Wankan JANABA

Wankan JANABA
Wankan HAILA
Wankan JUMMU'A
Wankan SHIGA MUSULUMCI


Dukn wadanan Wankan Iri daya
bam-bancinsu shine NIYYAH

Niyar wankan JANABA
( nawaitu Guslul jannabaty Farlun)

Niyar wankan HAILA
( nawaitu Guslul Hailaty Farlun)

Niyar wankan JUMMU'A
(Nawaitu Guslul JUMMU'AT Sunnatun)

YANDA AKE WADANAN wankan..

Ka samu ruwan mai Tsarki, kuma mai tsarkakewa, wanda bai hadu da komai ba,
ka zuwa ruwan cikin Kwanon wanka, ko bocket, ko robar wankanka
ka aje robar wankanka bangaren hannunka na Dama Sunnah ne yin hakan

sai kayi NIYYAH WANKAN DA ZAKAYI
sai kafara debo ruwa da hannunka na Dama ka wanke hannayenka sau uku (3x),

Sai ka fara wanke wajen da jannaba take ( daga cibiyarka/ki zuwa gwuiwarka/ki)

sai kuyi Alwallah zakuyi Niyyah Alwala ( Nawaitu fara'illul wudu'i bismillahi )

sai ku wanke gabobin Alwala sau daya-daya ( 1x )

ama idan kunzo wajen kai ( Head ) sau uku ake wankewa (3x) kamar haka

1.. Tsoma hannunka/ki cikin ruwa zakuyi ki fito dashi ba tare da kun dibo ruwan dashi ba sai ku mu-murza hannayenku a kanki har gaba daya kan ya jike da ruwan... ( Domin sanda Jannaba ke fita jikinka Dukan kafofin gashinka suna budewa kuma jannaba tana fita daga dukan kaffar gashin dake kanmu sanda kake sha-shafe kanka da Damshin ruwan daka jika hannunka dashi yana rufe duk wata kaffar gashin kanka dake bude domin idan ka zuba ruwa da yawa to ruwan zai iya shiga kanka ta kaffofin gashin da suka bude wanda hakan yana haifarda cututtuka sosai Allah yasa za,a kiyaye)

2.. Sai ka debo ruwa da hannunka ka wanke sosai.

3.. Ka sake debowa a na uku ka wanke sosai.

MATA

Idan kunada kitso a kanku idan kun zuba ruwan zaku dinga bubuga hannunku a gashin kanku a hankali har Ruwan su shiga cikin kan sosai

Sai shafar Kunnuwa bayan an wanke kai
sai wanke Kafaffuwa gaba daya
kasa hannunka ka tse-tsefe yatsun kafafuwa sosai idan kanada Faso ( kaushi) shima katabbatar ruwa ya shiga cikinsa sosai duk inda kasan sakone a jikinka ka tabbata ka wankeshi sosai
daga bayan wanke kaffafuwa
ama akwai wasu Mallamai da suka nuna amfison mai wanka ya bari sai ya gama wankansa sannan ya wanke kafaffuwansa ama duk wanda kayi yayi

Sai ka wanke Gefen Jikinka na dama ka wanke sosai ko ina ka zuba ruwa kuma kattabatar ruwan game ko ina na jikinka
sai Gefen jiki na hagu shima kamai yanda kama na baya
sai ku sake zuba ruwa a jiki gaba daya ka cucuda ko ina har jikinka ya hade da ruwa ya hade ko ina
inda ake son mai wanka ya kulla dasu yayin wankansa

1.. Cibiya domin wasu cibiyarsu tanada Lunguna sosai to ka tabbatar ka wanketa ruwa ya shiga ko ina

2.. Matse-matsi lungu da sake tsakanin cinyoyinka ka wankeso sosai

3.. Tafin Kafa da yatsun kafafuwa

4.. Bayanka domin wasu wadanda hannayensu basa iya zagaya bayansu dashi domin gudun kar wani waje bai samu ruwaba zasu iya amfani da Sanda, ko Katako domin wanke ko ina ama kuma Sandar ko katakon kutabattar sunada Tsarki..

5.. Hannunka idan kanada Zobe ka jujjuya zoben sosai har ruwa ya shiga kasan zoben.

Alwalar da kayi Wajen WANKA tana karyewa idan har..

1.. Kayi ( tusa ) yayin wanka ko bayan ka gama wankan ama kuma wankanka nan Awlalarce kawai ta karye

2.. Idan Namiji ya shafi Al'aurarsa ( azakarinsa) da hannunsa bayan ya gama wanka , mace Kuma Idan har ta shigarda yatsanta a cikin Gabanta ( farjinta ) ama don ta shafi samansa Alwalalrta tanan
kuma wannan Alwalar zaku iyayin Sallah da ita, da dukan ayyukan Ibadah

Duk wanda ya mance wani Wajen bai wanke ba wajen Wankan JANNABA to Idan gabbar Alwalace idan yazo Alwallah ya wanke wajen to wankear Alwallah ta isar masa
idan kuma wajen ba wajen Alwala bane to sai ka sake Dibar ruwa kaje Bayi (toilet)

Kayi Niyyar wankan sai ka wanke dai dai wajen daka manta baka wanke ba shikenan

Allah yasa mudace

Idan nayi wani kuskure cikin wannan jawabin Allah ya gaffartamin idan kuma wani yaga kuskurena sai ya gyaramin
nagode ina fatan mutane zasu Amfana da wannan jawabin nawa

Comments