana nawa ya rage na zama mallakin gaba
d'aya, ka kwantar da hankalinka nan da kwana
uku Teema ta zama ta ka kai kad'ai".
Wata ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe
idonsa, ya ce "fatyna kin san hausawa sun ce
aski in ya zo gaban goshi ya fi zafi, Allah kwana
ukun nan da ya rage ji nake kamar shekara
uku".
Dariya Fateema ta yi sosai tare da cewa "ni fa
kana ba ni mamaki idan ka fad'i haka, kai ba
saurayi ba, ba kuma tuzuri ba, ga yayata a kusa
da kai, to saurin me ka ke yi kuma".???
Hmmm! Ba za ki gane ba ne Fateema ni fa son
ki a jinina yake, Allah dai ya kai mu lokacin".
"ameen" Fateema ta ce, suka cigaba da hirarsu
cikin nishad'i kamar ba gobe.
Washe gari Ummy ta had'a k'ayattacciyar
walima ta mata zalla, wadda aka gabatar anan
harabar gidan, malamai da dama sun
wa'azantar tare da nasihohi duk akan zaman
aure.
****
Ranar lahadi Misalin 11:00am dubban jama'a
suka shaida d'aurin auren FATEEMA & FAROUQ
akan sadaki dubu hamsin.
Duk wanda ya kalli farouq ya san yana cikin
tsantsar farin ciki a wannan lokacin,abokan
arzik'i sai zuwa ake yi ana masa Allah sanya
alkhairi.
6:00pm ***
Motocin ango suka dira k'ofar gidan su Fateema
don tafiya da ita gidan aurenta, a lokacin har an
gama shiryata cikin wata dakakkiyar lafaya red
da ratsin black ta yi matuk'ar kyau, sai wani
mahaukacin k'amshi dake tashi daga jikinta, don
ko zama ta yi a guri sai ya dad'e bai daina
k'amshi ba, haka idan mutum ya ra6eta tabbas
shi ma zai kwashi irin k'amshi, don wasu
turaruka ne, na musamman wadda ta mata
gyaran jiki ta mata amfani da su.
In ban da kuka ba abinda fateema ke yi, ta
k'wak'ume Ummy tana fad'in "ita ba za ta je ba,
ta fasa auren ba za tafi ta bar Ummynta ba, duk
dauriya irin na ummy sai da Teema ta sakata
kuka, rungumeta ummy ta yi sosai tana hawaye
tana fad'in
" yi hak'uri mamana, duk 'ya mace ta haka ce,
muma duk haka aka mana, wata rana sai labari,
ina dai kuma nanata miki ki yi hak'uri, zaman
duniya duk d'an hak'uri ne, ki bi mijinki sau da
k'afa, matuk'ar bin bai shafi sa6awa shari'a ba,
ki kuma yiwa abokiyar zamanki biyayya daidai
gwargwado, duka nasihohin dana dad'e ina miki
Azzarah ban yarda ki jefar da ko d'aya ba, Allah
ya miki albarka ya baki zaman lafiya a gidan
aurenki, tare da zuri'a d'ayyaba".
Duk wanda ke gurin sai da ya amsa da ameen,
sannan aka 6an6are fateema da k'yar daga jikin
ummy, aka wuce da ita wurin Abbanta, shi ma
naseeha ya yi mata sosai sannan aka fito da ita
aka sa ta a mota sai gidan Farouq.
Kamar yadda aka saba bisa al'ada akan fara kai
amarya ne wurin uwar gida kafin akaita na ta
d'akin, to haka ce ta kasance da Fateema don
sai da aka fara kaita wurin Nadeeya aka damk'a
mata amana sannan aka wuce da ita
6angarenta.
K'arfe takwas kusan duk 'yan kawo amarya sun
watse, daga amarya sai faty da wasu
k'awayensu guda uku, a dole Fateema ta ware
lafayar ta tashi don d'auro alwala ta yi sallah
Faty sai tsokanarta take yi ganin kayan da ke
ciki, riga da skirt ne na wani rantsatstsen swiss,
d'inkin ya yi kyau sosai tamkar tare aka halicce
shi da jikinta ya yi bala'in fitar da kyakkyawar
surarta, ta yanda ita kan ta sai da ta ji kunya
ganin irin kallon da sauran friends d'in su ke
mata.
Tana idar da alwala ta d'auki lafayar ta mai da,
Faty na mata mitar tana idar da sallah za ta
warware mata lafayar don ba za ta ma yayanta
k'wange ba".
Sauran 'yan matan suka bushe da dariya, d'aya
daga cikin su mai suna safeena tace" ke ma
Fatyma da son zance, yau yayanki ai har...
Wacce ke kusa da ita ta bige mata baki tare da
cewa "ke fa safeena akwai iskanci, ki na so ku
yi fad'a da Faty ke nan don ta sha gaya mana
yayanta ba d'an iska ba ne don haka ki yi shiru
da bakinki."
" uhmm" kawai Fateema ta ce ta koma bakin
gado ta zauna don ita duk Jin su take yi, ita
kad'ai ta san abinda take tunani.
K'arfe 9:40pm Farouq ya shigo gidan shi da
abokinsa Abbas, sai da suka fara zuwa wurin
Nadeeya ya jiye mata irin ledar da ya shigowa
Fateema da ita, Abbas yana ta bata baki ita
kuma sai wani cika take tana batsewa, a haka
dai suka barota suka yo part d'in Fateema.
A bakin k'ofa suka ci Karo da Faty ta za ta fito,
da sauri ta yi wurin yayanta tana cewa "ga
ango, ga ango".
Murmushi ya yi ya ce "Fatyma yau na zama dai
abokin wasanki ko"??
Ita ma murmushin ta yi ta ce" yayana ni fa nan
jira nake mu siye baki, sannan mu tafi".
D'an zaro ido Abbas ya yi, ya ce "zamani
k'anwa da siyen bakin wa."
Dariya suka saka gaba d'ayan su, sannan
Farouq ya janyo hannun Fatyma yana cewa
" yanzu mu k'arasa ciki k'anwata akwai kyauta
ta musamman da na kaiwa Umma ta ajiye miki,
don kin taka muhimmiyar rawa ganin na aure
k'awarki, thank yhu so much".
Fatyma ta ce "never mind bros, farin cikinka
shine nawa so dole na ba ka gudummawa don
ganin hak'an ka ya cimma ruwa".
Sakin hannun faty da yayi, yai daidai da
k'arasawarsa, inda fateema ke zaune, yana daf
da K'arasawa saitin fuskarta da ta ja mayafin
lafaya ta rufe... Abbas ya katseshi ta hanyar
cewa "Farouq wooo! Ka na ji ana maka magana
amma gaba d'aya hankalinka ya tafi gun
amaryarka, shafa sajen dake kwance a fuskarsa
ya yi tare da cewa
" am sorry! Me ka ce ne"??
Abbas ya ce
"ba ni nai magana ba k'awayenta ke ta Maka
magana ka share su, "oh! Sannunku
k'awayenmu ban ji ba ne". Cewar Farouq gaba
d'aya suka kwashe da dariya.
Lokacin Faty ta dawo daga part d'in Nadeeya
tana cewa
"to na yiwa Aunty Nadeeya sai da safe, don
haka kuma ku kwaso bags d'in ku mu yi gaba".
Abbas ne ya ce
"ke da kika ce sai kun saye baki, kuma kike
maganar su zo ku tafi".
Dariya Faty ta yi ta ce
"ya Abbas dama da wasa nake yi, kai muke jira
ka kai mu gida, ka ga dare ya rigaya ya yi, don
na san bros ko bai zo da kowa ba, zai zo tare
da kai, shi yasa muka tsaya jiranka, idan ka zo
ka mai da mu."
Haka ne Abbas ya ce tare da ja musu, doguwar
addu'a ta fatan zaman lafiya, su faty suka amsa
da ameen, sannan suka mik'e da zummar tafiya.
Farouq ko irin rakiyar nan da ake yi wa abokan
ango bai yi wa Abbas ba, suna fito ya rufo
k'ofar ya datse da key, ya nufi wurin amaryarsa
zuciyarsa taf farin ciki kamar wanda aka yiwa
bushara da aljanna.
Nima ganin haka na tarkato takarduna na yo
waje, tun kafin su Fateema su wuce, don na
samu su d'an la6ani ko a hanya sa saukeni, don
haka sai dai na ce "asuba tagari Farouq da
Fateema, Nadeeya kuma Allah ya ba da ikon
danne kishi" ...
Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [8/30,2016) phatyma
🌻: ▪BALLAGAZAR MACE ▪37-40
©MRS SAIF
Duk sammakon da na yi, don ganin yanayin da
amaryar ta tashi a banza, don ko da na isa na
tarar Fateema har ta yi wanka ta shek'a
kwalliya cikin dark purple shadda wadda aka
yiwa aiki da zare pink, ta sha English gold mai
kyau yari da sarqa d'aya daga cikin na lefenta.
Ta kashe d'auri ya zauna d'as akanta tamkar
gwaggwaro, fuskarta ta sha maka-up mai kyan
tsari, sai walwali take yi tamkar tauraruwa,
jikinta sai wani asirtaccen k'amshi ke tashi, tana
cikin zira wani flatshoe pink colour mai kyan
gaske, Farouq ya bud'e k'ofar ya shigo, shi ma
ga dukkan alamu bai dad'e da gama shiri ba, ya
yi kyau sosai ka na ganin shi ka ga ango mai
cike da farin ciki da annushuwar halin da ya
tsince kansa a ciki.
A bakin k'ofar ya tsaya tare da kafe Fateema da
ido, fuskarsa d'auke da murmushi ya ce "yhu
look very beautiful, komai na ki burgeni ya ke
fatyna".
"thanks" ta fad'i tare da k'okarin gyara igiyar
takalmin da ya d'an karkace, K'arasawa inda
take sunkuye ya yi,ya d'agata ya zaunar da ita
akan gefen gado sannan ya ce" lemme help
yhu"... Yana k'okarin kai hannunsa kan
takalmin, ya gama gyara takalmin sarai, amma
sai ya kasa sakin k'afar, yana k'arewa
had'ad'd'en Jan lalle da zanen bak'n fulawan da
ke k'afar kallo.
Shirun da ta ji yayi ne ya tabbatar mata ya
gama gyara mata takalmin, don haka ta ce "bari
na je na gaishe da mutanen gidan, kar su jini
shiru".
"hmm"Farouq ya ce tare da lumshe ido sannan
ya jingina bayan sa a kujerar da yake zaune.
Don ko kad'an ba ya son missing k'amshn
jikinta, in dai yana tare da ita sai ya manta
duniyar da yake, rufe idonsa ya yi sosai don
tuna irin farin cikin da ya samu a daren jiya,
sosai yake Jin k'aunar Fateema a ransa, fatan
da yake Allah ya sa ta d'ore a haka, don daga
gani za ta yi sanyin hali.
Bata wani sha wahala ta gano part d'in Nadeeya
don ba wani nisa ne na ku zo mu gani ba a
tsakanin su, kuma tsarin wurin d'aya ya ke da
na ta.
Da sallamarta ta kutsa kai cikin parlourn, sai dai
da alama Nadeeyan ba ta parlourn sai Ansar da
ke zaune ya bud'e gwangwanin madara duk ya
barbazar a gurin, ya kuma d'iba ya saka a jikin
sa, da alama tea suka gama sha ba a kwashe
kayan ba.
Da d'an hanzarinta ta k'arasa gurin yaron ta
d'aga shi tana kakka6esa masa, a ranta ta ce
"wow! Yaron kyakkyawa da shi".
Dama Fateema akwai masifar son yara, duk
wanda ya san ta ya San halinta na son yara.
Da ta ga madarar duk ya manne a jikinsa ya k'i
fita, don da danshin ruwa a jikinsa, sai kawai ta
tu6e masa kayan,ta bar shi daga shi sai diaper
tana cewa "bari mummynka ta fito sai a chanza
ma wani kayan ko"??
[8/30,16,5:16 PM] phatyma :
Ta k'arasa maganar tare da sakarwa yaron
murmushi kamar yasan, me take cewa shima ya
6angale baki yana dariya, sai dai tun da ta cire
masa kayan take Jin d'an wani wari - wari yana
tashi, don haka ta bi jikin yaron da kallo daga
k'arshe idonta ya sauka kan diaper'n yaron
wadda ta cika mak'il har ya fara zuba, da alama
tun jiya yake a jikinsa ba'a cire masa ba.
D'an fito da ido waje Teema ta yi tana kallon
yaron, ta rasa mai za ta yi masa, ga shi har
yanzu mamansa ba ta fito ba, don da alama
tana cikin toilet don ta ji motsin mutum a ciki.
×××××××××
Daga k'arshe ta yanke shawarar ta tafi da yaron
side d'in ta kawai ta masa wanka a can idan
mamansa ta fito ta dawo da shi a saka masa
wani, don haka ta sunkuya da nufin d'aukan shi
su tafi, ta ji an banko k'ofar toilet da k'arfi an
fito.
Nadeeya ce d'aure da zani da alama daga
wanka ta fito, kana ganinta kasan ba ta fita,
jikinta sai wata walk'iya yake yi na alamar
daud'a ta taso amma ba a samu damar darjeta
ba, tamkar watsa ruwan ta yi ta fito.
Kallo d'aya Fateema ta yi mata ta sadda kanta
k'asa tare da fad'in ina kwana"?
"lafiya " ta bata amsa a tak'aice, Sannan ta
cigaba da fad'in " ya aka yi na ga kin cire masa
kaya, ko kinibibi ne irin na amare masu neman
shiga za ki fara akansa.??
Ja gale Fateema ta yi tana kallonta, a ranta ta
ce "to fa ita na ta salon kishin kenan...??
" kin shigo d'akin mutum kin ga baya nan ba sai
ki fita".
Maganar Nadeeya ta katse mata tunanin.
Nuna Ansar ta yi da hannu, ta ce "yaro na tarar
yana 6arna na tsaya gyara shi, sai kuma daga
baya na ankare da ya cika diaper'n sa, so shine
da zan tafi da shi na yi masa wanka sai ga shi
kin fito".
"To uwar iya zance, na ji na kuma gode kya iya
tafiya, Nadeeya ta fad'a tare da gyara mazaunin
zanin dake jikinta.
Murmushin takaici Teema ta saki tare da kad'a
kai ta yi hanyar fita, dogon tsakin da Nadeeya
ta saki shi ya tilasta mata jiyowa, daidai lokacin
ta kakka6e kayan Ansar dake k'asa tana niyyar
mai da masa.
Mamaki sosai Fateema ke yi tana tunanin,
wannan wace irin mace ce, tana nufin haka zata
maidawa yaron kayan ba tare da ko diaper'n
jikinsa ta cire masa ba.
"Tab" ta ce a ranta lallai akwai magana a gidan
nan, da wannan tunanin ta k'arasa part d'in ta,
in da ta bar Farouq har lokacin yana zaune a
gurin, sai dai yanzu ya mai da hankalinsa ga TV,
yana kallon news na safe.
Sallamar da ta yi shi ya dawo da hankalinsa
gareta, cikin k'ank'anin lokaci ya fuskanci
sauyawar da fuskarta ta yi, a hankali ya taka
zuwa inda take, gaba d'aya ya janyota jikinsa,
cikin muryar rad'a yake cewa
"something troubling yhu babe, what
happened???
A hankali ta girgiza kanta alamar ba komai, don
har ga Allah ba ta so ya gane damuwarta ba,
domin abun da Nadeeya ta mata ba ta d'auke
shi wani abu, don ta shirya d'aukan k'alubalen
da ya fi wannan.
Sai dai Farouq ya santa sosai, fiye da yadda
yasan yunwar cikin sa, ta yanda a kowa ne hali
take ciki zai iya tantancewa.
Cikin son bagarar da zancen ta ce "Qalby ni fa
yunwa na ke ji".
Murmushi Farouq ya yi ya ce
"Ai ke ce na ce zan fita na siyo mana abinda za
mu yi breakfast kin k'i, kin ce sai dai ki girka da
kanki ni kuwa yaushe zan bar amarya ta shiga
kitchen washe garin ranar da ta tare, ki yi
hak'uri baby idan kin k'ara hutawa sai ki mana,
ni kai na zan yi matuk'ar farin ciki da hakan, na
yiwa Umma waya yanzu haka fatyma na hanya
za ta kawo mana breakfast.
Bai dad'e da rufe baki ba suka jiyo sallamar
Fatyman, cikin d'auken ganin juna, suka
rungume juna suna murna kamar wad'anda suka
shekara ba su ga juna ba.
Sannan Faty ta juya tana gaishe da yayanta,
kafin daga bisani su shige kitchen Faty rik'e da
foodflask da ta shigo da shi, Fateema kuma ta
kar6a mata d'ayan teaflask da ke hannunta.
Kunun gyad'a ne mai kyau a cikin teaflask, sai
kuma yam fritters with chicken souce a d'aya
foodflask d'in, bayan sun gama zubawa a plates,
sai suka d'oro akan tray tare da cups, suka
dawo parlourn.
A dining table suka dire kayan sannan suka yi
kiran Farouq, anan suka ba je suna cin
abincinsu cikin nishad'i suna firansu jefi-jefi har
da Farouq, Faty tana son tambayar Fateema
first night amma Farouq ya kasa ya tsare ya k'i
ba su damar su d'an ke6e, kun san 'yan mata
da maitar son Jin ya first night ya
kasance...lolz......
Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [8/31, 4:24 PM]
Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪41&42
©Mrs Saif
Sati d'aya cif suka yi suna kwasar amarci,
tamkar za su had'iye junansu don so da kulawa,
yayin da Fateema ta shige lungu da sak'o na
zuciyar Farouq, ta yadda ba shi da wani muradi,
da ya wuce kasancewa tare da ita.
A kwanakin da suka yi kullum Fateema ke jigilar
kawo musu abincin safe kasancewar suna cikin
hutu, na rana da dare kuwa Farouq ke turawa a
kar6o, don in dai ta Nadeeya ne sai dai su mutu
ba su ci ba, don yanzu haka, 'yan aikin da
Farouq ya kawo kafin tariyar Fateema suke
girkin gidan, idan sun gama Nadeeya ta yi zaune
ta nad'i abinta tashi, ita kam Fateema tun da ta
ga haka ta ce "ba za ta iya ci ba, don ba ta
saba da cin girkin masu aiki ba, don a gidansu
ita da ummynta ke girki, ko da wasa Ummy ba
ta saka masu aiki a harkar da ya shafi kitchen".
"musamman wad'an nan ta ga ko tsaftar kirki
ba su da shi, daga su har uwar d'akin ta su,
don cikin sati d'ayan da ta yi ta gane wacece
Nadeeya, don haka ta k'udurci niyyar kawo
gyara a cikin gidan ko don samun kwanciyar
hankalin mai gidan, domin da Farouq ya amince
da zancen ta da tuni ta tsufa a kitchen, amma
ya dage ta bari ko sati d'aya ne ta yi, sannan ta
fara shiga kitchen kafin lokacin ta k'ara hutawa,
ba ta son yi masa musu shi yasa ta amince, don
haka yanzu jira kawai take yi, girki ya kuma
zagayowa kanta, ta fara shiga office mai daraja
ga duk macen da tasan kanta."
*************
Tun safe yau da ya tashi yake Jin shi wani iri,
kamar ba shi ba duk jikinsa ya yi sanyi, ba wani
fara'a a tare da shi ba kamar yadda ya saba a
'yan kwanakin nan ba.
Fateema har ta kula da yanayin da ya ke ciki,
don haka a gurguje ta k'arasa shirinta cikin
atampa super lucca's grey colour, fitted gown ce
wadda ta zauna jikinta cas ta yi kyau sosai,
fuskar nan ta yi fayau ta k'ara hasken amarci,
kana ganinta ka ga amaryar da ke samun
cikkakiyar kulawa gun angonta.
K'arasawa ta yi kan gadon da yake zaune ya
jingina bayansa da pillow, ta zame pillown sai ta
yi replacing kanta da pillown, sosai ya ji dad'in
kwanciya fiye yanda ya ke a da.
Cikin salon maganarta mai Jan hankali ta ce
"Qalby wai me ke damunka ne, na ganka yau a
cikin wani yanayi please gaya mun abinda ke
damunka"?? Ta k'arasa maganar cikin sigar
shagwa6a kamar za ta yi kuka.
Rufe idonsa ya yi sosai, sannan ya bud'e su
akan fuskar Fateema, ya ce" ke"a tak'aice. Zaro
ido Fateema ta yi tare da nuna kanta da yatsa,
"ni kuma"??
Gyd'a kai ya yi alamun hakan ya ke nufi,sannan
ya yi murmushi ganin yadda take masa wani
kallo na rashin fahimta, ya ce
" I'll miss yhu Fatyna, rashinki a tare da ni, ji na
ke tamkar na rasa wani 6angare na jikina, zan yi
missing wannan daddad'an k'amshi dake tashi
daga jikinki, k'amshin parlourn ki da d'akin ki...
nd everything from yhu babe"
********
Murmushi Teema ta yi tare da fad'in
"common! Qalby I guess two days ne kawai, za
ka yi ka dawo wurina".??
"haka Nadeeya ke so,amma ni na gaya mata
idan ta yi girki yau gobe ki yi, ku rik'a kwana
d'ai d'aya kawai".
Shiru fateema ta yi tana nazarin maganarsa, don
duk ta fahimce abinda ke damunsa,don d'an
zaman da suka yi ta fuskanci Farouq mutum
ne,mai matuk'ar son k'amshi, da k'amshi kawai
za ka iya siye zuciyarsa, don haka ta k'udiri
aniyar zage damtse don ganin ta faranta masa
ta kowace fuska, haka ba za ta yiwa Nadeeya
k'eta ba, za ta lurar da ita, idan ta fahimceta shi
kenan, don akwai gyara sosai a lamuranta,
domin ba ta Jin ko d'an turaren nan, na stick
Nadeeya na sakawa a d'akinta, domin idan ta
shiga part d'in ta tana Jin d'an wani bashi-bashi
yana tashi wanda ko ita da take mace Allah
Allah ta ke ta fito, bare kuma namiji, ko ajikinta
ba ta ji tana saka turare yanda ya kamata".
Gyara kwanciya Farouq ya yi, yana shirin
komawa barci, sai a lokacin Fateema ta ankare
ta ce
"Qalby ni kam ina ga, da ka hak'ura an yi yanda
take so, ni dai in don ta ni ne, na amince da
hakan, zai fi ma a rik'a kwana biyu,don
mafiyawancin gidaje na ga haka ake yi".
"ni dai to ban amince da haka ba, ba zan iya
rashinki har na kwana 2 ba".
"haba Qalby, ka ga za ta ga kamar an danne
hakk'inta ne, tunda har ta riga ta gaya ma ga
yadda ta ke so, in dai don k'amshin part d'in
nan ne, duka turarukan da air fresheners da na
ke using da su anan, duka na maka amfani da
su a part d'in ka, ai ka shiga ka ga ni ko"???
Ta k'arasa maganar tare da zuba masa ido,
"hmm" kawai ya ce, don da alama har barci ya
fara fizgarsa.
Bin shi ta yi da kallo daga k'arshe, ta sauke
idonta akan agwogwan da ke manne a bangon
d'akin, 11:43am ya nuna,zaro manyan idanunta
waje ta yi, tana cewa har lokaci ya tafi haka, a
hankali ta sa hannu a jikin sa ta fara k'ok'arin
tashin shi, duk da bata son tashin shi idan yana
barci amma ya zama dole, don kar ya shiga
Hak'k'in Nadeeya, gwanda ya je can part d'in ta
ya kwanta, ko part d'in sa,don abinda ba ta so
a mata, ba za ta bari a yiwa wata ba, d'an
girgiza shi ta fara tana k'okarin d'aga shi daga
jikinta... Ta ji an turo k'ofar an shigo ba ko
sallama.
Nadeeya ce ta shigo, k'ik'am ta yi a kan su ta
zuba musu ido, cike da masifa ta fara magana
"aa dole ka manta da k'urar da ta kwasoni,
kana nan ta wani rungumeka sai ka ce d'an
goye ana nuna maka karuwanci".
Fateema ba ta ce komai ba illa k'okarin d'aga
kan Farouq daga cinyarta da take yi.
Farouq da tun shigowarta ya farka ya fara
magana ba tare da ya tashi daga kwancen da
yake ba, ya ce
"yanzu shigowar da kika yi ba tare da neman
izini ba kin kyauta kenan"???
Nadeeya ba ta ce komai ba illa karkad'a jiki da
ta fara.
Don haka Farouq ya cigaba, "sannan mai kika
tarar ana yi da har kike kiran karuwanci,mace ta
zama sama da karuwa ma in dai a gidan ta ne
ai ba laifi ba ne...
Nadeeya ta katse shi ta hanyar cewa " Farouq
ya ishe ni haka, ya za a yi a gaban yarinya ka
zo kana ci mun fuska, dama an ce in dai namiji
ya yi sabon aure, dole sai ya wulak'anta ta gida,
to na gode da ka fara gwada mun kalar ka ta
d'a namiji tun kafin aje ko'ina", daga haka ba ta
kuma cewa komai ba ta nufi hanyar fita daga
d'akin.
Mum Twins 😘
[10/16, 4:23 PM] mrm kd: [9/2,16, 7:59 PM]
phatyma : ▪BALLAGAZAR MACE ▪43
©Mrs Saif
Ranta a matuk'ar 6ace ta koma part d'in ta, ta
yada zango a parlor tare da zubewa akan d'aya
daga cikin kujerun wurin.
Yanzu a duniya ba ta da wata matsala da ya
wuce Fateema, ta tsani ta bud'e ido ta ganta
cikin gidan, wani mahaukacin kishinta take
ji,tashi ta yi daga zaunan da take ta fara safa
da marwa, don duk ta lalubo mafita amma ta
kasa samu, daga k'arshe dai ta yanke shawarar
yin amfani da magungunan da mai maganin
mata ta bata, ko ta dace hankalin Farouq ya jiyo
gareta ita kad'ai.
Da wannan tunanin ne ta samu hankalinta ya
d'an kwanta, don ta d'au alwashin in dai
hankalin Farouq ya dawo gareta lallai sai
Fateema ta raina kan ta a cikin gidan, don zama
gidan sai ya mata wahala.
Farouq kuwa tun bayan fitar Nadeeya Fateema
ta takurashi sai ya fito zuwa part d'in Nadeeya,
ba don ya so ba ya fito, da kamar ya wuce
6angaren sa, sai kuma ya ga rashin kyautawar
hakan don haka ya fara shiga part d'in Nadeeya.
Ko da ya tarar da ita sai wani cin magani take,
shi dariya ma ta so ba shi ya dai gimtse ya ce
"yanzu me ye abun fushi, mu fa ki ka yiwa laifi,
sannan ki juye abun ya dawo kan mu"???
"haka ma za ka ce, bayan sanin kanka ne kun
shiga hakkina, kamata yayi ace zuwa yanzu ka
yi sallama da amaryarka ka dawo wurina, har
zuwa lokacin da za ta kuma kar6ar girki".
'au haba, dama haka mu ka yi dake? Ni fa ba
wasu k'aidoji da za ki gindaya mun, don nasan
abinda na ke yi, ba ki isa ki ce mun wai don kin
kar6i girki ba, shi kenan sai na fito daga d'akin
Fateema tun da asuba na dawo gun ki, all i
know yau kwanakin ne, ba zan kuma d'auka na
kai wa Teema ba, don nima ina da burin adalci
a tsakanin ku."
"hmm!haka dai ka ce", Nadeeya ta fad'a tare da
K'arasawa cikin d'aki don d'auko Ansar da ya
fara kuka, da alama tashinsa ke nan daga barci.
Saboda haka shi ma Farouq ya fice daga
parlourn don dama fita yake son yi duk da ba
aiki zai je ba, don hutunsa sai gobe Monday zai
k'are, amma yana so ya je gaishe da Ummansa.
[9/2, 7:59 PM] phatyma ▪BALLAGAZAR MACE
▪44
©Mrs Saif
Tun bayan fitar Farouq Nadeeya ta fara
had'ed'an kayan da za ta yi amfani da su, daga
na sha har zuwa na inserting, maimakon ta
had'a da gyara lungu da sak'o na jikinta, a'a ba
ta san da haka ba ta dai yi wanka yau, shi ma
bur-bur ba yanda ya kamata ba.
Sai bayan takwas na dare ya dawo don Umma
ta d'an tsaida shi da hira, yana shigowa ya
tarar da Nadeeya sai cika take tana batsewa
akan ya jima bai dawo ba, ko sannu da zuwa ba
ta yi masa ba ta hau yi masa k'orafi.
"yanzu Farouq abinda ka yi ya dace ina fa gani
kwanan ba ka zuwa ko'ina kana mak'ale a
d'akin amarya, amma saboda yau mak'iyarka ta
kar6i girki shine sai yanzu ka ke dawowa
gida"??ta k'arasa maganar da rawar murya
alamar kuka ya taho mata.
Tausayinta Farouq ya ji, ya tako zuwa inda take
zaune ya ce "haba Nadeeya ki daina fad'an ke
mak'iyiya ta ce in da ina k'in ki da ba zan zauna
da ke ba, har kawo wannan lokacin, ke ki ka
kasa fahimta ta tun tuni, kuma daren da na yi
Umma ce ta tsaidani".
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "shi kenan".
Ganin ta sauko ya sa Farouq cewa "bari na je
na watsa ruwa sai na fito".
"to " ta ce da shi sannan ya haura sama don
zuwa part d'in sa.
*****9:45pm
Ya fito cikin brown jallabiya, sai k'amshi ke
tashi daga jikinsa main parlourn su ya zauna
yana jiran fitowar Nadeeya cikin d'an k'ank'anin
lokaci kuwa ta fito, tana fad'in" bari a kawo
maka abinci".
Bayan ta d'auko abincin ta ajiye akan dinning
table, ya ce" Fateema fa"??
Sai da ta 6ata fuska ta ce "na saka su Raleeya
su kira ta ci, amma da ta zo bud'e abincin
kawai ta yi ta ce
" ta k'oshi".
K'wafa ta ja, tace "ai yarinyar nan sai na koya
mata hankali sai ta rik'a nuna kamar ta fi
kowa".
Bai ce da ita komai ba, ya nufi dinning area,
bud'e abincin ya fara yi tuwon shinkafa ne
amma ya wani cakalkale daga ga ni an sakarwa
shinkafar ruwa fiye da k'ima, sai miyar d'anye
ku6ewa wadda itama ga ta nan ne dai, don yana
bud'e miyar k'arnin naman da aka yi miyar ya
dake hancinsa tamkar ba a dafa shi ba.
Rufewa ya yi sannan ya mik'e yana shirin barin
wurin, cikin rashin fahimta Nadeeya ta ce
"ina za ka je kuma"??
"zan je duba Teema ne".
Bin shi ta yi da kallo tare da ta6e baki, bayan
ya juya baya ta bi shi da harara.
Teema na zaune a cikin d'akinta ta sauya kayan
jikinta zuwa wadatacciyar night gown, plate ne
d'auke da indomie da fried egg, sai ruwan lipton
a cup da take kur6a a hankali kasancewar ta ji
cikinta duk ba dad'i, ta kasa cin abincin.
Farouq ya turo k'ofar ya shigo la66ansa d'auke
da sallama, amsa sallamar ta yi sannan ta
d'auke kan ta daga kallonsa, haka kurum itama
yanzu sai ta ji tana tsakanin kishinsa, yau ita
d'aya zata zauna kamar mayya, sai kuma wata
zuciyar ta ce da ita "haba fateema ki zo ki
aurewa mace miji, don zai koma wurinta shine
har za ki fara Jin haushi, to ita kuma kwanakin
da ya kwashe tare da ke sai ta mutu ke nan".
Da wannan tunanin ta k'arfafa zuciyarta har ta
k'wak'ulo wani murmushi ta ce
"sannu da shigowa".
Bai amsata ba illa mazauni da ya yiwa kan sa,
sannan ya kar6i cup d'in hannunta ya yi kur6a
d'aya ya ajiye, tare da cewa "Fatyna ban yarda
da wannan fake murmushin ba don na hango
damuwa a idanunki, gaya mun me ke
damunki"???
[9/2, 7:59 PM] phatyma : ▪BALLAGAZAR MACE
▪44
©Mrs Saif
Murmushin ta kuma yi ta ce "ba komai".
"ban yarda ba akwai komai gaya mun what's
wrong with yhu".
"nothing, but... am just feeling lonely".
"olright, ya fad'a tare da watsa hannayensa
duka biyu, sannan ya cigaba da fad'in "na fasa
zuwa wurin Nadeeyar bari na yi zama tare da
ke", ya k'arasa maganar tare da d'aga mata
kira.
Zaro ido ta yi waje tana fad'in "a'a wallahi ba
haka nake nufi ba, ka yi hak'uri ka je wurinta,
bana son ka janyo mun magana, ko ba haka ba
ma, ba kyau abinda ka ke shirin yi".
Sosai dariya ta zowa Farouq ya danne, don
yadda ya ga duk ta rikice, yana sane ya gaya
mata haka don ta saki ranta.
Ya ce "okay, yanzu ki ci abinci sosai ina ga ni,
idan har kina so na tafi, kin ga nima yunwa na
ke ji, amma ganin ki cikin wani yanayi ya sa na
manta da ita".
"a haba! Ka zo mu ci wannan kawai a zai ishe
mu".
Ba musu ya zauna, ita kuma ta tashi ta d'auko
masa folk, sannan suka fara ci, Farouq bai an
kara ba ya kwashe abincin tas sai maimaita
dad'insa ya ke yi.
Fateema kuwa sai dariya take masa, ta ce "ai
wannan agurguje na yi shi, don na d'an samu
abinda zan sakawa cikina, da na san za ka ci ai
wanda ya fi wannan zan dafa Maka".
Murmushi Farouq ya yi ya ce "Allah Fatyna
amma kuwa zan yi farin ciki sosai ki ka kasance
gwana wurin iya kirki".
******
Da haka dai ya yiwa Fateema sallama ya nufi
sashen Nadeeya, nan ma wata rigimar ce ta
6arke, don ta ji haushin dad'ewar da yayi d'akin
Fateema, bayan nan kuma ya ce "sai dai ta biyo
shi part d'in sa, don shi tun daga parlourn ta da
k'yar yake iya had'iye yawu, yanda ya ji gurin
na wani tsami-tsami kamar an ajiye kwanannen
abinci.
Yayin da ita kuma Nadeeya ta tsaya kai da fata,
sai dai ya kwana anan 6angarenta, tunda
amarya ma bin ta, yayi ba ita ta je ba.
Ganin za ta 6ata masa lokaci yasa ya fice daga
parlourn ya bar ta tsaye, don ya gaji da shak'ar
gubar d'akin ta.
Ganin ba Sarki sai Allah ya sa ta ajiye girman
kai ta yi shirin bin sa, ko ba komai tana da
buk'atar mijinta, sannan tana son gwajin
magungunan da aka ba ta.
Farouq dai kusan duk abinda ya wakana
tsakanin sa da Nadeeya zan iya cewa ba a
hayyacinsa ya ke ba, tsabagen hamami da warin
dake tashi a jikinta, don ji yake kamar har tafi
da, ko don ya saba da k'amshin Fateema ne???
Ya jefawa kan sa wannan tambayar, don sai
yanzu yake tabbatarwa kan sa da lallai Nadeeya
ba za ta rasa warin k'ashi ba.
Juyawa ya yi gefen da take kwance yana
kallonta, tana ta shak'ar barci hankalinta
kwance, wanka ya je yayi sannan ya koma
d'akin ya d'auki pillownsa ya koma parlour ya
kwanta.
Abinda Farouq bai sani ba cushe-cushen da
Nadeeya ta yiwa kan ta shiya k'ara tsananta
warin jikinta, saboda ta yi cushe-cushe da yawa
sannan ga shi ba wata cikakkiyar tsafta, don
haka abin ya had'e mata biyu.
******
Da k'yar Farouq ya ga kwana biyun Nadeeya ya
wuce don ji yake kamar yana prison, yau kuwa
cikin annuri ya tashi, don Jin sa yake kamar
wanda aka yiwa gafara.
Kamar yadda ya saba fita haka yau ma shirya
ya fita.
Nadeeya ko yana fita itama ta sa kai ta fice,
don tana son had'uwa da mai magani.....
Mum Twins 😘
[10/16, 4:38 PM] mrm kd: [9/5, 5:29 PM]
Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪46
©Mrs Saif
Fateema na fitowa ta ga bata nan don haka ta
kira su Raleeya (masu aiki) tana tambayar in da
Nadeeya ta je, suka ce "ba su sa ni ba, don
suma ta kai musu Ansar ta ce su rik'e shi har
ta dawo".
Hannu ta sa ta kar6i yaron duk ya yi wani kaca
- kaca ta ce "ku yanzu don Allah ko yaron ba za
ku iya gyarawa ba, to miye amfanin ku ke
nan"???
Shiru suka yi suka kasa cewa komai, saboda
haka Fateema ta cigaba" yanzu ku kalli parlourn
nan, sannan ku kalli jikin ku tare da nuna
qaramar da ya tsa ta cigaba da cewa "ke kam
ina ga tun da na zo da wannan kayan na ke
ganinki, ba ki chanza ba, hatta aikin da aka
kawo ku yi ba wani yi kuke yi ba iya kacin ku ku
yi girki ku ci ku je ku kwanta, ba ruwanku da
gyaran gida,kalli parlourn nan bana Jin yau kun
gyara shi"??
Babbar ce ta fara magana cikin sark'ewar murya
"hajiya ai mu ba a sanar da mu aikin da za mu
yi ba, mu dai mun san hajiya na cewa mu yi
girki kuma duk...
Fateema ta katseta" ku ba ku san abin da ya
kamata ku yi ba sai an gaya muku, ko anan
gidan kuka fara yin aiki".
Girgiza kai ta yi alamar a'a, "don haka ku
saurari abinda zan gaya muku domin idan ta ni
ce bana buk'atar wasu 'yan aiki amma tun da
an kawo ku, ba ni da ikon korarku amma zan
gindaya muku sharud'a don ni bana buk'atar
girkinku duk ranar girkina.
Don haka daga yau idan kun tashi a gyara
parlourn nan ciki da waje, da kitchen da toilets
na nan da na 6angaren ku, daga cikin gidan nan
har farfajiyar gidan nan bana son na ga ko
tsinke a k'asa aikinku ne wannan,zan nuna
muku duk yadda za ku yi, idan maman Ansar za
ta had'a mu ku da gyaran part d'in ta shi kenan
amma ni dai wad'annan ayyukan na ke so duk
ranar aiki na".
D'an rusunawa suka yi suka ce "shi kenan
hajiya yanda kike so haka za'a yi".
Fateema ta ce "yawwa bari yanzu na je na yiwa
Ansar wanka sai ku fara aikin, amma kafin nan
je ki d'auko mun kayansa set d'aya na samu na
saka masa idan na masa wanka".
Jim kad'an Raleeya ta fito ta ce "hajiya ai kayan
nasa duk ya yi daud'a iya wanda na gani".
Juyawa Fateema ta yi tana kallonta cike da
mamaki ta ce "yanzu don Allah Raleeya kayan
Ansar ba za ku iya wankewa ba har sai sun yi
datti gaba d'aya"?
K'asa raliya ta yi da kanta alamun Jin kunya ya
bayyana a fuskarta.
" shike nan yanzu ki je ki kwaso kayan ki bawa
Habi ta wanke, yasso sai ke ki fara wani aikin
kafin ta gama".
Haka kuwa aka yi nan da nan suka hau ayyukan
gidan Fateema na taya su, har suka gama yayin
da ita kuma ta yiwa Ansar wanka ta gyara shi
tsaf sai k'amshi yake yi, zuwa lokacin har ta
gama girkin rana amma ko alamar dawowar
Nadeeya babu...
[9/5, 5:29 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE
▪47
©MRS SAIF
K'arfe uku Teema ta fara preparing dinner, zuwa
lokacin zuciyarta cike take da tunanin inda
Nadeeya ta je ta bar
yaro, duk da dai ta yayeshi amma ita a
tunaninta bai kamata ace ta dad'e kamar haka
ba, shi kam yaron ko ajikinsa sai wasan sa yake
yi hankali kwance.
*****
Nadeeya kuwa tunda ta fita bata zame ko ina ba
sai gidan maman Nabeela ranta a jagule ta
shiga gidan, maman Nabeela na ganinta ta san
ba lafiya ba.
Da hanzarinta ta nufeta tare da fad'in "lafiya
Nadeeya na ganki da sassafen nan"??
Wata katuwar ajiyar zuciya ta sauke ta ce" ina
fa lafiya ai yau matar nan ko ni ko ita don sai ta
biyani kud'i na,wai har ni zata yaudara cewa ta
yi muddun na yi amfani da magungunan nan tun
daren ranar zan ga sauyi, zan kuma sha
mamaki".
"au bai yi ba ne"?? Maman Nabeela ta tambaya.
A na sha mamaki amma fa na wulak'anci, don
ba ki ga yanda muka k'ark'e da Farouq ba, don
maganin tamkar bak'in jini ya k'ara mun a
wurinsa, baki ga wulak'anci ba, har wani d'auke
numfashi ya ke yi idan muna tare, sai ka ce
wanda ke tare da ja6a, wallahi maman Nabeela
daren jiya na k'unshe bak'in ciki, don duk son
6oyewar da yayi sai da na gano shi don
yanayinsa kawai ya nuna mun komai yake yi
don dole ne don ransa na so ba."
Ajiyar Numfashi maman Nabeela ta yi sannan ta
ce "ni dama ai kin ji sai da na yi magana a
gabanta na ce mata, na matsin nan warinsa ya
yi yawa, ta ce ai idan kin yi amfani da turarukan
tsugunno da miski ba za'a ji warin ba, kuma duk
Kin yi haka"??
Ta6e baki Nadeeya ta yi ta ce" ni ba abinda na
yi, kasa kud'i irin haka ka saye magani sannan
sai ka had'a da wani turare-turen jiki ba zan iya
ba gaskiya, ni na fison yanke take".
Shiru maman Nabeela ta yi don babbar matsalar
Nadeeya k'in d'aukar shawara, duk da haka ta
ce "kin san fa su magungunan nan musamman
na matsi matsala ne da su, sai kin san irin
wanda za ki na amfani da shi, tabbas akwai
masu kyau da inganci, amma ni wanda aka ba ki
tun fil'azal warin da suke yi bai mun ba, har da
wai wani kashin birbiri ka kuma kwasa ka cusa
a jikinka guri mai k'ima da daraja ga duk wata
'ya mace, ni don na ga kin rud'e akan kayan ne
kawai na yi shiru amma...
"don Allah ni tashi mu je gidanta tun bata kad'a
ta je wani wuri ba, duk Kin cika ni da surutu".
Ko da suka je gidan ba su tarar da ita ba har ta
fita sai yaranta' yan mata a cikin gidan, don
haka Nadeeya ta ce "ba ta ga ta tafiya ba har
sai ta jira dawowarta".
Maman Nabeela da ta ji shiru ba ta dawo ba, ta
yi gaba don tana da abin yi a gida ta bar
Nadeeya anan tana jiran gawon shanu.
[9/5, 5:29 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE
▪48
©MRS SAIF
K'arfe 5:47pm zuwa lokacin Fateema ta gama
aikinta tsaf, in da ta dafawa Qalbynta
had'd'ad'en girki mai kyau wanda zai saka
kunnensa motsi, oriental rice ne ta dafa tare da
nugget fish, kasancewar ta fuskanci Farouq
akwai son kifi sai paw-paw slush wanda ya ji
k'ananan ice a ciki.
Hatta su Raleeya da suka ci abincin sun mutu
da dad'insa don tamkar za su tafi da yatsun
hannunsu don gard'in da suka ji yayi musu,
tambaya Teema ta sha ta a wurinsu ta yadda
ake girkin, ita kam murmushi kawai take musu
tana ba su amsa, don d'an zaman da suka yi da
ita sun fuskanci ba ta da wulak'anci ko kad'an
ga ta da faran-faran ga jama'a.
***
Ita kan ta Fateeman ta kuma yin wanka ta cake
cikin wasu english wears yellow and black rigar
yellow skirt black 'yar k'arama ce rigar mai
siririn hannun ko cibiyarta ba ta rufe ba, gaban
rigar net ne black colour wanda ta cikin net d'in
ba abinda ba a gani, shi kansa skirt d'in d'an
k'arami ne don bai kai guiwarta ba ga shi very
tight don ko motsin arzuki baya barin ta ta yi,
ganshin kanta tattare shi ta cure a tsakiyar
kanta sannan ta matse da ribbon yellow, light
makeup ta yi daga powder sai lipstick pink da ta
saka sai kwallin da ta zizara a kyawawan
idanunta mai k'ara musu haske da kyau, simple
Indian earing ne a kunnenta golden colour da
stones black.
Teema ta yi kyau sosai tamkar 'yar tsana, kan
three seater ta zauna ta mik'e k'afa abinta, a
main parlour ta zauna don a cewar ta ta gaji da
k'ullewa cikin part d'in ta ita kad'ai kamar
mayya, gwanda ta zauna anan ta sha iska ko
banza za tana Jin motsin su Raleeya.
Gaba d'aya hankalinta na kan TV tana kallon
wani series, Ansar na gefenta yana shan sweet
abinsa, tun daga gate d'in gidan ya ji wani
k'amshi ya cika masa hanci take ya ji zuciyarsa
ta yi wani haske, parking ya yi ya fito a lokacin
gaba d'aya k'amshi gidan ya gama rikita shi,
don ya rasa wanne ya fiso a ciki, k'amshin
girkin da yake ji yana tashi ne ta wani 6angaren
gidan ko kuma na wani mayataccen k'amshin
turaren wuta wanda 'yan kwanakin nan har ya
saba da daddad'an k'amshin sa a part d'in
Fateema.
****
Tsaye yake k'yam yana k'are mata kallo wanda
ko alamar tsayawarshi ba ta ji ba, bare sallamar
da ya yi, K'arasawa ya yi inda take zaune gaba
d'aya ya sa hannu ya d'agata sama yana juyi
da ita kamar irin babba ya d'auki yaro yana
masa wasa.
Da farko har ta d'an tsorata da ta ji ta a sama
ba tsammani amma tana ganin Farouq ne sai ta
sakar masa wani lallausan murmushi tare da
k'ok'arin saukowa amma ko alama ta kasa in
ban da dariya ba abinda Farouq ke yi, a haka
Ansar da ke gefe a zaune ya taso shima yana
mik'awa Abbansa hannu alamar ya d'auke shi,
Farouq ko lura da shi bai yi ba don gaba d'aya
Fateema ta gama rikita masa lissafi, sai
Fateema ce ta ankare da shi a haka ta mik'o
hannunta zuwa k'asa da zummar d'aukan Ansar,
sannan Farouq ya lura da shi, duk da haka bai
sauke Fateeman ba, bai yi yunk'urin d'aukan
Ansar ba, sai Fateema ke ta yunk'urin kai hannu
ta d'auke shi ta kasa, Farouq sai dariya ya ke
mata don ta masifar masa kyau a hakan da take
ko don shine first time da ya ganta da english
wears, hatta Ansar sai ya ga yaron ya masa
kyau yau don har haske ya qara.
Maganar Fateema ce ta katse masa tunani
"don Allah Qalby ka saukeni na d'auke shi,
murmushi ya sakar mata tare da kwaikwayon
yadda ta yi magna ya ce "o'o ba zan sauke ki
ba".
Sannan ya k'ara wullata sama ya cafe, har da
'yar k'ararta alama ta tsorata.
Dai_dai lokacin Nadeeya ta shigo idonta ya
sauka kan su, wani tarin bak'in ciki da tsananin
kishi ne ya lullu6e mata zuciya, cike da tsiwa da
masifa ta fara magana...
Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪49
©MRS SAIF
"Amma wallahi an yi girman ka wai yanzu kai
ko kunya ba ka ji, ka biye mata ko shakkar wani
ya shigo ya sameku haka ba ka yi ,kalli kayan
jikinta sai ka ce wata tsohuwar ashawo da haka
ai... Farouq ya yi saurin katseta ta hanyar d'aga
mata hannu sannan ya dire Fateema ya fara
magana daga gani shima ransa ya 6aci da
Kalaman na ta.
"wai ke make damunki komai abin k'orofi ne a
wurinki, daga yau duk abinda kika gani na ki ido
ne, idan ba za ki iya ba ki bar wurin that's all,
and then ina kika je na ga kin fito daga waje"??
Nadeeya da haushi ya cikata tun fara
maganarsa ta kasa cewa uffan don taikaci, illah
harare-harare da take yi.
"uhmm say something bakinki yana motsi kin
kasa magana".
Wurga masa harara ta yi ta k'ara tsuke bakinta,
don yadda take jin zuciyarta na tafasa kamar ta
zabga masa mari ta tabbatar idan har ta furta
wata kalma dole ta kasance masa mai d'aci, so
ya fi kawai ta kama bakinta ta yi shiru".
"Nadeeya ki na ji ina miki magna kin wa mutane
shiru".
Can k'asa-k'asan murya ta ce "mak'ota na je".
"ban hana ki zuwa ko ina ba sai kin tambaye
ni"??
Banza ta masa kamar ba ta ji shi ba.
Ganin haka yasa Fateema mik'a hannu d
zummar ta d'aukan Ansar ta yi gaba, don ba ta
so Nadeeya ta ga kamar ta tsaya Jin abinda ke
tsakaninsu.
Ai kuwa tana mik'a hannu Nadeeya ta doke
hannun tare da fad'in "munafurcinki ya tsaya iya
gun ubansa kar ki sake ki kuma ra6ar mun yaro
idan ban da rashin zuciya irin naki ki yi ta cusa
kanki in da ba za'a kar6eki ba,wannan ai shine
cusa kai ba kwarjini".
Fateema ba ta ce da ita k'ala ba illa nufar
shashinta da ta yi, ta bar ta da Farouq suna
cigaba da fafatawa.
*******8 months later
Haka rayuwa ta cigaba da gara musu, Nadeeya
kwata - kwata ta k'i fuskantar Fateema komai
ta yi haushinta take ji, amma ita kanta ta san
Fateema ta yi mata fincikau ta ko ina
musamman a zuciyar Farouq.
Amma abin mamaki duk ranar da Fateema ke
girki kowa na gidan murna yake yi, har Nadeeyar
saboda sun san ranar za su kwashi girki mai
dad'i, ranar girkin Nadeeya kuwa sai dai a bawa
almajirai, zuwa yanzu kuwa Farouq ya saba da
abincin Fateema ta yanda duk inda ya je ya
dawo sai ya zo gida zai ci abinci, tun Nadeeya
na mita har ta gaji ta hak'ura don komai dare
idan ya kasa cin abincin da Nadeeya ta dafa
ranar girkinta zai tashi Teema ta dafa masa
wani, a dole Nadeeya ta hak'ura da hakan tunda
ita ba zata iya yi masa kalar wanda ya ke so
ba, don yana da kadara irin Fateema ba zai rik'a
bin gidajen cin abinci ba.
Sai dai girman kan da Nadeeya ta dorawa kan
ta, ta kasa sauke shi duk yanda Fateema ta so
nuna mata hanya sai ta rufe idonta ruf ta k'i bi,
k'arshe sai cin mutunci da zagi ya biyo baya.
Zuwa lokacin Nadeeya na d'auke da ciki na
kusan 6 months, don haka Fateema ta kar6i
girkin gidan gaba d'aya, ga shi lokacin karatu ya
musu zafi don suna second semester 300 level,
amma duk da haka ba ta ta6a nuna gajiyawa
ba, ta tsara ayyukanta dai_dai yanda ba zata
wahala sosai ba.
A lokacin Farouq ba shi da wani buri da ya wuce
ya ga Fatynsa da ciki yanda ya ga tana masifar
son yara,don yana ganin yadda Nadeeya ke
mata wulaqanci akan Ansar tana shanyewa.
Fateema har ta fuskanci hakan sai dai ta
tabbatar komai lokaci ne, sai lokacin da Allah ya
nufeta da samu zata samu duk zumud'inta.
▪BALLAGAZAR MACE ▪50
©Mrs Saif
Sanye take da wata riga peach colour da ratsin
sky blue, rigar armless ce sai wata igiya da ake
zagaye wuya da ita a d'aure da kad'an tsayin
rigar ya rufe cinyoyinta, sai dai ta bud'e daga
k'asa sharp d'in umbrella iya sama ne kawai a
tsuke, k'ananun calba ne akanta wanda suka
zubo har kafad'arta, ta yi kyau har ta gaji.
Sai safa da marwan jera abincin kan dining table
take yi, Farouq ne ya shigo da murmushi d'auke
a fuskarsa ya kar6i trayn hannunta tare da cewa
"haba Fatyna na ce idan ina nan ki rik'a kawo
wani abun ina tayaki, yanzu sai mai za a kuma
d'aukowa ranki ya dad'e"??
Dariya Teema ta yi sosai don yanayin sigar da
yayi maganar ya bata dariya kamar irin d'an
aiken tan nan.
"duka na gama jerawa fa da ma wannan ne na
k'arshe".
"okay".
Zaunar da ita yayi a d'aya daga cikin kujerun d/
table d'in ya d'ago fuskar ta yana kallonta
almost 5mnts bai ce k'ala ba illa ido da yake bin
ta da shi
"Qalby lafiya kuwa"??
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce
"babe I really don't know where to start, don ba
ni da bakin magana, I didn't have words to
express how i feel about yhu, Teemana kin zama
jinin jikina a kowane second da numfashi na ke
fita tare da kaunar ki ne, kin gama siye zuciyata
ta kowane fanni, I really luv yhu so very much,
kin ga yanda kayan nan ya miki kyau kuwa,
you're more than beautiful."
"Thanks " ta fad'a tare da mik'ewa don ta fara
serving nasa kafin fitowar Nadeeya, tana Jin
dad'in yanda Farouq ke yabonta amma ta fison
in suna part d'in ta ko na shi don bata son
masifar Nadeeya.
" me kika dafa mana ne,? Don na ji k'amshi har
ya cika mun ciki kafin na ci".
Murmushi ta yi ta ce
"cous-cous with veggies sai grilled fish da na
maka, don na ga ka kwana biyu ba ka ci
mutumin na ka ba".
Murmushi sosai Farouq ya yi, ya ce
"fatyna shi yasa kike k'ara shiga raina don duk
wani abu da nake so, kin san shi, yanzu kalli
kifin nan kin iya sarrafa shi nau'i kala_kala ba
abinda zan cewa Allah sai dai godiya".
Nadeeya ce ta k'arasa wurin da suke zauna ta
tsaya tare da 6arkewa da wata mahaukaciyar
dariya, don tun d'azu tana tsaya a k'ofar
parlourn tana Jin duk abinda suke fad'a.
Sai da ta yi dariyar ta gama ba wanda ya tanka
ta, sannan ta fara magana "ni kam ku na ba ni
mamaki kullum cikin soyayya kamar kwa had'iye
junanku, amma har yau cikin nan an kasa samu
sai mu da ba' a so muka yi, ai ni wannan
soyayyar ta ku sam bata birgeni ba kyau a ce
zuwa yanzu kina nan da tsohon ciki, kin ga da
kin huta da wannan d'an banza son yaran naki,
amma ina sai soyewar amma har yanzu result
ya k'i fitowa"...
Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: [9/8, 7:20 PM]
Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪52
©MRS SAIF
********Bayan wata Uku********
Fateema na zaune a parlour hannunta rik'e da
wani hausa novel kasancewar suna cikin hutu
kuma zaman haka duk ya isheta, mai suna
Muguwar sakayya, littafin ya tafi da ita sosai
duk da haka lokaci zuwa lokaci takan kalli part
d'in Nadeeya, don ta yi mamakin har zuwa
yanzu k'arfe 2:30 ba ta lek'o waje ba tun daren
jiya.
Ba zato ta jiyo muryar Faty na k'wala sallama,
k'arasowa ta yi cikin parlourn ta ce
"oh! Friendy wai me kike yi haka ina ta sallama
shiru".
Cikin murna Fateema ta rungumeta ta ce "sorry
tawan ban ji ba ne, ya gida ya su Umma"??
" lafiya Lau".
Ta fad'a tare da neman wurin zama.
"wai ni kam yau na ji gidan na ku shiru lafiya "?
Lafiya Lau, su Raleeya na part d'in su Ansar
kuwa kin san yana Dutse, sai dai Mamansa ce
ban ji motsinta ba".
Ta6e baki ta yi ta ce "hmm ita ta sa ni kar ma
ta fito, ni ai Aunty Nadeeya ta gama ba ni
mamaki wai har ni zata rik'a gaba da ni, ko
magana na mata ba ta amsawa".
Fateema ta ce "bari ke dai ai abun na ta sai
addu'a, yanzu ki lek'a ki gaishe ta kin san ta da
d'an banzan k'orofi".
"ba in da zani ni, duk k'orafinta sai dai ta yi ta
gama tunda ai ba zata dake ni ba ko".
"eh amma kin san idan ta gayawa umma za ta
miki fad'a".
"Ai duk Umma ce ke d'aure mata gindi take
abinda ta ga dama". Cewar Faty.
"Yanzu dai don Allah namesake je ki, ki dubata
duka duniyar nawa take kowa ya yi nagari
kansa".
*****
Da k'yar Fateema ta shawo kan ta, ta nufi part
d'in Nadeeyar, sai dai yanayin da ta tarar da
Nadeeyan ya d'aga mata hankali ba ta san
lokacin da ta fito hankali tashe tana kiran
Fateema.
Da gudu suka burma cikin d'akin Nadeeyar,
rud'ewa da Fateema ta yi har ba a magana, don
dukkan su ba wanda ya ta6a ganin yadda ake
labour sai yau, musamman ita Nadeeya ta
wahala ba kad'an ba don duk ta yi wani wujiga-
wujiga numfashinta har wani sama da k'asa
yake yi kamar zai d'auke.
Cikin rashin sanin taikamammen abin yi
Fateema ta fara magana har da 'yar k'wallar
tausayi a fuskarta,"sannu sannu... "abinda ta ke
ta maimaitawa kenan.
Faty ce ta yi dabaran kiran Farouq ta sanar da
shi.
Shima cikin tashin hankali ya bar office ya nufo
gida,yana zuwa ba su tsaya wani abu, suka nufi
asibiti kowa hankalinsa a tashe.
K'arfe 6:39pm Allah cikin hikimarsa ya nufi
Nadeeya da haihuwar ' yar ta kyakkyawar
gaske, ba inda ta baro Farouq dogon hancinsa
ta d'auko da manyan idanunsa sai dai hasken
fatarta na Nadeeya ne,don fara ce sosai don har
tafi Nadeeya fari ko don ita Nadeeyar ta dafe ne
oho!.
Har zuwa lokacin su Fateema na asibitin, suna
zaune a reception sun yi jugum-jugum wata
nurse ta fito da baby ta mik'iwa Farouq tare da
masa congratulations.
K'ok'arin kai hannu yake yi ya Kar6i babyn
amma ina Fateema ta riga shi kai hannu ta
kar6eta, murmushi Farouq ya yi tare da mai da
hannunsa baya yana lek'en fuskar babyn daga
hannun Fateeman.
"wow! Hasbunallah Wani'imal Wakil" Fateema ta
fad'a tare da zaro duka idanunta waje, "friendy
zo ki ga babyn nan don Allah".
Haka Faty ta zo ita ma ta gama santin kyan
babyn Farouq yana kallonsu yana murmushi, a
ransa ya ce "ina ma baby nan ta tsatson
Fateema ta fito da farin cikin da ya ke ciki sai
ya linka wanda yake yi a yanzu sau dubu,don
yasan yanzu wuyarta Nadeeya ta wartsake ba
lallai ta amincewa Fateeman ba ta rik'a ra6ar
babyn ba,don yasan halin ta sarai na son
k'untatawa Fateema ta wannan hanyar, daga
k'arshe ya jadadda godiyarsa ga Allah na
wannan ga garumar kyauta da ya masa.
Mum Twins 😘
[9/8, 7:20 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE
▪53
©MRS SAIF
washe garin ranar da ta haihu aka sallamo
musu daga asibiti, Nadeeya ta warke ras kamar
ba ita ba, ko da ta isa gida ta tarar da 'yan
uwanta sun iso daga dutse.
Duk wanda ya kar6i babyn sai ya ya ba da
kyawun da ta ke da shi.
Fateema dai tsakaninta da baby sai hange daga
nesa don yadda Nadeeya ta fuskanci tana son
yarinyar yasa duk wata hanya da zai sa babyn
ta kai hannun Fateema ta datse, k'iri-k'iri idan
ta zo d'aukan ta za ta ce bacci take yi, ko kuma
yunwa take ji da dai sauran dalilai, idan ma fa
da idon jama'a a wurin take mata wannan
kawaicin, idan kuwa ba kowa sai dai ta ce ba za
ta ba ta ita ba idan ta yi zuciya ta haifi ta ta.
Farouq ya sha yi mata fad'a akan hakan, yana
nuna mata duk wanda ya ce yana son naka ya
gama maka komai sai dai hausawa sun ce
"wanda ya yi nisa ba ya Jin kira". Don kuwa
Nadeeya ko a gefen gyalenta.
A wani bangare na zuciyarsa yana mamakin son
yara irin na Fateema, ya ci ace zuwa yanzu ta
yi watsi da shiga shirgin yaran Nadeeya amma
ina wata rana har kuka take masa ya d'auko
mata baby ta gani,a dole ya ke zuwa ya
d'aukota don shi kansa babyn ta shiga ransa
fiye ma da Ansar.
Sai dai k'aunar da take nunawa yaran, ba
k'aramin rura wutar soyayyarta a zuciyarsa yake
yi saboda ko banza yaran jininsa ne kuma duk
wanda ya so yaransa dole ya k'auna ce shi bare
kuma Fateemansa.
****
Yau ya kama kwana bakwai cif da zuwan baby
duniya, saboda haka tun asubar fari aka fara
hidima don daga ganin alama taro za a yi ba na
wasa ba.
K'arfe biyun rana gidan ya cika taf da jama'a
'yan taron suna, mai jego da baby an sha kyau,
Fateema ma ta yi kyau sosai abun ta kamar
sabuwar amarya, sai kai da kawo take yi don
ganin komai ya tafi dai_dai duk da' yan uwan
Nadeeyar sun cika gidan da dangin su Farouq
amma duk da haka bai sa Fateema ta zauna ba.
Wasu mata ne suka shigo su biyu yanzu, bayan
sun shiga wurin maijego sun mata barka, sai aka
mik'o musu baby d'aya ta ce
"babyn TubarakallAllah! Me ye sunan ta ne "??
Sai ko wace ta mik'o musu babyn ta ce" ni
inama na san sunanta na zo sai kwasar sinasir
na ke yi amma ban San sunan 'ya ba, barin in
tambayo muku".
A haka ta rik'a bin jama'a tana ratsawa tana
wucewa kuma duk wanda ta ga ni sai ta
tambaya ya sunan baby ya ce "Ai bai sa ni ba".
Tun tana ganin abun kamar wasa har kuma ta
fara mamaki, daga k'arshe ta dangana da wurin
maijego.
"Nadeeya wai ya sunan baby kowa na tambaya
sai ya ce bai sa ni ba".
Jim ta yi alamun tunani, ganin kowa ya zuba
mata ido yana jiran amsa, yasa cikin takaici ta
ce "ni kai na ban San sunanta ba".
Gaba d'aya d'akin suka d'au salati.
Wata tsohuwa dake gefe ta ce "garin yaya haka
ta faru 'yar nan"??
Yak'e ta yi ta ce" sha'afa na yi har maigidan ya
fita ban tambaya ba".
Waya ta d'auka ta kira Farouq, yana d'agawa ta
ce "wai an sawa yarinyar nan suna kuwa ga
jama'a nan sai tambayan sunan baby suke yi,
ko ka manta ne ba ka rad'a mata suna ba"??
Ya ce" suna ai tun ranar da ta zo duniya na
rad'a mata ke ce dai ba ki nemi sani ba".
"meye sunan"??
Nadeeya ta tambaya cike da Jin haushin
maganarsa.
"FATEEMA" Farouq ya fad'a kaitsaye ba tare da
shakka ba.
Wata irin zabura Nadeeya ta yi tare da lailayo
wata ashar ta danna, wadda ta yi sanaddiyar
jawo hankalin duk wanda ke d'akin.
Tuni Faruk ya kashe wayarsa don dama ya san
za a yi haka, sai dai duk abinda zata yi sai dai
ta yi ba zai ta6a chanza k'udirinsa ba.
Nan da nan Nadeeya ta fita daga hayyacinta sai
maganganu take yi "ba zan ta6a yarda a saka
mata sunan wadda na fi tsana a gaba d'aya
duniyar nan ba, dole a sauya sunan nan ko da
hakan zai yi sanaddiyar bari na duniya, ba zan
taba lamuntar 'ya ta amsa sunan FATEEMA ba
muddun ina numfashi...
Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪51
©MRS SAIF
Farouq ne ya d'aga kan sa ya kalleta cike da
mamakin kalamanta don sautari idan ta yi
magana sai ya ji maganarta ta kamar ta marasa
ilimi, sai da ya kur6i sanyayyen lemon pineapple
& yoghurt ice da Fateema ta had'a ya ce
"tunda an gaya miki ni ke ba da haihuwar ba, ko
kuma ke da kika samu k'arfin ki ne ya baki".
Ta6e baki ta yi ta ce
"Ai na tabbatar da ba kai ke bayarwa ba, don da
kai ke bada haihuwa da ba wannan cikin a
jikina, don nasan ba k'aunata ka ke yi ba, sai
dai ka bawa wacce kullum ka ke so ka ke kuma
riritawa".
Ta k'arasa maganar muryarta na rawa alamar
kuka na son taho mata.
"Ya ILLAH!", Ya fad'a tare da mikewa zuwa inda
Nadeeya ke zaune, kujerar dake fuskantarta ya
ja ya zauna sannan ya fara magana
"duk lokacin da kika furta irin wad'annan
kalaman sai ki saka zuciyata cikin tararrabin
anya kuwa ina adalci a takaninku"??
"Duk da na gama amincewa zuciyata da ina
adalcin tsakininku don wallahi Allah ne shaidana
ba ni da burin danne hakkinki duk abinda ya
rataya a wuya ina k'ok'arin saukewa kamar
yadda na ke wa Fateema ko da kuwa hakan zai
yi sanadiyar rasa farin cikina."
Ajiyar numfashi ya yi sannan ya cigaba da cewa
"sai dai kin manta abu d'aya, domin hadisin
Annabi Muhammad (S.A.W) yace
"An halicce zuciya da son mai kyautata mata."
Saboda haka ba zan iya hana zuciyata k'aunar
Fateema ba, don kuwa ita ta yi k'ok'arin gina
soyyatar a cikin zuciyata ginin da ba abinda zai
iya rusa shi, saboda da haka ki yi k'ok'arin gina
naki 6angaren ke ma, ba wai ki zauna kina
haukan kishi akanta ba, da za ki yiwa kan ki
fad'a da kin gyara halayenki, ki ga in akwai
wanda zai kuma Jin kanmu".
Wani mugun tsaki ta ja tare da cewa
"kai kullum maganarka na gyara halayena me na
ke yi wanda ba shi da kyau".
Zuba mata ido yi yana nazarin maganar ta
sannan ya ce abubuwa da dama wanda in zan
fara k'irgo sai mun ci dogon lokaci ba mu gama
ba, yanzu ki kalli dogon tsakin da kika mun a
matsayina na mijinki, don Allah ki na ganin
Fateema na yi mun ko makamancin haka??
Me yasa ba za ki kwaikwayi kyawawan
halayenta ba, domin ki ci ribar zama da ita".
A zafafe ta mik'e tsaye har tana bige d'an
cikinta da ya fara fitowa ta ce
"ba zan ta6a kwaikwayonta ba, domin ni ban ga
abin kwaikwayo a gareta ba, ka ma raina mun
hankali yarinyar ta zo bayan bayana sannan don
komawa baya na zo ina kwaikwayonta, ba zai
ta6a yiyuwa ba, don da na kwaikwayi abinda
take yi gwanda mu mutu a yanda muke".
Sannan ta juyawa wurin da Fateema ke zaune
tun d'azu tana bin su da ido ta ce "ke kuma mu
zuba ni da ke shege ka fasa, sai ki wani zubowa
mutane ido kamar na mujiya kina kallon mutane
ba za ki ce komai ba, wai ke ga ki saliha, bacin
na tabbatar ba haka abun yake a zuciyarki ba,
Allah kad'ai yasan mugun abun da ki ke
shiryawa to ni dai na fi k'arfinki komai ki ke yi
sai dai ya koma kanki.....
*******
Daga haka ba ta kuma cewa k'ala ba ta nufi
part d'in ta.
Fateema da ke zaune sai juya spoon d'in
hannunta take yi ta kasa k'ara kai ko loma
d'aya bakinta, ba ta san sanda ta ji wani
hawayena bin kuncinta ba, don takaicin Kalaman
Nadeeya.
Ya salam! Farouq ya fad'a tare da janyota zuwa
jikinsa, "Fatyna why are you crying, ba dai
maganar Nadeeya ne yasa ki kuka ba"??
Ba ta yi magana ba illa sautin kukanta da ta
k'ara.
Sosai Farouq ya shiga damuwa ganin ta k'i yin
shiru.
" please stop crying babe, kukan ki ba k'aramin
ta6a mun zuciya ya ke yi ba, in dai don ta
maganan Nadeeya ne ki share ba wani abu ba
ne idan kika yi la'akari da yanayin da take ciki".
Still ba ta yi shiru ba sai dai ta rage sautin
kukan, "don Allah ki yi hak'uri ki share
hawayenki Teemana ki yi mata uzuri ko don
cikin dake jikinta, kin sa fa ko shi yana iya sa ta
yawan masifa, ina yabonki Fateema fili da
bad'ini kyawawan halayenki suna burgeni ba
don ke Nadeeya ta samu a matsayin kishiya ba
da ta gane kuskuranta, da ko wannan abun da
take yi baza ta yi ba, ina rok'onki alfama ki
cigaba da hak'uri da ita sakamakonki sai a
wurin Allah don ko ni ba ni da abinda zan saka
miki da shi, sai dai ba zan gushe ina nema miki
ki rahmar ubangiji ba, Allah ya miki albarka ya
kuma nuna min lokacin da zan d'auki babyn ki
da hannuna, huh!! ranar ban san inda zan tsoma
kai na ba don farin ciki ga Fatyna d'auke da
gudan jinina, musamman baby girl kyakkyawa
like yhu".
Fateema ba ta san lokacin da ta saki wata
dariya ba tare da rufe idonta ita a dole ta ji
kunya.
Sai kuwa Farouq ya d'aga cak ya sa6ata a
kafad'arsa ya nufi part d'in sa yana cewa ba dai
kunya ki ke ji ba bari mu je sai na sauke miki
ita".
Ita kuwa sai wutsil-wutsil take da k'afa tana
dariya kamar za ta fad'o ,sai dai Farouq ya
rik'eta tamau a dole ta hak'ura ta ce "ni kam
Qalby ka mai da ni kamar 'yar tsana d'aukana
kwata-kwata baya ma wahala".
Murmushi ya yi ya ce kamar ko kin sani don
idan na d'auke ji nake kamar na d'auki baby
sabuwar haihuwa".
Dai_dai lokacin Nadeeya ta saki labulen parlourn
ta don ganin sun wuce ba suma lura da k'urar
da ta kwasota ba, zuciyarta cike da k'una ta
shige cikin d'aki.....
Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪54
©Mrs Saif
Nan da nan wurin ya hargitse da hayaniyar
jama'a sakamakon gaya musu da Nadeeya ta yi
yanda suka yi da Farouq, daga masu cewa ba
kyauta ba sai masu cewa ai ba wani abu ba ne,
saboda ba sunan kishiyarta za ta duba mai
asalin sunan shi ne abun duba.
Nadeeya duk ba ta ma fiskantar mai suke cewa
daga k'arshe ta fito daga d'akin ta nufi part d'in
Fateema sai dai wayam ba ta nan, don kuwa
tun lokacin da Faty ta zo suka fita don dama ta
gayawa Farouq za ta lek'a bikin wata k'awarsu
da ake yi.
Haka dai taron suna ya watse ba wani armashi,
sai 'yan tsirarin dangin Nadeeya da ba su tafi
ba, sai jibi.
K'arfe 8:10pm Farouq ne ke driving Fateema na
gefensa don tunda suka yi dare ya ce su yi
zaman su idan ya gama abinda yake yi zai zo
ya d'aukesu sun baro sultan road kenan
Fateema ta juya tana kallon Farouq ta ce
"ni kam wai ya sunan baby ne sai fa da muka
fito Faty ke tambayana, na ce ban sa ni ba,
kamar mu koma mu tambayo kawai kuma sai
muka share don ba kowa ya ga fitar mu ba".
"Faty da ke baya ta ce wallahi fa, sai ka ce an
shafewa kowa tunanin tambayar sunan".
Murmushi Farouq ya yi ya ce sunan Ku d'aya ai,
Fateema".
A tare suka zaro ido alamun mamaki, Fateema
ta ce
"what a pleasant surprise, wai da gaske ka ke yi
Qalby"??
"sosai kuwa da gaske na ke".
Faty ta saki wata dariya mugunta tare da cewa
"lallai ka ce Aunty Nadeeya za ta sha poison ta
mutu don bak'in ciki".
Murmushi Fateema ta yi tare da cewa
"huh! Thanks sooo much babe da Namesake da
ka yi mana, we really appreciate".
Faty ta kar6e "millions thanks to you bros, duk
da ba mu da bakin godiya".
"my pleasure darlings, kun zarce haka a wurina,
ina masifar son sunan dama can ina da ra'ayin
sa ma 'ya ta Fateema".
***********
Tun kafin ya yi parking ya ke jiyo ihun yarinya
kamar za ta tsaga gidan, a hanzarce ya yi
parking ya fito ko kulle matar bai yi ba, Fateema
ce ta tsaya kullewa, sannan ta shiga cikin gidan.
Wata k'anwar Nadeeya ce rik'e da babyn dama
daga ita sai wata gwaggon su Nadeeya suka
rage, yarinyar sai kuka take yi, buduwar da ke
rik'e da ita sai jijigata take yi ta k'i yin shiru.
Nadeeya na gefe sai cika take tana batsewa ko
kallon in da suke ba ta yi.
Yana shigowa kaitsaye part d'in Nadeeya ya yi,
yana shiga ya ci Karo da su, hannu ya sa ya
karbi babyn yana cewa "ina mamanta ta je take
wannan kukan ha.....
Ba k'arasa rufe baki ba ya hango Nadeeyan
" wai mai ya faru yarinya na kuka irin haka kin
k'yaleta"??
Shiru ta masa, sai k'anwarta ce ta ce
"tun d'azu yarinyar ke kuka tana Jin yunwa,
amma ta k'i kar6anta ba irin bakin da ba a bata
ba amma ta k'i bawa yarinyar abincinta". Ta
k'arasa maganar tana kallon gefan da Nadeeya
ke zaune.
Mum Twins 😘
▪BALLAGAZAR MACE ▪55
©MRS SAIF
Kallonta Farouq ya yi ya ce
"akan wani dalili ne ki ka yanke mata wannan
hukuncin"??
A tsawace ta ce
"akan sunan da ka saka mata muddun ba ka
cire mata wannan sunan ba sai dai kai ka
shayar da ita, ko kuma ita wadda ka sa sunan
na ta ta shayar da ita".
Ran Farouq in ya yi dubu ya 6aci cikin zafin rai
ya ce "yanzu me ye na ta a ciki da za ki d'auki
alhakinta har haka an ya Nadeeya ki na da
hankali??
To tun muna cike da juna ki kar6i yarinyar nan
ki ba ta abincinta".
Ya k'arasa maganar tare da d'ora mata yarinyar
a cinyarta, zunbur ta mik'e ba don Allah ya sa
Farouq ya yi zafin naman kai hannu ya tare
yarinyar ba da tuni ta sha k'asa.
Rungume yarinyar ya yi tsam a k'irjinsa sannan
ya d'aga hannu ya zabgawa Nadeeya wani uban
mari har sau biyu gefen hagu da dama har sai
da Nadeeya ta ga wasu stars sun gilma ta
idanunta.
Cikin k'unan rai ya fara magana
"sai yau na tabbatar da rashin hankalinki ko na
ce rashin imani to kin yi kad'an ki wulak'anta
mun 'ya a gabana, kina tunanin sai da ke za ta
rayu ki rubuta ki ajiye ba ke ba ita har abada
zan kai wa wacce kika ce akaiwa ina da
tabbacin za ta rik'eta da amana kuma cikin
kulawa fiye da ke kanki da kika haifeta, a gurinki
idan ban da k'azanta da munanan halaye mai
zata koya, tsayuwata anan ji nake kamar amai
zai taho mun idan ban da k'arni ba abinda ke
tashi, ana miki kawaici ana rangonta miki
saboda wasu dalilai amma ba ki san haka ba,
gani ki ke kamar tsoron ki ake yi, to daga yau
na shata layi duk irin rayuwar da ta kama ita
zan yi da ke a cikin gidan nan, baby kuma ko ki
na so ko ba kya so sai ta amsa sunan FATEEMA
sai ki shirya barin duniya ko ki had'iye zuciya ki
mutu don bak'in ciki".
Daga haka bai kuma cewa komai ba ya fice
daga d'akin, kaitsaye wurin Fateema ya nufa bai
rufe mata komai ba ya gaya mata duk abinda ya
faru.
Fateema tuni tausayin yarinyar ya kamata har
da hawayenta a ce baby kamar wannan rabonta
da abinci tun bayan Azahar kai gaskiya Nadeeya
ba ta da imani akan wata hujjar banza ta yiwa
'yar cikinta haka.
Kai dubansa ya yi ga babyn da wahala ta sakata
baccin dole ya ce
"ina ga fateema zuwa kawai za ki yi mu je
asibiti mu nemi shawarar doctors akan yanda ya
kamata a kula da ita musamman ta 6angaren
abinda za ta ci".
Fateema da ke rungume da little Teema ta ce
"sosai nima tunanin da na ke yi kenan".
A cikin daren nan suka nufi PREMIER
kasancewar akwai wani Dr. abokin Farouq da ke
aiki acan, ba su fita ba sai da ya sanar da shi a
waya.
Ba su sha wahala ba suna zuwa ya had'a su da
wata consultant a pediatric Dr Amisha, da yake
matar akwai kirki ta yi musu bayani dalla - dalla
yanda za su kula da babyn daga k'arshe ta ce
su gwada ba ta madara NAN1 insha Allah za a
dace ta kar6eta amma sai dai su rik'a ba ta
ruwa akai-akai,suka yi mata godiya suka fito.
Nadeeya kuwa tun fitar Farouq ta durk'ushe
tana wani irin kuka da na kasa tantace na me
ye, ba abinda yake mata yawo a k'wak'walwa
irin kalamansa, ta ji ciwon Kalamansa ba kad'an
ba, sai dai ta saka a zuciyarta ba ita ba yarinyar
har abada kamar yadda ya ce, gidansa ma za ta
bi duk hanyar da za ta bi ta bar masa kayansa
kawai don tana shakkar mamansu ne da ba
abinda zai hana ta barin gidan a yau d'in nan
.....
Hehehe! masu cewa Fateema ta yi yawa a buk
d'in nan, ku yi hak'uri saboda I dedicated this
buk to all my namesakes (FATEEMA'S) so fagen
namu ne sai sorry akwai wasu ma anan gaba
lol.
Asma'u (Husna), Aysha & Hafsat Birum, kun san
ina son sunayenku cox akwai sunan my mum &
my elder sister a ciki so duka sunayen suna da
daraja a wurin, da duk wani sunan d'an musulmi
mai asali ina alfahari da shi wallahi.
Sai mun had'u a happy Sallah idan Allah ya nufe
mu da gani ❤👌🏻
Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: [9/17, 5:17 PM]
Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪60
©MRS SAIF
THREE MONTHS LATER
Har zuwa lokacin Nadeeya ba ta samu tudun
dafawa ba, duk abubuwa sun cakud'e mata, ta
rasa me ke mata dad'i cikin fad'in duniyar nan,
yanzu har Mamanta ba ta jindad'in yadda ta ke
mata, don ita ma yanzu goyon bayan Farouq
take 100%.
Tana ji tana gani Farouq ya siya musu motoci
masu masifar kyau ita da Fateema, amma
Mama ta ce "ya siyar da tata ya aiko mata da
kud'in ta ajiye har sai lokacin da ta yi hankali
sannan a koma siya mata wata".
Da yake yanzu Farouq sun had'a business
tsakaninsa da abokinsa Abbas suka bud'e
k'aton wurin sayar da motoci, dama shi Abbas
sana'arsa kenan, sai dai yanzu da suka had'a
hannu da Farouq Allah ya k'ara sawa wurin
albarka don a 'yan watannin da suka yi suna
kasuwancin ba k'aramar riba suka samu ba.
Juyi ta kuma yi don tuna yadda Fateema ke
hawa tata motar hankali kwance, da
kyaututtukan da take samu wurin abokan harkar
Farouq duk ta sanadin Fatyma (Basma), a' yan
kwanakin nan kawai an yiwa yarinyar kyautan
English gold, ya kai guda uku, kuma duk sun
mata yawa sai ajiyewa Fateema ke yi,kud'i kam
ba a maganarsa don kullum cikin su Fateema
take,ba ya ga kayayyakin da Farouq ke siya
mata, don komai ya samu yarinyar.
Runtse idonta ta yi sosai tana Jin wani ciwo na
shiga cikin k'irjinta wanda ke zarcewa har
zuciyarta, da yanzu 'yar ta na hannunta duk
wani alkhairi ita zata samu, ba wanda zai bi ta
kan Fateema, amma yanzu komai za a yi a
gidan in dai ta 6angaren Farouq ne Fateema ce
kan gaba kowa ma ya fi saninta, don sai a yi
bak'i a gidan su zo har su tafi ba su san da
wata k'urar Nadeeya ba.
Wata zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta ce
"dole na d'auki mataki akan yarinyar nan ba zai
yiwu ta zo a bayan-bayana ta k'wace gida
ba,duk da zuwa yanzu na gane akwai abubuwan
da dama da na yi watsi da su tun farko, wanda
hakan shi ya bata damar samun matsayin da
take kai".
Ta k'arasa maganar tare da Jan wata doguwar
k'wafa, don har yanzu ba ta wani tunanin gyara
halinta, don gani take idan har ta chanza
halayenta tamkar ta fad'o ne, don za a rik'a
ganin kamar ta kwaikwayi Teema ne, ita kuma
girman kan ta, ba zai bar ta ta yi haka ba.
*****
Fateema ce sak'ale da Basma a kafad'arta sun
shirya tsaf da su, sun yi kyau har sun gaji, baby
Basma ta k'ara girma abinta don yanzu tana da
six months, ta daina shan madara frisogold take
sha, ya kar6eta sosai wayonta har ya wuce
watannin ta, don tuni ta fara rarrafe har kama
abu take ta mik'e tsaye.
Rik'e take da handbag da key d'in mota da
alama fita za su yi, suna daf da fita parlourn ita
da Habi don idan zata je school tare take zuwa
da ita, ta rik'e mata Basma har ta gama
lectures sannan su dawo gida.
Mum Twins 😘
[9/17, 5:18 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪61
©Mrs Saif
Suka ci karo da wasu 'yan mata su biyu, cikin
fara'a Fateema ke musu sannu da zuwa duk da
ba ta gane su ba, ko na ce bata san su ba.
Fuska suma' yan matan suka saki suna amsa
gaisuwar ta.
Ganin haka yasa Fateema komawa zuwa cikin
parlourn suma suka bi bayanta, sai da suka
zauna sannan ta k'walawa Raleeya kira don ta
kawo musu abin ta6awa.
D'aya daga cikin su ce ta fara magana " An ya
kuwa ba mu yi 6atan kai ba"?
Kallonta Fateema ta yi cikin rashin fahimtar
maganar ta ce" kamar ya, wani guri kuke nema
ne"??
"eh, gidan wata Nadeeya nan aka kwatanta
mana aka ce gidanta yake sai dai kuma yanzu
na ke tunanin, kamar ba nan ba ne".
Murmushi Fateema ta yi, ta ce
"ba batan da kuka yi nan ne, Raleeya je ki kira
musu Maman Ansar".
"to,"Raleeya ta fad'a tare da nufan part d'in
Nadeeya.
Kallonsu Fateema ta yi ta ce "bari na tafi dama
school zan je, ku gaida gida".
Da fara'a d'auke a fuskarsu suka ce "yawwa
mun gode".
"ba komai". Fateema ta fad'a tare da nufar
hanyar fita.
Su kuma suka bi ta da ido cike da sha'awar
babyn hannunta.
"lalalalala! Su zee na ke gani yau, ko dai kun yi
6atan kai ne"???
Nadeeya ce ke fad'an haka bayan ta fito.
Harara suka watsa mata ta wasa, sannan suka
ce
"bayan mu kad'ai ke neman ki, ke ba neman mu
kike to ba, ko sanin tashin ku fa ba mu yi ba,
sannan idan mun kira wayarki ba ma samu, sai
da muka je unguwar ku ta da sannan wata
makociyarki ta mana kwatancen nan".
"hhhhmm! Ku dai tashin bana dad'i ba shi yasa
ba wanda ma ya sa ni sai na jiki sosai".
"to me ya faru?, mu tambayoyi ne nan fal cikin
mu, lokacin da za mu shigo mun ga wasu
flowers masu masifar kyau ina ga kamar 'ya da
uwane su waye halan".
Nadeeya da ba ta fuskanci mai suke nufi ba ta
ce
"flowers kuma, ban gane me kuke nufi ba"?
Dariya suka kwashe da ita sannan suka ce
"wata fa kyakkyawa muka gani zata fita yanzun
nan tare da wata kyakkyawar baby a hannunta".
"mtss, wacce ku ka gani ba kowa ba ce sai
kishiyata, babyn hannunta kuma da take fashion
da ita ba kowa ba ce illa 'ya ta da na haifeta da
ciki na...
Mum Twins 😘
[9/17, 5:19 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪62
©Mrs Saif
Dariya suka bushe da ita, suna mata kallon ko
kin fara shaye - shaye ne.
Cikin takaici Nadeeya ta kalle su ta ce
"wai wannan dariyar ta miye ko ba ku yarda da
abinda na ce ba ne"??
Gyad'a kai suka yi alamar eh.
Hannunsu Nadeeya ta kama tare da fad'in "ku
zo mu je part d'ina na fayyace muku duk abinda
ya faru".
Ba musu suka bi ta, sai dai shigarsu part d'in ta
shi ya tabbatar musu da hali na nan ba abinda
ya sauya,don sai suka fi jindad'in zaman su a
parlourn da suka fara zama akan na Nadeeyar,
amma ba halin komawa dole su hak'ura su
zauna tunda suna son Jin k'wak'waf.
****
Nadeeya ba ta rage musu komai ba dangane da
abinda ya faru, duk ta kwashe ta gaya musu,
cikin ta'ajibi suke jinjina kai.
Zee ta ce
"tunda dai haka ne nima na watsar da makamai
na, na hak'ura da k'udurina, don na tabbatar da
ba nasara saboda ko lokacin da ya ke tare da
BALLAGAZAR MACE bai amincewa buk'ata ta
ba, bare kuma yanzu da ya samu MACE irin
Fateema".
Cikin rashin fatimar inda maganar Zee ta dosa
Nadeeya ta fara magana
"ni fa kin sa ni a duhu gwanda ki fitar da ni, don
ban fahimce ki ba".
Sai da zee ta d'an muskuta sannan ta ce
"yanzu a tsakanin mu ba wani 6oye-6oye zan
gaya miki gaskiyar abinda ya faru, a da na so
mijinki dan kuwa har tallan kaina na kai masa,
sai dai sam ya nuna bana gabansa, ba irin
bibiyar da ban masa ba amma ya wulak'anta ni
amma duk da haka ban hak'ura ba, don yanzu
haka zuwan da na yi don na d'ora in da na
tsaya ne, sai dai labarin da kika ba ni yasa na
zubar da makamaina na hak'ura da shi, zan
kuma ba ki shawarar da ta dace, wata kila Allah
sai ya ga zuciyata ya sauya mun da mafi
alkhairi gare".
Wani kallo Nadeeya ke watsa mata tun fara
maganarta, wanda na kasa tantace na meye.
"hmm! Ke na ke saurare fad'i shawarar ta ki ".
" gaskiya Nadeeya zan gaya miki lokaci ya yi da
zaki daina wannan bak'ar k'azantar ta ki, da
rashin ta idon da kike yiwa Farouq, ki gyara
halinki ki daina wannan ballagazanci, ki rungumi
abokiyar zamanki ku yi zaman Amana don daga
ganinta za ta yi dad'in zama, ki kuma kai
gwiwoyinki k'asa ki nemi afuwar mijinki, na san
ba zai... Nadeeya ta katseta ta hanyar d'aga
mata hannu.
"ki mun shiru zainab, wato kin gama yawon
dandin ki, za ki zo ki ce za ki mun wa'azi, ai ke
ba ki da darajar da zan tsaya na saurareki, bin
mazan ki ya kai har wurin mijina, sai dai ki ga ni
ki k'yale don kuwa Farouq ya yi k'arfinki, shi
yasa sai fama kuke da hanya kun k'i
auruwa.......
A zafafe zainab ta katseta "ke dabba ke ga ni
kike yi har macece,?? Barin in gaya miki kin ci
darajar kishiyarki ne, don na fuskanci ita
cikakkiyar MACE ce, amma in dai don irin ki ne
kwace miji a wurin ku ba wani abu mai wahala
ba ne, ni shawara ce na ba ki idan ki ga dama ki
d'auka idan ba ki ga dama ba, ki watsar ".
Daga haka ba ta kuma cewa k'ala ba, ta ja
hannun k'awarta suka fice.
Kan kujera Nadeeya ta zube tana mai da
numfashi, a ranta take cewar
" me yasa ne kowa ya d'ebo shararsa ya ke
watsa mun ne, me na yi wa mutane ne haka".
Rashin mai ba ta amsa yasa ta fashe da wani
irin kuka, wanda na kasa tantace ma'anarsa......
Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: [9/20, 9:26 PM]
Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪63
©Mrs Saif
Haka rayuwa ta cigaba da gudana a gidan
Farouq yayin da Fateema da 'yar ta ke cikin
nutsuwa da kwanciyar hankali, don ba su da
wata damuwa, idan ban da Fateema da ke fama
da kasala da yawan barci a' yan kwanakin nan.
A 6angaren Nadeeya kuwa sam abun ba haka
yake ba, don yanzu ta rasa natsuwarta gaba
d'aya, muradin ta bai wuce ta ga 'yarta ta dawo
hannunta ba, don wata irin k'aunar yarinyar take
yi, wadda yanzu tana ji a zuciyarta ko da za' a
kirata da Fateema za ta amince, burinta kawai a
bata 'yar ta.
Sai dai tun bayan zuwan su Zee gidan take
neman ta yadda za ta 6ullowa lamarin amma ta
kasa samun mafita ga shi lokaci sai tafiya ya
ke, tunda har an ci wata uku da zuwan su,
amma har yau shiru mak'atau, wai an aiki bawa
garinsu.
"Fateema! Fateema!!", Farouq ne ke tashin
Fateema tare da girgiza k'afarta, don ta tashi
daga nauyayyan barcin da take yi tun safe.
Da k'yar ta iya bud'e idonta ta ce "don Allah
Farouq ka bar ni na yi barcin nan ka ji".
Murmushi ya sakar mata, ya ce "haba babe, ke
ma kin san ba don na san kina da test 11 ba, ba
abinda zai sa na tasheki ko da kuwa za ki
kwana ki na barcin nan".
Ai da sauri Fateema ta diro daga kan gadon
tana mutsutstsike idonta, ta ce
"ni ba na manta ba".
Murmushin dai Farouq ya kuma yi sannan ya ce
" shi yasa na had'a miki breakfast, na kuma
yiwa Basma wankan, don na rage miki aiki, sai
ki yi sauri ki shirya, ki k'arasa shiryawa Basma
sai na fara ajiyeki a school sannan na wuce
office don yanzu gaskiya kin daina driving har
sai mun je asibiti na ji dalilin wannan barcin,
gudun kar ki je ki na driving barci ya kwasheki,
ki je ki kaini ki baro ni."
Hararar wasa Fateema ta watsa masa tare da
cewa "haba sai ka ce wadda tsetsefly ya ciza".
Dariya ya yi sosai tare da mik'ar da ita tsaye,
"don Allah yi sauri ki shiga wanka kafin nima na
makara da yawa".
A cikin mintunan da ba su gaza talatin ba ta
shirya ta shiryawa Basma cikin wata doguwar
riga fara k'al sai ratsin red flowers a jikin rigar,
twisting ne akanta ya yi kyau sosai, don idan ka
gani sai ka rantse ba gashinta ba ne attach.ne
domin ya sauko sosai kamar ba gashin 'yar
9mnths ba.
Abinda ya ke k'ara bawa kowa mamaki da
yarinyar saurin iya tafiyarta, don yanzu haka
tafiya take sosai, kamar wadda ta bawa shekara
baya....
Mum Twins 😘
[9/20, 9:26 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪64
©Mrs Saif
Fitar su ke da wuya Nadeeya da ke la6e tana
kallonsu, ta yi wuf ta fito daga ma6uyarta, ta
fara wani tsallen murna har da rawa, ta d'auki
tsawon lokaci tana rawar har da juyi
kasancewar ba kowa a gidan, don su Raleeya
sun je ganin gida, Ansar kam ya zama d'an
dutse don bai fiye zama a wurin Nadeeya ba.
Sai da ta yi mai isar sannan ta nufi part d'in ta,
cikin sauri ta janyo wani trolley ta fara loda
kaya a ciki, sai da ta zuba duk abinda ta ke
buk'ata, sannan ta saka hijabinta ta yo waje
jaye da trolleyn.
Fateema kuwa tunda suka fito gabanta ke
fad'uwa, dama tun jiya ta yi wani mafarki mai
ban tsoro wanda ta kasa gayawa kowa, sai
yanzu da gabanta ya tsananta fad'uwa take
gayawa Farouq.
Juyawa ya yi yana Kallonta cikin kulawa ya ce
"Fatyna ki cigaba da addu'a duk da na san kina
yi, idan Allah ya yarda ba koma sai alkhairi".
"to, ni dama addu'a na bai wuce Allah ya k'ara
tsare mun ita ba, don idan wani abu ya same ta
ban san ya rayuwata za ta kasance ba". Ta
k'arasa maganar tare da gangarowar hawaye
daga idanunta.
"Ya Salam, Teema mai yasa kuka wallahi bana
son kukanki ko na second, ki yi hak'uri ki yi
shiru Insha Allah ba abinda zai faru da ita kin ji
Fatyna". Ya k'arasa maganar cikin sigar
rarrashi.
*****
Daidai lokacin su ka k'arasowa gate d'in BUK,
bayan ya ajiyeta daidai faculty d'in su, ta fito ta
zagaya bayan motar tana k'ok'arin fiddo Basma
da ke bayan... Farouq ya ce "haba Fateema ina
kuma za ki je da ita bayan kin san kwanan
wurin Umma ki ke kai ta in dai za ki zo school
kasancewar su Habi ba sa nan".
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce
"Ni kam yau da ita zan je, don bana son barin ta
a wani wuri".
K'uri ya yi yana kallonta don yau ya fuskanci
tana cikin wani yanayi.
Cikin tattausan lafazi ya fara magana
"Babe ki yi hak'uri, ki bar ta na kai ta gun
Umma kin ga test ne kawai za ki yi, don haka
kina gamawa ki yi kirana zan zo na d'auke ki
sai mu je mu d'aukota na wuce da ku gida, kin
ga yanzu idan kin je da ita da wane za ki ji ga
ta ga test ga ki ke kanki ba ishasshiyar lafiya
ba, don Allah ki yi hak'uri kin ji Fatyna".
Da k'yar dai Farouq ya shawo kanta, ta amince,
amma har ta shige hall d'in tana jiyowa tana
kallon Basma.
Mum Twins
[9/20, 9:26 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪65
©Mrs Saif
Nadeeya na fita ba ta zarce ko ina ba sai gidan
su Farouq, tun daga gate ta bawa mai gadi
ajiyar trolley'n ta, ta ce "ya ajiye mata yanzu za
ta fito ba ta son ta yi ta gayansa".
Ba tare da komai a ransa ba ya kar6a ya ajiye
mata, tunda yasan wace ita a gidan.
Ko da ta shiga Basma na cinyar Umma tana
mata wasa, da yake har ta saba da ita 'yan
kwanakin nan.
Cikin mamaki Umma ta fara magana
"yau ke ce a gidan na mu Nadeeya"?
Cikin kunya Nadeeya ta ce "eh Umma".
Don ba za ta iya tuna dogon lokacin da ta
d'auka ba ta je gaishe da Umman ba.
Umma ba ta nuna mata komai ba, ko a fuskarta,
don haka suka cigaba da hirarsu kamar yadda
suka saba a lokutan baya.
Har agogon dake manne da bangon parlourn ya
buga k'arfe d'aya dai_dai, adaidai wannan
lokacin ne masallacin da ke jikin gidan suka fara
kiran Azahar, saboda haka ne Umma ta mik'e ta
ce
"barin je na yi sallah".
Murmushi Nadeeya ta yi cike da zumud'i ta ce
"to Umma sai kin fito kawota na rik'e miki har
ki fito".
Kallonta Umma ta yi sosai sannan ta ce
"ke fa ba sallar za ki yi ba"?
Cikin Jin kunya ta ce "a'a ba yi zan ba".
Kamar Umma kar ta mik'a mata ita sai kuma ta
ba ta, ta ce "Ai ni ma ba dadewa zan yi ba
yanzu zan fito".
Tana shigewa d'aki Nadeeya ta bi bayanta da
harara, sai da ta tabbatar ta fara Jin k'arar
ruwa alamun an shiga toilet sannan ta fito a
sukwane d'auke da Basma, lokacin mai gadi
yana masallaci shi ma, don haka trolley'n ta
kawai ta ja ta fice daga gidan.
*******
Kaitsaye adaidaita sahu ta tara straight Kano
line ta nufa don shiga mota, don ta k'udurce a
ranta sai ta kar6i 'yar ta shi yasa ta dad'e tana
shirya wannan ranar sai yau burinta ya cika, don
ta sawa ranta ba za ta nufi Dutse ba, domin
Mama ba za ta goyi bayanta ba, Kazaure za ta
nufa gidan wani Baffanta kasancewar ba zuwa
wurin sa suke yi ba, ba wanda zai kawo tana
can, sai dai ita za ta rik'a neman su a waya
idan har sun amince mata ta rik'e 'yar ta sai ta
dawo, idan ba su amince ba kuwa har court ta
iya kai su , don yadda take Jin Basma a ranta
yanzu za ta iya asarar komai domin ta.
Ba su k'arasa tasha ba, ta ga wata mota k'irar
Gulf a gefen hanya ana lodi, ga dukkan alamu
hanyar su za ta yi ga shi ta kusa cika, saboda
haka ta sa d'an sahu ya ajiyeta anan.
Illai kuwa mutum biyun gidan gaba suke nema,
nan da nan Nadeeya ta biya kud'in ta shige
gaba, kafin k'yaftawar ido sun chilla kan titi
kamar walk'iya haka drivern ke gudu, Nadeeya
sai murna ta ke yi ta samu abinda ta ke so don
bata son su ja wani dogon lokaci har a biyo
sawunta.
Gudu ya ke ba na wasa ba nan da nan suka gan
su a D'anbatta, sai dai me?? kafin su shiga cikin
garin D'anbattar motar ta k'wacewa drivern da
ya zo shan kwana saboda tsananin gudun da
yake yi, haka motar ta rik'a sama da k'asa tana
lolli da su, kafin daga bisani k'ofar da ke gefen
su Nadeeya ta bud'e, ba ta an karaba, Basma
da ke hannunta ta su6uce ta fad'a saboda
k'arfin iskar da ke fizgar su, cikin tashi hankali
Nadeeya ta saki wani razanannen ihu da
zummar fad'awa ta d'auko Basma da k'arfi
wani mutum ya sa hannu ya janyota, idan ban
da salati ba abinda ake yi a cikin motar, cikin
taimakon Allah motar ta tsaya da gudu Nadeeya
ta fito kamar mahaukaciya tana neman Basma,
hango ta yi a hannun wani mutum da gudu da
k'arasa in da ya ke tsaye, sai dai sau d'aya ta
kalli yarinyar ta kau da ganta tare da fashewa
da wani kid'imammen kuka, gaba d'aya kayan
jikin yarinyar ya koma Jan jini, don duk ga6o6in
jikinta zuba yake da jini duk da ka na ganinta
ka san ba ta da rai, kusan duk mutanen da ke
wurin hawaye suke yi baya ga masu kuka
wiwi.....
Innalillahi Wa'inna'ilaihirraji'un! (ni kai na
maman Twins hawaye ya hana ni typing ku biyo
ni zuwa gobe don Jin yadda za ta kaya)..........
Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: [9/21, 7:17 PM]
Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪66
©Mrs Saif
Nan da nan aka kira police ba da jimawa ba aka
kwashesu don zuwa asibiti domin da yawan
mutanen da ke ciki sun d'an samu raunuka,
Nadeeya ma ta samu tarkad'e a hannu lokacin
da take k'ok'arin fita d'auko Basma, jawowar da
aka mata da k'arfi ya yi sanadiyyar samun
tarkad'enta.
Cikin garin Kano aka dawo da su direct AKTH
aka wuce da su 6angaren A&E, Doctors da yawa
suka yo kan su musamman Basma sai dai
gwajin farko ya nuna musu yarinyar ba ta da rai,
ban da wani azababben kuka ba abinda
Nadeeya ke yi don gaba d'aya ta kid'eme,
tunani take yi ina ma a mafarki ta ke ganin
wannan abun da ke faruwa da tafi kowa murna
a wannan duniyar,sai dai ina zuwa lokacin da
likita ya tabbatar mata da mutuwar Basma ta
tabbatar da ba mafarki ba ne a zahiri komai ke
faruwa.
Fateema na rubuta test amma sam ta kasa
nutsuwa kaf hankalinta ya kasa kwanciya, a
gurguje ta gama rubuta test d'in ta yi
submitting ta fito, ko tsayawa jiran Faty ba ta yi
ba,hatta Farouq da ya ce ta kira shi idan ta
gama ba ta bi ta kansa ba ta nemi keke napep
ta hau sai gidan su Farouq.
Umma kuwa bayan ta idar da sallah ta fito
zuwa parlour in da ta bar Nadeeya da Basma a
zaune, sai dai wayam ba kowa, sai ta d'auka ko
ta shiga toilet nan ma dai shiru, daga baya take
tunanin ko da toilet ta shiga ya kamata ta ga
Basma tunda ba da ita zata shiga ba.
Wasa - wasa sai da Umma ta duba ko'ina cikin
gidan ba alamar su Nadeeya, ba shiri ta nufi
bakin gate.
"Iro! Iro!! "
Umma ke k'wala kiran maigadi a hargitse ya fito
daga cikin d'akinsa dake daf da k'ofar gate d'in
gidan.
" na'am Hajiya, Allah ya sa lafiya".
"ina fa lafiya, ka ga Nadeeya ta fita d'azu"??
Umma ta fad'a tana haki kamar wadda ta yi
gudu.
"A'a ban ga fitar ta ba, don akwatin da ta ba ni
ajiya ma ina masallaci ta d'auki abin ta, don ko
da na dawo ban ganshi ba, ina ma shirin zuwa
yanzu na tambayi ko ta d'auka ne, domin na
tabbatar gudun samun matsala sai ga ki kin
fito".
Salati Umma ta saki tare da tafa hannu,sannan
ta ce
"wato har da akwati ta zo?".
kafin Iro ya bata amsa suka ji tsayuwar d'an
sahu a waje, ba d'auki wani dogon lokaci ba
Fateema ta kunno kai cikin gidan.
Yanayin da Fateema ta tarar da su Umma ne ya
sa gabanta mummunan fad'uwa, da k'yar ta
k'arasa ciki.
Cikin nauyin baki ta ce
"Um...Umma lafiya na gan ku a tsaye anan kun
yi jugum-jugum"??
Kasa magana Umma ta yi illa hannun Fateema
da ta kama suka shiga ciki...
[9/21, 7:17 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪67
©Mrs Saif
Anan Umma ta juyewa Fateema duk abinda ya
faru, tuni hawaye ya wanke ma Fateema fuska
tana fad'in
"shi kenan na rasa Basmana, ni na san na
rasata ba zan kuma ganin kyakkyawar fusk.....
Sai kuma kuka ya ci k'arfinta ta kasa k'arasa
maganar.
Rungumeta Umma ta yi, cikin sigar rarrashi ta
fara magana "ki yi hak'uri Fateema, gudun
Nadeeya ba zai rage ki da komai ba don kuwa
dole ta dawo, domin duk in da za ta je na san
ba zai wuce Dutse ba, don haka wannan ba
wata babbar matsala ba ce, yanzu zan kira
Farouq sai a san yadda za a 6ullowa lamarin".
Ba a d'auki dogon lokaci ba Farouq ya iso
sakamakon kiransa da Umma ta yi zuwa lokacin
ita ma Faty ta dawo nan da nan Umma ta fad'a
musu abinda ke faruwa, idan Farouq ransa ya yi
dubu to duk sun 6aci, ba tare da 6ata lokaci ba
ya yanke shawarar bin bayan su Nadeeya.
Saboda haka Umma ta ce
"a tafi har da ita, tunda ba su San yadda za ta
kaya ba idan an je can ba".
Fateema da Faty suka ce suma za su je, adole
dai aka shirya tafiyar dukan su.
******
Suna daf da shiga mota wayar Farouq ta hau
ringing alamar call ya shigo, hannu yasa ya
d'auko wayar duk da bai san number ba haka ya
d'aga.
A d'ayan 6angaren wanda ya kira shi ya ce
"don Allah da Farouq na ke magna?".
Da sauri Farouq ya ce "eh".
"okay, idan ba damuwa ka zo Aminu Kano
yanzu 6angaren A&E".
Cikin rashin k'warin jiki Farouq ya ce
"me zan zo na yi Accident and Emergency
kuma"??
Mutumin ya ce
"ba wani abun tashin hankali ba ne, matarka ce
suka d'an samu matsala a hanya, amma ka
kwantar da hankalinka ga ta ma ku yi magana".
Bai jira abinda Farouq zai ce ba ya mik'awa
Nadeeya wayar, duk da muryar ta ba ta fita
sosai sakamakon kukan da ta ci, amma hakan
bai hana shi tambayar Basma ba tunda ya ji
tata lafiyar, kukan da ta 6arke da shi yasa ya
katse wayar a gurguje ya yiwa su Umma bayani,
sannan suka shiga mota don zuwa asibitin,
kowa zuciyarsa cunkushe da damuwa barin
Fateema idan ban da kuka ba abinda take yi.
Innalillahi Wa'inna'ilaihirraji'un kawai suke
maimaitawa sakamakon ganin gawar Basma da
suka yi, gaba d'aya kuka suke yi har Umma idan
ka cire Farouq da Nadeeya don ita Nadeeya ta
yi kukan har idonta ya bushe sai na zuciya
kuma, shi kuma Farouq hawayen ma ya kasa yi,
sai tafasa da zuciyarsa ke yi tamkar za ta huda
k'irjinsa ta fito, idonsa ya yi ja jajur addu'a yake
yi Allah ya sa ya samu ko da d'igon hawaye ne
ya fito daga idonsa ko ya samu ragin rad'ad'in
da ya ke ji a zuciyarsa.
Fateema ce ta yi kukan kura ta cafko wuyan
Nadeeya ta fara magana cikin ficewar hankali
"tunda kika kasheta nima sai na kasheki, kowa
ya huta sai da na gayawa Farouq kasheta za ki
yi ya ce mun ba haka ba wai mafarki ne, ai ga
shi nan ya faru a zahiri".
Sosai Fateema ta shak'e wuyan Nadeeya tana
wasu suratai tamkar ta6a66iya kuma duk cikin
gunshek'ar kuka.
Jin Nadeeya ta fara wani kakari yasa Umma da
Faty suka ruga kansu dan jaye hannun Fateema
daga wuyan Nadeeya, da k'yar da taimakon
wasu Nurses guda biyu suka 6an6are hannun
Fateema daga wuyan Nadeeya.
Wani kuka Nadeeya ta saki wanda daga Jin fitar
kukan ka san yana tattare da nadama da tarin
bak'in ciki, cikin kukan ta fara magana
"Umma na cuci kaina na yiwa kaina gi6in da ba
zai ta6a cikewa ba a rayuta, na yi nadama na yi
danasani marar misaltuwa, da kun bar Fateema
ta k'arasa ni da na fi farin ciki, don na san zan
huta da wannan azababben rad'ad'in da
zuciyata ke mun... Don Allah Fateema ki
kasheni... Ki kasheni na huta kin ji.... Sai kuma
ta zube a wurin tana wani irin kuka tare da fitar
wani wahallallen numfashi kad'an-kad'an.
Da sauri Nurses d'in dake gurin suka yi kanta
don ganin numfashinta na k'ok'arin d'aukewa,
ashe ba su sa ni ba ita ma Fateema tuni ta
suma anan, don tun lokacin da aka 6an6are
Nadeeya daga hannunta, ta ji wani mugun jiri na
d'ibanta wanda ya hana ta aiwatar da komai illa
zubewa da ta yi anan.
Cikin tashin hankali aka bawa Nadeeya gado
kafin daga bisani aka bawa Fateema na ta
gadon, kuka kam kala_kala ba wanda Umma da
Faty ba su yi ba.
Faruk kam rasa duniyar da yake ya yi, don wani
irin juyawa kan sa ke yi, wanda bai ta6a Jin irin
sa ba a rayuwarsa, da k'yar ya sa hannu ya
dafe bangon wurin tare da lumshe ido, tuni
hawayen da yake muradin zuwansu, suka wanke
masa fuska......
Mum Twins 😘
[10/16, 4:46 PM] mrm kd: [9/22, 10:47 PM]
Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪68
©Mrs Saif
A dole aka yi wa dangin Nadeeya waya aka
sanarda su halin da ake ciki, haka ma Fateema
sai waya aka yiwa su Ummy aka sanarda su
Fateema ba lafiya tana kwance a asibiti, ba su
d'auki dogon lokaci ba suka iso hankali a tashe,
daidai wannan lokacin ne aka ba da gawar
Basma don yi mata jana'iza kamar yadda addini
ya tanadar.
Bayan kwana uku da mutuwar Basma aka
sallamo su Fateema daga asibiti, zuwa lokacin
Fateema ta dangana don likita ya tabbatar mata
tana d'auke da juna biyu, saboda haka ya ba ta
shawarar ta rage yawan damuwa don samun
ingatacciyar lafiyarta tare da ta d'an da ke
cikinta.
Kaitsaye gida Ummy ta wuce da Fateema don ta
samu kulawa sosai tunda har yanzu jikin na ta
da saura.
Nadeeya ma tun ranar da abun ya faru,
Mamansu ta iso, ranta ba k'aramin 6aci ya yi
ba, akan abinda Nadeeya ta yi, fad'a sosai ta yi
mata, don ma Umma na ta ba ta baki.
Ta ce "duk da Nadeeya ce sila amma Allah ya
riga ya k'addaro hakan sai ya faru, don haka
babu tsimi babu dabara".
Har kawo yau da aka ba su sallama, Maman ba
ta wani saki ranta ba, sai haushin Nadeeya ta
ke ji.
Sam Nadeeya ba ta Jin ciwon abinda Maman
take mata don ita kanta haushin kanta take ji,
duk ta wani rame ta rafke lokaci guda kamar
wadda ta shekara tana cuta.
******
Zaune suke sun yi jugum-jugum, kowa da
abinda yake sak'awa a ransa, tun d'azu da aka
ba su sallama suke jiran Farouq ya zo ya biya
kud'i su san tudun dafawa.
"ni kam Farouq ina ya je har zuwa yanzu bai
k'araso ba"?? Umma ce ke wannan maganar
bayan ta duba lokaci a agogon wayar da ke
hannunta.
Murmushi Mama ta yi ta ce
"Halimatu kenan kin san fa yau akwai sabga a
gabansa tunda yau ne uku, da yawan mutane
sai yau za su zo masa gaisuwa".
Umma ta ce
"haka ne amma na ga su Fateema sun tafi tun
d'azu".
Kafin Mama ta ce wani abu suka jiyo sallamar
Farouq daga bakin k'ofa.
Bayan ya shigo ya gaishe da su Umma, Mama
ta dad'a masa gaisuwa, sannan ya kalli Umma
ya ce
"Umma don Allah ki yi mun gafara ki yafe mun,
don na yanke wani hukuncin da na san ba zai
miki dad'i ba, amma ni hakan shi zai samar
mun da nutsuwa, don duk lokacin da na ganta
zan na tunawa da abinda ya faru da Basma ta
sanadinta".
"Farouq wai me ka ke son ka ce ne?,ka fayyace
mun manufarka don ban fahimci bayanin ka ba".
Hannu ya sa a aljihu ya ciro wata farar takarda
mai d'auke da rubutu ya mik'awa Nadeeya.
Jiki na rawa ta kar6a ta bud'e ta fara
karantawa abinda ke ciki kamar haka :Ni Farouq
na SAKI matata Nadeeya saki d'aya kamar
yadda shari'ah ta ba ni dama, idan ta samu miji
ta yi aure.....
[9/22, 10:47 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪69
©Mrs Saif
Kukan da Nadeeya ta saki shi ya dawo da
hankulan su Umma kanta, da sauri Umma ta
kar6i takardar ta karanta, cikin razana ta yi kan
Farouq idonunta cike da 6acin rai.
Da hanzari Mama ta sha gabanta tana fad'in
"wai me ya faru"??.
" sakinta fa ya yi, bayan ban ba shi umurnin yin
haka ba".
Murmushin takaici Mama ta saki ta ce
"akan wannan ki ke tada jijiyoyin wuya?, ki ma
daina damun kan ki, domin abinda Farouq ya yi,
yayi dai_dai sakamakonta kenan, dama ta dad'e
tana neman sakin,
sai ta kai dubanta zuwa inda Nadeeya ke zaune
ta cigaba da fad'in yau burinki ya cika sai ki
d'ebi kayanki mu tafi".
Sosai Umma ta nuna damuwarta sai dai Maman
Nadeeya tana ta nuna mata ba wata matsala
har zuciyarta ta ga dacewar abinda Farouq ya yi
don hakan da ya yi zai sa Nadeeyar ta k'ara
koyon darasi akan rayuwa.,, duk da zuwa yanzu
ta fahimci Nadeeyan na cikin tsananin nadama
tare da datasani akan abubuwan da ta akaita,
amma wannan ba zai zama hujjar da za ta
nema mata afuwa ba gun Farouq, gwanda ta
barta ta d'and'ani d'acin zawarci ta ji yadda ya
ke, domin ko nan gaba idan ta yi wani auren ya
zamar mata Izina.
Haka suka tattara yanasu - yanasu suka wuce
tasha don zuwa Dutse.
Sai da Farouq ya je ya biya kud'ad'en da ake bi
, sannan ya d'auki Umma a mota don maidata
gida, a hanya ban da fad'a ba abinda Umma ke
yi, shi dai Farouq ba shi da bakin magana, sai
hak'uri ya ke ba ta don dama yasan dole za a yi
haka, da k'yar ya shawo kanta ta daina mita,
har ya d'an samu ta saki ranta kafin ya tafi.
Ko da ya koma gidansa sai ya ga gidan ya
masa tangameme, ba ka Jin motsin kowa, nan
da nan kewar mutanen gidan ta cika shi,
saukowa ya yi daga saman sa ya bud'e side
d'in Fateema ya shiga, yana shiga parlourn
manyan toys d'in Basma tare da sauran
tarkacen kayan wasanta suka yi masa welcome,
wanda ko shi ko Fateema ke siya mata, wanda
da yawa daga cikin kayan sun fi k'arfin
watanninta.
Teddy d'aya ya d'auka ya rungume, sai ya ke ji
kamar Basman sa ya rungume tuni mutuwarta
ta dawo masa sabuwa fil, bai yi aune ba ya ji
hawaye na bin kumatunsa, a fili ya ce
"ba zan iya rashin dukanku ba, Fateema ki yi
hak'uri ki dawo gareni nima zan kula da ke
kamar yadda Ummy za ta yi, tabbas idan na
cigaba da zama ni d'aya na tabbatar da ciwon
rashinku zai mun mummmunan kamu....
Mum Twins 😘
[10/16, 4:47 PM] mrm kd: [9/23, 9:53 PM]
Phatyma: ▪BALLAGAZAR MACE ▪70
©Mrs Saif
Kuka sosai Farouq ya ke yana sambatu shi
kad'ai har sai da ya fara Jin kansa na wani
mugun sarawa sannan ya rarrashi kansa ya yi
shiru, ya fi k'arfin 30mnts zaune a wurin daga
k'arshe ya ga zaman na shi damuwa kawai ya
ke k'ara masa saboda haka ya zari key d'in
motarsa ya fita da zummar zuwa gidansu
Fateema.
Ko da ya isa gidan Fateema ta yi barci, sai
Ummy ya tarar, bayan sun gaisa ya ke sanarda
ita buk'atarsa na son a maida masa da matarsa,
don yana tsananin buk'atarta a kusa da shi.
Guri Ummy ta nema ta zauna sannan ta ce
"Farouq ka yi hak'uri Fateema ta d'an k'ara
warwarewa ka san har yanzu akwai damuwa a
tare da ita,tana buk'atar kulawa ta musamman,
zamanta anan ina kyautata zaton zai taimaka
mata wurin saurin mantawa da mutuwar Basma,
ka yi hak'uri har a kwana biyu sai a dawo maka
da ita, tunda ga Nadeeya.
Girgiza kai ya yi sannan ya ce
"Ummy mun rabu da Nadeeya".
"Subhannallah! Ummy ta fad'a cikin mamaki.
"Ai da ba ka saketa ba, komai ai muk'addari
ne,dama haka Allah ya tsara bai mai nisan
kwana ba ce yarinyar".
Farouq dai bai ce komai ba illa bin ummy da ido,
don shi kad'ai yasan irin halin da yake ciki a
yanzu.
Shiru ita ma Ummy ta yi tana nazari domin duk
wanda ya ga Farouq dole ya tausaya masa
musamman yanzu da ta ji sun rabu da Nadeeya
ta tabbatar shima yana da buk'atar mai
rarrashinsa, amma kuma idan ta amince masa
Fateema ta koma a yanda take gaskiya akwai
matsala don a yarda take aiki ko na kitchen ne
ba kamata ta yi ba don cikin jikinta bai yi k'wari
ba, ga shi likita ya ja musu kunne sosai akan
kula da yanayin motsinta don ana son ta samu
hutu sosai, don Allah ne ya kiyaye ba ta samu
miscarriage ba,don haka gaba d'aya kan Ummy
ya kulle ta ma rasa mai za ta ce da Farouq.
Kamar ya san abinda ta ke tunani ya ce
"Ummy kar ki sawa kan ki damuwa wallahi zan
kula da Fateema sosai, duk wani abu da ya
kamata a yi mata zan yi kokarin yi, kuma ba zan
bar ta ta yi ko wane irin aiki ba, sannan zan kira
Faty ta dawo gidan da zama har zuwa lokacin
da za ta warware, zan kuma yiwa Umma
magana ta tuntu6i su Raleeya idan ba yanzu za
su dawo ba, a nemi wasu kawai".
Ajiyar zuciya Ummy ta sauke ta ce
"shi kenan ba matsala sai ta koma, amma sai
zuwa gobe tunda ka ga yanzu ta yi barci".
Murmushi Farouq ya yi ya ce
"ba komai na gode Allah ya k'ara girma".
Har ya mik'e da zummar tafiya, Ummy ta ce
"Amma Farouq kafin ta dawo ka yi k'ok'arin
kwashe duk wani kaya da ya shafi Basma a
wurin da za ta iya gani, za ka iya kai su ko part
d'in Nadeeya ne ka kulle".
"okay, to Ummy dama nima na yi wannan
tunanin, insha Allah zan yi yadda kika ce".
Yana gab da fitowa daga parlourn, Abbansu
Nadeeya ya dawo tare da yayyanta guda biyu,
anan ya tsaya suka gaisa tare da k'ara masa
gaisuwa, sannan ya fito daga gidan...
[9/23, 9:53 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪71
Kwanaki na k'ara shud'ewa lokaci na tafiya,
cikin Fateema yanzu har ya kai wata bakwai
zuwa lokacin sun rubuta final exams d'in su,
don haka yanzu ba su da wani lokaci da ya
wuce na rainon cikinta, kullum Farouq na
mak'ale da ita, idan har yana nan baya barin
Fateema yin komai, da zarar za ta yi wani aiki
zai kar6e ya ce shi zai yi ita ta zauna ta huta,
ba yanda ta iya dole ta hak'ura ta bar masa ya
yi.
Fateema ce zaune a parlourn Farouq akan rug
ta mik'e k'afarta Farouq na matsa mata k'afar
da ta d'an fara kumbura.
Dariya ya saki sannan ya ce
"babe an ya cikin nan ba 'yan hud'u ne a ciki ba,
na ganshi wata bakwai amma kamar yau za ki
haihu yayi wani k'atoto". Ya k'arasa maganar
yana kwatanta girman cikin da hannunsa.
Pillow ta janyo daga kan kujera ta jefa mishi
cikin sigar wasa ta ce
"wallahi ban ji bakin ka ba, duk son yarana
hud'u sun mun yawa ni kam".
Dariya sosai Farouq ya yi ya ce
"ni dai in har ke za ki haifa mun ko goma ne ina
so".
Dariya itama ta yi ta ce
"ni ban ma ta6a Jin d'an Adam ya haifi yara
goma ba, sai ka ce Tinkiya"
Ai kuwa Farouq Me zai yi idan ban da dariya
haka yai ta dariya Fateema na taya shi.
*****
DUTSE
Nadeeya ce a kitchen ke kiciniyar had'a girkin
rana, don tun safe da ta tashi ba ta zauna ba
ita ta yi share-sharen gidan da goge-goge,
dama tun zuwanta ita Mama ta sakarwa aikin
gidan, da kafin zuwanta yayyen ta ke yi
wad'anda aka sako, to su yanzu Allah ya
tarfawa garinsu nono don kuwa sun samu
mazan aure sun d'aga sun bar Nadeeya.
Ga shi yanzu ba irin da ba ne don komai tsaftsaf
suke yin sa, domin Mama ta d'auki darasi yanzu
ba ta ta6a barin yaro ya zauna haka nan
sasakai musamman Nadeeya da gayya take
sakata ayyuka masu wahala don ta gane
kuskuranta.
Adalilin k'azantar da suka tafka yasa, sai da
suka saida gidan su, suka siye wani a wata
anguwar daban, saboda ba k'aramin tambari
mutanen unguwar suka musu ba, takai ko zuwa
neman auren 'yan gidan ba a yi, saboda
tsegumin da ' yan unguwar ke kaiwa duk wanda
ya fito neman aurensu, daga k'arshe suka yanke
shawarar tashi daga unguwar.
"Mama don Allah khadija ta zo ta k'arasa soya
funkasun nan, bayana har ya k'age ga shi ina
son na je na yi wanka don duk na yi gumi".
Nadeeya ce ke maganar daga cikin kitchen.
"wai sau nawa zan gaya miki sai kin gama aikin
nan tsaf kin wanke kwanikan da aka yi amfani
da su kin share kitchen d'in kin goge sannan ki
yi maganar fitowa, gwanda ma ki yi sauri kafin
lokacin zuwa makarantarki ya yi".
Sai da Nadeeya ta gama aikin nan tsaf ta yi
shirin zuwa makaranta, da yake tana zuwa
makarantar islamiyya mai suna Mar'atussaleh,
ba abinda ba koyarwa ta fuskar addini sannan
ana koyawa mata duk wasu sirrika na mallakar
miji a sauk'ak'e ba boka ba Malam.
Sai a sannan Nadeeya ta fuskanci ta yi babban
kuskure a baya da take tunanin shan maganin
mata ne kawai zai sa miji ya so ka, sai yanzu
ta gane ashe sam abun ba haka ba ne, shi yasa
ta k'udire a ranta duk mijin da ta aura nan gaba
za ta zame masa salihar MACE mai biyyya ga
miji, ta kuma bi duk wasu matakai da ta koya na
siye zuciyarsa miji.
Tunda ta jefa k'afarta cikin gidan ta ji
mayataccen k'amshin turarensa, ko kallon gefen
da yake ba ta yi ba, ta yi hanyar shiga d'akin
su.
Shi ko sai d'ashe baki ya ke yi a dole ya ga
masoyiyarsa.
"Nadeeya! Nadeeya!"Mama ke k'wala mata kira
lokacin da ta hango shigewarta.
[9/23, 9:53 PM] Phatyma: ▪BALLAGAZAR
MACE ▪72
©MRS SAIF
Dawowa ta yi ta tsaya ba tare da ta juya ba
Ta ce "ga ni mama".
"au yanzu wulak'ancin na ki ya kai ki na ganin
mutum ki share shi ki wuce".
"ni fa Mama ban gan shi ba". Nadeeya ta fad'a
tare da d'an turo baki.
"to barin in gaya miki ki shiga hankalinki, idan
ba haka ba zan mugun sa6a ki, a wannan
zamanin 'yan mata ma ya suka cika bare ke
bazawara, don kin samu mashinshini shine har
kike masa wulak'anci, to ahir na san hankalinki
duk yana wurin tsohon mijinki, dama hak'ura
kika yi da shi don na tabbatar zuwa yanzu
Farouq ya manta da wata halitta ki, yana can da
matarsa hankalinsa kwance, ko Ansar watansa
nawa bai zo ya gan shi ba, ki na gani sai dai
kakarsa ta zo duba shi, amma ni ban ga laifinsa
ba, don duk ke ki ka jawo, don bahaushe ya ce
na ji dad'i shine gari ba na saba ba".
Tunda Mama ta sako zancen Farouq Nadeeya ta
fara share hawaye, don yanzu kuka akan Farouq
ya zame mata jiki, ba ta da wani buri a duk
duniyar nan da ya wuce ta kuma auren Farouq a
karo na biyu, sai dai ita kanta ta san ya mata
nisa, nisan da ba za iya tarar da shi ba.
Mama ce ta katse mata tunani ta hanyar fad'in
"yanzu haka maganar sa rana ya zo yi, kuma ni
na ba shi damar gobe ya je gun baffa babba su
yi magana yasso daga baya ya turo wakilansa
kawai a d'aura aure ba wani abu da za a tsaya
jira".
Ai kuwa tuni kukan Nadeeya ya tsananta fiye da
d'azu.
"eh lallai! za ki wuce ki je ki same shi ko
kuwa"?
"to " kawai ta ce, ta shiga d'akin su jaka kawai
ta ajiye ta fito fuskarta duk ta kumbura alamar
ta yi kuka, ta nufi inda bak'on na ta ke zaune.
Ko da ta gama tad'in ba ta kwanta ba sai da ta
wanke tulin kayan wankin Mama sannan ta
kwanta cike da gajiya da tsantsar tunanin
abinda ke shirin faruwa da ita.
Yanzu ba ta da wani buri da ya wuce ta ganta
gidan Farouq a matsayin matarsa, yanda ta ke
Jin kaunar Farouq a yanzu ko rabinta ba ta ji ba
lokacin aurensu, tana matuk'ar son ta koma
auren Farouq a karo na biyu ko don ta gyara
kurakuran da ta yi, sai dai ina har yanzu
zuciyarta ta kasa hasko mata mafita, dole tana
ji tana gani za ta auri mutum da ba son sa ko
d'igo a zuciyarta.
Wani hawaye ta ji yana bin fuskarta wanda ba
ta damu da ta goge ba, Ansar da ke gefenta a
kwance ta rungume tana Jin tsananin k'aunar
mahaifinsa na ratsa ko ina na sassan jikinta.
Ta d'auki tsawon lokaci a haka, kafin daga
bisani ta kwantar da shi, ta d'auro alwala ta
tayar da Nafila, ta dad'e tana jera nafifili sannan
ta yi sallama ta d'aga hannayenta sama cikin
kuka ta fara addu'a.
"Ya Allah, ya mad'aukakin Sarki, ya mai amsa
buk'atun bayinsa ya Allah ka fini kusa da jijiyar
dake wuyana ya Allah ka san na yi nadamar
abun da na aikata ya Allah ka kawo mun mafita
mafi alkhairi, idan har komawa Farouq alkhairi
ne ya Allah ka tabbatar mun, idan ba alkhairi ba
ne ka sauya mun da mafi alkhairi".
Ta shafa addu'ar tare da sakin wani irin kuka
mai ban tausayi...
Mum Twins
[10/16, 5:08 PM] mrm kd: [9/26, 7:24 PM] Mum
Twins : ▪BALLAGAZAR MACE ▪73
©Mrs Saif
Da sauri - sauri ya ke shirin kasancewar ya d'an
makara zuwa office, Fateema da ke zaune a
gefen gadon d'akin tana kallonsa, sai wani
ciccin magani take, yanda ta wani had'e fuska
abun har ya so ya bawa Farouq dariya sai dai
ya daure don kar ya tsokano wa kansa rigima
don yasan k'iris take jira.
Sai da ya gama shirin tsaf, ya juya da kallonsa
gareta ya ce
"Fatyna zan tafi, sai na dawo"?
K'ara tsuke fuska ta yi ta ce
"uhmm".
D'an zaro ido waje Farouq ya yi cikin mamaki
ya ce
"yau ko daddad'ar addu'ar nan ba za a mun ba,
bare kuma rakiya"??
Gyd'a kai ta yi alamar eh.
Murmushi Farouq ya yi ya ce "lallai yau sarautar
ta motsa, tunda haka ne na fasa fitar nima," ya
k'arashe maganar tare da ajiye briefcase d'in
hannunsa ya fad'a kan gadon ya yi lamo kamar
wanda zai yi barci.
Shirun da ta ji ya yi yawa ne yasa ta kai hannu
ta juyowa da fuskarsa, ba barci yake yi ba
amma idonsa a rufe yake, cikin muryar
shagwa6a ta ce
"don Allah ni ka tashi ka tafi aikinka".
Bud'e idonsa ya yi ya d'ora akan fuskarta ya ce
"ba zan je ba har sai kin gaya mun dalilin
wannan fushin".
"Ai ka fi ni sanin dalilin, wata nawa ina binka da
magana d'aya amma ka k'i saurarata".
Ajiyar numfashi ya yi sannan ya ce
"Fateema ki share zancen na dawo da Nadeeya,
kimanta da maganar don ba ya cikin tsarina
gaskiya, haka kurum muna zaman zaman mu ki
jaji6o mana ita ta zo ta wargaza mana jindad'in
rayuwa, ba zan iya ba gaskiya".
"Haba Farouq ka yi hak'uri ka yafe mata tunda
ta yi nadama, ta rok'i afuwa ba sai a mata ba,
Allah ma fa muna masa laifi kuma ya yafe
mana, yawan nacin kirana da take yi ba dad'i
sai ta ga kamar nima bana son ta dawo shi
yasa na k'i mata kokarin shawo kan ka, tun
tana kiranka ka na mata wulak'anci har ta
hak'ura ta dawo kaina, don tabbacin da ta da
shi na zan taimaka mata".
"ke ma yanzu idan ta kiraki ki ce kar ta kuma
kiranki, don na k'i amincewa faqat, kin ga sai
kuma ta nemi wani tunda aikinta kenan bibiyar
dangina".
"gaskiya ni kam ba zan iya cewa kar ta kuma
kirana ba, ai sai ta ga kamar na mata
wulakanci".
"Okay, amma don Allah ni ko ta k'ara kiranki kar
ki kuma gaya mun don bana son maganarta
kwata_kwata don tuni na rufe shafinta a cikin
rayuwata".
"Amma ai..... Farouq ya saurin katseta ta
hanyar d'ora hannunsa akan lips d'in ta ya ce
"shhhhhhh! Babe yaushe ki ka fara musu ne?
Bana son maganar nan abarta haka."
"alright, yanzu tashi mu je na rakaka domin
lokaci sai tafiya ya ke".
Murmushi ya yi ya ce
"ko kefa, dama na san maganar duk ta k'arfin
hali ce kike don dai Farouq na Fateema ne ita
kad'ai".
Dariya Teema ta yi sosai don ko Farouq ya
harbo jirginta, a ranta ta ce
"dama wa zai so kishiya sai dai idan ta zame
ma dole ba yanda za ka yi".....
Mum Twins
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR
MACE ▪74
©Mrs Saif
Three weeks later
******
Zuwa lokacin Nadeeya ta zama abin tausayi,
don duk ta fige ta lalace, don ciwo take yi ba na
wasa ba, kuma ba abinda ya yi sanadinsa irin
damuwa da tunani, don bikinta da Alh Sani
saura sati biyu kacal, tun Mama na shareta har
ta fara tausayinta, kun san tsakanin d'a da
mahaifi, sai dai ta san ciwon Nadeeyar ba na
komai ba ne illa na son Farouq, kuma ga shi ta
yi rantsuwa ba za ta kuma shiga maganar
aurenta da Farouq ba.
Wasa - wasa ciwo har sai da ya kai ta da
kwanciya asibiti,a lokacin gaba d'aya ta saduda
da rayuwar kira kawai take a kira mata Farouq
ta nemi afuwarsa kafin ta mutu.
Sosai Mama ta shiga damuwa ba shiri ta kira
Umma a waya ta sanarda ita duk halin da ake
ciki.
*******
Don haka ne yau tunda safe Umma ta kira
Farouq ta ce "idan ya tashi daga aiki ya je tana
nemansa".
Bayan sun gaisa ne Umma ta fara magana
kamar haka
"Farouq ba komai yasa na kira ka ba sai don
maganar Nadeeya, bana son takura maka a karo
na biyu, shi yasa ka ga duk tsawon lokacin nan
ban yi ma maganar ka dawo da ita ba, amma
jiya labarin da na ji akanta abin ya girgiza ni
matuk'ar gaske".
Anan ta kwashe labarin komai ta gaya masa,
sannan ta cigaba da cewa
"don haka na ke nema mata alfarma ka yi
hak'uri ka dawo da ita, ka manta da duk abinda
ya faru a baya, insha Allah dawowarta zai zama
alkhairi gare mu baki d'aya".
Ajiyar zuciya ya sauke tare da fad'in
"Umma ba na tunanin akwai wanda za ki
nemawa alfarma a wurina na kasa yi miki
matuk'ar abin bai fi k'arfina ba, don haka na
amince da auren Nadeeya a karo na biyu Allah
ya sa hakan ya zama alkhairi."
"ameen "
Umma to fad'a cikin jindad'i, sannan ta shafa
kan sa ta ce" Allah ya maka albarka Omar
Farouq, yasa ka samu yara masu maka biyayyya
fiye da yanda ka ke mun".
"ameen, ameen Umma " ya fad'a tare da
mik'ewa tsaye don tafiya.
Cikin d'an k'ank'anin lokaci aka sa tafiya dutse,
da Faruk ya so ya waske ya k'i zuwa Umma ta
ce dole ya je, ba yanda ya iya dole ya ajiye
ayyukansa ya tafi.
Tabbas shi ma ya ga canjin da ake cewa
Nadeeya ta yi, don ta koma wata saliha ga
nutsuwa har wani kunyarsa ta ke ji abun har
mamaki ya bawa Farouq.
Matsala d'aya suka samu ta Alh Sani don ya
tsaya kai da fata ba zai janyewa Farouq ba,
tunda an riga an sa musu rana, da k'yar da
sud'in goshi ya amince ya jaye.
Daga k'arshe aka yanke shawarar sati mai zuwa
za a d'aura aure a yi bikin da ya sawwak'a
amarya ta tare a gidan angonta.
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR
MACE ▪75
©Mrs Saif
Haka aka yi kuwa sati na zagayowa aka d'aura
aure aka sha biki amarya ta tare, daren farkon
su Farouq ya k'ara tabbatar da chanzarwa
Nadeeya, don sam ko alamar warin da take yi
ada bai ji ba,,idan ban da k'amshi dake tashi
daga kowacce ga6a ta jikinta ba abinda ya ke ji,
dama gashi ta samu ingattatun magungunan
mata ta yi amfani da su tsaf ta d'inke abinta
kamar sabuwar budurwa.
Ai kam Farouq ya sha mamaki a daren ranar sai
yake ji kamar wata Nadeeyar ce ta daban aka
kawo masa ba wadda ya sani ada ba.
Washe gari ko da ya tashi sai ya tsinci kan sa
cikin annushuwa, wacce ko a daren farkon auren
su na fari bai yi ba, har Fateema sai da ta
fuskanci haka.
Nan da nan ta ji wani kishin Farouq na
nuk'urk'usarta,kun san an ce
"kishi kumallon mata".
Sai dai da ta yi tunanin duk abinda Nadeeya za
ta yi daga baya ne, don ita ta riga ta wuce
wannan shafin, ta riga ta wa Nadeeya nisa a
zuciyar Farouq, nisan da duk gudunta ba za ta
iya tarar da ita ba, sannan ita ma ai ba zama za
ta yi ba, za ta d'ora ne a inda ta tsaya don ta
riga ta gama sa nin Farouq cike da bai, saboda
da haka hanyoyin mallakarsa a tafin hannunta
suke, don haka me zai sa ta rik'a kishi ma da
Nadeeya da sai yanzu ne take gane waye
Farouq, da wannan tunanin ta watsar da duk
wani abu da shaid'an ke bijiro mata da shi a
zuciyarta.
*******
Zaman su suke yi lafiya Lau cike da fahimtar
juna, domin tuni zaman na su ya sauya salo
idan ka gansu kamar ba kishiyoyi ba, sai ka
rantse da Allah ya da k'anwa ne, ko gidan ka
shigo ba za ka ta6a gane mai girki ba don tare
suke shiga kitchen, musamman yanzu da
Fateema ta yi nauyi haihuwa ko yau ko gobe,
Nadeeya ce ta kar6i girkin gaba d'aya ta ke yi,
sai dai fateema ba ta son zaman kawai ba ta
komai, don haka lokaci zuwa lokaci ta kan shiga
kitchen d'in ta taya Nadeeya aiki koda ba mai
wahala ba, Nadeeya ta yi ta mata mitar ta je ta
zauna ta huta amma ta k'i, a dole take
k'yalleta.
Farouq ne ya dawo daga aiki tunda parlour ya
ke jiyo tashin hirarsu a hankali daga kitchen
murmushi ya yi ya nufi kitchen d'in, dukkan suka
jiyo suna masa sannu da zuwa, cikin fara'a ya
amsa musu.
Fateema da ke zaune tana tsige d'ayan zogole a
wani d'an k'aramin bowl ta yi k'ok'arin mik'ewa
don kar6an ledojin hannunsa da sauri ya zaunar
da ita yana fad'in "oh! Fatina ki zauna abin ki
zan ajiye da kaina, ke kanki kamata ya yi na
rik'a d'aukan ki duk inda za ki je,Allah ina
tausaya miki cikin har ya fi ki girma". Ya
k'arasa maganar tare da kai hannunsa kan
cikin.
Dariya Nadeeya ta yi ta ce
"wallahi fa kamar ba na farin ba". Murmushi
Farouq ya sakar mata ya ce
"Amryata wai me kuke dafa mana ne, na ji gidan
ya d'umame da k'amshi".
"mai cikin gidan nan ce yau ke son dambu, ka
ga kuwa dole na mik'e na dafa shi".
"wow! Gaskiya kin kyauta Amryata kin san nima
na dad'e ban ci dambu ba, musamman dambun
amare akwai dad'i". Ya k'arasa maganar yana
kannewa Nadeeya ido d'aya."
Shiru ta masa ba ta amsa shi ba, ganin haka
yasa Fateema kwashewa da dariya don ta san
abinda yasa Nadeeya yi masa shiru.
"Maman Ansar gwanda fa ki hak'ura da amaryar
nan don kin san yanzu ni ce uwargida sarautar
mata sai sorry". Fateema ta k'arasa maganar
tare da sakin wata dariyar mugunta.
Shi ma Faruk dariyar ya ke mata, don haka
Nadeeya ta ajiye ludayin da ke hannunta ta juyo
garesu ta ce
"Abban Ansar da kai da Teema ina tunanin sai
na kai ku court alk'ali ya mana shari'a da ku
sannan kuma ba ni certificate da zai tabbatar da
ni ce Uwargida a gidan nan, ku kuma a saka
muku hukuncin mai tsauri ga duk wanda ya
k'ara kirana da Amarya".
Farouq da Fateema me za su yi idan ban da
dariya, Teema dariya har da hawaye, tana cikin
dariyar ne ta ji mararta ta wani murd'a, tuni
d'an da ke cikinta ta ji yana mata wani mugun
juyi, dama tunda ta tashi take Jin ciwon mara
kad'an-kad'an sai dai na yanzu yayi tsamari, ba
shiri ta cakumo rigar Farouq tare da
ruk'unk'ume shi tana fad'in "Farouq bayan
marata, washhh"!!!
Cikin tashin hankali Farouq ya d'agata ya
sunkuceta sai cikin mota, Nadeeya kanta ta
shiga rud'ani irin yadda ta ga fateema ta fita
hayyacinta lokaci d'aya.
Cooker gas kawai ta kashe ta fito daga kitchen
d'in da gudu ta yi part d'in ta sako hijabi don
bin su.
Sai dai tana fitowa mai gadi na rufe gate alamar
har sun fice.
Cikin gidan ta koma ta shiga part d'in Fateema
ta had'a mata duk kayan da ake buk'ata kama
daga na ta har na baby kasancewar komai an
siya, don dai Farouq ya rud'e ne shi yasa ba su
tsaya d'auka ba......
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR
MACE ▪76
Kaitsaye labour room aka wuce da Teema, ko da
aka dubata she's almost 8cm ashe a tsattsaye
take labour, Farouq na tsaye yana safa da
marwa wata Midwife ta fito ta ce
"kai ne ka kawo wadda aka shiga da ita yanzu
nan".
Cikin zak'uwa Farouq ya ce
"eh".
Insha Allah muna sa ran haihuwarta nan da
20mnts, don haka sai ka kawo kayanta a shiga
da shi zan turo a kar6a yanzu".
"to " kawai Farouq ya ce don shi sai yanzu ma
ya tuna da zancen kaya. Cikin sauri ya koma
inda yayi parking mota ya figa sai gida.
Yana isa Nadeeya ta gama shiri har kayan ta
fito da shi zuwa main parlourn su, ta zuba
ruwan zafi a teaflask, da kayan tea duk ta had'a
komai na buk'ata.
Ai kuwa Farouq ya ji dad'i kayan kawai aka sa a
booth, Nadeeya ta bawa su Raleeya Ansar ta ce
"su lura da gida kafin ta dawo".
Fifteen minutes later
*****
Fateema ta haifo santaleliyar yarinyarta, sai dai
abun mamakin Jin da ta yi midwives da ke gurin
na cewa ta yi nishi ga wani kan baby nan tafe.
Cikin kid'ama da rud'ewa baki na rawa ta ce
"wai... wai me... kuke nufi da... sai dai wani
azababben ciwo ne ya hana ta k'arasa
maganar, a dole ta saki wani wahalallan nishi
da ya yi sanadin zuwan wata babyn.
Gaba d'aya midwives d'in suka hau ihun murna,
wasu daga cikin su sai addu'a suke Allah ya ba
su yara kamar babies d'in nan, nan da nan aka
gyara yaran, suka fes identical Twins ba k'arya
kyawawa kuma ajin farko.
1st born d'in aka fara mik'owa Fateema, saboda
da kid'emewa sai da fatyma ta silmiyo daga kan
gadon da take kwance, idonta ta k'ara maidawa
kan yarinyar tabbbas ba idonta ke mata gizo ba,
fuskar Basma ce a jikin babyn sak tamkar
Basma na jaririya, tuni hawayen farin ciki da
jindad'i ya zubo a fuskar Fateema, kwantar da
babyn ta yi a gefe sannan ta kai goshinta k'asa
tana mai yin 'sujudu-shshukur' ga Sarki Allah
mai yanda yaso a lokacin da yaso.
Ba ta k'ara girmama al'amarin ba sai da aka
kawo mata 2nd born, ba bambanci a tsakaninsu
kamar kwabo da kwabo Allah ya so an musu
alama da komai k'wak'war mutum ba zai gane
wadda aka riga haihuwa a cikin su ba.
Wani murmushi ne ya su6ucewa Fateema don
tuna. yadda Farouq zai ji yau ga Basman sa har
biyu Allah ya dawo masa da ita.
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR
MACE ▪77
©Mrs Saif
Suna tsaye shi da Nadeeya don ko zama sun
kasa sai gani suka yi an fito da babies biyu an
nufo inda suke, kan Nurses d'in su k'araso har
Farouq ya k'arasa gun su, da sauri ya ce "Allah
dai yasa ta haihu"
Da murmushi d'auke a fuskarsu suka ce
"ta haihu lafiya k'alau ga ma yaranka".
Cikin zaro ido waje Farouq ya ce "yarana??".
"sosai kuwa, don ko matarka ta haifi Twins
duka mata, suka k'arasa maganar tare da mik'a
masa babies d'in lokaci d'aya.
Diriricewa Farouq ya yi ya kalli wannan ya kalli
waccan ya ma rasa wa zai kar6a a ciki, ganin
haka Nadeeya ta mik'a hannu ta kar6i d'aya
cike da tsantsar farin ciki, sai dai fuskar yarinyar
da ta gani sosai ya yi masifar bata al'ajabi don
sak Basma ba maraba da lokacin da take baby.
Tuni son yarinyar ya tsarga zuciyar Nadeeya, ba
ta yi aune ba ta ji hawaye na bin kuncinta don
tunawa da Basman ta da ta yi.
Wohoho! Farouq kam murna kusan zauta shi ta
yi, kar6ar babies d'in ya yi ya had'a su ya
rungume tsam a k'irjinsa, ba abinda ya ke yi da
ya wuce Tasbihi, gaba d'aya kud'in jikinsa sai
da ya rabawa mutanen da ke zaune tsakanin
labour room da postnatal.
Wad'anda suka masa albishir da haihuwar kam
cewa ya yi "su ba shi account number d'in su
zuwa gobe da yardar Allah za su ji alert, haka
suka yi godiya cike da murna suka bar wurin.
Nan da nan Farouq ya fara sanarda 'yan uwa a
waya na ko wane bangare kan ka ce me an cika
asibitin mak'il domin duk wanda ya ji sai ya
cika da mamaki, uwa uba ya zo ya ga babies da
idonsa, tsantsar k'auna kam da kulawa ba
wadda Fateema ba ta gani ba daga kan Farouq
har danginsa, ba a maganar danginta, hatta 'yan
uwan Nadeeya sun mata kara sosai.
RANAR SUNA
*****
Tsayawa fad'in shagalin da aka kwasa ranar
suna 6ata lokaci ne, yara sun ci sunan Fateema
Zahra da Fateema Zuhra.
Tun a daren ranar da suka dawo daga asibiti
Farouq ya ke gayawa Fateema sunan da ya
sakawa yaran.
Cikin mamaki ta ce
"haba Qalby sunan bai yi yawa ba dukan su
Fateema".
Murmushi ya yi tare da cewa
"l like the name, you're more than all the sweet
names in the world."
Murmushin Teema ta mai da masa sannn ta ce
Thanks alots babe really appreciate".
Sai da ya yi pecking babies d'in a goshi sannan
ya yi wa Fateema sai da safe ya ja musu k'ofar
ya fice.
*****
Haka rayuwar su ta cigaba da garawa cikin
kwanciyar hankali ba wani tashin hankali
tsakaninsu kan su a had'e yake tsaf, kun san
Zuhra ma a hannun Nadeeya ta ke, idan ka
ganta a gun Fateema to tabbata ta je cin abinci
ne.
Shi yasa Farouq yanzu ba shi da wata damuwa
kullum cikin nishad'i ya ke, shima yana kokarin
kyautata musu iya kar k'arfinsa don komai ya
samu darlings d'in sa, ba ya nuna wariya
tsakanin su, yana kokarin yin adalci a duka
6angarorin biyu, sai dai so d'aya ne tak, yasan
Fateensa ya ke yiwa shi, sai dai zuwa yanzu
Nadeeya ta zama wani babban jigo daga cikin
rayuwarsa, wanda rashinsa ba k'aramin
barazana ne ga rayuwarsu ba.
One Year later
*****
Yau Twins suke cika shekara d'aya a duniya,
don haka ne Nadeeya ta shirya musu
k'ayataccen birthday party na zallar yara sai
iyayensu, anan dai cikin harabar gidansu za a yi,
an yiwa wurin decoration mai kyau an gyara
gurin sosai, sai k'aton cake da aka ajiye a
tsakiyar wurin da aka k'awata shi fiye da ko ina.
******
4pm wurin ya cika mak'il da jama'a kasancewar
ranar Sunday kusan duk wad'anda aka gayyata
sun samu zuwa, Faty amarya ma (kasancewar
an sa ranar bikinta nan da 3mnths za a yi ita da
masoyinta Naseer) ta zo tun safe da ita ake
hudimar.
Huuuuuuuuh! Twins na hango tare da Mamansu
suna tahowa, yaran kyawawa na bugawa a
jarida sun sha ado cikin wasu dakakkun english
wears riga da skirt pink colour da ratsin silver
color a jiki yaran sun yi matuk'ar kyau ba
kad'an ba, haka Fateema da Nadeeya abun dai
gwanin sha'awa, Farouq ma ba a bar shi a baya
ya cake cikin wani yadi tissue mai matuk'ar
kyau da tsada, tamkar wani sabon ango, duk
wanda ka gani a wurin yana cikin farin ciki.
Gifts kam Twin sun samu ba kad'an ba, don
kyaututtaka na ban mamaki abokan Farouq suka
ba su, duk wanda ka gani a wurin da irin kyautar
da ya ba su....
[9/26, 7:24 PM] Mum Twins : ▪BALLAGAZAR
MACE ▪78
©Mrs Saif
Daga k'arshe Farouq ya rik'e hannun Zahra
Fateema ta rik'e na Zuhra suka d'ora
hannayensu akan wuk'ar yanka cake d'in suka
yanka, nan da nan wurin ya gaure da tafi tare
da wak'ar happy birthday..... Farouq ne ya fara
d'iba ya kaiwa Fateema a baki har ta bud'e
bakin zai sa mata karaf idonta ya had'u da na
Nadeeya da sauri ta kai hannu ta janyota,
hannu suka sa a tare suka d'ibi cake d'in suka
kaiwa Farouq a baki, ba yanda ya iya dole ya
bud'e bakin duk suka saka masa da k'yar ya iya
had'iyewa saboda yanda ya cika masa baki.
Yanda ya ke tauna cake d'in ya bawa kowa
dariya a gurin, ai kuwa mutane mai za su yi in
ba dariya ba, sai da kowa ya yi mai isar shi,
sannan Abbas ya matso daf da su (da yake ya
zo shi da matarsa da yaransa biyu) ya bawa
Farouq hannu ya ce "ina yiwa Twins fatan
rayuwa mai albarka tare da tsawon kwana mai
amfani, kai kuma Allah ya k'ara had'a maka kan
zuri'arka tare da farin ciki mai d'orewa".
"ameeeeeeen"gaba d'aya wurin aka amsa da
shi.
Sannan Abbas ya k'ara damk'e hannu Farouq
ya fara magana cikin zolaya,
"ka ga yayan Fateema mijin Fateema kuma
Baba ga Fateema's... Bai kai ga k'arasa abinda
zai ce ba ya hango Nadeeya sai ya cigaba da
cewa "kuma miji ga Uwargida Nadeeya amma
fa mai retire.....".Gaba d'aya wurin aka hau
dariya tare da tafi raf! raf!! raf!!.
TAMMAT BIHAMDULILLAH
Godiya ta tabbata ga Allah da ya ba ni ikon fara
littafin nan lafiya na kuma gama lafiya, Ya Allah
kurakuran da na yi a ciki a bisa rashin sa ni ko
kuma ajizanci na d'an Adam ya Allah ka yafe
mun.
I dedicated this buk to all my namesakes
(FATEEMA'S)
Bazan ta6a mantawa da ke ba matuk'ar
numfashina yana tare da gangar jikina, beloved
daughter kuma namesake
Fateema Basma Saifullah Allah ya kai rahma
k'abarinki tare da 'yan uwa musulmi, Allah ya
sa ki zama mai ceton iyayenki.
Kin wuce k'awa kin zarce aminiya sai dai na
kiraki da
rabin jiki Fateema Farouq Azzarah, Allah ya bar
k'auna
Namcy dia Teema Cool, you're one of the best
Ku na Raina.....

Comments

Post a Comment